2017/01/20

hudubar Masallacin Annabi ta Subaitiy 22 RabiyusSaniy 1438h daidai 20 Janairu 2017m










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 22 /RabiyusSaniy/1438H
daidai da 20/ Janairu/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA


MAXAUKAKIYAR HIMMA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: MAXAUKAKIYAR HIMMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna,

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Bayan haka:

            Jin zuwa albishir, da fatan samun alkhairi, suna daga qa'idodin musulunci, da xabi'ar musulmai, a cikin kowani hali, Allah ta'alah yana faxa ta harshen annabinsa; Ibrahim (عليه السلام):
"Kuma babu mai xebe qauna daga rahamar Ubangijinsa face vatattu" [Hijr: 54].

            Kuma busharar jin cewa alkhairi ne ke tafe, yana haifar da kuzari (qarfin jiki), kuma yana zaburar da himmomi, yana kuma tunkuxa mutane zuwa ga aiki, kuma yana samar da rayuwar gaba, mai kyau (ga xaixaiku da al'umma).

Kuma duk lokacin da wani abu, mai vata wa musulmai rai, wutarsa ta kunnu, a wani wuri a bayan qasa, sai buqatar tuno ko halarto da ababen albishir ya qara qarfi, Kuma wannan shine shiriyar Manzon al'umma; annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم); domin sau dayawa, ya juya bala'i da kyakkyawar fatansa, izuwa ga ni'ima, ya kuma tayar da fatan kyau, daga cikin raxaxi.

Yana daga manyan ababen janyo farin ciki da sabubban albishir a rayuwar mumini, Yaxuwar addinin Ubangijin halittu, da shiryiwar waxanda ba musulmai ba zuwa ga musulunci.
Yaxuwa kuma, cikin gaggawa yana daga tabbatattun ababen da musulunci ya kevanta da su, waxanda su ka fito daga musuluncin, kuma (hakan yak an kasance) a kowani lokaci da zamani, koda mabiyan musuluncin sun yi qaranci, ko masu taimakonsa sun yi sakaci, ko maqiyansa sun tsananta.
Saboda musulunci ya fara ne daga Makkah, daga mutane 'yan kaxan masu rauni (da ake qara raunana su); waxanda su ka sha nau'ukan kamun qeta da cutarwa, Amma a cikin taqaitattun shekaru, sai musulunci ya shiga ko-ina a tsibirin larabawa (Jaziyratul Arab). Sai kuma aka samu al'ummar da ta xauki saqon musulunci tana yaxa shi, a tudu da kwari, da cikin duwatsu da faqo, sai sautin musulunci ya yaxu, kuma faxaxuwarsa ta yalwata; sai al'ummai su ka shiga cikinsa, jama'a-jama'a, da saurin da ba a san irinsa, a tarihi ba. Wannan kuma yana daga manya-manyan mu'ujizozi, kuma gaskatawar alqawarin Allah ne, da ke nuna cewa, kyakkyawan gobe na addinin musulunci ne.

Msulunci yana yaxuwa ne, saboda shi ne addinin da Allah ta'alah ya yarda da shi ga mutane gabaxaya, kuma ya xauki alhakin kiyaye shi, da yaxa shi, Allah (تعالى) yana cewa: "Shi ne wanda ya turo ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin ya rinjayar da shi akan addinai gabaxaya, kuma Allah ya isa Mai shaida" [Alfat'h 28].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai wannan addinin zai kai wurin da dare da yini su ka kai, kuma Allah ba zai bar gidan laka ko na tanti ba, face ya shigar da wannan addinin, da buwayar mai buwaya, ko da qasqancin maqasqanci, wanda zai samu buwaya da buwayar Allah, a cikin islama, kuma ya qasqantar da shi a cikin kafirci", Alhakim a cikin almustadrak ya ruwaito shi.

            Mutane kuma, sun so musulunci ne; saboda alamominsa a bayyane su ke, kuma (shi, wato musulunci) gaskiya ne da ta ke a fili, wanda ya dace da fixirar da aka halicci mutane akanta miqaqqa, da hankula madaidaita, kuma musulunci ya haskaka duffai, ya sanya rayuka cikin sa'ida, kuma ya yaye qiraza, "Halittar Allah ne wanda ya halicci mutane akanta, babu canji ga halittar Allah" [Rum: 30].

