2019/02/18

LITTAFIN USULUS SALASA DA DALILANSU الأصول الثلاثة وأدلتها Wallafar Muhammadu dan Abdulwahhab







LITTAFIN
USULUS SALASA DA DALILANSU
الأصول الثلاثة وأدلتها


Wallafar
Sheikh Muhammadu dan Abdulwahhab (1115-1206H)


Tarjamar
Abubakar Hamza


Bismil Lahir Rahmanir Rahim
Ka sani –Allah ya yi maka rahama-
(Lallai yana wajaba akanmu mu koyi mas'aloli guda hudu)
Mas'alar farko: ILIMI, )Shine ilimin sanin Allah, da sanin AnnbinSaصلى الله عليه وسلم  da sanin addinin Musulunci, tare da dalilai).
Mas'ala ta biyu: AIKI DA ILIMIN.
Mas'ala ta Uku: YIN DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI).
Mas'ala ta hudu: Hakuri kan cutarwa a cikinsa).
Dalili akan abinda ya gabata shine fadinsa Madaukaki:"INA RANTSUWA DA ZAMANI * LALLAI MUTUM YANA CIKIN HASARA * FACE WADANDA SUKA YI IMANI, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN KWARAI, KUMA SUKA YI WA JUNA WASIYYA DA BIN GASKIYA, KUMA SUKA YI WASIYYA DA YIN HAKURI".
Shafi'iy –رحمه الله- ya ce: Da Allah bai saukar da wata hujja ga halittunsa ba, sai wannan sura, to da ta isar musu)(1).
 (Kuma Bukhariy –رحمه الله- ya ce: Babin da ya kunshi bayani kan: Ilimi shine gabanin zance da aiki).
 (Dalili akan haka shine fadin Allah Ta'alah: SAI, KA SANI, LALLAI BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA, FACE ALLAH, KUMA KA NEMI GAFARAR ZUNUBANKA) [Muhammadu: 19]. Sai Allah ya fara da batun ilimi, gabanin zance da aiki).


Ka sani, Allah ya yi maka rahama; Lallai yana wajaba akan kowane Musulmi namiji da mace, su koyi wadannan mas'alolin guda uku, kuma su yi aiki da su).
MAS'ALAR FARKO: Lallai Allah ya halitta mu, kuma ya azurta mu, kuma bai bar mu kara zube ba, sai ya aiko mana da wani Manzo; wanda ya masa biyayya ya shiga Aljannah, wanda kuma ya saba masa ya shiga wuta) (1).
Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki: "Lallai ne Mu, mun aiko wani Manzo zuwa gare ku, Mai shaida akanku, kamar yadda muka aika wani Manzo zuwa ga Fir'auna * Sai Fir'auna ya saba wa Manzon, saboda haka Muka kama shi, kamu mai tsanani" [Muzammil: 15-16].
MAS'ALA TA BIYU: Lallai ne Allah, baya yarda a hada shi da wani cikin bautarsa; Mala'ika ne makusanci, ko kuma Annabi Manzo).(Dalili akan haka kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
MAS'ALA TA UKU: Lallai duk wanda ya yi da'a ga Manzo, kuma ya yi tauhidin Allah, baya halatta a gare shi, ya so ko ya jibinci wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, koda kuwa dangin da yafi kusanci ne).
Dalili kan wannan mas'alar shine fadinSa madaukaki: "BAZA KA SAMU MUTANEN DA SUKA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE SUNA YIN SOYAYYA DA WANDA YA SABA WA ALLAH DA MANZONSA BA; KODA KUWA SUN KASANCE UBANNINSU NE, KO 'YA'YANSU, KO 'YAN'UWANSU, KO DANGINSU, WADANNAN ALLAH YA RUBUTA IMANI A CIKIN ZUKATANSU, KUMA YA KARFAFA SU DA WANI RUHI DAGA WURINSU, KUMA ZAI SHIGAR DA SU ALJANNONI WADANDA KORAMU KE GUDANA KARKASHINSU, SUNA MASU DAWWAMA A CIKINSU, ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUMA SUN YARDA DA SHI, WADANNAN SUNE KUNGIYAR ALLAH, KUMA LALLAI KUNGIYAR ALLAH SUNE MASU BABBAN RABO" [Mujadalah: 22]

