2017/10/12

ABDULMUHSIN KASIM 23 Muharram 1439 daida da 13 oktoba 2017M










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 23/MUHARRAM/1439H
Daidai da 13 /OKTOBA / 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

       Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da kuma a bayyane.

       Ya ku Musulmai …
            Sunayen Allah sune mafi kyau, SifofinSa kuma mafi xaukaka, kuma ayoyinSa -سبحانه- na halitta, da na shari'a suna nuni akan haka, kuma sun zama shaida.
            Kuma kowane suna da siffan Allah suna hukunta wani nau'i na bauta, da wani lamari, kamar yadda suke hukunta samar da halitta da kasantarwa, don haka, kowane suna da sifa suna da wani dangi na bauta da ta kevance su, wanda yana daga abinda sani ko samun ilimin wannan sunan da imani da shi ke lazimtawa, ko ya hukunta, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yana da sunaye mafiya kyau, sai ku roqe shi da su, kuma ku bar waxanda suke ilhadi a cikin sunayenSa, za a saka musu da abinda suka kasance suna aikatawa" [A'araf: 180].

            Lallai AS-SALAMU suna ne na Allah Ta'alah, wanda ya qunshi dukkan sifofin Allah, ya ke kuma nuni kan tsarkake Ubangiji, da barratarSa daga kowane aibi, da kuma xaukakarSa daga dukkan ababen da ba su dace da darajarSa da kamalarSa da girmanSa ba.
            Allah ya kuvuta daga dukkan cuta, kuma ya barranta daga kowace naqasa, don haka; Allah Shi ne Wanda ya kuvuta daga dukkan aibobi da naqasa, saboda cikar kamalarSa cikin zatinSa da sunayenSa da sifofinSa da ayyukanSa, Allah (سبحانه) ya ce: "Shi ne Allah, Wanda babu abin bautawa daga gaskiya face shi, Mai mulki, Mai tsarki, Tarkakakke, Mai Aminci da amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai nuna isa, Tsarki ya tabbata a gare shi daga abinda suke masa na shirka" [Hashr: 23].

            Cancantarsa (سبحانه) ga sunan (AS-SALAMU), shi yafi cikar kamala daga cancantar dukkan abinda ake kiransa da shi, kuma wannan shine haqiqanin tsarkakewa, Wanda Allah ya tsarkake kanSa da shi, kuma ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) ya tsarkake Shi da shi.

            Shi ne wanda ya tsarkaka daga riqon mata, da xa, kuma ya kuvuta daga kini, da tsara, da kwatankwaci da makamanci, kuma ya kuvuta daga kishiya da abokin tarayya.
            RayuwarSa kuma (Subhanahu Wa Ta'alah) kuvuta ce daga mutuwa da gyangyaxi, da barci.
Tsayayye ne kan halittunSa; sai ya tsarkaka daga gajiya da gajiyawa, da kuma wahala.
IliminSa kuma, ya tsarkaka daga jahilci da gafala da mantuwa.
KalmominSa adalci ne da gaskiya; kuma sun kuvuta daga qarya da zalunci.
Kuma kowace sifa, ta kuvuta daga abinda ke kishiyantar kamalarta, ko ya ke bada wahamin naqasa a cikinta.

Kuma kamar yadda Allah yake tsarkakke cikin zatinSa, da sunayenSa, da sifofinSa, To daga wurinSa Maxaukaki salama da aminci suke, kuma daga gare shi ake neman tsarkaka, Kuma duk wanda ya nemi samun salama daga wanda ba Allah ba, to ba zai same ta ba, sai kamar wanda zai samu ruwan sha daga kawalwalniya, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Ya Allah kai ne Mai tsarki, kuma daga wurinka ake samun tsarkaka, Ya Ma'abocin girma da girmamawa", Muslim ya ruwaito shi.

