2018/05/05

ABABEN DA SUKE LALATA AZUMI مبطلات الصيام


ABABEN DA SUKE LALATA AZUMI
(مبطلات الصيام)
          Azumi wanda shine bauta wa Allah, ta hanyar kamewa daga ci da sha da jima'i, daga fudowar alfijir na gaskiya, har zuwa faduwar rana.

          Kuma WAJIBI NE Musulmi ya kiyaye azuminsa daga ababen da za su lalata shi, wanda kuma sune, ci da sha, da abinda ke daukar ma'anarsu daga ababen da suke baiwa jiki abinci, kamar ruwan da ake dorawa ko allurai masu dauke da abinci, da daukan jini da karinsa, da yin jima'i, da fitar maniyyi ba a cikin barci ba, ko ta hanyar wasa da al'aura (istimna'i), da makamancinsu.
Amma yin mafarkin saduwa (da fitar maniyyi), to lallai basu karya azumi da ijma'in maluma. Haka shima fitan maziyyi –ga zancen da yafi inganci-.

          Haka Yin Amai –da ganganci-, Amma idan amai ya rinjaye shi, to azuminsa ingantacce ne, saboda fadinSa –sallal lahu alaihi wa sallama-:
"من ذرعه القيء فليس عليه قضاء، ومن استقاء عمدًا فليقضِ". رواه أبو داود والترمذي وصححه الألباني في إرواء الغليل.
Ma'ana: "Wanda amai ya rinjaye shi, babu ramuko akansa, Wanda kuma ya janyo amai da ganganci, to ya rama azumi" Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito, kuma Albaniy ya inganta shi, a cikin littafin Irwa'ul galil.
          Yin Kaho, haka kuma bada taimakon jini, Kuma duk wanda ya bukaci bayar da taimakon jini a cikin yini, to ya karya azuminsa, sai kuma ya biya azumi daya, a madadinsa.

          Yana daga abinda ke lalata azumi, da ijma'in maluma Fitan jinin haila ko haihuwa a cikin kowane dakika cikin yini, koda kuwa fitan nasa gabanin faduwar rana ne, da minti daya.

          Wanda ya aikata wani abu daga cikin ababen da suke karya azumi, yana mai jahiltar hukuncin, ko a halin manta shi, ko a halin tilascin da aka masa, to azuminsa ingantacce ne. sai dai haila da jinin biki (nifasi)su kam suna lalata azumi ta ko-yaya.

          Lallai azumi yana da FARILLAI da IYAKOKI, wadanda wajibi ne a kiyaye su. Kuma Allah Ta'alah yana cewa a karshe-karshen jerin ayoyin azumi:
"تلك حدود الله فلا تقربوها، كذلك يبين الله آياته للناس لعلهم يتقون"، [البقرة: 187].
Ma'ana: "WADANCAN SUNE IYAKOKIN ALLAH, KADA KU KUSANCE SU, KAMAR HAKA NE ALLAH KE BAYYANA AYOYINSA GA MUTANE, LA'ALLA SU SAMU TAKAWA", [Bakara: 187].

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...