ZABABBUN
HADISAI KAN AZUMI (30)
أحاديث مختارة تتعلق بالصيام
TATTARAWAR DA TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على
أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار النبوية التي تتعلق بالصيام أو
برمضان، والله أسأل القبول والإخلاص، منها ما ورد في:
أنّ صوم رمضان من الخمس
التي بني عليها الإسلام
عَنِ عبد الله بْن عمر رضي الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ
الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ،
وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه البخاري
ومسلم.
NA
DAYA: AZUMIN RAMADHANA NA CIKIN GINSHIKAI BIYAR DA AKA GINA MUSULUNCI AKANSU
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace: Naji Manzon
Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan
abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma
Muhammadu manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da yin hajjin wannan
xakin, da azumin watan ramadana".
Bukhariyy
[8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
صيام رمضان هو الفرض والتطوع مطلوب
عَنْ طَلْحَة بْن
عُبَيْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، قال: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَإِذَا هُوَ يَسْأَلُهُ عَنِ الإِسْلاَمِ، فَقَالَ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خَمْسُ صَلَوَاتٍ فِي
اليَوْمِ وَاللَّيْلَةِ»، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهَا؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا
أَنْ تَطَّوَّعَ»
فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَصِيَامُ شَهْرِ رَمَضَانَ»، قَالَ: هَلْ
عَلَيَّ غَيْرُهُ؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا أَنْ
تَطَّوَّعَ»، قَالَ: وَذَكَرَ لَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الزَّكَاةَ، ... الحديث متفق عليه([2]).
NA
BIYU: AZUMTAR WATAN RAMADHANA SHINE FARILLA, SAIDAI ANA SON A RIKA YIN AZUMIN
NAFILA
An ruwaito daga Dalhah xan Ubaidullahi (r.a) yace: Wani Mutum ya zo zuwa ga
Manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi kan musulunci, Sai Manzon Allah (s.a.w)
yace masa: "Salloli biyar ne cikin yini da dare,
Sai mai tambayar ya ce: Shin akwai wasu a kaina? Sai ya ce: A'a; saidai idan za ka yi sallar taxawwu'iy –ta
nafila-. Sai Manon Allah (s.a.w) ya sake cewa: Da
azumtar watan ramadhana, Sai mai tambayar ya ce: Shin akwai
wasu aumin a kaina? Sai ya ce: A'a; saidai idan
za ka yi na taxawwu'iy –nafila- . Ya ce: Sai Manzon
Allah (s.a.w) ya ambata masa zakka…. Bukhariy (46, da 2678) da Muslim (11) suka
ruwaito shi .
تكفير السيئات مِن فضل
صيام رمضان إلى رمضان
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "الصَّلَـوَاتُ
الْخَمْسُ، وَالْـجُـمُعَةُ إِلَى الْجُـمُـعَةِ، ورمضـان إلى رمضـان: مكفِّرات
لِمَا بَيْنَهُمَا مَا اجْـتـنبَت الْكَبَائِر"([3]).
NA
UKU: KANKARE KURA-KURAI NA DAGA CIKIN FALALAR AZUMTAR RAMADHAN ZUWA RAMADHAN
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) daga Annabi (s.a.w) ya
ce: (Salloli guda biyar, da kuma juma'a zuwa wata juma'ar, da azumin
ramadana zuwa wani ramadan: masu kankare qananan zunuban da su ka kasance a
tsakaninsu ne; matuqar an nisanci manyan-manyan laifuka", Muslim ya
ruwaito shi (233).
غفران الذنوب المتقدمة
مِن فضل صيام رمضان إيمانا واحتسابا
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ،
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَنْ قَامَ لَيْلَةَ القَدْرِ
إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْـبِهِ، وَمَـنْ صَامَ
رَمَـضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِه»([4]).
