2015/01/28

Yaya ake yin wankan janaba?

SIFFAR WANKAN JANABA

بسم الله الرحمن الرحيم
Tambaya:
Yaya ake yin wankan janaba?
Amsa:
Wankan janaba tana da siffofi guda biyu; 
(1) Yanayi da ke isarwa na wajibi, 
(2) Da kuma siffa cikakkiya ta mustahabbi([1]).
Amma siffar da ta ke isarwa ga wanda yayi ta kuma ta wajibi: Itace Bawa ya game jikinsa da ruwa tun daga farkon farawa tare da niyya; Ma'anar wannan: Shine bawa ya game jikinsa da ruwa ta kowace fiska yaga dama tare da niyya. Haka zai isar wa mutum; Yayi niyya sai yayi nitso cikin wani kududdufi ko kuma kogi; ta yadda ruwan zai zama ya game jikinsa; Idan ya aikata haka tare da niyya to ya tsarkaka daga janaba.
Amma ita kuma siffa ta biyu cikakkiya ta mustahabbi Itace:
Na farko: Bawa ya wanke tafukansa guda biyu sau uku gabanin tsunduma su cikin ruwa.
Na biyu: Sai ya sanya hannunsa cikin ruwa don ya wanke al'aurarsa da duk wurin da dauxar janaba ta riga ta tava.
Na uku: Sannan sai ya wanke hannunsa da qasa ko da sabulu don gusar da dauxar janaba da ya tava da hannunsa.
Na hudu: Sai kuma ya yi alwalarsa cikakkiya irinta sallah; ma'ana: Ya kurkuri baki, da shaqa ruwa a hanci, ya wanke fiskarsa, sau uku, da hannayensa biyu zuwa guiwowinsu, sau uku, ya kuma shafi kansa da kunnuwa, sannan sai ya wanke qafofinsa sau uku uku.
Na biyar: Sai kuma ya wanke kansa sosai, yana mai shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa; Idan har yayi zaton cewa ruwan ya shiga tushensu to sai ya kwara ma kansa kamfata uku.
Na shida: Daga nan; Sai ya wanke sauran jikinsa da ruwa sau xaya, yana mai farawa da saman jikinsa, har ya taho qasa.
Na bakwai: In har kuma ya so zai iya jinkirta wanke qafarsa a yayin alwalarsa har sai ya zo qarshen wankarsa gabaxaya, sai ya koma gefe don wanke qafofinsa.
Waxannan bayanan zasu bayyana cikin hadisan dake tafe:
Na farko: Hadisin Maimunah (RA), ta ce:
"وَضَعْتُ لِرَسُولِ اللهِ r غُسْلاً وَسَتَرْتُهُ فَصَبَّ عَلَى يَدِهِ فَغَسَلَهَا مَرَّةً، أَوْ مَرَّتَيْنِ -قَالَ سُلَيْمَانُ: لاَ أَدْرِي أَذَكَرَ الثَّالِثَةَ أَمْ لاَ-، ثُمَّ أَفْرَغَ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَغَسَلَ فَرْجَهُ، ثُمَّ دَلَكَ يَدَهُ بِالأَرْضِ أَوْ بِالْحَائِطِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَيَدَيْهِ، وَغَسَلَ رَأْسَهُ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ تَنَحَّى فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ خِرْقَةً فَقَالَ بِيَدِهِ هَكَذَا، وَلَمْ يُرِدْهَا" ([2]).
Ma'ana: (Na sanya wa Manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ruwan wankansa, na kuma suturce shi, sai ya zuba wa hannunsa sai ya wanke shi sau xaya ko sau biyu, -Sulaiman Al-a'amash ya ce: Ban sani ba ya faxi wanke hannu a karo na uku ko a'a-, Sa'annan sai ya zuba ruwa daga hannun damansa i zuwa "hagu" xinsa sai ya wanke "gabansa", sa'annan sai ya xauraye hannunsa da qasa ko da katanga, sa'annan sai ya kurkuri baki ya kuma shaqa, ya wanke fiskarsa da hannayensa, kana ya kuza ruwa a sauran jikinsa, sa'annan ya koma gefe ya wanke qafofinsa guda biyu. Matar manzon Allah Maimunah ta ce: Sai na miqa masa tsumma don tsanar da jiki, amma sai ya karkaxe ruwa da hannayensa; bai buqaci tawol ba). 
