2016/09/29

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A 30 ZULHIJJAH 1437H Daidai da 30 SATUMBA 2016M ta DR. ABDULMUHSIN dAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 30/ZULHIJJAH/1437H
Daidai da 30 /SATUMBA / 2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
FALALAR HAXIN KAI DA NA ZUKATA
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a ta 28 zulhijjah, 1437H, mai taken: FALALAR HAXIN KAI DA NA ZUKATA, Wanda a cikinta ya tattauna, kan haxin kai, da na zukata, da riqo da littafi da Sunnah, Yana mai bayyana falalarsa, da girman tasirinsa, da kasancewarsa sababi ne na tsiran wannan al'ummar daga fitintinu, yana kuma tsawatarwa kan rarrabuwar kai da savani da jayayya; saboda abinda su ke sabbabawa na saukar jarabawa da bala'oi ga musulmai, da rarrabuwar kalmarsu, da kecewar sahunsu.

بسم الله الرحمن الرحيم

HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

       Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, saboda taqawar Allah ita ce hanyar shiriya, sava mata kuma shi ne hanyar tavewa.

       Ya ku musulmai …
            Allah ya halicci bayi, ya azurta su, yana kuma jujjuya lamuransu.
kuma Allah ya yi rahama ga bayi da addinin musulunci, wanda a cikinsa gyaruwar duniyar bayi da lahirarsu ta ke, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya bi shiriyata, to ba zai vata ba" –wato: a duniya- "kuma ba zai tave ba" wato: a lahira-[Xaha: 123 ].

            Addini ne mai girma (wato: muslunci), wanda yana daga cikin muhimman ginshiqansa da ababen da ya kevanta da su, da qa'idodinsa masu girma, KWAXAITARWARSA AKAN TATTARA MA'ABUTANSA KAN GASKIYA, DA XINKE TSAKANIN ZUKATANSU, kuma wannan (wato, haxin kai) ni'ima ce mai girma, wanda Allah ya yi baiwa da ita ga bayinsa, Allah yana cewa: "Shi ne wanda ya qarfafe ka da nasararSa, da kuma muminai * Kuma ya xinke tsakanin zukatansu, da za ka ciyar da abinda ke cikin qasa gabaxaya, da baka xinke tsakaninsu ba, saidai Allah Shi ya xinke tsakaninsu, lallai ne shi Mabuwayi ne Mai hikima[Anfal: 62-63].
            Kuma waxannan da su ka tattara akan kalmar musulunci, waxanda su ke bin Alqur'ani da Sunnah su ne muminai na gaskiya, koda kuwa masu sava musu sun  yawaita ko sun yi qarfi.
            Kuma haqiqa manzanni sun haxu (ittifaqi) akan tattara al'ummominsu a bisa gaskiya, Sai su ka yi umurnin a tsayar da musulunci, da tsayuwa akansa ta fiskar ilimi da aiki, da aqida da hali, da tattaruwa akan haka, Allah yana cewa: "Ya shar'anta addini a gare ku, irin abinda ya yi wasici ga Nuhu, da abinda mu ka yi wahayi izuwa gare ka, da abinda mu ka yi wasici ga Ibrahima da Musa da Isa; cewa: Ku tsayar da addini, kuma kada ku rarraba a cikinsa[Shura: 13].
Dukkan Annabawa sun yi kira izuwa ga a bauta wa Allah shi kaxai, tare da kwaxaitar da mutanensu, akan haxuwa kan haka, Sai kowani Annabi ya ce wa al'ummarsa: "Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautan wanda ba shi ba"
[A'araf: 59, 65, 73, 85, Hud: 50, 61, 84, Muminun: 23  ].
Kuma shima Annabi (صلى الله عليه وسلم) an turo shi ga mutanen da suke rarrabe cikin addininsu, suna masu jayayya ga junansu, a cikin lamuran duniyarsu, "Kowace qungiya da abinda ke wurinsu, masu alfahari ne" [Muminun: 53, Rum: 32]. Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi hani, kan yin koyi da su, sannan ya yi umurni da a haxa kai. Sai lamarin addini ya tsayu, jahiliyya kuma ta kau. Sai kuma lamuran mutane su ka gyaru sakamakon tsayuwarsu akan addini.

