2015/07/31

HUDUBAR MADINA (06) 15 shawwal 1436h Ta Alhuzaifiy








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 15 /SHAWAAL/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai baiwa,     Mai gafarta zunubai,      Mai karvar tuba,      Mai tsananin aquba,          Ma'abocin ni'imah da falala,           Babu abun bautawa da gaskiya sai shi,     Makoma zuwa gare shi take,      Ina yabo wa Ubangijina kuma ina gode masa,         Ina tuba zuwa gare shi,       Ina kuma neman gafararSa,       Ina kuma shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,      Maxaukaki         Mai girma.         Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa,        Mai yin bushara da gargaxi.        Allah ka yi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu,         da iyalanSa, da sahabbanSa,    Waxanda suke rigaye zuwa ga kowace falala da alkhairi.
Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ta hanyar yin aiki da abinda yayi umurni, da kuma nisantar abubuwan da ya yi hani akansu ya tsawatar,

Ya ku bayin Allah!
Ku aikata aiyuka na kwarai don gyara lahirarku,    kuma kada ku vata aiyukan;        Sai ku yi asarar kayukanku,     Allah maxaukaki yana cewa:
"Kace: kuma ku yi aiki, da sannu Allah zai ga aikinku, da ManzonSa, da Muminai,      Kuma za a mayar da ku zuwa ga masanin abinda ke fake, dana bayyane,     Sa'annan ya baku labari kan abinda kuka kasance ku ke aikatawa", [Taubah,  105].
Har ila yau Allah ta'alah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku yi biyayya ga Allah, kuma ku yi biyayya ga wannan Manzon,       kuma kada ku vata aiyukanku", [Muhammadu, 33].
Allah ta'alah yana cewa:
"Kace,       Lallai waxanda suka yi hasara sune waxanda suka yi hasarar rayukansu da iyalansu, ranar qiyamah,      Lallai wancan itace hasara mabayyaniya", [Zumar, 15].

Kuma –Musulmai- ku gyara duniyarku ta hanyar neman halal,     da kuma ciyar da shi ta qofofin alkhairi na wajibi, dana mustahabbi, da na halal,         Ita kuma wannan duniyar ku sanya ta ta zamto wurin yin guzurinku zuwa gidan ni'imah,      Kuma kada ku bari duniya ta ruxe ku da abubuwan qyalqyalin da suke cikinta,      Kuma kada ta fitine ku kan lahirarku,    
Sai ka yi aiki –Ya kai musulmi- don gyara duniyarka,     ka kuma yi aiki tuquru don gyara lahirarka,         Ya zo a cikin wani hadisi:
"Ba shine mafi alherinku ba Wanda ya bar lahirarsa don duniyarsa,       Ko kuma wanda ya bar duniyarsa don lahirarsa".
An rawaito daga Almustaurid xan Ash-shaddad (رضي الله عنه)  yace:
"Wata rana mun kasance a wajen Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) sai muka tattauna akan duniya da lahira,     Sai wassu suka ce: Kawai duniya guzuri ce na lahira;      A cikinta akwai aiki, akwai sallah, akwai zakkah.     Sai wassu kuma suka ce:      Lahira a cikinta akwai aljannah,      Suka faxi abubuwan da Allah ya nufe su da faxa.       Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:     Duniya ba komai ba ce idan aka kwatanta da lahira,     Sai kamar yadda xayanku zai tafi zuwa kogi, Sai ya tsoma yatsarsa a cikinsa,        Duk abinda ya fita a cikinsa shine misalin duniya",  [Alhakim ya rawaito shi a cikin littafin Almustadrak].
Kuma Alhakim ya sake ruwaitowa daga Sa'ad xan Xariq,    daga BabanSa, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Madalla da gidan duniya ga mutumin da yayi guzuri a cikinta ga lahirarsa,     har UbangijinSa ya yarda da shi.    Tir da gidan duniya ga wanda ta hana shi neman lahirarSa,    Har ya kasa samun yardar UbangijinSa".

            Alhasan Albasariy (رحمه الله) yace:
"Madalla da gidan duniya ga bawa mumini;       saboda mumini yayi aiki a cikinta xan kaxan, ya kuma xauki guzurinsa daga cikinta zuwa ga Aljannah.      Tir da wannan duniyar ga kafiri da munafiqi;    saboda ya tozarta dararenSa,     Sannan yayi guzurinsa daga cikinta zuwa gidan wuta",    [Ahmad ya rawaito shi a cikin littafinsa:    Azzuhud].

