2019/05/29

رحيل رمضان 26 Ramadhana 1440H daidai da 1 Jun 2019M ta Dr Abdulmuhsin Alkasim











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26/Ramdhana/1440H
daidai da 1/Juniyo/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
Sheikh Dr. Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim


TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
BANKWANA DA WATAN AZUMI (RAMADHANA)
(رحيل رمضان)
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TAFIYAR WATAN AZUMI, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da kuma a bayyane (a lokacin ganawa).

Ya ku Musulmai
Musulmai sun rayu a cikin wannan wata (na Ramadhana) mai albarka, a ciki wani lokaci mai falala, wanda yininsa azumi, darensa kuma salloli, an rayar da Masallatai a cikinsa da ayyukan xa'a, da kuma karatun Alqur'ani, kuma Halittu a cikinsa sun kusanci Allah Mai karamci Mai jin-qai, a lokacin da suke jujjuyawa a cikinsa a tsakanin zikiri da addu'a da bayar kyauta da baiko. Zukata sun samu natsuwa, gavvai kuma sun fiskanto Allah, sai Bayi a cikinsa suka xanxani wani abu na halawar imani da zaqinsa, to amma ga kwanakinsa suna shelanta tafiya, kuma sun yi kusa da qarewa. Don haka; Wanda aka masa dace, shine Mutumin da ya ribaci sauran abinda ya rage daga cikinsa, saboda ayyuka suna zama abin lura ne da abinda aka cike su da shi. Kuma abin dubawan shine kamalar qarshen ayyuka, ba naqasar farko-farkonsu ba.
Kuma duk wanda ya kasance cikin watansa yana mai mayar da al'amari ga Allah, kuma cikin ayyukansa yana mai dace da sunnah, to sai ya qara kyautata gininsu, kuma ya yi godiya wa Allah akan ni'imomi, kuma kada ya kasance kamar wanda ta warware zaren saqarta filla-filla, a bayan ya yi qarfi.
Kuma kiyaye aikin xa'a shine yafi wahalarwa akan aikata ta, kuma yana ciki addu'ar salihai "Ya Allah, muna roqonka aikata aiki na kwarai, da batun kiyaye shi (daga lalacewa)".
Wanda kuma ya zama ta xaya vangaren, to sai ya yi gaggawan tuban gaskiya, saboda qofar tana a buxe yake, Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Hancinsa ya bugi turvaya; Mutumin da watan Ramadhana ya shiga, sa'annan ya fita, gabanin a gafarta masa" Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma ku kasance dangane da al'amarin karvar aiki, kun fi tsananin himmatuwa fiye da aiwatar da shi (aikin), saboda, kawai Allah yana karvar aiki ne daga masu taqawa.
Kuma Mumini yana haxa tsakanin kyautata aiki, da tsoron qin karva, saboda halinsa kamar faxin Allah Ta'alah ne: "Kuma waxanda suke bayar da abinda suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace, domin su masu komawa ne ga Ubangijinsu" [Mu'uminuna: 60].
A'isha -رضي الله عنها- ta ce: "Ya Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- shin sune suke shan giya kuma suke sata? Sai ya ce: Ya 'yar gidan Siddiqu! A'a, sune suke yin azumi, kuma suke yin sallah suke yin sadaka, amma suke tsoron kada ya zamto ba a karva musu ba, (Waxannan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri, alhali kuwa suna masu rigaye a cikinsu)" [Muminuna: 61]. Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma koda watan azumi ya shuxe, to lallai aiki baya yankewa, sai idan an mutu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr: 99].
Kuma aiki dawwamamme kaxan, shine yafi alheri akan mai yawa, mai yankewa, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Aikin da yafi soyuwa a wurin Allah, shine wanda aka fi dawwama akansa, koda kaxan ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma yana daga alamar karvar aikin kwarai, yin wani aikin na kwarai a bayansa.
Kuma yana da kyau a aikata kyakkyawa a bayan mummuna; domin ya kankare shi.
Abinda kuma yafi kyau shine aikata mai kyau da biyar da shi bayan wani mai kyan!
Kuma yana daga falalar Allah da karramawarSa: Yadda ayyukan watan azumi suka kasance masu dawwama a tsawon kwanakin shekara, misalin tilawar Alqur'ani da sadaka da azumi, da umrah da addu'a da sallolin dare, da wasun waxannan daga cikin abinda Allah ya shar'anta aiwatar da su a tsawon rayuwa.
Kuma cikin dawwamar aikin xa'a da tsawaitar zamaninsa akwai ni'ima mai girma ga salihan Mutane, da sanyi ido ga Muminai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai waxanda suka ce: Ubangijinmu shine Allah, sa'annan suka daidaitu, Mala'iku suna sauka akansu (a lokacin mutuwa, suna ce musu:) Kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ku yi bushara da Aljannah, wanda ta kasance ake muku alqawali" [Fussilat: 30].
Kuma a qarshen Ramadhana akwai albishir ga Ma'abuta azumi da sallah, "Wanda ya yi azumin Ramadhana cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa, Kuma wanda ya yi tsayuwar lailatul qadari cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa" Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma "Wanda ya yi qiyamul laili na dararen Ramadhana an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
"Kuma mai azumi yana da farin ciki nau'i biyu da yake yinsu; na farko a lokacin buxa-bakinsa, da kuma wani farin cikin a lokacin haxuwa da UbangijinSa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai...
Rayuwa numfashi ne kidayayyu, kuma ajali ne iyakantacce, kuma dukkan rayuwar da ake qididdige ta da numfashi to mai saurin qarewa ce.
Kuma cikin qarewar Ramadhana akwai darasi dangane da qarewar Duniya da abinda yake cikinta, Kuma kamar ga ku, alhalin ayyuka sun qare, Duniya kuma ta shuxe, a lokacin kowane Bawa jingine yake da abinda ya aikata, kuma wanda zai samu rabo shine wanda ya amsa wa mai kiran Ubangijinsa, kuma ya kasance daga cikin masu kyautatawa (muhsinai).
A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM: "Wanda ya aikata aiki na kwarai, daga namiji ko kuwa mace, alhali yana Mumini, to haqiqa zamu rayar da shi rayuwa mai daxi, kuma haqiqa zamu saka musu ladansu da mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahl: 97].