NA
HUDU: GAFARTA ZUNUBAN DA SUKA GABATA NA DAGA CIKIN FALALAR AZUMTAR RAMADHAN
CIKIN IKHLASI
An ruwaito daga Abu-hurairah (RA), daga Annabi (SAW) ya ce: (Wanda ya yi
tsayuwar lailatul-kadri, yana mai imani da kuma neman lada an gafarta masa abin
da ya gabata daga zunubansa, kuma wadda ya yi azumin ramadana yana mai imani,
da kuma neman lada: an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa).
DAGA CIKIN SHARUDAN WAJABCIN AZUMI:
الطهر من الحيض ودم النفساء من شروط
صحة الصلاة والصوم
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُ الخُدْرِيِّ، قَالَ: قَالَ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلَيْسَ
إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ تَصُمْ؟ فَذَلِكَ نُقْصَانُ دِينِهَا»([6]).
TSARKAKA
DAGA HAILA DA JININ NIFASI SUNA CIKIN SHARUDAN INGANCIN SALLAH DA AZUMI
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy (r.a) ya ce: Manzon
Allah (s.a.w) ya ce: "Shin mace ba ta kasance, idan ta yi haila ba
ta sallah kuma ba ta azumi ba? To wannan na daga tawayar addininta!".
وعَنْ مُعَاذَةَ،
قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ فَقُلْتُ: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ، وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ.
فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ.
قَالَتْ: «كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ
بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ»([7]).
Kuma an ruwaito daga Mu'azatu, tace: Na tambayi A'isha, Na
ce: Me yasa Mace mai haila ta ke biyan azumi, amma bata yin ramukon sallah? Sai
ta ce: Ke daga matattarar khawarijawa; Harura'u, ki ke? Sai nace: Ni ba daga
garin Harura'u nake ba, saidai ina yin tambaya ne kawai, Sai ta ce:
"Hakan ya kasance ya kan same mu; sai a umurce mu da yin ramukon
azumi, amma ba a umurtarmu da mu rama sallah".
بمَ يدخل شهر رمضان، وبمَ ينتهي؟
عَن ابْن عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ
عَنْهُمَا، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
يَقُولُ: «إِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَصُومُوا، وَإِذَا
رَأَيْتُمُوهُ فَأَفْطِرُوا، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَاقْدُرُوا لَهُ»،
متفق عليه([8]).
وفي رواية عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، في آخره: فَإِنْ غُبِّيَ
عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ»([9]).
SHIGAN
WATAN RAMADHANA YANA TABBATA DA GANIN JINJIRIN WATA, KO CIKAN WATAN SHA'ABAN
30, HAKA KUMA YA KAN FITA DA GANIN JINJIRIN WATAN SHAWWAL, KO CIKAR RAMADHANA
30
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace: Na ji Manzon
Allah (s.a.w) yana cewa: "Idan ku ka ganshi –ma'ana:
jinjirin wata- to sai ku yi azumi, Idan kuma kuka gan shi sai ku ajiye azumi
–bikin sallah-, Idan kuma an yi muku hazo to sai ku qaddaramasa (cikar talatin). Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi. A wata ruwaya, daga hadisin Abu-Hurairah (r.a), ya ce: "Idan aka yi
muku hazo to sai ku cika kirgen sha'aban ya zama yini talatin.
وعَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي
الله عنهما، قَالَ: «تَرَائِى النَّاسُ الْهِلَالَ» فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنِّي رَأَيْتُهُ فَصَامَهُ، وَأَمَرَ
النَّاسَ بِصِيَامِهِ"([10]).
An
ruwaito daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: Mutane sun fita dobiyar
wata, Sai na bada Manzon Allah –S.A.W- labari cewa ni na gan shi, Sai ya azumce
shi (ramadhan), ya kuma umurci Mutane da su azumce shi".
وقت النية في صوم الفرض والتطوع
عَنْ
عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ، عَنْ حَفْصَةَ رضي الله عنهما، عَنِ النَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَنْ لَمْ يُبَيِّتِ الصِّيَامَ
قَبْلَ الْفَجْرِ، فَلا صِيَامَ لَه» ([11]).