            Kuma lallai kowani mutum ya sani ilimi na yaqini; cewa zai qaura ya bar wannan gida na duniya,       yana mai barin duk abinda Allah ya bashi a cikin wannan gida, a bayan bayansa,    Ta yadda babu wani abu     da zai kasance tare da shi, sai aikinsa kawai,       Idan na alheri ne ya ga alheri,         In kuma na sharri ne to sai ya ga sharri,           Kuma idan har ya zama halin mutum zai qare ne zuwa ga haka, kuma zai tafi zuwa ga wannan makomar         To, ya zama wajibi  mutum yaje wajen UbangijinSa da mafi girman abinda bawa zai iya aikatawa na aiyukan kwarai,          Saboda babu wata hanya da bawa zai tsira a wajen  UbangijinSa sai ta hanyar aiyuka na kwarai,     Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma dukiyoyinku da 'ya'yanku basu kasance za su kusantar da ku da wani kusanci ba a wurinmu,     Saidai wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na kwarai,     To waxannan kam suna da sakayya na ninki saboda abinda suka aikata,    kuma Su suna cikin banaye suna amintattu", [Faxir,    37].

            Kuma –ya kai musulmi- damuwarka –a ko yaushe- ta kasance kan rabauta da sha, daga dausayin Annabi Muhammadu; shugaban 'ya'yanAdam (صلى الله عليه وسلم) ;  Saboda shine farkon abun shan 'yan aljannah.       Kuma duk mutumin da Allah ya datar da shi; ya yi baiwa a gare shi da samun sha daga wannan dausayin to lallai bashi da wani tsoro a bayan haka.      Kuma duk waxanda zasu sha daga wannan dausayin to lallai Allah ya sauqaqe musu wahalhalun da suke a gabanin haka,       Kuma lallai yin imani da wannan dausayin yana cikin imani da ranar qarshe,          Saboda haka; Duk wanda bai yi imani da wannan dausayin ba to ba shi da imani kwata-kwata;       Wannan kuma saboda rukunnan imani ba a rabe su;      Don haka, Duk wanda bai yin imani da rukuni guda xaya daga cikin rukunnan imani ba, to lallai ya kafirce da su gabaxaya,      
            Kuma shi wannan dausayin karramawar Allah ta'alah ne ga annabinSa Muhammadu,      Wanda al'ummarSa za su sha daga gare shi, a filin da za a tattara halittu, da matsayar hisabi, ranar qiyamah,  a yinin da tsayinsa shine gwargwadon shekara dubu hamsin, a wajen kafirai.     Amma sai Allah ya taqaice tsayinsa ga mumini.
            Zai lulluve mutane a cikin wannan yini, a filin hisabi irin abubuwan da ba za su iya jure musu ba na baqin ciki,      Kuma ba don Allah ya bada qarfi a jikinsu na juriya, da wanzuwa ba = to da sun mutu gabaxaya.
            Kuma a filin hisabi qishi mai tsananin gaske wanda ke qona hanta, irin wanda mutane basu tava jinsa ba zai kama su,      To sai Allah ya karrama annabinSa Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya azurta shi da dausayin ruwa, wanda al'ummarSa zata sha daga gare shi,         Alhalin shi kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana tsaye a farkon wannan tafkin yana kallon al'ummarSa,     yana kuma yin farin ciki da haka, matsanancin farin ciki,  kana kuma yana kiran al'ummarSa don su sha daga wannan dausayin.    
Kuma faxin wannann dausayin da siffar ruwansa hadisan annabi masu yawa (mutawatirai) sun zo da bayaninsa,       Kuma alqur'ani shima ya ambace shi a cikin suratul kausar,    
Kuma kowani Annabi yana da tafkinsa.            Hadisi ya zo daga Samurah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)  yace:
"Lallai annabawa suna alfaharin wa yafi yawan mabiya daga al'ummarSa,      Ni ina fatan a wannan yinin na kasance na fi su yawan masu gangarowa zuwa ga dausayi,       Kuma kowani annabi a cikinsu a wannan yinin yana kan wani dausayin da yake cike, a hannunsa akwai wata sanda, yana kiran wanda ya sani daga cikin al'ummarSa,   Kuma kowace al'ummah tana da wani alama, wanda annabinta zai gane ta da shi",     [Attirmiziy ya rawaito shi, da Axxabaraniy].