A kwai kwatankwacin wannan hadisin daga A'ishah (RA), wanda kuma shi ne:
Hadisi na biyu: Hadisin A'ishah (RA) wanda Imamul Bukhariy da Muslim suka rawaito shi.
ta yadda ya zo a cikinsa:
عَنْ عَائِشَةَ، قَالَتْ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الْجَنَابَةِ يَبْدَأُ فَيَغْسِلُ يَدَيْهِ. ثُمَّ يُفْرِغُ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَيَغْسِلُ فَرْجَهُ، ثُمَّ يَتَوَضَّأُ وُضُوءَهُ لِلصَّلَاةِ، ثُمَّ يَأْخُذُ الْمَاءَ فَيُدْخِلُ أَصَابِعَهُ فِي أُصُولِ الشَّعْرِ، حَتَّى إِذَا رَأَى أَنْ قَدْ اسْتَبْرَأَ حَفَنَ عَلَى رَأْسِهِ ثَلَاثَ حَفَنَاتٍ، ثُمَّ أَفَاضَ عَلَى سَائِرِ جَسَدِهِ، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ» ([3]).
Ma'ana: (Manzon Allah –saw- ya kasance idan ya zo yin wankan janaba; ya kan fara da wanke hannunsa guda biyu, sannan sai ya kwara ruwa daga hannunsa na dama zuwa ga hagu don ya wanke farjinsa, Sannan sai ya yi alwalarsa irinta salla, sannan sai ya xauki ruwa sai ya shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa, idan yaga cewa ya isar da jiqajiqan ruwa to sai ya xibi kamfata uku, Sannan sai ya kwara ruwa ga sauran jikinsa, Sannan sai ya wanke qafofinsa guda biyu". Wannan hadisin da wanda ya gabace shi, sun yi bayanin siffar wankan manzon Allah (sallallahu alaihi wasallama).
A dunqule; dangane da cikakken yanayi ko siffar wanka: To shi ne, Bawa ya wanke hanayensa, sa'annan ya wanke farjinsa, da duk gunda dauxa ta tava, sa'annan ya yi alwala alwalarsa irin ta sallah, sa'annan ya xauki ruwa a hannunsa don ya tsettsefe gashin kansa da shi, yana mai shigar da yatsunsa a cikin tushen gashin kansa; don ya jijjika fatarsa, sa'annan ya xebi kamfata uku don wanke kansa, kana ya kwara ruwa a sauran jikinsa.
Kuma ba wajibi ne mace ta warware gashin kanta a wankan janaba ba. Amma hakan wajibi ne akanta a wankan haila; saboda hadisin Ummu Salamah (RA), ta ce: Na ce: Ya manzon Allah lallai ni mace ce da nake xaure gashin kaina; Shin zan warware shi don wankan janaba? Sai ya ce:
"لا، إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْثِي عَلَى رَأْسِكِ ثَلاثَ حَثَيَاتٍ، ثُمَّ تُفِيضِينَ عَلَيْكِ الْمَاءَ؛ فَتَطْهُرِينَ" ([4]).
Ma'ana: (A'a; Ai zai ishe ki kawai ki xebi kamfata guda uku ki kwara akanki, sa'annan sai ki kwara ruwa a jikinki; sai ki zama kin yi tsarki).

Walhamdu lillah!
Laraba/ 08/ Rabius saniy/1436h 
Daidai da 28/01/2015m




([1]) SHI YANAYI DA KE ISARWA GA WADDA YA YI AIWATAR DA SHI SHINE: Wankan ya kunshi wajibai kawai. YAYIN DA SHI KUMA CIKAKKEN WANKA shi ne ya kunshi wajiban da kuma mustahabbai
([2]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 266), da Muslim (lamba:  317). 
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 272), da Muslim (lamba:  316). 
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 330).  

2015/01/23

AKIDAR YAN SHI'A KAN UWAR MUMINAI A'ISHA (KAFIRTA A'ISHAH, TUHUMAR TA DA YIN ZINA, D. S)













BAYANI KAN
MATSAYAR 'YAN SHI'A ISNAA ASHARIYYA (RAFIDA) DANGANE DA UWAR MUMINAI A'ISHAH
(RADIYALLAHU ANHA)



















FASSARAR:
ABUBAKAR HAMZA


بسم الله الرحمن الرحيم
TAMBAYA:
Wassu masu wa'azi da da'awa suna ganin cewa: Tuhumar Uwar muminai A'isha; mai gaskiya yar mai gaskiya da cewa ta kafirta, wai kuma tayi alfasha (na zina), tuhuma ce da wassu tsiraru suka yi mata daga cikin maluman shi'a, kuma wai abinda maluman shi'a; irin su Yasir Habib da Mujtabah As-shiyraziy da wassunsu suka yi na kafirta ta da cin mutuncinta = zance ne na tsiraru da bashi da gindin zama a cikin addinin shi'a, Wai kuma "aqidun shi'a imamiyya" masu imamai guda goma sha biyu (12) basu qunshi irin waxannan tuhumce-tuhumcen ba, kuma wai sun barranta daga dukkan abubuwan da ake danganta mata, kamar yadda malumansu masu takiyyah suke riyawa, DA FATAN ZAMU SAMU BAYANI AKAN HUKUNCIN SHARI'AR MUSULUNCI KAN WANNAN MAS'ALAR, Allah ya bada lada?
