Matashiya akan azumin Ramadhana (01)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
madaukakin sarki.
Salati
da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da sahabbansa masu
karamci.
Bayan
haka,
Abinda
zai rika zuwa muku a kullum, hadisai ne kan azumin watan ramadhana, da
kwadaitarwa kan nau'uka, ko dangogin ibadodin da su ke cikin watan, kamar
sallar tarawihi da falalarta, da yawaita karatun Alkur'ani, da yawaita kyautuka
da sadakoki, da falalar yin umrah a cikin watan, da i'itikafi, da neman
lailatul kadari, da zakkar kono (fidri), da idin azumi da hukunce-hukuncensa,
da sauransu.
Da
fatan Allah ya azurta mu da ikhlasi cikin zance da aiki, saboda ya zo cikin
hadisin da ke tafe cewa:
عن عُمَر بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه،
قال:
سَمِعْتُ
رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«إِنَّمَا
الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ
هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ،
وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا
فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
أخرجه
البخاريّ [1] ومسلم [1907].
Fassara:
An
ruwaito daga Umar dan Alkhaddabi -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Na
ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:
"Dukkan ayyuka su kan ingantu ne da niyya, kuma lallai kowane
mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda
Allah ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa. Wanda
kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniyar da zai same ta, ko saboda wata
matar da zai aura, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da ya yi hijira dominsa".
Bukhariy [1] ya rawaito shi, da Muslim [1907].
Sai
dai kuma
LOKACIN
NIYYA A AZUMIN FARILLA; YANA BANBANTA DA NA NAFILA kamar yadda ya
tabbatu a cikin hadisin da ke tafe;
عَنْ
عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ، عَنْ حَفْصَةَ رضي الله عنهما،
عَنِ
النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«مَنْ لَمْ
يُبَيِّتِ الصِّيَامَ قَبْلَ الْفَجْرِ، فَلا صِيَامَ لَه».
أخرجه
الترمذي [733]، والنسائي [4/196]، وابن ماجه [1700]،
وصححه
الألباني في صحيح الترمذي [583].
Fassara:
An
ruwaito daga Abdullahi dan Umar, daga Hafsat -Allah ya kara yarda a gare su-,
daga
Annabi -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Duk wanda bai kwana da niyyar azumi gabanin ketowar alfijir
ba to bashi da azumi".
Tirmiziy
[733] ya rawaito shi, da Nasa'iy [4/196], da Ibnu-majah [1700].
Kuma
Albaniy ya inganta shi, cikin [Sahihut Tirmiziy, 583].
Kuma
hadisi, ya zo
عَنْ
عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ:
دَخَلَ
عَلَيَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ فَقَالَ:
«هَلْ
عِنْدَكُمْ شَيْءٌ؟»
فَقُلْنَا:
لا،
قَالَ:
«فَإِنِّي إِذَنْ صَائِمٌ».
ثُمَّ
أَتَانَا يَوْمًا آخَرَ فَقُلْنَا:
يَا
رَسُولَ اللهِ، أُهْدِيَ لَنَا حَيْسٌ فَقَالَ:
«أَرِينِيهِ،
فَلَقَدْ أَصْبَحْتُ صَائِمًا»،
فَأَكَلَ.
أخرجه
مسلم [1154].
Fassara:
An
ruwaito daga A'ishah -Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce:
Annabi
–sallal lahu alaihi wa sallama- ya shigo kaina, a wani yini, sai ya ce:
"Shin, akwai wani abu a wajenku?"
Sai
mu ka ce: A'a; babu, Sai ya ce:
"To na dauki azumi!"
Sa'annan
sai ya zo wurinmu a wani yinin na daban, Sai mu ka ce:
An
kawo mana kyautar Haisa,
Sai
ya ce:
"Nuna min shi, Hakika da na wayi gari ina azumi",
Sai,
ya ci.
Muslim
[1154] ya rawaito shi.
Tsokaci
Wadannan
hadisan suna nuna;
(1) Wajabcin niyya, da
kasancewar ibada, azumi ko waninsa, basu zama ingantattu, kuma karbabbu a wurin
Allah face da niyya.
(2) Azumin farilla, dole
ne a kwana da niyya. Yayin da azumin nafila, ya halatta mutum ya niyyaci yinsa
da rana.
Allah
Shi ne mafi sani.
No comments:
Post a Comment