MUHIMMAN ADDU’OI
·
سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ، سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيم، {لاَ إِلَهَ
إِلاَّ أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ}.
SUBHANAL LAHI WABI
HAMDIH, SUBHANAL LAHIL AZIIM. LA'ILA ILLA ANTA SUBHANAKA INNIY KUNTU MINAZ
ZALIMIN.
Ma'ana: "Tsarki ya tabbata ga
Allah, kuma godiya tasa ce, tsarki ya tabbata ga Allah mai girma. Babu abun
bauta da gaskiya sai Allah, tsarki ya tabbata maka, lallai ni na kasance daga
cikin azzalumai".
· «لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ،
وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ، وَلَهُ الْفَضْلُ، وَلَهُ
الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ
وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ».
LA ILAHA ILLAL LAHU, WALA
NA'ABUDU ILLA IYYAHU, LAHUN NI'IMAH, WA LAHUL FADL, WA LAHUS SANA'UL HASAN, LA
ILAHA ILLAL LAHU MUKHLISINA LAHUD DINA WA LAU KARIHAL KAFIRUUNA.
Ma'ana:
"Babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma bama bauta ga wani sai kai,
ni'ima tasa ce, kuma falala nasa ne, kuma yabo mai kyau nasa ne, babu abun
bauta da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkakae masa addini, koda kafirai sun
ki".
· «لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ
إِلَّا بِاللَّهِ».
LA HAULA WALA
KUWWATA ILLA BIL LAH.
Bawa bashi da dabarar barin sabo,
bashi da karfin iya biyayya ga Allah, sai ya samu taimakon Allah.
· ﭽ ﯜ ﯝ
ﯞ ﯟ ﯠ
ﯡ ﯢ ﯣ
ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البقرة: ٢٠١.
RABBANA ATINA FID-DUNYA HASANATAN, WA FIL
AKHIRATI HASANATAN, WA KINA AZABAN NAAR.
Ma'ana:
"Ya ubangijinmu ka bamu abu mai kyau a duniya, a lahirama mai kyau, ka
kare mu daga azabar wuta".
· «اللهُمَّ أَصْلِحْ لِي دِينِي
الَّذِي هُوَ عِصْمَةُ أَمْرِي، وَأَصْلِحْ لِي دُنْيَايَ الَّتِي فِيهَا
مَعَاشِي، وَأَصْلِحْ لِي آخِرَتِي الَّتِي فِيهَا مَعَادِي، وَاجْعَلِ الْحَيَاةَ
زِيَادَةً لِي فِي كُلِّ خَيْرٍ، وَاجْعَلِ الْمَوْتَ رَاحَةً لِي مِنْ كُلِّ
شَرٍّ».
ALLAHU ASLIH LIY DIYNIY AL-LAZIY HUWA
ISMATU AMRIY, WA ASLIH LIY DUNYAY AL-LATIY FIYHA MA'ASHIY, WA ASLIH LIY
AKHIRATIY AL-LATIY FIYHA MA'ADIY, WAJ'ALIL HAYATA ZIYATAN LIY FIY KULLI KHAIR,
WAJ'ALIL MAUTA RAHATAN LIY MIN KULLI SHARR.
Ma'ana:
"Ya Allah ka gyara min addinina wanda shi ne mai gyara mini lamarina, ka
kuma gyara mini duniyata wacce a cikinta rayuwata ta ke, ka kuma gyara min
lahirata wacce zuwa gare ta makomata ta ke, ka sanya rayuwa ta zama karuwa ce a
gare ni cikin kowani alkhairi, mutuwa kuma ta zamo hutu daga aikata dukkan
sharri".
·
أَعُوذُ بِاللَّه «مِنْ جَهْدِ الْبَلَاءِ، وَدَرَكِ الشَّقَاءِ، وَسُوءِ
الْقَضَاءِ، وَشَمَاتَةِ الْأَعْدَاءِ».
