2019/02/18

LITTAFIN USULUS SALASA DA DALILANSU الأصول الثلاثة وأدلتها Wallafar Muhammadu dan Abdulwahhab







LITTAFIN
USULUS SALASA DA DALILANSU
الأصول الثلاثة وأدلتها


Wallafar
Sheikh Muhammadu dan Abdulwahhab (1115-1206H)


Tarjamar
Abubakar Hamza


Bismil Lahir Rahmanir Rahim
Ka sani –Allah ya yi maka rahama-
(Lallai yana wajaba akanmu mu koyi mas'aloli guda hudu)
Mas'alar farko: ILIMI, )Shine ilimin sanin Allah, da sanin AnnbinSaصلى الله عليه وسلم  da sanin addinin Musulunci, tare da dalilai).
Mas'ala ta biyu: AIKI DA ILIMIN.
Mas'ala ta Uku: YIN DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI).
Mas'ala ta hudu: Hakuri kan cutarwa a cikinsa).
Dalili akan abinda ya gabata shine fadinsa Madaukaki:"INA RANTSUWA DA ZAMANI * LALLAI MUTUM YANA CIKIN HASARA * FACE WADANDA SUKA YI IMANI, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN KWARAI, KUMA SUKA YI WA JUNA WASIYYA DA BIN GASKIYA, KUMA SUKA YI WASIYYA DA YIN HAKURI".
Shafi'iy –رحمه الله- ya ce: Da Allah bai saukar da wata hujja ga halittunsa ba, sai wannan sura, to da ta isar musu)(1).
 (Kuma Bukhariy –رحمه الله- ya ce: Babin da ya kunshi bayani kan: Ilimi shine gabanin zance da aiki).
 (Dalili akan haka shine fadin Allah Ta'alah: SAI, KA SANI, LALLAI BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA, FACE ALLAH, KUMA KA NEMI GAFARAR ZUNUBANKA) [Muhammadu: 19]. Sai Allah ya fara da batun ilimi, gabanin zance da aiki).


Ka sani, Allah ya yi maka rahama; Lallai yana wajaba akan kowane Musulmi namiji da mace, su koyi wadannan mas'alolin guda uku, kuma su yi aiki da su).
MAS'ALAR FARKO: Lallai Allah ya halitta mu, kuma ya azurta mu, kuma bai bar mu kara zube ba, sai ya aiko mana da wani Manzo; wanda ya masa biyayya ya shiga Aljannah, wanda kuma ya saba masa ya shiga wuta) (1).
Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki: "Lallai ne Mu, mun aiko wani Manzo zuwa gare ku, Mai shaida akanku, kamar yadda muka aika wani Manzo zuwa ga Fir'auna * Sai Fir'auna ya saba wa Manzon, saboda haka Muka kama shi, kamu mai tsanani" [Muzammil: 15-16].
MAS'ALA TA BIYU: Lallai ne Allah, baya yarda a hada shi da wani cikin bautarsa; Mala'ika ne makusanci, ko kuma Annabi Manzo).(Dalili akan haka kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
MAS'ALA TA UKU: Lallai duk wanda ya yi da'a ga Manzo, kuma ya yi tauhidin Allah, baya halatta a gare shi, ya so ko ya jibinci wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, koda kuwa dangin da yafi kusanci ne).
Dalili kan wannan mas'alar shine fadinSa madaukaki: "BAZA KA SAMU MUTANEN DA SUKA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE SUNA YIN SOYAYYA DA WANDA YA SABA WA ALLAH DA MANZONSA BA; KODA KUWA SUN KASANCE UBANNINSU NE, KO 'YA'YANSU, KO 'YAN'UWANSU, KO DANGINSU, WADANNAN ALLAH YA RUBUTA IMANI A CIKIN ZUKATANSU, KUMA YA KARFAFA SU DA WANI RUHI DAGA WURINSU, KUMA ZAI SHIGAR DA SU ALJANNONI WADANDA KORAMU KE GUDANA KARKASHINSU, SUNA MASU DAWWAMA A CIKINSU, ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUMA SUN YARDA DA SHI, WADANNAN SUNE KUNGIYAR ALLAH, KUMA LALLAI KUNGIYAR ALLAH SUNE MASU BABBAN RABO" [Mujadalah: 22]

Ka sani –Allah ya shiryad da kai zuwa ga biyayya a gare shi-, Lallai mikakken addini; tafarkin annabi Ibrahima, shine: Ka bauta wa Allah, shi kadai, kana mai tsantsanta addinni a gare shi, kuma da aikata haka, Allah ya umarci dukkan mutane, kuma ya halitta su don haka, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJANI BA, FACE SU BAUTA MIN".
Ma'anar: "SU BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi umarni da shi, shine, Tauhidi, wanda kuma shine: kadaita Allah a cikin bauta.
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi hani akansa, shine shirka, wanda kuma ita ce: Rokon wanin Allah tare da Allah.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KU BAUTA WA ALLAH, KADA KU HADA SHI DA KOWA" [Nisa'i: 36]

Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama wajibi mutum ya sansu?
Sai ka ce: Bawa, ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- (1).
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka?
Sai ka ce: Ubangijina, shine Allah, wanda ya ke rainona, kuma ya reni dukkan talikai, da ni'imominSa, kuma shine abin bautata, bani da wani abin bauta, idan ba shi ba.
Dalili akan haka shine fadinSa Madaukaki:
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI". Kuma dukkan abinda ba Allah ba halitta ne, Ni kuma daya ne daga cikin wadannan halittun.
Idan kuma aka ce maka: Da me ka san Ubangijinka?
Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa, Kuma daga cikin ayoyinsa, akwai dare da yini, da rana da wata, Daga cikin halittunsa, akwai sammai bakwai, da kassai bakwai, da abinda suke cikinsu da abinda suke cikinsu.
Kuma dalili shine fadinSa Madaukaki: "DAGA AYOYINSA AKWAI DARE DA YINI DA RANA DA WATA, KADA KU YI SUJJADA GA WATA KO RANA, KU YI SUJJADA GA ALLAN DA YA HALITTA SU, IDAN KUN KASANCE GA SHI KADAI KUKE YIN BAUTA".
Da fadinSa: "LALLAI NE UBANGIJINKU SHINE ALLAN DA YA HALITTA SAMMAI DA KASA, A CIKIN YINI GUDA SHIDA, SA'ANNAN YA DAIDAITA A SAMAN AL'ARSHI, YANA SHIGAR DA DARE YA RUFA YINI, YANA NEMANSA DA GAGGAWA, KUMA RANA DA WATA DA TAURARI HORARRU NE DA UMARNINSA, KUMA HALITTA TASA CE, UMARNI NASA NE, ALBARKAR ALLAH UBANGIJIN HALITTU TA BAYYANA".
Kuma Ubangiji shine abin bauta, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "YA KU MUTANE KU BAUTA WA UBANGIJINKU DA YA HALITTA KU, DA WADANDA SUKE GABANINKU, DOMIN KU SAMU KARIYA * WANDA YA SANYA MUKU KASA SHIMFIDA, SAMA KUMA GINI, KUMA YA SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA, SA'ANNAN YA FITAR DA ABINCI DAGA 'YA'YAN ITACE, DA SHI, SABODA KU, DON HAKA, KADA KU SANYA WA ALLAH KISHIYOYI, ALHALI KUNA SANE".
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya halicci wadannan ababen shine ya cancanci bauta".

Kuma nau'ukan ibada wadanda Allah ya yi umarni da su, Misalinsu shine: Musulunci, da Imani, da Ihsani, kuma daga cikin ibada akwai, addu'a, tsoro, fata, tawakkali, bayyana kwadayi, da tsoro, da khushu'i, da khashyah, da maida lamari ga Allah, da neman taimako, da neman tsari, da neman agaji, da yanka, da bakance, da abinda wannan ba daga cikin na'ukan ibada, wadanda Allah ya yi umarni da su, dukkansu ana yinsu ga Allah Ta'alah.
Dalili kuma shine: FadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
Kuma duk wanda ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah shi mushriki kafiri, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA DUK WANDA YA ROKI WANI ABIN BAUTAR TARE DA, BASHI DA HUJJA AKAN HAKA, TO LALLAI HISABINSA YANA WURIN UBANGIJINSA, KUMA LALLAI SHA'ANIN, KAFIRAI BASA SAMUN RABO".
Ya zo a cikin hadisi, "Addu'a itace ibada".
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA UBANGIJINKU YACE, KU ROKE NI, ZAN AMSA MUKU, LALLAI WADANDA SUKE GIRMAN KAI, BASA MIN BAUTA ZASU SHIGA JANNAMA, SUNA KASKANTATTU".
Dalili kan ibadar tsoro shine, fadinSa Madaukaki: "KUMA KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA IDAN KUN KASANCE MUMINAI"(1).
Dalilin ibadar fata kuma shine fadinSa Madaukaki: "DUK WANDA YA KASANCE YANA FATAN HADUWAR UBANGIJINSA, TO YA AIKATA AIKI NAGARI, KUMA KADA YA HADA WANI CIKIN BAUTAR UBANGIJINSA".
Dalilin Tawakkali shine fadinSa Madaukaki: "GA ALLAH NE, ZA KU DOGARA, IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Da fadinSa: "KUMA DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH, TO YA ISAR MASA"(1).
Dalilin ibadar kwadayi da fargaba da khushu'i, shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE, SU, SUN KASANCE SUNA YIN SAURIN AIKATA ALKHAIRORI, KUMA SUNA ROKONMU CIKIN KWADAYI DA FARGABA, KUMA SUN KASANCE A GARE MU MASU KHUSHU'I".
Dalilin ibadar tsoro: shine fadinSa Madaukaki: "KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA" (1).
Dalilin ibadar maida lamari ga Allah: shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU MAYAR DA LAMARI ZUWA GA ALLAH, KU MIKA WUYA A GARE SHI"(2).
Dalilin ibadar neman taimako: shine fadinSa Madaukaki: "A GARE KA MUKE YIN BAUTA, KUMA DAGA GARE KA MUKE NEMAN TAIMAKO".
Ya zo cikin hadisi: "Idan zaka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah"(3).
Dalilin ibadar neman tsari: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN SAFIYA".
Da "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN MUTANE"(4).
Dalilin ibadar neman agaji: shine fadinSa Madaukaki: "A YAYIN DA KUKE NEMAN AGAJIN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA MUKU"(5).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: LALLAI NE SALLATA DA YANKANA, DA RAYUWATA, DA MUTUWATA, NA ALLAH NE UBANGIJIN TALIKAI * BASHI DA ABOKIN TARAYYA".
Ya zo cikin sunnah: "Allah ya tsine wa wanda ya yi yanka, ga wanin Allah".
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "SUNA CIKA BAKANCE, KUMA SUNA TSORON YININ DA SHARRINSA KE YADUWA".

