2018/01/18

hudubar 2 Jumadal Ula 1439H daidai 19 Yanairu 2018M ta Dr. Subaity







HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 2/JUMADAL ULAH/1439H
Daidai da 19/JANAIRU/2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY DAN AUWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
ALBARKAR RAYUWA
   Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 2/ Jumadal Ulah, 1439H, mai taken: ALBARKAR RAYUWA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna akan aminci da zaman lafiya, da yadda sha'anonin rayuwa gaba daya su ke rataye da shi, kuma cewa ba zai yiwu rayuwa ta miqe ba, ai idan akwai zaman lafiya, sannan ya ambaci sabuban da su ke rushe samun zaman lafiya, ko su ke girgiza gininsa, kamar yadda ya bayyana yadda ake samar da aminci da zaman lafiya.

HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya mana baiwa da ni'imar samun aminci da zaman lafiya, Ina yin yabo a gare shi (سبحانه) kuma ina godiya a gare shi, kuma ina roqonsa wa'aztuwa da xaukar izina.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, wanda ya ke cewa: "Kuma kowani abu a wurinsa yana da gwargwado" [Ra'ad: 8].
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, yayi kira (da'awah) zuwa ga Allah cikin hikima, da gwanancewa. Allah yayi qarin salati a gare shi da iyalansa matukar dare da yini suna canjin aiki.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah.
        Allah, ya sanya kasa a matsayin mazauni ga rayuwar bayi, ya kuma yi albarka a gare ta, ya kuma cike ta da alkhairori, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ya sanya, a cikinta, duwatsu kafaffu, daga samanta, kuma ya sanya albarka a cikinta, kuma ya kaddara ababen ci, daga cikinta" [Fussilat: 10].
        Allah (تعالى) ya zabi AnnabawanSa, kuma ya musu ni'imar albarka, a cikin rayuwarsu da ayyukansu, Allah (تعالى) ya ke fadi dangane da Annabi Nuh (عليه السلام): "A ka ce: Ya kai, Nuhu, ka sauka cikin aminci daga gare mu, da kuma albarkoki akanka, da kuma wasu daga al'ummomin da ke tare da kai" [Hud: 48].
A dangane da, annabi Isah (عليه السلام), Allah ya ce:  "Kuma ya sanya ni, Mai albarka, a duk inda nake" [Maryam: 31].
        Kuma albarkar Annabi (صلى الله عليه وسلم) ta tabbatu, kuma sahabbansa –Allah ya kara yarda a gare su- sun ganta, da idanuwansu.
        Kuma Alkur'ani yana da albarka; cikin binsa,da aiki da shi, kamar yadda Allah ya ke cewa: "Kuma wannan littafi ne da muka saukar da shi, mai albarka; sai ku bi shi, kuma kuyi takawa; domin ayi muku rahama" [An'am: 155].
        Ita kuma ALBARKA tana nufin, Bunkasa da daukaka, kuma idan albarka ta sauka ga abu, kadan sai ta yawaita shi, idan kuma ta tabbatu ga wani wuri, sai tasirinta ya bayyana, kuma alkhairinta ya yi yaduwa, kuma amfaninta sai ya game dukiya da 'ya'ya, da lokaci, da ilimi, da aiki, da gabbai gaba daya.
        Allah ya sanya albarka, ga dakinsa mai alfarma, da Madina gari mai dadin zama, da kuma masallacin Aksah da ke garin Kudus da bagiren da ya kewaye shi; Sai Allah ta'alah ya ce: "Lallai farkon dakin da aka sanya wa Mutane; shi ne ya ke garin Makkah; Mai albarka, kuma shiriya ga talikai" [Ali-imrana: 96].
        Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya Allah ka sanya wa garin Madina ninkin abinda ka sanya wa Makkah na albarka", Bukhariy ya ruwaito shi.
        Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar Isra'i da bawansa, daga Masallaci mai alfarma, zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda muka sanya albarka a gefensa, domin mu nuna masa daga ayoyinmu" [Isra'i: 1].
        Allah ya sanya albarka ga al'ummar Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ta yi ta bunksa dana samun daukaka, sai ta wayi gari ta rigayi dukkan al'ummai, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai cikin bishiyoyi akwai wata bishiya, wanda ganyenta kadewa, kuma wannan bishiyar it ace misalign musulmi, Ku ban labarin wace bishiya ce?", Ya ce, Sai mutane suka yi ta ambaton bishiyoyin jeji da kauye, Abdullahi dan Umar ya ce, sai ya darsu a zuciyata cewa it ace, bishiyar dabino. Sa'annan sahabbai suka ce: Ka bamu labarin wace bishiya ce, ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: "Lallai ita ce, itaciyar dabino", Bukhariy ya ruwaito shi.
        Shi musulmi yana kirdadon samun albarka a duk inda ta ke, domin ta game jikinsa da rayuwarsa da duk abinda ya ke kewayensa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan 'ya'yan itatuwa suka nuna, akan zo masa da su, sai ya ce: "Ya Allah ka sanya mana albarka ga Madinarmu, Ya Allah ka mana albarka cikin sa'inmu, Ya Allah ka sanya wa mudunmu albarka, Ya Allah ka sanya albarka ga Madinarmu, Ya Allah, ka sanya albarka biyu, a madadin daya", Muslim ya ruwaito shi.
        Mumini kan janyo albarka ga gidansa, ta hanyar dawwamar da ambaton Allah a cikinsa, da karanta suratul bakara, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan dayanku ya shiga gidansa, sai ya ambacin sunan Allah a lokacin shigansa, da lokacin cin abincinsa, Sao Shedan ya ce: Bani da wurin kwana a wurinku da abinci", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku karanta suratul bakara, domin karantata albarka ne, Kuma masu sihiri basa iya ta", Muslim ya ruwaito shi. Lafazin "بطلة" da ya zo cikin hadisin ma'anarsa shi ne, masu sihiri.
        Kuma ana janyo albarka ta hanyar lazimtar "istigfari", a cikin addu'ar annabi Nuh (عليه السلام) Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Sai na ce: Ku nemi gafarar Ubangijinku, domin shi ya kasance mai yawan gafara * Zai saki ruwan sama akanku, mamako * Sai kuma ya karfafe ku da wata dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku lambuna, kuma ya sanya muku koramu" [Nuh: 10-12].
Mumini yana kirdadon samun albarka ta hanyar lazimtar fita sallar asuba tare da jama'a, saboda a cikin sallar jam'i akwai samun rabo mai girma.
Kuma ana samun albarka ta hanyar yin sammako, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya Allah ka sanya albarka wa al'ummata cikin sammakonta", kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan zai tura zarata, ko runduna, yak an tura su, da farkon yini. Kuma maruwaicin hadisin mai suna Sakhar ya kasance mutum ne attajiri, sai ya kasance idan zai aika masu masa tijara, yak an aika su, da farkon yini, sai ya yi kudi; kuma dukiyarsa ta yawaita. Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne, hasan. Kuma Ibnu-Hibbana ya inganta shi.
Yin addu'an albarka shine mafi alherin abinda ke janyo samun falalarta, kuma yana kwalalo ni'imarta, saboda an ruwaito daga Akil dan Abu-dalib (رضي الله عنه) lallai shi ya auri wata mata daga kabilar Banu-Jushm, sai wadannan mutanen suka shigo wurinsa suka ce masa: Allah ya bada daidaitar hali, da ciki da goyo, Sai ya ce: "Kada ku aikata haka, Sai suka ce, to me za mu ce, Ya Abu-Zaid? Sai ya ce: Ku ce: BARAKAL LAHU LAKUM, WA BARAKA ALAIKUM, addu'ar albarka, domin da fadin haka, muka kasance ake umartarmu", Ahmad ya ruwaito shi, da isnadi ingantacce.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan zai yi addu'ar rakiyar ma'auraci, ya kan ce: "BARAKAL LAHU LAKA, WA BARAKA ALAIKA, WA JAMA'A BAINAKUMA FIY KHAIRIN, Wato, Allah ya maka albarka, ya sanya maka albarka, kuma ya sada tsakaninku da alkhairi", Tirmiziy ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.