AMSA:
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah shi kaxai.
Salati da sallama su qara tabbata ga wanda babu annabi bayansa. Bayan haka:
Lallai yana daga cikin abubuwan da suke baqanta rai; yadda wannan yaudara ko rufa-ido ta kama kwakwalen wassu masu wa'azi da da'awa, har suke gaskata masu aqidar "taqiyyah", a lokacin da masu wa'azin ke quduri cewa lallai tuhumar uwar muminai sayyidah A'ishah (radiyallahu anha) wai baya cikin aqidun shi'a imamiyyah.
Sai dai kuma bincike ya bayyanar da cewa hakan (tuhumar uwar muminai A'ishah) aqida ce tabbatacciya wacce 'yan "shi'a imamiyya isnaa ashariyya" suka gaskata ta.
Daga cikin manya-manyan maluman shi'a da suke sukar matar manzon Allah (sallal lahu alaihi wa sallama) kuma uwa ga muminai; a jiya da yau akwai: Malaminsu/ Majlisiy, da Kummiy, da Ayyashiy, da An-nabaxiy al-bayadiy, da Hashim al-bahraniy, da Yusuf al-bahraniy, da Ja'afar Murtadah al-amiliy, da Muhammadu al-qummiy an-najafiy, da Khumainiy, da Muhammadu Jamilu al-amiliy, da wassunsu dayawa.
A ta xaya hannun kuma, bamu ga wani malami babba ko marja'i da shi'a ke dogara da shi: yana neman a qona littatafan da suke cin mutuncin matar manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama), ko dai, alal aqalli yace ya barranta dasu ko da maluman da suka wallafa su, ko ya barranta daga aqidun da suka zo a cikinsu, ko yayi hukuncin fita daga musulunci (riddah) ga mutumin da ya qudurci munanan aqidun da suke cikin littatafan (to, me yasa haka?).
INA CEWA: Lallai yana daga cikin aqidun shi'a imamiyyah KAFIRTA UWAR MUMINAI A'ISHAH (radiyallahu anha), kuma wai ita 'yar wuta ce, wai harma tana da kofar shiga wuta da aka tanada mata na musamman (da ya kevanta da ita), kuma wai itace uwar sharri, da wassun waxannan tuhumomin waxanda mutum mai hankali adali ba zai tava gaskata su ba, koda kuwa ba musulmi ba ne.
Malamin shi'a mai suna Ja'afar Murtadah al-amiliy a cikin littafinsa mai taken "hadisin tuhumar A'ishah da aikata zina (hadisul ifki)" [a shafi na: 17] yace:
"إننا نعتقد كما يعتقد به علماؤنا الأفذاذ –وهم جهابذة الفكر والتحقيق- أنّ زوجة النبيّ يمكن أنْ تكون كافرة كامرأة نوحٍ وامرأة لوط، ولكن لا يمكن أنْ تكون فاجرة !!"، فبرَّأها من الزنا، ثم حكم عليها بالكفر.
Ma'ana: "Lallai aqidarmu itace aqidar malumanmu zarata -waxanda kuma sune jigajigen ilimi da tahqiqi- cewa: Lallai matar wannan annabin zata iya kasancewa kafira, kamar matar annabi Nuhu, da matar annabi Ludu, Sai dai kuma ba zai yiwu ta kasance fajira (mazinaciya ba)". Sai wannan malami ya barrantar da A'ishah (radiyallahu anha) daga aikata zina, sannan ya mata hukunci da kafirci (wai ta bar musulunci).
          Haka kuma malaminsu Al-ayyashi a cikin [tafsirinsa, juzu'i2 / shafi: 22], da Almajlisiy a cikin [Biharul anwaar], da Albahraaniy a cikin littafinsa [Alburhaan, juzu'i2 / shafi 383] Sun Ambato maganar da suka yi qaryar jingina ta zuwa ga Ja'afar As-sadiq, a tafsirin faxin Allah ta'alah:
((ولا تكونوا كالتي نقضت غزلها من بعد قوة أنكاثًا)) [سورة النحل: 92]
Ma'ana: "Kuma kada ku kasance kamar wacce ta warware saqar da tayi bayan ya riga yayi qarfi warwarewa" [Nahli: 92]. Wai yace:
(التي نقضت غزلها من بعد قوة أنكاثًا: عائشة، هي نكثت إيمانها).