Allah ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa, kuma godiya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; ina mai girmama sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai ninkuwa.

Bayan haka
Allah ya kevance wannan wata (na Ramadhana)da zakkar fid-da-kai, a lokacin qarewarsa, domin ta zama tsarkaka ga masu azumi, kuma abinci ga miskinai.
Gwargwadonta shine: Sa'i xaya, daga galibin abincin Mutanen wannan garin.
Kuma Mutum zai fitar da ita wa kansa da iyalansa.
Kuma lokacin fitar da ita na mustahabbi shine, daga gabanin sallar idi, amma ya halatta a fitar da ita gabanin haka da yini xaya ko biyu.
Kuma a qarshen Ramadhana, sunna ce mai qarfi a riqa kabbara, daga faxuwar ranar yinin qarshe, har zuwa lokacin sallar idi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah akan yadda ya shiryar da ku, kuma tsammaninku za ku gode" [Baqara : 185].
Kuma wanda ya yi azumin Ramadhana, sai ya biyar da shida a bayansa daga watan Shawwal, to kamar ya azumci kwanakin shekara ne gaba xayansu.
Sannan ku sani, Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa, a inda yake cewa: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].

2019/05/24

Tsakurowa daga huɗubar Juma'a, ta Masallacin Annabi SAW 19 Ramadhana 1440H


Tsakurowa daga huɗubar Juma'a, ta Masallacin Annabi SAW

1- Kuma lallai kala-kalan ibadodin da aka shar'anta, a cikin jerin manufofin samar da su kaso na biyu, da hikimominsu mabanbanta, suna xauke da abinda yake sanya Musulmi yin ado (qawa) da halaye masu girma, da kuma sifantuwa da sifofi maxaukaka, domin al'umma gaba xayanta; rayuwarsu ta tsayu a cikin tsari, qarqashin jeringiyar halayya managarta, da xabi'u masu kyau, waxanda za su  sanya al'ummar ta kasance al'umma mai walwala da jin daxi, wanda falaloli da dukkan nau'ukansu za su riqa yaxuwa a cikinta, haka xabi'un kirki masu yawa mabanbanta da dukkan kalolinsu.

2- A cikin azumin watan Ramadhana, akwai tarbiyyantar da Halittu akan nisantar munanan halaye masu yawa, da kautar da rayuka daga nisantar xabi'un banza, Annabi -صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar zancen zur da aiki da shi ba, ,,, to, lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa", Bukhariy ya ruwaito shi.

                3- A watan Ramadhana a cikinsa, akwai tarbiyyantar da Musulmi akan xabi'ar tausayi (rahama), da dukkan kalolinsa da nau'ukansa. Kuma yana daga abinda zai bayyanar da hakan, abinda ya zo, na falalar yin sadaka a cikin wannan watan, da falalar shayar da mai azumi, da ciyar da mai jin yunwa, da toshe matsalolin mabuqata. Kuma da aikata hakan, Musulmi zai tuna cewa, lallai sifar tausayi (rahama), da ma'anoninta masu faxi da gamewa, masu kyau, sifa ce, da ya wajaba Musulmi ya riqa sifantuwa da ita, a cikin dukkan zamaninsa (na azumi da gabaninsa da bayansa), da gaba xayan mu'amalolinsa.