            Musulunci yana yaxuwa ne saboda aqida ne na imani, wacce ta ke cike, ko qosar da guraben da su ke cikin zukata, kuma ta ke tsarkake ximuwar rayuka, ta cike filin da ke cikin tunani, kuma ta ke amsa buqatun rayuka, ta basu aminci, ta qosar da qishinsu.

            Mutane suna shiga cikin addinin Allah, jama'a-jama'a ne, saboda shi ne addinin da ya tabbatar wa mutum karamarsa da darajarsa, kuma ya xaukaka mutum; ta vangaren ruhi da jiki, da hankali da zuciya, da nufi da soyayya, ya buxe masa qofofin sama, ya hore masa duniya, bai kuma haramta masa abubuwa masu daxi ba.

Kyakkyawar safiya tana ga wannan  addinin, saboda abinda ake gani na tasirinsa mai girma; wanda ba a iya siffantawa, da aikinsa mai girma wanda ba a iyakance shi, domin ya ciro mutum daga qasqanci irin na savo, zuwa buwayar xa'a, haka, ya kan fitar da mutum daga iyakokin duniya zuwa ga yalwar gidan dawwama (aljanna), yana kuma fitar da shi, daga qaiqashewar zukata, zuwa ga farfajiya irin ta soyayya, da kuma rahama faffaxa.

Musulunci yana yaxuwa ne; saboda yana daraja ilimi, kuma yana karrama maluma, kuma yana yin yabo ga hankali da tunani. Kuma duk lokacin da addinin musulunci ya isa wani gari, daga cikin garurruka, to sai ya qawata shi da ilimi, ya haskaka shi da sani; Sai wannan al'ummar (musulmai) su ka bada gudumawa wajen gina ilimi da wayewa ga mutane, kuma sai wayewar musulunci ta wayi-gari ita ce gadar da ta haifar da dukkan wayewar da su ka yi ta zuwa (a duniya) a bayan juna.

Mutane sun natsu da musulunci ne, saboda yana tabbatar wa mutane adalci a cikin zamantakewa, ta dukkan vangarorin rayuwa, kuma shi ne ya qarfafa igiyar 'yan'uwanta, kuma ya rayar da qa'idodin taimakakkeniya, ya kuma assasa ma'anoni irin na zamantakewa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)  ya ce: "Kuma xayanku ya tafi, tare da xan'uwansa; wajen biya masa buqata, shi ya fi falala akan ya yi i'itikafi a masallacina wannan; na tsawon wata biyu –sai ya yi nuni da yatsarsa-", Alhakim ya ruwaito shi, a cikin Mustadrak xinsa.

Adalci a musulunci, abun nuninsa mai haske ne, kuma fahimta ce tabbatatta, wanda ma'aunin wannan fahimtar baya tasirantuwa da matsayi ko dangantaka, ko daraja ko dukiya,
kuma suna cin gajiyar adalci, dukkan waxanda su ke zaune a qasar musulunci; Musulmai ne, ko wasunsu, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani, ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci, kuma kada qiyayyar wasu mutane ta xauke ku, a kan ba za ku yi adalci ba, ku yi adalci domin shi ne mafi kusa da taqawa, kuma ku bi Allah da taqawa, lallai Allah Masani ne ga abinda ku ke aikatawa" [Ma'ida: 8].

Kuma alhakin yaxa musulunci yana rataya ne ga wuyan musulmai, da isar da shi ga dukkan saqon duniya, farawa da annabinta (صلى الله عليه وسلم), Allah ta'alah yana cewa: "Ya kai wannan Manzo, ka isar da abinda aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka" [Ma'ida: 67].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)  ya ce: "Ku iyar mini koda aya xaya ce", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bi dukkan sabuban faxaxa lko yaxa musulunci, wannan ya sanya a lokacin da Abu-zarri Algifariy (رضي الله عنه) ya musulunta sai Annabi ya umurce shi da ya zauna a cikin qabilar Xiyan-gifar (بنو غفار), domin ya musu da'awa zuwa ga musulunci, haka kuma a lokacin da Axxufail bn Amru Ad-dausiy ya musulunta sai ya umurce shi da ya zauna a cikin qabilarsa; Daus (دوس), domin ya riqa yaxa musulunci a cikinsu.