Kuma albarka tana tabbatuwa, ta hanyar lazimtar gaisuwar musulunci, wanda tana daga cikin abinda wannan al'ummar mai albarka ta kebanta da su, Allah (تعالى) ya ce: "Idan za ku shiga gidaje, sai ku yi sallama ga kayukanku, gaisuwa ce daga Allah, mai albarka mai dadi" [Nur: 61].
A cikin tijarar kasuwanci kuma, ana janyo albarka ne ta hanyar yin gaskiya, da bayyana aibin kaya,Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mai saye da mai sayarwa, suna da zabi matukar basu rabu ba, ko kuma ya ce: har zuwa su rabu. Idan har suka yi gaskiya wa juna, suka bayyana aibi, sai a sanya musu albarka a cikin kasuwarsu, Idan kuma suka boye, suka yi karya, sai a kwashe albarkar kasuwarsu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Shima sadar da zumunci yana tsawaita rayuwa kuma yana sanya albarka a cikin arziki, Bukhariy da Muslim sun fitar da hadisi daga Anas (رضي الله عنه), cewa Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Duk wanda zai faranta masa a yalwata arzikinsa, ko a tsawaita ajalinsa, to ya sadar da zumuncinsa".

Shima dinke Baraka da hadin kai, Yana janyo samun albarka, da saukarta, kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana kwadaitar da sahabbansa kan hadin kai, da nisantar rarrabar kai, a cikin dukkan yanayinsu, Sahabbai su ka ce, Ya MAnzon Allah, Lallai muna cin abinci, bama koshi, Sai ya ce: "Shin kuna haduwa ne wajen cin abincinku, ko kuna ci a rarrabe?" sai suka ce: A a muna ci ne a rarrabe, Sai ya ce: "Ku rika haduwa akan abincinku, ku ambaci sunan Allah, sai a sanya muku albarka", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, a cikin sahihinsa.

Raunanan mutane a cikin al'umma, wani fage ne ga mutumin da ke neman yawaitar albarka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin za a baku nasara ne, ko arziki, ba don raunanan cikinku ba?", Bukhariy ya ruwaito shi. A wata riwayar kuma "Ku nemo min raunanan cikinku, Shin za a baku arziki, da nasara ne, ba don saboda raunananku ba?", Tirmiziy ya ruwaito shi da isnadi ingantacce.

Kuma idan albarka ta sauka, a cikin rayuwar musulmi, sai Allah ya azurta shi da hankali nunanne da sanin addini, da zuciyar da take raye da ilimi da imani, saboda an ruwaito daga Ibnu-Abbas (رضي الله عنهما) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya shiga makewayi domin biyan bukata, sai Ibnu Abbas ya sanya masa ruwan alwala, Sai ya ce: "Wanene ya ajiye min wannan?" sai aka bashi labara, sai y ace: "Ya Allah ka fahimtar da shi addini", Bukhariy ya ruwaito shi. Sai Allah ya amsa wa Annabinsa, Sai Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ya samu ilimi, Wani daga cikinsu yace: "Na ga Abdullahi bn Abbas, alhalin dubban daliban hadisi sun taru a wurinsa".

Kuma albarka tana bayyana a rayuwar musulmi ta yadda za a datar da shi da yada ilimi mai yawa, da fitar da rubuce-rubuce masu tarin alkhairi, daya-bayan-daya cikin lokaci kadan, ba tare da wahala mai yaw aba, Wannan kuma taimako ne na musamman, da ake karfafar mutum da shi, wanda ke zame masa agaji wajen aikin biyayya, da ibada.

