2019/08/09

8 Zulhijjah 1440 Huzaifiy












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 7/MUHARRAM/1441H
daidai da 6/SEFTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI
(الحث على اغتنام الأوقات)
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allahn da ya halitta dukkan komai, kuma ya kaddara su kaddarawa, kuma ya sanya dare da yini akan yanayi na mayewa ga wanda yake nufin ya yi tunani ko yake son ya yi godiya.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi daya ne Makadaici, bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya kasance tamka a gare shi.
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa amintacce, ya isar da manzanci, ya sauke amana, ya yi nasiha ga al'umma, ya yi jihadi a al'amarin Allah iyakar jihadi, har mutuwa ta zo masa.
Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu da shiriyarsa, ya bi sunnarsa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:
Lallai mafi gaskiyar zance shine littafin Allah, kuma mafi karfin igiya ita ce kalmar takawa (LA ILAHA ILLAL LAHU), mafi alherin addinai addinin annabi Ibrahima, mafi kyan kissosi Alkur'ani, mafificin shiriya shiriyar annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, mafi sharrin al'amura sune kirkirarrunsu, kuma kowace bidi'a bata ce.
Ya ku, Bayin Allah…
Ku yi takawar Allah cikin abinda ya bada umurni, kuma ku hanu daga abinda ya yi hani kuma ya tsawatar, "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Lallai cikin juyawar yini da dare, da saurin zamani da canzuwan halaye, da zuwan sabin shekaru, da yadda ajali ke kokarin riskar ma'abutansa, dukansu dalili ne akan al'amarin gushewa da makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da buri: "Allah yana juyar da dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
Ka yi tunani akan Duniya da idon basira
Za ka ga Duniya walakantacciya ta shude kamar a mafarki

Wanda suke cikinta gaba daya, lallai za su kare
Sai fiskar Ubangijinka Ma'abucin girma ta wanzu

"Lallai a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da yini, da jiragen da suke gudana a cikin teku da abinda yake amfanar Mutane, da abinda Allah ya saukar daga sama na ruwa, sai ya rayar da kasa da shi a bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikin kasa daga dukkan dabba, da juyawan iskoki, da girgijen da aka hore a tsakanin sama da kasa, cikinsu gaba daya, akwai ayoyi ga Mutane masu hankalta" [Bakara: 164].

Ya ku taron Musulmai!!!
Kowace shekara ana kaddarata da lissafi, sai a sanya lokatan kaddara a cikinta, da ajalin yara da tsofi da samari, kuma ba a tsawaita shekarun mai shekara, kuma ba a tauye wani abu daga rayuwarsa, face yana cikin littafin (kaddara).
Tsareku suna karewa, burace-burace suna yankewa, ajali yana karewa, "Kuma dukkan wanda yake kan kasa mai karewa ne * kuma fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karamci ita ce take wanzuwa" [ArRahman: 26-27].
Sai ku ribaci damar shekaru da rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kanku, kuma kada ku rika jinkirta aiki, domin cikin hakan akwai hana rai aikin kwarai, kuma ku ribaci rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa da ayyuka, da wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta, "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga ubangijinku, kuma ku sallama masa, gabanin azaba ta zo muku, alhalin ku ba za a taimake ku ba * kuma ku bi mafi kyan abinda aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku gabanin azaba ta zo muku bisa auke, alhalin ku baku sani ba * sai rai ta ce: Ya nadamata akan abinda nayi sakaci a cikin sashen Allah, kuma hakika na kasance daga masu izgili * ko kuma kada ta ce: Da Allah ya shiryar da ni, da na kasance daga masu takawa * ko kuma kada -a lokacin da take ganin azaba- ta ce: Da ace ina da wata komawa (ga Duniya), domin in kasance daga cikin masu kyautatawa" [Zumar: 54-58].

Ya ku Musulmai!!!
Shekara ta kare, an rufe ayyukanta, an nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci damarsa, ya mori lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
Ku saurara!
Lallai mun shiga farkon sabuwar shekara, wanda hakan yake mana rakiya zuwa kaburbura, yake tafiya da mu zuwa yinin tayarwa a bayan mutuwa, to ya dace da mu, mu rika tafiyar da rayuwarmu cikin biyayyar Allah, "Kuma duk abinda kuka gabatar da shi na alheri za ku same shi a wurin Allah" [Muzzammil: 20].

