2019/09/20

HARE HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS Hudubar 21 Muharram 1441 Dr Abdulbariy dan Awwadh












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HARE-HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS
(الأحداث في البقيق والخريص)
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh  AsSubaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HARE-HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye a bayan kasa ne, na manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowar dukiya masu yawa, a karkashin kulawar Mutane, domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].
Kuma dukkan umurni da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin tabbatar da ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma domin umurni da hani a shari'a  suna komawa ne ga/ Kiyaye manufofin shari'ar, a cikin halittu. Kuma wadannan manufofin dole babu makawa, sai an basu kulawa, gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka rasa su, to maslahohin Duniya ba za su tabbatu ba.
Musulunci ya rataya mafi tsananin azaba, akan kawo barna a ban kasa; kuma duk wanda ya yi barna a bayan kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci ne.
Matsala zata iya samun Mutane saboda makircin makirai, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi, wannan kuma domin Allah ya jarrabi Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewar su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan asalin tushensu.  Kuma hakikanin al'ummomi yana bayyana ne a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma (bayan ibtila'i) sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa, himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiya ko gudanar rayuwa, a'a al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai hare-hare masu radadi da suka auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijrah da Kharis, kuma suka yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa na wannan al'ummar, aiki ne abin kyama, Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma ba za su samu muradinsu na barna ba, kuma da falalar Allah, sannan da fadakar shugabannin wannan kasa, da azamar jami'an tsaronta da masu gadin iyakoki, hare-haren za su koma da asara mabayyaniya.
Kuma idan masu barna da 'yan rushe-rushe suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi ta'addanci, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasar da bunkasata ya cigaba.

Duk da wadannan hare-haren kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa aminci da zaman lafiya.

Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin neman a tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta tun a farkon fari, ana mata haka domin ita ce cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya -masu aikin wofi- su sani, lallai ba za su iya rushe tsaron wannan kasar ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba, domin kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana tsananin yakar ta'addanci; kuma saboda alakokin 'ya'yanta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar Allah ganuwa ce mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin kiyayewarsa, sakamakon daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune ginshikin hukuncinta, mabubbuga ga shari'arta, salo kuma ga rayuwarta, matabbatan samun iko a cikinta, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shi zai sanya al'amarin tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta karfinsa, kuma Mutane suna fatan ganin bunkasarsa.

Danganta kai ga kasarka al'amari ne wanda a al'adance aka dasa shi a jikin Mutane, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro ta daga danganta kai ga addini, sai su tafi a tare, Kuma yaya Mutum ba zai kaunaci kasar da yake rayuwa akanta ba, ya taso a kan turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da tarihinta? Kuma yaya ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki domin dakatar da masu ta'addanci a gare ta ba?
Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa al'amarin tsaronsu da dukkan nau'ukansa, sai ya karfafa dangatakar 'yan kasar ta cikin gida, wanda kuma hakan shine zai kare su, daga wanda yake son kunno fitintinu da tashin-tashina a cikin kasarsu.

Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata, shine hanyar samun nasara, da daukaka, kuma shine sinadarin samun karfi, da natsuwa da zaman lafiya. kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawa suke raunata kulle-kullen makirci, suke dauke abu mai cutarwa.

Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, ta Saudiya, shine ginshikin amincin al'ummar Musulmai, saboda Saudiya ita ce zuciya mai bugawa na al'ummar, kuma guzurin al'umma mai tunkuda. Kuma lallai munana wa kasar nan munanawa ne ga zaman lafiyar daukacin Musulmai. Kuma gangar jikin al'umma ba zai gushe yana cikin alheri ba, matukar zuciyarta tana bugawa, domin alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani basu yankewa. Kuma hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasar, da kare ta daga makircin makiya da kaidin masu kaidi, abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumowa da wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana hidima ne ga makiyan Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako. Kuma duk yadda kiraye-kiraye barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare ta ya yawaita, to lallai barna gininsa mai girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].

Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk yadda masu kaidi suke kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci, masu jiran ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai wannan kasar mai kariya ga harami biyu, gininta yana nan da karfinsa, madaukaki, wanda zai gagari makiya, Mai neman ya taba girman kasar zai kaskanta, mai adawa da ita zai fadi ya wulakanta, wannan kuma babu makawa akansa, saboda Musulunci shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta, kuma lallai daukakarta yana karkashin bin addininta, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: "Mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai Allah ya daukaka mu da Musulunci".

