2016/10/28

HUDUBAR masallacin Annabi 3 شوال 1437 daidai 08 July 2016M, Ta Husain Alus-sheikh








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
 JUMA'A, 03/SHAWWAL/1437H
Daidai 08/JULY/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI?
     Shehin Malami wato: Husaini xan Abdul'aziz Alu Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI, Wanda a cikinta kuma ya tattauna, akan watan ramadana da tunatarwa kan shuxewar yinin ramadana da dadarensa, da abinda suka qunsa a cikinsu na aiyukanmu; na alherinsu da sharrinsu, da abinda ke wajaba akan musulmi na biyar da kyakkyawan aiki bayan kyakkyawa, Sannan ya ambaci lamarin tayar da boma-bomai da ya zama sababin zubar da jinane da kashe rayuka a qasar Harami biyu, Yana mai faxakar da iyaye da Maluma da wayayyu da kafafen sadarwa cewa su riqa koyar da samari suna faxakar da su kan shari'ar Allah (تعالى).

HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da ba a qididdige su.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da abokin tarayya, a lahira da duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, annabi zavavve, kuma bawa zavavve.
Ya Allah! ka yi daxin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta gaskiya da tsoron Allah ( taqawa).
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

'Yan'uwan Musulunci
Mamakin saurin shuxewar kwanaki, da wucewar watanni!
Shi mai hankalin da aka yi masa dacen taufiqi shine ke riqan kwanaki da watanni a matsayin lokatan kusantar Allah majivinci –جل وعلا-, tare da kiyaye yin biyayya a gare shi, a sirrance da a bayyane.

Kuma lallai abinda ya wajaba akan musulmi a cikin wannan rayuwar shine: Ya yi qoqarin tabbatar da manufar samar da shi, a tsawon rayuwarsa gabaxayanta; ta hanyar tsayuwa akan tauhidin Allah (جل وعلا), da bin dokokinsa, da biyayya wa Majivincinsa (Allah); Saboda rayuwa gabaxayanta; Manufarta mafi girma itace, yin aiki da umurnin Allah, da qoqarin tabbatar da bauta a gare shi (سبحانه), kamar yadda Allah (جل وعلا) ya ke cewa: "Ka ce: Lallai sallata da yanke-yankena, da rayuwata, da mutuwata ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya, kuma da aikata haka aka umurce ni, kuma nine farkon musulmai" [An'aam: 162-163].
Da faxinsa (جل وعلا): "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana ambaton Allah a dukkan lokutansa.

          Ya ku taron Musulmai!!
            Idan Musulmi ya tsayu a cikin watan ramadana don ya amfana da lokutansa, ta hanyar gaggawa cikin aikata aiyukan alkhairi, da kusantar Ubangiji da sauran mustahabbai, To wajibi ne akansa ya yi godiya wa Allah (جل وعلا) akan haka, Sai kuma ya yi iya qoqarinsa a cikin shekararsa gabaxayanta, wajen aikata dangogin xa'a, gwargwadon iko, saboda Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Aikin da Allah ya fi so, shi ne wanda aka dawwama akansa, koda ya yi kaxan", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Kuma hanyoyin samun lada, da damammakin kwasar garavasar kyawawan aiyuka, a cikin shari'ar rangwame da sauqi da rahama da falala (wato: shari'ar musulunci), suna da matuqar yawa, kuma nau'i-nau'i ne, a cikin zantuka da aiyuka.

       'Yan'uwan Musulunci!!
            Sha'anin da yafi girma, Shi ne musulmi ya tsayu wajen aikata aiyuka na wajibi, da nisantar munana; ababen kyama da shari'a ta yi hani akansu, Allah (تعالى) yana cewa: "Ka tsayu, kamar yadda aka umurce ka, da waxanda suka tuba a tare da kai, kuma kada ka qetare iyaka" [Hud: 112].     
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ka ce: Na yi Imani da Allah, sa'annan ka tsayu".

       Ya ku bayin Allah!
            Ku kiyaye aiyunku kyawawa, kuma ku nisanci gurvata abinda Allah ya yi muku ni'imar aikata su, saboda fallasasshen Mutum na haqiqa a madubi na shari'a, kamar yadda nassoshi su ka nuna shi ne: Wanda zai gina aiyuka kyawawa manya-manya, sa'annan sai ya rushe su, ta hanyar sakar wa gavvansa linzami cikin zaluntar halittun Allah, da yin ta'addanci a gare su, cikin magana ko aiki.

