2017/08/29

hudubar IDIN LAYYA 1438H عبد المحسن القاسم










HUXUBAR IDIN LAYYAH
DAGA MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/ZULHIJJAH/1438H
Daidai da 01 /SATUMBA / 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,

ALLAHU AKBAR,Duk lokacin da safiyar idi ta bayyana, tana mai haskakawa, ALLAHU AKBAR duk lokacin da mai faxin LA ILAHA ILLAL LAHU, ya faxe ta, ko ya yi kabbara, ALLAHU AKBAR duk lokacin da hasken samun nasara ya haska, ga mutumin da nufin xakin Allah mai alfarma, ALLAH NE MAI GIRMA, a duk lokacin da masu zikirinsa su ka ambace shi, a wuraren bauta masu alfarma, ALLAH NE MAI GIRMA, a duk lokacin da ababen hawan bege suka tunzura su zuwa ga filin tsayuwar Arfah, da duk lokacin da kansu a wannan matsayar, har aka kankare musu zunubai, ALLAH NE MAI GIRMA, gwargwadon wanda ya yi xawafin xaki mai girma, ya kuma yi tawali'u ga UbangijinSa ya qan-qan-da kai a gare shi,  ALLAH NE MAI GIRMA, daidai da adadin abin yankan da ake kusantar Allah da baikonsu, da kuma duk  lokacin da mai yin labbaika ya yi labbaika, da duk lokacin da masu xawafi suka yi xawafi, da duk lokacin da masu layya suka yi layya.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,
 Yabo ya tabbata ga Allah; Babu mai sauke wanda ya xaukaka, babu mai xaukaka wanda ya sauke, babu mai hana abinda ya bayar, babu mai bayar da abinda ya hana, Ya xaukaka da rinjayenSa, da matsayinSa da zatinSa, a saman dukkan halittunSa, kuma ya qagi halittu akan abinda ya so, sai ya kyauatata abinda ya sana'anta,
Daga wurinSa ake neman falala, kuma ake samun karramawa,  
Ina yin yabo a gare shi (SWT) kan ni'imominsa masu yawa, kuma ina godiya a gare shi akan falalarSa mai ninninkuwa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya, Ya sanya idi suka zama lokutan farin cikin masu biyayya, da kwanakin annashuwar masu bauta.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne; Annabin rahama da shiriya, kuma kogin kyauta, annabi mai babban girma, kuma manzon da ya fi matsayi.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; taurarin haskaka duhu, kuma zaratan shiriya.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,

