WATAN AZUMI YA KUSANTO
(واقترب رمضان)
'Yan kwanaki kadan suka rage gabanin
shigan watan azumi!
LAMURAN
DA SUKA DACE GA MUSULMI YA KULA DA SU A WATAN SHA'ABAN
DAGA CIKINSU: Akwai biyan bashin
watan azumin da ya shude; Duk wanda akwai ramukon azu,im Ramadanan da ya shude,
sakamakon halin tafiya ko jinya ko haila da makancinsu, to sai yay i gaggawan
biyan wannan bashin gabanin shigowan watan Ramadana, saboda A'ishah –Allah ya
kara yarda a gare ta- ta ce:
(كان يكون علي الصوم من
رمضان، فما أستطيع أن أقضيَه إلا في شعبان).
Ma'ana: "NA KASANCE, AZUMI YA KAN KASANCE A KAINA, NA RAMADANA, SAI NA KASA SAMUN
DAMAN BIYANSA, SAI A WATAN SHA'ABAN".
Kuma
baya halatta a yi bikin daren tsakiyan watan Sha'aban (15), ko kebance wannan
daren da wata ibada ta musamman, Imam An-Nawawiy –Allah ya yi rahama a gare
shi- yake cewa, dangane da sallar RAGA'IB da ake yinta a watan Rajab, da sallar
daren tsakiyan watan Sha'aban raka'oi dari:
((وهاتان الصلاتان بدعتان
منكرتان)).
Ma'ana: "Wadannan salloloin guda
biyu, bidi'oi ne ababen kyama".
Kuma yana daga cikin hadisai raunana
na karya wadanda suka yadu, kan falalar wannnan sallah:
(إذا كانت ليلة النصف من
شعبان فقوموا ليلها وصوموا نهارها) ((السلسلة الضعيفة، برقم: 2132، قال الشيخ
الألباني: ضعيف جدا أو موضوع)).
Ma'ana: "IDAN DAREN RABIN WATAN SHA'ABANA -15- YA ZO, SAI KU KWANA KUNA SALLAR
DAREN, KUMA KU AZUMCI YININSA".
Shekh Albaniy yake cewa (a cikin
littafin AS-SILSILATUS SAHIHAH, 2132): Hadisi ne mai rauni sosai, ko na karya.
Da kuma hadisin da ke cewa:
(خمس ليال لا تُرد فيهن
الدعوة: أول ليلة من رجب، وليلة النصف من شعبان، وليلة الجمعة، وليلة الفطر، وليلة
النحر). ((السلسلة الضعيفة، برقم: 1452، قال الشيخ الألباني: موضوع)).
Ma'ana: "DARARE GUDA BIYAR, BA A KIN AMSA ADDU'A A CIKINSU; DAREN FARKO A WATAN
RAJAB, DA DAREN TSAKIYAN WATAN SHA'ABAN, DA DAREN JUMA'A, DA DAREN SALLAN
AZUMI, DA DAREN SALLAR LAYYAH".
Shekh Albaniy yake cewa (a cikin
littafin AS-SILSILATUS SAHIHAH, 1452): Hadisi ne na karya.
Shekh IbnuBazin –Allah yay i rahama a
gare shi- ya ce:
((كل الأحاديث الواردة
فيها موضوعة وضعيفة لا أصل لها)).
Ma'ana: ((Dukkan hadisan da suka zo
kan wannan dare, na karya ne, da masu rauni, wanda basu da wani asali)).
Sannan
idan karshen watan Sha'aban ya zo, to baya halatta ya azumci rana daya ko biyu
na karshen watan Sha'aban, saidai idan ya dace da yi9nin da mutum ya saba yin
azuminsu, ko kuma idan ya kasance cikin ramukon azumin Ramadana, saboda fadinsa
–عليه الصلاة والسلام-:
((لا تقدموا رمضان بصوم
يوم ولا يومين، إلا رجل كان يصوم صومًا فليصم)). متفق عليه
Ma'ana: "KADA KU RIGAYI WATAN RAMADANA DA AZUMIN YINI DAYA, KO YINI BIYU, SAIDAI
MUTUMIN DA YA KASANCE YAKE YIN WANI AZUMI, TO YA AZUMCE SHI".
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma
babu laifi, a rika yin murna, kan shigowan watan Ramadana; saboda abinda ke
cikin shiga watan na ni'ima da alkhairi.
No comments:
Post a Comment