2017/11/23

huzaifiy 6 RABIYUL AWWAL 1439h daidai 24 Nobemba 2017M






HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى  الله عليه وسلم )
JUMA'A, 06/RABIYUL AWWAL/1439h
DAIDAI DA 24/11/2017M



LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah Mai rahama Mai jin kai; Mai ilimi Mai hikima, Ma'abucin falala mai girma,        Ina yin yabo ga Ubangina kuma ina yin godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare shi ina neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Ma'abucin al'arshi mai karamci,   
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawanSa ne manzonsa ne; Ma'abucin halayya masu girma,
Ya Allah ka yi karin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu kira zuwa ga Allah, da shiryatarwa zuwa ga hanya madaidaiciya.

Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah ta hanyar yin aiki da abubuwan da suke yardar da shi, da kuma kaurace wa ababen da ya haramta;  domin ku rabautu da samun yardarSa da kuma ni'imomin aljannoninSa,  sannan ku samu tsira daga fushinSa da kuma ukobobinSa,

Ya ku musulmai…
Lallai Ubangijinmu mabuwayi da daukaka ya yawaita kofofin alkhairi, da kuma hanyoyin ayyuka kyawawa, Falala da rahama da kuma kyauta daga ma'abucin buwaya da daukaka; domin musulmi ya shiga kowace kofa ta alkhairori,  ya kuma bi kowace hanya daga cikin hanyoyin biyayya;  sai Allah ya gyara duniyarSa,  ya kuma daukaka shi zuwa ga darajoji a lahirarSa; Sai Allah (سبحانه) ya karrama shi ta hanyar bashi rayuwa daddada, da kuma rabauta a cikin rayuwarsa, daga karshe sai ya samu ni'ima tabbatacciya, da kuma yardar Ubangiji, bayan mutuwarsa.  Allah (تعالى) yana cewa: "Sai ku yi tsere zuwa ga ayyukan alkhairi. Kuma duk inda kuka kasance Allah zai zo da ku gaba daya, Lallai Allah akan komai Mai iko ne" [Bakarah: 148].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa a dangane da annabawansa; wadanda kuma sune abin koyi ga mutane (Allah yayi dadin salati da sallama a gare su gaba daya): "Lallai ne sun kasance suna yin tsere cikin ayyukan alkhairi, Kuma suna yin bauta a gare mu akan kwadayi da fargaba, kuma sun kasance a gare mu masu tsoro ne" [Anbiya'i: 90].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa sahabinsa Mu'azu (رضي الله عنه): "Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga kofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta. haka sallar mutum a cikin dare. Sannan sai ya karanta fadin Allah: (Gefen jikinsu yana nisantar wuraren kwanciya, suna rokon Ubangijinsu cikin fargabar tsoro da kwadayi, kuma daga cikin abinda muka azurta su suna ciyarwa. Kuma rai bata san abinda aka boye mata na sanyin ido ba, sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa).
Sa'annan yace: Ba zan ba ka labari dangane da, kan wannan lamari ba, da ginshikinsa, da kololuwar tozonsa?
Sai na ce: Eh, ka bani labara, ya Manzon Allah!
Sai ya ce: Kan wannan lamari shine: Musulunci. Ginshikinsa kuwa sallah. Kololuwar tozonsa shine: Jihadi fiysabillah.  Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.

KUMA YANA DAGA CIKIN KOFOFIN ALKHAIRORI, DA HANYOYIN KYAWAWAN AYYUKA DA DA'OI, KUMA YANA DAGA CIKIN SABBUBAN SHAFE MUNANAN AYYUKA: NEMAN GAFARA; Saboda neman gafara sunnar Annabawa da Manzanni ne (عليهم الصلاة والسلام), Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayen 'yan-adam; guda biyu (Adam da Hauwa'u) Allah ya yi salati mai yawa da rahama da karin albarka a gare su: "Suka ce: Ya Ubangijinmu lallai mun zalunci kayukanmu, Idan baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Nuhu (عليه السلام): "Ya Ubangijina ka gafarta mini, da iyayena biyu, da wanda ya shiga gidana yana mumini, da kuma muminai maza da muminai mata" [Nuh:   28].
Kuma Allah mabuwayi da daukaka yana fada dangane da Ibrahimul khalil (عليه السلام): "Ya Ubangijinmu, ka gafarta mini, da iyayena biyu, da kuma muminai, a ranar da hisabi ke tsayawa" [Ibrahim: 41].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Musa (عليه السلام): "Ya Ubangijina, ka yi gafara a gare ni, ni da dan'uwana, kuma ka shigar da mu cikin rahamarka; lallai kai ne mafi jin-kan masu rahama" [A'araf: 151].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Sai annabi Dawud ya tabbata cewa: lallai jarrabarsa muka yi, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma fadi yana mai sujjada, ya kuma mayar da al'amari ga Allah" [Sad: 24].
Kuma Allah (تعالى), a inda yake umartar annabinSa (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Kuma ka sani, Lallai babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma ka nemi gafarar zunubanka, da kuma ga muminai maza, da mata" [Muhammadu: 19].