Ya kuvutar da waliyyanSa da bayinSa daga aqubarSa, kuma ya tseratar da dukkan halittunSa daga zaluncin da ya tsarkake kanSa daga gare shi. Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Allah baya yin zalunci daidai da kwayar zarra" [Nisa'i: 40].
Kuma domin shine Mai tsarki kuma daga wurinSa ake samun tsarkaka ya zama ba za a ce: TSARKI YA TABBATA GA ALLAH BA, Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Kada ku ce: Tsarki su tabbata ga Allah, saboda Allah shine Tsarkakakke", Bukhariy ya ruwaito shi.
Ya yi sallama ga AnnabawanSa da ManzanninSa, saboda tsarkakar abinda suka faxa, daga tawaya da aibi, Allah ya ce: "Tsarki ya tabbata ga UbangijinKa, Ubangijin rinjaye, daga barin abinda suke siffantawa * Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni" [Safatti: 180-181].
Sai kuma ya rubuta aminci ga bayinSa salihai, Ya ce: "Ka ce: godiya ta tabbata ga Allah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bayinsa, Waxanda ya zava" [Naml: 59].
Kuma ya keve wanda ya so daga cikin talikai, da sallamar aminci, kamar annabi Nuhu da Ibrahim da Musa da Haruna, da Ilyasina.
Kuma Allah ya karrama annabinSa Yahya (عليه السلام) ya keve shi da aminci, a wurare ukun da halittu suka fi kasancewa da matsanancin kewa a cikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, da ranar da yake mutuwa, da ranar da ake tayar da shi; rayayye" [Maryam: 15].

Kuma Allah Ta'alah ya shar'anta wa bayinSa addinin da a cikinsa akwai shiriya da aminci, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai addini a wurin Allah shine musulunci" [Ali-imrana: 19].
Hukunce-hukuncensa da aqidunsa sun kuvuta daga qari da ragi, Allah Ta'alah ya ce: "A yau, na kammala muku addininku, kuma na cika ni'imata akanku, kuma na yarda da musulunci ya zama addini a gare ku" [Ma'ida: 4].
Kuma cikin bin wannan addinin tsira a duniya da lahira suke kasancewa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya" [Daha: 47].
Kuma qarshen makomar ma'abuta musulunci ita ce; Aljanna; gidan aminci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yana kira zuwa ga gidan aminci, kuma yana shiryar da wanda ya ke so zuwa ga tafarki madaidaici" [Yunus: 25].
Kuma duk wanda ya ke son aminci da salama ga kansa da iyalansa da al'ummarsa, sai ya yi riqo da addinin musulunci, domin shari'oinsa da aqidodinsa aminci ne da walwala da xebe kewa da natsuwa .
Kuma duk lokacin da wata al'umma ta qara riqo da musulunci, sai aminci da zama lafiya su mamaye ta, "Waxanda suka yi imani, kuma basu gauraya imaninsu da zalunci ba, waxannan suna da aminci, kuma sune shiryayyu" [An'am: 82].
Kuma amincin wannan addinin ya game dukkan halitta da izza da xaukaka.

Rayukan ma'abuta musulunci da dukiyoyinsu da mutuncinsu kiyayayyu ne, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "An umarce ni da na yaqi mutane, har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya face Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, kuma su tsayar da sallah, su bada zakkah, idan suka aikata haka, sun kare jinanensu da dukiyoyinsu daga gare ni, kuma sakamakonsu yana kan Allah" Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma duk wani tsoratarwa da za a yi ga wanda shari'a ta bashi kariya, to akwai narkon azaba akansa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya xaga wani qarfe ga xan'uwansa, to lallai Mala'iku suna la'antarsa, har sai ya ajiye shi, koda xa'uwansa ne ta wajen uwarsa da ubansa" Muslim ya ruwaito shi.
Kuma suma rayukan kafiran alqawari da amana da waxanda aka aminta da su, ababen girmamawa ne, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji qamshin Aljjana ba", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma har awaki da dabbobi, musulunci ya zo da abinda ya tabbatar da amincinsu da salamarsu, Sai "Wata mata ta shiga wuta saboda kuliya" Bukhariy da Muslim. "Karuwa kuma, da ta shayar da kare sai aka gafarta mata", Bukhariy da Muslim.

Kuma Musulmi an umarce shi da yaxa aminci da salama a tsakanin halittu; da aikinsa da kuma maganganunsa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Musulmi shine wanda musulmai suka kuvuta daga harshensa da hannunsa" Bukhariy.

Kuma babbar alama ta zaman lafiya ita ce, da'awa zuwa ga Allah, da sanar da mutane wanene Ubangijinsu, da annabinsu da addininsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanene mafi kyau ga magana, daga wanda ya yi kira zuwa Allah, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma ya ce: Lallai ni ina daga musulmai" [Fussilat: 33].