       Ya ku taron Musulmai!
            A qarshe-qarshen watan azumi, a lokacin da musulmai su ke farin cikin qarisa azumi da salloli ko tsayuwar dare, bayan kuma Allah ya yi wa Musulmai dacen kammala tilawar maganar Allah Mai hikima, Masani: Sai kwatsam musulmai su ka tashi da jin labarin aika-aikan kaiwar harin boma-boman da su ka zubar da jinni, su ka kuma kashe rayuka, su ka tsoratar, har guda uku, a qasar harami biyu, wanda a cikinsu su ka tara mafi girman ababen qi, Daga cikin laifuka kuma, su ka qunshi mafi muninsu, Daga cikin kaba'irai kuma mafi girmansu, daga wata qungiya, wanda ta karkace daga koyarwar wahayin alqur'ani da sunnah, sannan (qungiyar) ta fice daga jama'ar musulmai, kuma ta haifar da ababen da su ka jawo varna mai girma a qasashen musulmai, da kuma sharri mai yaxuwa, Wanda babu mai farin ciki da aukuwar hakan sai maqiyan addini.
            Shin waxannan, ba za su ji tsoron damqar Mai girma Allah (maxaukaki da buwaya) ba?!
Shin ba za su yi taqawar Mabuwayi Mai gafara ba?!
Ina su ke lokacin da Ubangijinsu zai tambaye su, kan kashe rayukan mutanen da basu ji ba, basu gani ba?!
Menene kuma matsayansu dangane da mahaliccinsu, alhalin suna yawo da varna mai faxi, ta hanyar razanar da amintattu, masu bauta, da sallah, ta hanyar kashe marasa laifi, masu azumi, musamman a kusa da masallacin ManzonSa amintacce, a cikin wata mai girma, alhalin sauran mutane suna cikin salloli, da qanqan-da-kai ga Ubangijin talikai!

       Ku saurara!
       Ya ku samari Musulmai!
            Ku tsaya, tsayawa ta tunani da hankalta, kuma ku xauki darasi daga munanan qarshe, wacce aqidun waxanda su ka karkace daga jama'ar musulmai, su ke kai su, mutanen da su ka halatta jinin masu bauta, masu azumi, da salloli, da i'itikafi (don yin bauta) ga Ubanjinsu, suna masu sujjada da qanqan-da kai (a gare shi).
            Ya wanda aqida ta sanya shi zamewa daga (turbar) daidai, har ya kauce wa hanya ya bar tafarkin gaskiya… Ka tuba zuwa ga Ubangijinka (جل وعلا) gabanin ka sadu da shi, Ka dawo zuwa ga hanyar muminai kamar yadda Ubangijinka ya umurce ka da aikata hakan, kuma Manzonka (صلى الله عليه وسلم) ya umurce ka da aikata hakan, Ka komo izuwa ga kewayen jama'ar musulmai, saboda nassoshin shari'a sun tsawatar maka, daga fanxarewa ga jama'a, kuma sun hane ka, kan raba kai, da nisantar jama'a.
Kuma mafi girman hanya a tarihin al'ummar musulmai, mafi girman hanyar da Shexanun aljanu ko na mutane su ke bi, don vata kwakwale, kuma domin fitar da su daga shiriya miqaqqa, ita ce: Nisantar jama'ar masu sallah, da shiriyar masu bauta, da turbar ko tafarkin muminai, "Kuma kada ku bi hanyoyin shexan, lallai shi a gare ku, maqiyi ne bayyananne" [Baqara: 168, da 208, da An'aam: 146].
Kuma Alqur'ani da sunna basu nusar da mu ba, sai izuwa ga ababen da za su gyara halayenmu, Kuma a duk lokacin da mu ka yi nisa da haka, sai varna mai faxi ta auku.