                4- Lallai Ramadhana lokaci ne na haxuwar Mutane da cunkoso, a yayin sallolin farillai da kuma tsayuwan dare, da kuma lokacin haxuwar Mutane domin buxa-baki, da wajen ibadar i'itikafi, da yayin ibadar umrah, don haka, abinda yake wajibi shine a irin waxannan wuraren ayi matsanancin kwaxayin riqo, kuma ana bayyana mafi kyan sifofin tausayi, rahama, da natsuwa, tare da bayyanar da sauran mu'amaloli masu kyau, da ayyuka kyawawa waxanda za su riqa nuna girman wannan addinin namu  (na Musulunci).

                5- Ya ku Limamai: Ku riqa tuna sifar tausayi, har a cikin sallolinku na dare, da tahajjudin da kuke yi da Mutane, a lokacin qiyamu Ramadhana, tare da kwaxayin riqo ko aiki da sunnah, gwargwadon ikonku, kuma ku nisanci tsawaitawa a cikin addu'ar alqunuti, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan xayanku ya yi sallah tare da Mutane, to ya sassauta, saboda a cikin Mutane akwai mai rauni da maras lafiya da mabuqaci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

6- Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana qoqari a cikin goman qarshen Ramadhana, qoqarin da baya irinsa a wasu kwanakin ba su ba, Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da sahihu Muslim, daga hadisin A'isha -رضي الله عنها- ta ce: Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- "Ya kasance -idan goman nan (na qarshe) suka shigo- ya kan raya darensa, ya riqa tayar da iyalansa, kuma ya tamke kwarjallensa".

Huɗubar juma'a a taƙaice 19 Ramadhana 1440H


Huɗubar juma'a a taƙaice
RAMADHANA WATAN TAUSAYI DA RAHAMA NE
1/ Lallai jiga-jigan DABI'U DA HALAYE MASU KARAMCI, a addinin Musulunci suna da matsayi mai girma da sha'ani cikakke, saboda nassoshin shari'a mutawatirai sun zo suna kwadaitarwa akan kyawawan halaye, da xabi'u na kwarai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai kai, haqiqa kana kan xabi'un kirki masu girma" [Qalam: 4].

2/ Watan Ramadhana, a cikinsa an shar'anta ibadodi da ayyukan kusancin da suke tsaftace zukata, kuma suke tsarkake su, sannan su tsaftace gavvai, sai su gyara su, ta yadda Musulmai gaba xayansu za su fa'idantu da samun tarbiyyar da zata jagorance su ga bin mafi alherin hanyoyi, suna masu aiki da mafi kyan halaye.

                3/ Jabir xan Abdullahi -رضي الله عنه- ya ce: "Idan kana azumi, to, lallai jinka, da ganinka, da harshenka, su yi azumi daga qarya da savo, kuma ka bar cutar da hadiminka. Sa'annan ka sifantu da shiru da natsuwa a ranar azuminka".

                4/ Xabi'ar Tausayawa halittu, sifa ce mai daraja, kuma manufa ce mai girma daga cikin manufofin tarbiyya, a cikin dukkan ibadodi, saboda Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].

                5/ Kuma duk lokacin da waxannan jeringiyar sifofi masu kyau suka vuya daga rayuwar Musulmi, (aka rasa su) a cikin mu'amalolinsa da alaqoqinsa, to sai ya faxa cikin tavewa da asara, Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba a cire xabi'ar tausayi sai daga shaqiyyi".

2019/05/23

19 Ramadhana 1440 Husain Alus Sheikh الرحمة بالناس في رمضان











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 19/RAMADAHANA/1440H
daidai da 24/MAYU/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUS-SHAIKH