Kuma Allah ya yi yabo ga wanda ya nemi zaman lafiya da jahili, kuma ya fiskanci wanda ya munana da aiki mai kyau, a inda ya ce: "Kuma idan jahilai suka yi magana da su, sai su ce, salama; a zauna lafiya" [Furqan: 63].

Kuma yana daga MANYAN ALAMOMIN WANNAN ADDINI GAISUWAR NEMAN AMINCI, ta hanyar ambato sunan Allah Ta'alah; AS-SALAM, da neman aminci daga wurinsa, tare da qulla alqawarin musulmi ba zai samu sharri daga mai yin sallama, ko wata cutarwa ba, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Yahudawa basu muku hassadar komai irin yadda suke muku hassada akan yin sallama da faxin: Amin", Ibnu-Majah ya ruwaito shi.

Kuma ita ce gaisuwar da Allah ya yarda da ita ga annabi Adamu da zurriyarsa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce, dangane da farkon halittar Adamu: "A yayin da ya halicce shi, sai ya ce: Je, ka yi sallama ga taron Mala'ikun da suke zaune, sai ka ji abinda za su gaishe ka da shi, saboda shine gaisuwarka da gaisuwar zurriyarka, Sai ya ce: ASSALAMU ALAIKUM, Sai suka ce: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI, Sai suka qara: WA RAHMATULLAH", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma musulunci ya kwaxaitar kan fara yin sallama, "Kuma wanda ya fi mutane kusanci da Allah, shi ne wanda ke fara sallama a gare su", Abu-dawud.

Kuma an umarci mutane da aikin yaxa sallama, Bara'u bn Azib (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya umarce mu da abu bakwai, daga cikinsu akwai yaxa sallama", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma yana daga hanyoyin yaxa musulunci, Abdullah ibn Salam (رضي الله عنه) ya ce: Farkon isowar Annabi (صلى الله عليه وسلم) farkon abinda ya fara faxa shi ne:  "Ya ku mutane! Ku yaxa sallama, kuma ku riqa ciyar da abinci, ku yi salla alhalin mutane suna barci, za ku shiga Aljanna da aminci", Tirmiziy ya ruwaito shi.

Kuma Allah ya bada umarnin a maida sallama da kwatankwacinta, ko da abinda ya fi ta, a inda ya ce: "Kuma idan aka gaishe ku da wata gaisuwa, sai ku yi gaisuwa da abinda yafi ta kyau, ko ku mayar da ita" [Nisa'i: 86].
Ibnu-Kasir –Allah ya yi masa rahama- ya ce: "Yin qarin mustahabbi ne, faxin irin abinda mai sallamar kuma ya faxa, wajibi".

Yin sallama yana daga mafi alherin xabi'un musulunci da kuma mafi girman ressansa, saboda wani Mutum ya tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wane aikin musulunci yafi alkhairi? Sai ya ce: Ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda ka sani, da wanda baka sani ba", Bukhariy da Muslim.

Kuma duk wanda ya yi sallama za a rubuta masa ladan kyawawan aiki guda goma, har zuwa talatin, saboda wani mutum ya zo wurin Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ya ce: ASSALAMU ALAIKUM, Sai ya amsa masa sallama, sa'annan ya zauna, sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: goma. Sai kuma wani ya zo ya ce: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI, Sai ya amsa masa, sai ya zauna, sai ya ce: ashirin. Sa'annan sai wani ya zo ya ce: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU, Sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: talatin. Abu-dawud ya ruwaito shi.