A'UZU BILLAHI MIN JAHDIL BALA'I,
WA DARAKISH SHAKA'I, WA SUW'IL KADA'I, WA SHAMATATIL A'ADA'I.
Ina
neman tsarin Allah wahalhalun bala'i, da kuma riskar wahala, da mummunar
kaddara, da dariyar keta daga makiya.
·
«اللَّهُمَّ
إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ، وَالْعَجْزِ وَالْكَسَلِ،
وَالْجُبْنِ وَالْبُخْلِ، ومِنَ الْمَأْثَمِ وَالْمَغْرَم، وَمِن ضَلَعِ الدَّيْنِ
وَقَهْرِ الرِّجَالِ. اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْبَرَصِ وَالْجُنُونِ
وَالْجُذَامِ وَسَيِّءِ الأَسْقَام».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU
BIKA MINAL HAMMI WAL HAZAN, WAL AJZI WAL KASL, WAL JUBNI WAL BUKHL, WA DALA'ID
DAINI, WA GALABATIR RIJAAL.
ALLAHUMMA INNIY A'UZU
BIKA MINAL BARASI, WAL JUNUNI, WAL JUZAAMI, WA SAYYI'IL ASKAAM.
Ma'ana: "Ya Allah lallai ni ina
neman tsarinka daga bakin ciki, da gajiyawa da kasala, da tsoro da rowa, da
kuma sabo, da bashi, da kuma nauyinsa (bashi), da rinjayen mazaje.
Ya Allah ka tsare ni
daga ciyon kuturta, da hauka, da kuturta mai yanke yatsu, da munanan
cutuka".
· «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ، فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ».
ALLAHUMMA INNIY
AS'ALUKAL AFWA WAL AFIYAH, FID DUNYA WAL AKHIRAH.
Ma'ana: "Ya Allah ina rokonka afuwa da
lafiya, a duniya da lahira".
· «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي وَمَالِي».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL AFWA WAL AFIYAH,
FIY DIYNIY, WA DUNYAY, WA AHLIY, WA MALIY.
Ma'ana: "Ya Allah lallai ni ina rokonka
afuwa da lafiya, a addinina da duniyata da iyalaina da dukiyata".
· «اللَّهُمَّ اسْتُرْ
عَوْرَاتِي، وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ،
وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَـــــــــــــــــــالِي، وَمِنْ
فَوْقِي، وَأَعُوذُ –بِعَظَمَتِكَ- أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي».
ALLAHUMMAS TUR AURAATIY, WA AMIN
RAU'AATIY, ALLAHUMMAH FAZNIY MIN BAINI YADAYYA WA MIN KHALFIY, WA AN YAMIYNIY,
WA AN SHIMALIY, WA MIN FAUKIY, WA A'UZU –BI AZAMATIKA- AN UGTALA MIN TAHTIY.
Ma'ana: "Ya Allah ka suturce min
al'aurata, ka amintar da tsorona, Ya Allah ka bani kariya ta gaba gare ni da
kuma ta bayana, da ta damana da ta hagun dina, da ta samana, kuma ina neman
tsari –da girmanka- kan halaka ni ta kasana (kamun kasa ko makamancinsa).
· «اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي
خَطِيئَتِي وَجَهْلِي، وَإِسْرَافِي فِي أَمْرِي، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ
مِنِّي».
ALLAHUMMAG FIR LIY KHADIY'ATIY WA
JAHLIY, WA ISRAFIY FIY AMRIY, WAMA ANTA A'ALAMU BIHI MINNIY.
Ma'ana:
"Ya allah ka gafarta mini kurakuraina da jahilcina, da wuce iyakata a
cikin lamura, da abin da kaine mafi saninsa fiye da ni".
·
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي جدي وَهَزْلِي، وخَطَئِي وَعَمْدِي، وَكُلُّ ذَلِكَ
عِنْدِي.