       Ya samarin musulunci!
            Lallai mafi girman takobi ko makamin da masu qiyayya da musulunci, kuma maqiya annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) su ke bi; domin kekketa riga ko ganuwar addini, ko domin yaqar garurrukan musulmai: Mafi girman makaminsu shi ne Ta hanyar qosar da sabbuban  jawo rabuwar kai (a cikin al'ummah), da fitar da samari daga jama'ar musulmai, da hujjojin da zahirinsu rahama ne, baxininsu kuma azaba, wato: hujjar taimakon addini, da yin hidima wa lamuransa. Hakan kuma baya kasancewa daga gare su sai bayan sun nesanta samari daga Maluma na Allah, da jiga-jigan faqihai masu ilimi na tantancewa, da shugabanni masu neman kawo gyara.
Kuma duk wanda ya karanta tarihi to hakan zai bayyana masa qarara; Saboda (a tarihance) babu abinda ya sha gaban al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) wajen yin hidima ga addininta, da yaxa saqon Annabinta, fiye da fitinar (khawarijawa) ta fanxarewa ga jama'ar musulmai, wanda dukkan ma'abuta musulunci gabaxaya su ke tare da ita. Saboda idan akwai irin waxannan fitintinun to ba za a iya hidima wa addini ba, kuma ba zai yiwu a yi masa hidima ba, kuma ba za a iya tsayar da wata rayuwa managarciya ba. Hasali ma fanxarewa jama'ar musulmai bai jawo komai ga musulunci da musulmai ba, sai varna mai girma, ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da kuma sharri mai yaxuwa. wanda harshen mai fasaha (a cikin huxuba) bai isa ya qididdige irin varnar ba, a wuri irin wannan.

Ya ku Mutanen wannan qasa !
Lallai qasarku ana nufinta da sharri, cikin hidimarta ga harami biyu, da kuma cikin abinda Allah ya yi mata na ni'imomi masu yawa, sai ku haxa kanku akan alkhairi, ku nisanci rabuwar kai da dukkan nau'ukansa, ku kiyaye daga aukawa cikin tarkon maqiya, da masu jiran ganin aukuwar sharri, waxanda su ke yin fata a gare ku, da al'ummarku, da 'ya'yanku da jikokinku masu zuwa, su ke muku fatan qarewa da halaka da rugujewa.

Lallai hanyoyin sadarwa wajibi ne akansu su gyara tafiyarsu, kuma su zama an fiskantar da su domin kawo amincin al'ummai, da kiyaye yara da jikoki.

Kuma wajibi ne akan dukkan musulmai su nisanci makami mai illa, wanda raunin da ya ke yi yana zubar da jini, Shine: Jita-jita masu mugun manufa, da qarerayi masu jijjiga mutane.

Wajibi ne ga ma'abuta garin harami biyu, su zama jini da tsoka tare da jagororinsu, suna xauka daga malumansu na Allah, waxanda aka yi musu shaida da zurfin ilimi da addini da tsantseni da hikima da sanin jiya-da-yau.

Kuma wajibi ne akan kowa, ya rinjayar da maslahohi na gabaxaya, akan na xaixaiku.
Kuma su yi ta faxi-tashi wajen hidima wa qasarsu, da gaskiya da ikhlasi, suna masu neman lada da sakayya (a wurin Allah), saboda kasancewarta qasar harami ne guda biyu da ta ke yin hidima wa addini, kuma ta ke yin hidima wa musulmai gabaxaya, wajibi ne su yi qoqari wajen haka, suna xaukar haka daga faxakarwar addininsu da manufofin shari'arsu.

Wajibi ne akan iyalai su riqa kula da 'ya'yansu samari, suna bibiyar halayensu, suna dubi cikin yanayinsu, kuma su riqa sanya musu ido cikin ababen da su ke fiskanta, tare da komawa zuwa ga Allah (جل وعلا) da yin addu'ar cewa ya kiyaye 'ya'yansu daga kowace fitina da jarabawa da kuma aqida vatatta, saboda yin addu'a daga iyaye biyu sababi ne mai girma na samun gyaruwa.

Ya malaman wannan al'ummar!
Himmatuwa da lamuran wannan al'ummar ya kasance kuna sanya hikima a cikinsa da kaifin hankali, da kyautata duban mai zai-je ya komo, kuma mu kiyayi kowace magana ko fatawar da samari za su iya fahimtarta ba a gurbinta ba, ko su su xora ta ba a ingantaccen wajen xaukar ta ba. Wannan kuma ba zai yiwu ba, sai idan ana lura da manufofin shari'a, waxanda maluman musulunci su ka yi bayaninsu, tare da kyautata karatun fahimtar addini ta hanya miqaqqa, wanda zai xauki samari izuwa ga aiki da hikima da bi sannu-sannu, da tausasawa, da nisantar gaggawa.

