DARUSSA GAME DA AZUMI RAMADHANA
(دروس رمضان)
TANADAR
ABUBAKAR HAMZA MISAU
Matashiya akan azumin Ramadhana
(01)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yabo da godiya sun tabbata ga
Allah madaukakin sarki.
Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da
sahabbansa masu karamci.
Bayan haka,
Abinda zai rika zuwa muku a kullum, hadisai ne kan azumin watan
ramadhana, da kwadaitarwa kan nau'uka, ko dangogin ibadodin da su ke cikin
watan, kamar sallar tarawihi da falalarta, da yawaita karatun Alkur'ani, da
yawaita kyautuka da sadakoki, da falalar yin umrah a cikin watan, da i'itikafi,
da neman lailatul kadari, da zakkar kono (fidri), da idin azumi da
hukunce-hukuncensa, da sauransu.
Da fatan Allah ya azurta mu da ikhlasi cikin zance da aiki, saboda ya zo
cikin hadisin da ke tafe cewa:
عن عُمَر بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه،
قال:
سَمِعْتُ
رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«إِنَّمَا
الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ
هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ،
وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا
فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
أخرجه
البخاريّ [1] ومسلم [1907].
Fassara:
An ruwaito daga Umar dan Alkhaddabi -Allah ya kara yarda a gare shi- ya
ce:
Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:
"Dukkan ayyuka su kan ingantu ne da niyya, kuma lallai kowane
mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda
Allah ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa. Wanda
kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniyar da zai same ta, ko saboda wata
matar da zai aura, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da ya yi hijira dominsa".
Bukhariy [1] ya rawaito shi, da Muslim [1907].
Sai dai kuma
LOKACIN NIYYA A AZUMIN FARILLA; YANA BANBANTA DA NA NAFILA
kamar yadda ya tabbatu a cikin hadisin da ke tafe;
عَنْ
عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ، عَنْ حَفْصَةَ رضي الله عنهما،
عَنِ
النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«مَنْ لَمْ
يُبَيِّتِ الصِّيَامَ قَبْلَ الْفَجْرِ، فَلا صِيَامَ لَه».
أخرجه
الترمذي [733]، والنسائي [4/196]، وابن ماجه [1700]،
وصححه
الألباني في صحيح الترمذي [583].
Fassara:
An ruwaito daga Abdullahi dan Umar, daga Hafsat -Allah ya kara yarda a
gare su-,
daga Annabi -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Duk wanda bai kwana da niyyar azumi gabanin ketowar alfijir
ba to bashi da azumi".
Tirmiziy [733] ya rawaito shi, da Nasa'iy [4/196], da Ibnu-majah [1700].
Kuma Albaniy ya inganta shi, cikin [Sahihut Tirmiziy, 583].
Kuma hadisi, ya zo
عَنْ
عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ:
دَخَلَ
عَلَيَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ فَقَالَ:
«هَلْ
عِنْدَكُمْ شَيْءٌ؟»
فَقُلْنَا:
لا،
قَالَ:
«فَإِنِّي إِذَنْ صَائِمٌ».
ثُمَّ
أَتَانَا يَوْمًا آخَرَ فَقُلْنَا:
يَا
رَسُولَ اللهِ، أُهْدِيَ لَنَا حَيْسٌ فَقَالَ:
«أَرِينِيهِ،
فَلَقَدْ أَصْبَحْتُ صَائِمًا»،
فَأَكَلَ.
أخرجه
مسلم [1154].
Fassara:
An ruwaito daga A'ishah -Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce:
Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya shigo kaina, a wani yini, sai
ya ce:
"Shin, akwai wani abu a wajenku?"
Sai mu ka ce: A'a; babu, Sai ya ce:
"To na dauki azumi!"
Sa'annan sai ya zo wurinmu a wani yinin na daban, Sai mu ka ce:
An kawo mana kyautar Haisa,
Sai ya ce:
"Nuna min shi, Hakika da na wayi gari ina azumi",
Sai, ya ci.
Muslim [1154] ya rawaito shi.