        KUMA YANA DAGA SHIRIYAR MANZONMU: YAWAITA NEMAN GAFARA, tare da cewa Allah Ta'alah ya gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa, da abinda ya jinkirta; Ya zo daga Dan Umar (رضي الله عنهما) yace: "Mun kasance muna qidaya wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a majalisa daya, sau dari: RABBI IGFIR LIY WA TUB ALAYYA; INNAKA ANTAT TAWWABUR RAHIM.
Ma'ana: Ya Ubangijina, ka gafarta mini, ka karbi tubata, lallai kai mai yawan karbar tuba ne, Mai jin-kai". Abu dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma an ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance gabanin mutuwarsa yana yawaita fadin: سبحان الله وبحمده، أستغفر الله وأتوب إليه  
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da gode masa, Ina neman gafarar Allah, ina kuma tuba zuwa gare shi. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: "Ban ga mutumin da yafi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yawaita fadin ASTAG FIRUL LAHA WA ATUBU ILAIHI".
Ma'ana: Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi. Annasa'iy ya ruwaito shi.

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance bayan yin sallamar fita daga sallah yana cewa: Astagfirul laha, har sau uku. Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Sauban (رضي الله عنه). Sai kuma daga bisani, ya fadi zikirorin da aka shar'anta fadinsu a bayan sallolin farilla.

Kuma lallai NEMAN GAFARA Dabi'ar salihan mutane ne, kuma aiki ne na masu biyayya da takawa, kuma alama ce ta muminan mutane,  Allah (تعالى) yana cewa: "Ya Ubangijinmu ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu, kuma ka dauki rayukanmu tare da masu biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Wadanda suke cewa: Ya Ubangijinmu lallai ne, mun yi imani; sai ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar wuta   *   Masu hakuri, da masu gaskiya, da masu kankan da kai, da masu ciyarwa, da masu yin istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma sune wadanda, idan suka aikata wata alfasha ko suka zalunci kayukansu sukan tuna Allah; sai su nemi gafarar zunubansu, Kuma wanene ke gafarta zunubai idan ba Allah ba, kuma basa dogewa akan abinda suke aikatawa, alhalin suna sane" [Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace: ((Shi neman gafara daga zunubai shine: neman lullube su, kuma lallai bawa yana da matukar bukatar hakan; saboda ko-yaushe ya kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA DA NEMAN GAFARA ya maimaitu a cikin alkur'ani, kuma an yi umarni da su, an kwadaitar akansu)). … Maganarsa ta qare.

        Kuma lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da daukaka, Allah yayi alkawarin cewa zai amsa, kuma zai yi gafarar.
        Kuma lallai an shar'anta bawa ya nemi gafara akan zunubi ayyananne, sananne; saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم): "Lallai bawana ya aikata wani zunubi, Sannan ya ce: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata wani zunubi; sai ka gafarta mini, Sai Allah ya ce: Bawana lallai ya san cewa  yana da Ubangijin da ke  gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da shi, to lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin  Abu-hurairah (رضي الله عنه).

        Kamar yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya rika neman gafara mudlakan, (a sake ba tare da ya qayyde wani zunubi ba; kamar ya ce: Ya Ubangijina, ka gafarta min, kuma kayi mini rahama.
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka ce: Ya Ubangijina, ka yi gafara kuma ka yi rahama, domin kai ne mafi alherin masu jin-kai" [Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana sanar da mutumin da ya musulunta da cewa ya rika yin addu'a da wadannan kalmomin: "Ya Allah ka yi gafara a gare ni, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka azurta ni", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Darik dan Ashyam (Allah ya kara yarda a gare shi).

