MASU SACE GARABASAR WATAN AZUMI!
(لصوص رمضان)
A lokacin karantowar watan azumi (Ramadana),
kasuwannin Musulmai suna cika da ababen ci, da na sha, kuma ababen bukatu da
ciyarwa suna ninninkuwa, kuma rigaggeniyar gidajen Talabishon yana karuwa, kuma
mutane dayawa suna neman jadawalin jerin fina-finai da musabakoki. Su kuma masu
bibiyar gidajen Tibi, su kan kara rudewa, su kidime, kan wace tashar Tibi za su
rika bibiya, kuma ga wane jerin finafinai za su yi zabi.
Wadannan
sune mushkiloli, da matsaloli da kisisina da ake kullawa domin cin dunduniyar
watan Ramadana, wadanda za su cire maka azuminka daga ma'anarsa, kuma su hana
ka samu ko tsinkar fa'idodinsa da falalolinsa. Sannan su hana ka samun khushu'i
a cikin sallar tarawihi, da yin tunani cikin tilawar Kur'ani.
Lallai Magabatan
kwarai, idan watan azumi, ya shiga, sun kasance su kan yi watsi da ababen
duniya masu shagaltarwa, da sha'awowin duniya, sai kuma su fiskanci neman gidan
lahira, Sai ka same su "SUNA KASANCEWA, A
LOKACI KADAN NE CIKIN DARE SUKE YIN BARCI * KUMA A LOKATAN SAHUR SUNA ZAMAN
NEMAN GAFARA".
Kuma suna wadatuwa da kadan daga ababen ci da sha.
Kuma a cikin abotakar Alkur'ani suke rayuwa.
Sai ka
kiyaye, Kada shagalin Duniya, da sha'awowi masu kautar da hankula, da barayin
watan azumi, su kautar da kai daga ribatar wannan wata mai karamci.
No comments:
Post a Comment