Zarata akan iyakokinmu suna yin zaman dako (ribadi), suna kiyaye addini da kasa, suna gwabzawa da makiyansu suna lankwame su, kuma basu girgiza, cikin kudurinsu, suna masu karfi da azamarsu da zukatansu, domin yanke (katse) karshen masu ta'addanci, da kakkabe ko buge makamansu na barna.
A nan, Muna jinjina ga gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasarmu, da wargaza tsare-tsarensu tun a farkon fari. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sai su yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Kuraish: 3-4].

Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Mumini a lokacin tsanani da fitintinu, alakarsa da UbangijinSa tana kara karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da MajibincinSa, yana neman fakewa a mafakarSa, "Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa ga Allah, da nuna masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta.
Kuma idan Musulmii ya bayyana bukatarSa ga MajibincinSa, to ya hada bukatarsa da aiki da kuma lazimtar addu'a, kuma lallai Allah ya yi alkawarin amsa addu'ar wanda ya roke shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga Allah, to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za ta samu gurbi ba a zuciyarsa, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma zuwa gare shi lamura suke tafiya.

Kuma Al'ummar Musulmai za su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana hasashen zuwa lokaci na gaba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu cewar Allah zai cika alkawarinsa, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya kaddara ga dukkan komai" [Dalak: 3].

2019/09/18

د ثبيتي 21 المحرم 1441 إن الله لا يصلح عمل المفسدين Hudubar












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
I
(إن الله لا يصلح عمل المفسدين)
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh  AsSubaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: K, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Bayan haka:
Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye su a bayan kasa, na manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowan dukiya masu yawa, a karkashin kulawan Mutane domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].

Kuma dukkan umurni da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin su tabbatar ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma saboda kallafe-kallafen shari'a (umurni da hani)  suna komawa ne zuwa ga kiyaye manufofinta a cikin halittu. Wadannan manufofin kuma babu makawa sai an kula da su gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka rasa su maslahohin Duniya ba za su tsayu ba.
Musulunci ya rataya mafi tsananin narkon azaba, akan kawo barna a bayan kasa; kuma duk wanda ya kawo barna a bayan kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci ne.
Matsala zata iya samun Mutane saboda makircin masu makirci, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi, wannan kuma domin Allah ya jarrabi bayinsa Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewarsu su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan asalin tushensu.  Kuma hakikanin al'ummomi yana bayyana a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa, himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiyar tayu na rayuwa, a'a al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai musiba mai radadi wanda ya auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijratu Kharidh, kuma ya yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa da wannan al'ummar, aiki ne abin kyama, ya nuna wauta da jahilci da rashin hankalin wanda ya sanya ha'inci ya zama mazhabarsa, cin amana kuma dabi'arsa, makirci da yaudara kuma suka zama al'amarinsa. Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma ba za su samu muradinsu na barn aba, kuma da falalar Allah za su koma da asara mabayyaniya, haka kuma da fadakar jagororin al'amarin wannan kasa, da azamar jami'an tsaro da masu gadi iyakoki.
Kuma idan masu barna da 'yan rusau suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi ta'addanci akan mallakin al'umma, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin sanya iyaka ga wawayen hankula da makirce-makirce masu munanan manufofi da tottoshe kafofin masu makiya, da gyara abinda abinda ya karkace, sai amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasa da bunkasata ya cigaba.

Duk da wadannan musibun kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa aminci da zaman lafiya.

Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin a tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta, domin itace cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya masu aikin kawai su sani, lallai su ba za su iya rushe tsaron wannan kasa ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba, domin wannan kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana da tsananin fada da ta'addanci; domin alakokinta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar Allah ganuwa ne mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin kiyayewarsa, saboda tana daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune ginshikin hukuncinta, kuma mabubbugar shari'arta, kuma salon rayuwarta, kuma matabbata ga samun gindin zama, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shine zai sanya tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta al'amarin karfinsa, kuma rayuka suna fatan ganin bunkasarsa.

Danganta kai ga kasarka al'amari ne da aka dasa shi a jikin Mutane a al'adance, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro shi daga danganta kai ga addini, sai ya tafi tare da shi, Kuma yaya Mutum ba zai so kasar da yake rayuwa akantaba, ya taso aka turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da tarihinta? Kuma yaya Mutum ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki don hana masu ta'addanci a gare ta ba?

Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa lamarin tsaron kasar da dukkan nau'ukansa, sai ya samar kuma karfafa dangatakar 'yan kasan na cikin gida, wanda zai kare ta, daga wanda yake son kunno fitintinu da tashin-tashina a cikin kasar. Kuma yana daga abinda hakan yake hukuntawa:
Son kasarsa, da aiki tukuru dominta, da kada dan kasa ya zama kafa ga masu nufinta da sharri, ko duk wanda yake nufinta cutar da ita. Sannan ya yi kokari wajen duk wata maganar da zata kashe wata fitina, ko ta haifar kyakkyawan fata, ta kiyaye tsaro ta karfafa zaman lafiya, ta toshe kofar bala'i da tashin-tashina, ta rinjayar da maslahar kasa, ta karfafa alakokin al'umma. Wannan kuma yana hukunta kada ka amsa wa masu tsegumi da ma'abuta tutotin karya, wadanda nufinsu shine sace guiwa, da kawar da hadin kan jama'a da rushe abinda kasa ta samar kuma al'umma take girmamawa.

Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata shine hanyar samun nasara, da daukaka, kuma shine ginshikin samun karfi, tare da natsuwa da zaman lafiya, kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawar Allah yake raunata kulle-kullen makirci, yake dauke abu mai cutarwa.

Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, wato masarautar larabawa ta Saudiya, shine ginshikin amincin wannan al'umma (Musulmai), saboda Saudiya ita ce zuciyarta mai bugawa, kuma guzurinta mai tunkuda. Kuma lallai munana mata munana wa zaman lafiyar Musulmai ne (gaba daya). Kuma gangar jikin al'umma ba zai gushe ba yana cikin alheri matukar zuciyar tana bugawa, don haka, alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani kuma basu yankewa. Kuma hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasa da kare ta daga makircin makiya da kaidin masu kaidi abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumawa da wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma duk wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana hidima ne ga makiyan addinin Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako,Kuma duk yadda kiraye-kiraye barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare shi ya yawaita, to lallai barna gininsa mai girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].

Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk yadda masu kaidi suka kullo kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci, masu dakon ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai wanna kasar mai bada kariya ga harami biyu, tana nan da karfinta, madaukakiya, gagararriya, wanda ya nemi ya taba girmanta sai ya kaskanta, wanda ya yi adawa da ita zai fadi ya kaskanta, wannan kuma babu wata ruduwa a cikin haka, saboda Musulunci shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta mai karfi, kuma daukakanta yana karkashin bin addini, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi ya ce-: "Mu mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai Allah ya daukaka mu da Musulunci".

Da zaman dako (ribadin) zarata akan iyakoki, masu kiyaye addini da kasa, suna gwabzawa da makiya suna lankwame shi, kuma su basu girgiza, cikin kudurinsu, masu karfi da zamarsu da zukatansu, domin katse karshen masu ta'addanci, da bugu ga makaman barna.
Kuma muna yin jinjina kan gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasa, da wargaza tsare-tsarensu tun suna farko. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sais u yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Kuraish: 3-4].

Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Mumini a lokacin tsanani da fitintinu alakarsa da Ubangiji tana kara karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da Majibincinsa, ya nemi fakewa a mafakarSa, "Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa zuwa ga Allah, da nuna masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta. Kuma idan Musulunci ya bayyana bukatarSa ga Majibincinsa, to sai ya hada bukatarsa da aiki da kuma lazimtar addu'a, kuma lallai Allah yay i alkawarin amsawa duk wanda ya roke shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga Allah to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za ta samu gindin zama a zuciyarsa ba, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma zuwa gare shi ake mayar da lamura.

Kuma Al'ummar Musulmai za su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana has ashen zuwa lokaci nag aba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu da cika alkawarin Allah, Allah Ta'alah ya ce:   "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai" [Dalak: 3].


Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,




2019/09/06

tsakurowa daga hudubar Dr Abdullahi Albuaijan ta Haramin Madina 7Muharram 1441H


KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI
1-   Lallai cikin juyawar yini da dare, da saurin zamani da canzuwan halaye, da zuwan sabin shekaru, da yadda ajali ke kokarin riskar ma'abutansa, dukansu dalili ne akan al'amarin gushewa da makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da buri: "Allah yana juyar da dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
2-   Mafi alherinku shine wanda rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi sharri kuma shine wanda rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni. Kuma daga cikinku kowa za a tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da samartakarsa ta yaya ya tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci, da mafi girman lokatai!
3-   Ku sani, lallai Allah ya zabi zababbu daga halittunSa, sai ya zabi manzanni 'yan aika daga cikin Mala'iku, suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga cikin magana kuma ya zabi ambatonsa, a doron kasa kuma ya zabi masallatai, daga cikin watanni kuma ya zabi watan Ramadhana da watanni masu alfarma, daga cikin kwanaki kuma yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai ku rika girmama abinda Allah ya girmama!
4-   Ku saurara! Lallai ga ku a farkon watan Muharram, kuma farkon shekarar hijira, kuma lallai wannan watan yana cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda Allah ya girmama su, ya ce: "Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha biyu, a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga cikinsu akwai hudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku zalunci  kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
5-   Hakika Musulmai tun zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin hijirar Annabi -SAW- daga garin Makkah zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi da shekarar hijira, saboda Allah ya rarrabe tsakanin gaskiya da barna da al'amarin hijira. Kuma sahabbai sun fari kidayar shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya tabbatu akan haka, kuma sai al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.
6-   An ruwaito daga Ibnu-Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –SAW– yana kirdadon yinin da ya fifita shi akan waninsa ba, fiye da wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana nufin watan Ramadhana", Bukhari da Muslim.

HUDUBAR MADINA A TAKAICE DR ABDULLAHI ALBUAIJAN KAN Kwadaitawa kan ribatar lokatai 7Muharram 1441H


1-   Ku ribaci damar shekaru da rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kanku, kada ku rika jinkirta aiki, domin cikin hakan akwai hana rai aikin kwarai, sai ku ribaci rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa da ayyuka, da wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta.
2-   Shekara ta kare, an rufe ayyukanta, an nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci damarsa, ya mori lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
3-   Lokatan rayuwa dama ne na yin aiki, kuma ni'ima ne da suke hukunta godiya, "Idan za ku nemi kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim: 34]. Kuma lokaci yana wucewa, rayuwar kadan ce, ayyukan wajibai wani akan wani, hakkoki kuma suna dayawa, don haka; babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin hutawa da sakaci.
4-   Ku ji tsoron Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma ku tabbatar da zantukanku da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum ita ce abinda ya tafiyar da ita a cikin biyayyar Allah, kuma "Mai hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai kuma yake kwallafa wa Allah buri".
5-   Lallai zalunci –Ya ku Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya girmama alfarmar watanni hudu masu alfarma, sai ya sanya aikata zunubi a cikinsu yafi girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin shima yafi girma.
6-    A cikin Sahihu Muslim, lallai Annabi –SAW- ya ce: "Azumtar yinin Arafah, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take gabaninsa da wanda take a bayansa. Azumtar yinin Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take a gabaninsa".

2019/09/05

DR. BUAIJAN 7 MUHARRAM 1441 الحث على اغتنام الأوقات












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 7/MUHARRAM/1441H
daidai da 6/SEFTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI
(الحث على اغتنام الأوقات)
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allahn da ya halitta dukkan komai, kuma ya kaddara shi kaddarawa, kuma ya sanya dare da yini akan yanayin mayewa ga wanda yake nufin ya yi tunani ko yake son ya yi godiya.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi xaya Makadaici, bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya kasance tamka a gare shi.
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa amintacce, ya isar da manzanci, kuma ya sauke amana, yay i nasiha ga al'umma, ya yi jihadi a al'amarin Allah iyakar jihadi, har mutuwa ta zo masa.
Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu da shiriyarsa, ya bi sunnarsa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:
Lallai mafi gaskiyar zance shine littafin Allah, kuma mafi karfin igiya ita ce Kalmar takawa, mafi alherin addinai addinin annabi Ibrahima, kuma mafi kyan kissosi Alkur'ani, kuma mafificin shiriya shiriyar annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma mafi sharrin al'amura sune kirkirarrunsu, kuma kowace bidi'a bata ce.
Ya ku, Bayin Allah…
Ku yi takawar Allah cikin abinda ya bada umurni, kuma ku hanu daga abinda yay i hani kuma ya tsawatar, "Yak u wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Lallai cikin juyawar yini da darare, da saurin zamani da canzuwa halaye da sabuntar shekaru, da yadda ajalin yake riskar, dukansu dalili ne akan gushewa (mutuwa) da al'amarin makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da burace-burace: "Allah ya juyar da dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
Ka yi tunani akan Duniya da idon basira
Za ka ga walakantacciyar Duniya ta shude kamar a mafarki

Wanda suke cikinta gaba dayansu lallai za su kare
Sai fiskar Ubangijinka Ma'abucin girma ta wanzu