Ka sani –Allah ya shiryad da kai zuwa ga biyayya a gare shi-, Lallai mikakken addini; tafarkin annabi Ibrahima, shine: Ka bauta wa Allah, shi kadai, kana mai tsantsanta addinni a gare shi, kuma da aikata haka, Allah ya umarci dukkan mutane, kuma ya halitta su don haka, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJANI BA, FACE SU BAUTA MIN".
Ma'anar: "SU BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi umarni da shi, shine, Tauhidi, wanda kuma shine: kadaita Allah a cikin bauta.
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi hani akansa, shine shirka, wanda kuma ita ce: Rokon wanin Allah tare da Allah.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KU BAUTA WA ALLAH, KADA KU HADA SHI DA KOWA" [Nisa'i: 36]

Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama wajibi mutum ya sansu?
Sai ka ce: Bawa, ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- (1).
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka?
Sai ka ce: Ubangijina, shine Allah, wanda ya ke rainona, kuma ya reni dukkan talikai, da ni'imominSa, kuma shine abin bautata, bani da wani abin bauta, idan ba shi ba.
Dalili akan haka shine fadinSa Madaukaki:
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI". Kuma dukkan abinda ba Allah ba halitta ne, Ni kuma daya ne daga cikin wadannan halittun.
Idan kuma aka ce maka: Da me ka san Ubangijinka?
Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa, Kuma daga cikin ayoyinsa, akwai dare da yini, da rana da wata, Daga cikin halittunsa, akwai sammai bakwai, da kassai bakwai, da abinda suke cikinsu da abinda suke cikinsu.
Kuma dalili shine fadinSa Madaukaki: "DAGA AYOYINSA AKWAI DARE DA YINI DA RANA DA WATA, KADA KU YI SUJJADA GA WATA KO RANA, KU YI SUJJADA GA ALLAN DA YA HALITTA SU, IDAN KUN KASANCE GA SHI KADAI KUKE YIN BAUTA".
Da fadinSa: "LALLAI NE UBANGIJINKU SHINE ALLAN DA YA HALITTA SAMMAI DA KASA, A CIKIN YINI GUDA SHIDA, SA'ANNAN YA DAIDAITA A SAMAN AL'ARSHI, YANA SHIGAR DA DARE YA RUFA YINI, YANA NEMANSA DA GAGGAWA, KUMA RANA DA WATA DA TAURARI HORARRU NE DA UMARNINSA, KUMA HALITTA TASA CE, UMARNI NASA NE, ALBARKAR ALLAH UBANGIJIN HALITTU TA BAYYANA".
Kuma Ubangiji shine abin bauta, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "YA KU MUTANE KU BAUTA WA UBANGIJINKU DA YA HALITTA KU, DA WADANDA SUKE GABANINKU, DOMIN KU SAMU KARIYA * WANDA YA SANYA MUKU KASA SHIMFIDA, SAMA KUMA GINI, KUMA YA SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA, SA'ANNAN YA FITAR DA ABINCI DAGA 'YA'YAN ITACE, DA SHI, SABODA KU, DON HAKA, KADA KU SANYA WA ALLAH KISHIYOYI, ALHALI KUNA SANE".
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya halicci wadannan ababen shine ya cancanci bauta".