Fara yin sallama da amsata, yana daga haqqoqin musulmai sashensu akan sashe, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Haqqoqin musulmi akan musulmi guda shida ne, daga cikinsu, idan ka haxu da shi, ka masa sallama", muslim ya ruwaito shi.
A wajen Bukhariy kuma "da amsa sallama".
"Kuma bai halatta musulmi ya qaurace wa xan'uwansa musulmi ba, fiye da kwanaki uku, har su haxu, wannan ya kawar da kai, wannan ya kawar da kai. Kuma mafi alherinsu shi ne wanda ya ke fara sallama" Bukhariy da Muslim.
Watsa sallama bayyanar da aminci ne, kuma qarin danqon qauna da soyayya a tsakanin halittu, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Na rantse da wanda raina ke hannunsa, ba za ku shiga Aljannah ba, har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba face kun so juna, Shin ba zan nuna muku abinda idan kuka aikata shi za ku so juna ba? Ku riqa yaxa sallama a tsakaninku", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma cikin yin sallama akwai saukar alkhairi da albarka, Allah Ta'alah ya ce: "…Sai ku yi sallama ga kayukanku, gaisuwa daga Allah mai albarka, daddaxa", [Nur: 61].
Kuma amsa sallama yana daga haqqin hanya ga wanda ya zauna a gefensa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Ku kiyayi zama akan hanyoyi, Sai su ka ce: Bamu da makawa; saboda wuraren zamanmu ne da muke tattaunawa a cikinsu, Ya ce: Idan kuka qi, sai waxannan wuraren zaman, to ku bayar wa hanya haqqinta, suka ce: To menene haqqin hanya? Sai ya ce: Runtse gani, da kamewa daga cutarwa, da amsa sallama, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna", Bukhariy da Muslim.

Kuma yana daga laddubansa, Qarami ya yi sallama ga babba, mahayi kuma ga mai tafiya, mai tafiya kuma ga na zaune, kaxan kuma ga masu yawa.
Sallama kuma ana game ta ga wanda mutum ya sani, da wanda bai sani ba, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai yana daga alamomin qiyama, mutum ya yi sallama ga mutum, ba komai ya sashi yin sallama ba, sai sanayya", Ahmad ya ruwaito.
Kuma sahabbai sun kasance, suna qirga yin sallama ga kowa, daga cikin imani, Ammar bn Yasir (رضي الله عنه) ya ce: "Abubuwa uku, wanda ya haxa su, to lallai ya haxa imani, Yin adalci wa kanka, da yin sallama ga duniya, da ciyarwa a lokacin talauci".

Kuma an shar'anta maimaita sallama, idan akwai buqatar hakan, Anas (رضي الله عنه) ya ce: "Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan zai yi sallama ya kan yi sau uku", Bukhariy.

Kuma yin sallama ga qananan yara sunna ce ta Annabi, kuma cikin hakan, akwai tawali'u, da tausasa mu'amala tare da yara, da koyar da su yin aiki da ladduban shari'a, An ruwaito daga Anas bn Malik (رضي الله عنه) lallai shi ya wuce wasu qananan yara sai ya musu sallama, sannan ya ce: "Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana aikata hakan", Bukhariy da Muslim.
"Kuma idan xayanku ya haxu da xan'uwansa, to ya masa sallama, idan bishiya ta shiga tsakani, ko katanga ko dutse, sa'annan sai ya sake haxuwa da shi, to ya sake sallama a gare shi", Abu-dawud ya ruwaito shi.
To, kuma kamar yadda yin sallama an shar'anta shi ga hanyoyi, to yinsa a majalisosi shari'a ne, a lokacin shiga majalisosin da lokacin fita daga cikinsu, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan xayanku ya iso majalisa, to ya yi sallama, idan kuma ya yi nufin ya tashi, ya sake sallama, saboda ta farkon bata fi ta qarshen cancanta ba", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma gaisuwar musulunci ta hanyar faxin ASSALAMU… ta kevanci  musulmai ne kawai, saboda Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Kada ku fara yin sallama ga Yahudawa da Nasara", Muslim ya ruwaito. "Kuma idan Ahlul kitabi suka muku sallama, sai ku ce: kuma WA ALAIKUM", Bukhariy da Muslim.

Kuma mustahabbi ne a xaga sauti a lokacin sallama, gwargwadon yadda za a iya ji, Abdullah ibn Umar (رضي الله عنهما) ya ce: "Idan ka zo yin sallama ka jiyar, saboda ita gaisuwa ce, daga Allah mai albarka mai daxi", Bukhariy ya ruwaito shi cikin Adabul Mufrad.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana shigowa da dare, sai ya yi sallamar da ba za ta tayar da mai barci ba, kuma wanda ke farke zai ji", Muslim ya ruwaito.
Kuma babu abinda ke hana sallama ko amsata, in banda huxuba, saboda wajabcin a saurare ta, da kuma lokacin biyan buqata, saboda (makewayi) ba wurin gaisuwa da zikiri ba ne.