ALLAHUMMAG FIR LIY
JIDDIY, WA HAZLIY, WA KHADA'IY WA AMDIY, WA KULLU ZALIKA INDIY.
Ma'ana: "Ya Allah ka gafarta min
gaskena da wargina, da kuskurena da gangancina, saboda akwai dukkan hakan daga
wajena".
· "اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي
مَا قَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، وَمَا أَنْتَ
أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي، أَنْتَ الْمُقَدِّمُ وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ، وَأَنْتَ عَلَى
كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ".
ALLAHUMMAG FIR LIY MA KADDAMTU
WAMA AKKHARTU, WAMA ASRARTU WAMA A'ALANTU, WAMA ANTA A'ALAMU BIHI MINNIY, ANTAL
MUKADDIMU WA ANTAL MU'AKKHIRU, WA ANTA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR.
Ma'ana:
"Ya Allah ka gafarta mini abin da na gabatar, da abin da na jinkirtar, da
abin da na asirta (boye) da abin da na bayyanar, da kuma abin da kaine mafi
saninsa fiye da ni, kai ne mai gabatarwa, kai ne kuma mai jinkirtarwa, kuma kai
mai iko ne akan komai".
· "اللَّهُمَّ إِنِّي
أَسْأَلُكَ الثَّبَاتَ فِي الْأَمْرِ، وَالْعَزِيمَةَ عَلَى الرُّشْدِ،
وَأَسْأَلُكَ شُكْرَ نِعْمَتِكَ، وَحُسْنَ عِبَادَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ قَلْبًا
سَلِيمًا، وَلِسَانًا صَادِقًا. وَأَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا تَعْلَمُ، وَأَعُوذُ
بِكَ مِنْ شَرِّ مَا تَعْلَمُ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا تَعْلَم، وَأَنْتَ عَلَّامُ
الْغُيُوبِ".
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAS SABATA
FIL AMR, WAL AZIYMATA ALAR RUSHD, WA AS'ALUKA SHUKRA NI'IMATIKA, WA HUSNA
IBADATIKA, WA AS'ALUKA KALBAN SALIYMAN, WA LISANAN SADIKAN, WA AS'ALUKA MIN
KHAIRI MA TA'ALAM, WA A'UZU BIKA MIN SHARRI MA TA'ALAM, WA ASTAGFIRUKA LIMA
TA'ALAM, WA ANTA ALLAMUL GUYUUB".
Ma'ana:
"Ya Allah lallai ina rokonka tabbatuwa cikin wannan lamari (addini), da
azama akan shiriya, Ina kuma rokonka godiya ga ni'imominka, da kyautata bauta a
gare ka, kuma ina rokon ka bani zuciya kubutacciya, da harshe mai gaskiya, Ina
kuma rokonka alharin abin da ka sani, ina neman tsarinka daga sharrin da ka
riga ka sanshi, ina kuma neman gafararka daga abin da ka sani, kuma kai ne
masani abubuwan da su ke fake (boye, na gaibu).
·
اللَّهُمَّ رَبَّ النَّبِيِّ عليه الصلاة والسلام مُحَمَّدٍ اغْفِرْ لِي
ذَنْبِي، وَأَذْهِبْ غَيْظَ قَلْبِي، وَأَجِرْنِي مِنْ مُضِلاَّتِ الْفِتَنِ مَا
أَبْقَيْتَنِي.
ALLAHUMMA RABBAN NABIYYI
MUHAMMADIN (ALAIHIS SALATU WAS SALAM), IGFIRLIY ZANBIY, WA AZHIB GAIZA KALBIY,
WA AJIRNIY MIN MUDILLATIL FITAN MA ABKAITANIY.
Ma'ana:
"Ya Allah ubangijin annabi (Muhammadu) tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, ka gafarta mini zunubina, ka tafiyar dab akin cikin zuciyata, ka kare
ni daga fitintinu masu batarwa tsawon lokacin da ka wanzar da ni (a raye).