Tsokaci
Wadannan hadisan suna nuna;
(1) Wajabcin niyya, da kasancewar ibada, azumi ko
waninsa, basu zama ingantattu, kuma karbabbu a wurin Allah face da niyya.
(2) Azumin farilla, dole ne a kwana da niyya. Yayin da
azumin nafila, ya halatta mutum ya niyyaci yinsa da rana.
Allah Shi ne mafi sani.
Matashiya kan azumin watan Ramadhana (02)
بمَ
يدخل شهر رمضان؟
1/ عَن ابْن عُمَرَ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ:
سَمِعْتُ
رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
"إِذَا
رَأَيْتُمُوهُ فَصُومُوا، وَإِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَأَفْطِرُوا، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ
فَاقْدُرُوا لَهُ"،
أخرجه
البخاري [1900]، ومسلم [1080].
وفي
رواية عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ:
"فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ".
أخرجه
البخاري [1909]، ومسلم [1081].
SHIGAN
WATAN RAMADHANA YANA TABBATUWA DA GANIN JINJIRIN WATAN, KO CIKAN WATAN SHA'ABAN
30, HAKA KUMA YA KAN FITA DA GANIN JINJIRIN WATAN SHAWWAL, KO CIKAR RAMADHANA
30
An ruwaito daga Abdullahi dan Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya
ce:
Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:
"Idan ku ka ganshi –ma'ana:
jinjirin wata- sai ku yi azumi, Idan kuma kuka gan shi, sai ku ajiye azumi –ku
yi idi-, Idan kuma aka yi muku hazo, sai ku kaddara masa (cikar talatin)".
Bukhariy ya ruwaito shi [1900], da Muslim [1080].
A wata riwaya, daga hadisin Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare
shi-, ya ce:
"Idan aka yi muku hazo, sai ku
cika kirgen Sha'abana kwanaki talatin".
Bukhariy ya ruwaito shi [1909], da Muslim [1081].
2/ وعَنِ ابْنِ عُمَرَ
رضي الله عنهما، قَالَ:
"تَرَائِى
النَّاسُ الْهِلالَ، فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، أَنِّي رَأَيْتُهُ فَصَامَهُ، وَأَمَرَ النَّاسَ بِصِيَامِه".
أخرجه
أبو داود [2342] والحاكم [1/423]، وصححه.
Fassara:
An ruwaito daga Abdullahi dan Umar -Allah ya yarda a gare su- ya ce:
Mutane sun fita dubiyar wata, Sai na bada Manzon Allah -sallal lahu
alaihi wa sallama- labarin cewa, na gan shi, Sai ya azumce shi, kuma ya umarci
Mutane da azumtarsa".
Abu-dawud [2342] ya rawaito shi, da Alhakim [1/423], kuma ya inganta
shi.
Tsokaci
Wadannan hadisan suna nuna;
(1) A Musulunci an gina lamarin azumin Ramadhana ne, a kan
abu na zahiri, wanda kuma shi ne, ganin jinjirin watan Ramadhan, a lokacin da
Sha'abana ya kai yini 29.
Idan kuma ba a ganshi ba, sai a cika kidayar watan kwanaki 30.
(2) Ba dole sai kowa ya ga jinjirin watan da kansa ba,
saboda Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya dau azumi, kuma ya
umarci mutane da su dauka, lokacin da Abdullahi bn Umar, ya ga jinjirin watan.
Don haka, matukar mutumin da ya ganin Musulmi ne, adali, mai gani ba makaho ba,
to shi kenan.
(3) Shugaba shi ke da alhakin umartar mutane, da cewan su
dau azumin.
Su kuma mabiya ana neman su isar masa da labarin ta hanyoyin da su ka
dace.
(4) Yana da kyau a rika fita, dubiyar wata, musamman bayan
gari (inda babu abinda zai shamakance ganin watan).
Allah Shi ne mafi sani.