ASALI NA BIYU: SANIN ADDININ MUSULUNCI, DA DALILAI.
SHINE, Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta daga shirka da ma'abutansa.
Kuma addini martabobi uku ne, musulunci, da imani, da ihsani. Kuma kowace martaba tana da rukunnai.
Martabar farko: Musulunci.
Kuma rukunnan musulunci guda biyar ne:
Shaidawa babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bayar da zakkah, da azumin ramadhana, da hajjin dakin Allah mai alfarma
Dalilin Kalmar shahada shine fadinSa Madaukaki: "ALLAH YA SHAIDA CEWA: LALLAI NE BABU ABIN BAUTAWA DA CANCANTA FACE SHI, KUMA MALA'IKU DA MA'ABUTA ILIMI SUN SHAIDA, YANA TSAYE DA ADALCI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA FACE SHI, MABUWAYI MAI HIKIMA".
Kuma ma'anar kalmar (LA ILA ILLAL LAHU) shine babu abin bautawa da cancanta, face Allah, saboda "LA ILAHA" tana kore cancanta ne ga dukkan ababen da ake bauta musu, koma bayan Allah. "ILLAL LAHU" kuma, yana tabbatar da cancantar bautan ne ga Allah shi kadai; bashi da abokin tarayya cikin bautarsa, kamar yadda bashi da abokin tarayya cikin mulkinsa.
Kuma tafsirin (LA ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki: "KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA KAGI HALITTA TA, LALLAI SHINE ZAI SHIRYAR DA NI * KUMA YA SANYA (WANNAN MAGANAR) KALMA MAI WANZUWA, A CIKIN ZURIYARSA TSAMMANINSU SU KOMA DAGA BATA".
Da fadinSa: "KA CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU DA KU, KADA MU BAUTA WA KOWA, FACE ALLAH, KUMA KADA MU HADA KOME DA SHI, KUMA KADA SASHENMU YA RIKI SASHE, UBANGIJI, BAICIN ALLAH, IDAN KUMA SUKA BIJIRE, SAI KACE: KU YI SHAIDA CEWA, LALLAI NE MU MASU SALLAMAWA NE".
Dalili akan shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine fadinSa Madaukaki: "HAKIKA WANI IRIN MANZO DAGA CIKIN KAYUKANKU YA ZO MUKU, ABINDA KE WAHALAR DA KU YANA BUWAYARSA, KUMA MAI KWADAYI NE A GARE KU, GA MUMINAI KUMA MAI TAUSHI NE, MAI JIN KAI".
Ma'anar shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine: Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a bauta wa Allah sai da abinda wannan annabin ya kawo na shari'a.
Kuma dalili kan sallah da zakkah da kuma fassarar tauhidi shine fadinSa Madaukaki: "BA A UMARCE SU DA KOMAI BA, FACE BAUTA WA ALLAH SUNA MASU TSARKAKE ADDININSU A GARE SHI KUMA MASU KARKATA ZUWA ADDINI GASKIYA, KUMA SU TSAYAR DA SALLAH, SU BADA ZAKKAH, KUMA WANNAN SHINE ADDINI MIKAKKE"(1).
Kuma dalilin azumi shine fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA WADANDA KE GABANINKU, LA'ALLA KO ZA KU SAMU TAKAWA"(2).
Kuma dalilin hajji shine fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA WAJABTA WA MUTANE HAJJIN DAKINSA GA WANDA YA SAMU HANYAR ZUWA GARE SHI, KUMA WANDA YA KAFIRCE, TO LALLAI ALLAH YA WADATA DAGA TALIKAI".

MARTABA TA BIYU: ITACE; IMANI;
Kuma imani sifofi ko rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU, Kuma mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya, Kuma kunya reshe ne na imani.
Kuma rukunnan imani guda shida ne, kamar yadda ya zo cikin hadisi, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittatafanSa, da ManzanninSa, da Ranar karshe, kuma ka yi imani da kaddara na alkhairinsa da sharrinsa".
Kuma dalili akan wadannan rukunnan guda shida, fadinSa Madaukaki: "BA KAWAI SHINE ADDINI BA, KU JUYAR DA FISKOKINKU, WAJEN GABAS KO YAMMA BA, AMMA ADDINI SHINE GA WANDA YA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE, DA MALA'IKU, DA LITTATAFAI, DA ANNABAWA".

Kuma dalilin kaddara FadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MU, KOWANE ABU MUN HALICCE SHI DA KADDARA".

MARTABA TA UKU: IHSANI (KYAUTATA BAUTA)
Rukunnansa, Yana da rukuni daya ne, kuma shine ka kyautata bautar Allah, kamar kana ganinsa, domin idan kai baka ganinsa, ai shi yana ganinka; dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE ALLAH YANA TARE DA MASU TAKAWA, WADANNAN DA SUNE MASU KYAUTATA BAUTA".
Da fadinSa: "SAI KA YI TAWAKKALI GA MABUWAYI MAI RAHAMA * WANDA KE GANINKA A LOKACINDA KAKE TSAYUWAR SALLAH * DA JUJJUYAWARKA A CIKIN MASU SUJJADA * LALLAI NE SHI, SHINE MAI JI MASANI".
Da fadinSa: "BA ZA KA KASANCE CIKIN WANI SHA'ANI BA, KO KA KARANTA KUR'ANI, KO KU AIKATA WANI AIKI, FACE MUN KASANCE MUNA HALARCE, A LOKACIN DA KUKE KUKKUTSAWA A CIKINSA".

Dalili kuma daga cikin sunnah, shine shahararren hadisin mala'ika Jibrila, wanda aka ruwaito shi daga Umar –رضي الله عنه-ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, Sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, kuma babu wani daga cikinmu da ya sanshi, har ya zauna kusa da Annabi –صلى الله عليه وسلم-; Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma dora tafukansa akan cinyoyinsa, yace: Ya Muhammadu! Bani labari akan Musulunci?  Yace: Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, kuma ka tsayar da salla, ka bada zakka, ka yi azumin watan ramadana, ka yi hajjin daki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi. Sai yace: ka yi gaskiya, Sai muka yi mamakinsa; yana tambayarsa kuma yana gaskata shi.
Sai yace: ka bani labari akan imani? Yace: Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi imani da kaddara; na alkhairinsa dana sharrinsa.
Yace: To ka bani labari akan "ihsani"? Sai yace:Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to shi yana ganinka.
Yace: To ka bani labari akan kiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba.  Sai yace: To ka bani labari akan alamominta? Sai yace: Baiwa zata haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa takalma, tsiraru, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace: Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani lokaci, Sa'annan  sai yace: Ya kai Umar, shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai yace: Allah ne da manzonsa suka sani.
Yace: Lallai shi mala'ika Jibrilu ne, ya zo muku, domin ya karantar da ku addininku".