Tsawon rayuwa, tare da kyan zance da aiki, yana daga misalan albarkar da Allah ke bada ita ga wadanda ya datar da su, daga cikin bayinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Albarka tana tare da wadanda suka fi girman shekaru a cikinku", Ibnu-hibbana yay a ruwaito sbhi a cikin sahihinsa.

Yana daga misalan albarka a rayuwar musulmi, a azurta shi da mace saliha; tagari, mai yawan haihuwa da soyayya, sai kuma a bashi zurriya na-kirki da ita, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ana auren mace domin abubuwa hudu; saboda dukiyarta, da danginta, da kyanta, da kuma addininta; sai ka rabauta da ma'abuciya addini hannayenka zasu damki turbaya", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi. Ita kuma ma'abuciyar addini zata yawaita albarka a cikin gidan, saboda turbaya alama ce bunkasa da karuwar alkhairi.

Allah ya kwalala wa mutum dukiya mai tarin yawa, sannan ya datar da shi, wajen ciyar da wannan dukiyar ta fiskokin alkhairi da kyautatawa, albarka ce a fili, kuma ni'ima mai gamewa, kuma albarka tana kara albarka a duk lokacin da ake tsarkake dukiya daga abinda ka iya shiga masa. Duk kuma wanda ya sanya dukiyarsa cikin fushin Allah, ya kuma hana hakkin Allah, to sai a cire albarkar dukiyar, Allah (تعالى) ya ce: "Allah yana kwashe albarkar riba, kuma yana kara albarkar sadakoki, kuma Allah baya son dukkan yawan kafirci mai zunubi", [Bakara: 276].

        Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alkur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,    Ina fadar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUDUBA TA BIYU
        Alhaki ne akan musulmai gaba daya, su rika neman albarka a cikin kasashensu da al'ummarsu, da kokarin samar da sabubanta, Kuma babba daga cikin sabuban albarkar shine: RAYA KASA DA YIN AIKI DA TSARI KO SHARI'AR ALLA, Allah (تعالى) ya ce: "Da ma'abuta alkaryu za su yi imani, su yi takawa, da mun bubbude musu kofofin albarkoki, daga sama da kasa, Amma kuma sun karyata sai muka kama su da abinda suka kasance suke aikatawa", [A'araf: 96].

        Kuma babu mai hankali shiryayye da zai yi musun cewa lallai kawar da kai daga aiki da tsari ko shari'ar Allah, sababi ne na gushewar albarka, da tafiyar alkhairi; saboda Allah ya bamu labarin mutanen garin Saba'I; wadanda aka canza musu, bayan basu albarka da bunkasa, aka canja musu, da kwashe albarkar, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma hakika saba'awa (mutanen garin Saba'i) ya kasance suna da ayar lura a wurin zamansu; gonakin lanbu biyu ta dama da hagu; sai muka ce musu ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi godiya a gare shi; gari mai dadin zama, da kuma Ubangiji Mai yawan gafara * Sai suka bijire, sai muka saki malalin arami na dam akansu, kuma muka musanya musu gonakinsu biyu da wadansu gonaki masu 'ya'yan itace kadan; talakiya da goruba, da wani abu na magarya kadan", [Saba'i: 15-16].



Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa.         Ya Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu da iyalansa da sahabbansa masu krimci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
        Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini, Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
        Ya Allah! Ka karvi azuminmu da sallolinmu da ruku'inmu da sujadanmu, Ya Allah! Ka sanya mu daga cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba.
        Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
        Ya Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka kiyaye su a ko-ina suke, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai tagaza musu, Ya Allah! Ka karvi wanda ya mutu daga cikinsu yana mai shahada, Ya Allah! Ka xaukaka darajarsu cikin darajar "illiyuna", Ya Allah! Ka ninnika kyawawansu, kuma ka yi musu rangwame akan munanansu, kuma ka xinke karayar iyalansu da danginsu, Ya Ubangijin talikai.
        Ya Allah! Wanda ya nufe mu, ko ya nufi musulmai da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa Ya mai amsa addu'a.
        Ya Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Ubangijin halittu.
        Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, kuma ka bashi lafiya, Ya ubangijin talikai.
        Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya mafi rahamar masu rahama.
        "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
        "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN, WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA" []…..
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,



2018/01/04

خطبة 18 ربيع الثاني للدكتور عبد المحسن القاسم MASALLACIN MANZON ALLAH saw










HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/RABIYUS-SANIY/1439H
Daidai da 5 /JANAIRU / 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN ALKASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar da shi, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a cikin musulunci da igiya mai karfi (ta LA ILAHA ILLAL LAHU).

        Ya ku musulmai …
        Tauhidi, hakkin Allah ne akan bayinsa, Kuma da tauhidi Allah ya tayar da ManzanninSa, kuma don shi ya saukar da littatafanSa.
        Kuma      HAKIKANIN TAUHIDI shine kadaita Allah a cikin bauta.
        Ita kuma BAUTA suna ne da ta game dukkan abinda Allah ke sonsa, kuma ya yarda da shi, na daga zantuka, da ayyuka, na zahirinsu da na boye; don haka Zuciya tana da ibadodin da suka kebance ta,
        Kuma IBADAR ZUCIYA tafi girma a kan ibadar gabbai, kuma ibadun zuciya sun fi yawa, kuma sun fi dawwama, kuma shigan ayyukan zuciya cikin "sunan imani", shine yafi cancanta a kan shigan ayyukan gabbai, don haka, Addinin da ke tsayuwa a zukata na daga imani; ta fiskar sanin imanin da aiki da shi, shine ginshikin da ake nufin halittu su samar da shi. Su kuma sauran ayyuka na zahiri suna biye da shi, kuma suna cike shi. Kuma ayyukan gabbai basa zama ingantattu karbabbu a wurin Allah, sai idan sun bi ta hanyar ayyukan zukata; don haka; ayyukan zuciya sune tsantsar bauta tsagwaronta. Kuma idan ayyukan gabbai na zahiri suka wofanta daga ta'allaka da aikin zuciya sai su kasance tamkar mataccen jikin da bashi da rai. kuma da gyaruwan zuciya, gangar jiki ke gyaruwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta baci, to dukkan jiki ya baci, Ita ce: zuciya", Bukhariy da Muslim.