Daga qarshe:
Kalmar godiya ce, ga jami'an tsaro a qasarmu, da kuma shi mutum na farko mai kula da tsaro (wato shugaba), saboda suna kan tozo na azama, da hasama, da kula da hidima wa musulmai, da kiyaye musu amincinsu, da zaman lafiya, bayan Allah (جل وعلا); da fatan Allah ya saka musu da mafi alkhairin sakamako.
kuma ya kiyaye su daga kowani mummuna.
Kuma ya karvi wanda ya mutu daga cikinsu cikin shahidai.
kuma Allah ya warkar da kowani maras lafiya mai rauni.

Ina faxar wannan maganar,
kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran musulmai daga kowani zunubi,
sai ku nemi gafararsa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
            Ina godiya wa Ubangijina kuma ina yin yabo a gare shi.

       Ya ku Musulmai:
            Yana daga falalar Allah (جل وعلا) ga al'umma: Abinda ya shar'anta a gare su, na aiyukan biyayya da xa'a; waxannan da za su basu lada mai yawa, Saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya faxa cewa: "Wanda yayi azumin ramadana, sannan ya biyar da guda shida a watan shawwal, to kamar ya azumci shekara ne".

            Kuma baya halatta –a xayan zancen maluma guda biyu da ya fi fitowa fili-, ga wanda akwai ramukon azumi na wajibi akansa ya gabatar da azumi na mustahabbi; saboda yin hakan ya saba wa qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi ingantattu.

            Sai ku kasance –Ya ku bayin Allah- kuna masu xaukar darasi daga watan azumi, wanda zai kai ku izuwa ga falaloli masu girma, da halayya kyawawa. Kuna masu siffantuwa da sifar kyauta a rayuwarku gabaxaya, da kuma kyautatawa da jin qai a asirce da a bayyane.
Saboda al'ummar annabi Muhammadu al'umma ce da ya wajaba ta rayu a duniya da halayya maxaukaka, da kyawawan ababe masu girma. Kuma yin hakan, yana cikin MANUFOFIN ADDININMU DA MANYAN HADAFIN SHARI'AR UBANGIJINMU na farlanta farillai, da wajabta wajibabbu.

            Sannan yana daga cikin aiyuka mafi girma: Yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
            Ya Allah! Kayi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu, masoyinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
            Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye su da kiyayewarka, da kulawarka da kariyarka,
Ya Allah! Ka yaye baqin cikinsu, ka kawar da vacin ransu.
            Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulunci,
Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulmai,
Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya Ma'abucin girma da karramawa,
Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya  Mabuwayi Ya Mai hikima.
            Ya Allah! Ka gafarta wa muminai maza da muminai mata, da musulmai maza da musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu.
            Ya Allah! Ka datar da majivincin lamarinmu zuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda, Ya Ma'abucin girma da karramawa.  
            Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai,
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
            Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu,
Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu,
Ya Allah! Ka qarfafe su, ka datar da su, ka tagaza musu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
            Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah,
Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah,
Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
Kuma ka mayar da su zuwa qasashensu cikin lafiya da riba, Ya Rayayye, Ya Tsayayye.
            Ya Allah ka bamu mai kyau a duniya, A lahira ma mai kyau, Ka kare mu daga azabar wuta".
            Ya Allah! Ka sanya mu cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu, kuma ka gafarta musu zunubansu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
            Ya Allah! Ka samar wa musulmi wani lamari na shiriya, Ya Allah! Ka samar wa musulmi gabaxaya wani lamari na shiriya, wanda za ka gyara halinsu da shi, Ya rayayye Ya tsayayye.


Qarshen addu'armu shine: ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.

2016/10/27

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم, 27 Muharram1438H daidai da 28 Oktoba2016M ta DR. ABDULBARIY AS-SUBAITIY











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27 /Muharram/1438H
daidai da 28/ Oktoba/ 2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
MAXAUKAKIYAR HIMMA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: MAXAUKAKIYAR HIMMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan xaukaka himma, da wajabcin samar da ita a cikin musulmai, musamman a wannan lokaci, yana yin ishara ga abinda ke aukuwa a cikin faya-fayen bidiyo dayawa, na watsa ko yaxa bidiyoyi marasa qima, waxanda ba su da wani amfani, sai ma cutarwa, yana mai bayyana cewa lallai akan kafafen sadarwa, da samari, da 'yan'mata, da wassunsu daga cikin vangarorin al'umma, rawar takata, da wasu aiyuka, waxanda suka dace da matsayinsu a cikin al'umma, wajen yaqar waxannan ababen marasa qima.