Kuma dausayin Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) yafi yawan mazowa, kuma ya fi girma, ya kuma fi zaqi, kamar shari'arSa;       An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه)  daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai tafkina yafi Ailah zuwa Adan nisa,      Kuma yafi nono fari,       Yafi zuma zaqi,      Yafi qanqara sanyi,    Kofunan shansa sun fi adadin taurari yawa",  [Muslim ya rawaito shi]. A wata riwayar da ba ta Muslim ba, "Qamshinsa yafi turaren almiski daxi".

Daga Abu-zarrin (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:    
"Na rantse da wanda raina yake hannunSa,     Kofunan shan wannan tafki sun fi taurarin sama yawan adadi, a cikin dare mai duhu, wanda bata da hazo ko gajimare,      daga cikin kofunan aljannah,    Duk wanda ya sha daga wannan dausayi to ba zai tava jin qishi ba, qarshen abinda ke kansa.    Indaroro guda biyu ne suke tunkuxowa da qarfi daga gidan aljannah don qara shi",    [Ahmad da Muslim da Annasa'iy suka ruwaito shi].

Daga Abu-Umamah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Dausayina tsayinsa kwatankwacin abinda ke tsakanin garin Adan da Amman ne,     Shi kuma yafi faxi sosai,      A jikinsa akwai vangarori guda biyu na zinari da azurfa –ma'ana: indaroro guda biyu-,    Abin shansa yafi nono fari,     yafi zuma zaqin xanxano,    yafi turaren almisku qamshi,    Duk wanda ya sha daga gare shi ba zai tava jin qishi ba, kuma ba za a baqanta fiskarsa ba har abada"    [Ahmad da Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana suka ruwaito shi].

 Daga Zaid xan Khalid (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Shin kun san menene alkausara? Wani kogi ne da Ubangijina ya bani shi a cikin gidan aljannah,     A cikinsa akwai alheri dayawa,      Al'ummata zata sha daga gare shi ranar qiyamah,     Yawan kofunansa kamar adadin taurari ne,    Wani bawan daga cikinsu za a karkatar da shi,  sai nace: Ya Ubangijina! lallai yana daga cikin al'ummata?     Sai ace: Lallai kai ba ka san abinda ya qirqiro ba a bayanka"    [Ahmad da Muslim da Abu-Dawud suka ruwaito shi].

            Saboda waxannan dalilan shi Dausayi qasa ce mai faxi, a filin tsayuwar qiyama, Wanda Allah zai cike ta da ruwa, daga kogin alkausara,       Indararo guda biyu ne suke zuba a cikin wannan dausayin,  na zinari da azurfa,       daga kogin alkausara,       kuma wannan tafkin ruwansa baya raguwa,      Kuma kowani mumini namiji da mumina mace za su sha daga wannan dausayin,     alhalin suna kan matsanancin qishi mai girma,      To daga nan kuma babu wani mutum da zai ji qishi har abada, bayan shansa.  
            Kuma lallai waxanda za su zo wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) akan tafkinsa sune:       WAXANDA SUKE BIN SUNNARSA (عليه الصلاة والسلام) SUKE RIQO DA TAFARKINSA, SUNE KUMA MASU NISANTAR MANYAN LAIFUKA (الكبائر) DAGA ZUNUBAI,         Allah ta'alah yana cewa:
"Idan kuka nisanci alkaba'iran da aka hane ku,      to sai mu kankare muku qananan laifukanku,     kuma mu shigar da ku mashiga mai karamci" [Nisa'i:  ].
Kuma bayan riqonsu da sunnar Annabi (صلى الله عليه وسلم) da shiriyarsa, suna kiran mutane zuwa ga Allah (da'awah),  akan ilimi da basira, Allah ta'alah yana cewa:
"Ka ce: Wannan itace hanyata; ina yin kira zuwa ga Allah, akan basira,      Ni da wanda ya bi ni, Kuma tsarki ya tabbata ga Allah,   Ni ban zama daga cikin mushirkai ba" , [Nahli:    ].
Sai suke kira zuwa ga/    Shari'ar Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) , suke kuma nisantar bidi'oi da qirqirarrun abubuwa a cikin addini,  da abubuwan da shari'a ta kyamata,     Tare da lazimtar yin ikhlasi wanda yake kore RIYA DA YI DON MUTANE SU JI (SUM'AH).
            Kuma yana daga cikin sabbuban sha daga dausayin Annabi (عليه الصلاة والسلام) yawaita yin salati da sallama ga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).