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
RAMADHANA WATAN TAUSAYI DA RAHAMA NE
(رمضان شهر الرحمة)
Shehin Malami wato: Husain xan Abdul'aziz Alus-Sheikh–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TASIRIN AZUMI AKAN HALAYEN MUTANE,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Lallai jiga-jigan DABI'U DA HALAYE MASU KARAMCI, a Musulunci suna da matsayi masu girma da sha'ani cikakke, saboda nassoshin shari'a mutawatirai sun zo suna kwadaitarwa akan kyawawan halaye, da xabi'u na kwarai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai kai, haqiqa kana kan xabi'un kirki masu girma" [Qalam: 4].
Kuma lallai kala-kalan ibadodin da aka shar'anta, a cikin jerin manufofin samar da su kaso na biyu, da hikimominsu mabanbanta, suna xauke da abinda yake sanya Musulmi yin ado (qawa) da halaye masu girma, da kuma sifantuwa da sifofi maxaukaka, domin al'umma gaba xayanta; rayuwarsu ta tsayu a cikin tsari, qarqashin jeringiyar halayya managarta, da xabi'u masu kyau, waxanda za su  sanya al'ummar ta kasance al'umma mai walwala da jin daxi, wanda falaloli da dukkan nau'ukansu za su riqa yaxuwa a cikinta, haka xabi'un kirki masu yawa mabanbanta da dukkan kalolinsu.
'Yan uwa Musulmai
Watan Ramadhana, a cikinsa an shar'anta ibadodi da ayyukan kusancin da suke tsaftace zukata, kuma suke tsarkake su, sannan su tsaftace gavvai, su gyara su, ta yadda Musulmai gaba xayansu za su fa'idantu da samun tarbiyyar da zata jagorance su ga bin mafi alherin hanyoyi, suna masu aiki da mafi kyan halaye.
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas -رضي الله عنهما- ya ce: "Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya kasance, yafi dukkan Mutane kyauta, kuma ya kasance yafi yawaita kyautarsa a cikin watan Ramadhana, a lokacin da mala'ika Jibrilu yake haxuwa da shi, kuma ya kasance yana haxuwa da shi a cikin kowane dare na Ramadhana, sai ya yi bitar Alqur'ani da shi. Kuma Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم - yafi iska sakakkiya yawan kyautar alheri", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kalmar "judu; kyauta" a cikin hadisin, ta qunshi dukkan kyawawan xabi'u da halayya masu falala.
'Yan'uwa Musulmai
A cikin azumin watan Ramadhana, akwai tarbiyyantar da Halittu akan nisantar munanan halaye masu yawa, da kautar da rayuka daga nisantar xabi'un banza, Annabi -صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar zancen zur da aiki da shi ba, ,,, to, lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Wannan ya sanya, Jabir xan Abdullahi -رضي الله عنه- yake cewa: "Idan kana azumi, to, lallai jinka, da ganinka, da harshenka, su yi azumi daga qarya da savo, kuma ka bar cutar da hadiminka. Sa'annan ka sifantu da shiru da natsuwa a ranar azuminka".
Muradin -a nan- shine, istiqama da tabbatuwa akan waxannan halayyen, da yin tafiya ko-yaushe akan waxannan xabi'un.
Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan ranar azumin xayanku ta kasance, to kada ya yi kwarkwasa a wannan ranar, kuma kada ya yi shewa, kuma idan wani ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi, to ya ce, lallai ni Mutum ne mai azumi".
A watan Ramadhana a cikinsa , akwai tarbiyyantar da Musulmi akan xabi'ar tausayi (rahama), da dukkan kalolinsa da nau'ukansa. Kuma yana daga abinda zai bayyanar da hakan, abinda ya zo, na falalar yin sadaka a cikin wannan watan, da falalar shayar da mai azumi, da ciyar da mai jin yunwa, da toshe matsalolin mabuqata. Kuma da aikata hakan, Musulmi zai tuna cewa, lallai sifar tausayi (rahama), da ma'anoninta masu faxi da gamewa, masu kyau, sifa ce, da ya wajaba Musulmi ya riqa sifantuwa da ita, a cikin dukkan zamaninsa (na azumi da gabaninsa da bayansa), da gaba xayan mu'amalolinsa, saboda faxin Allah Ta'alah: "Sa'annan ya kasance daga waxanda suka yi imani, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haquri, kuma suka yi wa juna wasiyya da tausayi" [Balad: 17].
Da kuma saboda faxin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Misalin Muminai cikin, tausayawarsu ga juna, da qaunarsu, da tausasawarsu, kamar jiki ne guda xaya, idan wata gaba a cikinsa ta yi ciyo, sai sauran jikin su taya ta kururuwa, da rashin barci da kuma jin raxaxi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma dangane da wannan sifar Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Masu tausayawa, Mai rahama (Allah) yana tausaya musu, ku ji tausayin halittun qasa, sai wanda yake sama ya ji tausayinku".
Don haka, Xabi'ar Tausayawa halittu, sifa ce mai daraja, kuma manufa ce mai girma daga cikin manufofin tarbiyya, a cikin dukkan ibadodi, saboda Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma bamu turo ka ba, face jin-qai ga talikai" [Anbiya'i: 107].
Kuma Allah Ta'alah yake faxa a inda yake sifanta Annabinsa -صلى الله عليه وسلم-: "Kuma ga muminai mai tausayi ne mai jin-qai" [Taubah: 128].
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah -رضي الله عنه- ya ce: "An ce, Ya Manzon Allah, ka yi addu'ar halaka ga mushirkai? Sai ya ce, lallai ba a turo ni domin la'anta ba, lallai an turo ni domin na zama rahama", Muslim ya ruwaito shi.