·
اللَّهُمَّ رَبَّ السَّماوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا
وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، مُنْزِلَ التَّوْرَاةِ وَالإِنْجِيلِ وَالْقُرْآنِ، فَالِقَ
الْحَبِّ وَالنَّوَى، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ
شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ، أَنْتَ الأَوَّلُ لَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ،
وَأَنْتَ الآخِرُ لَيْسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ لَيْسَ فَوْقَكَ
شَيْءٌ، وَأَنْتَ الْبَاطِنُ لَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ، اقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ،
وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْر.
ALLAHUMMA RABBAS SAMAWATIS
SABA'I, WA RABBAL ARSHIL AZIIM, RABBANA WA RABBA KULLI SHAI'IN, MUNZILAT
TAURATI WAL INJILI WAL KUR'AN, FALIKAL HABBI WAN NAWAH, LA'ILAHA ILLA ANTA,
A'UZU BIKA MIN SHARRI KULLI SHAI'IN ANTA AAKHIZUN BI NASIYATIHI, ANTAL AUWALU
FA LAISA KABLAKA SHAI'UN, WA ANTAL AAKHIRU FA LAISA BA'ADAKA SHAI'UN, WA ANTAZ
ZAHIRU FA LAISA FAUKAKA SHAI'UN, WA ANTAL BADINU FA LAISA DUNAKA SHAI'UN, IKDI
ANNAD DAINA WA AGNINA MINAL FAKR.
Ma'ana:
"Ya Allah ubangijin sammai guda bakwai, ubangijin al'arshi mai girma,
ubangijinku kuma ubangijin komai da kowa, wanda ya saukar da littafin attaurah
da injilah da alkur'ani, kai ka kagi halittar kwayan tsirrai da kwallonsu, Ina neman tsarinka daga dukkan
sharri wanda kai ne ka ke rike da makyamkyamarsa, Ya Allah kai ne farko; babu
wani abu gabaninka, kuma kai ne karshe; babu wani a bayanka, kai ne madaukaki;
babu wani abu a samanka, kai ne kuma iliminka ya game; babu wani abu da ya fice
daga iliminka, (ya Allah) ka biya mana bashin da ke kanmu, kuma ka wadatar da
mu daga talauci".
· «اللَّهُمَّ ائْتِ نَفْسِي
تَقْوَاهَا، زَكِّهَا أَنْتَ خَيْرُ مَنْ زَكَّاهَا، أَنْتَ وَلِيُّهَا
وَمَوْلَاهَا».
ALLAHUMMA A'ATI NAFSIY TAK'WAHA,
ZAKKIHA ANTA KHAIRU MAN ZAKKAHA, ANTA WALIYYUHA WA MAULAHA.
Ma'ana:
"Ya Allah ka bawa raina takawarta, ka tsarkake ta; saboda kaine mafi
alherin wanda ya jibniceta kuma masoyinta".
·
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ ، وَالْجُبْنِ
وَالْهَرَمِ ، وَالْبُخْلِ وَعَذَابِ الْقَبْرِ.
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL
AJZI WAL KASAL, WAL JUBNI WAL HARAM, WAL BUKLI WA AZABIL KABR.".
Ma'ana"
Ya Allah ina tsarinka daga gajiyawa da kasala, da tsoro, da mummunan tsufa, da
rowa da azabar kabari".
· «اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ،
وَبِكَ آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ،
اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي، أَنْتَ
الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».
ALLAHUMMA LAKA ASLAMTU, WA BIKA
AMANTU, WA ALAIKA TAWAKKALTU, WA ILAIKA ANABTU, WA BIKA KHASAMTU, ALLAHUMMA
INNIY A'UZU BI IZZATIKA, LA ILAHA ILLA ANTA, AN TUDILLANIY, ANTAL HAYYU ALLAZIY
LA YAMUTU, WAL JINNU WAL INSU YA MUTUNA.