LOKACIN
YIN NIYYA A AZUMIN FARILLA DA NA NAFILA
An ruwaito daga Abdullahi dan Umar, daga Hafsat (r.a), daga
Annabi (s.a.w) yace: "Duk wanda bai kwana da niyyar azumi gabanin
ketowar alfijir ba to bashi da azumi".
وعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها،
قَالَتْ: دَخَلَ عَلَيَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ
فَقَالَ: «هَلْ عِنْدَكُمْ شَيْءٌ؟»
فَقُلْنَا: لَا، قَالَ: «فَإِنِّي إِذَنْ صَائِمٌ». ثُمَّ
أَتَانَا يَوْمًا آخَرَ فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، أُهْدِيَ لَنَا حَيْسٌ
فَقَالَ: «أَرِينِيهِ، فَلَقَدْ
أَصْبَحْتُ صَائِمًا» فَأَكَلَ ([12]).
An ruwaito daga A'ishah (R.A), ta ce: Annabi –S.A.W- ya
shigo kaina, a wani yini, sai ya ce: Shin akwai wani abu a
wajenku? Sai
mu ka ce: A'a; babu, Sai ya ce: To na dauki azumi!". Sa'annan sai
ya zo wurinmu a wani yini na daban, Sai muka ce: An kawo mana kyautar Haisa,
Sai ya ce: "Nuna min shi, Hakika da na wayi gari ina azumi", Sai ya ci.
الأعذار المبيحة للفطر في رمضان،
فمنها: السفر:
فعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ
اللَّهُ عَنْهَا: أَنَّ حَمْزَةَ بْنَ عَمْرٍو الأَسْلَمِيَّ قَالَ لِلنَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَأَصُومُ
فِي السَّفَرِ؟ وَكَانَ كَثِيرَ الصِّيَامِ -، فَقَالَ: «إِنْ
شِئْتَ فَصُمْ، وَإِنْ شِئْتَ فَأَفْطِرْ» ([13]).
DAGA
CIKIN UZURORI DA SU KE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI BULAGURO:
An ruwaito daga A'isha (r.a), tace: Lallai Hamza dan Amru
Al-sulamiy, ya ce wa Annabi (s.a.w): Shin zan yi azumi a halin bulaguro? –Kuma
ya kasance mutum ne mai yawan yin azumi-, Sai ya ce: "In ka so ka
yi azumi, in kuma ka so sai ka karya".
وعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، حين
سُئِلَ عَنْ صَوْمِ رَمَضَانَ فِي السَّفَرِ؟ قَالَ: «كُنَّا نُسَافِرُ مَعَ
النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم فَلَمْ يَعِبِ الصَّائِمُ عَلَى المُفْطِرِ، وَلاَ المُفْطِرُ
عَلَى الصَّائِمِ» ([14]).
An ruwaito daga Anas dan Malik (R.A) a lokacin da aka tambaye
shi, akan azumtar ramadhana a halin tafiya, Sai ya ce: "Mun kasance
muna yin tafiya tare da annabi –SAW-; mai azumi bai kasance yana aibanta wa
mutumin da ya karya ba, haka shima wadda ya karyan bai kasance yana aibanta mai
azumi ba).
وعَنْ جَابِرِ بْنِ
عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله
عليه وسلم فِي سَفَرٍ، فَرَأَى زِحَامًا وَرَجُلًا قَدْ ظُلِّلَ عَلَيْهِ،
فَقَالَ: «مَا هَذَا؟»، فَقَالُوا: صَائِمٌ، فَقَالَ: «لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ فِي السَّفَرِ» ([15]).
An
ruwaito daga Jabir dan Abdullahi (r.a), Ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance
a cikin wata tafiya, sai ya ga wani cunkoso, da wani mutum wanda aka yi masa
inuwa, sai ya ce: Menene wannan? Sai aka ce: Me azumi ne, Sai ya ce:
"Baya cikin xa'a wa Allah yin azumi a halin tafiya", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito.
DAGA
CIKIN UZURORI DA SUKE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI ZUWAN JININ HAILA (hadisin ya
gabata).