Kuma nau'ukan ibada wadanda Allah ya yi umarni da su, Misalinsu shine: Musulunci, da Imani, da Ihsani, kuma daga cikin ibada akwai, addu'a, tsoro, fata, tawakkali, bayyana kwadayi, da tsoro, da khushu'i, da khashyah, da maida lamari ga Allah, da neman taimako, da neman tsari, da neman agaji, da yanka, da bakance, da abinda wannan ba daga cikin na'ukan ibada, wadanda Allah ya yi umarni da su, dukkansu ana yinsu ga Allah Ta'alah.
Dalili kuma shine: FadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
Kuma duk wanda ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah shi mushriki kafiri, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA DUK WANDA YA ROKI WANI ABIN BAUTAR TARE DA, BASHI DA HUJJA AKAN HAKA, TO LALLAI HISABINSA YANA WURIN UBANGIJINSA, KUMA LALLAI SHA'ANIN, KAFIRAI BASA SAMUN RABO".
Ya zo a cikin hadisi, "Addu'a itace ibada".
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA UBANGIJINKU YACE, KU ROKE NI, ZAN AMSA MUKU, LALLAI WADANDA SUKE GIRMAN KAI, BASA MIN BAUTA ZASU SHIGA JANNAMA, SUNA KASKANTATTU".
Dalili kan ibadar tsoro shine, fadinSa Madaukaki: "KUMA KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA IDAN KUN KASANCE MUMINAI"(1).
Dalilin ibadar fata kuma shine fadinSa Madaukaki: "DUK WANDA YA KASANCE YANA FATAN HADUWAR UBANGIJINSA, TO YA AIKATA AIKI NAGARI, KUMA KADA YA HADA WANI CIKIN BAUTAR UBANGIJINSA".
Dalilin Tawakkali shine fadinSa Madaukaki: "GA ALLAH NE, ZA KU DOGARA, IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Da fadinSa: "KUMA DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH, TO YA ISAR MASA"(1).
Dalilin ibadar kwadayi da fargaba da khushu'i, shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE, SU, SUN KASANCE SUNA YIN SAURIN AIKATA ALKHAIRORI, KUMA SUNA ROKONMU CIKIN KWADAYI DA FARGABA, KUMA SUN KASANCE A GARE MU MASU KHUSHU'I".
Dalilin ibadar tsoro: shine fadinSa Madaukaki: "KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA" (1).
Dalilin ibadar maida lamari ga Allah: shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU MAYAR DA LAMARI ZUWA GA ALLAH, KU MIKA WUYA A GARE SHI"(2).
Dalilin ibadar neman taimako: shine fadinSa Madaukaki: "A GARE KA MUKE YIN BAUTA, KUMA DAGA GARE KA MUKE NEMAN TAIMAKO".
Ya zo cikin hadisi: "Idan zaka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah"(3).
Dalilin ibadar neman tsari: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN SAFIYA".
Da "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN MUTANE"(4).
Dalilin ibadar neman agaji: shine fadinSa Madaukaki: "A YAYIN DA KUKE NEMAN AGAJIN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA MUKU"(5).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: LALLAI NE SALLATA DA YANKANA, DA RAYUWATA, DA MUTUWATA, NA ALLAH NE UBANGIJIN TALIKAI * BASHI DA ABOKIN TARAYYA".
Ya zo cikin sunnah: "Allah ya tsine wa wanda ya yi yanka, ga wanin Allah".
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "SUNA CIKA BAKANCE, KUMA SUNA TSORON YININ DA SHARRINSA KE YADUWA".