Mutane maslaharsu ta duniya da ta lahira ba za ta cika ba, face akan tattaruwa akan gangariyan musulunci, da yin taimakakkeniya, da agaza wa juna.
            Kuma saboda muhimmanci, ko wajabcin riqo da musulunci, da tattaruwan mutane akansa, ya kasance ginshiqi da manzanci ya yi ittifaqi akansa, kuma ya zama manufa mai girma a cikin dukkan shari'o'i.
Kuma (haxin kai) abu ne na dole a rayuwar duniya, wanda rayuwa ba za ta gyaru ba sai da shi, kuma ba za a samu aminci da zaman lafiya ba, matuqar babu haxin kai.
Kuma lamuran bayi a tsakaninsu ba za su cika ba, kuma maslahohinsu ba za su samu ba, face da shi.
Kuma shi ne hanyar da al'umma za ta dawo da matsayinta, ta kuma xinke varakarta, ta samu buwaya, da kariya ga al'ummai.
Kuma haxin kai shi ne hanyar da ta fi zama daidai wajen tabbatar da burace-buracen musulmai, da tunkuxe raxaxi a gare su.
Kuma shi ne mahaxa ta gaskiya da ta kulla tsakanin musulmai.
Kuma da shi ake iya kare addinin musulunci.

            Kuma haxuwa akan addini na gaskiya da tara zukata akansa, wajibi ne na shari'a akan al'ummah, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba" [Ali-Imraan: 103].
Ibnu-Jarir  -رحمه الله- ya ce: Yana nufin: "Ku yi riqo da addinin Allah, wanda ya umurce ku da shi, da kuma alkawarinSa da ya yi da ku, a cikin littafinsa, na haxe tsakanin zukata da taruwa akan kalmar gaskiya, da miqa wuya ga lamari ko umurnin Allah".
           
            Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada muhimmanci ga wannan lamarin mafi tsananin bada muhimmanci, sai ya bayyana shi ga sahabbansa, da zance, ya kuma kusanto da shi ga kwakwalensu da yin zane a qasa, domin wannan lamari mai muhimmanci ya tabbatu a cikin kwakwalensu, Abdullah ibn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zana mana wani zane, sannan ya ce: Wannan shi ne hanyar Allah! Sa'annan sai ya zana wasu zanen ta dama da shi da hagu, sa'annan ya ce: Waxannan hanyoyi ne mabanbanta, akan kowace hanya daga cikinsu akwai shexanin da ya ke yin kira zuwa gare ta", Sa'annan ya karanta: "Kuma lallai wannan hanyata ce miqaqqiya, sai ku bi ta, kada ku bi qananan hanyoyi, sai su kautar da ku daga hanyar Allah [An'am: 153]. Ahmad ya ruwaito shi.

Kuma Allah ya tunatar da wannan al'ummar, da wannan ginshiqi mai girma a inda ya ke cewa: "Lallai wannan al'ummarku ce al'umma guda xaya, Ni kuma nine Ubangijinku, sai ku bauta mini" [anbiya'i : 92].
            Cikin haxuwar mutane akan shiriya akwai saukar rahama, don haka; yana daga cikin sifofin muminai kasancewarsu masu jin qai ga junansu.
Kuma lallai haxin kai ni'ima ce da Allah ke yin baiwarta ga bayinsa, Allah ya ce: "Kuma ku ambaci ni'imar Allah akanku, a yayin da ku ka kasance maqiya, sai ya daidata tsakanin zukatanku, sai kuka wayi gari da ni'imarsa kuna 'yan'uwa", [Ali-Imran: 103].
            Kuma Allah ya umurci muminai da haxin kai, ya hane su savani da rarrabuwar kai, Kuma ya basu labarin cewa, lallai ne waxanda su ka rigaye su, sun halaka ne da yin jayayya ko husuma a cikin addinin Allah, Allah (سبحانه) yana cewa:  "Lallai waxanda su ka rarrabe addininsu, su ka zama qungiya-qungiya, baka cikinsu a wani abu, kuma lallai lamarinsu yana ga Allah, sa'annan ya basu labari akan abinda su ke aikatawa[An'am: 159].