Ma'ana: "Matar da ta warware abinda ta saqa bayan ya riga yayi qarfi warwarewa: Itace A'isha; ta warware imaninta".
(sallallahu alaihi wa sallama)
Haka kuma malaminsu Hashim Albahraniy a cikin tafsirinsa [juzu'i 4/ shafi: 358] ya Ambato daga Abu-abdillahi, lallai shi wai yace dangane da tafsirin faxin Allah ta'alah:
((ضرب الله مثلا للذين كفروا امرأة نوح وامرأة لوط كانتا تحت عبدين من عبادنا صالحين فخانتاهما فلم يغنيا عنهما من الله شيئًا وقيل ادخلا النار مع الداخلين)) [التحريم: 10].
Ma'ana: "Allah ya buga misali kan waxanda suka kafirta; matar annabi Nuhu, da matar annabi Luxu, sun kasance qarqashin bayina guda biyu daga cikin bayina salihai, sai suka ha'ince su, Basu wadatar dasu komai ba daga Allah, Sai aka ce: Ku shiga cikin wuta tare da masu shiga" [Tahrim: 10].  Wai yace:
(مثلٌ ضربه الله سبحانه في عائشة وحفصة أنْ تظاهرتا على رسول الله وأفشتا سِرّه).
Ma'ana: "Wannan misali ne da Allah (SWT) ya buga shi akan A'ishah da Hafsah saboda wai sun taimaki junansu akan manzon Allah, sun kuma yaxa sirrinsa".
          Shima malaminsu mai suna Muhammadu Xahiru Alqummiy an-najafiy ya ambata a cikin littafinsa [Al-arba'ina fiy imamati al-a'immatix xahirina, shafi: 610] cewa:
(مما يدل على إمامة أئمتنا الاثني عشر أنّ عائشة كافرة مستحقة للنار، وهو مستلزم لحقيقة مذهبنا وحقيقة أئمتنا الاثني عشر... –ثم قال: وكل من قال بإمامة الاثني عشر قال باستحقاقها للعن والعذاب).
Ma'ana: "Daga cikin dalilan da suke nuna imamancin limamanmu guda goma sha biyu kasancewar A'ishah ta kafirta, kuma wait a cancanci shiga wuta, wannan kuma shine abinda qudurta mazhabarmu, da cewa limamanmu goma sha biyu ne ke hukuntawa. … Sannan yace: Duk mutumin da qudurta cewa limaman shi'a guda goma sha biyu ne (12), to lallai dole ya qudurta cancantar A'ishah ga tsinuwa, da kuma azaba".
          Shi kuma malaminsu Yusuf albahraniy cewa yayi A'ishah ta kasance munafiqa ce, sannan kuma sai ta yi ridda bayan wafatin annabi (SAW), a cikin littafinsa [Ash-shihaabus saqib fiy bayani ma'ana an-naasib, shafi: 236]:
(إنها كانت في حياته صلى الله عليه وسلم من المنافقين، لجواز كونها مؤمنة في ذلك الوقت، وأنها ارتدت بعد موته كما ارتد ذلك الجم الغفير المجزوم بإيمانهم سابقًا).
Ma'ana: "Lallai A'ishah ta kasance a lokacin rayuwan manzon Allah (sallallahu alaihi wasallama) daga cikin munafiqai, saboda a wannan lokacin akwai yiwuwan kasancewarta mumina. Sai kuma tayi riddah bayan rasuwarSa, kamar yadda mutane masu yawa waxanda ake da tabbacin kasancewarsu masu imani a da, suka yi riddah".
          Lamarin a wajen malaminsu mai suna an-nabaxiy albayadiy ya kai ga yana riya cewa son da annabi (sallallahu alaihi wasallama) yake yi ma A'ishah wai ba zai amfane ta ba, a inda yake cewa:
(قالوا: هي محبوبة النبي صلى الله عليه وآله، وتوفي بين سحرها ونحرها، قلنا: لا تنفعها المحبة) [الصراط المستقيم لمستحقي التقديم، ج3/ص165].
Ma'ana: "Sun ce: A'ishah abun so ce a wurin annabi (sallallahu alaihi wa alihi), kuma ya rasu ne a tsakanin qirjinta da wuyanta. Sai muka ce: Son da yake mata ba zai amfanar da ita ba" [Littafin/ As-siraxul mustaqim limustahiqqit taqdim, juzu'i 3, shafi: 165].