Ya ku taron Musulmai
Lallai Ramadhana lokaci ne na haxuwar Mutane da cunkoso, a yayin sallolin farillai da kuma tsayuwan dare, da kuma lokacin haxuwar Mutane domin buxa-baki, da wajen ibadar i'itikafi, da yayin ibadar umrah, don haka, abinda yake wajibi shine a irin waxannan wuraren ayi matsanancin kwaxayin riqo, kuma ana bayyana mafi kyan sifofin tausayi, rahama, da natsuwa, tare da bayyanar da sauran dangogin mu'amaloli masu kyau, da ayyuka kyawawa wanda za su riqa nuna girman wannan addini (na Musulunci).
Wannan ya sanya Annabi ya tsawatar ga Muminai; da cewar kada mu'amalolinsu su wofinta daga  wannan sifa mai kyau; da kuma xabi'a mai girma (ta rahama), a inda yake cewa:  "Allah baya tausaya ma wanda baya tausayin Mutane" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma duk lokacin da waxannan jeringiyar sifofi masu kyau suka vuya daga rayuwar Musulmi, (aka rasa su) a cikin mu'amalolinsa da alaqoqinsa, to sai ya faxa cikin tavewa da asara, Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba a cire xabi'ar tausayi sai daga shaqiyyi", Tirmiziy ya ruwaito, kuma ya ce: hadisi ne hasan, kuma Hafizan Maluma sun ce, hadisi ne hasan.
Sai a yi tausayin qaramin yaro, muna masu girmama babban Mutum, kuma mu taimaki mai rauni, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Baya cikinmu; wanda baya tausayin qaraminmu, kuma bai san girman babbanmu ba", Ahmad ya ruwaito shi da Tirmiziy, kuma ya ce, hadisi ne mai kyau ingantacce.

Ya ku Limamai: Ku riqa tuna sifar tausayi, har a cikin sallolinku na dare, da tahajjudin da kuke yi da Mutane, a lokacin qiyamu Ramadhana, tare da kwaxayin riqo ko aiki da sunnah, gwargwadon ikonku, kuma ku nisanci tsawaitawa a cikin addu'ar alqunuti, saboda Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Idan xayanku ya yi sallah tare da Mutane, to ya sassauta, saboda a cikin Mutane akwai mai rauni da maras lafiya da mabuqaci", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
kuma lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai nakan tsayu a cikin sallah, ina son tsawaita ta, sai na ji kukan qaramin yaro, sai in taqaita sallata, tsoron kada in takura wa Mahaifiyarsa", Bukariy da Muslim suka ruwaito shi.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana qoqari a cikin goman qarshen Ramadhana, qoqarin da baya irinsa a wasu kwanakin ba su ba, Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da sahihu Muslim, daga hadisin A'isha -رضي الله عنها- ta ce: Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- "Ya kasance -idan goman nan (na qarshe) suka shigo- ya kan raya darensa, ya riqa tayar da iyalansa, kuma ya tamke kwarjallensa".
Sai ku raya dararen -Allah ya muku rahama- da ayyukan alkhairori, kuma ku yi gaggawa zuwa ga kyawawan ayyuka, domin ku samu yardar Ubangijin sammai da qasa.


2019/05/10

5 Ramadan 1440h, daidai 10Mayu 2019M, Dr Huzaifiy kan YI MA KAI HISABI WAJEN KWAZON IBADODI











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/Ramadhana /1440H
daidai da 10/Mayu/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
NI'IMAR ALQUR'ANI DA IMANI
(نعمة القرآن والإيمان)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YI WA KAI HISABI A WATAN RAMADHANA,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo na Allah ne; Ubangijin kasa da sammai, Ma'abucin ni'imomi da albarkoki,
Ayyukan xa'a basu amfanar da shi, kuma munana basu cutar da shi, kawai suna amfanar ko su cutar da wanda ya aikata su ne, saboda Allah Wadatacce ne; baya buqatar halittu,
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda muke sani, da waxanda bamu sani ba, saboda yabo da godiya nasa ne a cikin dukkan halaye
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake, bashi da abokin tarayya, Yana da sunaye mafiya kyau, da mafi girman sifofi.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, wanda aka qarfafe shi da hujjoji da kuma mu'ujizozi.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da IyalanSa da SahabbanSa masu gaggawar aikata alkhairori.

Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah Mabuwayi da xaukaka ta hanyar ayyukan da suke yardar da shi, da nisantar fushinSa da savonSa, saboda babu mai samun rabo sai masu taqawa. Kuma babu mai yin hasara face mujirimai.

