2018/05/19

ZIKIRIN YARO MUSULMI (أذكار الطفل المسلم)








ZIKIRIN YARO MUSULMI
(أذكار الطفل المسلم)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Abokaina!
Me yafi zikiri (ko ambaton Allah) kyawu! Kuma me yafi tsananin bukatarmu ga zikirin Allah da yawaita shi!!
Saboda zikirin Allah Ta'alah yana da falala mai girma, da fa'idodi masu yawa, domin da zikirin ne, zuciya ke samun natsuwa, kuma ake gafarta zunuban bayi, kuma muke samun lada mai tarin yawa.
Allah Ta'alah ya ce:
"ألا بذكر الله تطمئن القلوب" [الرعد: 28].
Ma'ana: "Lallai da ambaton Allah zukata ke samun natsuwa" [Ra'ad: 28] .

Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"والذاكرين الله كثيرًا والذاكرات أعد الله لهم مغفرة وأجرًا عظيمًا" [الأحزاب: 25].
Ma'ana: "Da masu ambaton Allah dayawa maza, da masu ambatonSa Mata, Allah ya yi tanadin wata gafara, da wani sakamako mai girma a gare su" [Ahzab: 25].

Akwai ZIKIRORI NAU'I-NAU'I, WADANDA SUKA DACE A GARE MU –Ya ku abokaina-, mu kiyaye aiwatar da su, a lokutansu,

DAGA CIKINSU akwai: Zikirin lokacin barci, Sai mu rika cewa:
BISMIKA RABBIY WADA'ATU JANBIY, WA BIKA ARFA'UH, IN AMSAKTA NAFSIY FARHAMHA, WA IN ARSALTAHA FAHFAZHA BIMA TAHFAZU BIHI IBADAKAS SALIHINA.

Da kuma a lokacin TASHI, Nan kuma, zamu rika cewa:
ALHAMDU LILLAHIL LAZIY AHYANA BA'ADA MA AMATANA, WA ILAIHIN NUSHUR.

Haka a yayin FITA DAGA GIDA, Sai mu rika cewa:
BISMILLAH, TAWAKKALTU ALAL LAHI, ALLAHUMMA INNAH NA'UZU BIKA MIN AN NAZILLA AU NUZALLA, AU NAZLIMA, AU NUZLAMA, AU NAJHALA, AU YUJHALA ALAINA.

A lokacin shiga cikin gida kuma, za mu rika cewa:
BISMILLAHI WALAJNA, WA BISMILLAHI KHARAJNA, WA ALAL LAHI; RABBINA TAWAKKALNA.

A lokacin shiga bandakai kuma, za mu rika cewa:
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL KHUBUSI WAL KHABA'ISI.

A lokacin fitanmu kuma daga, Bandakai kuma, za mu rika cewa:
GUFRAANAKA.

A lokacin shiga Masallaci kuma, za mu rika cewa;
ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIKA.

A lokacin fita daga Masallaci kuma. Sai mu rika cewa:
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA MIN FADLIKA.

A lokacin hawa ababen kai-komo, kamar misalin mota kuma, sai mu rika cewa:

BISMILLAHI, ALHAMDU LILLAHI,
SUBHANAL LAZIY SAKKHARA LANA HAZA, WAMA KUNNA LAHU MUKRININA, WA INNA ILA RABBINA LA MUNKALIBUNA.

Haka yin zikiri, bayan kiran sallah; sai mu rika cewa:
ALLAHUMMA RABBA HAZIHID DA'AWATIT TAAMATI, WASSALTIL KA'IMAH, AATI MUHAMMADANIL WASILATA, WAL FADILAH, WAB AS-HU, MAKAMAN MAHMUDAN ALLAZIY WA'ADTAHU.

Wannan kuma kari akan, ZIKIRORIN SAFIYA DA MARAICE.

Kuma mu sani, ya ku abokaina, Lallai idan har muka tabbatu akan wadancan zikirorin, to lallai za mu kasance cikin kulawar Allah da samun kariyarsa; don haka babu wani abu da zai cutar da mu, da izininSa Madaukaki.

YA ALLAH KA TAIMAKE MU, KAN YAWAITA AMBATONKA, DA YIN GODIYA A GARE KA, DA KYAUTATA YIN BAUTA A GARE KA.

Wassalamu alaikum wa rahmatul Lahi wa barakatuhu.


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...