       Ya ku musulmai,,,;
Mutane a gabanin turo Annabi (صلى الله عليه وسلم) sun rayu a cikin jahiliyya da vata, suna bautawa bishiyoyi da duwatsu, kuma suna roqon wanda ba Allah ba, wanda basa amfanar da su basu cutar da su,  kuma sun riqi shexanu waliyyansu koma bayan Allah, kuma suna zaton su shiryayyu ne, har aka shafe alamomin addini, fixirar addini kuma ta samu koma baya, Abu-Raja'ul Uxaradiy –رحمه الله- ya ce: "Mun kasance muna bautar dutse, idan muka sami dutsen da ya fi na farkon alkhairi, sai mu jefar da shi, sai mu xauki xayan, idan kuma bamu samu dutsen ba, sai mu tattara kamfatar qasa, sai mu zo da akuya, sai mu tatsi nononta akan wannan qasan, sa'annan mu riqa yin xawafi da shi", Bukhariy ya ruwaito shi.
            Ximammu cikin lamuransu, shu'umci da canfi shine xabi'ar rayuwarsu, basu da wata kyakkyawar manufa, sashensu yana kasha sashe, kuma wutar yaquka saboda raquma, ko doki, babu wat shari'a da ta ke hukunci a tsakaninsu, suna cin mataccen nama, suna aikata alfasha, suna shan jini da giya, kuma suna yi xawafin xakin Allah tsirara, suna kashe 'ya'yansu domin tsoron talauci, kuma suna kashe 'ya'yansu masa mata domin tsoron abin kunya, "Kuma idan aka yi albishir ga xayansu da 'ya mace, sai fuskarsa ta wuni tana baqa qirin, alhalin kuwa yana mai cike da baqin ciki" [Nahl: 58].
Mace a wurinsu tana ballagaze a wulaqance, ana rataye auren mace, ana kuma haramta mata yin aure, ana sanya ta cikin kayan gado, ba a barinta ta yi gado, ana kashe ta, zalunci shi ne rigarsu, jahilci kuma tufafinsu, "Kuma idan suka aikata wata alfasha, sai su ce: mun sami iyayenmu ne akanta, kuma Allah shine ya umarce mu da ita" [A'araf: 28].
Zamannai masu duhu, ingantaccen addini a wurin Ahlulkitabi da suka wanzu samunsa yana qaranta; ba a riskarsa, Zaid bn Amrin xan Nufailin wata rana ya fita, zuwa yankin Sham yana neman addinin gaskiya, kuma ya kasance yana cewa: "Ya Ubangina, da na san mafi soyuwar fiska a wurinka da na bauta maka da ita, sai dai ban san hakan ba. Sa'annan sai ya yi sujjada akan abin hawansa".
            Kuma Ahlulkitabi –a jahiliyya- sun kasance suna neman taimako a kan mushirkai da kafirai da batun zuwan Annabin musulunci, Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma sun kasance a gabanin haka, suna fatar taimako da shi akan waxanda suka kafirta, To a lokacin da abin da suka sani ya je musu sai suka kafieta da shi, saboda haka; la'anar Allah ta tabbata akan kafirai", [Baqarah: 89].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah ya yi dubi ga mutanen duniya, sai ya qamace su, larabawansu da ajamawansu, sai 'yan kaxan daga Ahlulkitabi", Muslim ya rawaito shi.
            Jahiliyya ce, wanda dufunta ya mamaye duniya, sai Allah ya tayar da AnnabinSa Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) a lokacin yankewar annabta, sai hasken musulunci ya yaxu, duhu kuma ya yaye, sai duniya ta haskaka da hasken shiriya da hujjoji, Allah (سبحانه) ya ce: "Haqiqa, haske ya je muku daga Allah, da kuma littafi mabayyani", [Ma'ida: 15].
Kuma da wannan hasken mutane suka fita daga duffai zuwa ga haske, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Littafi ne, mun saukar da shi zuwa gare ka, domin ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske", [Ibrahim: 1].

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALL
AHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,

Mafi girman ni'imar da Allah ya yi wa bayinSa ita ce, addinin da a baya, da gaba ba za a samu kwatankwacinsa ba, Umar bn Alkhaxxab (رضي الله عنه) ya ce: "Wanda bai san jahiliyya ba, ba zai san musulunci ba".

Allah bashi da wani addini na gaskiya a bayan qasa, idan ba musulunci ba, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai addini a wurin Allah shi ne musulunci", [Ali-imrana: 19].
Kuma "musulunci" shi ne "hanyar Allah", da "tafarkinsa madaidaici", Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma wannan hanyata ce, miqaqqiya, sai ku bi ta, kuma kada ku bi qananan hanyoyi; sai su kautar da ku daga hanyarSa", [An'aam: 153]
Allah ya yarda da musulunci ga bayinsa, a inda ke cewa: "Kuma na yarje muku musulunci ya zama addini" [Ma'ida: 3].
Kuma Allah baya karvar wani addini daga halittu idan ba musulunci ba, "Kuma duk wanda ya nemi wanin musulunci ya zama addini, to ba za karva masa ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara", [Ali-imrana: 85].
Kuma Allah baya son wani addini idan ba musulunci ba, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Mafi soyuwan addini a wurin Allah, shi ne miqaqqen addini mai sauqi", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma babu wani addinin da ke shigarwa Aljannah idan ba musulunci ba, "Kuma suka ce: Babu mai shiga Aljannah sai waxanda suka kasance Yahudu ko Nasare, wannan tatsuniyoyinsu ne, Ka ce: Ku kawo dalilinku idan kun kasance masu gaskiya * Na'am, Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa, to, yana da ladansa a wurin UbangijinSa, kuma babu tsoro a tattare da su, kuma ba za su zama suna baqin ciki ba", [Baqara: 111-112].
Addini ne kammalalle babu wata tawaya a cikinsa ta kowace fuska, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma, a yau na cika muku addininku, kuma na cika ni'imata a kanku", [Ma'ida: 3].
Shi ne mafi kyan addini, mabiyansa kuma sune suka fi dukkan kyan addini, Allah (سبحانه) ya ce: "Babu wanda yafi kyan addini fiye da wanda ya miqa wuyansa ga Allah, alhalin yana mumini", [Nisa'i: 125].
Kuma saboda kyan musulunci ne, kafiri zai qaunaci da ya kasance daga ma'abutansa, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce:  "Dayawa waxanda suka kafirta, ke burin da dai sun kasance musulmai", [Hijr: 2].