Ma'ana:
"Ya Allah a kai kawai na mika wuya, kuma da kai kawai na yi imani, akanka
na dogara, zuwa gare ka na mayar da lamarina, don kai kawai na ke husuma, Ya
Allah lallai ina neman tsarinka da buwayarka, babu abun bauta da gaskiya sa sai
kai kada ka batar da ni, kai ne rayayyen da baya mutuwa, da mutane da aljanu
duk suna mutuwa".
· «اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ
مِنْ عِلْمٍ لَا يَنْفَعُ، وَمِنْ قَلْبٍ لَا يَخْشَعُ، وَمِنْ نَفْسٍ لَا
تَشْبَعُ، وَمِنْ دَعْوَةٍ لَا يُسْتَجَابُ لَهَا».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MIN
ILMIN LA YANFA'U, WA MIN KALBIN LA YAKH'SHA'U, WA MIN NAFSIN LA TASHBA'U, WA
MIN DA'AWATIN LA YUSTAJAABU LAHA.
Ma'ana:
"Ya Allah lallai ina neman tsarinka daga ilimin da bashi da amfani, da
kuma zuciya da bata samun kushu'i (tsoron Allah), da raid a bata koshi, da kuma
addu'ar da ba a amsa mata".
·
«اللَّهُمَّ
جَنِّبْنِي مُنْكَرَاتِ الْأَخْلَاقِ، وَالْأَهْوَاءِ، وَالْأَدْوَاءِ».
ALLAHUMMA JANNIBNIY MUNKARATIL AKHLAQ, WAL'AHWA'I,
WAL'ADWA'I.
Ma'ana:
"Ya Allah ka nisantar da ni da munanan halayya, da son zuciya, da
cutuka".
· «اللَّهُمَّ أَلْهِمْنِي
رُشْدِي، وَأَعِذْنِي مِنْ شَرِّ نَفْسِي».
ALLAHUMMA AL-HIMNIY RUSHDIY, WA
A'IZNIY MIN SHARRI NAFSIY.
Ma'ana:
"Ya Allah ka min ilhamar shiriyata, ka kuma kare ni daga sharrin
kaina".
· «اللَّهُمَّ اكْفِنِي
بِحَلَالِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ».
ALLAHUMMA IKFINIY BI HALALIKA AN
HARAMIKA, WA AGNINIY BI FADLIKA AN MAN SIWAKA.
Ma'ana:
"Ya Allah ka wadatar da ni da halal dinka, ka wadatar da ni da falalarka
daga wanda ba kai ba".
·
«اللهُمَّ
إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى وَالتُّقَى وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL HUDAH, WAT TUKAH, WAL
AFAFA, WAL GINAH.
Ma'ana:
"Ya Allah lallai ina rokonka shiriya da takawa da kamewa da wadaci".
· «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْهُدَى وَالسَّدَاد».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL HUDAH
WAS SADAD.
Ma'ana:
"Ya Allah ina rokonka shiriya da dacewa".
· «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
مِنَ الْخَيْرِ كُلِّهِ؛ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ،
وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الشَّرِّ كُلِّهِ؛ عَاجِلِهِ وَآَجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ
مِنْهُ، وَمَا لَمْ أَعْلَمْ.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ
وَنَبِيُّكَ مُحَمَّدٌ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ
شَرِّ مَا استعَاذَ مِنْهُ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ مُحَمَّدٌ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ.
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ
قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ
قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ تَقْضِيهِ لِي
خَيْرًا».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA MINAL
KHAIRI KULLIHI AJILIHI WA AJILIHI, MA ALIMTU MINHU WAMA LAM A'ALAM, WA A'UZU
BIKA MINASH SHARRI KULLIHI; AJILHI WA AJILIHI, MA ALIMTU MINHU WAMA LAM A'ALAM.
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA MIN
KHAIRI MA SA'ALAKA ABDUKA WA NABIYYUKA MUHAMMADUN (SAW), WA A'UZU BIKA MIN
SHARRI MA ISTA'AZA MINHU ABDUKA WA NABIYYUKA MUHAMMADUN (SAW).