          Shi kuma malaminsu mai suna Majlisiy a cikin littafinsa:  [Al, I'itiqaadaat, shafi: 58]:
(ومما عُدّ مِن ضروريات دين الإمامية: استحلال المتعة، وحج التمتع، والبراءة من أبي بكر وعمر وعثمان ومعاوية وكل مَن حارب أمير المؤمنين صلوات الله عليه، والرافضة يعتبرون أنّ عائشة قد حاربت في موقعة الجمَل).
Ma'ana: "Yana daga abubuwan tilas ga addinin shi'a imamiyyah: halatta auren mutu'a, da hajjin tamattu'i, da barranta daga Abubakar da umar da Usman da Mu'awuya, da duk wanda ya yaqi Amirul muminina (Aliyu) –salawatullahi alaihi-, Shi'ah rafidah na xaukar A'ishah a matsayin wacce ta yi yaqi, a yaqin da ake ce masa: yaqin kan raqumi (jamal)". Wannan ya yansa malaminsu Xuwsiy a cikin littafinsa [Al, iqtisad fiyma yata'allaqu bi li'itiqaad, shafi: 358]:
(ظاهر مذهب الإمامية أنّ الخارج على أمير المؤمنين، والمقاتل له: كافرٌ، بدليل الفرقة المحقة على ذلك).
Ma'ana: "Zahirin mazhabar shi'a imamiyyah ya nuna cewa waxanda suka fita daga xa'ar amirul muminina; Aliyu, da wanda ya yaqe shi sun kafirta, dalili kuma shine, qungiyar gaskiya (ma'ana: shi'a a wajensa) sun kasance akan wannan ra'ayi".
A kan wannan ne 'yan shi'a suke kafirta A'isha (radiyallahu anha) cikin lafazi bayyananne. Tare da cewa A'ishah ta fita ne don kawo sulhu, ba don yaqi ba, kamar yadda 'yan shi'a rafidha  ke riyawa!
          Lamarin rafidha 'yan shi'a ya kai ga sanya ma A'ishah laqabin: Ummush shurur (ma'ana: uwar sharrai) a cikin littatafansu, kamar yadda malaminsu mai suna An-nabaxiy albayadhiy ya ambaci haka a cikin littafinsa: As-siraxul mustaqim limustahiqqit taqdim, juzu'i 3, shafi: 161] a inda yace:
(فصل في أم الشرور).
Ma'ana: "Fasalin dake bayani kan uwar sharrai"; Wai yana nufin uwar muminai A'ishah (radiyallahu anha).
          NA BIYU: Aqidar shi'a imamiyyah isnai ashariyyah dangane da kamammemiya tsarkakakkiya matar manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama), kuma uwa ga muminai; A'ishah (radiyallahu anha) mai cewa: Wai A'ishah (radiyallahu anha) tana da qofa ta musamman daga cikin qofofin wuta da zata shiga ta cikinsa, A inda shehinsu Al-ayyashiy a cikin [tafsirinsa, juzu'i 2/ shafi: 430] daga Abu-basir daga abu-Abdullahi, yace:
(يؤتى بجهنم لها سبعة أبواب؛ بابُها الأول للظالم وهو زريق، وبابها الثاني لحبتر، والباب الثالث للثالث، والرابع لمعاوية، والباب الخامس لعبد الملك، والباب السادس لعسكر بن هو سر).
Ma'ana: "Za a zo da wutan jahannama; tana da qofofi guda bakwai, qofarta ta farko na wanda yayi zalunci ne; wanda kuma shine: zariq (suna nufin Abubakar as-siddiq), qofarta ta biyun kuma na habtar ne (suna nufin Umar alfaruq), qofa ta uku kuma ga na ukun (suna nufin: zun-nuraini Usman), ta huxun kuma ga Mu'awuya, qofa ta biyar kuma ga Abdulmalik, qofa ta shida kuma ga askar bn huw sir". Malaminsu Majlisiy ya ambata a cikin littafinsa [Biharul anwaar, juzu'i 8/ shafi: 302] cewa:
(وعسكر بن هو سر كناية عن بعض خلفاء بني أمية أو بني العباس).
Ma'ana: "Sunan "askar bn huw sir" kinaya ne kan wani daga cikin halifofin zamanin daular umawiyyawa, ko abbasiyyawa". Sannan sai yace:
(ويحتمل أن يكون "عسكر" كناية عن: عائشة وسائر أهل الجمل؛ إذ كان اسم جمل عائشة "عسكرًا". وروي أنه كان شيطانًا).