            Allah ta'alah yana cewa:
Bimillahir rahmanir rahim:
(إنا أعطيناك الكوثر فصَلِّ لربك وانحر، إنّ شانئك هو الأبتر ).
"Lallai mune muka baka tafkin alkausara,    Sai kayi sallah wa Ubangijinka,    kuma ka yi suka -a gare shi-, Lallai wanda ke aibanta ka shine mai yankakkiyar albarka" [Alkausar,    1-3].

ALLAH YA YI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.
….
….
HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; ma'abocin girma da karramawa,    da mulkin da ba a cimmasa,    da kuma buwayar da bata qasqanta ,      Ina yin godiya ga Ubangijina akan ni'imomi dayawa,        
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,    Mamallaki Mai tsarki da Kamala,  
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa,     Mafificin salati da sallama su qara tabbata a gare shi.     Da kuma iyalanSa da sahabbanSa masu karamci.  
Bayan haka,

Ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa,        Kuma ku yi riqo a musulunci da igiya mai qarfi,,,

Ya ku bayin Allah!
Mamakin girman rabon mutumin da Allah ta'alah ya masa kyautayin zuwa tafkin Annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ; ya kuma sha daga gare shi, don ya rabauta da rashin jin qishi har abada.
Sai kuma ku yi mamakin girmar hasarar mutumin da aka haramta shan ruwan wannan tafkin a gare shi, sannan aka kore shi,            Kuma Ubangijinka baya zaluntar kowa!

Ya ku musulmai!
Lallai yana daga cikin sabbuban hana gangarowa zuwa ga tafkin Annabi (صلى الله عليه وسلمYIN BIDI'OI DA AIKI DA QIRQIRARRUN ABUBUWA A CIKIN ADDINI, DA KANGE MUTANE DAGA MUSULUNCI, DA ZANCE KO DA AIKI, KO FATAWA. Kamar yadda hakan ya zo a cikin hadisan da aka ruwaito, kan sabbuban da suka sanya aka kori wassu mutane daga cikin wannan al'ummar.       A cikin waxannan hadisan ance:     LALLAI KAI BA KA SAN ME SUKA QIRQIRO BA a bayanka, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:  
"A nisanta wanda ya canza addini a bayana mafi nisan nisantawa".

            Kuma yana daga cikin sabbuban da suke hana zuwa tafkin Annabi (صلى الله عليه وسلم): Aikata manyan zunubai,      saboda zunubai abubuwa ne da suke vata zukata.

            Kuma Riya da yi don mutane su ji (sum'ah) suma suna cikin abubuwan da suke hana sha daga wannan dausayin.

            Haka kuma zaluncin da ke kasancewa a tsakanin bayi, Shima sababi ne mai girma na hana sha daga dausayinSa.

            Kuma alaqa da take tsakanin yin sakayya da hana shan ruwa daga dausayinSa, da waxannan aiyukan (da suka zama sababin haka), a fili take ga wanda yayi tunani akan haka;    Saboda
Duk wanda a duniya ya bi shari'ar Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya kuma yi riqo da shiriyarSa to sai ya gangara tafkinSa a lahira, ya kuma sha daga gare shi.
Wanda kuma ya canza, ya qirqiro abubuwa a cikin addininSa sai a hana shi;     saboda ya kange mutane daga bin gaskiya.
      
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin,     Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallama mai yawa" [Ahzab: 56].
……………….
……………….
Addu'a ….
………………..
………………..