Asalin wannan addinin, da fitilar da ke xauko haskensa shi ne littafin da babu cakuxewa a cikinsa, "Littafi ne, da aka kyautata ayoyinsa, sa'an nan aka bayyana su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai qididdigewa", [Hud: 1].
Ya qunshin dukkan lamarin duniya dana addini, Allah ta'alah ya ce: "Ba mu yi sakacin barin komai ba a cikin littafi", [An'am: 38].
Ya haxa dukkan abinda mutane ke buqatarsa, Allah ta'alah ya ce: "Kuma mun sassaukar da littafi akanka, domin ya yi bayanin kowani abu", [Nahl: 89].
Littafi ne kiyayayye; wanda jirkitawa ko canji basa riskarsa, Allah ta'alah ya ce: "Lallai, mu ne muka saukar da Ambato (Alqur'ani), Kuma lallai mu, haqiqa masu kiyayewa ne a gare shi", [Hijr: 9].
Addini ne da ke shiryar da dukkan halittu, wanda ya dace da kowane zamani, mai sauqi ga dukkan mutane, wanda bai kevanta da wani launi ko jinsi ko zamani ko wuri ba, Allah ta'alah ya ce: "Ka ce: Ya ku mutane! Lallai ni manzon Allah ne zuwa gare ku gaba xaya", [A'araf: 158].
Rahama ne kuma jin-qai, ga dukkan mutane a tsawon lokaci da zamani, Allah subhanahu ya ce: "Kuma ba mu turo ka ba, face jin-qai ga talikai", [Anbiya'i: 107].
Addini ne matsakaici, cikin aqidunsa, da ibadodinsa, da mu'amalolinsa, da halayyarsa; saboda a cikinsa babu qari babu ragi, babu qetare iyaka (guluwwi) kuma babu taqaitawa, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma haka nan, muka sanya ku al'umma matsakaiciya", [Baqara: 143].
Addini ne da ke tsaye akan sauqaqawa da sassautawa, babu tsanantawa a cikinsa, babu wahalarwa, Allah ta'alah ya ce: "Allah yana nufinku da sauqi, baya nufinku da wahala", [Baqara: 185].
Kuma da wannan addinin Allah ya xauke ququmi da nauyace-nauyace ga al'umma, kuma Allah bai sanya wani qunci ba a cikin addini.
            Umarnin da su ke cikin musulunci an rataya su akan cancanta da iko, saboda Allah baya kallafa ma rai sai abinda ta ke iyawa, don haka, Babu wajibi tare da gazawa, babu kuma hara, a lokacin lalura. Kuma duk lokacin wani lamari ya yi qunci a cikin msulunci, sai a yalwata shi. Kuma Allah ya xauke zunubin abinda aka yi da kuskure ko da mantuwa, ko tilasta mutum akansa. Kuma allah ya yi afuwa ga wannan al'ummar kan abinda ta yi zancen zuci da shi, matuqar bata aikata shi, ko ta furta shi ba.
            Kuma qofar tuba, a musulunci a buxe ta ke, kuma abu ne mai sauqi da aka yassare.

            A fili musulunci ya ke, ta fiskar tushensa da manufofinsa, alamominsa a zahiri su ke, hukunce-hukuncensa a bayyane, babu cakuxa a cikinsu, ko vuya, yana shiryarwa zuwa ga walwala, kuma yana shafe wahala, Allah ta'alah ya ce: "Kuma ba mu saukar maka da Alqur'ani domin ka wahala ba", [Xaha: 2].
            Yana dacewa da kwakwale da fixirori, Allah subhanahu ya ce: "Ashe, wanda ya yi halitta ba zai iya saninta ba, alhali kuwa shi Mai tausasawa ne, kuma Mai labartawa", [Mulk: 14].