ASALI NA BIYU: SANIN ADDININ MUSULUNCI, DA DALILAI.
SHINE, Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta daga shirka da ma'abutansa.
Kuma addini martabobi uku ne, musulunci, da imani, da ihsani. Kuma kowace martaba tana da rukunnai.
Martabar farko: Musulunci.
Kuma rukunnan musulunci guda biyar ne:
Shaidawa babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bayar da zakkah, da azumin ramadhana, da hajjin dakin Allah mai alfarma
Dalilin Kalmar shahada shine fadinSa Madaukaki: "ALLAH YA SHAIDA CEWA: LALLAI NE BABU ABIN BAUTAWA DA CANCANTA FACE SHI, KUMA MALA'IKU DA MA'ABUTA ILIMI SUN SHAIDA, YANA TSAYE DA ADALCI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA FACE SHI, MABUWAYI MAI HIKIMA".
Kuma ma'anar kalmar (LA ILA ILLAL LAHU) shine babu abin bautawa da cancanta, face Allah, saboda "LA ILAHA" tana kore cancanta ne ga dukkan ababen da ake bauta musu, koma bayan Allah. "ILLAL LAHU" kuma, yana tabbatar da cancantar bautan ne ga Allah shi kadai; bashi da abokin tarayya cikin bautarsa, kamar yadda bashi da abokin tarayya cikin mulkinsa.
Kuma tafsirin (LA ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki: "KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA KAGI HALITTA TA, LALLAI SHINE ZAI SHIRYAR DA NI * KUMA YA SANYA (WANNAN MAGANAR) KALMA MAI WANZUWA, A CIKIN ZURIYARSA TSAMMANINSU SU KOMA DAGA BATA".
Da fadinSa: "KA CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU DA KU, KADA MU BAUTA WA KOWA, FACE ALLAH, KUMA KADA MU HADA KOME DA SHI, KUMA KADA SASHENMU YA RIKI SASHE, UBANGIJI, BAICIN ALLAH, IDAN KUMA SUKA BIJIRE, SAI KACE: KU YI SHAIDA CEWA, LALLAI NE MU MASU SALLAMAWA NE".
Dalili akan shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine fadinSa Madaukaki: "HAKIKA WANI IRIN MANZO DAGA CIKIN KAYUKANKU YA ZO MUKU, ABINDA KE WAHALAR DA KU YANA BUWAYARSA, KUMA MAI KWADAYI NE A GARE KU, GA MUMINAI KUMA MAI TAUSHI NE, MAI JIN KAI".
Ma'anar shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine: Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a bauta wa Allah sai da abinda wannan annabin ya kawo na shari'a.
Kuma dalili kan sallah da zakkah da kuma fassarar tauhidi shine fadinSa Madaukaki: "BA A UMARCE SU DA KOMAI BA, FACE BAUTA WA ALLAH SUNA MASU TSARKAKE ADDININSU A GARE SHI KUMA MASU KARKATA ZUWA ADDINI GASKIYA, KUMA SU TSAYAR DA SALLAH, SU BADA ZAKKAH, KUMA WANNAN SHINE ADDINI MIKAKKE"(1).
Kuma dalilin azumi shine fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA WADANDA KE GABANINKU, LA'ALLA KO ZA KU SAMU TAKAWA"(2).
Kuma dalilin hajji shine fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA WAJABTA WA MUTANE HAJJIN DAKINSA GA WANDA YA SAMU HANYAR ZUWA GARE SHI, KUMA WANDA YA KAFIRCE, TO LALLAI ALLAH YA WADATA DAGA TALIKAI".

MARTABA TA BIYU: ITACE; IMANI;
Kuma imani sifofi ko rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU, Kuma mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya, Kuma kunya reshe ne na imani.
Kuma rukunnan imani guda shida ne, kamar yadda ya zo cikin hadisi, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittatafanSa, da ManzanninSa, da Ranar karshe, kuma ka yi imani da kaddara na alkhairinsa da sharrinsa".
Kuma dalili akan wadannan rukunnan guda shida, fadinSa Madaukaki: "BA KAWAI SHINE ADDINI BA, KU JUYAR DA FISKOKINKU, WAJEN GABAS KO YAMMA BA, AMMA ADDINI SHINE GA WANDA YA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE, DA MALA'IKU, DA LITTATAFAI, DA ANNABAWA".

Kuma dalilin kaddara FadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MU, KOWANE ABU MUN HALICCE SHI DA KADDARA".