        BAYIN ALLAH, wani kan fi wani, saboda fifikon da ake samu na abinda ke cikin zukatansu, kuma da hakan ayyukansu suke samun fifiko, Kuma zuciya ita ce, wurin da ganin Ubangiji ke rataya, daga jikin bayinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah, baya yin dubi ga jikinku, ko surar halittarku, Kawai yana yin dubi ne zuwa ga zukatanku da ayyukanku", Bukhariy da Muslim.

        Yana daga cikin AYYUKAN ZUKATAN DA SUKA FI MUHIMMANCI; KYAUTATA ZATO GA ALLAH (حسن الظن بالله), domin yana cikin abinda musulunci ya farlanta, kuma daya ne, daga hakkokin tauhidi, da wajibansa.
        MA'ANARSA MAI GAMEWA kuma shi ne; Dukkan zaton da ya allaku, da kamalar zatin Allah (سبحانه) da kamalar sunayenSa da sifofinSa; saboda kyautata zato ga Allah, reshe ne na ilimi ko sanin Allah, kuma abinda kyakkyawan zato ya ginu akansa shine SANIN YALWAR RAHAMAR ALLAH, DA BUWAYARSA DA KYAUTATAWARSA, DA KUDURARSA, DA ILIMINSA, DA KYAKKYAWAN ZABINSA, To idan ilimin bawa ga hakan ya zama cikakke, to ba makawa, sai ya haifar masa da kyautata zato ga UbangijinSa. Kuma ibadar kyautata zato, wani lokacin ta kan samu ne sakamakon halarto da ma'anar wasu daga cikin sunayen Allah da sifofinSa.
Kuma wanda zuciyarsa ta dauki hakikanin ma'anonin sunayen Allah da sifofinSa, to sai kyautata zaton da ke da alaka da kowani suna, da sifa su tsayu a cikin zuciyarsa; saboda kowace sifa tana da nau'in bautar da ta kebantu da ita, da nau'in kyautata zaton da ya kebanca ta (sifar).

Kamalar Allah da girmanSa da kyanSa, da falalolinSa ga halittunSa, suna wajabta a kyautata masa zato (جل وعلا); kuma da hakan Allah ya umarci bayinSa, a inda ya ce: "Kuma ku kyautata, domin Allah yana son masu kyautatawa", [Bakara: 195].
Sufyanus sauriy –رحمه الله- ya ce: "Ma'ana: Ku kyautata zatonku ga Allah".
        Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) gabanin wafatinsa ya karfafa wannan lamari, saboda girman matsayinsa, Jabir dan Abdullahi (رضي الله عنه) ya  ce na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) gabanin rasuwarsa da yini uku yana cewa: "Kada wani daga cikinku ya mutu, face yana mai kyautata zatonsa ga Allah (عز وجل)", Muslim ya ruwaito shi.
        Kuma hakika Allah ya yi yabo ga bayinSa masu tawali'u a gare shi, da cewa suna kyautata zatonsu ga Allah, kuma ya sanya bushararsu ta gaggawa ita ce, saukake musu bautarsa, kuma ya sanya ta zama taimako a gare su, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku nemi taimako da yin hakuri, da salla, kuma lallai ne ita sallah, mai girma ce, face akan masu tsoron Allah * wadannan da suke da tabbacin cewa, su masu haduwa ne da Ubangijinsu, kuma lallai ne zuwa gare shi masu komawa ne", [Bakara: 45-46].

        Hakika Manzanni (عليهم السلام) sun samu matsayi madaukaki, ta fiskar saninsu ga Allah; sai suka fawwala lamuransu zuwa gare shi, suna masu kyautata zatonsu ga Ubangijinsu;
Ga annabi Ibrahima (عليه السلام) ya yi hijira zuwa ga dakin Allah, alhalin babu wani mutum a wannan lokacin a garin Makkah, kuma babu ruwa a garin, (tare da matarsa). A lokacin da annabi Ibrahima ya juya zai tafi, sai matar ta biyo shi, tana cewa: "Ya kai Ibrahima, ina zaka tafi, ka barmu a wannan kwarin, wanda babu wani mutum ko wani abu a cikinsa? Sai ta yi ta gaya masa hakan, dayawa, Sai ya zama baya juyawa zuwa gare ta, Sai ta ce, Shin Allah ne ya umarce ka, da aikata hakan? Sai ya ce, Na'am. Sai ta ce, To lallai ba zai tozarta mu ba", Bukhariy ya ruwaito shi. Sai ya zama karshen akibar kyautata zatonta ga Allah, shine, yadda ruwa mai albarka (na zamzam) ya bulbulo musu, kuma aka raya wannan daki da bauta, ambaton wannan matar kuma ya wanzu a duniya, danta Isma'ilu shi kuma ya kasance annabi, kuma daga zurriyarsa aka samu cika-makon annabawa, kuma jagoran manzanni (محمد صلى الله عليه وسلم).

        Annabi Ya'akubu (عليه السلام) ya yi rashin 'ya'yansa, sai ya yi hakuri, ya fawwala lamarinsa ga Allah, kuma ya ce: "Abin sani kawai, ina kai koken bacin raina da bakin cikina zuwa ga Allah", [Yusuf: 86]. Sai zuciyarsa ta wanzu, cike da kyautata zato ga Allah, da jin cewa shine mafi alherin masu kiyaye bayi, sannan ya ce: "Kuma akwai tsammanin Allah ya zo min da su gaba daya, domin shine Masani Mai hikima" [Yusuf: 83]. Kuma ya fadakar da sauran 'ya'yansa, da irin hakan, a inda ya ce: "Ya ku diyana, sai ku tafi, ku nemo labarin Yusufa da dan'uwansa, kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, Lallai ne babu mai yanke tsammani daga rahamar Allah, face mutane kafirai", [Yusuf: 87].