            Hukunce-hukuncensa da shari'oinsa a haxe su ke babu savani a tsakaninsu, Allah ta'alah ya ce: "Kuma da Qur'ani ya kasance daga wurin wanin Allah ne, haqiqa da sun samu a cikinsa sava wa juna dayawa", [Nisa'i: 82].
            Allah ya qaddara wanzuwa ga wannan addinin a bayan qasa, da tasiri, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Ba zai wanzu a bayan qasa ba, gidan laka, ko gashi –ma'ana: kowane gida a qauyuka da birane- face Allah ya shigar da Kalmar musulunci a cikinsa, da buwayar mabuwayi, ko qasqancin maqasqanci", Ahmad ya ruwaito shi.

            Musulunci, ya haxa tsakanin adalci da jin-qai da kawo gyara da kyautatawa, kuma da haka ne, sammai da qassai suka tsayu, Allah ta'alah ya ce: "Lallai ne Allah na yin umarni da adalci da kuma kyautatawa", [Nahl: 90].
            Baya yin umarni sai da abinda alherinsa ya ke a cike, ko yafi rinjaye. Kuma baya yin hani sai ga abinda sharrinsa ya ke cike, ko yafi rinjaye.
            Addini ne na ilimi da aiki, wanda ke shiryatarwa ga hanyar da ta fi miqewa, Allah ta'alah: "Shi ne wanda ya turo Manzonsa da shiriya, da addinin gaskiya, domin ya xaukaka shi akan addinai gaba xayansa", [Tauba: 33].
            Yana yin qira zuwa ga samun kamala da qarfi, Abbabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Mumini qaqqarfa, shine mafi alkhairi da soyuwa a wurin Allah, akan mumini mai rauni", Muslim ya ruwaito shi.
            Yana tabbatar da ginshiqan addini, baya cin karo da tabbatattun abubuwa na hankali da fixra.
            Ya kawo daidaito tsakanin buqatun ruhi da na jiki, ya kuma haxe tsakanin hankali da ilimi.
            Yana qira zuwa ga wayewa da raya qasa.
            Aminci da salama shine mafarinsa da qarshensa, kuma alamarsa, da gaisuwarsa.
Da musulunci ake samun miquwar lamuran a duniya da lahira.
Mai hikima ne cikin manuffinsa da ababen nemansa.
Hukunce-hukuncensa da shari'oinsa sun dace da yanayin halittu.
Yana buxe qofar kyakkyawan fata da kyautata zato, kuma yana yin hani kan cire fata da xebe tsammani.
Addini ne da ya tsayu akan gaskiya da nasiha, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Addini nasiha ne, Muaka ce: Ga wa Ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: Ga Allah, da littatafansa, da jagororin musulmai, da kuma talakawansu", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
            Babu wani alheri face yayi kira zuwa gare shi, babu kuma sharri face, ya tsawatar akansa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai yadda sha'anin ya ke, babu wani ba'annabe gabanina face haqqi ne akansa ya nusar da al'ummarsa ga alherin da ya sane musu shi, ya kuma gargaxe su sharrin da ya sanshi a gare su", Muslim ya ruwaito shi.
            Ya haxa kyawawa gaba xaya, ya kuma qunshi falaloli, waxanda su ke bada shaidar cikar ilimin Allah da hikimarsa, da kuma gaskiyar AnnabinSa, da gamewar manzancinSa.


ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,

            Addinin musulunci shi ne mafi tsarkin addinai, ta fiskar aqida da shari'a. Ya haxa tsakanin haqqoqin Mahalicci da halittu, ya ginu akan ginshiqai da tushe mai martabobi uku:
Musulunci da Imani da Ihsani.
Kuma kowace martaba tana da rukunnai, kuma da waxannan rukunnan ne ake samun gyaruwan zahiri da baxini.
kuma su kalmomin shahada biyu, sune rukunin musulunci wanda yafi girma. Kuma sune suke nuna musuluncin mutum, kuma sune hujjar samuwarsa, kuma a cikinsu ake samun ikhlasin aiki ga Allah, da yin koyi da AnnabinSa (صلى الله عليه وسلم).
            Ita kuma sallah ita ce qashin bayan addini, kuma ganawa tsakanin bawa da UbangijinSa.
            Kuma cikin zakkah akwai tsarkake dukiya, da rai, da dashen soyayya da jin-qai.
            Shi kuma azumi yana tsartace rayuka, kuma yana  tsarkake su.
            Hajji kuma an farlanta shi sau xaya a tsawon rayuwa, kuma da aikin hajji ne, cikar miqa-wuya ga Allah ke bayyana, da tabbatar da yin bauta a gare shi.

