2018/12/22

HUDUBAR dr. Salah dan Muhammadu Albudair, 14 RABIYYUS SANIY 1440H daidai21 Disemba 2018M











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 14/RABIYYUS SANIY/1440H
daidai da 21/DISEMBA/ 2018M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHMMADU ALBUDAIR



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KYAUTATA LADABI
(حسن الأدب)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Albudi–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:LADABI,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya tarbiyantar da mu da Alkur'ani da Sunnah da mafi kyan ladabi, kuma ya saukar da mu ga bazarar falalarSa mai yabanya, kuma ya ajiye mu cikin yalwar falalarSa mai fadi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, zuwa gare shi nake kira, kuma a gare shi nake mayar da lamura.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, an turo shi domin ya cika kyawawan halayya, kuma sune matsayi mai girma.
Allah, ya yi dadin salati da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, salatin da zamu samu cikakken lada da shi, da mafi girman rabo.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah; domin mai takawa ya kan samu babban rabo, kuma mabarnaci shakiyyi ya yi hasara,  "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imraana: 102].

Ya ku Musulmai
Samun daukakar Musulmi shine ladabinsa, kuma ladabi madaukaki yana wadatarwa daga matsayi  madaukaki da danganta madaukaki, saboda samun daukaka yana cikin himmomi madaukaka, ba daga dangantaka ko kasussuwan (iyaye da kakanni) da suka rududduge ba.
BAI CUTAR DA WANDA YA TATTALI LADABI DA HANKALI BA,
KASANTUWAR BAI FITO DAGA KABILAR ABDU-MANAFI BA

Falala cikakkiya itace ladabi ya kasance tabbatacce a cikin iyaye, sai kuma ya samu gindin zama a cikin 'ya'yansu da jikoki;
SUN KAWATA TSOFONSU DA KYAKKYAWAN NA ZAMANINSU,
DA KUMA HALAYEN GIRMA, DA KYAWAWAN DABI'U

MADALLA DA MUTANEN DA KAI NE RESHEN TUSHENSU,
KUMA MADALLA DA KAI, DOMIN DAGA ASALINSU RESHENKA YA SAMU

LADABI shine yin abin yabo; cikin zance da aiki.
Kuma Ladabi shine, aikata ababe masu falala, da barin masu muni.
Kuma shine, girmama na sama da kai, da tausasawa na kasa.
Kuma Ladabi shine, riko da kyawawan dabi'u, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma lallai kai kana kan wasu halaye masu girma" [Kalam: 4].
Adiyyatul Aufiy ya ce: "Wato, lallai kai kana kan ladabi mai girma".
Ladabi shine takawar Allah Ta'alah, da yin da'a a gare shi, da nisantar saba masa.
NA YI TARBIYYA GA KAINA, SAIDAI BAN SAMA MATA
LADABI BA, IDAN BA A CIKIN TAKAWAR ALLAH BA.
Mujahid –Allah ya yi rahama a gare shi- ya ce, alhalin yana tafsirin: "Ku kare kanku da iyalanku daga wata wuta" [Tahrim: 6], wato: "Ku yi wasiyya ga kanku da iyalanku da takawar Allah, kuma ku ladabtar da su".
YIN TARBIYYA A SANNU-SANNU, HAKIKA YANA AMFANAR KANANAN YARA
SAIDAI A BAYAN GIRMA, YIN TARBIYYA (A GALIBI) BAYA WANI AMFANI

SABODA RESSAN DANYEN BISHIYA IDAN KA NEMI DAIDAITA SU, SUKAN MIKE
AMMA BASU YIN TAUSHI IDAN KA NEMI DAIDAITA SU BAYAN SUN ZAMA ITACE (BUSASSHE)