2015/07/23

HUDUBAR MADINA (05) 8 SHAWWAL 1436 SHEIKH SALAH ALBUDAIR











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 8 /SHAWAAL/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم

HUXUBAR FARKO

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; mahaliccin rayuka,      Wanda yake rayar da qasussuwa bayan sun rududduge,      wanda kuma yake gwavava kyautuka da rabo,         Ina yin godiya a gare shi akan abinda ya ke ta qaruwa na ni'imomi, da wanda ya ninku na daga falala da kyauta,      Kuma ina shaidawa babu abun bauta da gaskiya sai Allah; shaidawar da take kawar da bawa daga karkatan vata, ta kuma tunkuxe masa azaba,      kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, shine wanda aka turo shi ga dukkan talikai;     Larabawa da ajamawa.      Allah ya yi daxin salati a gare shi da iylanSa; salatin da yake wanzuwa,      da sallama a jejjere,
Bayan haka;

Ya ku musulmai !
Ku bi dokokin Allah,     saboda kiyaye dokokin Allah (taqawah) shine mafi girman abinda mutum ya samar,        Yin biyayya kuma a gare shi shine mafi girman nasaba,     "Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-Imraan: 102].  

Ya ku musulmai !
Lallai duniya jin daxi ne xan kaxan da zai tafi ya qare,       da kuma wata dukiya wacce daga qarshe za a kwace,     da gidan da zai rushe,      Da kuma ran da za a cire ta !

Saidai kuma;
Madalla da matafiyin da a cikin taron matafiya yayi ta zaburar da abun hawanSa,
Ya kuma riski damar lokaci na rayuwa da ya samu; gabanin yayi qaura (ya mutu).

Har ya zama kamar mutumin nan da a qissarSa;

1.  Bai gushe ba  yana ambaton zai mutu yana kuma tuna haka
Har zuwa lokacin da mai raqumi ya tsaya a qofar gidanSa

2.  Sai ya same shi a faxake, cikin shiri
Da tanadi, yana wanda burace-burace basu shagaltar da shi ba.

Ya kai wanda ya manta makomarSa,       Ya kuma doge cikin nau'ukan vata    !!!

(1)       Ka riski rayuwarka ka gyara ta;      saboda zama a duniya gajere ne
Mutuwa kuma tana dufafar mai rai kwatsam, tana kuma kawo masa farmaki.

(2)       Idan kuma ka sava wa haka, to lallai zaka shiga cikin ramin qabari
Kuma lallai Mala'ikun; Munkar da Nakiru zasu yi tambayoyi a gare ka.

(3)       Lallai kuma zaka yi kuka, cikin qunar rai, tare da bayyanar da yin hasara
Lallai hisabi ga masu savo abu ne mai wahala

(4)       Saboda masu zunubai zuwa:   Wutar SA'IRA  makomarsu take
Sune; Waxanda suka yi sakaci,  Sai sakacinSu ya kai su cikin bala'i da kunyata
       
Ya kai wanda ya kame daga abubuwan da suke karya azumi a cikin watan ramadhana,       Ya kuma kiyaye dokokin Allah; abun bauta!        Ya wanda ya yanke dararenSa da yin tasbihi da tilawa da ruku'i da sujjada !!     Ya wanda ya bada dukiyarsa a matsayin bauta da kuma kyautatawa bayin Allah !!!,     Ya wanda ya yi yaqi da kanSa, sai ya kiyaye ta daga wuta, sannan ya xaukaka da ita !!!!,
Kada ka zama daga cikin bayin da suka yi aikin biyayya da xa'a, sa'annan suka yanke,

Kada kuma ka kasance daga cikin waxanda suka bada kaxan,      sa'annan suka qaranta; kuma suka hana,

Kada kuma ka kasance daga cikin waxanda suka qaurace wa savo,     sa'annan suka koma cikinsa,

Ya wanda ka kasance zuwa ga aiyukan alkhairi mai aikatawa,

Mai kuma nisantar sharri,

Mai tausasa wa faqiri da talakawa,

Mai yin tilawar alqur'ani,

Mai kusantar masallatai,

A cikin dare kuma, kana yin tsayuwa, da addu'oi,
kana yin sallah, kana khushu'i, kana ta kuka,

To, kada ka koma cikin savo bayan wucewar watan ramadhana,

Mai yin gaba da bayin Allah,

Mai yin rafkanuwa dangane da farillah,

Saboda

1-  Lallai ka tsayu wajen yin bauta na wani lokaci
Wanda kuma kwanakin suka kasance albarka a gare ka da cin nasara

2-  Kada ka dena yin tsayuwa cikin darenka (wato: sallah),      bayan kuma
Samman dararenka sun xaukaka da tilawar al'qur'ani, da yin sujjada,

3-  Kada kuma ka dena yin azumin yininka,      bayan kuma
An karya lagon yin azumi, cikin haquri,  da juriya

4-  Lallai wanda ya munana aiki idan har ya so ya tsira,
To sai yayi tuba ta gaskiya,      ya kuma ninnika aiyuka

5-  Kuma bawa yana kwaxayin a rududdugar da qasussuwanSa rududdugarwa
Sai kuma a dawwamar da shi a cikin aljannonin ni'imah dawwamarwa.