        'Ya'yan Ya'akuba, (wato, Banu-isra'ila) nau'ukan cutar da ba za a iya jure musu ba, sun riske su, amma tare da girman ababen bakin ciki, sai kyautata zato ga Allah ya zama abin fata, da mafita a gare su, Sai annabi musa, ya ke cewa Mutanensa: "Ku nemi taimakon Allah, ku yi hakuri, domin kasa ta Allah ne, yana gadar da ita ga wanda yake so, daga cikin bayinsa, kuma kyakkyawar makoma tana ga masu takawa * Su ka ce: An cutar da mu gabanin ka zo mana, da kuma bayan zuwanka. Sai ya ce: Ina kyautata zaton Ubangijinku zai halaka makiyinku, ya halifantar da ku a doron kasa, domin ya ga yaya za ku aikata", [A'araf: 128-129].
        Sai wahalar ta kara yin tsanani ga Musa (عليه السلام) da wadanda suke tare da shi, alhalin teku yana gabansu, Fir'auna kuma da rundunarsa, suna ta bayansu, a lokacin ne, "Sahiban Musa, suka ce, lallai mu, za a riske mu" [Shu'ara'i: 61], Sai amsar ba'annaben da Allah ya yi magana da shi ta kasance, tana kunshe da bayanin girman dogararsa ga Allah, da kyautata zaton da ke yi ga UbangijinSa, Mai iko: "Sai ya ce, A'a! lallai ni, Ubangijina yana tare da ni, kuma zai shiryar da ni" [Shu'ara'i: 62]. Sai wahayi ya zo da abinda bai darsu a cikin zuciya ba, "Sai muka yi wahayi ga Musa, da cewar, Ka doki teku da sandarka, sai tekun ya tsage, kowani tsagi ya kasance kamar falalen dutse mai girma * kuma muka kusantar da wadancan mutanen ga wurin * Sai muka tsiratar da Musa da wadanda ke tare da shi gaba daya * Sa'annan muka dulmuyar da wadancan a cikin teku" [Shu'ara'i: 63-66].

        Kuma mafi girman halittu wajen yin bauta ga Allah, da kyautata zato a gare shi, shine annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) saboda mutanensa sun cutar da shi, amma sai ya wanzu yana mai aminta da wa'adin da Allah ya yi masa, da jin samun taimakonsa, har Mala'ikan duwatsu yake cewa da shi: "Idan ka so, sai in tanitse su da duwatsun akh-shabaini biyu; Sai ya ce: A'a, fatata itace, Allah daga tsatsonsu ya fitar da wadanda za su bauta wa Allah; shi kadai ba tare da sun hada shi da kowa ba", Bukhariy ya ruwaito shi.

        Kuma duk tsananin kunci da dufunsa, Annabi, lamarin kyautata zatonsa ga ubangijinsa baya rabuwa da shi, Ya fita daga garin Makka (lokacin hijira), akan hanyarsa ya fake a cikin wani kogo, sai kafirai suka riske shi, sai ga su, a kewayen da ya ke, Amma sai yake ce wa sahibinsa (Abubakar) yana mai kara karfafar guiwarsa: "Kada, ka yi bakin ciki, lallai Allah yana tare da mu. Abubakar (رضي الله عنه) ya ce: Na ce, wa Annabi alhalin ina cikin kogon: DA 'DAYANSU ZAI KALLI KARKASHIN KAFOFINSA BIYU, DA ZAI GANMU, Sai ya ce: Menene zatonka, ga mutane biyun da Allah shine na ukunsu", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma tare da abinda ya hadu da shi na dangogin cutarwa da bakin ciki da fitar da shi da aka yi daga garinsa, da kai masa yaki ta kowani wuri, saidai kuma Manzon Allah ya amintu da cewan wannan addinin zai kai ko-ina, a cikin zamannai, kuma ya kasance yana cewa: "Wannan lamari –na addini- lallai zai isa ko-ina, kuma Allah ba zai bar gidar laka ko fata ba, face ya shigar da wannan addinin a cikinsa, da buwayar mabuwayi ko da kaskancin kaskantacce", Ahmad ya ruwaito shi.

        (Wata rana) wani balaraben kauye ya zaro takobi domin ya soke Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) alhalin yana barci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: ''Sai na farka, alhalin takobin yana hannunsa a zare, sai ya ce: Wanene zai kare ka daga hannuna? Sai na ce: Allah ne, har sau uku, amma Annabi  bai masa ukuba ba, sai kawai ya zauna", Bukhariy ya ruwaito shi.
A wurin Imam Ahmad kuma "Sai takobin ya fadi daga hannunsa".

        Sahabbai -in banda Annabawa-, sun fi dukkan halittu yakini; saboda kyautata zatonsu ga Ubangijinsu, Allah (تعالى) ya ce: "Wadannan da mutane suka ce musu, lallai mutane sun hade domin cutar da ku, ku ji tsoronsu, sai hakan ya kara musu imani, kuma suka ce, MUN DOGARA GA ALLAH, KUMA MADALLA DA ABIN DOGARO",
Ibnud-daginah ya zo wurin Abubakar (رضي الله عنه) domin Abubakar ya rika yin sallarsa da karatunsa a asirce, ko ya mayar wa Abubakar lamarin kula da makwabtakarsa da ya dauki alkawari, sai kuma ya baiwa kafiran kuraishawa samun ikon kama Abubakar, Sai Abubakar (رضي الله عنه) ya ce: "Lallai ni, ina mayar maka da makwabtakanka, kuma na yarda da makwabtar Allah (عز وجل)", Bukhariy ya ruwaito  shi.