ASALI NA UKU: SANIN ANNABINKU MUHAMMADU –صلى الله عليه وسلم-
Shine annabi: Muhammadu dan Abdullahi bn Abdulmuddalib, dan Hashim, Hashim kuma daga kabilar Kuraishawa ne, su kuma Kuraishawa daga al'ummar larabawa suke, larabawa kuma daga zurriyar annabi Isma'il dan Ibrahimul Khalil, Allah ya yi karin mafificin salati da sallama akansa, da kuma Annabinmu.
Ya rasu, yana da shekaru sittin da uku, shekaru arba'in gabanin annabta, shekaru ashirin da uku yana annabi manzo.
An bashi annabta ne da saukar "Ikra'a", an kuma turo shi da manzanci da saukar "Ya, ayyuhal muddasir".
Garinsa (na haifuwa) shine Makkah, ya kuma yi hijira zuwa ga Madina.
Allah ya turo shi da gargadi daga shirka, kuma domin ya yi kira zuwa ga Tauhidi;
Dalili kuma shine, fadinSa Madaukaki: "YA WANDA YA LULLUBA DA MAYAFI * KA TASHI DOMIN KA YI GARGADI * KUMA UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI * KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU * GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU * KADA KA YI KYAUTA KANA NEMAN KARI *  KUMA SABODA UBANGIJINKA, SAI KA YI HAKURI".
Ma'anar: "KA TASHI DOMIN KA YI GARGADI" wato yayi gargadi akan shirka, ya kuma kira zuwa ga tauhidi.
"KUMA UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI", Ma'ana: ka girmama shi da tauhidi.
"KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU", ma'ana: ka tsarkake ayyukanka daga shirka.
"GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU", Rujz: gumaka, kwaurace musu: shine barinsu da barranta daga gare su, da ma'abutansu.
Ya dauki shekaru goma yana yin da'awa akan tauhidi. Kuma bayan shekaru goma sai aka yi mi'iraji da shi zuwa sama, sai aka farlanta masa salloli biyar, kuma ya yi salla a garin Makkah tsawon shekaru uku, bayansu kuma aka umarce shi da yin hijira, zuwa garin Madina.

Hijira: ita ce: kaura daga garin shirka, zuwa garin musulunci.
Kuma hijira farilla ne, ga wannan al'ummar, daga garin shirka, zuwa garin musulunci, kuma aiki da ita yana nan, har zuwa tashin kiyama.
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI WADANNAN DA MALA'IKU SUKA KARBI RAYUKANSU, ALHALIN SUNA MASU ZALUNTAR KANSU, SU KAN CE MUSU: A CIKIN ME KUKE? SAI SUKA CE: MUN KASANCE WADANDA AKA RAUNANA A CIKIN KASA, SUKA CE: ASHE KASAR ALLAH BATA KASANCE MAYALWACIYA BA? DOMIN KU YI HIJIRA GARE TA, TO WADANNAN MAKOMARSU JAHANNAMA CE, KUMA TA MUNANA TA ZAMA MAKOMA * IN BANDA MASU RAUNI DAGA MAZA DA MATA DA YARA, WADANDA BASU IYA YIN WATA DABARA, KUMA BASU SHIRYUWA GA HANYA * TO WADANNAN AKWAI TSAMMANIN ALLAH YA YAFE LAIFI DAGA GARE SU, KUMA ALLAH YA KASANCE MAI YAFEWA NE MAI GAFARA".
Da kuma fainSa Madaukaki: "YA BAYINA, WADANDA SUKA YI IMANI, LALLAI NE KASATA MAI YALWA CE, SABODA HAKA KU BAUTA MINI".
Bagawiy –رحمه الله- ya ce: "Sababin saukar wannan ayar akan musulmin da suke garin Makkah ne, wadanda basu yi hijira ba ne, sai Allah ya kira su da sunan imani".
Dalili kuma akan hijira daga cikin hadisai, akwai fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Hijira bata yankewa har sai karban tuba ya yanke, kuma tuba bata yankewa har sai rana ta fudo daga mafadarta".
Yayin da ya zauna a garin Madina sai aka umarce shi da yin aiki da sauran shari'oi, misalin zakkah(1), da azumi, da hajji, da jihadi, da kiran salla, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da wasun wadannan daga cikin shari'oin musulunci.
Ya dauki shekaru goma akan haka, bayan haka kuma sai ya rasu, salatin Allah da sallamarsa su kara tabbata a gare shi(2).
Addininsa kuma mai wanzuwa ne, wannan shine addininsa, babu wani alkhairi face ya nusar da al'umma a gare shi, kuma babu wani sharri face ya tsawatar mata akansa.
Kuma alkhairin da ya nuna wa al'umma, shine Tauhidi da dukkan abinda Allah yake sonsa, kuma ya yarda da shi.
Sharrin kuma da ya tsawatar akansa, shine: Shirka da dukkan abinda Allah baya sonsa, kuma ya ke kinsa.
Allah ya aike shi da Manzanci zuwa ga mutane gaba daya, kuma ya farlanta yin da'a a gare shi, akan dukkan aljanu da mutane; Dalili kuma shine FadinSa Madaukaki: "KA CE: YA KU MUTANE, LALLAI NE NI 'DAN AIKAN ALLAH NE ZUWA GARE KU GABA DAYA".
Kuma Allah ya cika addini, da shi, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "A YAU NA CIKA MUKU ADDININKU, KUMA NA CIKE NI'IMATA AKANKU, KUMA NA YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI".
Kuma dalili akan mutuwarsa –صلى الله عليه وسلم-: "LALLAI NE KAI MAI MUTUWA NE, KUMA LALLAI SU MASU MUTUWA NE * SA'ANNAN KU, A RANAR KIYAMA, A WURIN UBANGIJINKU, MASU YIN HUSUMA NE".
Kuma Mutane idan suka mutu za a tayar su, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "DAGA KASA MUKA HALITTA KU, KUMA ZUWA CIKINTA ZA MU MAYAR DA KU, KUMA DAGA GARE TA ZA MU FITAR DA KU, A KARO NA GABA".
Da fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA TSIRAR DA KU DAGA KASA TSIRARWA, SA'ANNAN ZAI MAYAR DA KU CIKINTA, YA KUMA SAKE FITAR DA KU FITARWA".
Kuma bayan an tayar da su za a musu hisabi, kuma za a sakanta musu da ayyukansu, Dalili kuma akan haka shine fadinSa Madaukaki: "NA ALLAH NE, DUKKAN ABINDA KE CIKIN SAMMAI DA KASSAI, ZAI SAKANTA GA WADANDA SUKA MUNANA AIKI DA ABINDA SUKA AIKATA, KUMA YA SAKANTA WA WADANDA SUKA KYAUTATA DA ALJANNAH"(1).
Duk kuma wanda ya karyata lamarin sake tayar da mutane, to ya kafirta, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "WADANDA SUKA KAFIRTA SUN RIYA CEWA, BA ZA A TAYAR DA SU BA, KA CE, A'A, INA RANTSUWA DA UBANGIJINA, LALLAI NE ZA A TAYAR DA KU, SA'ANNAN A BAKU LABARIN ABINDA KUKA AIKATA, KUMA WANNAN GA ALLAH ABU NE MAI SAUKI"(2).
Kuma Allah ya turo Manzanni gaba dayansu, suna yin albishir, suna gargadi, Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki: "MANZANNI MASU ALBISHIR DA GARGADI".
Na farkonsu shine annabi Nuhu –عليه السلام-, Na karshensu kuma, annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma shine cika-makin annabawa.
Dalili akan farkon manzanni shine annabi Nuhu –عليه السلام- shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MUN YI WAHAYI ZUWA GARE KA, KAMAR YADDA MUKA YI WAHAYI GA NUHU DA ANNABAWAN DA KE BAYANSA".
Kuma Allah ya farlanta wa dukkan bayi su kafirce wa dagutu, su yi imani da Allah, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: Dagutu, shine dukkan wanda bawa ya wuce iyakarsa, na ababen bauta, ko wadanda ake bi, ko wadanda ake musu da'a.
Kuma kowace al'ummar da Allah ya tura mata manzo, tun daga lokacin annabi Nuhu har zuwa annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- yana umartarsu ne da ibadar Allah; shi kadai, kuma yana hana su bauta wa dagutu, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA HAKIKA MUN TAYAR MANZO GA KOWACE AL'UMMA; DA CEWAR; KU YI BAUTAR ALLAH, KU NISANCI DAGUTU".
Dagutu suna da yawa, amma manyansu guda biyar ne; Iblisu –Allah ya la'ance shi-, da wanda aka masa bauta alhalin ya yarda, da wanda ya kira mutane zuwa ga bauta a gare shi, da wanda ya riya sanin wani abu na ilimin gaibu, da wanda yay i hukunci ba da abinda Allah ya saukar ba, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "BABU TILASTAWA A CIKIN ADDINI, HAKIKA SHIRIYA TA BAYYANA DAGA BATA, DON HAKA, WANDA YA KAFIRTA DA 'DAGUTU, KUMA YA YI IMANI DA ALLAH, TO HAKIKA, YA YI RIKO DA IGAYA AMINTACCIYA".
Wannan kuma shine ma'anar (LA ILAHA ILLAL LAHU).
Kuma ya zo a cikin hadisi "Kan wannan lamari, shine musulunci, kuma kashin bayansa shine salla, kuma tozon kololuwarsa shine jihadi fiysabillahi".