Ma'ana: "Mai yiwuwa ne kuma "askar" ya kasance kinaya ne kan: A'ishah, da kuma sauran waxanda suka yi yaqin "jamal"; saboda kasancewar raqumin da A'ishah ta hau wai sunansa: askar. Sai dai kuma an rawaito cewa raqumin nata wani "shexani ne".
          Nan kuma xaya ne daga cikin maluman shi'a rafidha ke tuhumar A'ishah (radiyallahu anha) qarara da aikata zina;  malaminsu an-nabaxiy albayadiy a cikin [Littafinsa/ As-siraxul mustaqim limustahiqqit taqdim, juzu'i 3, shafi: 165] cewa yayi:
(قالوا: برّأها الله في قوله: (أولئك مبرؤون) [النور: 26]، قلنا: ذلك تنزيهٌ لنبيِّه عن الزنا لا لها، كما أجمع فيه المفسِّرون).
Ma'ana: "Sun ce: Allah ya kuvutar da ita a cikin faxinSa: Waxannan abun kuvutarwa ne" [Nuur: 26]. Sai muka ce: wannan kuvutarwa ne da Allah yayi ma annabinsa, bag a A'ishah ba, kamar yadda maluman tafsiri suka yi ijma'I kan hakan".
          Malaminsu mai suna Hashim albahraniy a cikin [tafsirinsa, juzu'i 4/ shafi: 358] ya faxa yace: Aliyu xan Ibrahim yace: Sannan sai Allah ya buga misali akansu su biyu, yace:
 ((ضرب الله مثلا للذين كفروا امرأة نوح وامرأة لوط كانتا تحت عبدين من عبادنا صالحين فخانتاهما فلم يغنيا عنهما من الله شيئًا وقيل ادخلا النار مع الداخلين)) [التحريم: 10].
Ma'ana: "Allah ya buga misali kan waxanda suka kafirta; matar annabi Nuhu, da matar annabi Luxu, sun kasance qarqashin bayina guda biyu daga cikin bayina salihai, sai suka ha'ince su" [Tahrim: 10]. Sannan yace:
(والله ما عني بقوله "فخانتاهما" إلا الفاحشة، وليقيمن الحدّ على فلانة؛ فيما أتت في طريق البصرة، وكان فلان يحبها. وفي نسخة: طلحة. ولما أرادت أنْ تخرج إلى البصرة قال لها فلانٌ: لا يحل لك أنْ تخرجي من غير محرم؛ فزوّجت نفسها من فلان، وفي نسخة: طلحة).
Ma'ana: "Wallahi! Allah bai nufi komai ba da faxinsa (Sai suka ha'ince su) in banda alfasha. Kuma tabbasa (mahdin shi'a) zai tsayar da haddi ga wacce; akan abin da ta aikata a hanyarta ta tafiya garin Basarah, dama kuma wane yana sonta, -A wani kofin littafin aka ce: Sahabi Xalhat. A lokacin da ta so ta fita zuwa ga Basarah sai wane yace mata: Baya halatta a gare ki, kiyi tafiya ba tare da muharrami ba; Sai kawai ta aurar da kanta ga wane -A wani kofin littafin aka ce ga: Sahabi Xalhat".
          Wannan yasa malaminsu mai suna Ahmad al,ahsa'iy a cikin littafinsa dake magana kan aqidarsu ta dawowa duniya gabanin qiyamah [Ar-raj'ah, shafi: 116] ya ambata cewa:
(أنّ مهدي الشيعة إذا خرج سيحيي أم المؤمنين عائشة ويقيم عليها الحدّ، فقد ذكروا أنّ أبا جعفر عليه السلام قال: أما لو قام القائم لقد رُدّت إليه الحميراء حتى يجلدها الحدّ، وينتقم لأمه فاطمة عليها السلام منها، قلتُ: -جُعلتُ فداك- ولِمَ يحدّها الحدّ؟ قال: لقذفها على أمّ إبراهيم).
Ma'ana: "Lallai Mahdin shi'a idan ya fito zai rayar da uwar muminai A'ishah, kuma wai zai tsayar mata da haddi; saboda sun ambata cewa lallai Abu-ja'afar alaihis salam yace: Idan mahdiy mai tasowa ya taso to lallai za a dawo masa da A'ishah da annabi ya mata laqabi da Alhumaira'u don ya tsayar mata da haddi, ya kuma xauki fansa daga gare ta, ga mamarsa Fatimah alaihas salamu Sai nace: -Allah ya sanya ni fansa a gare ka- Don me yasa zai mata irin wannan haddin? Sai yace: Saboda tayi qazafi ga baiwar annabi da ta Haifa masa xa Ibrahim". Dama suna cewa:
(قولهم إنّ المبرَّأة في قصة الإفك هي مارية القبطية لا عائشة رضي الله عنها).