Ya ku Bayin Allah!!!
Mafi alherinku shine wanda rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi sharri kuma shine wanda rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni.
Kuma daga cikinku kowa za a tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da samartakarsa ta yaya ya tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci, da mafi girman lokatai!
Dauki cewa, kuruciya tana bayyanar da uzurin ma'abucinta!
To menene uzurin masu furfurar da Shedan ya batar da su?

Ya ku taron Musulmai!!!
Lokatan rayuwa dama ne na yin aiki, kuma ni'ima ne da suke hukunta godiya, "Idan za ku nemi kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim: 34].
Kuma lokaci yana wucewa, rayuwar kadan ce, ayyukan wajibai wani akan wani, hakkoki kuma suna dayawa, don haka babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin hutawa da sakaci,
Ya ku bayin Allah! Sai ku ji jankunne mai tsoratarwa, da tattaunawa mai kama kunne, a inda Allah Ta'alah zai tambayi bayinSa: "Ya ce: Nawa kuka zauna a bayan kasa, na kidayar shekaru? * Za su ce: Mun zauna yini daya, ko rabin yini, sai ka tambayi masu kidayawa! * Ya ce: Ba ku zauna ba face kadan, da kun kasance kuna sani * Shin zato kuke yi cewa, Mun halitta ku ne domin wasa, kuma lallai ku zuwa gare mu ba za a mayar da ku ba!? * Allah Mamallakin Gaskiya ya daukaka, babu abin bautawa face shi, shine Ubangijin al'arshi mai daraja" [Muminuna: 112-116].
Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga akan kyautatawarsa, kuma godiya tasa ce akan datarwarSa da baiwarSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninsa.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa mai kira ga samun yardarSa.
Ya Allah ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa da sallamar aminci mai yawa.

Ya ku Musulmai!!!
Ku ji tsoron Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma ku tabbatar da zantukanku da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum ita ce abinda ya tafiyar da ita a cikin biyayyar Allah, kuma "Mai hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai kuma yake kwallafa wa Allah buri".

Ya ku Bayin Allah!!!
Cikin shudewar zamani akwai abin lura mai girma, kuma cikin jujjuyawar kwanaki akwai fadakarwa mai girma, "Lallai ne a cikin sabawar dare da yini, da abinda Allah ya halitta a cikin sammai da kasa, hakika akwai ayoyi ga Mutane masu takawa" [Yunus: 6].

Sannan ku sani!
Lallai Allah ya zabi zababbu daga halittunSa, sai ya zabi manzanni 'yan aika daga cikin Mala'iku, suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga cikin magana kuma ya zabi ambatonsa, a doron kasa kuma ya zabi masallatai, daga cikin watanni kuma ya zabi watan Ramadhana da watanni hudu masu alfarma, daga cikin kwanaki kuma yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai ku rika girmama abinda Allah ya girmama!

Ku saurara!
Lallai ku, ga ku a farkon watan Muharram, kuma farkon shekarar hijira, kuma lallai wannan watan yana cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda Allah ya girmama su, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha biyu, a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga cikinsu akwai hudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku zalunci  kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
Lallai zalunci –Ya ku taron Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya girmama alfarmar watanni (hudu) masu alfarma, ya sanya aikata zunubi a cikinsu yafi girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin shima yafi girma.
An ruwaito daga Abu-bakrah –رضي الله عنه-, daga Annabi –صلى الله عليه وسلم-  ya ce: "Lallai zamani ya juya, kamar yanayinsa, a lokacin da Allah ya halitta sammai da kassai. Shekara daya watanni goma sha biyu ne, daga cikinsu akwai guda hudu masu alfarma; guda uku a jere; zul ka'adah da zulhijjah da Muharram, da kuma Rajab na kabilar Mudar, wanda yake tsakanin jumadah da Sha'aban", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma hakika Musulmai tun zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin hijirar Annabi –صلى الله عليه وسلم- daga garin Makkah zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi da shekarar hijira, saboda Allah ya rarrabe tsakanin gaskiya da barna da al'amarin hijira. Kuma sahabbai sun fari kidayar shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya tabbatu akan haka, kuma sai al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.