        Kamar yadda aka shar'anta ga Bawa ya rika nema Ubangijinsa ya gafarta masa zunubansa gaba dayansu; wadanda ya san su da wadanda bai sansu ba; wannan kuma saboda zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai za a kama bawa akansu; saboda ya zo daga Abu-Musa Al'ash'ariy (رضي الله عنه) daga Annabi(صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar: "Ya Allah ka gafarta min kurakuraina da jahilcina, da ketare iyakana cikin lamari, da abinda kai ne ka fini saninsa. Ya Allah ka gafarta mini gaskena da wasana, da kuskurena da gangancina, kuma dukkan hakan akwai shi a wurina. Ya Allah ka gafarta mini abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na boye da abinda na bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa, kuma kai ne Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu Mai iko ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم): "Shirka a cikin wannan al'ummar tafi buya fiye da tafiyar tururuwa, Sai Abubakar (رضي الله عنه) yace: To ta yaya za a kubuta daga gare ta, ya Manzon Allah? Sai yace: Ka rika cewa: Ya Allah ina neman ka tsare ni kan yin shirka a gare ka alhalin ina sane, Ina kuma neman gafararka daga abinda ban sani ba", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga hadisin Abubakar. Da kuma Ahmad, daga hadisin Abu Musa.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a: "Ya Allah ka gafarta min zunubaina dukkansu; kananansu da manyansu, na kuskurensu dana gangancinsu, na sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na karshensu", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud.
        Idan bawa ya roki UbangijinSa gafarar zunubansa; wadanda ya sani daga cikinsu da wadanda bai sani ba, to lallai an datar da shi, dace mai girma.

        Kuma bawa ya roki Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roko mai tattare da kankan-da kai yana kunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROKON A DATAR DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana kunsan NEMAN GAFARAR; domin kowanne daga cikin ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da dayan ba, to yana kunsan ma'anan dayan,  Idan kuma ambatonsu ya hadu a cikin nassoshin Kur'ani ko hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI zai zama:
Neman shafe zunubi da gusar da alamarsa, tare da bada kariya kan sharrin da ya gabata na zunubin, da kuma suturce shi.
Ita kuma TUBA sai ma'ananta ya kasance: Komawa zuwa ga Allah ta hanyar barin aikata zunubai, da kuma kare bawa daga abinda ya ke tsoronsa na munanan ayyukansa a rayuwar da yake fiskanta, tare da yin azama ko niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai Ayar Allah ta ambaci ISTIGFAARI da TUBA a hade, a inda yake cewa: "Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku dadi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abucin girma girmansa, Idan kuma kuka juya, to lallai ni ina tsoron azabar yini mai girma akanku" [Hud: 3].
Da wassu ayoyin wadanda ba wannan ba.
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan tuba zuwa gare shi, tare da neman gafararSa; a kowani yini sau dari", Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).