2019/02/15

DOGARO DA TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH التوكل على الله تعالى DR. ALIYU ALHUZAIFY 10 6 1440











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/Jumadal Akhirah/1440H
daidai da 15/FABARAIRU/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH
(التوكل على الله تعالى)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara,  Mai hakuri abin godiya. Ga Ubangijinmu ne -Mabuwayi da daukaka- falala take, da yabo mai kyau, da ni'imomi na zahiri dana boye, ba mu iya kididdige yabo a gare shi, Shi kamar yadda ya yi yabo ne ga kanSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Masanin abinda suke a cikin kiraza.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa, wanda Allah ya turo shi domin rahama ga Talikai.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu da iyalansa da sahabbansa, salati da sallama masu dawwama, har zuwa ranar tayarwa da hisabi.
Bayan haka
Ku yi takawar Allah, ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, da kauracewa munana, domin hakan shine hanyar samun yardar Allah (سبحانه), da rabauta da samun darajoji a cikin Aljannoni, da gyaruwan halaye, a cikin wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwa.

Ya ku Musulmai
Ko yaushe, ku tuna Rahamar da Allah ya muku, a lokacin da ya zubo ni'imominSa akanku na zahiri da kuma a boye. Kuma ku girmama ni'imar Alkur'ani, da ni'imar sunnar Annabi mai yin bayani da fassara ga wannan Littafi Mabuwayi, saboda Allah ya daukaka Mutum ne da su, izuwa ga matsayin da yafi daukaka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, domin ku ne mafiya daukaka, idan kun kasance masu imani" [Ali-imrana: 139].
Kuma Allah (Subhanahu) ya ce: "A'aha! Lallai hakika, littafin masu da'a yana wuri madaukaki (na illiyuna)" [Mudaffina: 18].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:  "Kun kasance mafi alherin al'ummah, wanda aka fitar ga Mutane, kuna umurni da alheri, kuma kuna hani da abin ki, kuma kuna imani da Allah" [Ali-imrana: 110], don haka, Daukakar Mutum da kimarsa da alkhairinsa da matsayinsa suna kasancewa ne da akidarsa ta Musulunci, da kuma irin ayyukansa na kwarai, wadanda da su ne, yake kasancewa salihi, mai kawo gyara a cikin wannan rayuwar.
ALKUR'ANI MAI GIRMA, DA SUNNAR ANNABI MUHAMMADU saw, Allah ya raya zukata da su, kuma Allah ya warkar da kiraza da su, daga cututtuka, kuma ya bada basira da su daga makanta, kuma da su yake gusar da nau'ukan shirka da bata da kafirci da ilhadi, kuma yake tsarkake  hankula da zukata da su daga cutukan sha'awowi da shubuhohi, wadanda suke canza fidirar addini mikakkiya da hankula lafiyayyu. Wannan kuma rahama ce daga Allah Mabuwayi da daukaka ga Mutane.
Kuma bayan Allah (سبحانه) ya cire daudodi daga zukata, da munanan halaye, da sifofi ababen zargi, ta hanyar Alkur'ani da Sunnah, Sai ya cusa imani da rassansa a cikin zukatan, domin imani da rassansa ba za su samu gindin zama a zuciyar Mutum ba, sai zuciyar ta wofinta daga abinda yake kishiyantar imanin, saboda kwarya ko masaki ba zai kasance mai tsarki ba, sai an gusar da najasosi daga cikinsa, Sai kuma a sanya abubuwa masu tsarki. To ita ma zuciya kwatankwacin masakin take.
Kuma hakika Allah Ta'alah ya sanar da mu hakan, a farkon surar da Allah ya mayar da annabinSa Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) manzo da saukarta, saboda ya kasance annabi ne da saukar: Ikra'a, ya kuma kasance: Manzo, da saukar: Ya Ayyuhal Muddasir, a inda Allah (سبحانه) ya ce: "Ya wanda ya lulluba da mayafi * ka tashi domin ka yi gargadi * kuma Ubangijinka sai ka girmama shi * kuma tufafinka sai ka tsarkake shi * Kuma Gumaka sai ka kaurace muku" [Muddassir: 1-5].  Sai Allah ya umurce shi, a farko, da kiyayar shirka, da yin gargadi ga masu dogewa akansa, da bayanin muninsa, da girman ukubobinsa. Sa'annan sai ya umurce shi da girmama Ubangiji Ta'alah ta hanyar tauhidi da kuma kalmomin yabo. Sa'annan sai ya umurce shi, da yin tsarki, a farko a dunkule, sa'annan sai aka saukar da hukunce-hukuncensa dalla-dalla a bayan haka. Kuma ya umurce shi da kaurace wa Gumaka, da kyale su, da barranta daga masu yin bauta a gare su.
Kuma wadannan ayoyin kamar fadin Allah Ta'alah ne: "Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata, don haka, wanda ya kafirta da dagutu, kuma ya yi imani da Allah, to hakika ya yi riko da igiya mai karfi, babu yankewa a gare ta" [Bakara: 256]. Sai Allah ya fara da bayar umurnin cewa a kafirce wa Dagutu, domin imani ya tabbatu a cikin zuciya.