Ya ku taron Musulmai!!!  
        Lallai yana cikin shiriyar annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma yana cikin abinda suke kankare munanan laifuka, kuma yana daga godiyar Allah da girmama shi, yin azumin ranar Ashura, wanda shine ranar goma na watan Muharram.
An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: Yayin da Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya iso garin Madinah sai ya iske Yahudawa suna azumtar ranar Ashurah, Sai aka tambaye su akan haka, sai suka ce: Wannan shine yinin da Allah ya bada nasara wa annabi Musa da Banu-isra'ila a cikinsa akan Fir'auna, don haka muke azumtarsa domin girmama shi, sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mune muka fi jibintar Musa fiye da ku, sa'annan sai ya yi umurnin a azumce shi".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –صلى الله عليه وسلم – yana kirdadon yinin da ya fifita shi akan waninsa ba, fiye da wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana nufin watan ramadhana", Bukhari da Muslim ya ruwaito su.
        A cikin littafin Sahihu Muslim, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Azumtar yinin Arafah, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take gabaninsa da wanda take a bayansa. Azumtar yinin Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take a gabaninsa".
        Kuma a yayin da labari ya kai ga Annabi –صلى الله عليه وسلم- a karshen rayuwarsa cewa, lallai yahudawa suna rikon yinin Ashurah a matsayin idi, to sai yay i niyyar ya azumci ranar tara da goma, a shekarar da take tafe, amma sai mutuwa ta shiga tsakaninsu.
        An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce –a lokacin da Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya yi azumin yinin Ashurah, kuma ya bada umurnin a azumce shi- sai su ka ce: Ya Manzon Allah! Lallai Ashurah yini ne da Yahudawa da Nasara suke girmama shi, To sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: "To, idan shekara mai kamawa ta zo, insha Allahu, za mu azumci ranar Tara (Tasu'ah)", Yana nufin, tare da goma (Ashura). Ya ce: Shekara mai kamawan bata zo ba, face Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu. Muslim ya ruwaito shi.
        Don haka, abinda yafi falala –Ya ku Bayin Allah- shine a azumci yini daya gabanin Ashurah, domin a saba wa Yahudawa. Wanda kuma aka rinjaye shi ya kasa, to kada a rinjaye shi ga azumtar ranar Ashurah.

        Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai…


Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,



2019/08/02

Hudubar 1 zulhijjah 1440 a takaice kan FALALAR GOMAN FARKO NA ZULHIJJAH 1zulhijjah 1440 Subaitiy



1- Wanda ya ribaci lokatan ayyukan ɗa'a, kuma ya yi gaggawa zuwa ga aikata alkhairori, sai a bubbuɗe masa taskokin falala da taimako da rahama, kuma sai ya rabauta da rabo mai girma.
2- Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi Wasallama- ya shaida mana cewa, kwanakin sune mafifitan kwanakin Duniya, a cikin faɗinsa: "Mafifitan kwanakin Duniya sune guda goma", yana nufin goman farkon zulhijjah. Sai aka ce: A cikin fita yaƙi fiysabililLahi babu kamar goman? Sai ya ce, e, babu kamarsu a cikin yaƙi fiysabililLahi, sai ga Mutumin da ya turbuɗe fiskarsa da turɓaya (ya mutu a wurin gumurzu). Albazzar da Ibnu-Hibbana suka ruwaito shi.
3- A cikin kwanaki goman akwai Yinin Arafah, yinin rukunin hajji wanda yafi girma, kuma yinin gafarar zunubai. Kuma a cikin kwanakin akwai ranar layya, wanda shine gaba ɗaya mafificin yini, a wurin Allah.
4- Sababin da ya sanya kwanaki goman farkon zulhijjah suka yi fice da fifiko, shine domin haɗuwar jiga-jigan ibadodi a cikinsu, wanda su ne: Sallah, Azumi, Sadaka, da Hajji. Kuma lallai hakan baya yiwuwa a cikin wasu kwanakin idan ba su ba.
5- Waɗannan kwanakin guda goma lokaci ne mai girma, kuma babbar ni'ima, sannan dama ce wanda ya wajaba a tsaya a ci gajiyarsu, kuma (mustahabbi ne) Musulmi ya keɓance su da ƙarin ibadodi, yana mai yaƙar zuciyarsa a cikinsu, domin ya yawaita fiskoki na alheri da ayyukan ɗa'a.
6- Kuma yana daga cikin ayyukan: Yin azumi, wato azumtar kwanaki taran farko na watan zulhijjah, saidai wanda yafi muhimmanci a cikinsu shine azumin ranar Arafah ga wanda ba Mahajjaci ba. Kuma azumi yana cikin ayyuka mafiya fifiko, kuma Allah ya keɓe sanin azumi ga kansa.