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah, yabo ya tabbata ga Allah wanda ya kare zukatanmu daga vata, da kuma kafofin shigowar ababe marasa qima, Ina yabo a gare shi -سبحانه- kuma ina gode masa, akan dukkan alheri da falala, da kuma qari.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, wanda ya cike rayuka da imani, da kuma jin daxi.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, jagora abin misalicikin hukunci da jagoranci.
Allah ya qara salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, waxanda su ka jagoranci wannan al'ummar da kyakkyawan jagoranci.

Bayan haka:

            Ina yin wasiyya a gare ku, da kaina da tsoron Allah, Allah maxaukaki yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-imrana: 102].

Musulunci yana renon mutum musulmi da hukuncinsa da hukunce-hukuncensa da halayyarsa da laddubansa akan SIFANTUWA DA MAXAUKAKIYAR HIMMA, DA BADA MUHIMMANCI GA ABABE MAXAUKAKA, waxanda za su sanya rayuwar musulmi ta yi ta xaukaka, manufofinsa kuma su yi ta qara tabbatuwa, aiyukansa kuma, su yi ta ginuwa suna bada fa'ida, domin mutuntakarsa ta yi fice, ya kuma xaga kai daga, yasassun lamura, da qananansu marasa qima, ya kuma fiskanci aiki tuquru, da buri maxaukaki, wanda zai bunqasa shekarunsa, ta hanyar gina su, da aiyuka, da sadaukarwa. Waxannan sifofin basa canzawa don an samu canjin zamani da lokatai, kuma musulmi baya kaucewa daga aikata irinsu, duk yadda aka samu canje-canjen hanyoyi, ko banbancin fasahar zamani, Umar bn Abdul'aziz (رحمه الله) ya ce: "Lallai ne Ni ina da wata rai, mai tsananin bege da himma, ban tava samun wani abu ba face na yi sha'awar abinda ya fi shi alheri, Na yi sha'awar zama Gwamna, a yayin da na same shi, sai na yi sha'war na zama khalifa, a  yayin da na samu khalifa kuma sai na yi sha'awar samun abinda ya fi shi alkhairi; wato aljannah, kuma ina fatan zan same ta".

            Musulunci ya tsarkake xabi'ar musulmi daga kukkutsawa cikin qananan lamura marasa qima da amfani, ko aukawa cikin tavon varna, izuwa ga neman cimma manufofi masu girman xaukaka, da isa ga ababe masu muhimmancin daraja, da qulla rai ko rayuwar musulmi da yin bauta ga Allah (سبحانه وتعالى) wanda hakan shi ne mafi girman matsayi, kuma babbar manufa, kuma shi ya ke haskaka hanya, aiyuka kuma a jikinsa su ke rataya, kuma shi ne tushen abubuwa masu muhimmanci.

             Varna da bin qananan lamura marasa qima, su kan kautar da mutum daga manya-manyan lamura, kuma suna kashe ruhin aiki ko raunata shi, har ya zama ba za a yi fatan samun wani amfani ba, ko a aminta daga wata cuta (daga mai irin wannan hali).

            Zukatan da suka abauce, suna sauka daga aiyuka ko manufofinsu maxaukaka, sai su sanya lokutansu gabaxayansa ya zama a wargi, mafi yawan kwanakinsu kuma, ya kasance aikin kara-zube, haka kuma suna tozarta aikinsu na wajibi (dole), sai matsayinsu ya zagwanye, rayuwarsu kuma ta wayi gari a wofi, da aiyuka marasa qima.

            Himmomi suna yankwanewa, a lokacin da su ke dulmuya cikin lamura marasa qima, sai su xauki vangarori iri-iri daban-daban, kamar: QOQARIN TABBATAR DA LABARIN YASASSUN ABUBUWA MARASA QIMA,  DA JANYO ABABE MUNANA, KO WAUTA, A CIKIN WASU SHIRYE-SHIRYE (na radio ko talabijin) WULAQANTATTU, DA QOQARIN YAXA SU, TA HANYOYIN GANAWA NA AL'UMMAH (facebook), don neman suna, ko samun shaharar da ba ta asali ba, da qoqarin wasafta abubuwan da ke aukuwa marasa qima, masu cutarwar da ba sa amfanarwa, kuma masu jawo varna, wanda ba sa kawo amfani ba, sannan kuma suna munanta kama, ko tarihin mai aikata su, tare da kwaye tsiraicinsa, a lokacin da ke bayyana cikin wata tufa ko yanayi mummuna, ko ya ke wata magana ta alfasha, ko wani aiki mai aibi, ko cikin wani yanayin da zai sanya masu hankali a cikin al'umma su raina shi, masu mutunci kuma su ji qyamarsa.
A cikin hakan kuma, akwai munana wa addininsa, da qasarsa, da al'ummarsa.