            Kuma daidaitar zahirin mutum tushensa, na farawa ne daga daidaitar baxini, Allah ta'alah ya ce: "Bai zama addini kawai ba, ku juyar da fiskokinku, ta wajen gabas da yamma, amma addini shi ne ga wanda ya yi Imani da Allah, da Ranar lahira, da Mala'iku da littatafai, da annabawa", [Baqara: 177].
            Kuma haqiqanin imani shi ne gaskata lamarin gaibu, tare da amintuwa da samun natsuwa, wanda kuma zance da aiki ke gaskata shi.
            Shi kuma Ihsani shi ne yin bauta wa Allah, da cikar ikhlasi da kiyaye Allah.
            Ginshiqin addinin musulunci, ko gininsa shi ne yin bauta wa Allah tare da kaxaita shi, kuma da wannan ne Allah ya turo dukkan annabawanSa da manzanninSa, Allah subhanahu ya ce: "Kuma haqiqa mun tayar da manzo a cikin kowace al'umma, da cewa: ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci bautar xagutu", [Nahl: 36].
            Kuma gayar da yake son cimmawa, ita ce: Ayi aiki cikin duk abinda Allah yak e sonsa, kuma ya yarda da shi.
            Ba a banbancewa tsakanin Annabawan Allah da ManzanninSa, kuma dukkansu masu gaskiya ne abun gaskatawa.
            Aqidar musulunci ita ce, aqidar da tafi inganci, tafi sauqi, tafi kawo gyara ga halittu, kuma tafi miqewa.
            Tana dacewa da hankula, da fixirori.
            Kuma tana zaburarwa kan yin zance da aiki.
            Kuma nesa take daga cukurkuxewa ko tatsuniyoyi. Ta kuvuta daga abubuwan da ba za su yiwu ba, da kuma tufka-da-warwara. Kuma tana dacewa da mai rauni da mai qarfi.
            Hukunce-hukuncensa babu wanda yafi su kyau, kuma aiki da su ke kawo gyara ga bayi da qasashe, Allah ta'alah ya ce: "Babu wanda yafi Allah kyan hukunci, ga mutane masu yaqini", [Ma'idah: 50].
            Babu ruhbananci a  cikin ibadonsa, kuma babu wahala.
            Yana yin umarni da ayyuka masu kyau, kuma yana kiran mutane kan riqo da manyan halaye xaukaka, kamar su gaskiya kyauta cika alkawari, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai tabbas an turo ni domin na cika kyawawan xabi'u"Ahmad ya ruwaito shi.
            Halal xinsa a bayyane suke, kuma haramun xinsa a bayyane suke.
            Yana halatta daxaxan abubuwa, kuma yana haramta dauxa. Kuma baya haramta wani abu, face ya buxe ninkin baninkinsa na alkhairi.
            Mua'amala a cikin addini ana gina ta ne akan gaskiya, da yafiya, da soyayya, da 'yan'uwantaka, da yin nasiha ga kowace halitta.

            Manufofinsa suna kai-komo ne cikin kiyaye wa mutane lalura biyar da buqatoci, da dukkan abinda akwai kamala a cikinsa da maslahar mutane.