            Cikin lazimtar jama'ar musulmai akwai kariya da tsira daga fitintinu, kuma da aikata haka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi wasici ga musulmai idan fitintinu su ka sauka, Huzaifat –رضي الله عنه- ya ce: Shin bayan wannan alkhairin akwai sharri? Sai Annabi –tsira da aminci su qara tabbata a gare shi- ya ce: ya ce: "E, Masu kira ne akan qofofin jahannama; Duk wanda ya amsa musu zuwa gare ta, sai su jefa shi a cikinta".  Sai Huzaifat –رضي الله عنه- ya ce: "Da me ka ke umurtata idan hakan ya riske ni? Sai Annabi ya ce: Ka lazimci jama'ar musulmai da shugabansu. Muslim ya ruwaito shi.

            Yana daga cikin nasiha ga musulmai: Lazimtar jama'arsu ta hanyar yin muwafaqa a gare su, cikin ingantacciyar aqida, da aiki na kwarai, da yin aiki domin daidaita zukatansu,
kuma wanda ya fi mutane tsarkin zuciya shi ne wanda ya fi su lazimtar gaskiya, tare da jama'ar musulmai, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sifofi uku, zuciyar mutum musulmi bata xaukar gillu ko qyashi akansu, ikhlasin aiki ga Allah, da nasiha ga jagororin musulmai, da lazimtar jama'ar musulmai, domin addu'oinsu suna game wanda ke cikinsu".
Ma'anar wannan shi ne, lallai addu'ar musulmai ta kewaye su, kuma tana kare su, daga kaidin shexan, da kuma vacewa –wannan haidsin Tirmiziy ne ya ruwaito.

            Haxin kai, yana daga abubuwan da Allah ya yarje wa bayinsa, shi kuma bawa yana yarda wa kansa, da abinda Allah ya yarda a gare shi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai ne Allah, yana yarje muku abubuwa uku, kuma yana qiye muku abubuwa guda uku, Ya yarda muku, ku bauta masa kada ku haxa shi da kowa, kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba…". Muslim ya ruwaito shi.
Sheikh Muhammadu bn Abdulwahhab –رحمه الله- ya ce: "Wata matsala bata auku a cikin addinin mutane ko duniyarsu ba, sai da sababin sakaci akan waxannan abubuwan guda uku, ko sashinsu".

            Masu riqo da musulunci daga mavuvvugarsa tatacce; wato: Alqur'ani da Sunnah, za su ci-gaba da wanzuwa, suna waxanda ake taimakonsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wasu vangare na al'ummata ba za su gushe ba, akan gaskiya, suna maxaukaka, Wanda zai qi taimaka musu ba zai cutar da su ba, har sai lamarin Allah ya zo alhalin suna kan haka" . Muslim ya ruwaito shi.
            Kuma su ne suka fi dukkan mutane rabauta da samun haxewar zukata, da jin qan juna, da fahimtar juna a tsakaninsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma muminai maza da muminai mata sashinsu majivinta sashi ne, suna yin umurni dakyakkyawa, suna yin hani ga mummuna, suna tsayar da sallah, suna bada zakkah, suna yi biyayya ga Allah da manzonSa, Waxannan lallai Allah zai yi musu rahama, Lallai ne Allah Mabuwani ne Mai hikima" [Tauba: 71].

            Kuma tsakaitawa shine salo ko manhajinsu, basa wuce iyaka, kuma basa gajartawa, basa yin guluwwi, kuma basa yin jafa'i.
            Kuma su ne masu tsira daga bidi'oi da vata, da rarrabuwar kai, a duniya.
            Haka daga halaka, da kuma azaba a lahira. Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma lallai ne wannan addinin za su rarraba izuwa qungiyoyi saba'in da uku, saba'in da biyu suna cikin wuta, xayar kuma tana cikin aljannah, wanda kuma ita ce: Jama'a". Abu-dawud ya ruwaito shi.
A wurin Alhakim kuma, An ce wa Annabi (صلى اللع عليه وسلم) wacece guda xayan? Sai ya ce: "Abinda Ni na kasance akansa a yau, da sahabbaina"
            Kuma saboda tabbatarwar da Allah ya yi musu, su suna tabbace akan gaskiya, kuma babu wani banbanci ko savani cikin manhajinsu, koda an samu tsawon shekaru, kuma duk wanda ya leqa littatafansu da aqidunsu, kuma ya san tarihinsu, tun daga wanda suka yi rigaye daga cikinsu, da wadanda suka riski na farkon, zai samu cewa, duka suna kan turba ne guda xaya, kai ka ce aqidunsu da zantukansu sun fita ne daga zuciya guda xaya, aiyukansu kuma kamar sun kasance daga jiki guda xaya, savanin abinda wasunsu su ke a kai, domin ('yan bidi'a) su kan kasance hanyoyinsu nesa da ilimi ko dalili, hujjojinsu kuma suna da rauni (basu da qarfi), aqidunsu kuma ko zantukansu suna hannun riga da juna; saboda duk wanda ya bar gaskiya, to sai lamarinsa ya jirkice, addininsa kuma ya caccakuxe, Allah (سبحانه) yana cewa: "Lallai sun qaryata gaskiya ne, a lokacin da ta zo musu, don haka, su suna cikin wani al'amari da ke cakuxe" [Qaf: 5 ].