Ma'ana: "Lallai wacce Allah ya tsarkake a qissar qiren qaryar zina da aka yi ga matar manzon Allah itace: Mariya baqibxiya, ba A'ishah (Allah ya qara yardarsa a gare ta) ba". Malaminsu mai suna Alqummiy a cikin [tafsirinsa, juzu'i 2, shafi: 75] da wassunsa daga cikin maluma shi'a imamiyyah duk sun ambaci haka.
          Shi kuma babban malaminsu na wannan zamani dake neman haxewar ahlus-sunnah da 'yan shi'a kamar yadda yake riyawa, mai suna: Khumainiy ya bada hukuncinsa ne kan matar annabi (sallallahu alaihi wasallama) da sahabinsa Xalhat da Zubair (Allah ya yarda dasu gabaxaya) da cewa:
(بأنهم أخبث مِن الكلاب والخنازير).
Ma'ana: "Wai sun fi karnuka da aladai dauxa" [kitabux xaharah, juzu'i 3/ shafi: 457].
          Shi kuma xan shi'a da ake kiransa: Muhammadu Jamilu Hamud al,amiliy a cikin littafinsa mai taken: Ha'incin da A'isha tayi; tsakanin kore yiwuwarsa da aukuwarsa [Khiyanatu A'ishah bainal istihalati wal waqi'i, a shafi na: 30-31] cewa yayi:
(الدليل الخامس: لقد دلت الأخبار الكثيرة من طرق المخالفين على أنّ عائشة كانت تفتي برضاع الكبير، والإرضاع مقدمة للزنا قطعًا بل هو من أبرز مقدماته ... وإذا جاز لها الكشف عن نهديها لإرضاع رجل أجنبيّ عنها، جاز لها أنْ تمارس بقية العملية الجنسية معه بكل ارتياح، لا سيما إذا كان المرتضع بارعًا في الامتصاص واللمس؛ بحيث تنسى المرضعة نفسها، فضلا عن حولها، ولا سيما إذا كان المرتضع كطلحة مِن المتيَّمين بعائشة، حتى وصل به الغرام إلى التغزّل بها ولمسها في وليمة لعرس زينب بنت جحش حتى ظهر الغضب على وجه النبي الأكرم).
Ma'ana: "Dalili na biyar: Hadisai ta hanyoyin ahlus-sunnah masu yawa sun nuna cewa A'ishah ta kasance tana bada fatawa kan halaccin shayar da mutum babba, shi kuma shayarwa mataki ne dake gabatar zina, hasali ma shine mafi bayyanar matakai da suke gabatarsa… kuma idan har ta iya bubbuxe nonuwanta don shayar da mutum ajnabiyyinta babba, to ai ta samu dammar ta aikata sauran aiyukan sha'awa tare da shi, a sake, musamman idan shi wanda ake shayarwan ya gwanance wajen iya tsotso da shafe-shafe; ta yadda zai mantar da mai shayar da shi karan-kanta balle abinda yake kewaye da ita, musamman kuma idan wanda ake shayar da shi irin sahabin annabi Xalhat ne; wanda yake haukar son A'ishah; har lamarin sonta ya kai shi izuwa ga faxa mata maganganun batsa, da shafa jikinta, a walimar auren uwar muminai Zainab bint Jahsh, har fushi ya bayyana a fiskar annabi mai karamci".
          Xan shi'an ya ci gaba da tuhumarta a cikin [shafi: 40] a inda yake cewa:
(فالغاية من تحليلها للإرضاع إنما هو الشبق الجنسي الذي كانت تتصف به عائشة؛ فلم يكن بإمكانها الصبر عنه أبدًا).
Ma'ana: "Manufarta na halatta irin wannan shayarwar wai shine jarabar neman saduwar namiji da mace da A'ishah ta siffanta da shi, wanda kuma har abada ba zata tava iya haqura akansa ba".
          A wannan [shafin na: 40] ya ci gaba da cewa:
(ولكنها ابتدعت فتوى إرضاع الكبير ليتسنى لها ممارسة الجنس مع مَن تريد مِن رجال المسلمين).