            Shari'oinsa a cikinsu akwai kiyaye addini, da bada kariya ga ginshiqin addini, da yin hani kan jirkita wani abu cikin addini, ko canji. Sai musulunci ya yi umarnin a tsawatar ga masu juyawa baya, kuma ya tsananta wa 'yan bidi'a da masu qirqiro lamura cikin addini, kuma ya yi hani kan dukkan canfin da zai iya tava addinin musulmai, kamar rufa ido, da ilimin taurari, da makamantarsu daga cikin ayyukan shexanu.
            Saidai abinda zai bada tabbacin aiki da musulunci shine umarni da kyakkyawa, da kuma hani ga mummuna, kuma da hakan wannan al'ummar da kasance mafi alheri, kuma ta rabauta.
            Kuma cikin hukunce-hukuncen musulunci akwai abinda ke bada tabbacin kiyaye wanzuwar rayuka, wannan ya sanya musulunci ya yi umarni da yin aure, kuma ya kwaxaitar akansa, tare da kwaxaitarwa kan yawaita haihuwa da bada kulawa ga 'ya'ya.
            Kuma ya haramta kisa, da abubuwan da suke sabbaba shi, Allah ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya kashe mumini da ganganci, to sakamakonsa jahannama ne yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, kuma ya la'ance shi, kuma ya masa tanadin azaba mai girma", [Nisa'i: 93].
Kuma "Duk wanda ya kashe kafirin amana, ba zai shaqi qamshin Aljannah ba", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Kuma musulunci ya zo da abubuwan da su ke kiyaye wa mutum hankalinsa, kuma su tsarkake shi, ya kuma yi umarni kan nisantar abinda ke raunata kaifin hankali, ko ya gurgunta shi. Kuma kiyaye hankula da tsarkake su manufa ce ta shari'a, sai musulunci ya kiyaye su daga tatsuniyoyin jahiliyya, da varnace-barnacensu, ya kuma yi hani kan duk abinda zai  tauye hankali, ko ya karkatar da shi, Allah ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani lallai ne giya da caca da refu da kibiyoyin quri'a qazanta ne daga aikin shexan, sai ku nuisance shi, domin ku rabauta", [Ma'ida: 90].

            Kuma a cikin musulunci akwai batun gyaruwar dukiya da kiyaye ta, saboda ya halatta saye-da-sayarwa, kuma yharamta cin dukiya da varna, kamar riba da algus da kwace da sata.
Kuma musulunci ya halatta yalwatawa ga kai, ya kuma haramta varnatar da duliya da almubazzaranci.

Kuma ya kiyaye mutuncin mutane da nasabarsu, sai ya yi hani kan giba da annamimanci, da zunxe da nune, da sukar muqami ko nasaba, ya kuma haramta qazafi, ya la'anci ma'abutansa, kuma ya tsananta lamarin zina ya tsawatar kan kusantarsa, ya kuma yi hani kan hanyoyin da za su kai zuwa gare shi da sabuban zina, kamar cakuxuwar maza da mata, da fitar tsiraici, da kallon matan haram, da maganar alfasha, da sauraron kayan kaxe-kaxe.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,
Musulunci ya karrama xan-adam ya darajanta shi, ya bashi falala, "Kuma haqiqa mun karrama xiayn-adamu", [Isra'i: 70].
Kuma ya yi cikakken bayani kan haqqoqi, da ma'abutansu.
Kuma ya shar'anta wa bayi duk abinda zai gyara musu duniyarsu da lahirarsu; Sai musulunci ya yi umarni da:
Biyayya wa iyaye, da sada zumunci, da kula da zuriya, da yin tarbiyya a gare su, da kyautata wa makwabta, da masu rauni, da girmama babban mutum, da kuma jin-qan qananan yara, kuma musulunci ya karrama mace, ya kiyaye mata mutncinta, kuma ya sanya mata haqqoqi, ya tunkuxe mata zaluncin da jahiliyya ya mata.

Kuma yana daga rama wa kura aniyarta a musulunci, Son waxanda suka cirato mana wannan addinin na daga sahabbai, da tabi'ai.
Kuma yana daga kyawawan lamuran musulunci, ajiye masu girman shekaru a matsayarsu, sai musulunci ya yi kira cewa a girmama maluma, da komowa wurinsu.
Ya kuma yi umarnin nasiha ga majivinta lamura, da yin biyayya a gare su a cikin kyautatawa, da yin addu'a a gare su.
Kuma zai baiwa masu kare wannan addinin da wurarensa masu tsarki, ya basu matsayinsu.

Kuma mutane a cikin musulunci daidai suke; babu fifiko; saboda babu fifiko ga balarabe akan ba'ajame, sai da taqawa.
Addini ne na kyautatawa da tausasawa, yana kira zuwa ga jin-qan juna da taimako da soyayya, da haxin kai, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai Allah yana yin rahama ne ga bayinsa masu jin-qai", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Yana yin umarni da dukkan abinda zai haxe tsakanin zukatan mutane, kuma yana kira ga haxin kan halittu, kuma yana hani kan vata alaqoqi a tsakani, kuma yana tsawatarwa daga rabuwar kan bayi da samun savani a tsakaninsu.
Yana xauke duk abinda zai cutar yana tunkuxe shi. Kuma yana daga cikin manufofin musulunci: "Babu cuta babu cutarwa".
Kuma musulunci yana kiyaye fixirori daga dukkan abinda zai lalata su, na kamantacceniya, da munanan halayya, maqasqanta.
Kuma musulunci yana kira zuwa ga girmama qulle-qullen cinikayya da auratayya, da kuma cika su.


ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD,

Musulunci yana bada fa'idodin alkhairi ga ma'abutansa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Mutanen kowane gida; na larabawa ne, ko ajamawa ne, Allah ya nufe su da alkhairi, to sa shigar musu da musulunci", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma musulunci shine sababi na samun rayuwa daddaxa, da walwalar duniya da lahira, Allah ta'alah ya ce: "Wanda ya yi aiki na kwarai daga namiji da mace, alhalin yana mumini, to lallai za mu rayar da shi rayuwa daddaxa" [Nahl: 97].
Kuma a cikin musulunci akwai aminci da zaman lafiya, "Waxanda su ka yi Imani, kuma basu cakuxa imaninsu da zalunci ba, lallai waxancan suna da aminci, kuma su ne shiryayyu", [An'am: 82].

Kuma da musulunci ake samun hasken qirji, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Duk wanda Allah ya nufi shiryar da shi, sai ya buxa qirjinsa da musulunci", [An'am: 125].
Kuma musulunci haske ne ga ma'abutansa, Allah ta'alah ya ce: "Shin fa, wanda Allah ya buxa qirjinsa domin musulunci, sai ya kasance akan wani haske daga UbangijinSa (zai zama kamar waninsa?)" [Zumar: 22].
Kuam yana fitar da ma'abutansa daga duffai zuwa ga haske, Allah subhanahu ya ce: "Allah shi ne majivincin waxanda suka yi Imani yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske", [Baqara: 257].
Kuma a cikin musulunci akwai warware dukkan mushkilolin bayi, cikin addininsu da duniyarsu da aqidarsu da aikinsu da mu'amalolinsu. Musulunci tsarkaka ne da rabauta, "Haqiqa ya samu babban rabo, wanda ya musulunta, kuma aka azurta shi da biyan buqatu, sai kuma ya bashi wadatar zuci, ga abinda ya bashi", Muslim ya ruwaito shi.
Allah ta'alah ya ce: "Haqiqa, ya rabauta, wanda ya tsarkake ransa" [Shams: 9] .
Yana da xanxano da zaqi, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Ya xanxani daxin imani, wanda ya yarda da Allah, a matsayin Ubangiji, musulunci addini, annabi Muhammadu a matsayin manzo", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma musulunci garkuwa ne ga ma'abutansa da aminci, "Kuma lallai gushewar duniya yafi sauqi a wurin Allah, fiye da kashe mutum musulmi", Nasa'iy ya ruwaito shi.
Yana hukunta samun buwaya da qarfi, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma buwaya ta Allah, da ManzonSa da kuma muminai", [Munafiquna: 8].
Kuma Allah Mai taimakon musulmai ne, kuma yana tare da su, Allah ta'alah ya ce: "Lallai ne Allah yana bada kariya ga waxanda suka yi imani", [Hajji: 38].
Umar xan Alkhaxxab –رضي الله عنه- ya ce: "Mu wasu mutane ne da Allah ya bamu buwaya da musulunci, kuma duk lokacin da muka nemi buwaya ba da musulunci ba, sai Allah ya qasqantar da mu".

            Da musulunci ake tsira daga zunubai da laifuka, Allah ta'alah: "Ka ce: wa waxanda suka kafirta, za a gafarta musu abinda ya shuxe" [Anfal: 38]. Kuma y azo cikin hadisi cewa: "Musulunci yana rushe abinda ya kasance a gabaninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma duk wanda ya yi aiki a cikin musulunci, ba za a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacinsa na jahiliyya.
            A cikin musulunci akwai mafi alherin sakayya, wanda kuma yafi cika, saboda kyakkaywa xaya, ana bada sakamakonta ninki goma, har zuwa ninki xari bakwai (700).
Kuma ma'abuta musulunci ladansu ninkin na mutanen da suka rigaye su ne, Allah subhanahu ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da taqawa, kuma ku yi imani da ManzonSa, zai baku rabo biyu daga rahamarSa" [Hadid: 28].
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai Allah ba ya zaluntar mumini daidai da kyakkyawa xaya, za a bashi saboda ita a duniya, kuma a bashi sakamakonta a lahira", Muslim ya ruwaito shi.
            Kuma da musulunci ne ake samun shiga Aljannah, da kuma tsira daga faxawa wuta, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yadda sha'anin yak e, lallai babu mai shiga Aljannah face Rai musulma", Bukhariy da Muslim.
           
          BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
            Musulunci shi ne samun rabo ga halittu.
Kuma basu isa su wadatu da barinsa ba.
Kuma halayyar mutane ba za su tava gyaruwa ba, face da musulunci.
Kuma shine mafita daga fitintinu, da tsanani, da musibu, da vacin rai.
Kuma babu wanda zai nisanci musulunci, ko ya aibanta shi, ko yayi masa izgilanci, ko da ma'abutansa, face sakamakon jahiltarsa ga musuluncin.
Kuma xaukakar kowani musulmi yana cikin riqonsa ga musulunci, da jin izza da shi, da tabbatuwa akansa, da kiran halittu zuwa ga musulunci, da kwaxaitar da su akansa, da bayyanar da kyan musulunci cikin zance da aiki, da halayya, da salo ko manhajar rayuwa.
Kuma idan Allah ya yi nufin alkhairi ga bawansa, sai ya sanya shi ya zama mabuxin kowani alkhairi.  
A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Ya ku waxanda su ka yi imani, ku shiga cikin musulunci gaba xaya, kuma kada ku bi hanyoyin shexan, lallai shi a gare ku maqiyi ne mabayyani" [Baqara: 208].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …
             

HUXUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR Ya halitta halittu, kuma ya samar da duk wani kasantacce,
ALLAHU AKBAR Ya shar'anta addini, kuma ya kyautata shari'oi,
ALLAHU AKBAR Duk lokacin da sautuka suka xagu, domin neman rahamarSa,
ALLAHU AKBAR Duk lokacin da mahajjata suka zubar da hawaye
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU

Yabo ya tabbata ga Allah wanda ake yaba masa a kowani hali, da sifofin girma da kamala, wanda ake saninSa da qarin ni'imominSa da kuma bayar da falala,
Ina yin yabo a gare shi (سبحانه) wanda kuma shine abin yabo a kowani lokaci, da cikin kowani hali.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya; Ma'abucin girma da xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa, Ma'abucin gaskiyar zance.
Ya Allah, ka yi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, waxanda sune mafi alherin abokai, da iyalai.

Ya ku musulmai…
            Musulunci ya zo da lamarin shigar da farin ciki da jin daxi ga ma'abutansa. Kuma a lokacin idi, hakan yana maimaituwa a gare su. Sai ku yi godiya wa Allah akan ni'imominSa da falalolinSa,  kuma ku kiyayi abinda zai hukunta muku fushin Allah.
            Ranar idin layya, da yinin da ke biye da shi, sune mafi girman yini a wurin Allah, Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai mafi girman ranaku a wurin ta'alah, sune ranar layya, da kuma ranar tabbata (wato,a Mina)", Abu-daud ya ruwaito shi.
            Kuma mustahabbi ne a cikin kwanakin idi a yalwata ma kai, da iyalai, da abubuwa na halal.
            Yin layya kuma yana cikin ibadodi mafi daraja, a kwanakin idi, kuma lokacin fara yanka su yana faraway ne, daga bayan sallar idi, har zuwa faxuwar rana ta qarshe daga cikin kwanakin sallah (na Tashriq, wato 13/zulhijjah).
            Kuma rago ko akuya xaya yana isan mutum da iyalan gidansa. Raqumi da Saniya kuma, ga masu layya har mutane bakwai. Kuma mafificin kowani jinsi shine wanda yafi matsayi, kuma yafi tsadar kuxi.
            Sunna ita ce, mai yin layyan ya yanka dabbarsa da kansa, kuma bai halatta ya baiwa mahauci ladan fixansa daga dabbar layyar ba. Kuma bata isarwa ga layya; maras lafiyar dabbar da cutarta ya bayyana, haka kuma mai matsalar ido, wanda matsalarta ta bayyana, ko gurguwar da bata iya tafiya tare da masu lafiya. Ko ramammiyar da babu vargo a cikinta.
            Kuma a kwanakin idi, an shar'anta yin kabbarori bayan sallolin farilla, da kuma a kowani lokaci.        
>>> 
            Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
            Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.

                Bayin Allah!!!
                "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].

Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...