A ranar qiyama kuma masu bin Alqur'ani da sunna za su rabauta, Allah (تعالى) yana cewa: "Ranar da wasu fiskoki za su yi hasken fari, wasu fiskokin kuma su yi baqi, Amma waxannan da fiskokinsu su ka yi baqi, Shin, kun kafirce bayan imaninku, to ku xanxani azaba saboda abinda kuka kasance ku ke yi na kafirci * Amma su kuma waxannan da fiskokinsu suka haskaka, to suna cikin rahamar Allah, su a cikinta za su dawwama" [Ali-imran: 106-107].
Abdullahi xan Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Fiskokin Ahlus-sunnah wal jama'a za su yi haske, ma'abuta rarrabuwar kai da savani kuma, fiskokinsu za su yi baqi".

            BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
            Ya ishi, lamarin haxin kai, xaukaka, kasancewar hannun Allah yana kan jama'a, kuma Allah ya yarda da haxin kai, kuma a cikinsa akwai gyaruwan lamura, da alheri.
A cikin rarrabuwar kai kuma, akwai lalacewan lamura da watsewarsa da halaka.
            Shi kuma mai hankali, ba zai yi sakaci kan bin jama'ar da ta ke bin Alqur'ani da Sunnah ba, koda kuwa ya hangi wasu maslahohi na qashin-kai cikin barin binta, saboda za su kasance maslahohi ne da basu su ka fi muhimmanci ba, ko maslahohi. Kuma zai yi farin ciki ne da shiryarwar da Allah ya masa izuwa ga wannan addinin miqaqqe, sai kuma ya lazimci jama'ar musulmai, ya kuma riqa da'awar waninsa zuwa ga hakan.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Duk wanda ya sava wa Manzo, bayan hujjoji sun bayyana masa, kuma ya bi turbar da ba ita ce ta muminai ba, za mu jivinta masa abinda ya jivinta, kuma mu shigar da shi jahannama, kuma lallai makoma ta yi muni" [Nisa'i: 115].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA, ya kuma amfanar da ni, da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima, Ina faxan maganata wannan, kuma ina neman gafara wa ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya kasance Mai gafara Mai rahama.
             

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya;  Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
            "Sunnah" ana gwama ambatonta da "jama'a ko haxin kai",
            Masu yin riqo da sunna kuma sune ma'abuta jama'a, kuma tafarkinsu guda xaya ne; wanda shine:
Kaxaita Allah cikin bauta, da ikhlasin addini a gare shi.
Da tabbatar wa Allah sunayensa da sifofinsa, kamar yadda Allah ya siffanta kansa da su, a cikin littafinsa, kuma Manzonsa (صلى الله عليه وسلم) ya siffanta shi da shi, ba tare da canza wani abu, ko korewa ba, kuma ba tare da faxin yanayin sifa, ko misaltawa ba.
Da kuma tabbatar da rukunin imani da qaddara, ta hanyar yin imani da kasancewar Allah ya siffanta da sifar ilimi mai rigaye, ga duk abinda zai kasance, kuma ya rubuta shi a lauhul mahfuz, kuma Allah ya ke halittarsa, kuma babu wani abu da zai kasance a duniya face, idan Allah ya nufe shi.
Kuma yana cikin MANHAJIN AHLUS-SUNNAH: Tabbatar da bin Annabi (صلى الله عليه وسلم) da bin shiriyar sahabbansa –رضي الله عنهم-, da koyi da magabatan wannan al'ummar da bin shiriyarsu.
            Tare da gaskiyar riqo da Alqur'ani da Sunnah.
            Da neman sani cikin Alqur'ani da Sunnah, da yin aiki da abinda ke cikinsu.
            Kuma haxuwa kan riqo ko aiki da littafin Allah da sunnar Manzo ginshiqi ne daga ginshiqan Ahlussunnah wal Jama'ah; saboda (أهل السنة والجماعة) suna bin littafin Allah ne, da sunnar Manzo, kuma suna nisantar fanxarewa, da savani ko rarrabuwa.
Kuma suna kwaxayin ganin haxin kan musulmai gabaxaya, amma ba tare da an tozarta wata gaskiya ba, ta hanyar voye ta, ko cakuxa ta da varna.
Kuma suna mu'amalantar waxanda suka sava musu, da adalci, da rahama, ba tare da qetare iyaka ko zalunci ba.
                       