Kuma mafi girman ni'imar Ubangiji ga BawanSa, ita ce Allah ya bashi zuciya lafiyayya, wanda zai shiryar da shi da ita zuwa ga ILIMI MAI AMFANI, DA AIKI NA KWARAI, Allah Ta'alah ya ce: "Ranar da dukiya bata amfani, haka 'ya'ya * sai ga wanda yaje wa Allah da zuciya lafiyayya" [Shu'ara'i: 88-89].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya Allah, lallai ni ina rokonka tabbatuwa cikin wannan lamari (Musulunci), da azama akan ayyukan shiriya, kuma ina rokonka godiya ga ni'imominka, da kyautata ibadarka, kuma ina rokon ka bani harshe mai gaskiya, da zuciya lafiyayya" Tirmiziy ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana daga hadisin Shaddad dan Aus -رضي الله عنه-.

Daukakar Musulmi, tana ga yin imani, da daukacin ressansa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma daukaka ta Allah ne, da ManzonSa, da kuma Muminai, saidai Munafikai ba su sani ba" [Munafikuna: 8].
Kaskantuwar Mutum kuma, tana cikin ayyukan sabo da zunubai, Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai wadanda suke saba wa Allah da ManzonSa, lallai wadannan suna daga cikin mafiya kaskanci" [Mujadala: 20].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya fada a cikin ganawarsa da UbangijinSa Madaukaki: "Lallai Kai  kana yin hukunci, kai kuma ba a yin hukunci akanka, kuma lallai wanda ka jibinta baya kaskanta, kuma wanda ka ke ki baya samun daukaka, saboda albarkaka -Ya Ubangijinmu- ya yawaita, kuma ka daukaka" Ma'abuta littafin sunan suka ruwaito shi.
Kuma ya tabbata Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Imani rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu shine fadin: LA ILAHA ILLAL LAHU, Mafi kankantansu kuma: Gusar da abu mai cutarwa daga hanya. Itama kunya reshe ne daga imani".

Kuma Ubangijinmu Tabaraka wa Ta'alah ya shar'anta mana, abinda zai amfanar da mu a rayuwarmu, da kuma bayan mutuwarmu, ya kuma hane mu aikata abinda zai cutar da mu a cikin rayuwarmu da kuma bayan mutuwarmu. Kuma shi Mahalicci Mabuwayi da daukaka, aikin biyayya baya amfanar da shi, kuma saba masa baya cutar da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Allah hakika Mawadaci ne daga barin Talikai" [Ankabut: 6].

Kuma yana daga dalilan KUDURAR ALLAH سبحانه  da ILIMINSA da HIKIMARSA da RAHAMARSA da FALALARSA da KYAUTATAWANSA da BAIWARSA, Yadda ya shar'anta wa Musulmi ibadodin da zai samu daukaka zuwa ga darajojin kamala, da tsarkaka, da samun kyan hali da su, domin ya isa izuwa ga abinda aka kaddara masa (na matakan girma), kuma domin ya rabauta (ya samu sa'ida) a cikin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa, Allah Ta'alah yana fada dangane da sifofin Muminai: "Wadanda suke tsayar da sallah, kuma daga abinda muka azurta su suna ciyarwa * Wadannan sune muminai na hakika, suna da darajoji a wurin Ubangijinsu, da wata gafara, da arziki mai karamci" [Anfal: 3-4].
Sai Ubangiji Mai rahama ya bayyana AYYUKAN ZUKATA, a cikin Alkur'ani da Sunnah, kamar tsarkake niyya (Ikhlasi) da yakini, da rukunnan imani, da tsoro da fata, da wasun haka. Kuma Allah a cikin Alkur'ani da Sunnah ya bayyana AYYUKAN GABBAI, Misalin rukunnan Musulunci, da umurni da kyakkyawa, da hani da mummuna, da makamantansu. Kuma ya fifita sashen ayyukan akan sashe.
Kuma mafi girman abinda Musulmi zai kusanci Ubangijinsa da shi, shine ayyukan zukata, wadanda Allah ya yi umurni da su a cikin Alkur'ani da Sunnah.
Kuma ayyukan zukata sune ginshiki ga ayyukan gabbai.
Kuma Musulmai suna samun fifiko da ayyukan zukata, da kuma sanin ma'anoninsu, da sifantuwa da su, don haka ne Sahabbai -رضي الله عنهم- suka rigayi dukkan Mutane, cikin lamarin ayyukan zukata, kuma suka samu fifiko a cikinsu. Sa'annan sai Tabi'ai, saboda yadda suka san cikakken ma'anoninsu, kuma suke aiki da hakikaninsu, kuma saboda cikar fikihunsu ga harshen Larabci, da cikar tauhidinsu, hasanul Basariy ya ce: "Abubakar, ba ya fi ku ne, saboda yawan azumi da salla ba, saidai saboda abinda ya tabbatu a cikin zuciyarsa".