Umar (رضي الله عنه) ya ce, "Wata rana, Manzon Allah (صلى الله عليه وسم) ya umarce mu da yin sadaka, sai umarnin ya zo daidai da zuwan wata dukiya a wurina, Sai na ce: Yau zan rigayi Abubakar, saboda ban taba wuce shi ba. Sai na dauko rabin dukiyata na tafo, sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce, Me ka bari ga iyalanka? Sai na ce, Kwatankwacinsa. Ya ce: Sai Abubakar ya zo da dukkan abinda ya mallaka, sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce da shi: Me ka bari ga iyalanka? Sai ya ce: Na bar musu Allah, da ManzonSa", Abu-dawud ya ruwaito shi.

        KHADIJAH ita ce shugaban matan duniya, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya zo mata, farkon lokacin da wahayi ya fara sauka masa, sai ya ce: "Lallai na ji tsoro ma kaina, Sai Khadijah ta ke cewa, A'a, wallahi Allah ba zai tozarta ka ba; har abada, saboda kasancewarka kana sadar da zumunci, kana daukan nauyin gajiyayye, kana baiwa wanda bashi da shi, kuma kana bada abin tarbar bako, kuma kana taimakawa akan bala'oi na gaskiya", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Kuma akan kyautata zato ga Allah ne, Ma'abuta ilimi da salihai suka tafi, Sufyan As-Sauri  -رحمه الله- ya ce: "Bana son a baiwa hisabina ga iyayena biyu, Ubangina yafi alkhairi akan iyayena biyu".
Kuma ya kasance daga cikin addu'oin Sa'id bn Jubair –رحمه الله- yana cewa: "Ya Allah! Lallai ne ni ina rokonka, ka bani gaskiyar tawakkali akanka, da kyakkyawan zato a gare ka".

A cikin aljanu akwai salihai, wadanda zatonsu masu kyau ne, suna da yakini kan karfin Allah, da yalwar iliminsa, sai ya kasance daga cikin zancensu akwai "Kuma lallai ne mu, mun samu tabbacin ba zamu gagari Allah, a bayan kasa ba, kuma ba za mu buwaye shi da gudu ba", [Jinn: 13].

Kuma a cikin bayin Allah, akwai wanda inda zai yi rantsuwa ga Allah, da Allah ya kubutar da shi, ba wai saboda jin ya isa ba, a'a saboda tsantsar kyautata zato a gare shi (تعالى).

Shi kuma Mumini, yana daga sha'aninsa koyaushe, kuma a cikin kowane hali, kyautata zato ga Ubangijinsa, Kuma lokacin da yafi cancantar ya kasance kamar hakan, shine lokacin da ya roki Allah, ya gana da shi; ta hanyar bauta a gare shi, yana mai samun yakinin kusancinsa, da cewa yana amsa wa mutumin da ya roke shi, kuma baya hana wanda ya yi tunanin samun fatansa.

Kuma yana daga cikin SABUBBAN KARBAR TUBA; Kyautata zaton mai yinta ga UbangijinSa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) daga cikin abin da ke ruwaitowa daga Ubangijinsa yana cewa: "Lallai Bawana ya aikata zunubi, sai ya samu yakinin cewa yana da Ubangijin da ke gafarta zunubi, sannan ya share shi, ka aikata abinda ka so, lallai hakika na yafe maka", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma a lokacin tsanani da fitintinu, ake sana'anta kyawawan zato ga Allah, a kuma kwaranye munanan zato a gare shi, saboda a yakin Uhudu; sha'anin masu imani ya kasance tabbatuwa, su kuma wadanda ba muminai ba "Suna zaton abinda ba shine gaskiya ba, a game da Alllah" [Ali-imrana: 154].
A lokacin yakin Ahzabi, zace-zace nau'i-nau'i sun yi yawa dangane da Allah, sai Allah ya ke fada dangane da wasu bangare "A lokacin da munafikai ke cewa, da kuma wadanda a cikin zukatansu akwai cuta, ba komai Allah da Manzonsa suka alkawarta a gare mu ba, face rudi" [Ahzabi: 12]. Amma su kuma sahabbai, sai suka samu yakini cewar, wadannan fitintinun jarabawa ce daga Allah, wanda nasara da kwaranyewa ke biyo bayansu, Allah ya ce: " kuma a yayin da muminai suka ga kungiyoyin kafirai, sai suka ce, wannan shine abinda Allah da ManzonSa suka mana, wa'adi, Allah da ManzonSa sun yi gaskiya, kuma wannan bai kara musu komai ba, face imani da sallamawa", [Ahzabi: 22].
Saboda samun mafita, a lokacin kunci, yana nan ne cikin kyautata zato ga Allah, domin mutane ukun da aka jinkirta karbar tubansu, ba a kwaranye musu abinda ya sauka a gare su na bakin ciki ba, sai a lokacin da suka kyautata zato ga Allah shi kadai, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma Allah ya karbi tuban mutane ukun da aka jinkirtar, har kasa da yalwarta ta yi kunci akansu, kuma su ka yi zaton babu wata mafaka daga Allah, face komawa zuwa gare shi, sa'annan sai Allah ya karbi tubansu, domin su tabbatu akan tuba, Lallai Allah shine Mai karbar tuba, Mai jin kai", [Tauba: 119].