MARTABA TA UKU: IHSANI (KYAUTATA BAUTA)
Rukunnansa, Yana da rukuni daya ne, kuma shine ka kyautata bautar Allah, kamar kana ganinsa, domin idan kai baka ganinsa, ai shi yana ganinka; dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE ALLAH YANA TARE DA MASU TAKAWA, WADANNAN DA SUNE MASU KYAUTATA BAUTA".
Da fadinSa: "SAI KA YI TAWAKKALI GA MABUWAYI MAI RAHAMA * WANDA KE GANINKA A LOKACINDA KAKE TSAYUWAR SALLAH * DA JUJJUYAWARKA A CIKIN MASU SUJJADA * LALLAI NE SHI, SHINE MAI JI MASANI".
Da fadinSa: "BA ZA KA KASANCE CIKIN WANI SHA'ANI BA, KO KA KARANTA KUR'ANI, KO KU AIKATA WANI AIKI, FACE MUN KASANCE MUNA HALARCE, A LOKACIN DA KUKE KUKKUTSAWA A CIKINSA".

Dalili kuma daga cikin sunnah, shine shahararren hadisin mala'ika Jibrila, wanda aka ruwaito shi daga Umar –رضي الله عنه-ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, Sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, kuma babu wani daga cikinmu da ya sanshi, har ya zauna kusa da Annabi –صلى الله عليه وسلم-; Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma dora tafukansa akan cinyoyinsa, yace: Ya Muhammadu! Bani labari akan Musulunci?  Yace: Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, kuma ka tsayar da salla, ka bada zakka, ka yi azumin watan ramadana, ka yi hajjin daki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi. Sai yace: ka yi gaskiya, Sai muka yi mamakinsa; yana tambayarsa kuma yana gaskata shi.
Sai yace: ka bani labari akan imani? Yace: Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi imani da kaddara; na alkhairinsa dana sharrinsa.
Yace: To ka bani labari akan "ihsani"? Sai yace:Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, to shi yana ganinka.
Yace: To ka bani labari akan kiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba.  Sai yace: To ka bani labari akan alamominta? Sai yace: Baiwa zata haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa takalma, tsiraru, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace: Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani lokaci, Sa'annan  sai yace: Ya kai Umar, shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai yace: Allah ne da manzonsa suka sani.
Yace: Lallai shi mala'ika Jibrilu ne, ya zo muku, domin ya karantar da ku addininku".

ASALI NA UKU: SANIN ANNABINKU MUHAMMADU –صلى الله عليه وسلم-
Shine annabi: Muhammadu dan Abdullahi bn Abdulmuddalib, dan Hashim, Hashim kuma daga kabilar Kuraishawa ne, su kuma Kuraishawa daga al'ummar larabawa suke, larabawa kuma daga zurriyar annabi Isma'il dan Ibrahimul Khalil, Allah ya yi karin mafificin salati da sallama akansa, da kuma Annabinmu.
Ya rasu, yana da shekaru sittin da uku, shekaru arba'in gabanin annabta, shekaru ashirin da uku yana annabi manzo.
An bashi annabta ne da saukar "Ikra'a", an kuma turo shi da manzanci da saukar "Ya, ayyuhal muddasir".
Garinsa (na haifuwa) shine Makkah, ya kuma yi hijira zuwa ga Madina.
Allah ya turo shi da gargadi daga shirka, kuma domin ya yi kira zuwa ga Tauhidi;
Dalili kuma shine, fadinSa Madaukaki: "YA WANDA YA LULLUBA DA MAYAFI * KA TASHI DOMIN KA YI GARGADI * KUMA UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI * KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU * GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU * KADA KA YI KYAUTA KANA NEMAN KARI *  KUMA SABODA UBANGIJINKA, SAI KA YI HAKURI".
Ma'anar: "KA TASHI DOMIN KA YI GARGADI" wato yayi gargadi akan shirka, ya kuma kira zuwa ga tauhidi.
"KUMA UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI", Ma'ana: ka girmama shi da tauhidi.
"KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU", ma'ana: ka tsarkake ayyukanka daga shirka.
"GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU", Rujz: gumaka, kwaurace musu: shine barinsu da barranta daga gare su, da ma'abutansu.
Ya dauki shekaru goma yana yin da'awa akan tauhidi. Kuma bayan shekaru goma sai aka yi mi'iraji da shi zuwa sama, sai aka farlanta masa salloli biyar, kuma ya yi salla a garin Makkah tsawon shekaru uku, bayansu kuma aka umarce shi da yin hijira, zuwa garin Madina.

