I'ITIKAAFI
الاعتكاف
KEBANCEWA TARE DA ALLAH
(خلوة
مع الله)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Shin kana samun matsalar kaikashewar zuciya?
Shin kana koka yawaitar damuwa da bacin-rai, da ayyuka masu shagaltarwa,
da mushkilar sakaci ko karanta ibada??
Shin kana son karin yawaita kusantar Allah, sai dai baka samun iya
aiwatar da hakan???
Idan kana samun 'daya daga cikin wadannan matsalolin, to kada ka yi
sakaci kan aiki da wannan ibadar; wato: I'ITIKAAF!
Saboda I'ITIKAFI dama ne mai girma, domin kakkabe ko rage ayyukan da
suka shagaltar da zuci, tare da yin sauri ko yawaitar karin taku domin tafiya
zuwa ga Allah Ta'alah,
Kuma cikin yin i'itikafi, akwai bada foro ko yin training ga rai, kan
kyautata amfana da lokaci.
Da yawaita yin ibadodi.
Da neman kubuta daga wasu munanan al'adodi, kamar yawaita cin abinci, da
yawaita barci, da yawaita magana.
Kuma domin musulunci ya tsinki ALFANO KO FA'ODODIN I'ITIKAF, to ya dace, a
lokacin I'itikafinsa ya shagaltu da/
Ambaton Allah Ta'alah
Da salloli
Da tilawar Alkur'ani,
Da sauran abinda ke kama da wadannan daga dangogin ayyukan 'da'a,
Sai kuma ya nisanci dukkan abinda bashi da wata fa'ida, ko kuma ba a
bukatuwa zuwa gare shi.
Da dukkan abinda ke iya sace lokaci, ko ya dauke hankali, daga barin
ibada.
Lallai i'itikafi ibadar kebancewa ne, wanda Musulmi ke ribatarta, domin
kara-samun kusanci zuwa ga Allah Ta'alah; kuma Allah Ta'alah yana fada a cikin
hadisin kudusiy:
"إذا تقرب العبد إليّ شبرًا تقربت إليه ذراعًا، وإذا تقرب مني ذراعًا
تقربتُ منه باعًا، وإذا أتاني مشيًا أتيتُه هرولة"، رواه البخاري: 7536، ومسلم:
2675.
Ma'ana: "Kuma idan Bawana ya kusance ni
da kamar taki 'daya, to ni kuma zan kusance shi da kamar zira'i, idan kuma ya
kusance ni da kamar zira'i, to zan kusance shi da kamar tsawon hannu 'daya.
Idan kuma ya zo min cikin halin tafiyar kafa, ni kuma zan zo masa cikin sassarfa
" [Bukhariy: 7536, da Muslim: 2675].
No comments:
Post a Comment