Duk wanda rayuwarsa ta yi kunci, to cikin kyautata zatonsa akwai yalwa da kwaranye matsalolinsa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda talauci ya sauka masa, sai ya sauke shi ga mutane, to ba za a toshe talaucinsa ba, Wanda kuma talauci ya sauka a gare shi, sai ya sauke ta ga Allah, to yayi kusa Allah ya kawo masa arziki cikin gaggawa, ko kuma a can", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Zubairu bn Al-awwam –رضي الله عنه- ya ce ga 'diyansa Abdullahi: "Ya kai diyana, idan ka gagara biyan wani abu daga cikin bashin da ake bina, ka nemi taimako Majibincina; shugabana akan haka, Abdullahi ya ce: Wallahi ban gane abinda yayi nufi ba, sai da na ce: Wanene kuma shugabanka? Ya Mahaifina, Ya ce: Allah. Abdullahu ya ce: Ina rantsuwa da Allah, Ban auka cikin wani bakin ciki ba akan wani abu na bashinsa, face nace: Ya Majibincin Zubairu, ka biya masa bashinsa, sai ya biya masa", Bukhariy ya ruwaito shi.

Allah shine Mai karfi, Mai iko, kuma idan ya tashi bada nasara ga bayinsa, babu mai cin galaba akansu. Kuma yana daga cikin yakini, kyautata wa Allah zato akan hakan, Allah (تعالى) ya ce: "Idan Allah ya baku nasa, to babu mai rinjayarku, kuma idan ya kyale ku, to wanene zai taimake ku a bayansa?" [Ali-imrana: 160].
Kuma shi Allah Mai jin kai ne Mai rahama, ga wanda ya yi imani da shi (سبحانه) ya kuma aikata aiki na kwarai, kuma idan ya yi fatan samun rahamar Allah zai same ta, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yayin da Allah ya halitta halittu, sai ya rubuta a cikin wani littafi, wanda ke wurinsa, a saman al'arshi; cewa: Lallai rahamata ta rinjayi fushina", Bukhariy da Muslim.

Kuma shi Allah (سبحانه) Mai yalwar gafara da kyauta ne, Duk wanda ya kyautata zatonsa da shi, cikin wadacinSa da karamcinSa, da gafararSa, sai ya bashi abinda ya roka; domin ya kan sauka "zuwa saman Duniya, sai ya ce: Wa zai roke ni, in amsa masa?" kuma "Hannayensa suna cike; ciyarwa bata tauye su, yana yin baiwa cikin dare da yini".

Allah Mai yawan karbar tuba ne, yana farin ciki da tuban bayinSa, kuma yana shumfuda hannunsa da dare, domin wanda ya munana aiki da rana ya tuba, kuma yana shumfuda hannunsa da rana, domin wanda ya munana aiki da dare ya tuba. Kuma yana daga cikin kamalarSa; baya korar wanda ya fiskanto shi.

Kuma lokacin da bawa yafi tsananin bukatar ibadar kyautata zato ga ubangijinsa, shine idan ajalinsa ya kusanto shi, kuma yake bankwana da duniya, yake fiskantar UbangijinSa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) "Kada 'dayanku ya mutu, face yana mai kyautata zatonsa ga Allah (عز وجل)", Muslim ya ruwaito

Cikin kyautata zato ga Allah, akwai bin umarninSa, da tabbatar da bautarSa.
Kuma bawa a wurin Ubangijinsa zai samu irin abinda ya yi zato ne, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "…Ni, ina yadda bawana ya yi zatona, kuma ina tare da shi, idan ya ambace ni", Bukhariy da Muslim.
Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Ina rantsewa da wanda babu wani abin bauta face shi, Bawa ba zai kyautata zatonsa ga Allah Mabuwayi da daukaka ba, face Allahu (عز وجل) ya bashi abinda ke zato a wurinsa", Wannan kuma saboda alkhairi dukkansa yana hannunsa.
Kuma idan kyautata zato, kofarsa ta budu ga bawa, sai Allah ya bude masa kofar alkhairi mai girma a cikin addini, Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) yana cewa: "Ina rantsuwa da Allah, wanda babu abin bautawa da cancanta, face shi, Ba a baiwa bawa mumini wani abinda yafi alkhairi fiye da kyautata zato ga Allah (عز وجل)".

AYYUKAN MUTANE SUNA KASANCEWA NE gwargwadon yadda suke zaton Ubangijinsu, Saboda shi MUMINI ya kyautata zatonsa ga Allah, sai ya kyautata aiki, Shi kuma KAFIRI Ya munana zatonsa, sai kuma ya munana aiki.

Kuma cikin ibadar kyautata zato, akwai kyan musulunci, da kamalar imani, kuma wannan ibadar hanya ce ta zuwa Aljannah, ga ma'abucinta.
Ibadar tana gadar da Tawakkali ga Allah, da amintuwa da shi, Ibnul-kayyim –رحمه الله- yace: "Kuma gwargwadon kyautata zatonka ga Ubangijinka, da fatanka ga Ubangiji, gwargwadon haka, tawakkalinka a gare shi zai kasance, wannan ya sanya wasu maluman suka fassara tawakkali, da kyautata zato ga Allah. Sai dai maganar gaskiya itace, lallai kyautata zato a gare shi, yana janyo dogaro a gare shi (tawakkali); saboda a hankalce ba a iya fahimtar, mutum ya dogara ga wanda ya munana zato akansa, ko kuma ka yi tawakkali ga wanda baka fatan samun abinda ke hannunsa".

Kuma yana daga cikin FA'IDODIN kyautata zato ga Allah, samun natsuwar zuci, da fiskantar Allah, da tuba zuwa gare shi, saboda babu abinda yafi yaye matsalolin kirji, ko ya fadada zuciyar bawa, bayan imani, fiye da amintuwa da Allah, da fatan Allah, da kyautata masa zato.

Kuma a cikin kyautata zato, akwai abinda ke sanya ma'abutansa ga "Fa'al; kyakkyawar fata", Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Cuta bata rabuwa da-kanta, kuma canfi baya tasiri, Kyautata zato (na Fa'alu mai kyau) yana burge ni; wanda kuma shi ne, fadin kalma mai kyau", Bukhariy da Muslim.
Alhaliymiy –رحمه الله- ya ce, "Canfi munana zato ne ga Allah, shi kuma Fa'alu; kyautata zato ne ga Allah Ta'alah".