Hijira: ita ce: kaura daga garin shirka, zuwa garin musulunci.
Kuma hijira farilla ne, ga wannan al'ummar, daga garin shirka, zuwa garin musulunci, kuma aiki da ita yana nan, har zuwa tashin kiyama.
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI WADANNAN DA MALA'IKU SUKA KARBI RAYUKANSU, ALHALIN SUNA MASU ZALUNTAR KANSU, SU KAN CE MUSU: A CIKIN ME KUKE? SAI SUKA CE: MUN KASANCE WADANDA AKA RAUNANA A CIKIN KASA, SUKA CE: ASHE KASAR ALLAH BATA KASANCE MAYALWACIYA BA? DOMIN KU YI HIJIRA GARE TA, TO WADANNAN MAKOMARSU JAHANNAMA CE, KUMA TA MUNANA TA ZAMA MAKOMA * IN BANDA MASU RAUNI DAGA MAZA DA MATA DA YARA, WADANDA BASU IYA YIN WATA DABARA, KUMA BASU SHIRYUWA GA HANYA * TO WADANNAN AKWAI TSAMMANIN ALLAH YA YAFE LAIFI DAGA GARE SU, KUMA ALLAH YA KASANCE MAI YAFEWA NE MAI GAFARA".
Da kuma fainSa Madaukaki: "YA BAYINA, WADANDA SUKA YI IMANI, LALLAI NE KASATA MAI YALWA CE, SABODA HAKA KU BAUTA MINI".
Bagawiy –رحمه الله- ya ce: "Sababin saukar wannan ayar akan musulmin da suke garin Makkah ne, wadanda basu yi hijira ba ne, sai Allah ya kira su da sunan imani".
Dalili kuma akan hijira daga cikin hadisai, akwai fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Hijira bata yankewa har sai karban tuba ya yanke, kuma tuba bata yankewa har sai rana ta fudo daga mafadarta".
Yayin da ya zauna a garin Madina sai aka umarce shi da yin aiki da sauran shari'oi, misalin zakkah(1), da azumi, da hajji, da jihadi, da kiran salla, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da wasun wadannan daga cikin shari'oin musulunci.
Ya dauki shekaru goma akan haka, bayan haka kuma sai ya rasu, salatin Allah da sallamarsa su kara tabbata a gare shi(2).
Addininsa kuma mai wanzuwa ne, wannan shine addininsa, babu wani alkhairi face ya nusar da al'umma a gare shi, kuma babu wani sharri face ya tsawatar mata akansa.
Kuma alkhairin da ya nuna wa al'umma, shine Tauhidi da dukkan abinda Allah yake sonsa, kuma ya yarda da shi.
Sharrin kuma da ya tsawatar akansa, shine: Shirka da dukkan abinda Allah baya sonsa, kuma ya ke kinsa.
Allah ya aike shi da Manzanci zuwa ga mutane gaba daya, kuma ya farlanta yin da'a a gare shi, akan dukkan aljanu da mutane; Dalili kuma shine FadinSa Madaukaki: "KA CE: YA KU MUTANE, LALLAI NE NI 'DAN AIKAN ALLAH NE ZUWA GARE KU GABA DAYA".
Kuma Allah ya cika addini, da shi, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "A YAU NA CIKA MUKU ADDININKU, KUMA NA CIKE NI'IMATA AKANKU, KUMA NA YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI".
Kuma dalili akan mutuwarsa –صلى الله عليه وسلم-: "LALLAI NE KAI MAI MUTUWA NE, KUMA LALLAI SU MASU MUTUWA NE * SA'ANNAN KU, A RANAR KIYAMA, A WURIN UBANGIJINKU, MASU YIN HUSUMA NE".
Kuma Mutane idan suka mutu za a tayar su, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "DAGA KASA MUKA HALITTA KU, KUMA ZUWA CIKINTA ZA MU MAYAR DA KU, KUMA DAGA GARE TA ZA MU FITAR DA KU, A KARO NA GABA".