ومن الأعذار أيضا:
عَنْ أَنَسِ بْنِ
مَالِكٍ رضي الله عنه،،، قَالَ: أَغَارَتْ عَلَيْنَا خَيْلُ رَسُولِ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَتَيْتُ الرَّسُولَ وَهُوَ يَتَغَدَّى
فَقَالَ: «ادْنُ فَكُلْ» قُلْتُ: إِنِّي صَائِمٌ، قَالَ: «اجْلِسْ أُحَدِّثْكَ عَنِ
الصِّيَامِ، إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ وَضَعَ عَنِ الْمُسَافِرِ شَطْرَ
الصَّلَاةِ. وَعَنِ الْمُسَافِرِ وَالْحَامِلِ وَالْمُرْضِعِ الصَّوْمَ»([16]).
DAGA
CIKIN UZURORI DA SU KE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI CIKI DA SHAYARWA:
An ruwaito daga Anas (R.A) ya ce: Dokunan yaqin Manzon Allah
(S.A.W) sun kawo mana farmaki, Sai n azo wajen Manzon Allah alhalin yana
karyawa, Sai ya ce: "Matso, ka ci"; Sai na ce: Lallai ni ina azumi,
sai ya ce: "Ka zauna in baka hadisi kan azumi, Lallai Allah ya janye wa matafiyi
rabin sallah. Da kuma azumi ga Matafiyi, da Mai ciki, da Mai shayarwa".
في صحيح البخاري معلقا
(قبل حديث برقم: 4505): قَالَ الحَسَنُ، وَإِبْرَاهِيمُ:
«فِي المُرْضِعِ أَوِ الحَامِلِ، إِذَا خَافَتَا عَلَى أَنْفُسِهِمَا
أَوْ وَلَدِهِمَا تُفْطِرَانِ ثُمَّ تَقْضِيَانِ».
"Mai shayarwa da mai ciki idan har su ka ji tsoron wahala ga kansu,
ko ga 'ya'yansu to sai su karya azumi, kana sai su yi ramuko".
وعن ابن عباس رضي الله
عنهما، أنه قال: "وَالْمُرْضِع والْحُبْلَى إِذَا خَافَتَا عَلَى أَوْلادِهِمَا
أَفْطَرَتَا، وَأَطْعَمَتَا"([17]).
Saidai kuma an ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (R.A) cewa:
"Mai shayarwa da mai ciki idan har su ka ji tsoron wahala ga
'ya'yansu to za su karya azumi, kana –idan su ka yi ramuko- sai su ciyar".
DAGA
CIKIN ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI: AKWAI CI DA SHA DA GANGANCI:
fadinsa
(SAW):
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «مَنْ نَسِيَ وَهُوَ صَائِمٌ، فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ، فَلْيُتِمَّ
صَوْمَهُ، فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ اللهُ وَسَقَاهُ»([18]).
An
ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) yace: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Duk wanda
ya manta alhali yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; Allah ne
ya ciyar da shi, ya kuma shayar da shi".
DAGA
CIKI, AKWAI: YIN JIMA'I:
عَنِ أبي هُرَيْرَةَ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: "بَيْنَمَا
نَحْنُ جُلُوسٌ عِنْدَ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم، إِذْ جَاءَهُ رَجُلٌ
فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ هَلَكْتُ. قَالَ: مَا
لَكَ؟ قَالَ: وَقَعْتُ عَلَى امْرَأَتِي وَأَنَا صَائِمٌ، فَقَالَ
رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: هَلْ تَجِدُ
رَقَبَةً تُعْتِقُهَا؟ قَالَ: لاَ، قَالَ: فَهَلْ
تَسْتَطِيعُ أَنْ تَصُومَ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ، قَالَ: لاَ،
فَقَالَ:فَهَلْ تَجِدُ إِطْعَامَ سِتِّينَ مِسْكِينًا.