Musulmi ana umurtarsa da yin aiki domin yaxa musulunci, sai dai ba a wajabta masa ya tilasta mutane kan karvar addini da qarfi ba, da kuma tursasa musu akansa tursasawa, Allah ta'alah ya ce: "Ba komai ba ne akanka face isarwa" [Shurah: 48].
Kuma Allah ta'alah ya ce: "Ba akanka shiriyarsu ta ke ba, sai dai Allah shi ke shiryar da wanda ya ke so" [Baqara: 272].

Kuma alhaki ko nauyin yaxa musulunci ya kan kai, qololuwarsa, a wajen musulmin da ya rabu da qasarsa; zuwa ga qasashen waxanda ba musulmai ba, sawa'un ya kasance ambasada ne, ko wanda aka tura karatu, ko attajiri, ko ma'aikaci.

Aikin yaxa musulunci, yana daga mafi girman falaloli, da martabobi mafi xaukaka, Allah ta'alah ya ce: "Babu wanda ya fi kyan magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma ya ce: Lallai ni ina cikin musulmai" [Fussilat: 33].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma Allah, ya shiryar da mutum xaya ta hanyarka, ya fi maka alkhairi fiye da jajayen raquma", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.

Kuma za mu iya bada tabbacin cewa, lallai babban abinda ya fi taimakawa magabata wajen yaxa musulunci shi ne, tarihinsu mai haske, cikin shigar da musulunci garurruka, da adalcinsu cikin hukunce-hukuncensu, da xabi'unsu, ta fiskar riqo da addini, da kamun kai, da tsayuwa akan dokokin addini.
       Daga cikin nagaba-gaba wajen aikata hakan kuma, akwai jagororin buxa garurruka da shigar musu da musulunci da rundunoninsu, waxanda su ka kasance masu da'awa, ba mayaqa ba, saboda waxanda su ka yaxa musulunci (a tarihi); Sun siffantu da tsarkin zukata, da kuma tsarkin rai, da ji soyayya maxaukakiya,
kuma kowani xaya daga cikinsu, mavuvvuga ne da ke kwararar da alkhairi da rahama, kuma ya ke tultular da amfanarwa da albarka.

Hanyar da ta fi yawan tasiri wajen isar da musulunci, ita ce isar da Alqur'ani mai karamci zuwa kunnuwan mutane, kuma cikin ayar da ke tafe, akwai qarfafa muhimmancin jiyar da mushirkai alqur'ani mai girma, Allah ta'alah ya ce: "Kuma idan wani daga cikin mushirkai ya nemi makwabtaka da kai, to ka karvi bakwabtakarsa, har ya ji maganar Allah, sannan ka isar da shi ga wurin amincewarsa, Wannan kuma saboda su mutane ne da ba su sani ba" [Tauba: 6].

Kuma masu himmatuwa wajen yaxa musulunci sun san muhimmancin sadarwa ta zamani, da kuma amfani da hanyoyin ci-gaba na kafafen zamani wajen yaxa da'awa.
       Kuma duk da sakacinmu wajen yaxa musulunci, sai dai Allah ya hore waxannan kafofi ko minbarorin sadarwa, masu aikin tasiri, in har masu aiki da su sun kyautata amfani da su, a duniyance, domin isar da rangwamen musulunci da sauqinsa, da kuma tsayawa a fiskar wanda ke qoqarin munana fiska ko kamar musulunci, wato, masu sanya masa dabaibayin (da zai hana yaxuwarsa).
Kuma ba abu ne da ke vuya ba, cewa lallai musulunci lokaci bayan lokaci, yana fiskantar munanta surarsa don ta zama abar qi, da yi masa qarya da zalunci, da manna masa tuhumar tsanani da ta'addanci, ga shi musuluncin (kansa) da kuma mabiyansa, ta hanyar hotuna katun, da faya-fayen kafafen sadarwa mabanbanta, domin tsoratar da mutane daga addinin musulunci, da riya cewa; musulunci mavuvvugar shakku ne, da koma-baya ko ci-baya, da munanan abubuwa,
Sai dai kuma, dukkan waxannan basa canza komai daga haqiqanin musulunci, kuma basa sace guiwar 'ya'yansa; musulmai, kuma basa dusashe hasken musulunci mai haskakawa, ko kuma kyansa mai walqawa, Allah yana cewa: "Kuma suna nufin su dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuma yana cika haskensa, koda kuma kafirai suna qi" [Saff: 8].
Kuma Allah ta'alah ya ce: "kuma Allah yana qi, face ya cika haskensa, koda kafirai sun qi " [Tauba: 32].