Da fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA TSIRAR DA KU DAGA KASA TSIRARWA, SA'ANNAN ZAI MAYAR DA KU CIKINTA, YA KUMA SAKE FITAR DA KU FITARWA".
Kuma bayan an tayar da su za a musu hisabi, kuma za a sakanta musu da ayyukansu, Dalili kuma akan haka shine fadinSa Madaukaki: "NA ALLAH NE, DUKKAN ABINDA KE CIKIN SAMMAI DA KASSAI, ZAI SAKANTA GA WADANDA SUKA MUNANA AIKI DA ABINDA SUKA AIKATA, KUMA YA SAKANTA WA WADANDA SUKA KYAUTATA DA ALJANNAH"(1).
Duk kuma wanda ya karyata lamarin sake tayar da mutane, to ya kafirta, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "WADANDA SUKA KAFIRTA SUN RIYA CEWA, BA ZA A TAYAR DA SU BA, KA CE, A'A, INA RANTSUWA DA UBANGIJINA, LALLAI NE ZA A TAYAR DA KU, SA'ANNAN A BAKU LABARIN ABINDA KUKA AIKATA, KUMA WANNAN GA ALLAH ABU NE MAI SAUKI"(2).
Kuma Allah ya turo Manzanni gaba dayansu, suna yin albishir, suna gargadi, Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki: "MANZANNI MASU ALBISHIR DA GARGADI".
Na farkonsu shine annabi Nuhu –عليه السلام-, Na karshensu kuma, annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma shine cika-makin annabawa.
Dalili akan farkon manzanni shine annabi Nuhu –عليه السلام- shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MUN YI WAHAYI ZUWA GARE KA, KAMAR YADDA MUKA YI WAHAYI GA NUHU DA ANNABAWAN DA KE BAYANSA".
Kuma Allah ya farlanta wa dukkan bayi su kafirce wa dagutu, su yi imani da Allah, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: Dagutu, shine dukkan wanda bawa ya wuce iyakarsa, na ababen bauta, ko wadanda ake bi, ko wadanda ake musu da'a.
Kuma kowace al'ummar da Allah ya tura mata manzo, tun daga lokacin annabi Nuhu har zuwa annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- yana umartarsu ne da ibadar Allah; shi kadai, kuma yana hana su bauta wa dagutu, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA HAKIKA MUN TAYAR MANZO GA KOWACE AL'UMMA; DA CEWAR; KU YI BAUTAR ALLAH, KU NISANCI DAGUTU".
Dagutu suna da yawa, amma manyansu guda biyar ne; Iblisu –Allah ya la'ance shi-, da wanda aka masa bauta alhalin ya yarda, da wanda ya kira mutane zuwa ga bauta a gare shi, da wanda ya riya sanin wani abu na ilimin gaibu, da wanda yay i hukunci ba da abinda Allah ya saukar ba, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "BABU TILASTAWA A CIKIN ADDINI, HAKIKA SHIRIYA TA BAYYANA DAGA BATA, DON HAKA, WANDA YA KAFIRTA DA 'DAGUTU, KUMA YA YI IMANI DA ALLAH, TO HAKIKA, YA YI RIKO DA IGAYA AMINTACCIYA".
Wannan kuma shine ma'anar (LA ILAHA ILLAL LAHU).
Kuma ya zo a cikin hadisi "Kan wannan lamari, shine musulunci, kuma kashin bayansa shine salla, kuma tozon kololuwarsa shine jihadi fiysabillahi".

4 comments:

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...