            Dogewa cikin yasassun lamura, irin waxannan, ya kan sanya tsatsa cikin halayya, da tawaya cikin hankali, kuma yana nuni kan jahiltar abinda ake ce wa RAYUWA, da rashin zurfin tunani, da samun koma-baya cikin sani da wayewa. Kamar yadda ya ke kashe kyakkyawan nufi, ya ke raunata lamarin bunqasa. Kuma lallai ba zai vuya wa mai hankali ba, abin da hakan zai jawo, na varna a zamantakewa, da rayuwarsa da iyali.

            Duk wanda ya sauko, da tunaninsa zuwa ga lamura marasa qima  ko amfani, to sai ya girmama bin son zuciya, ya kuma yi sakaci, ko sako-sako da abubuwan da Allah ya haramta, Sai zuciyarsa ta yi dauxa da aikata savo, azamarsa ta yankwane, saboda aikata zunubai, fixirarsa ta addini kuma ta samu koma-baya.
Kuma ba zai vuya ga mai hankali ba cewa, lallai sababin da ya sanya wannan al'ummar samun kanta cikin qasqanci, har ta wulaqanta, a wurin Allah da halittunsa shi ne: Keta abubuwan da Allah ya haramta, Allah (تعالى) yana cewa: "Haka, Kuma duk wanda ya girmama haramiyar Allah, to shi ne mafifici a gare shi a wurin UbangijinSa" [Hajj: 30].

Miqa-wuya ga qananan lamuran marasa qima ko amfani, da abubuwan varna, na kaiwa zuwa ga/ rashin kulawar mutum ga mutane, da kuma baiyanar da aikin savo, wanda ke kashe xabi'ar kunya, wannan kuma shine abinda ManzonAllah (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar akansa, a cikin faxinsa: "Dukkan al'ummata za a musu afuwa, in banda masu bayyanar da laifi, kuma yana daga cikin bayyanar da laifi: Mutum ya aikata wani aiki cikin dare, sai ya wayi gari alhalin Allah ya rufa masa asiri, ya riqa cewa: ya kai wane: ai jiya da dare, na aikata kaza da kaza; shi ya kwana Ubangijinsa yana rufa masa asiri, sai ga shi ya wayi gari yana yaye sitirar da Allah ya yi masa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Allah (سبحانه وتعالى) Mai rufa asirin bawa ne, a ranar qiyama, kuma zai sanya sitirarsa ga wanda ya aikata laifi, matuqar dai bai bayyanar da shi ba, Manzon Allah (صلى الله9 عليه وسلم) yana cewa: "Lallai Allah zai kusantar da mumini, sai ya xora masa lulluvinsa, ya suturce shi, sannan ya ce: Shin ka san zunubi kaza? Shin ka san zunubi kaza, Sai ya ce: E, Ubangijina! Har sai ya sanya shi, ya tabbatar da zunubansa, ya kuma gani a cikin ransa cewa, ya halaka, Sai ya ce: Na rufa maka asiri akansu a duniya, kuma Ni zan gafarta maka su, a yau. Sai a bashi littafin kyawawan aiyukansa", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

Himmatuwa da abubuwa marasa qima, da bibiyar mutane marasa amfani: Zai sanya mu, mu samar da wassu taurari daga cikinsu, waxanda za su riqa fitowa a gaba-gaba a cikin lamura, alhalin su qazantattu ne ababen qyama, kuma za mu riqa tunkuxa su, don samun shahara, da tallen da mu ke yi wa aiyukansu munana, da fina-finansu qasqantattu, kuma hakan zai kai, a buxa musu fili domin vata jama'a, da rusa halayya, da kawar da mutane daga bunqasa a fagagen aiyukan nasara da bunqasa.
Abinda kuma ya fi xaci ko muni, Shine Ruxuwar waxannan mutane marasa qima ko amfani, da shahararsu, sai su baqanta wasu mas'aloli da basa fahimtar su, da kuma ilimin da basu mallaki mafarinsa ba; har a samu masu fitowa gaba-gaba suna fatawa cikin hukunce-hukuncen shari'a da addini cikin jahilci, da son zuciya, sai kuma a samu matar da ta fito ta ke nuna qarancin muhimmanci sanya hijabi, kuma ta ke izgili da shi, A samu wani na uku, yana izgili da karantarwar musulunci da hukunce-hukuncensa, wani na huxu kuma, yana cakalar mutuncin shugabanni, Na biyar kuma, a samu yana aibanta maluma da masu da'awa da xaliban ilimi. A zamanin da ana cewa: Idan ruwa ya fita daga cikin gora, to sai iska ta cika shi.