       Sun riya, karkatattun magana da qarya cewa, wai musulunci ya yaxu ne da kaifin takobi,
sai dai kuma, musulunci bai tilasta wani ya canza aqidarsa ba, kuma tarihi ya rubuta, da tawadar gaskiya da adalci, cewa lallai musulunci ya yaxu ne da hujjoji maxaukaka, da kuma dalilai bayyanannu, da kuma tausasawa, da adalci, Allah ta'alah ya ce: "Babu tilastawa a cikin addini, haqiqa shiriya ta bayyana daga vata" [Baqara: 256].
Kuma Allah ta'alah ya ce:  "Shin, kai kana tilasta mutane ne, har su kasance masu imani" [Yunus: 99].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
           
Bayan haka:
Lallai sashen musulmai suna aukawa da jahilci, cikin qoqarin munana kamar musulunci a idon mutane, ta hanyar binsu ga hanyoyi vatattu, da mazhabobi karkatattu, da manhajojin vata mabanbanta, waxanda su ke kekketa al'ummar musulmai, kuma su ke kawo rarrabuwa, su ke kuma raunata haxin kansu,
Wannan kuma yana da mummunan tasiri, da janyo koma-baya wajen aikin yaxa wannan addinin.

Kuma vangaren sadarwa da hanyoyinsa masu yawa, shima yana bada gudumawa wajen tsayar ko taqaita  yaxuwar musulunci, da mummunan tasiri, ga ingantaccen hoton musulunci a ido, ta hanyar sukar wannan addinin da yin isgilanci ga wasu daga shugabanninsa, da siffanta su da tsanani da tsanantawa, da kuma rufewar tunani, ko kuma ta hanyar munana wasu xabi'un (na musulunci).

Kuma ba voyayye ne, ga kwakwale ba, cewa lallai akwai alhaki mai girma akan musulman qasar masallatan harami biyu; na yaxa wannan addinin, saboda kasancewar (Makkah) alqiblar musulmai, (Madina) kuma wajen hijiran shugaban manzanni, (صلى الله عليه وسلم), Allah (تعالى) ya ce: "Kun kasance mafi alherin al'umma, wadda aka fitar ga mutane, kuna umurni da kyakkyawa, kuma kuna hani daga abin qi, kuma kuna Imani da Allah" [Ali-imrana: 110].

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.      
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman a garin Halab, da Shaam, da Mausil, da Iraqi, da Filasxinu, da kowani wuri ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
Ya Allah! Lallai su, masu jin yunwa ne ka ciyar da su, basu da takalma ka basu, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su ka taimake su,
Ya Allah! Duk wanda ya nufe su da mummuna to ka sanya kaidinsa a qirjinsa, kuma ka sanya rugujewarsu cikin tsare-tsarensu, Ya Mai amsa addu'a
Ya Allah ka rarraba kan maqiyansu, kuma ka wargaza haxuwarsu, ka sanya mummuna ya juyo akansu, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah Wanda ya saukar da littafi, wandas ke gudanar da gajimare, Mai ruguza qungiyoyi, ka ruguza maqiya musulmai, kuma ka taimake musulmai akansu, Ya Ubangijin talika, Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu, wanda shine qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce rayuwarmu ta ke cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda zuwa gare ta ake mayar da mu, kuma ka sanya rayuwa ta zamo qari a gare mu daga kowani alkhairi, kuma ka sanya mutuwa ta zama hutu a gare mu daga aikata kowani sharri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla musu akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu,
            Ya Allah! Ka sanya mu mu zama masu ambatonta, masu gode maka, masu tsoro a gare ka, masu yin kuka a gare ka, masu mayar da lamari,
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, kuma ka tabbatar da hujjarmu, ka daidaita harsunanmu, kuma ka cire dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da canzawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan fushinka.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada waraka ga marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, kuma ka sa mu cika da alheri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara sha'aninmu dukkansa, kuma kada ka dogarar da mu zuwa ga kayukanmu, daidai da kyaftawar ido,
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka kyakkyawan cikawa, da kuma afuwa kan abinda ya gabata, ko ya kasance
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana daga albarkokinka, da rahamarka, da falalarka, da arziqinka
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka –ya Allah- saboda kai ne Allah, wanda babu abin bauta sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma mu ne faqirai, Ya Allah ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama.
Ya Allah!, shayarwa ta rahama, ba na azaba, ko bala'i, ko rusau, ko nitsewa ba
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
            Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,




