KA RIBACI WATAN RAMADANA DA YIN AIKI
DA SUNNONINSA
(استثمر رمضان بسُننه)
Idan ka so ka samu LADAN AZUMI gaba
dayansa, kuma ka ji ko ka samu ruhin azumin, to sai ka yi kwadayin aiki da SUNNONIN
AZUMI;
DAGA CIKINSU;
1- YIN SAHUR A
KARSHEN DARE, Koda
kuwa da shan ruwa ne, kwankwada daya, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi
wa sallama- ya ce:
"السَّحور أكلُه
بركة، فلا تدَعُوه، ولو أنْ يجرع أحدُكم جَرعةً من ماء،
فإنّ الله وملائكته يصلّون على المتسحِّرين".
Ma'ana:
"Abincin sahur cinsa albarka ne; kada ku bar
yinsa, koda 'dayanku ya kwankwadi kwankwada guda daya ne na ruwa; saboda Allah
Mabuwayi da daukaka, da Mala'ikunsa suna yin salati ga masu yin sahur",
Ahmad.
2- GAGGAUTA YIN
BUDA-BAKI, DAGA LOKACIN KIRAN SALLAH, DA DABINON DA BA BUSASSHE BA, IDAN KUMA
BAI SAMU BA, TO YA YI DA BUSASSHE, IDAN KUMA BAI SAMU BA, SAI YA YI DA KURBIN
RUWA, kamar yadda
hakan ya zo cikin hadisi.
3- SAI KUMA YA
YI ADDU'A A LOKACIN DA YA YI BUDA-BAKINSA, DA WANNAN ADDU'AR TA ANNABI;
"ذهب الظمأ، وابتلت العروقُ، وثبت الأجر إنْ شاء الله"،
رواه .
Ma'ana: "Kishi ya tafi, jijiyoyi sun jika, kuma ladan ya tabbatu –Insha Allahu-".
4- SHAYAR DA MAI
AZUMI; Domin ya zo
cikin hadisi cewa,
"مَن فطّر صائمًا
كان له مثل أجره، غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيئًا"، رواه .
Ma'ana: "Wanda ya shayar da mai
azumi, to zai samu kwatankwacin ladansa, ba tare da ya tauye komai daga ladan
mai azumin ba".
5- YIN UMRA A
CIKIN WATAN RAMADANA; Saboda Annabi –sallalal Lahu alaihi wa sallama- y ace:
"العمرة في رمضان
تعدل حجة"، رواه .
Ma'ana: "Yin umrah cikin watan Ramadana
tana daidai da yin hajji", Bukhariy da Muslim.
6- YA CIKE
LOKACIN YININSA DA YIN ZIKIRI DA ADDU'A DA KUMA KARATUN ALKUR'ANI, DA KUMA
SAURAN NAU'OIN ABABEN BIYAYYA.
Lallai
watan Ramadana dama ce, na ayyukan karfafa imani, da kuma rabauta da Aljannah,
da tsira daga wuta, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"رغم أنف رجل دخل
رمضان، ثم انسلخ قبل أن يغفر له"، رواه .
Ma'ana: "Mutumin da watan Ramadana ya shigo, sa'annan ya fice, ba a gafarta masa ba,
hancinsa ya bugi turbaya (ya yi hasara ya tabe)".
No comments:
Post a Comment