        Kuma lallai bawa yana da matsananciyar bukatar YIN ISTIGFAARI, a ko-da-yaushe, musamman kuma a wannan zamanin; saboda yawaitan zunubai da fitintinu,    wannan kuma domin Allah ya datar da shi a rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma gyara masa sha'aninsa.    Saboda yin istigfaari ya kan bude kofofin alherori,   ya kuma tunkude sharrori da ukubobi.
        Kuma lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar bukata zuwa ga dawwamar da neman gafarar Allah; domin Allah ya yaye mata ukubobi da suka sauka a gare ta, ya kuma tunkuxe mata uqobobin da za su sake sauka a gare ta.
        Kuma babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa da albarkokinsa,  saboda falolin istigfari sun zo dayawa a cikin ALQUR'ANI da SUNNA; Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه السلام): "Ya ku mutanena Don me kuke gaggawan aikata mummunan aiki gabanin kyakkyawa, Da dai kun nemi gafarar Allah; don tsammanin za a yi rahama a gare ku" [Naml: 46].   Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى) yana fada dangane da annabi Nuhu (عليه السلام): "Sai nace: KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU lallai shi ya kasance mai yawan gafara ne *  Zai saki ruwan sama akanku; mamako   * kuma ya karfafe ku da wata irin dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya muku koguna" [Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى) yake fadi dangane da annabi Hudu (عليه السلام): "Kuma, ya mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya saki ruwan sama akanku, ya kuma kara muku wani karfi akan karfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi" [Hudu: 52].
Allah (تعالى) yace: "Allah bai kasance zai azabta su ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba; matukar suna neman gafara" [Anfaal: 33].
Abu-Musa yake cewa: ((Lallai wannan al'umma a cikinku akwai abubuwan samun aminci biyu; Amma dangane da wannan annabin –صلى الله عليه وسلم- to shi kam ya shude,  yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci-gaba da wanzuwa a cikinku har zuwa tashin kiyama)).
        Don haka; Wannan al'ummar ta yawaita istigfaari = zai dauke mata musibun da suka sauka ko suka auku, sannan ya tunkude mata ukubobin da za su sauka a gaba;   saboda bala'i baya sauka sai idan an yi ZUNUBI,  kuma ba a yaye shi, sai da yin TUBA da ISTIGFAARI,     An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (رضي الله عنهما) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Duk wanda ya lazimci yin istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani qunci, da kuma yayewa daga kowani baqin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani", Abu-dawud ya ruwaito shi.

        Kuma lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE, MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),  kuma lallai cikin fadin wadannan kalmomin akwai lada mai yawa;
        Yana daga cikinsu:
        Fadinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda ya fadi: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya fadi haka to an gafarta zunubansa, koda kuwa, ya gudu ne a wurin yaki", Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne ingantacce, akan sharadin Bukhariy da Muslim.
An ruwaito daga Abu-Sa'id alkhudriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai yace: "Duk wanda ya fada a lokacin da ya tafo zuwa ga shumfudinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYUL KAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to Allah zai gafarta zunubansa, koda sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Ubadah dan As-samit (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "Duk wanda ya tashi daga barcinsa, a cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR, SUBHANAL LAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG FIR LIY, Sai yayi addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an karbi sallarsa", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani hadisin cewa: "Duk wanda a gabanin ketowan alfijir din juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, an gafarta zunubansa koda sun kasance misalin kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito daga Shaddad dau Aus (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "Jagoran laffuzan neman gafara (سيد الاستغفار) shine bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA ANTA; KHALAKTANIY, WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTAXA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI ZANBIY; FAGFIR LIY; FA INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya faxi kalmomin nan cikin yini yana mai samun yaqini akansu sai ya mutu a wannan yinin nasa, gabanin yayi yammaci ya shiga aljannah. Wanda kuma ya faxes u cikin dare, alhalin yana da yaqini akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin 'yan aljannah", Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa: "Ya kai dan Adam da zunubanka za su cika sashen sama gaba daya, sannan sai ka nemi gafarata sai in gafarta maka, ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: hadisi ne mai kyau.

        Kamar yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH  a lokacin yin wata ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta magance abinda ya kasance a cikin ibadar na tawaya ko nakasa, tare da nisantar da mutum daga jiji-da kai, ko riya;    Allah (تعالى) yana cewa: "Sa'annan ku tafo ta wurin da mutane suke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Baqarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bada zakka, ku bada rance wa Allah rance mai kyau,    kuma duk abinda kuka gabatar ga kayukanku na alkhairi za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici kuma zai fi girma ga sakamako, Kuma ku roqi Allah gafara; lallai Allah Mai gafara ne Mai jin-kai" [Muzammil: 20].

        Haka kuma an shar'anta musulmi ya riqa neman gafara ga 'yan'uwansa muminai maza da muminai mata, da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da waxanda suka mutu,    wannan kuma a matsayin kyautatawarsa ne a gare su, da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da amfanar da musulmai, da kuma (tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah;    Allah (تعالى) yana cewa: "Da kuma waxanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi mana gafara, tare da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da Imani, kuma kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu dangane da waxanda suka yi Imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri: 10].
An ruwaito daga Ubadah xan Assamit (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi yace: "Duk wanda ya nemi gafara ga muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta masa lada a madadin kowani mumini namiji da mumina mace", Alhaisamiy yace: Isnadin wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar nema musu gafara Kenan a lokacin yin sallar janaza, da kuma nema musu gafara a maqabartai idan musulmi ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi ne da Mala'ikun da suke xauke da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku makusanta,   Allah (تعالى) yana cewa: "Wadanda suke rike da al'arshi, da wadanda suke kewayensa suna yin tasbihi da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin Imani da shi, suna kuma neman gafarar Allah ga waxanda suka yi Imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu! Lallai ka yalwaci kowani abu da rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga waxanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar jahim" [Gafir: 7]. 
Yin haka kuma yana daga cikin manyan haqqoqin muminai!