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL JANNATA
WAMA KARRABA ILAIHA MIN KAULIN AU AMAL, WA A'UZU BIKA MINAN NAARI WAMA KARRABA
ILAIHA MIN KAULIN AU AMAL. WA AS'ALUKA AN TAJ'ALA KULLA KADA'IN KADAITA LIY
KHAIRAH.
Ma'ana:
"Ya Allah ina rokonka alkhairi dukkansa; na gaggawa daga cikinsa da na
nesa, wanda na sani daga cikinsa da wanda ban sani ba. Ina kuma neman tsarinka
sharri dukkansa; na gaggawa daga cikinsa, da na nesa, wanda na sani daga
cikinsa da wanda ban sani ba.
Ya allah ina rokonka duk abin da
bawanka kuma annabinka Muhammadu (saw) ya roke ka, Ina kuma neman tsarinka daga
abin da bawanka kuma annabinka Muhammadu (saw) ya nemi tsarinka.
Ya Allah ina rokon aljannah da
duk abin da ke kusantarwa zuwa gare ta na zance ko aiki, Ina kuma neman
tsarinka daga wuta da duk abin da ke kusantarwa zuwa gare ta na zance ko aiki.
Kuma ina rokon da ka sanya dukkan abin da ka kaddara min ya zama alkhairi a
gare ni.
· «لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ
وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ
وَهُوَ حَيٌّ لَا يَمُوتُ، بِيَدِهِ الْخَيْرُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير.
سُــــبْحَانَ اللَّهِ، والْحَمْدُ لِلَّهِ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، وَلَا حَوْلَ
وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ العلي العظيم».
LA ILA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA
SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, YUHYIY WA YUMIYTU, WA HUWA HAYYUN LA
YAMUTU, BIYADIHIL KHAIRU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR.
SUBHANAL LAHI, WAL HAMDU LILLAHI, WAL LAHU AKBAR, WALA HAULA WALA
KUWWATA ILLA BIL LAHIL AL' ALIYYUL AZIM.
Ma'ana: "Babu wanda ya cancanci ayi masa bauta sai Allah shi kadai
ya ke bashi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiyama tasa ce, yana rayarwa
kuma yana kashewa, shi kuma rayayye ne da baya mutuwa, a hannunsa alheri ya ke,
kuma lallai shi mai iko ne akan komai.
Tsarki ya tabbata ga Allah, godiyama ta Allah
ce, Allah shi ne mafi
girma, babu dabara babu kuma karfi (ga bawa), sai in ya hada da Allah".
· «اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ
مُحَمَّدٍ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ فِي
الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَـارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ
وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى آلِ
إِبْرَاهِيمَ فِي الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيد».
"ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA ALA
ALI MUHAMMADIN, KAMA SALLAITA ALA ALI IBRAHIMA WA ALA ALI IBRAHIMA FIL ALAMINA
INNAKA HAMIDUN MAJID.
ALLAHUMMA BARIK ALA MUHAMMADIN WA ALA ALI
MUHAMMADIN, KAMA BARAKTA ALA IBRAHIMA WA ALA ALI IBRAHIMA FIL'ALAMINA INNAKA
HAMIDUN MAJIiD".
·
ﭽ
ﯜ ﯝ ﯞ
ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ
ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البقرة: ٢٠١.
RABBANA ATINA FID DUNYAH, WA FIL AKHIRATI HASANATAN,
WA KINA AZABAN NAAR.
Alhamdulillah, Ma Sha Allah, with your peemission i would like to spread your publications to various web sites. Find me on instagram as soddiq68, twitter as saddiq68, linkedin as Abubakar Ibrahim, Google+ as Abubakar Ibrahim. Email address.. abubakaribrahim176@gmail
ReplyDeleteMasha Allah.Allah ya saka da alkhairi.
ReplyDelete