Kuma yana daga cikin MAFI GIRMAN AYYUKAN ZUKATA, WADANDA SUKA FI DAUKAKA: DOGARO KO TAWAKKALI GA ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ga Allah, za ku dogara, idan kun kasance Muminai" [Ma'idah: 23]. don haka, Tawakkin Bawa ga Allah Ta'alah ibada ne, saboda Allah ya yi umurni da shi, a cikin wannan ayar, da kuma wasu ayoyin. Ma'ana: Ku fawwala al'amuranku gabadayansu zuwa gare shi.
Shi kuma fadinSa (سبحانه): "idan kun kasance Muminai" ya nuna cewa lallai Tawakkali sharadi ne na imani, wato imanin yana koruwa a lokacin da tawakkalin ya tafi.
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma gaibin sammai da kasa na Allah ne, kuma zuwa gare shi ake mayar da dukkan al'amura, sai ka bauta masa, kuma ka dogara akansa" [Hudu: 123]. Sai ya ware tawakkali da ambato, bayan ambaton ibada (saboda muhimmancinsa).
MENENE TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH?
Ma'anar Tawakkali: Shine Dogaro ga Allah سبحانه cikin lamura gaba dayansu, na Duniya da Lahira, da gaskiya cikakkiya, da kuma tsarkake niyya wanda ya barranta daga shakku, da fawwala dukkan al'amura zuwa ga Mahalicci Mai jin kai Mai iko akan komai, da jin amintuwa da Allah Mai girma, tare da barrantar zuciya daga jin tana wayo da karfi, da yarda da abinda Allah ya hukunta wa Bawa na dukkan al'amura. Duk wanda ya samu wannan matsayi na tawakkali (dogaro ga Allah) to ya samu mafi girman abin nema, kuma Allah ya hada masa dukkan abin samu, kuma Allah Ta'alah ya jibinci al'amuransa, sai ya kasance daga cikin Bayin Allah salihai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Majibincina shine Allah wanda ya saukar da wannan littafin, kuma shine yake jibintar Salihai" [A'araf:  196].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ku saurara! Lallai ne Waliyyan Allah (masoyansa) babu wani tsoro akansu, kuma su ba za su yi bakin ciki ba * Wadannan da suka yi imani, kuma suka kasance masu takawa" [Yunus: 62-63].
Kuma Allah a cikin hadisin kudusiy ya ce: "Ni ina ga yadda Bawana ya yi zatona, kuma lallai ina tare da shi idan ya ambace ni", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-Hurairah.

Tawakkali shine mafakar Annabawa -عليهم الصلاة والسلام- wanda yake kare su daga makircin makiyansu.
Kuma Tawakkali shine karfin da ba a rinjayarsa daga makiya Annabawa -عليهم السلام-, kuma da shi Annabawan a cikin rayuwarsu suke fiskantar nau'ukan tsanani da bakin ciki, da musibun da suke sauka, sai su rinjayi kowane tsanani da bacin rai da tawakkali, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka karanta musu labarin Nuhu, a lokacin da ya ce wa Mutanensa, Ya ku Mutanena, idan matsayina da tunatarwata game da ayoyin Allah sun kasance sun yi nauyi akanku, to ga Allah na dogara, sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan shirkinku, sa'annan kada al'amarinku ya kasance rufaffe akanku, sa'annan ku nemi gamawa da ni, kada ku yi mini jinkiri" [Yunus: 71].
Abdullahi dan Abbas -رضي الله عنه- ya ce: "Kalmar HASBUNAL LAHU WA NI'IMAL WAKIL Ma'ana: Allah ya isar mana, Annabi Ibrahim -عليه السلام- ya fade ta, a lokacin da aka jefa shi a cikin wuta" Bukhariy ya ruwaito.
Kuma Allah Ta'alah yake fada ga AnnabinSa Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-: "To, idan sun juya baya, sai ka ce: MA'ISHINA SHINE ALLAH, BABU ABIN BAUTAWA FACE SHI. A GARE SHI NA DOGARA, Kuma shine Ubangijin Al'arshi mai girma" [Taubah: 129].
Kuma Allah Ta'alah yake fada dangane da annabi Hudu -عليه السلام-: "Lallai ni na dogara ga Allah Ubangijina kuma Ubangijinku, babu wata dabba face shine Mai riko ga makwarkwadarta, hakika Ubangina yana kan tafarki madaidaici" [Hudu: 56].
Kuma Allah Subhanahu ya ce: "Sai Musa ya ce: Ya ku Mutanena! Idan kun kasance kun yi imani da Allah, to a gare shi kawai za ku dogara, idan kun kasance Musulmai * Sai suka ce: Ga Allah muka dogara" [Yunus: 84-85].
Kuma Allah (سبحانه) yake fada dangane da dukkan Manzanninsa: "Kuma menene a gare mu, ba za mu dogara ga Allah ba, alhali kuwa ya shiryar da mu ga hanyoyinmu? Kuma lallai ne, mu yi hakuri ga abinda kuka cutar da mu, kuma ga Allah ne masu dogaro za su dogara" [Ibrahim: 12].
Don haka, duk wanda ya tabbatar da ibadar tawakkali ga Allah, to lallai shine mai samun rabo, abin taimako akan kansa, da kuma makiyansa na daga Aljanu da Mutane.
Wanda kuma ya tozarta ibadar tawakkali, ba za a taimake shi ba, kuma zai bata, kuma babu abinda zai amfane shi.
Kuma tawakkali yana daga cikin sifofin Muminai masu tauhidi, Allah Ta'alah ya ce: : "Lallai Muminai, sune wadanda suke idan an ambaci Allah, zukatansu suke firgita, kuma idan an karanta ayoyinSa akansu, su kan kara musu imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara" [Anfal: 2].