: "Lallai a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da yini, da jirage wadanda suke gudana a cikin take da abinda yake amfanar Mutane, da abinda Allah ya saukar daga sama na ruwa, sai ya rayar da kasa da shi a bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikin kasa daga dukkan dabba, kuma da juyawan iskoki, da girgijen da aka hore a tsakanin sama da kasa, cikinsu gaba daya, akwai ayoyi ga Mutane masu hankalta" [Bakara: 164].
Ya ku taron Musulmai!!!
Kowace shekara ana kaddarata da lissafi, sai a sassaka lokatan kaddara a cikinsu, da ajalin yara da tsofi da samari, kuma ba a tsawaita shekarun mai shekara, kuma ba a tauye wani abu daga rayuwarsa, face yana cikin littafin (kaddara).
Tsareku suna karewa, burace-burace suna yankewa, ajali yana karewa, kuma "Kuma dukkan wanda ke kan kasa mai karewa ne * kuma fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karamci it ace take wanzuwa" [ArRahman: 26-27].

Sai ku ribaci damar shekaru da rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kayukanku, kuma kada ku rika jinkirta aiki, domin cikin haka akwai haka rai aikin kwarai, sai ku ribaci rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa, da wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta, "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga ubangijinku, kuma ku sallama masa, gabanin azaba ta zo muku, alhalin ku ba za a taimake ku ba * kuma ku bi mafi kyan abinda aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku gabanin azaba ta zo muku bisa auke, alhalin ku baku sani ba * sai rai ta ce: Ya nadamata akan abinda nayi sakaci a cikin sashen Allah, kuma hakika na kasance daga masu izgili * ko kuma kada ta ce: Da Allah ya shiryar da ni, da na kasance daga masu takawa * ko kuma kada a lokacin da take ganin azaba ta ce: Da ace ina da wata komawa (ga Duniya), domin in kasance daga cikin masu kyautatawa" [Zumar: 54-58].

Ya ku Musulmai!!!
Shekara ta kare, an rufe ayyukanta, kuma na nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci damarsa, ya mori lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
Ku saurara! Lallai mun shiga farkon sabuwar shekara, wanda hakan yake raka mu zuwa kaburbura, yake tafiya da mu zuwa yinin tayarwa bayan mutuwa, to ya dace da mu, al'amarin tafiyar da rayuwarmu cikin biyayyar Allah, "Kuma duk abinda kuka gabatar da shi na alheri za ku same shi a wurin Allah" [Muzzammil: 20].

Ya ku Bayin Allah!!!
Mafi alherinku shine wanda rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi sharrinku kuma shine wanda rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni.
Kuma kowa daga cikinku za a tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da samartakarsa ta yaya ya tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci, da mafi girman lokatai!
Dauki cewa, kuruciya tana bayyanar da uzurin ma'abucinta!
To menene uzurin masu furfurar da Shedan ya batar da su?

Ya ku taron Musulmai!!!
Lokatan rayuwa dama ne na yin aiki, kuma ni'ima ne da yake hukunta godiya, "Idan za ku nemi kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim: 34].
Kuma lokaci yana wucewa, kuma rayuwar kadan ce, ayyukan wajibai lodi-lodi ne, hakkoki kuma suna dayawa, don haka babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin hutawa da sakaci,
Ya ku bayin Allah! Ku ji jankunne mai tsoratarwa, da tattaunawa mai kama kunne, a inda AllahTa'alah zai tambayi bayinsa: "Ya ce: Nawa kuka zauna a bayan kasa, na kidayar shekaru? * Su ka ce: Mun zauna yini daya, ko rabin yini, sai ka tambayi masu kidayawa! * Ya ce: Ba ku zauna ba face kadan, da kun kasance kuna sani * Shin zato kuke yi cewa, Mun halitta ku ne domin wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba za a mayar da ku ba!? * Allah Mamallakin Gakiya ya daukaka, babu abin bautawa face shi, shine Ubangijin al'arshi mai daraja" [Muminuna: 112-116].
Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga akan kyautatawarsa, kuma godiya tasa ce akan datarwarsa da baiwarsa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninsa.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa mai kira ga samun yardarSa.
Ya Allah ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa da sallamar aminci mai yawa.

Ya ku Musulmai!!!
Ku ji tsoron Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma ku tabbatar da zantukanku da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum shine abinda ya tafiyar da shi cikin biyayyara Allah, kuma "Mai hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma yay i aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai kuma yake kwallafa wa Allah burace-burace".