        Kuma –wallahi- tir da bawan da a cikin watan ramadhana zai yi ta yin bautar UbangijinSa,       Amma idan watan ya fice    sai yayi nauyin jiki kan ibada,     Sannan ya sanya rigar qaranta bayan ta qari,      Sannan yayi biyayya wa shexanu, harma da masu taurin kai,      

        Ya kai bawan Allah   Kada ka kasance daga cikin waxanda suka koma bayan qeyyarsu,         Suka kuma canza alqiblar tafiyarsu,          Sannan suka warware abinda hannayensu suka qulle shi da kyau,       Suka kuma rusa abinda suka qawata; suka kuma kyautata gininsa,   

Ya kai bawan Allah!  
Kayi azamar aikata alkhairi, iya azama,    ka kuma tabbatu akan aiyukan, tabbatuwa;        saboda
Duk wanda aka azurta shi da yin azama, tare da dogewa, Sai alkhairori da albarkoki su nufo shi,         Wanda kuma aka yi masa baiwar tabbatuwa kan aiyukan alkhairi to sai buxi da kyaututtuka su fiskance shi,        Saboda ita azama tana umurtar mutum ne da aikata abinda yafi amfani,       Shi kuma tabbatuwa da sabati yana xaukarsa zuwa ga aiki da abinda yafi xaukaka da girma,     Hadisi yazo daga Shaddad xan Aus (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya gaya mini cewa:
"Ya kai shaddad xan Aus! Idan har kaga Mutane suna yin taskar zinari da azurfa To sai ka yi taskar WAXANNAN KALMOMIN:
Ya Allah lallai ni ina roqonka neman tabbatuwa cikin lamari (n addini), da azama akan aiyuka na shiriya,    
Kuma ina roqonka ka bani abubuwan da suke hukunta samun rahamarka, da sabbuban gafararka,      
Kuma ina rokonka ka bani yin godiya kan ni'imominka, da kyautata yin bauta a gare ka,     
Kuma ina roqonka zuciya kuvutacciya, da harshe mai gaskiya,      
Kuma ina roqonka ka bani alherin da ka sani,      sannan ka kare ni daga sharrin da ka sani,    kuma ina neman gafararka kan abinda ka riga ka sani,     
Lallai kai ne masanin abinda ya vuya (na gaibu)"   Axxabaraniy ya rawaito shi.

Don haka,    Ya kai bawan Allah,     
Ka tafi akan siffar tabbatuwa da kuma yin azamar aikata aiyukan alkhairi,   kan halinka mai kyau,       da kuma hanyarka mai kyau miqaqqiya,        Sannan aikinka ya zama wanda ake tabbatuwa ne a dawwama akansa,          Hadisi ya zo daga Alqamah, yace: Nace ya ke Uwar-Muminai, Yaya aikin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم); Shin ya kasance ya kan keve wassu yinin?    A nan sai A'isha (رضي الله عنها) tace:   A'a  ;    Aikinsa ya kasance wanda yake dawwama ne akanSa,      Wanene daga cikinku zai   iya irin abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yake aikatawa.   Muslim ne ya rawaito shi.    
Kuma lallai mafi soyuwan aiyuka a wurin Allah shine wanda aka dawwama akansa; koda kaxan ne,     Shi kuma aiki xan kaxan dawwamamme yana girma yana tsarkaka yana qaruwa,         Yayin aiki mai yawa, mai wahalarwa ya ke gadar da/ qosawa, da gajiyawa, da kuma yanke aikata shi, da gaza ci gaba.         Ya Allah ka arzurta mu da tabbatuwa akan aikata xa'a, da kuma gaggawa cikin aiyukan alkhairori, da kuma tabbatuwa akan gaskiya har zuwa mutuwa, Ya mai ji, ya mai karamci, ya mai amsa addu'oi !        

A nan huxubar farko ta qare!  

HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya xaukaka mu; da alqur'ani da sunnah,        Kuma ya sanya mu daga cikin mafi alherin al'ummai,      Ina gode masa akan ni'imominSa masu yawa,       Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shaidawar da take kasancewa mafi alherin kariya ga wanda yayi riqo da ita,         Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa;  UbangijinSa ya turo shi don ya zama rahama ga talikai.     Allah ya yi daxin salati da sallama a gare shi, salati da sallaman da za su zama a haxe, a miqe, har zuwa ranar sakamako!
        Bayan haka!
       
Ya ku musulmai!
        Ku bi dokokin Allah, ku kiyaye shi, sannan ku yi masa biyayya; kada ku sava masa!
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Taubah: 119].
       
Ya ku musulmai  !!
        Yin azumin yini shida a cikin watan shawwal sunnah ce tabbatacciya, a mafi ingancin zancen maluma,      Dalili kuma wanda jigajigan maluman riwayar hadisi suka tabbatar da karvuwarsa; kana suka inganta shi = yayi nuni akan wannan azumin,      Hadisi yazo daga Abu-Ayyub Al-ansariy (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم ) yace:
"Duk wanda yayi azumin watan ramadhana sa'annan ya biyar da guda shida daga shawwal to kamar ya yi azumin shekara ne",      Muslim ne ya rawaito shi.         An kuma rawaito daga Sauban (رضي الله عنه ) daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), lallai yace:
"Duk wanda yayi azumi guda shida bayan sallar azumi, to hakan shine cikon azumtar shekara (WANDA YA ZO DA KYAKKYAWA GUDA XAYA TO YANA DA GUDA GOMA KWATANKWACINSA", Ahmad da Ibnu-Majah suka rawaito shi .

Kuma cikin azumtar yini guda shida na shawwal ##
Akwai falala, a wajen ma'abota girma,    
Kuma lallai azumtarsu bayan idi yana daga cikin gaggawa zuwa ga alkhairi, da kuma saurin aikata ibada,    Kuma ana samun falalar azumtarSu idan aka yi su a jejjere, ko a rarrabe,      A farkon wata ne ko a qarshenSa,        Saidai kuma baya inganta ayi azuminsu da nufin haxa niyyarsu da kuma biyan abinda ake bin bawa na bashin ramadhana da ya wuce,     Duk kuma wanda ya aikata haka, to lallai bashin da ake binsa bai sauka akansa ba.      Kuma haramun ne a riqi rana ta takwas na watan shawwal a matsayin ranar idi ga mutumin da ya cika azuminsa guda shida na shawwal,    harma ya yi abinci na murna irin na idi,    ayi masa gaisuwa irin ta idi,   Har wassu jahilai su kira shi da sunan: IDIN MASU BIYAYYA (عيد الأبرار), Sai ka ji wanda ya kammala azuminsa guda shida yana cewa: WANNAN SHINE IDINA,     Duk wanda ya aikata wani abu daga cikin haka; to lallai ya qirqiro bidi'a a cikin addini,     kuma ya sava wa turbar salihan magabata,     Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah ta'alah yayi masa rahama- yace:
"Amma yinin takwas ga watan shawwal to ba ranar idi ba ne, a wajen mutanen kirki ko fajirai,    Kuma baya halatta wani mutum ya qudurta cewa wannan yinin na idi ne,    Kuma bai halatta a fari wani abu daga cikin alamomi ko aiyukan idi a cikin wannan yinin ba".   
       
        Sai ku yi salati da sallama ga mai shiryarwa, wanda zai ceci halittu gabaxaya,       saboda duk wanda ya yi masa salati guda xaya to Allah zai yi masa guda goma;
        ALLAHUMMA SALLI WA SALLIM ALA NABIYYINA WA SAYYIDINA MUHAMMADIN, wanda ke bishara da rahama da kuma lada,   mai kuma yin gargaxi kan kamun Allah da uquba,     mai yin ceto, wanda kuma za a ba shi ceton a ranar hisabi.
        Ya Allah kuma ka yarda da dukkan iyalanSa da sahabbai,     Ka haxa da mu Ya mai karamci,   Ya mai yin baiwa!
        Ya Allah ka xaukaka musulunci, kuma ka taimaki musulmai, kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai ….,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
……………….
……………….
Addu'a ,,,,,,,,,,,
……………….
……………….

………,,,,,,,,,,,, 

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...