Kuma  wanda aka azurta shi da ilimi mai amfani, da kuma aiki na kwarai, sai kuma ya nisanci shubuhohi da sha'awowi, to wannan ya kasance daga cikin bayin Allah masu rabauta.

            Sannan ku sani; Lallai  Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa …
Sai yace, a cikin mafi kyan littafin da ya saukar: "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
            Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.
            Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
            Ya Allah Ka sanya qasashensu su zama wurin aminci da zaman lafiya, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka haxa kalmarsu akan gaskiya da shiriya, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga shiriyarka, ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Kuma ka datar da xaukacin jagororin lamuran musulmai zuwa ga aiki da littafinka, da yin hukunci da shari'arka, Ya ma'abucin girma da karramawa.
            Ya Allah! Ka taimaki rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka taimake su akan maqiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi.
            "Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
            Ya Allah Ka karva wa mahajjata hajjinsu, ka mayar da su, garurrukansu, suna kuvutattu, masu riba, Ya ma'abucin girma da karramawa.

       Bayin Allah!!!
            "Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.

2016/09/16

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) 15 ZULHIJJAH 1437H Daidai da 16 SATUMBA 2016M ta ABDULBARIY AS-SUBAITIY








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 15/ZULHIJJAH/1437H
Daidai da 16/SATUMBA/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KANKARE ZUNUBI A LOKACIN HAJJI
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a, 14 zulhijjah, 1437H, mai taken: KANKARE ZUNUBI A LOKACIN HAJJI , Wanda kuma a cikinta ya tattauna lokacin hajji, wanda aiyukansa su ka kusanci qarewa, da shirin mahajjata domin komawa qasashensu, Yana mai bayyana cewa babbar falalar aikin hajji shi ne kankare zunubai, da kasancewar mahajjaci zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi, da fefa sabuwa, Yana mai tunatar da mahajjata kan wajabcin kiyaye fefofinsu, tsarkaka daga zunubai,kamar yadda ya ambaci abubuwa na aiyuka masu falala, waxanda da sababinsu Allah ke kankare zunuban bayi.

بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka a cikinsa.
Yabo ya qara tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke cikin sammai.  
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke cikin qassai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon abinda ke tsakanin sama da qasa.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon adadin kowani abu.

Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin sammai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin qassai.
Yabo ya tabbata ga Allah, gwargwadon cikin sama da qasa.
Yabo ya qara tabbata ga Allah, gwargwadon kowani abu.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu, kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa.
Allah yayi qarin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da qarin sallama.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah,  Allah (تعالى) yana cewa: "Yak u waxanda su ka yi Imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Tauba: 11].      

Ragowar aiyukan hajji sun kusanci karewa, Tawagogin Mahajjata su kuma sun fara daddaure kayayyakinsu domin komawa garurruka ko kasashensu, bayan gama hajji a wannan lokaci mai tarin nasara,wanda ya cika da tarin hidimomi da suka kammala, da kuma nasarori masu girma, da kuma aiyuka wanda dukkan bangarori na hukuma (wato: ma'aikatu) su ka yi aiki tukuru akansu, tare da bunkasa tunani-tunanin zamani, domin ganin sun yi hidima ga masu ziyara da mahajjata; Don haka;
Allah ya yi sakayyar alkhairi ga shugabannin wannan kasa, wadanda suka kashe dukiya a yalwace, kuma suka zuba ido a lokacin gudanar da aiyukan ...
kuma (Allah) ya yi albarka ga mazaje masu gaskiya da su ka aikata aikin daukaka, da kyautata tsare-tsaren hajji, sai su ka mayar da sharewar da ta ke ta haushi kurame, wadanda su ke munana surar nagartattun abubuwa, su ke kuma kirkiro labarun abubuwan karya, Shi hasken rana idan far ya fito, hannu baya boye shi!