Ya ku Bayin Allah!!!
Cikin shudewar zamani akwai abin lura mai girma, kuma cikin jujjuyawar kwanaki akwai fadakarwa mai girma, "Lallai ne a cikin sabawar dare da yini, da abinda Allah ya halitta a cikin sammai da kasa, hakika akwai ayoyi ga Mutane masu takawa" [Yunus: 6].

Sannan ku sani!
Lallai Allah ya zabi zababbu daga halittunsa, sai ya zabi manzanni 'yan aika daga cikin Mala'iku, suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga cikin Magana kuma sai ya zabi ambatonsa, daga cikin kasa kuma ya zabi masallatai, daga cikin watanni kuma ya zabi watan Ramadhana da watanni masu alfarma, daga cikin kwanaki kuma yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai ku rika girmama abinda Allah ya girmama!

Ku saurara!
Lallai ku, ga ku a farkon watan Muharram, a farkon shekarar hijira, kuma lallai wannan watan yana cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda Allah ya girmama su, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne kidayayyun watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha biyu, a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga cikinsu akwai fudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku zalunci  kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
Lallai zalunci –Ya ku taron Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya girmama alfarmar watanni (hudu) masu alfarma, ya sanya aikata zunubi a cikinsu yafi girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin yafi girma.
An ruwaito daga Abu-bakrah –رضي الله عنه-, daga Annabi –صلى الله عليه وسلم-  ya ce: "Lallai zamani ya juya, kamar yanayinsa, a lokacin da Allah ya halitta sammai da kassai. Shekara daya watanni goma sha biyu ne, daga cikinsu akwai guda hudu masu alfarma; guda uku a jere; zul ka'adah da zulhijjah da Muharram, da kuma Rajab na kabilar Mudar, wanda yake tsakanin jumadah da Sha'aban", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma hakika Musulmai tun zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin hijirar Annabi –صلى الله عليه وسلم- daga garin Makkah zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi da hijira, domin Allah ya rarrabe tsakanin gaskiya da barna da lamarin hijira. Kuma sun fari shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya tabbatu akan haka, kuma sai al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.

Ya ku taron Musulmai!!!  
        Lallai yana cikin shiriyar annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma yana cikin abinda suke kankare munanan laifuka, kuma yana daga godiyar Allah da girmama shi, yin azumin ranar Ashura, wanda shine ranar goma na watan Muharram.
An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: Yayin da Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya iso garin Madina sai ya samu Yahudawa suna azumtar ranar ashurah, Sai aka tambaye su akan haka, sai suka ce: Wannan shine yinin da Allah ya bada nasara wa annbi Musa da Banu-isra'ila a cikinsa akan Fir'auna, don haka muke azumtarsa domin girmama shi, sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- y ace: "Mune muka fi jibintar Musa fiye da ku, sa'annan sai ya yi umurnin a azumce shi".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –صلى الله عليه وسلم – yana kirdadon yinin da ya fifita shi akan waninsa ba, fiye da wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana nufin watan ramadhana", Bukhari da Muslim ya ruwaito su.
        A cikin littafin Sahihu Muslim, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Azumtar yinin Arafah, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take gabaninsa da wanda take a bayansa. Azumtar yinin Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take a gabaninsa".
        Kuma a yayin da labari ya kai ga Annabi –صلى الله عليه وسلم- a karshen rayuwarsa cewa, lallai yahudawa suna rikon yinin Ashurah a matsayin idi, to sai yay i niyyar ya azumci ranar tara da goma, a shekarar da take tafe, amma sai mutuwa ta shiga tsakaninsu.
        An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce –a lokacin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya yi azumin yinin Ashurah, kuma ya bada umurnin a azumce shi- sai su ka ce: Ya Manzon Allah! Lallai Ashurah yini ne da Yahudawa da Nasara suke girmama shi, To sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: "To, idan shekara mai kamawa ta zo, insha Allahu, za mu azumci ranar Tara (Tasu'ah)", Yana nufin, tare da goma (Ashura). Ya ce: Shekara mai kamawan bata zo ba, face Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu. Muslim ya ruwaito shi.
        Don haka, abinda yafi falala –Ya ku Bayin Allah- shine a azumci yini daya gabanin Ashurah, domin a saba wa Yahudawa. Wanda kuma aka rinjaye shi ya kasa, to kada a rinjaye shi ga azumtar ranar Ashurah.

        Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai…


Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...