Ya ku musulmai …
Yin hisabi ga Rai, da qoqarin yin ayyukan xa'a, da neman qara kyawawan ayyuka, da kiyaye abinda Allah ya taimaki bawanSa ya masa taufiqin dace; na daga ayyuka nagari, da nisantar lamurran da suke vata ayyukan xa'oi = sune haqiqanin samun rabo da tsira a cikin wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwa; Allah Ta'alah ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwar gaban UbangijinSa, sai ya kange ransa daga son Rai * to lallai Aljannah ita ce makoma" [Nazi'at: 40-41].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce dangane da ma'abuta Aljanna: "Sai sashensu ya fiskanci sashe suna tambayar juna * suka ce: Lallai mu, mun kasance a gabanin wannan (a Duniya), a cikin iyalanmu munan jin tsoro * Sai Allah ya yi mana kyautar falala, kuma ya tsare mu daga azabar iskar zafi" [Xur: 25-27].
Kuma Allah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani ku yi xa'a ga Allah, kuma ku yi xa'a ga ManzonSa, kuma kada ku vata ayyukanku" [Muhammadu: 33].
Ibnu-kasir –Allah ya yi masa rahama- yake faxa dangane da tafsirin faxin Allah Ta'alah: "Kuma Rai ta yi dubi kan abinda ta aikata domin gobe" [Hashr: 18], Ma'ana: Ku yi hisabi ga rayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku yi dubi kan abinda kuka yi tanadi ga kayukanku na kyawawan ayyuka, domin ranar da za a dawo da ku, kuma a bijiro da ku ga Ubangijinku. maganarsa ta kare.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa, sannan ya yi aiki domin abinda zai kasance a bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya biye wa son zuciyarsa; sai yake ta kwallafa buri ga Allah". Hadisi ne hasan.
Yi ma kai hisabi, yana kasancewa cikin abinda ya gabata,  da kuma cikin yininka, da lokacin da kake fiskanta, ta hanyar tuba daga dukkan zunubai, da kiyaye kyawawan ayyuka daga abubuwan da suke lalata su, da qoqarin qara ayyukan alkhairi. 

Kamar yadda TAVEWA DA HASARAR RAYUWA YAKE CIKIN BIN SOYE-SOYEN ZUCIYA, DA AIKATA HARAMUN, DA BARIN AYYUKAN XA'A, KO AUKAWA CIKIN ABABEN DA SUKE RUGUZA KYAWAWAN AYYUKA, kuma lallai, ya ishi Mutum sharri, ya riqa aikata abunda zai tauye masa ladansa!

Ya ku Musulmai…
Lallai kuna ganin saurin tafiyar darare da yini, da yadda shekaru suke ta wucewa, Kuma lallai duk yinin da ya shuxe, to lallai ya tafi da abinda aka yi a cikinsa; ba zai dawo ba.
Kuma rayuwa gaba xayanta ba komai ba ce, face wasu darare da yini, sai ajalin Bawa ya sauka a gare shi, aikinsa ya yanke, sai kuma Mutum ya samu yaqini kan yadda guri ya rude shi.

Bayan haka
Kuma lallai ku, a farko-farkon watanku (na Ramadhana) mai albarka, haqiqa Allah a cikinsa ya buxe muku qofofin alheri, kuma ya sauqe muku sabubba, sai ku shiga qofofin alkhairi, kuma ku kiyayi shiga qofofin halaka, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani, ku shiga cikin Musulunci gaba xaya, kuma kada ku bi hanyoyin Shexan, lallai shi a gare ku maqiyi ne mabayyani" [Baqara: 208].

Ya ku Musulmai!!!