2017/01/06

HUdUBAR Sheikh Abdullahi Albu'aijan ta MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) 08/Rabis Saniy/1438H daidai da 06/Janairu/ 2017M











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/Rabiyus Saniy/1438H
daidai da 06/Janairu/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TAYAR DA KYAKKYAWAR FATA A ZUKATA
Shehin Malami wato: Abdullahi Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TAYAR DA FATAN, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, majivincin muminai, mai bada nasara ga masu taqawa, Mai rinjaye akan bayinSa, Mai hikima, Mai bada labari.
Muna yin yabo a gare shi, cikin yanayin farin ciki da cuta, da tsanani da wadaci, da lafiya da bala'i, Yabo nasa ne a duniya da lahira, kuma hukunci nasa ne, kuma zuwa gare shi za a mayar da ku.

Ina shaidawababu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, ya turo shi da shiriya, da kuma addinin gaskiya domin ya xaukaka shi akan addinai gabaxayansu koda mushirkai sun qi.
Allah ka yi daxin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, da sallamar aminci masu yawa.

Bayan haka:
Ku bi dokokin Allah –ya ku bayin Allah- da taqawa, kuma ku yi masa xa'a, kuma ina hana ku yanke tsammani daga rahamar Allah (S.W.T), saboda babu mai xebe tsammani daga rahamar Allah face mutane kafirai.

Ya ku taron musulmai !! …
Lallai jarabtar mutane sunna ce daga sunnonin Allah a wannan duniyar, domin (Allah) shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa, domin ya jarrabe ku,
kuma jarrabawa abu ne da hikimar Allah ke hukuntawa, Mabuwayi da xaukaka, cikin gwabzawa tsakanin gaskiya da varna, domin rabe tsakanin masu gaskiya da maqaryata "Ashe, mutane zato su ke yi, su ce: "Mun yi imani" alhali ba za a fitine su ba? Kuma haqiqa mun jarrabi waxanda ke a gabaninsu, domin Allah ya san waxanda su ka yi gaskiya, kuma ya san maqaryata" [Ankabut: 2-3].  
Kuma jarrabawa xauraya ce domin jarraba gwargwadon qarfin imani da tabbatuwa, da kuma sanin qarfin yaqini, kuma da shi ake gusar da waxanda aka cusa, a cikin sahun muminai, "Allah bai kasance zai bar muminai, akan abin da ku ka kasance a kansa ba, face ya rarrabe mummuna daga mai kyau" [Ali-imrani: 179].

Kuma jarabawa salo ne na tarbiyya, wanda Allah ke tsamar da mutumin da ya rubuta masa rabo irin na shiriya, ta hanyar jarraba, sai ya tashi daga barcin gafalarsa, ya qara fiskantar  Ubangijinsa, ya kuma koma ga addinin Allah.

Ya ku, bayin Allah !! …
Cikin tarin jarabawar rayuwa masu yawa, da fitintinu, haqiqa abin qi na qara girma, kayan vacin rai na qara tsanani, yayewar bala'i na qara jinkiri, har zaton xabe tsammani ya tabbatu a zukata, to "Ko kuna zaton ku shiga aljanna, tun gabanin misalin waxanda su ka shuxe gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cuta sun shafe su, kuma aka girgiza su, har manzonsu da waxanda su ka yi imani tare da shi, su ce: Yaushe nasarar Allah za ta zo?" [Baqara: 214].
To, a irin wannan yanayi, wajibi ne a nemi mafaka daga Allah, kuma a kyautata masa zato, saboda a wurin Allah akwai mafita daga kowani kunci, da yayewa daga kowani baqin ciki, kuma Allah yana wurin kyakkyawan zaton bayinsa muminai, domin Allah baya tavar da zaton wanda ya kyautata masa zato.