Kuma yana daga cikin tawakkali, YIN AIKI DA SABUBBAN DA ALLAH YA SHAR'ANTA, da mu'amalantarsu. Da kuma yin aiki da sabubban da aka sansu ta hanyar jarraba su, da yin riko da su, tare da rashin dogaro akansu, a'a dogaron zai kasance ne ga Allah shi kadai.
Saboda barin sabubba baya cikin tawakkali, kuma sabubban halittu ne na Allah; idan Allahn ya yi nufi sai ya bata su; ya zama ba su yin wani amfani. Idan kuma ya so sai ya sanya amfani a cikinsu, don haka al'amarin gaba dayansa na Allah Ta'alah ne.
Kuma BABBAR SHIRKA a babin tawakkali shine, Mutum ya fawwala al'amarinsa zuwa ga 'dan'uwansa mahaluki, rayayye ko matacce, sai kuma ya dogara akansa, akan irin abinda halittar bata da iko a kai, sai Allah Mabuwayi da daukaka, kamar dogaron Mutum ga wani shehi, da cewa zai gafarta masa zunubansa, ko ya taimake shi akan makiyinsa, ko zai amsa masa addu'arsa, ko ya dogara akansa, da cewa zai masa ceto. Domin ceton Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- a ranar kiyamah tana kasancewa ne, ga kowane Musulmi, da kuma kowane salihi, da izinin Allah. Ko ya dogara ga wata halitta cewa, ita zata warkar da shi, ko ta masa baiwar 'da, da makamancin haka.
Shi kuma kaso na biyu na SHIRKA A BABIN TAWAKKALI, Shine shirkar da bata kai ga babbar shirka ba, wanda kuma ita ce: Ya dogara ga wani cikin wani al'amari daga nau'in al'amurran da yake da iko akansu, kamar ya dogara akansa cewa, shi zai samar masa aiki yi, a inda zai iya, sai ya manta da UbangijinSa Mabuwayi da daukaka, ya yi fatan samu daga 'Dan'uwansa halitta. To wannan nau'i bai kai ga babbar shirka ba. Kuma wajibin shine ya sanya wannan halittar a matsayin daya daga cikin sabubban da yake aiki da su, Amma sai ya dogara ga Allah shi kadai, Wani daga cikin Magabatan kwarai yana cewa: "Wani ba zai yi fatan samun wani abu daga wurin wani ba, face ya rasa fatansa a inda bukatarsa tafi tsananta a gare shi".

Amma, bada wakilci a cikin abinda ake iya na'ibci a cikinsa, misalin saye da sayarwa, to wannan ya halatta, tare da wajabcin kudurta, cewa lallai wakili baya iya cika maka muradinka, sai da taimakon Allah, da ikonsa.
Kuma hakika Allah ya yi alkawarin bayar da mafi girman sakayya akan tawakkali, a inda yace: "Lallai ne Allah yana son masu tawakkali" [Ali-imrana: 159]. Saboda, duk wanda Allah ya kaunace shi, to zai bashi alkhairori, kuma zai kiyaye shi daga sharri da ababen ki, Allah Ta'alah ya ce: "Wanda ya dogara ga Allah, to lallai Allah ne ma'ishinsa" [Dalak: 3]. Wato, UbangijinSa ya isar masa abinda ya dame shi, ya ke bakanta masa, kuma zai gyara masa al'amuransa a cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa. Wannan kuma shine mafi girman sakamako da lada. Kuma Allah bai ambaci irin wannan sakamakon a wata ibadar da ba ta tawakkali ba. Kuma wannan ya ishe tawakkali falala.
Kuma Ahmad da Ibnu-Majah da Nasa'iy sun ruwaito daga Abu-zarrin, Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم-  ya karanta masa wannan ayar, sai ya ce masa: "Da dukkan Mutane za su yi riko da wannan ayar da ta isar musu".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas -رضي الله عنهما- daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda yake son ya kasance yafi Mutane karfi, to ya dogara ga Allah", Abdu Ibnu Humaidin ya ruwaito shi.
Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma ka dogara akan Rayayye wanda ba ya mutuwa, kuma ka yi tasbihi game da gode masa. Kuma Allah ya isa zama Mai kididdige laifuffukan BayinSa" [Furkan: 58].

Allah ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai * Mai rahama Mai jin-kai. Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominnsa gaba daya, wadanda muka sani da wadanda ba mu sani ba.
            Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya Madaukaki Mai girma.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai karamci.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa, kuma ku yi tawakkali a gare shi, domin duk wanda ya dogara gare shi zai isar masa.

Ya ku Bayin Allah
Ku yi riko da sabubban tawakkali, kuma ku cike matakansa, kuma ku kiyayi abinda yake kishiyantarsa, ko yake rage cikar kamalarsa, saboda tawakkali shine guzurinku a cikin wannan rayuwar, kuma dalilin amintuwa a gare ku bayan mutuwarku daga dukkan azaba da fitina da bakin ciki, Allah Ta'alah ya ce: "Babu hukunci face daga Allah. a gare shi na dogara, kuma a gare shi masu dogara za su dogara" [Yusuf: 67].
Kuma Allah Ta'alah: "Kuma ga Allah ne kadai Muminai za su dogara" [Ibrahim: 11].
Kuma ku rika neman arziki na halal, domin a rika karbar ibadodinku, da addu'oinku, kuma ku nemi shi ta hanyar tawakkali ga Allah Mabuwayi da daukaka, saboda ya zo cikin hadisi, daga Umar dan Alkhaddab -رضي الله عنه- daga Annabi -صلى الله عليه وسلم-, ya ce: "Da za ku dogara ga Allah, hakikanin tawakkali, da ya azurta ku, kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana fita da safiya da yunwa, sai ya koma da yammaci a koshe", Imam Ahmad ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma ya ce: Hadisi ne hasan sahih.

Ya ku Bayin Allah!
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...