            Wanda ke bibiyar abubuwa marasa qima, da mutane marasa amfani: Ya kan cika yininsa da jayayya, imaninsa kuma da tawaya, azamarsa kuma da rauni, da kuma xabi'arsa ta hanyar yaxa jita-jita, sai kuma ya cutar da al'ummarsa da yaxa qare-rayi, da kawo koma-baya cikin zaman lafiya. Kuma sau nawa ne, waxannan qananan lamura marasa qima su ka haifar da rabuwar da babu haxin kai bayanta, da gaba ko adawar da bata warkewa!

            Son shahara ko neman suna cuta ne a cikin zuciya voyayya, kuma idan ya bunqasa a cikin tunanin mutum sai ya iza shi zuwa ga jin halaccin bin kowace hanya, sai ya sanya shi tsallaka kowace qima, ya kuma sanya masa wata yana a cikin zuciyarsa, ta yadda ba zai ga makamar alkhairi da hasken gaskiya, da ita ba, don haka ne, shari'a ta tsawatar daga son shahara, ko bayyana da neman suna, wanda rayuka da suke fama da cutar riya, mai rushe aiyuka, a ma'aunin shari'a su ke fama da shi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya sanya tufar neman shahara ko suna, Allah zai tufatar da shi ranar qiyama da tufar qasqanci", Ibnu-Majah.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka ce: Lallai ne sallata da yanke-yankena, da rayuwata da mutuwata, ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya" [An'am: 162-163].

            Bayan wani lokaci, wanda ya shagaltu da ababe marasa qima zai falka, bayan kuma waxanda suka ci nasarar rayuwa sun wuce shi, kuma masu yin abu babu wargi sun xaukaka sun barshi (a qasa), To, a wannan lokacin ne kuma zai ciza yatsun nadama, a lokacin da zai ga kansa cikin barci mai nauyi, da kawalwalniya mai yaudara, (saboda bai canza ba) yana nan a wurinsa na da, bayan jahilcinsa ya yasar da shi, kuma himmarsa qasqantatta ta rumbuxar da shi, lokacin gyara kuma ya wuce, kwata-kwata kuma babu damar aiki da nadama!

            Shi musulmi, ma'abucin wani saqo ne, a cikin rayuwa, yana yin nesa da kansa daga faxawa tavon lamura marasa qima da varna, da himmarsa maxaukakiya, da kuma bada lokaci cikin abinda Allah zai  yardar da shi, kuma ya amfanar da addininsa da qasarsa, da al'ummarsa, da ilimi mai amfani, da kuma aiki managarci.

            Wasiyyoyin musulunci masu gamewar ma'ana sun zo, waxanda su ke kare al'umma daga tasirin munanan xabi'u, da su ke cin karo da ginshiqan da halayya su ka ginu akansu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:  "Lallai Allah, Mai karimci ne, yana son kyauta, da maxaukakan halaye, kuma yana qin qasqantattu daga cikinsu", Alhakim ya ruwaito shi a cikin Mustadrak xinsa.
             
            Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah; yabon da bashi da iyaka.
            Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya, kuma bamu da Ubangiji; idan bashi ba.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, manzonsa, kuma zavavvensa.
            Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa dasahabbansa da waxanda su ka shiryu da shiriyarsa.

            Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah iyakar jin tsoronsa, kuma ku kiyaye shi a cikin sirri da gannawa.

Su iyalai sune kariya mai qarfi ta farko wajen yaqi da yadda 'ya'ya ke bada muhimmanci  ga lamura marasa qima, ta hanyar siffantuwa da sifa mai kyau, da kasancewa abin koyi nagari, da samar da wuraren bada tarbiyya ko horo domin gina himmomi, da zana manufofin xaukaka zuwa ga samun ababen xaukakar.