Ya ku taron musulmai !! …
Lallai watsa natsuwa da albishir, da tayar da fata a cikin zukata, a lokacin tashin hankali da tsoro, manhaji ne na qur'ani, kuma shiriya ce ta Manzon Allah (S.A.W),
Allah (تعالى) ya ce wa Musa da Haruna (عليهما السلام) domin su fiskanci qetare iyakar Fir'auna : "Kada ku ji tsoro, lallai Ni ina tare da ku, ina ji, ina gani" [Xaha: 46].
Kuma annabi Yusuf (عليه السلام) ya ce wa xan'uwansa, bayan abinda ya auka musu na bala'i: "Lallai ni xan'uwanka ne kada ka yi baqin ciki dangane da abin da su ka kasance su ke aikatawa" [Yusuf: 69 ].
Kuma annabi Shu'aibu ya ce wa Musa (عليه السلام), bayan an yi zaman mitin don ganin an kashe annabi Musa, bayan kuma ya fita daga garin Fir'auna a ankare (yana jiran me zai faru da shi): "Kada ka ji tsoro, ka tsira daga mutane azzalumai" [Qasas: 25].
Kuma annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa sahibinsa Abubakar (رضي الله عنه) alhalin suna cikin kogo: "Ya Ababakrin! Menene zatonka ga mutane biyu, wanda Allah shi ne na ukunsu, Kada ka yi baqin ciki, lallai Allah yana tare da mu" [Tauba: 40].
           
            A yaqin Badar yawan rundunar musulmai sun kasance mutane xari uku ne da goma sha wani abu, adadin mushirkai kuma ninkin musulmai har uku, kuma rashin kwanciyar hankali ya dabaibaye rundunar musulmai wanda bata yi shiri ko tanadin yaqi ba, kuma adadinsu bai cika ba, haka tanadinsu, a lokacin da su ke jiran bataliyar (mushirkai) mai qarfi, wanda ta ninninka su, bayan kuma adadinsu ya cika, da tanadinsu. To a cikin wannan yanayin ne, sai ayoyin qur'ani waxanda su ke sanya natsuwa, kuma su ke tayar da fata, a cikin rayukan musulmai, kuma su ke zaburar da su, su ke qarfafa zukatansu, kuma su ke jansu zuwa ga fito-na-fito, su ka sassauka, Ku saurari faxin Allah (تعالى) lokacin da ke magana da ManzonSa: "Kuma a lokacin da Allah ke nuna maka su, a cikin barcinka (mafarki), suna kaxan, kuma da ya nuna maka su, suna dayawa, lallai da kun ji tsoro, kuma lallai da kun yi jayayya a cikin lamarin, sai Allah ya tsare ku, lallai shi masani ne na abinda ke cikin qiraza * kuma a lokacin da ya ke nuna muku su, a lokacin da kuka haxu (a fagen daga), a cikin idanunku suna kaxan, kuma ya qarantar da ku a cikin idanunsu, domin Allah ya hukunta al'amarin da ya kasance abin aikatawa, kuma izuwa ga Allah ake mayar da al'amura" [Anfal: 43-44].
Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Haqiqa an qarantar da adadinsu a cikin idanunmu, har na ke ce wa wani mutumin da ke gefena, kana ganin sun kai saba'in? Sai ya ce: Ina ganin sun kai xari. Ya ce: sai mu ka kama wani fursuna daga cikinsu, sai mu ka ce masa: Nawa ne yawanku? Sai ya ce: mu dubu ne".
            Kuma mun samu, alqur'ani yana tabbatar da irin wannan salo, ta wani yanayin na daban, a qissar wannan yaqin, domin alqur'ani ya tayar da kyakkyawar fata a cikin rayukan musulmai, kuma ya tabbatar musu da samun nasara, yana kuma alqawarta musu cewa zai gadar musu da qasa, a inda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Kuma a lokacin da Allah ke muku alqawarin (bada nasara akan) xayan qungiyoyi biyu, cewa lallai ita, ta ku ce, kuma kuna burin lallai qungiyar da bata da qaya (ko makamai) ta kasance gare ku, kuma Allah yana nufin ya tabbatar da gaskiya, da kalmominSa, kuma ya katse qarshen kafirai * domin ya tabbatar da gaskiya, kuma ya vata qarya, koda kuwa masu laifin (kafirci) sun qi" [Anfal: 7-8].