KYAU BA SHINE, TUFAFIN DA SUKE KAWATA MU BA,
LALLAI KYAU (NA HAKIKA) SHINE KYAN ILIMI DA LADABI

Kuma an yi wa ladabi sunan ladabi ne, saboda yana ladabtar da Mutane ya dora su akan abubuwan yabo, ya kuma hana su aikata munanan ayyuka.
Ladabi shine, kyautata magana, da kyan zance, da dadinsa, da kyautata shirya zance, da kwarewa cikin mu'amala, da kula da kyan yanayi (na tufafi), da gyaran zuciya da gangar jiki.
Ladabi (wato أدب) ba kawai shine fasaha da balaga da hardace ilmuka da wakokun Labarawa ba, Saidai hakikanin ladabi shine sifantuwa da kyakkyawan halaye.
Da yin farin ciki da abinda Allah ya yi ga wani na ni'ima, da nisantar hassada, da kubuta daga dabi'ar kyashi.
Duk wanda hankalinsa ya cika, ladabinsa da tarbiyyansa suka zama kawa a gare shi, sai maganarsa tayi karanci, sai shirunsa ya yawaita, lafazinsa ya yi kyau, hakurinsa ya bayyana.
SAI KA KASANCE MAI KARAMCI, MAI HAKURI, MAI HANKALI, FADAKAKKE,
MAI TSAFTAR HALAYE, DAGA WAUTA, DA FUSHI

KA KIYAYE HARSHENKA, DAGA ZAMBO, DA WAUTA,
DA KUMA ABOTAR SAKARKARU, KA NISANCI KARYA.

Ana cewa: Dabi'u guda uku, Mutum a tare da su baya zama bako: Nisantar wadanda ake zargi, da kyakkyawan ladabi (tarbiyya), da nisantar cutarwa.
YANA KAWATA BAKO A YAYIN BAKUNCINSA
DABI'U GUDA UKU; DAGA CIKINSU AKWAI KYAUTATA LADABI

NA BIYUNSU: SHINE KYAUTATA DABI'ARSA,
NA UKUNSU KUMA, NISANTAR WURAREN ZARGI
IbnulKayyim –رحمه الله- ya ce: "Ladabin Mutum shine tambarin samun sa'idarsa da nasararsa, Shi kuma karancin ladabinsa shine tambarin tabewarsa da halakarsa, domin ba a iya janyo alherin Duniya da lahira da sai da ladabi. Kuma ba a janyo talaucin Duniya da lahira sai da dabi'ar karanta ladabi. Ka duba lamarin ladabi ga iyaye biyu; yadda ya tseratar da Ma'abucinsa daga zaman kogo a lokacin da dutse ya sauko akansu, kuma ka yi dubi ga ladabin Abubakar siddik -Allah ya yarda da shi- ga Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- a lamarin sallah, wato lokacin da ya ki ya shiga gabansa, kuma ya ce: BAI DACE GA IBNU-ABIY KUHAFAT, YA SHIGA GABAN MANZON ALLAH -SAW-, yadda hakan ya gadar masa da samun matsayinsa da jagorantar al'umma a bayansa". Maganarsa ta kare.

LALLAI NE NI, DABI'U MASU KARAMCI SUNA FARANTA MIN,
IRIN FARIN CIKIN BAKO A LOKACIN DA YA KOMO, YA SADU DA MASOYANSA

KUMA YIN TUNANI KAN MUTUNTAKA DA KYAUTA A CIKIN JERIN KYAWAWAN HALI
YANA JIJJIGA NI, JIJJIGAWAR MUTUMIN DA KE CIKE DA SHAUKI

IDAN AKA AZURTAKA DA DABI'A ABAR YABO,
HAKIKA MAI RABIYAR ARZIKI, SHINE YA ZABE KA

MUTANE, WANNAN RABONSA DUKIYA, WANNAN KUMA
ILIMI, WANNAN KUMA KYAWAWAN DABI'U

SHI ILIMI, IDAN DABI'UN DA ZASU DAUKAKA SHI BASU DABAIBAYE SHI BA,
SAI YA KASANCE ABIN HAWAN ZILLEWA,

KADA KA YI ZATON ILIMI ZAI YI AMFANI, SHI KADAI
MATUKAR MA'ABUCINSA BAI YI KAWA DA DABI'U BA

SAU NAWA MAI ILIMI YA SHUMFUDA IGIYOYIN ILIMI
DOMIN CIN MUTUNCIN MUTANE, DA YANKE ZUMUNTA, DA RARRABA KAI!

SHI KUMA MALAMIN WASU MUTANE YA RIKA KAFA FIKIHUNSA
DOMIN MAKIRCI, KO YA ZAMA MAI NEMAN HALATTA SHIKA!