Tsakurowa daga hudubar 1 Zulhijja 1440 kan falalar goman farkon Zulhijjah


1- Allah a kwanakin rayuwa ya sanya wasu lokatai na alheri, ya kuma bada damammaki domin a iya guzuri da ayyukan ɗa'oi, waɗanda Musulmi a cikinsu zai samu mafi ƙoƙoluwar darajoji, ya rabauta da samun rahamar Allah da falalarSa. Hakan (kawo lokutan alkhairi) ya kasance ne saboda hikimomi masu girma, da hanyoyin tarbiyyah maɗaukaka. Mafi girmar hikimar kuma itace, domin Bawa ya kasance mai ƙaƙƙarfar alaƙa da UbangijinSa.
2- Waɗannan lokatan suna ƙara imani, suna haɓaka taƙawa, suna kuma ɗaukaka maka ma'aunin ayyukanka kyawawa. Waɗannan lokatan suna tsarkake ruhi, suna tsaftace rai, suna ƙarfafar himma, suna zama canji ga tawaya ko matsalar da ake samu a cikin ibada, suna tunkuɗe ɗabi'ar ƙosawa da ibada da samun raunin himma, ko rashin marmarin ibada, kuma suna bubbuɗe ƙofofi masu faɗi na tsere.
3- Haƙiƙa Allah ya umurci bayinSa da aikata alkhairori, da yin gaggawa gare su, kuma ya yaba wa ma'abuta waɗannan sifofin, a inda ya ce: "Sai ku yi tsere ga ayyukan alherori" [Ma'idah: 48]. Wannan kuma faɗakarwa ne ga himmomin ma'abuta hankula, da cewar su yi gaggawa ko saurin aikata ayyukan kwarai gabanin ƙurewar lokaci.
4- Lokutan alheri basu yankewa a cikin al'ummar Musulunci, Yanzu haka, ga al'ummar ta fiskanci mafi falalar lokutan alheri wanda suka fi girma (wato, kwanaki goman farkon watan zulhijjah). Allah ya yi rantsuwa da kwanakin, domin ya nuna mana matsayi da girman falalarsu, kuma Allah Mai girma, baya yin rantsuwa sai da abu mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ina rantsuwa da alfijir * Da dararuwa goma" [Fajr: 1-2]. Dararen sune na sanannun yini; waɗanda Allah ya shar'anta yawaita zikirinSa a cikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu, saboda abinda ya azurta su da shi na dabbobin ni'ima" [Hajj: 28].
5- Duk aiki na kwarai da ya auku a cikin kwanaki goman farkon zulhijjah, to shine yafi soyuwa a wurin Allah Ta'alah, idan irinsa ya auku a cikin kwanakin da ba su ba. Idan kuma aiki ya kasance shine mafi soyuwa to shine mafi falala. Kuma mai yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shine mafifici, akan wanda ya fita jihadi fiysabililLahi, matuƙar ya dawo da ransa da kuma dukiyarsa.
6- Yana daga cikin kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin guda goma: Tilawar Alƙur'ani, da zikirin Allah, da aadu'oi, da sadar da zumunci, da biya wa Musulmai buƙatunsu, da ziyartar marasa lafiya, da rakiyar gawa, da ciyar da abinci, da sauran ayyuka, tare da yawaita faɗin La ilaha illa Lah (Hailala) da Allahu Akbar (Kabbara) da faɗin Alhamdu lillahi (Hamdala), a cikin dukkan lokatai, a kuma kowane irin hali. Saboda idan Mutum ya san ƙimar abinda yake nema, to sai ya raina abinda yake bayarwa. Kuma lallai kayan sayarwar Allah yana da tsada, kuma lallai kayansan shine Aljannah.