Hakika Allah ya yi mana ni'imar lokutan xa'a, waxanda alherorinsu su ke bibiyar juna, kuma a cikinsu ne rahamomin Ubangiji (سبحانه) su ke lullube mu, da kuma gafara,,, 
Daga cikin waxanda aka yi musu gamda-katar ko dace -Allah ya ya sanya mu daga cikinsu; mu da ku- akwai wanda ya koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi (shi ne wanda ya yi hajj mabruur), 
Daga cikinsu kuma, akwai mutumin da Allah ya gafarta masa zunuban shekaru biyu...(shine mutumin da ya yi azumin yinin arfa kenan)

Wancan ita ce martaba maxaukakiya wanda mutanen da aka yi musu dace su ka kai izuwa gare ta, kuma sabuwar farar fefa mai tsarki wacce mutanen da suka zage damtse su ka same ta, ta kan tattara tunanin mai hankali, ta sanya shi yin aiki don kiyaye wannan xaukaka, da qoqarin wanzuwa akan wannan matsayi na xaukaka, wanda da shi ne, zai samu xaukakar gafara, da tatacciyar rahama.

Aiyukan masu taqawa a kowani lokaci shine tunkuxe munanan aiyuka da kyawawa, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne kyawawa suna tafiyar da munana" [Hud: 114].

            Qoqarin tsarkaka na yau da kullum, daga dauxoxin rayuwa, da dawwamammen tsarkake takardar aiki basa karewa, da karewar lokutan ibadu na musamman, kuma lamarinsu baya takaituwa da wani wuri kevantacce (kamar Makka da arfa, da Madina), ko da wani lokaci sananne (kamar: kwanaki goman zulhijja); wannan kuma kasancewar shu'umcin yin zunubai ya kan gadar da hana bawa aikata wani alheri, kuma ya haifar masa da tavewa, kuma lallai dabaibayin zunubai yana hana bawa tafiya zuwa ga biyayyar Allah, ko ya hana bawa gaggawa izuwa ga hidimar Ubangijinsa, Kuma don haka ne, Musulmi ya ke neman aiyukan da suke kankare zunubai, suke kuma xaga darajoji, domin ya tsarkake ransa, yana cikiyar samun tsarkaka da xaukaka.

YANA DAGA CIKIN MANYAN SABUBAN SAMUN GAFARA Tauhidin Allah da kaxaita shi cikin bauta; saboda duk wanda ya tabbatar da kalmar tauhidi a cikin zuciyarsa, to sai ta fitar masa so, da girmama, ko ganin kwarjinin duk abinda ba Allah ba, daga nan kuma sai zunubansa da kura-kurensa su qoqqone, gabaxayansu, koda sun kai kamar kunfan teku, kai wani lokacin suna ma iya juya zunuban zuwa ga aiyuka kyawawa.

Kuma ana kankare zunubai: Da yin guzurin bin dokokin Allah ko takawa, wanda shine mafi alherin guzuri, Allah ta'alah yana cewa: "Duk wanda ya yi takawar Allah yana kankare masa munanan aiyukansa, kuma sai ya girmama masa lada" [Xalaq: 5].