            Ya ku bayin Allah !! …
   Haqiqa tarbiyyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) (ga mutane) ta kasance daidai, ko akan wannan manhaji, saboda Annabi ya kasance idan vacin rai ko baqin ciki ya dami musulmai, ko kuma ya tsorace wa zukatansu wani tsoro ko rashin kwanciyar hankali, da xebe tsammani, to sai ya kunno ruhin fata, ya watsa natsuwa, da aqidar amintuwa da Allah a cikin zukatan mutane,
Wannan ya sanya, lokacin da rundunoni suka taru a yaqin ahzab, domin su yaqi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), kuma su ka gayyato sojoji guda dubu goma (10,000), kuma musulmai yanayinsu ya kasance a cikin hali na qunci, ga kuma yanayin tsoron da ya dabaibaye rayukansu, har ya kasance xaya daga cikinsu baya iya fita domin ya biya buqatarsa, kuma yunwa ya tsananta a gare su, har su kan xaure dutse ga cikinsu, kuma kwanaki masu yawa su kan shige, ba tare da sun samu abincin da za su ci ba, ko sauran abin xanxanawa. Kuma sanyin funturu ya fiskance su a lokacin motsawarsa da tsananinsa.
Yaudara kuma da ha'inci da munafurci sun samu damar shiga cikin sahun musulmai kamar yadda hakan it ace al'adarsu, domin su kekketa qarfin musulmai, ,,, Kuma haqiqa alqur'ani ya siffanta halinsu a inda ya ke cewa: "A lokacin da su ka zo muku ta sama da ku, da ta qasa daga gare ku, kuma a lokacin da gani su ka karkata, kuma zukata su ka kai ga maqosai, kuma ku ka yi zaton zace-zace (munana) game da Allah * a can aka jarrabi muminai, kuma aka girgiza su girgizawa mai tsanani" [Ahzab: 10-11].

A irin wannan yanayin ne kuma

Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fara tayar da fatan alkhairi a cikin rayukan sahabbansa, kuma ya rayar da aqidar jin amintuwa da natsuwa a cikin zukatansu, yana mai  alqawarta musu samun nasara, da cewa za su gaje duniya, kuma yana musu busharar samun nasara mabayyaniya, sai ya musu alqawarin samun mabuxan taskokin Rumawa da Farisa da San'a'a, ,,,
An ruwaito daga Albara'a bn Azib (رضي الله عنه) ya ce: "Yayin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya umurce mu da tonon gwalalo (wato: khandaq) sai wani dutse ya bijiro mana daga cikin wannan ramin, wanda ya qi karvar bugun gaturra, sai mu ka kai kuka ga Annabi –صلى الله عليه وسلم-, sai ya zo ya xauki gatari, ya ce: Bismillahi, sai ya yi duka guda, sai ya karya xaya bisa ukunsa 1/3, sannan ya ce: Allahu akbar, an bani mabuxan qasar Shaam, wallahi! a yanzu na ga benayensu jajaye. Sannan ya yi duka na biyu, sai ya karya xaya bisa ukun 1/3,, sai kuma ya ce: Allahu akbar, an bani mabuxan qasar Farisa, wallahi! lallai ne ni na ga benen garin Mada'ina farare. Sai kuma ya yi duka na uku, kuma ya ce: Bismillahi, sai ya sare sauran dutsen, sannan ya ce: Allahu akbar, an bani mabuxan qasar Yaman, wallahi! lallai ni ina ganin qofofin garin San'a'a daga wurina wannan, a wannan lokacin".
Kuma mala'ika Jibrilu ya bani labari cewa lallai al'ummata za ta samu xaukaka akansu, ina muku albishir.
Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi albishir a gare su, da abinda zai kasance na shigar da musulunci a waxannan garurrukan, alhalin sahabbai (a lokacin) an hana su shigi-da-fici a jikin gololon khandaq, ga sanyi yana dukansu, da kuma yunwa (mai tsanani).

            Su kuma munafikai (a lokacin), haqiqa halinsu ya siffantu da tsoro (matsananci), da tsegumi, tare da qin taimakon muminai, sai su ka yi izgilanci daga wannan albishir (na Manzon Allah S.A.W), har su ke cewa: YANA MANA ALQAWARIN SAMUN TASKOKIN SARKIN KISRA DA QAISARA, ALHALIN XAYANMU BAYA IYA FITA DOMIN KASHI, "Allah da Manzonsa basu mana alqawarin komai ba face ruxi" [Ahzab: 12].
Amma su kuma musulmai (masu gaskata Allah da Manzonsa) sai su ka natsu, kuma su ka ce: "Wannan ne abinda Allah da Manzonsa su ka yi mana alqawari, kuma Allah da Manzonsa sun yi gaskiya, kuma wannan bai qara musu komai ba face imani da sallamawa" [Ahzab: 22].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo na Allah ne shi kaxai;
ya cika alqawarinsa,
ya taimaki bawansa,
ya kuma ruguza qungiyoyin kafirai shi kaxai xinsa.
Salati da sallama su qara tabbata ga wanda babu wani annabi a bayansa.