2019/08/01

hudubar 1 zulhijja 1440 Subaitiy فضل العشر من ذي الحجة










HUƊUBAR MASALLACIN ANNABI SAW
JUMA'A 1/ZULHIJJAH/1440H
Daidai da 2/August/2019M






LIMAMI MAI HUƊUBA
Shehun Malami Dr. Abdulbariy ɗan Awwadh AsSubaitiy








TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA


بسم الله الرحمن الرحيم

Allah a kwanakin rayuwa ya sanya wasu lokatai na alheri, ya kuma bada damammaki domin a iya guzuri da ayyukan ɗa'oi, waɗanda Musulmi a cikinsu zai samu mafi ƙoƙoluwar darajoji, ya rabauta da samun rahamar Allah da falalarSa. Hakan (kawo lokutan alkhairi) ya kasance ne saboda hikimomi masu girma, da hanyoyin tarbiyyah maɗaukaka. Mafi girmar hikimar kuma itace, domin Bawa ya kasance mai ƙaƙƙarfar alaƙa da UbangijinSa.
Waɗannan lokatan suna ƙara imani, suna haɓaka taƙawa, suna kuma ɗaukaka maka ma'aunin ayyukanka kyawawa.
Waɗannan lokatan suna tsarkake ruhi, suna tsaftace rai, suna ƙarfafar himma, suna zama canji ga tawaya ko matsalar da ake samu a cikin ibada, suna tunkuɗe ɗabi'ar ƙosawa da ibada da samun raunin himma, ko rashin marmarin ibada, kuma suna bubbuɗe ƙofofi masu faɗi na tsere, Allah Ta'alah ya ce: "To, a cikin wannan, masu tsere sai su yi ta gwagwarmayar nema" [Mudaffifina: 26].
Yin gaggawa wajen aikata alkhairori, da neman maɗaukakan darajoji sifa ce ta Muminai makusanta Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Da masu gaggawa masu tsere * waɗannan sune aka kusantar * A cikin Aljannonin ni'ima" [Waki'ah: 10-12].
Wanda ya ribaci lokatan ayyukan ɗa'a, kuma ya yi gaggawa zuwa ga aikata alkhairori, sai a bubbuɗe masa taskokin falala da taimako da rahama, kuma sai ya rabauta da rabo mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma muka sanya su  jagorori suna shiryarwa da umurninmu, kuma muka yi wahayi zuwa gare su; da su aikata alkhairori, da tsayar da Sallah, da bayar da zakkah, kuma sun kasance masu bauta ne a gare mu" [Anbiya'i: 73].

Haƙiƙa Allah ya umurci bayinSa da aikata alkhairori, da yin gaggawa gare su, kuma ya yaba wa ma'abuta waɗannan sifofin, a inda ya ce: "Sai ku yi tsere ga ayyukan alherori" [Ma'idah: 48]. Wannan kuma faɗakarwa ne ga himmomin ma'abuta hankula, da cewar su yi gaggawa ko saurin aikata ayyukan kwarai gabanin ƙurewar lokaci.

Kuma Allah ya yi bushara ga masu tsere cikin ayyukan alkhairi da cewar suna da tabbataccen rigaye, da rabauta da samun alƙawarin Allah tabbatacce, a inda ya ce: "Waɗannan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alherori, kuma su a gare su, masu samun rigaye ne" [Muminuna: 61].

Kuma Mutum, lallai idan damar kusanci da yin biyayya ta halarto, to sai ya yi azama iyakar azama, wajen ribatar wannan damar da yin gaggawa zuwa gare ta. Kuma gajiyawa ta tabbata ne cikin jinkirtata, da cewa zan yi abin da sannu. Kuma lallai mai nawa da jinkiri bashi da wani rabo, a filin tseren rigaggeniya, kuma idan falalar samun alkhairi ya kuɓuce masa to zai tauni yatsu; domin nadama, a lokacin da nadamar ba za ta masa amfani ba.

Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kwaɗaitar da mu; dangane da ribatar shekarun samartaka gabanin saukar furfura da tsufa, da ribatar faragar lokaci gabanin yawaitar ayyuka da shagali, da morar lafiyarka gabanin cuta ta rafke ka kwatsam, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taƙawar Allah, kuma rai ta yi dubi kan abinda ta gabatar domin gobe, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne game da abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].