Kuma sallama aminci ne da addu'a. Kuma yana daga cikin kyan musulunci da cikarsa, yadda ya sunnanta yin haka ga rayayyu da matattu, kuma babu wanda yafi buqatar addu'a fiye da mutumin da ya mutu,.
Kuma yana daga shiriyarSa (عليه الصلاة والسلام) idan ya zo maqabarta ya kan ce: "ASSALAMU ALAIKUM DARA QAUMIN MU'UMININA", Muslim ya ruwaito.

Kuma gaisuwar muminai daga Ubangijinsu a lahira ita ce, salamar aminci, Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma gaisuwarsu a ranar da za su haxu da shi ita ce, SALAM", [Ahzab: 44].
Masauqansu kuma Aljanna gidan aminci, kuma babu mutuwa a cikinta, kuma babu vacin rai, babu baqin ciki, babu cutuka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna da gidan aminci a wurin Ubangijinsu" [An'am: 127]. Kuma za a riqa ce musu: "Kuma ku shige su da salama kuna masu aminci", [Hijr: 46].
Kuma za a bubbuxe musu qofofin Aljanna, sai masu gadinsu su zo tarbarsu, suna masu cewa: "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji daxi, ku shige su kuna masu dawwama" [Zumar: 73].
Kuma idan suka shiga cikin Aljannoni, "Ba su jin wata yasassar magana a cikinta, kuma ba su jin sun yi laifi * sai dai magana mai daxi, salamun, salamun", [Waqi'a: 25-26].
"Suna masu dawwama a cikinsu, da izinin UbangijinSu, gaisuwarsu ita ce, salamun", [Ibrahim: 23].
"Kuma Mala'iku suna shiga musu ta kowace qofa * (suna cewa) aminci ya tabbata akanku, Madalla da ni'imar aqibar wannan gida", [Ra'ad: 23-24].

Kuma idan 'yan Aljanna suka shagaltu da abinda Allah ya ni'imta su a cikin Aljannoni, to cikar ni'imtuwarsu tana cikin ganin da za su yi ga Ubangijinsu, da sallamar da zai musu, Allah Ta'alah ya ce: "AMINCI, zance ne daga Ubangiji Mai jin-qai", [Yasin: 58].

          BAYAN HAKA,
YA KU MUSULMAI!
            Addinin Allah ya qunshi karantarwa a gaba xayan rayuwa, kuma ya dace da kowane zamani da kowane wuri, kuma cikin hukunce-hukuncensa gyaruwan lamuran duniya da lahira da walwalar dukkan mutane suke, yana kira zuwa ga samun aminci, kuma ya kawo tabbaci kan samun jin-qai a tsakanin halittu.
Kuma a cikin kowane lamari yana shiryarwa zuwa ga hanyar da ta fi miqewa.
Wanda ya yi riqo da musulunci ya samu babban rabo, kuma ya xaukaka, wanda kuma ya yi sakaci wajen binsa ya yi hasarar kansa, kuma bai cutar da Allah da komai ba.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Ya ku waxanda su ka yi imani, ku shiga musulunci gaba xaya, kada ku bi hanyoyin Shaixan, saboda shi maqiyi ne a gare ku mai bayyana adawa" [Baqara: 208].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …
             

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa; 
Godiya tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Ya Allah, ka yi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
            Sanin sunayen Allah da sifofinSa shine ilimin da ya fi xaukaka.
Kuma da wannan ilimin ake isa ga son Allah da girmama shi, da tsoronsa, da fatan samun abinda ke wurinsa.
Kuma duk lokacin da ilimin bawa (ta wannan fiskar) ya qara qarfi, sai ya qara fiskantar Allah, ya kuma lazimci aiki da umarninsa da hanuwa da haninsa.
Kuma bauta, da dukkan nau'ointa tana komawa ne ga ababen da sunayen Allah da sifofinSa suke hukuntawa.
Kuma qarshen sa'ada da walwala da kuma samun darajoji maxaukaka, suna cikin tafiya zuwa ga Allah ta wannan hanyar (bauta wa Allah ta hanyar sunayensa da sifofinsa).
Kuma Allah (سبحانه) yana son sunayenSa da sifofinSa, kuma yana son bayyanar tasirin sunayen a cikin halittunSa.
>>> 

            Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].

            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,             Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.

                Bayin Allah!!!

                "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...