Ma'ana: "Wai, A'ishah ta qirqiro fatawar shayar da babban mutum ne domin ta samu damar yin zina da wanda take so daga cikin mazajen musulmai". (Mai qarya xan wuta!). Ya kuma sake cewa [a shafi na: 41]:
(وثمَّة قرائن كثيرة تشير إلى أنَّ عائشة كانت أكثر نساء النبيّ الأكرم صلى الله عليه وسلم عُرضة للشائعات الجنسية الطابع، كقصتها مع صفوان بن المعطل السلمي، كما في قصة الإفك).
Ma'ana: "Akwai dalilai da yawa da suke nuna cewa; A'ishah an fi jifanta da maganganun yin lalata fiye da sauran matan annabi mai karamci (sallallahu alaihi wasallama), kamar qissarta tare da Safwan xan Almu'axxal, as-sulamiy, a cikin qissar qiren qarya ta zina".
A [shafi na 47] kuma bayan ya ambato qissishin qarya cewa yayi:
(فيه من الدلالة على تعاطيها قيادة الدعارة في مكة بحسب الظاهر، عندما هجرت المدينة أيام عثمان بن عفان فمكثت في مكة حدود السنتين، وهو غير بعيد في حقها).
Ma'ana: "A cikinsa akwai dalili da ke nuna cewa itace take shugabancin karuwanci a garin Makkah, gwargwadon abin da ya bayyana, a lokacin da ta qaura daga garin Madinah a halifancin Usman xan Affan, ta je ta zauna a garin Makkah kusan shekaru biyu. Wannan kuma ba abu ne da za a ce ba zai yiwu ba a wurinta". A [shafi na: 49] ya qara da cewa:
(مَن كانت بهذه المستوى مِن الجُرأة الجنسية فلماذا يُستبْعد في حقّها صدور الفاحشة بعد موت رسول الله، وقد اتّهمت به في حياته).
Ma'ana: "Matar da lamarin sha'awarta ya kai wannan matsayi to ta yaya za a nisanta yiwuwan faruwar alfasha a wurinta bayan rasuwar manzon Allah, alhalin kuma an tuhume ta da aikata shi tun yana da rai!". Sai kuma a qarshen littafinsa [shafi: 99] ya ke cewa:
(فتحصل مما تقدم: أنّ عائشة خائنة للرسول الأعظم في عقيدته، وخائنة له في فراشه، هذا ما وصلنا إليه بمقتضى سعينا الخالص وجهدنا في البحث والتحقيق لفهم الخيانة الواردة في سورة التحريم، والأخبار، بحق عائشة وحفصة).
Ma'ana: "Sai muka fahimta daga abinda ya gabata cewa: Lallai A'ishah ta ha'inci manzo mai girma ta fiskar aqidarsa (kafirta), ta kuma ha'ince shi a shumfuxinsa (zina). Wannan kuma shine qoqarinmu da bincikenmu saboda mu fahimci lafazin "ha'inci" da ya zo cikin "suratut tahrim", da kuma hadisai, kan A'isha da Hafsah suka kaimu zuwa gare shi".

          'Yan shi'a sun ce: A'ishah (radiyallahu anha) ta kasance baqar mace ce, mummuniya. Don haka:
(فلم تسلَم عائشة رضي الله عنها لا في عِرضها، ولا في إيمانها، ولا في خِلقتها.
فهذا هو معتقد الشيعة الإمامية كافة في أم المؤمنين؛ أنها كافرةٌ، بغيٌ، ابنةُ زنديق).
Ma'ana: "A'ishah –radiyallahu anha- bata kuvuta a wajen 'yan shi'a ba, la ta fiskar mutuncinta, da kuma ta vangaren imaninta, haka kuma ta fiskar sukansu kan halittarta. Wannan kuma shine aqidar 'yan shi'a imamiyyah gabaxayansu akan uwar muminai; ma'ana: ITA KAFIRA CE, a wurinsu MAZINACIYA (KARUWA), 'YAR ZINDIQI (wato: Abubakar as-siddiq)".

          Abin da muka ambata ya wadatar (wajen amsa tambayar da ta gabata), Allah ya qara yarda ga uwar muminai, A'ishah, ya kuma tayar da mu a qiyamah tare da ita, da kuma annabi Muhammadu, da sahabbansa masu karamci da xa'a ma Allah.
Salatin Allah da sallamarsa su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu da iyalansa, da sahabbansa.
          WASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU…
Marubucin wannan bayani
ABDULLAHI XAN MUHAMMADU AS-SALAFIY
Allah ya gafarta masa shi da iyayensa biyu, da xaukacin musulmai
Talata: 26/Shawwal/1431h
Fassarar
Abubakar hamza
Juma'a: 03/04/1436h = 23/01/2015m.

A garin Madinah.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...