Allah Subhanahu ya bayyana cewa, lallai shiri domin fiskantar lokatan alheri -wanda kuma kadan ne mai wucewa- dalili ne da yake nuna gaskiyar Mutum, a inda Allah Subhanahu ya ce: "Don haka, idan al'amari ya ƙullu, to, da sun yi wa Allah gaskiya, lallai da hakan ya kasance mafifici a gare su" [Muhammadu: 21].

Wannan al'ummar tana da busawar rahama a cikin yinin zamaninta, Anas ɗan Malik -Allah ya ƙara yarda a gare shi- yana cewa: "Ku nemi alheri a tsawon zamaninku gaba ɗayansa, kuma ku bijiro da kayukanku ga wuraren busawar rahamar Allah Ta'alah; saboda Allah yana da wuraren busawar rahamarSa, wanda yake shafan wanda ya so da su daga Bayinsa".

Lokutan alheri basu yankewa a cikin al'ummar Musulunci, Yanzu haka, ga al'ummar ta fiskanci mafi falalar lokutan alheri wanda suka fi girma (wato, kwanaki goman farkon watan zulhijjah).
Allah ya yi rantsuwa da kwanakin, domin ya nuna mana matsayi da girman falalarsu, kuma Allah Mai girma, baya yin rantsuwa sai da abu mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ina rantsuwa da alfijir * Da dararuwa goma" [Fajr: 1-2].
Dararen sune na sanannun yini; waɗanda Allah ya shar'anta yawaita zikirinSa a cikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu, saboda abinda ya azurta su da shi na dabbobin ni'ima" [Hajj: 28].

Manzon Allah -Sallal Lahu alaihi Wasallama- ya shaida mana cewa, kwanakin sune mafifitan kwanakin Duniya, a cikin faɗinsa: "Mafifitan kwanakin Duniya sune guda goma", yana nufin goman farkon zulhijjah. Sai aka ce: A cikin fita yaƙi fiysabililLahi babu kamar goman? Sai ya ce, e, babu kamarsu a cikin yaƙi fiysabililLahi, sai ga Mutumin da ya turbuɗe fiskarsa da turɓaya (ya mutu a wurin gumurzu). Albazzar da Ibnu-Hibbana suka ruwaito shi.

A cikin kwanaki goman akwai Yinin Arafah, yinin rukunin hajji wanda yafi girma, kuma yinin gafarar zunubai.

Kuma a cikin kwanakin akwai ranar layya, wanda shine gaba ɗaya mafificin yini, a wurin Allah.

Sababin da ya sanya kwanaki goman farkon zulhijjah suka yi fice da fifiko, shine domin haɗuwar jiga-jigan ibadodi a cikinsu, wanda su ne: Sallah, Azumi, Sadaka, da Hajji. Kuma lallai hakan baya yiwuwa a cikin wasu kwanakin idan ba su ba; Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wasu yini wanda aiki nagari, ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah, fiye da waɗannan kwanakin", wato, goman farko na watan hajji. Sai su ka ce: Ya Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne, fiy sabilillah? Sai ya ce: "Koda jihadi ne, fiy sabilillah, sai ga Mutumin da ya fita da kansa, da kuma dukiyarsa baki ɗaya, amma shi da dukiyar babu wanda ya koma". Isnadinsa ingantacce ne akan sharaɗin Bukhari da Muslim.
Don haka, duk aiki na kwarai da ya auku a cikin kwanaki goman farkon zulhijjah, to shine yafi soyuwa a wurin Allah Ta'alah, idan irinsa ya auku a cikin kwanakin da ba su ba.
Idan kuma aiki ya kasance shine mafi soyuwa to shine mafi falala. Kuma mai yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shine mafifici, akan wanda ya fita jihadi fiysabililLahi, matuƙar ya dawo da ransa da kuma dukiyarsa.


Ana fiskanta ko shiga waɗannan kwanakin ne guda goma, da tuba ta gaskiya, da kulla azama kan ribatarsu, da nisantar ayyukan saɓo, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya -Ya ku Muminai- domin ku samu babban rabo" [Nur: 31].