        Ya ku bayin Allah… !
        Ku amsawa umurnin Ubangijinku,    Allah yana cewa a cikin hadisin qudusiy: "Ya ku bayina ! lallai ku, kuna yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gaba daya; sai ku nemi gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abi-zarrin.

Sai ku fiskanci Ubangijinku da neman gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da falalarSa, da albarkokinSa, kuma za ku sami shafe aiyukanku munana, da xaukaka darajoji,      Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Na rantse da wanda raina ke hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah ta'alah ya tafiyar da ku, kuma da ya zo da wassu mutanen waxanda suke yin zunubi; sai suna neman gafarar Allah ta'alah sai ya gafarta musu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda kasancewarsa Allah maxaukaki Mai yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da karamci,    Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki, ko ya zalunci kansa, sa'annan sai ya nemi gafarar Allah, to lallai zai sami Allah Mai yawan gafara Mai rahama" [Nisa'i: 110].


        Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma

HUXUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah, Mai yawan gafara da godiya, Kuma sunaye mafiya kyau na Ubangajina ne, da kuma sifofi madaukaka. Ina yin yabo ga Ubangijina akan ni'imominSa masu girma.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya. 
Ina kuma shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababbe,  
        Ya Allah ka yi salati da sallama da karin albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu takawa.

Bayan haka;;;
        Ku kiyaye dokokin Ubangijinku Madaukaki, ta hanyar neman yardarSa, da yin aiki da da'a a gare shi, da kuma nisantar haramiyarSa,
Kuma lallai Ubangijinku ya baku damar yin aiki na kwarai, kuma ya sanya wannan duniyar ta zama gidan yin aiki ne, Lahira kuma gidan sakamako.
Kuma hakika masu yin aiki da ikhlasi da kyautatawa a wannan gida na duniya sun samu babban rabo, Masu kuma barna da kautar da kai ga addini sun tabe.
Ku kaddara ga ku, kamar ajalinku ya riga ya zo shi, burinku shi kuma ya kare.
Kuma lallai kuna da abin daukar izina cikin lamarin wadanda suka rigaye ku, kuma a cikin labarunsu da tarihinsu akwai abin wa'aztuwa; domin ma'abuta kabari dayansu yana burin ya dawo duniya, domin ya sallaci raka'oi guda biyu, ya nemi gafarar Allah dayawa, Saidai faufau ba za a amsa masa wannan bukatar ba, Allah Ta'alah ya ce: "Har idan mutuwa ta je wa dayansu, Sai ya ce: Ya Ubangijina, a mayar da ni (duniya)  * tsammanina in aikata aiki na kwarai cikin abinda na bari, Kayya, wannan kalma ce, da shi yake fadanta, a gaba gare shi akwai rayuwar barzahu, har zuwa lokacin da za a tayar da su" [Mu'uminuna: 99-100].
        Don haka, Kada ka raina aikin alkhairi duk karancinsa, kuma kada ka raina aikin sharri duk karancinsa, saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Ina tsawatar muku kan raina zunubai saboda karantarsu, domin su kan hadu ga mutum, sais u halaka shi".
Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa: "Kada ka raina wani abu, daga aikin alkhairi".

Ya ku bayin Allah,,,

"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin,   Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].


       Addu'a;;;;;;;;;;;;;;;;

2017/11/18

sufi inyas

من شرك الصوفية في نوعي الدعاء

   خامسًا: وهو في ديوان شِفاء الأسقام في مدح خير الأنام r قال مغاليًا في الناهي عن إطرائه r:
حمانِي رسولُ الله مِن كُلّ رامحِ
علَى رَغْمِ غادٍ للبِرَاز ورائِحِ
حمانِي رسولُ الله عَن مَكْرِ ماكِر
وشُؤْمٍ لِذِي شُؤْمٍ، وكُلّ الجوَائِحِ
وسِحرٍ لذِي سِحْرٍ، وعَيْنٍ لِعائِنٍ
فَمَنْ رامَ ضُرِّي قد سَعَى في مصالِحِ([27]).
([27]) شِفاء الأسقام في مَدْحِ خير الأنام r، ص145 ، ضمن الدواوين الست.