قَالَ: لاَ، قَالَ: فَمَكَثَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم، فَبَيْنَا نَحْنُ
عَلَى ذَلِكَ أُتِيَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم بِعَرَقٍ فِيهَا تَمْرٌ
-وَالعَرَقُ المِكْتَلُ- قَالَ: أَيْنَ السَّائِلُ؟ فَقَالَ:
أَنَا، قَالَ: خُذْهَا، فَتَصَدَّقْ بِهِ،
فَقَالَ الرَّجُلُ: أَعَلَى أَفْقَرَ مِنِّي يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ فَوَ اللَّهِ
مَا بَيْنَ لاَبَتَيْهَا -يُرِيدُ الحَرَّتَيْنِ- أَهْلُ بَيْتٍ أَفْقَرُ
مِنْ أَهْلِ بَيْتِي، فَضَحِكَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم حَتَّى بَدَتْ
أَنْيَابُهُ، ثُمَّ قَالَ: أَطْعِمْهُ أَهْلَكَ"([19]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (R.A) ya ce: "Wata rana
muna zaune a wajen Annabi –S.A.W- sai wani mutum ya zo masa, ya ce: Na halaka!
Sai ya ce: Me ya same ka? Sai ya ce: Na auka wa matata alhali ina azumi, Sai
Manzon Allah –S.A.W- ya ce: Shin zaka samu baiwa da zaka
'yanta ta?
Sai ya ce: A'a! Sai ya ce: Shin zaka iya azumin wata
biyu a jere?
Sai ya ce: A'a! Sai ya ce: Shin kana da damar ciyar da
miskinai sittin?
Sai ya ce: A'a!, Sai ya ce: Sai Annabi –S.A.W- ya zauna, muna nan a cikin wannan
hali Sai aka zo wa Annabi –S.A.W- da wani masaki da dabino a cikinsa, Sai ya
ce: Ina mai wannan tambayar? Sai na ce: Ni ne, Sai ya ce: Karvi
wannan ka yi sadaka da shi, Sai mutumin ya ce: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai wanda ya
fi ni talauci? Na rantse da Allah! Tsakanin duwatsu biyu na Madina –unguwar
gabas da ta yamma- babu wasu iyalai da suka fi iyalaina talauci. Sai Annabi
–S.A.W- ya yi dariya har sai da fiqoqinsa su ka bayyana, sa'annan ya ce: Ka je ka
ciyar da shi iyalenka".
DAGA
CIKIN HAKA AKWAI: YIN AMAI (KO HARASWA) DA GANGANCI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ ذَرَعَهُ
القَيْءُ فَلَيْسَ عَلَيْهِ قَضَاءٌ، وَمَنْ اسْتَقَاءَ عَمْدًا فَلْيَقْضِ"([20]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a), lallai Manzon Allah
(s.a.w) ya ce:"Duk wanda amai ya rinjaye shi, to babu ramuko akansa, wanda kuma ya
jawo amai da ganganci to ya rama".
DAGA
CIKIN HAKA AKWAI: YIN KAHO:
عَنْ ثَوْبَانَ رضي
الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "أَفْطَرَ الْحَاجِمُ
وَالْمَحْجُومُ"([21]).
"Mai kahon
da wanda aka yi masa azuminsu ya karye".
DAGA
CIKIN HAKA AKWAI: FITAN JININ HAILA DA NA HAIHUWA (Hadisi akan
haka ya gabata).
MUSTAHABBAN
AZUMI
(1) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN SAHUR:
عن أَنَس بْن مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ،
قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَسَحَّرُوا فَإِنَّ فِي
السَّحُورِ بَرَكَةً» ([22]).
An
ruwaito daga Anas dan Malik (r.a) yace: Manzon Allah (s.a.w) yace "Ku yi
sahur; saboda akwai albarka a cikin sahur".
(2) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI JINKIRTA YIN SAHUR:
عَنْ أَنَسٍ، عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ رَضِيَ
اللهُ عَنْهُ، قَالَ:«تَسَحَّرْنَا
مَعَ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم، ثُمَّ قُمْنَا إِلَى الصَّلاةِ»، قُلْتُ: كَمْ كَانَ قَدْرُ مَا بَيْنَهُمَا؟ قَالَ:
خَمْسِينَ آيَة([23]).