Kyautata zato, yana taimakon ma'abucinsa kan bada kyauta, da gwarzantaka, kuma yana haifar masa da samun karfi, Abu-Abdullahi As-Sajiy –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya aminta da Allah, to lallai ya taskance karfinsa".
Kuma kyautata zato, shine mafi alherin guzuri, kuma madalla da shi ga abinda aka tattala, An ce wa Salamah bn Diynaar –رحمه الله- Ya Aba-Hazim, Me ya same ka? Sai ya ce,"Amintuwa ne da Allah, da debe zato kan abinda ke hannun mutane".

Kuma wanda ya kyautata zatonsa ga Ubangijinsa, sai ransa ta zama mai kyauta, ya rika rabar da dukiyarsa, yana mai samun yakini kan fadin Allah "Kuma duk abinda kuka ciyar, to Allah zai bada mayewarsa" [Saba'i: 39], Sulaimanud Daraniy ya ce: "Wanda ya aminta da Allah cikin lamarin arzikinsa, sai dabi'unsa su kara kyau, sai kuma ya gadar masa da hakuri, ransa ta yi ta kyauta tana ciyarwa, waswasinsa su yi karanci cikin sallarsa".

Kyautata zato, jagora ne zuwa ga kyakkyawan fata, ga samun abinda ke wurin Allah, da kuma amintuwar samun abinda ya yi wa'adi da shi, da aikata alkhairi; cikin fatan samun falalarsa, kamar yadda ya ke cewa: "Kuma duk abinda suka aikata na alkhairi, to ba za a yi musu musunsa ba" [Ali-imrana: 115].

Allah yana mu'amalantar bayinsa ne, gwargwadon yadda suke zatonsa, kuma sakayya ta kan zama daga jinsin aiki; don haka Duk wanda ya yi zaton samun alkhairi, to yana da hakan.
Wanda kuma ya yi zaton kishiyar haka, to kada ya zargi wani sai kansa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Ni ina yadda bawana ya yi zatona; sai bawana ya yi zatona kamar yadda ya ga dama; domin idan ya yi zaton alkhairi zai samu, idan kuma ya yi zaton sharri, shima zai samu", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma duk lokacin da bawa ya zama mai kyautata zato ga Allah, to lallai Allah baya kunyata ma'abuta kyautata zatonsu a gare shi; kwata-kwata.
Saboda cikakken karramawa na kasancewa ne a ranar kiyama, kuma a can ne, wanda ya kyautata zatonsa ga Ubangijinsa zai ce: "Ku karba ku karanta littafina * lallai ne ni na tabbata cewa ni mai haduwa ne da hisabina * saboda haka shi yana cikin wata rayuwa yardadda, a cikin aljanna madaukakiya" [Alhakkah: 19-22].

BAYAN HAKA;
Ya ku Musulmai;;;
Allah Mai girma ne Mai Karfi da Buwaya, idan ya nufi abu, sai yace, ya kasance, sai kuma ya kasancen, ya yi alkawarin kiyaye littafinsa, kuma ya sanya kyakkyawan karshe –a ko-yaushe- ga masu takawa, kuma yana azurta wanda ya so ba tare da lissafi ba, kuma yana kwaranye bakin cikin mutumin da ya sanya mafakarsa zuwa ga Allah.
Kuma duk wanda iliminsa da Allah ya karu, sai yakininsa ga Allah ya karu, kuma duk wanda ya munana zato ga Allah, to hakan ya haifu ne sakamakon jahiltar kamalar sunayen Allah da sifofinsa, kuma hakan yana daga cikin sifofin mutanen jahiliyya, Allah (سبحانه) ya ce: "Suna zaton abinda ba shine gaskiya ba, a game da Allah; irin zaton jahiliyya" [Ali-imrana: 154].  

Kuma yana daga FA'IDODIN IMANI DA SUNAYEN ALLAH DA SIFOFINSA, Kyautata zato a gare shi, da dogaro akansa, da fawwala lamura zuwa gare shi.
 A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:

"Duk wanda ya ke fatan haduwa da Ubangijinsa; to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa, ga bauta wa Ubangijinsa" [Kahf: 110].

        ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. …
         

HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Ya Allah, ka yi dadin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
        Hakikanin kyautata zato ga Allah yana kasancewa ne cikin kyautata aiki, kuma kyautata zato zai yi amfani ne idan ya kasance tare da "ihsani (bautar Allah da kyau; kamar mutum yana ganinsa).
Kuma wanda yafi dukkan mutane kyautata zato ga UbangijinSa shine wanda yafi su yin da'a a gare shi.
Kuma duk lokacin da zaton bawa ga UbangijinSa ya kyautatu, sai aikinsa babu makawa, ya yi kyau.
Wanda kuma aikinsa ya yi muni, sai zace-zacensa ga Allah, su yi muni.
Kuma ta yaya wanda ya abauce ga Allah, ta hanyar aukawa cikin ababen da suke fusata shi, yake kinsu zai iya kyautata zatonsa ga Ubangijinsa.
Wanda kuma ya riya kyautata zato ga Allah, sai ya zama baya tsoronsa, to wannan yana yaudarar kansa; saboda duk lokacin da kyautata zato ya hada hanya da aikata zunubai, to mai aikata shi yana amintuwa ne daga makircin Allah.
Kuma kyautata zato, idan ya kwashi mai shi, izuwa ga biyayyar Allah, to wannan shine mai amfani, Idan kuma ya kai shi ga aikin badala, da dulmuya cikin sabo, to wannan rudi ne.
>>> 

        Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].

        Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
        Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka hada da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
        Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran kasashen Musulmai.


        Bayin Allah!!!
          "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...