Ya ku taron musulmai !! …
Ku sani! Lallai ne Allah ya rubuta rinjaye, ga wannan addinin, da ma'abutansa,
kuma ya yi alqawarin bada nasararsa ga musulmai, a inda ya ce: "Allah ya rubuta cewa: Lallai zan yi rinjaye Ni da Manzannina, Lallai Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [Mujadala: 21].
Kuma ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani, idan ku ka taimaki Allah, zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku"[Muhammadu: 7].
Kuma ya ce: "Kuma lallai Allah zai taimaki wanda ya taimake shi, lallai ne Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [Haj: 40].

            Kuma koda musulmai sun qi taimakon addininsu, to lallai Allah zai taimaki addininSa, kuma zai zo da wasu mutanen da za su tsaya (su rungumi lamarin) addini, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani duk wanda ya yi ridda daga addininsa, to, Allah zai zo da wasu mutane, yana sonsu, kuma suna sonsa, masu tawali'u ga muminai, masu izza ga kafirai, suna yin jihadi a cikin hanyar Allah, kuma ba su tsoron zargin wani mai zargi" [Ma'ida: 54].
Kuma ya ce: "Kuma idan kuka juya baya, zai musanya waxansu mutane wanda ba ku ba, sa'annan ba za su kasance kwatankwacinku ba" [Muhammadu: 38].

            Kuma duk yadda sabuban su ka jujjuya, halayen su ka caccanza, to lallai musulmai suna cikin alkhairi madawwami, "Kuma kyakkyawar makoma ta masu taqawa ce" [Qasas: 83].
            Kuma ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya ce: "Mamakin lamarin mumini, lallai lamarinsa dukansa alheri ne, kuma babu hakan ga wani face mumini, Idan abin farin ciki ya same shi sai ya yi godiya, sai hakan ya zama alheri a gare shi, Idan kuma cuta ce ta same shi sai ya yi haquri sai hakan ya kasance alkhairi a gare shi" .

            Sai ku yi taqawar Allah a cikin rayukanku, kuma ku kiyaye xebe tsammani, da xabi'ar tsegumi a lamarin al'ummarku, saboda hakan makamin yaqi ne, sannan kaidin maqiyanku su ke qoqarin cuso shi a cikin sahunku.
            Kuma ku yi bushara, ku yi kyakkyawar fata, ku amintu da Allah, sai ku zama waxanda su ka fi xaukaka, "Lallai kalmarmu ta yi rigaye ga bayinmu manzanni, lallai su, sune masu samun nasara, kuma lallai rundunarmu, su ne masu yin galaba"' [safat: 83].

            Kuma kada rinjayen qarfin varna ya ruxe ku, domin Allah, mai rinjayar lamarinsa ne, koda kafirai sun  qi. 

            Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai, ka bada nasara ga bayinka masu tauhidi,
kuma –ya Allah- ka sanya wannan qasar ta zama cikin aminci da zama lafiya da sauran qasashen musulmai.              
Ya Allah! Ka bamu aminci a cikin qasashenmu, kuma ka gyara shugabanninmu masu jivintar lamuranmu.
Ya Allah! Ka datar da majivincin lamuranmu da datarwarka, ka qarfafe shi da qarfafawarka, kuma ka bada buwaya wa addininka da shi, Ya Allah! Ka datar da shi, da masu na'ibtarsa zuwa ga abinda a cikinsa alkhairin musulunci da musulmai ya ke, kuma zuwa ga abinda gyaruwar qasa da bayi su ke, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka bada nasara ga rundunoninmu da su ke ribaxi, akan iyakoki, Ya Allahn ka daidaita jifansu, kuma qarfafa niyyoyinsu, ka taimake su da taimakonka, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka karvi shahidansu, kuma ka warkar da marasa lafiyansu, kuma ka warkar da karyayye daga cikinsu.
Ya Allah! Ka kare su cikin iyalansu da dukiyoyinsu da zurriyarsu, ya Mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka gyara halayen musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance (mai taimakon) 'yan'uwanmu a qasar Sham.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikinsu, ka xauke cutarsu, ka jivinci lamuransu, kuma ka gaggauta yayewar matsalolinsu, kuma ka haxa kansu ya Ubangijin talikai.

Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.


,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...