An
ruwaito daga Anas (r.a) daga Zaidu dan Sabit (r.a) yace: Mun yi
sahur tare da manzon Allah –SAW- sa'annan sai mu ka tashi izuwa ga sallah, Sai na ce: Menene
tsakanin sahur da sallan? Sai ya ce: Gwargwadon karanta aya hamsin).
(3) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI GAGGAUTA BUDA-BAKI:
عَنْ سَهْلِ بْنِ
سَعْدٍ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ،
قَالَ: "لاَ
يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ، مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ"([24]).
An ruwaito daga Sahl dan Sa'ad (r.a), cewa lallai Annabi
(s.a.w) ya ce: "Mutane ba za su gushe ba cikin alheri; matukar suna gaggauta
buda-baki".
(4) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN BUDA BAKI DA DABINON DA BA BUSASSHE BA
عن أَنَس بْن مَالِكٍ رضي الله عنه قال: «كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله
عليه وسلم يُفْطِرُ عَلَى رُطَبَاتٍ قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ، فَإِنْ لَمْ
تَكُنْ رُطَـبَاتٌ، فَعَلَى تَمَرَاتٍ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ حَسَا حَسَوَاتٍ مِنْ
مَاءٍ»([25]).
An
ruwaito daga Anas dan Malik (R.A), ya ce: Manzon
Allah –SAW- ya kasance yana buda-baki da dabinon da ba busasshe ba "rudab"
gabanin ya yi sallah, in kuma bai samu "rudab" ba, to sai ya karya da
busasshen dabino, in kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa".
(5) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN ADDU'A A LOKACIN BUDA-BAKI, DA KUMA YAYIN AZUMI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ،
قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ثَلاَثَةٌ لاَ
تُرَدُّ دَعْوَتُهُمْ: الصَّائِمُ حَتَّى يُفْطِرَ، وَالإِمَامُ العَادِلُ،
وَدَعْوَةُ الْمَظْلُومِ يَرْفَعُهَا اللَّهُ فَوْقَ الغَمَامِ وَيَفْتَحُ لَهَا
أَبْوَابَ السَّمَاءِ وَيَقُولُ الرَّبُّ: وَعِزَّتِي لأَنْصُرَنَّكِ وَلَوْ
بَعْدَ حِينٍ"([26]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) ya ce: Manzon Allah
(s.a.w) ya ce: "Mutane uku ba a mayar da addu'oinsu: mai azumi har sai ya sha ruwa,
da shugaba adali, da addu'ar wanda aka zalunta, Allah yana daga ta a saman
girgije, kuma yana bude mata kofofin sammai, kuma Ubangijina yana cewa: Na
rantse da buwayata, zan taimake ki, koda bayan wani lokaci".
(6) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI: AKWAI YAWAN YIN SADAKA, DA KUMA TILAWAR ALKUR'ANI, DA SHAYAR
DA MASU AZUMI, DA SAURAN AIYUKAN DA'A:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ
رضي الله عنهما، قَال: "كَانَ
رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ أَجْوَدُ مَا
يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَـلْقَاهُ جِـبْرِيلُ، وَكَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ
لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَـيُدَارِسُهُ القُرْآنَ، فَلَـرَسُولُ اللَّهِ صلى الله
عليه وسلم أَجْـوَدُ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ"([27]).
An
ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (R.A), ya ce: "Manzon
Allah ya kasance shi ne yafi kowa kyauta ta alkhairi, kuma kyautarsa tafi yawa a
watan ramadhana a lokacin da Mala'ika jibrilu ke saduwa da shi, kuma jibrilu ya
kasance ya kan hadu da shi a cikin kowani dare; sai ya yi bitar alkur'ani tare
da shi; lallai Manzon Allah –S.A.W- a lokacin da mala'ika jibrilu ke saduwa da
shi yafi iska sakakkiya kyautar alkhairi".
(7) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI: AKWAI KOKARI WAJEN YIN SALLAR DARE:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا،
قَالَتْ: «كَانَ النَّبِيُّ صلى الله عليه
وسلم إِذَا دَخَلَ العَشْرُ شَدَّ مِئْزَرَهُ، وَأَحْيَا لَيْلَهُ،
وَأَيْقَظَ أَهْلَه»([28]).