Kuma dukkan aiyuka masu falala suna kankare zunubai, kuma fage su ke, mai faxi don tsarkake rai daga dauxar sabo, kuma su kan yaye wa zukata qurar gafala da rafkana;
Kuma yana daga cikin haka: Kyautata alwala da xahara (tsarki), da girmama lamarin yin sallah a kan lokacinta, a cikin jam'i, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin ba zan nuna muku abinda Allah ke share kura-kurai da shi, kuma ya xaga darajoji da shi? Sai su ka ce: E, ka bamu labari ya Manzon Allah! Sai ya ce: Cika alwala a lokacin qin tava ruwa, da yawan taku zuwa ga masallatai, da jiran sallah bayan salla, yin hakan kamar ribaxi ne".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya yi tsarki –wato: alwala- daga gidansa, sai ya tafi zuwa ga wani xaki daga cikin xakunan Allah, domin ya aiwatar wata farilla daga cikin farillan Allah, takunsa guda biyu su kan kasance; xayan ya kan kankare masa kura-kurai, xayan kuma ya kan xaga daraja".
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Kuna kuna, kuna kuna -idan ku ka aikata savo- amma idan ku ka yi sallar asuba sai ta wanke su. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka sallaci azahar sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka sallaci la'asar sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka yi sallar magrib sai ta wanke shi. Sannan sai ku kuna, ku kuna, idan ku ka yi sallar isha sai ta wanke shi. Sannan sai ku yi barci, ba za a rubuta muku savo ba har sai kun tashi daga barci".

Kuma ana kankare munana, ana xaga darajoji ta hanyar bayar da dukiya da ciyarwa da sadaka, Allah (تعالى) ya ce: "Idan ku ka yi sadaka a bayyane to madalla da ita, idan kuma ku ka voye ta, ku ka baiwa fakirai to alheri ce a gare ku, kuma sai ya kankare muku wasu daga cikin munananku" [Baqarah: 271], Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ita sadaka tana kashe tasirin laifi kamar yadda ruwa ke kashe wuta*.

Umurni da kyakkyawa, da hani da mummuna yana cikin ababen da suke kankare zunubai, su daga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Fitina ko jarabawar da ake yi wa mutum cikin iyalansa da dukiyarsa da makwabcinsa salla tana kankare su, da azumi, da yin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna*.

Yin gaskiya wa Allah, da yin gaskiya wa rai, da yin rayuwa cikin gaskiya suna daga ababen da suke kankare zunubai, Allah (تعالى) yana cewa: "Wannan, da ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata shi, waxannan sune masu takawa * Suna da abinda suke so a wurin Ubangijinsu, wannan shine sakamakon masu kyautatawa * Domin Allah ya kankare musu mafi munin abinda suka aikata, ya kuma sakanta musu ladansu da mafi kyan abinda su ka kasance suke aikatawa" [Zumar: 33-35].

Kamar yadda imanin da ya samu tabbatuwa a lokacin da aka jarraba mutum shi ma yana kankare zunubai, kuma yana daga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu abinda zai samu mumini na wahala ko gajiya ko cuta ko bacin rai, har damuwar da zata dame shi, face an kankare masa munanan aiyukansa da shi".

Bunqasa rayuwa ta hanyar raya qasa da gyara ta, shi ma yana kankare zunubai. Yin alheri ta hanyar kyautata wa Mutune shi kuma yana xaga darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya akan wata hanya sai ya samu reshen bishiyar qaya sai ya xauke shi, Sai Allah ya gode masa akan haka, kuma ya gafarta masa".

A tsakiyar nuna farin cikin isowar rayuka waxannan lokuta na musamman masu falala, da kuma kamfatar wani abu na falalansu da ladansu; Bawa ke qan-qan da kai, ya roqi Ubangijinsa cewa ya yi masa ilhama ko baiwar shiriya da tabbatuwa, sai ya riqa cewa, kamar yadda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ya ke faxi: "Ya Allah lallai ne ni ina rokonka tabbatuwa cikin lamarin addini, da azama akan shiriya". Kuma yana cewa: "Ya Mai jujjuya zukata, ka tabbatar da zuciyata akan addininka".


            Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa,    lallai ne shi Mai gafara ne Mai rahama.
>>> 

HUXUBA TA BIYU
            Yabo na Allah ne wanda masu taqawa suka samu yardarSa.

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Muminai kuma sun tabbatar da haka.
            Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, Masu binsa kawai su, za su samu cetonsa,
Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa da sahabbansa, duk lokacin da masu Ambato su ka ambace shi. 
           