      وقال ضارعًا في مناداة النبِيّ r ومناجاته لِيَرْحَمَه –على زعمه- ويَنْظُر لحالِه:
أُنادِي حبيبَ الله طه محمدًا
أبا القاسِمِ الْهادِي الْمُقَفّى مناجِيَا
لِتَرحَم خَديْمًا ضارعًا عند بابِك الْـ
ـمُؤَمَّل، يا محمود فانْظُر لحالِيَا([28]).
([28]) المصدر نفسه، ص147، ضمن الدواوين الست.

      ونادَى النبِيّ r وزَعَم أنّه حاضِرٌ سامعٌ، ثم طَلَبَ منه أنْ يُجِيرَه، فقال:
أيَا سيِّدِي خَيْرَ الْوَرى نبِيَّنَا
يقينًا أُناِدي حاضِرِي الدّهْرَ سامِعِي
أجِرْنِي جِوَارًا هاشمِيًّا فَلَم أخَفْ
فلَمْ يَكُ يومًا مَن تَجِرْه بضائِعِ([29]).
([29]) المصدر نفسه، ص155، ضمن الدواوين الست.

   وجَعَلَ خَبَر ثلاث جُمَلِ لا يَفعَلُها إلا الله تعالى (جَعَلَ خبَرها مُحمدًا ... r)، فقال:
وأفَضلُ مَن يُدْعَى لِدَفْعِ نوائِبٍ
وأفْضَلُ مَنْ يُسْدِي العطَا ويُواسِ .. ([30]).
([30]) المصدر نفسه، ص160 (البيت وبيتان بعده، ضمن الدواوين الست).

   وزَعَم أنَّه مُنقِذُه مِن كُلّ البليات، فقال:
محمدُ أُنْسِي وَهْوَ كنزِي وملجَئِي
وسِرّي ومِن كُلّ البليات مُنْقِذِي([31]).
([31]) شِفاء الأسقام، ص164، وللازدياد من هذه الأبيات الغالية في هذا الديوان اقرأ، ما جاء في ص 140، 147، 151، 162، 164، 167، ضمن الدواوين الست.

   سادسًا: في ديوان مناسك أهل الوداد في مَدح خير العباد r قال مغاليًا في الناهي عن إطرائهr:
فَمِنْ جُودِه الْكَونان والعالَمُ الذي
تَقاصَر حِسٌّ عنه وهْوَ كبيرُ([32]).
([32]) مناسك أهل الوداد في مدح خير العباد r، ص182، ضمن الدواوين الست.

   وقال وهو يَزعُم أنّه عُرِج به إلى الله، ولقِي رسولَ الله r يقظة وجهارًا:
جِهارًا لَقِيْتُ المصطفى بِعُرُوجِي
إلى الله مِن ذَا الْكَونِ وقْتَ خروجِي
  إلى أن قال بعده بستة أبياتٍ:
رُجُوعِي مِنَ الْمولَى لأحمدَ نازلا
إلى الملإ الأعلى فُوَيقَ بُرُوجِ
كأنّي بَريد السِّرّ للكُلّ قاذفًا
بِوَقتِ هُبُوطِي مثلَ وقْتِ عُرُوجِي
تلقّاه مِنّي كُلّ رُوحٍ مُجرَّدٍ
صفَا وقْتُهُم والأمر غيرُ مَرِيج([33]).
([33]) مناسك أهل الوداد، ص176، ضمن الدواوين الست.

   وقال:
رأَيتُ رَسولَ الله نَصّ بأنّنِي
سفيرٌ له في الكائنات مُخَلِّص([34]).
  ([34]) مناسك أهل الوداد، ص187، وللازدياد من الأبيات الغالية في هذا الديوان وزوائده اقرأ ما في ص، 171، 173، 205، 212، 217، 218 ضمن الدواوين الست.


