YA MAI NEMAN ALKHAIRI; KA SHIRYA!!
(يا باغيَ الخير استعدْ)
'Yan kasuwa, ma'abuta kasuwanci su kan
yi cikakken shiri, a lokutan kasuwanci, domin fatan samun fiyayyen riba.
Su kuma Muminai, suna yin shiri domin
fiskantar watan azumi na Ramadhana (wato, WATA MAI TARIN ALBARKA) da nau'ukan
bauta, Sai su
1- Yawaita yin
azumi a Sha'aban, domin ya kasance shiri ga azumtar watan Ramadana.
2- Da kuma yin Tuba
ta gaskiya, da ficewa daga ayyukan zunubai, da mayar da kayan da suka zalunta,
izuwa ga Ma'abutansu.
3- Da yafiya da
yin sulhu, da kawar da dukkan sabani, da warware jayayya, domin mu kasance mun
cancanci samun gafarar Allah.
4- Da kuma,
koyan hukunce-hukuncen azumi, da laddubansa, da ababen da suke bata azumi, da
abinda ke halatta ga mai azumi, da wanda baya halatta, domin azuminmu ya
kasance ingantacce.
5- Da nisantar ayyuka
masu shagaltarwa, gwargwadon iko, domin mu samar da lokacin yin ibadodi a cikin
watan Ramadana, Kuma hakika Sufyan As-Sauriy idan watan azumi ya shigo, ya kan bar
kowane abu; domin ya fiskanci karatun Alkur'ani.
6- Kuma lallai
watan azumi, dama ce mai matukar girma domin nisantar munanan al'adu, da
azizita halaye ababen yabo, Allah Ta'alah ya ce:
(يا أيها الذين ءامنوا
كُتب عليكم الصيامُ كما كُتب على الذين من قبلكم لعلكم تتقون) [البقرة: 183].
Ma'ana: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI AN WAJABTA AZUMI AKANKU, KAMAR YADDA AKA
WAJABTA SHI GA WADANDA SUKE A GABANINKU, TSAMMANINKU ZA KU SAMU TAKAWA"
[Bakara: 183].
Allah yasaka da mafi alkairi
ReplyDelete