Matashiya
kan azumin watan Ramadhana (03)
لا
يجوز تقدُّم رمضان بصومٍ للاحتياط
1/ عن أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه،
عَنِ
النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
"لاَ
يَتَقَدَّمَنَّ أَحَدُكُمْ رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ أَوْ يَوْمَيْنِ، إِلاَّ
أَنْ يَكُونَ رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمَهُ فَلْيَصُمْ ذلِكَ الْيَوْم".
أخرجه
البخاري [1914]، ومسلم [1082].
BAI
HALATTA A RIGAYI RAMADHANA DA AZUMTAR YINI BIYU KO DAYA A GABANINSA, DON
TSANTSENI KO NEMAN FITAR DA KAI DAGA SABANI
Fassara:
An ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Kada ku rigayi Ramadana da
azumtar yini daya, ko biyu, sai dai ga mutumin da ya kasance ya ke yin wani
azumi, to ya azumce shi".
Bukhariy [1914] ya rawaito shi, da Muslim [1082].
2/ وعَنْ صِلَةَ بْنِ
زُفَرَ رحمه الله قَالَ:
كُنَّا
عِنْدَ عَمَّارِ بْنِ يَاسِرٍ فِي الْيَوْمِ الَّذِي يُشَكُّ فِيهِ، فَأُتِيَ
بِشَاةٍ مَصْلِيَّةٍ، فَقَالَ: كُلُوا، فَتَنَحَّى بَعْضُ الْقَوْمِ، فَقَالَ:
إِنِّي صَائِمٌ،
فَقَالَ عَمَّارٌ:
«مَنْ صَامَ الْيَوْمَ الَّذِي يَشُكُّ فِيهِ النَّاسُ، فَقَدْ عَصَى
أَبَا الْقَاسِمِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ".
أخرجه
أبو داود [2334]، والترمذي [686]، وقال:
حديث
حسن صحيح.
Fassara:
An ruwaito daga Silatu bn Zufar -Allah ya yi masa rahama-, ya ce:
Mun kasance a wurin sahabi; Ammar bn Yasir -Allah ya kara yarda a gare
shi- a ranar da ake shakku a kansa, sai aka zo masa da akuyar da aka gasa
namanta,
sai Ammar ya ce: ku ci,
sai wani daga cikin mutanen ya matsa can gefe,
Sai Ammar ya ce:
"Wanda ya yi azumin yinin da
mutane ke kokwanto a kansa, to hakika ya saba wa Abul-kasimi -sallal lahu
alaihi wa sallama".
Abu-dawud [2334] ya ruwaito shi, da Tirmiziy [686],
kuma ya ce: hadisi ne hasan ingantacce.
Tsokaci
Wadannan hadisan suna nuna;
(1) Hani kan rigayar watan Ramadhana da azumin yini daya ko
biyu, da nufin idan wannan yinin ya kasance -a hakikanin lamari- daga kwanakin
Ramadhana, to, shi dai ya kubuta, idan kuma baya cikinsu, to hakan ya zame masa
nafila.
Da kasancewar aikata hakan saba wa Manzon Allah ne, sallal lahu alaihi
wa sallama, saboda ya shar'anta mana a tashi da azumi Ramadhana idan aka ga
wata, bayan dubiyar wata, da ganinsa, a lokacin da watan Sha'abana ya ke da
kwanaki 29.
Idan kuma ba a gani ba, to sai ya yi hani kan azumtar yinin da ke biye,
ya kuma umarci halittu da mu cike kidayar Sha'abana kwanaki 30, sa'annan sai mu
tashi da azumin Ramadhana bayan hakan.
(2) Azumi a musulunci an gina shi ne akan abu na sarari,
wato ganin jinjirin wata, ko cike kidayar Sha'abana kwanaki 30.
(3) Wanda ke da sauran azumin kaffara akansa, ya halatta ya
cigaba da yin azumi, koda kuwa a cikin yini daya ko biyu da su ka rigayi
Ramadhana ne.
Haka mutumin da ya saba azumin ranakun litinin da alamis, idan su ka
kasance a ranar shakku (wato, yinin da ya zo bayan 29/Sha'abana, idan ba a ga
watan Ramadhana a daren 29n ba).
Allah Shi ne mafi sani
No comments:
Post a Comment