Su ma kafafen sadarwa, su cika da aiyukan da ba za a yi sakaci da su ba,  wajen tottoshe wurare ko mavuvvugar ababen da basu da qima, da hana fitowar mutane marasa qima ko amfani, tare da tottoshe kafofin da su ke shigowa.
Kuma hanyar da ta fi bayyana a fili wajen aikata haka; ita ce: Aiki da tabbatattun mas'alolin aqida, da gino sifa maxaukakiya.

Kuma samarinmu masu albarka suna da rawar takawa, wajen bunne lamura marasa qima, ta hanyar, qin yaxa su, ko tallata su, ko sauraren sharewarsu.

Amma ita kuma, budurwa musulma, to kunyarta shi ne tushen izzarta da kyanta; Saboda qyale kafofin ababe marasa qima magangarar rugujewar halayya ce mai hatsari, kuma sharri ne mai yaxuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kunya da Imani an gwama su a tare, kuma idan aka xage xayansu to an xauke xayan", Alhakim a cikin Mustadrak ya ruwaito shi.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku sassauta magana; domin kada wanda a cikin zuciyarsa akwai cuta, ya kwaxaitu" [Ahzab: 32].

            Kuma musulmi zai kare kansa ne daga yasassun lamura marasa qima ko amfani, da kuma varna, ta hanyar dawwamar da tunanin haxuwa da Allah, wanda hakan zai bashi kariya mai qarfi daga duk ganin da ya qaru akan na buqata, da jin da ya wuce wanda ake buqata, da maganar da ta wuce wanda ake buqata, da hulxar da ta wuce wacce ake buqata.

            Kamar yadda dawwamar da jin cewa Allah yana ganin bawa, ya kan sanya shi, ya rataya da neman matsayin da ke wurin Allah, wanda ya fi girman xaukaka akan neman suna ko son samun shahara da bayyana.

            Kuma ma'aunin gidan lahira ba shi ne ma'aunin duniya ba, Allah (تعالى) ya ce: "Idan mai aukuwa ta auku * Babu wata rai mai qaryatawa ga aukuwarta * Mai qasaqntarwa ce, mai xaukakawa" [Waqi'ah: 1-3].

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.      
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman a garin Halab, da Shaam, da Mausil, da Iraqi, da Filasxinu, da kowani wuri ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
Ya Allah! Lallai su, masu jin yunwa ne ka ciyar da su, basu da takalma ka basu, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su ka taimake su,
Ya Allah! Duk wanda ya nufe su da mummuna to ka sanya kaidinsa a qirjinsa, kuma ka sanya rugujewarsu cikin tsare-tsarensu, Ya Mai amsa addu'a
Ya Allah ka rarraba kan maqiyansu, kuma ka wargaza haxuwarsu, ka sanya mummuna ya juyo akansu, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah Wanda ya saukar da littafi, wandas ke gudanar da gajimare, Mai ruguza qungiyoyi, ka ruguza maqiya musulmai, kuma ka taimake musulmai akansu, Ya Ubangijin talika, Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu, wanda shine qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce rayuwarmu ta ke cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda zuwa gare ta ake mayar da mu, kuma ka sanya rayuwa ta zamo qari a gare mu daga kowani alkhairi, kuma ka sanya mutuwa ta zama hutu a gare mu daga aikata kowani sharri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla musu akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu,
            Ya Allah! Ka sanya mu mu zama masu ambatonta, masu gode maka, masu tsoro a gare ka, masu yin kuka a gare ka, masu mayar da lamari,
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, kuma ka tabbatar da hujjarmu, ka daidaita harsunanmu, kuma ka cire dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da canzawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan fushinka.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada waraka ga marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, kuma ka sa mu cika da alheri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara sha'aninmu dukkansa, kuma kada ka dogarar da mu zuwa ga kayukanmu, daidai da kyaftawar ido,
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka kyakkyawan cikawa, da kuma afuwa kan abinda ya gabata, ko ya kasance
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana daga albarkokinka, da rahamarka, da falalarka, da arziqinka
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka –ya Allah- saboda kai ne Allah, wanda babu abin bauta sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma mu ne faqirai, Ya Allah ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama.
Ya Allah!, shayarwa ta rahama, ba na azaba, ko bala'i, ko rusau, ko nitsewa ba
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
            Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,


TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...