An ruwaito daga A'ishah (R.A) ta ce: "Annabi
–S.A.W- ya kasance idan wadannan goman su ka shiga ya kan tamke kwarjallensa,
ya kuma raya darensa, ya kuma tayar da iyalensa".
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ،
عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم، قَالَ: "مَنْ قَامَ رَمَضَانَ
إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ"([29]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (R.A), daga Annabi (S.A.W) ya
ce: "Duk wanda ya yi tsayuwar dare a ramadana yana mai imani da neman
lada, to an gafarta abin da ya gabata na daga zunubansa".
(8) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN UMRAH:
وعَنْ ابْن عَبَّاسٍ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قال: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم
لِامْرَأَةٍ مِنَ الأَنْصَارِ:«مَا مَنَعَكِ أَنْ تَحُجِّينَ مَعَنَا؟»، قَالَتْ: كَانَ لَنَا
نَاضِحٌ، فَرَكِبَهُ أَبُو فُلاَنٍ وَابْنُهُ، لِزَوْجِهَا وَابْنِهَا، وَتَرَكَ
نَاضِحًا نَنْضَحُ عَلَيْهِ، قَالَ: «فَإِذَا كَانَ رَمَضَانُ اعْتَمِرِي فِيهِ، فَإِنَّ عُمْرَةً
فِي رَمَضَانَ حَجَّةٌ»([30])، وفي رواية: "عُمْرَةً فِي رَمَضَانَ تَعْدِل حَجَّةً".
An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (r.a) ya ce: Manzon
Allah (s.a.w) ya ce wa wata mata daga cikin Ansar: "Me ya hana ki kiyi hajji tare da mu? Sai ta
ce: Ya kasance muna da raqumin hawa da xebu ruwa guda daya, Sai baban wane ya
hau shi; shi da dansa, Tana nufin mijinta da xanta. Sai kuma ya bar mana rakumi
daya da muke debo ruwa a kansa. Sai ya ce: "To,
idan watan Ramadhan ya zo, sai ki yi umrah a cikinsa; saboda yin umrah a watan
ramadana tana daidai da yin hajji".
(9) DAGA CIKIN
MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI FADIN CEWA ''NI MAI AZUMI NE'' GA WANDA YA ZAGE SHI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قال: قَالَ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "قَالَ اللَّهُ: كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ، إِلَّا
الصِّيَامَ، فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، وَالصِّيَامُ جُنَّةٌ، وَإِذَا
كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَصْخَبْ، فَإِنْ سَابَّهُ
أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ، فَلْيَقُلْ: إِنِّي امْرُؤٌ صَائِمٌ"([31]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) ya ce: Manzon Allah
(s.a.w): "Allah ya ce: Dukkan aikin dan adam nasa ne, in banda azumi, lallai
shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, kuma azumi garkuwa ne, kuma
idan ranar azumin dayanku ya zo, to kada ya yi kwarkwasa, kada kuma ya yi ihu,
Idan wani ya nemi zaginsa ko yin fada da shi to ya ce: Ni Mutum ne mai azumi".
MAKRUHAN
AZUMI
1- DAGA CIKIN MAKRUHAN
AZUMI AKWAI: KAIWA MAKURA LOKACIN KURKURAN BAKI, DA SHAKA RUWA A HANCI;
في حديث لَقِيطِ بْنِ صَبْرَةَ رضي الله عنه لما وفدوا علَى رَسُولِ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وفيه، قال: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ،
أَخْبِرْنِي عَنِ الْوُضُوءِ، قَالَ: «أَسْبِغِ الْوُضُوءَ، وَخَلِّلْ بَيْنَ الْأَصَابِعِ، وَبَالِغْ
فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا» ([32]).