Bayan haka:
Ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin dokokin Allah, da taqawa.
Zikirin Allah ko ambatonsa yana kwararo da tarin albarkoki da rahamomi, kuma ya kan kasance cikin kalmomi marasa yawa, a cikin lokatai takaitattu, da niyya ta gaskiya, Sai kuma, a share zunubai, kuma Musulmi ya samu mafi kololuwar darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR a cikin yini, sau 100, yana daidai da ya 'yanta bayi guda 10, kuma za a rubuta masa ladan kyawawa guda 100, a kuma, goge masa munana 100, kuma za su kasance tsari ne a gare shi daga shexan, tsawon wannan yinin nasa har ya kai yammaci, kuma babu wani mutum da ya zo da fiye da abinda ya zo da shi, sai mutumin da ya aikata fiye da nasa*.

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya faxa a lokacin da ya ke jin mai kiran salla, WA ANA ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, RADIYTU BILLAHI RABBAN, WA BI MUHAMMADIN RASULAN, WA BIL ISLAMI DIYNAN an gafarta masa zunubansa".

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: SUBHANAL LAHI WA BI HAMDIHI a cikin yini, sau 100, to an kankare masa kura-kuransa, koda sun kasance misalin kumfar teku ne".

Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ce: SUBHANALLAHI sau 33 a bayan kowace sallah, ya ce: ALHAMDU LILLAHI sau 33, ya ce: ALLAHU AKBAR sau 33, sun zama 99, sai ya cikate xarin da faxin: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR to an gafarta zunubansa koda sun kasance kamar kumfar teku ne".

Wannan kaxan ne daga tarin rahama ko albarkokin Allah Mai karimci Mai baiwa.
Mai rabo kuma shine, wanda ke qoqarin neman karamomi, kuma ya ke qoqari domin a kankare masa zunubai, a kuma xaga darajojinsa, domin ya haxu da Ubangijinsa da fefofin aiyuka tsarkaka, tatattu; kasancewar Allah -Mabuwayi da xaukaka- yana shumfuxa hannunsa da dare, domin wanda ya munana a cikin yini ya tuba. Kuma yana shumfuxa hannunsa da rana domin mutumin da ya munana aiki cikin dare ya tuba, har zuwa lokacin da rana za ta fudo daga mafaxarta".

            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati ga iyalan Ibrahima. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka ga iyalan Ibrahima, lallai ne kai Abin godiya ne Mai girma.     
Ya Allah!Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan Annabi da sahabbansa masu karimci, ka haxa da mu da afuwarka, da karramawarka, da kyautatawanka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu, kuma ya nufi musulunci da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa, Ya Mai amsa addu'oi.
Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su, a kowani wuri, Ya Allah ka kasance musu mai qarfafawa kuma mai taimako;
Ya Allah! Lallai su mayunwata ne, ka ciyar da su, marasa takalma, ka basu, tsirara sai ka tufatar da su, An zalunce su, sai ka taimake su, Ya Allah an zalunce su, ka taimake su, lallai an zalunce su, ka taimake su.
Ya Allah wanda ya saukar da littafi, mai gudanar da gajimare, mai rushe rundunoni; ka rushe maqiyanka; maqiya addini, kuma ka taimaki musulmai akansu, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shi ne qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wanda it ace mu ke rayuwa a cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda it ace makomarmu, kuma ka sanya rayuwa ta zama qari ne a gare mu cikin kowani alheri, mutuwa kuma hutu daga kowani sharri, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana akansu, kada ka qulla musu akanmu, kuma ka shiryar da mu, ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu.
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da rahamarka da falalarka da arziqinka.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da juyawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da xaukacin fushinka.
            Ya Allah! Ka gafarta wa iyayenmu da iyayensu, Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, kuma ka warkar da marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu.
kuma ka datar da xaukacin majivinta lamuran musulmai, wajen yin aiki da littafinka, da hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya Allah! Ka kiyaye su cikin zurriyarsu da abinda su ka bari, da dukiyoyinsu, da 'ya'yansu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka kiyaye su da kiyayewarka, ka basu kariya da kulawarka, lallai kai mai iko ne akan kowani abu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Allah ka gafarta mana, da 'yan'unmu da su ka rigaye mu da imani, kuma kada ka sanya qyashi a zukatanmu, ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai ne kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 201].
            Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata xakinka mai alfarma, Ya Allah! Ka mayar da su zuwa garurrukansu suna kuvutattu masu ribata, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka sanya hajjin ya zama hajji na biyayya, kuma aiki abin godewa, da zunubin da aka gafarta, kuma aiki nagari karvavve lafiyayye, Ya Ubangijin talikai.
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].


     "Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...