معنى المصطلحات الواردة في الأبيات
الدعاء: الرغبة إلى الله والتوجه إليه في تحقيق المطلوب أو دفع المكروه والابتهال إليه في ذلك إما بالسؤال أو التذلل والخضوع والرجاء والخوف والطمع.
الاستعاذة: لاذ به ولجأ إليه واعتصم،  وحقيقة معناها الهروب من المخاوف إلى من يعصمك منه.
الاستجارة: هي طلب دفع الضر والمكاره (قل إني لن يجيرني من الله أحد)
اللياذة: يكون لطلب جلب الخير
الاستغفار: طلب تغطية الذنوب وسترها والعفو عنها.
الشفاعة: الطلب للغير، وهو طلب في تجاوز عن الذنوب والجرائم.
السؤال: طلب الإنسان وأمنياته  (واسألوا الله من فضله)
النداء: الصياح والرغاء وهو الدعاء بأرفع الصوت بالإجماع وضده النّجاء، في كتاب مدارج السالكين: وقد أخبر سبحانه في كتابه أنه ناداه وناجاه، فالنداء من بعد، والنجاء من قرب.
الجؤار: (فإليه يجأرون): رفع الصوت والاستغاثة  ... (إذا هم يجأرون)
الابتهال: الاجتهاد في الدعاء وإخلاصه لله والمبالغة في السؤال، وفي القران  (ثم نبتهل فنجعل لعنة الله على الكاذبين).

وفي ختام النماذج أقول: إنْ لَم يكُن في هذه النماذج إطراء النبيّ r الْمنهي عنه، والشرك بأنواعه الثلاثة؛ الشرك في توحيد الإلهية (في الدعاء والاستغاثة خصوصًا) وفي الربوبية والأسماء والصفات، فما قرأتُ شركًا في كتاب! أما قائلُه فقد يكون تاب عن ذلك، ومات على غير هذه العقيدة، وأقول فيه كما قال ابن تيمية –رحمه الله- عن سلَفه البكري  الشافعي: «فإنّا بعد معرفة ما جاء به الرسول نعلم بالضرورة أنّه لم يشرع لأمته أنْ تَدْعُوَ أحَدًا من الأموات؛ لا الأنبياء ولا الصالحين ولا غيرهم، لا بلفظ الاستغاثة ولا بغيرها، ولا بلفظ الاستعاذة ولا بغيرها، كما أنّه لم يَشْرَع لأمته السجود لميت ولا لغير ميّتٍ، ونحو ذلك. بل نعلم أنّه نَهى عن كلّ هذه الأمور، وأنّ ذلك مِن الشرك الذي حرّمه الله تعالى ورسولُه، لكن لغلبة الجهل، وقلة العلم بآثار الرّسالة في كثيرٍ من المتأخرين: لم يكن تكفيرهم بذلك حتى يتبين لَهم ما جاء به الرسول r مما يخالفه، ولِهذا ما بيّنْتُ هذه الْمسألة قطّ لِمن يَعرف أصلَ الإسلام إلا تفطّن وقال: هذا أصل دين الإسلام. وكان بعض الأكابر من الشيوخ العارفين مِن أصحابنا يقول: هذا أعظم ما بَيَّنْتَه لنا؛ لِعِلْمِه بأنّ هذا أصلُ الدين. وكان هذا وأمثاله في ناحية أخرى يَدْعُون الأموات ويسألونَهم، ويستجيرون بِهم، ويتضرّعون إليهم، وربما كان ما يفعلونه بالأموات أعظم؛ لأنّهم إنما يقصدون الميت في ضرورة نزَلَتْ بِهم؛ فيدعونه دُعاءَ الْمُضطرّ، راجين قضاء حاجتهم بدعائه، والدعاء به، أو الدعاء عند قبره، بخلاف عبادتِهم الله تعالى ودعائهم إيّاه؛ فإنّهم يَفعلونه في كثيرٍ من الأوقات على وجه العادة والتكلّف، حتى إنّ العدو الخارج عن شريعة الإسلام لَمّا قدم دمشق خرَجُوا يستغيثون بالموتى؛ عند القبور التي يَرْجُون عندها كَشْفَ ضرّهم...»([35]).

([35]) الاستغاثة والرد على البكري، (ج2/ص731-732) بتحقيق: محمد بن علي عجال.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...