Daga hadisin Lakid dan Sabrah (r.a) a lokacin da tawagarsu
ta zo wajen Manzon Allah (s.a.w), A cikinsa ya ce: Na ce: Ya Ma'aikin Allah ka ba
ni labari akan alwala Sai ya ce: "Ka cika alwala, kuma ka
tsettsefe tsakanin yatsu, ka kuma, kai makura wajen shakar ruwa, sai dai in ka
kasance kana azumi".
2- DAGA CIKIN MAKRUHAN
AZUMI AKWAI: YIN SUMBA GA WANDA ZATA MOTSA SHA'AWARSA, KUMA BAYA AMINCE WA
KANSA:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا، قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ «يُقَبِّلُ وَهُوَ صَائِمٌ،
وَيُبَاشِرُ وَهُوَ صَائِمٌ، وَلَكِنَّهُ أَمْلَكُكُمْ لِإِرْبِهِ»([33]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a) ta ce: "Manzon
Allah (s.a.w) ya kasance yana yin sumba, alhalin yana yin azumi, kuma yana
runguma, alhalin yana azumi, saidai ya kasance ya fi ku iya mallakar bukatarsa".
([5]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 4401), da
An-nasa'iy (6/ 156), kuma Albaniy ya inganta shi a cikin (Irwa'ul galil,
lamba: 297).
([10]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2342),
da Alhaakim a cikin almustadrak (1/423), ya kuma inganta shi.
([11]) At-tirmiziy ya ruwaito shi (lamba: 733), da
An-nasa'iy (4/196), da Ibnu-majah (lamba: 1700), lafazin An-nasa'iy ne, Albaniy
kuma ya inganta shi cikin (Sahihu At-tirmiziy, lamba: 583).
([16]) At-tirmiziy ya ruwaito (lamba: 715), yace: hasan ne, da
An-nasa'iy (2/103), da Ibnu-majah (lamba: 1667), Albaniy yace: hadisi ne hasan
(Sahih sunan An-nasa'iy, lamba: 2145).
([17]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2337, 2318), Albaniy ya
inganta shi, a cikin littafin (Irwa'u algalil, 4/ 18, 25). An ruwaito kwatankwacinsa daga: Abdullahi bn Umar
(RA).
([20]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2380), da At-tirmiziy
(lamba: 720), da Ibnu-majah (lamba: 1676), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu
Ibni-majah, lamba: 1368).
([21]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2367), da Ibnu-khuzaimah
(lamba: 1983), kuma Albaniy ya inganta isnadinsa (Atta'aliq ala Ibni-khuzaimah,
3/236).
([25]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2356),
da At-tirmiziy (lamba: 696), kuma ya ce: hasan ne, Albagawiy a cikin littafinsa
(Sharhu assunah, ya fitar da shi, 6/266), ya kuma ce hadisi ne: hasan, Albaniy
kuma ya inganta shi a cikin (Sahihu At-tirmiziy, lamba: lamba: 560), Malam
Al-arna'ux ya ce: isnadinsa mai karfi ne a cikin ''ta'aliqinsa ga littafin:
Sharhu assunnah") .
([26]) At-tirmiziy ya ruwaito shi (lamba: 2526), kana ya ce:
hasan ne, kuma Albaihaqiy ya fitar da shi (3/345), da waninsu; daga Anas (R.A),
daga Annabi (S.A.W) da lafazin:
" ثَلاَثُ دَعَوَاتٍ لاَ
تُرَدُّ، دَعْوَةُ الْوَالِدِ، وَدَعْوَةُ الصَّائِمِ، وَدَعْوَةُ الْمُسَافِر".
Ma'ana: «Adduo'i guda uku ba a raddinsu, addu'ar iyaye, da ta mai
azumi, da addu'ar matafiyi»,
Kuma Albaniy ya inganta shi a cikin (Silsilatu as-sahihah, lamba: 1797).
([32]) At-tirmiziy ya ruwaito shi, (lamba: 788), ya kuma
inganta shi, da Imamun An-nasa'iy, (1/66, lamba: 87), da Ibnu-majah, (lamba:
407), kana kuma Albaniy ya inganta shi (a cikin sahihun nasa'iy, lamba:
85).
No comments:
Post a Comment