Ku girmama ni'imar imani da ni'imar Alkur'ani, saboda ba a tava baiwa wani kyauta wanda tafi imani da Alqur'ani fala ba.
Kuma Musulmi ba zai yi azumin ramadhana cikin imani da neman lada ba, face ya samu wani abu na imani, kuma ya samu albarkar Alqur'ani.
Kuma ahalin Alqur'ani sune masu aiki da shi, koda basu hardace shi ba. Wanda kuma bai yi aiki da Alqur'ani ba, to baya cikin ahalin Alqur'ani, koda ya hardace shi.
Kuma farkon ni'ima ga wannan Al'ummar ta hanyar shiryar da ita, da rahama gamammiya da kevantacciya, da samun rayuwa mai karamci ya kasance da saukar Alqur'ani ne, a cikin watan Ramadhana; saboda saukar Alqur'ani  a cikin watan azumi shine mafarin alkhairai, da albarkoki, da gyaran rayuwa, da samun rabo a Lahira da maxaukakin darajoji, kuma shine mafarin haske mai yaye duffai, mai xauke jahilci da vata, Allah Ta'alah ya ce: "Kamar haka, muka yi maka wahayin ruhi daga al'amarinmu, baka kasance ka san menene littafi da imani ba, saidai mu mun sanya shi haske muna shiryar da wanda muke so daga cikin Bayinmu, kuma lallai kai kana shiryarwa izuwa ga hanya madaidaiciya" [Shura: ].
Kuma Allah ya ce: Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku Mutane, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, kuma lallai mun sauqar muku da haske mabayyani * Amma waxanda suka yi imani da Allah, kuma suka yi riqo da shi, to lallai zai shigar da su cikin wata rahama daga gare shi da falala, kuma ya shiryar da su zuwa gare shi, hanya madaidaiciya" [Nisa'i:].
Don haka, Wanda ya yi imani da Alqur'ani mai karamci daga na farkon wannan Al'ummar, ko kuma wanda ya yi imani da Alqur'ani, bayan haka, har zuwa qarshen Duniya, to haqiqa ya yi godiyar ni'imar Alqur'ani gamammiya cikakkiya, kuma ya gode wa ni'imar imani cikin abinda ya kevance shi.
wanda kuma bai yi imani da Alqur'ani ba, to haqiqa ya kafirce wa ni'imomi gaba xayansu, kuma lallai zai dawwama a cikin wuta, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya kafirce da shi daga cikin qungiyoyi, to lallai wuta ce makomarsa" [].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya kafirta da shi, to waxannan sune asararru" [].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai waxanda suka qaryata ayoyina, kuma suka yi girman kai da barinsu, ba za a bubbuxe musu qofofin sama ba, kuma ba su shiga Aljannah sai raqumi ya shiga ta kafar allura, kuma kamar haka ne muke saka wa masu laifi * suna da wata shumfuxa daga Jahannama, kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne muke saka wa azzalumai" [A'araf: 40-41].
Yana daga cikin rahamar Allah a gare mu, da hikimarsa, da gamewar iliminsa, yadda ya farlanta mana azumtar watan Ramadhana mai albarka, sai Manzon Allah kuma -صلى الله عليه وسلم- ya sunnata mana tsayuwar dare a cikinsa, kuma ya kevance shi da wasu falaloli, koma bayan waninsa, Sai mafi girman ibadodi suka haxu a cikin watan, da nau'ukan ayyukan biyayya, sai Allah ya ninninka ladan ayyuka a cikinsa, domin Musulmi ya tsayu wajen godiya kan ni'imar Alqur'ani da ni'imar Imani, saboda ni'imomi wajibi ne a yi godiya ga mai bayar da ni'imomin Mabuwayi da xaukaka, domin ya kiyaye su daga gushewa, kuma domin ya qara wasu ni'imomin a nan, da kuma makoma.

Kuma godiya wa Allah akan ni'imominsa yana kasancewa da nau'oin ibadodi, kuma mafi girmansu shine Tauhidi (kaxaita Allah). Kuma yana kasancewa ta hanyar kyautatawa ga halittunsa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne mu, mun yi maka kyauta mai yawa * sai ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka soke raqumi" [kausar: 1-2]. Kuma abinda ake nufi da kalmar "kausar" shine alheri mai tarin yawa wanda ba mai kewaye da iliminsa in ba Allah ba, yana kuma daga cikinsa, tafkin alkausara, wanda yake cikin Aljannah.
Sai Allah –a nan- ya shiryar da Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- zuwa godiya ga ni'imominsa, da nau'ukan ibadodi, da kuma al'amarin kyautata wa halittunsa da nau'ukan kyautatawa da amfani.
Kuma haqiqa shugabanmu annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- ya baiwa waxannan matakan haqqinsu, kuma ya bi umurnin Ubangijinsa cikakken bi, da fatan Allah ya yi sakayya wa Annabinmu Muhammadu -صلى الله عليه وسلم- akanmu da mafi alherin abinda ya sakayya ga wani annabi akan al'ummarsa, saboda ya isar da manzanci, kuma ya sauke amanar Allah, ya yi nasiha ga al'umma.

Kuma Allah Ta'alah yake faxa dangane da annabi Musa –عليه الصلاة والسلام-: "Ka yi riko da abinda na baka, kuma ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ku aikata godiya –Ya ku diyan dawuda-, kuma kadan ne mai godiya daga cikin bayina" [Saba'i: 13].
Wasu daga cikin Maluman tafsiri suke cewa: Babu wata sa'a da ta shuxe cikin dare ko yini, face wasu daga iyalan annabi Dawud suna cikin ruku'i ko sujjada.
Kuma a lokacin da Allah ya ambaci ni'imominSa ga Maryama –عليها السلام- sai ya umurce ta da yin godiya, a inda ya ce: "Ya Maryamu! Ki Qanqan-da-kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujjada, kuma ki yi ruku'i tare da masu ruku'i" [Ali-imrana: 43].
Kuma Allah Ta'alah yake faxa dangane da sahabbai –Allah ya qara yarda a gare su-: "Kana ganinsu suna masu ruku'i, masu sujjada, suna neman falala daga Allah, da yardarSa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu na guraben sujjada" [Fat-h: 29].
Don haka, yin ibadodi a cikin watan Ramadhana da waninsa suna daga godiyar Allah akan ni'imar imani da ni'imar sauqe Alkur'ani.