Waɗannan kwanakin guda goma lokaci ne mai girma, kuma babbar ni'ima, sannan dama ce wanda ya wajaba a tsaya a ci gajiyarsu, kuma (mustahabbi ne) Musulmi ya keɓance su da ƙarin ibadodi, yana mai yaƙar zuciyarsa a cikinsu, domin ya yawaita fiskoki na alheri da ayyukan ɗa'a, Annabi SAW ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki ya fi girma kuma ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah fiye da waɗannan kwanakin goma; sai ku yawaita hailala a cikinsu". (Wato, faɗin: LA ILAHA ILLAL LAHU) da kabbara (faɗin: ALLAHU AKBAR) da hamdala (faɗin: ALHAMDU LILLAHI). Ahmad ya ruwaito shi.

Yana daga cikin waɗannan ayyukan: Yawaita sallolin nafilfili, Manzon Allah SAW ya ce:  "Ina horonka da yawaita sujjada ga Allah, saboda ba zaka yi sujjada ɗaya ga Allah ba, face ya ɗaukaka darajarka da ita, ya kuma kankare maka zunubi da ita". Muslim ya ruwaito shi.

Kuma yana daga cikin ayyukan: Yawaita sadakoki, da nufin samun kusanci zuwa ga Allah, da neman yardarSa da ladanSa, ko ta hanyar kyautuka da kyautatawa da toshe buƙatar faƙirai da Miskinai da marayu, Manzon Allah SAW ya ce: "Akan kowane Musulmi akwai sadaka, Sai suka ce: Ya Annabin Allah, Wanda kuma bai samu ba? Ya ce: Ya yi aikin hannunsa sai ya amfanar da kansa ya yi sadaka, Sai suka ce: Idan kuma bai samu ba? Ya ce: Ya taimaki gajiyayye. Sai suka ce: Idan kuma bai samu ba? Ya ce: Ya yi aiki da kyakkyawa, ya kuma kame daga aikata sharri, to lallai hakan sadaka ne". Bukhariy ya ruwaito shi.

Yana daga ayyukan kwarai: Sallolin dare; wato Bayi su tsayu suna neman gafara, suna zikiri, Allah Ta'alah ya ce: "Sune waɗanda suke kwana ga Ubangijinsu suna masu sujada da tsayuwa". [Furƙan: 64].


Huɗuba ta biyu

Yana daga cikin kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin guda goma: Tilawar Alƙur'ani, da zikirin Allah, da aadu'oi, da sadar da zumunci, da biya wa Musulmai buƙatunsu, da ziyartar marasa lafiya, da rakiyar gawa, da ciyar da abinci, da sauran ayyuka, tare da yawaita faɗin La ilaha illa Lah (Hailala) da Allahu Akbar (Kabbara) da faɗin Alhamdu lillahi (Hamdala), a cikin dukkan lokatai, a kuma kowane irin hali. Saboda idan Mutum ya san ƙimar abinda yake nema, to sai ya raina abinda yake bayarwa. Kuma lallai kayan sayarwar Allah yana da tsada, kuma lallai kayansan shine Aljannah, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku yi gaggawa zuwa samun wata gafara daga Ubangijinku, da kuma Aljannar da faɗinta shine faɗin sammai da ƙassai, an tanade ta ga masu taƙawa" [Ali-imrana: 133].


Kuma yana daga cikin ayyukan: Yin azumi, wato azumtar kwanaki taran farko na watan zulhijjah, saidai wanda yafi muhimmanci a cikinsu shine azumin ranar Arafah ga wanda ba Mahajjaci ba. Kuma azumi yana cikin ayyuka mafiya fifiko, kuma Allah ya keɓe sanin azumi ga kansa, kamar yadda ya zo cikin hadisin Ƙudusiy: "Dukkan aikin Ɗan Adam nasa ne, in banda azumi, shi kam nawa ne, kuma nine Mai yin sakayya akansa". Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah SAW ya kasance yana azumtar kwanaki taran farkon zulhijjah, kuma Manzon Allah SAW ya ce:  "Wanda ya yi azumin yini ɗaya fiysabililLahi, Allah zai nisantar da fiskarsa daga wuta na tsawon shekaru saba'in". Bukhariy ya ruwaito shi.
Addu'a ….
……………….



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...