Kuma Alqur'ani yana da qarfin tasiri ga ruhi, a cikin watan Ramadhana, saboda raunin masu fizga zuwa ga sharri, da qarfin sifofin alkhairi, a sakamakon azumi, da raunin qarfa-qarfar Shexan.
Sai ku yawaita tilawarsa da nazari cikinsa.
Kuma halin Musulmai ba zai gyaru ba, sai da Alqur'ani da sunnah.
Kuma da masu hikimar Duniya za su haxu gaba xayansu, daga farkonsu har na karshensu, da rayayyunsu da matattunsu, domin warware matsala xaya daga cikin matsalolin Duniya, to lallai da ba za su shiryu zuwa ga hakan ba, Saidai Alkur'ani ya bayyana  gaskiya cikin kowace mushkila.

Dubi MAS'ALAR AQIDAR HALITTU KAN ALLAH TA'ALAH DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA DA AYYUKANSA, DA HAQQINSA NA A MASA BAUTA, akidu nawa ne akan wannan mas'alar? Ba za su iya kididdiguwa ko kirguwa ba?
Kuma gaskiya a cikin mas'alar aqida shine abinda Alkur'ani ya faxa.

Kuma matsalar TATTALIN ARZIKI a Duniya itama ta gagari masu hikima, kuma gaskiya a cikinta shine abinda Al-qur'ani mai karamci ya faxa akanta.

Wasu masu hikima daga cikin waxanda ba Musulmai ba, sun amfana da shari'ar Musulunci a cikin wasu mas'alolin.

Kuma ba zai yiwu Mutane gaba xayansu su kasance Musulmai ba. Saidai kuma wajibi ne akan Musulmai su yi riqo da Alkur'ani da sunnah, har idan sauran Mutane suka ga abin koyi mai kyau, daga kowane Musulmi, sai su amfana da su, koda kuwa cikin al'amuransu na Duniya ne.
Kuma Alqur'ani mai girma shine garkuwa ga Al'umma, da qarfinta, da dalilin wanzuwarta da buwayarta, Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai ne wannan Alkur'anin yana shiryarwa ga hanyar da tafi miqewa, kuma yana yin albishir ga Muminai waxanda suke aikata ayyuka kwarai, cewa: Lallai suna da lada mai girma" [Isra'i:9].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Mai qagar halitta, kuma ya mayar da ita (bayan mutuwa)Mai aikata abinda yake nufi, Mulki na Ubangijina ne, kuma godiya tasa ce, yana hukunta abinda yake so.
            Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan falalarSa, kuma muna roqonsa qari.
            Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Majivinci abin godiya.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa shiryaryayyu.
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah a cikin kowane hali; domin ku rabauta da samun kykkyawar aqiba a cikin al'amurranku gaba xaya, a Duniya da Lahira.

Ya ku Bayin Allah
Lallai farillar azumi, a cikinta kuna da mafi girman lada, tare da abinda ke cikinta na amfani a wannan rayuwar, ga wanda ya yi tunanin hakan, da tunani mai haske.
Saidai kuma azumi ba zai bayar da fa'idarsa ba, kuma ma'abucinsa ba zai amfana da shi ba, sai idan ya tsarkake shi da kyawawan ayyuka, kuma ya kiyaye shi daga abubuwan da suke vata shi, da kuma abubuwan da suke tauye ladansa, na daga zununbai da savo.
Don haka, Idan ka yi azumi -Ya kai Musulmi- to jinka ya yi azumi, da ganinka, da harshenka da sauran gavvai, daga dukkan haram; domin ranka ta tsarkaka da aikata xa'oi, Allah Ta'alah ya ce: "Ya waxanda suka yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi biyayya wa Manzo, kuma kada ku vata ayyukanku" [Muhammadu: 33].
Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Idan ranar azumin xayanku ya kasance, to kada ya yi kwarkwasa, kuma kada ya yi fasikci, Idan wani Mutum ya zage shi, ko nemi faxa da shi, sai ya ce: Lallai ne, mai azumi ne".
Kuma Annabi -SAW- ya ce: "Azumi garkuwa ne, matuqar bai keta ta ba", wato makuqar bai keta shi da zunubai kamar giba da annamimanci ba.
Kuma ka yi hisabi ga kanka -Ya kai Musulmi- a cikin watan azumi, domin hisabin ya yi sauqi akanka a qiyama,
Kuma ka tambayi kanka, shin ka tsayar da sallah kamar yadda umurce ka?
Shin ka bada zakkarka tare da azumi?
Shin ka tuba zuwa ga Allah daga zunubai?
Shin ka tuba daga cin dukiyar haram, kamar riba, da saye-da-sayarwa na haram?
Shin ka sadar da zumuncinka?
Shin ka yi biyayya ga iyaye biyu?
Shin ka yi umurni da kyakkyawa, kuma ka yi hani daga mummuna?
Shin ka yi qoqari wajen riqo da shiriyar Annabi, domin ka kasance tare da shiryayyu?
Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma ku faxi magana madaidaiciya * Zai gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta da babban rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

Ya ku Bayin Allah!
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].


TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...