UWA KUMA, MAKARANTA CE, IDAN KA TATTALE TA,
TO, KA YI TATTALIN AL'UMMA, MAI KYAWUN HALAYE!

UWA DAUSAYI CE, IDAN AKA BITA DA BAYIN RUWA,
SAI DAUSAYIN YA BADA YABANYA DA CIKAKKEN GANYE

UWA ITACE MALAMAR MALAMAN DA FALALARSU
TA CIKE SARARIN SAMANIYAR DUNIYA

KU YI TARBIYYA TAGARI GA 'YA'YANKU MATA
DOMIN NAGARTA SHINE MAFI ALHERIN ABIN RIKEWA

YANA  WAJABA 'YA'YANKU MATA SUSAN
HASKEN SHIRIYA, KUMA SU SAN KUNYA
Kuma hakika, littatafan sihah da sunan da musannafaat, sun bada kulawa wajen tattaro hadisai, kuma babu wani littafi daga cikin wadannan littatafan masu girma wadanda ake daukansu a matsayin madogarar ma'abuta Musulunci, face mawallafinsa ya ware littafin ladabi, ko babi-babi akan ladibi, Duba littafin ladabi a cikin sahihul Bukhariy, da littafin ladabi a cikin sahihu Muslim, da littafin ladabi a cikin sunan na Abu-dawuda, da littafin ladabi a cikin sunan na Tirmiziy, domin ka yi mamakin girman ladabi a cikin addinin Musulunci, da matsayinsa a cikin sunna da shari'a.

Kuma yana daga manyan sunnoni a babin ladduba da halayya: Abinda aka ruwaito daga Abu-Umamah Albahiliy -رضي الله عنه-, ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai ni na lamunce da bayar da gida a gabar Aljannah ga wanda ya bar jayayya, koda yana da gaskiya. Da wani gidan a tsakiyar Aljannah ga wanda ya bar karya koda a cikin wasa ne. Da wani gidan a kololuwar Aljannah ga wanda ya kyautata halayensa", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Abdullahi bn Almubarak ya ce: "Mu, lallai mun fi bukatar kadan daga ladabi fiye da ilimi mai yawa".
Imamu Maliku ya ce: "Mahaifiyata ta kasance tana daura min rawani, sai ta ce: Ka tafi ga malam Rabiy'ah, ka koyi ladabinsa gabanin koyan iliminsa".
Abdullahi dan Wahaf ya ce: "Abinda muka koya na ladabin Maliku yafi abinda muka koya na iliminsa".
Isma'il dan Ulayyah ya ce: "Lallai a majalisar Imamu Ahmad Mutane dubu biyar suna taruwa, ko hakan da doriya, kuma kamar dari biyar, suna rubuta iliminsa, sauran kuma suna koyan kyakkyawan ladabinsa, da halayya".
Kuma Alkhadib Albagdadiy -رحمه الله- ya ce: "Wajibi shine daliban hadisi su kasance sun fi sauran Mutane cikar ladabi, da tsananin tawali'u, kuma su fi su tsantseni da riko da addini, kuma sufi karancin wauta da fushi, wannan kuma saboda hadisan da suka kunshi kyawawan halayyar Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ko-yaushe sukan  kwankwasa kunnuwansa, da batun laddubansa, da tarihin magabatan kwarai, daga iyalan gidansa da sahabbansa, da hanyoyin Maluman hadisi, da labarun falalar Mutanen baya, sai dalibin hadisi ya yi aiki da abinda yafi kyau yafi dacewa, ya kuma kauce wa munanan hanyoyi da ayyuka".

Ina fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya kasance ga masu  komawa gare shi, Mai yawan gafara.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya bada mafaka ga wanda ya nemi fakewa ga tausasawarSa,
            Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya bada lafiya cikin ni'imtarwarsa, ga wanda ya debe tsammanin samun waraka daga cutukansa.
            Kuma na shaida lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, wanda ya bi shi ya shiryatu ya dau hanya, wanda kuma ya saba masa ya bata ya bar turba,
            Allah ya yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa,  salati mai ninkuwa, da sallama mai wanzuwa,
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah kuma ku kiyaye shi, kuma ku yi da'a a gare shi kada ku saba masa, "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma ku kasance tare da masu hakuri" [Tauba: ].

Ya ku Musulmai
Ku yi godiyar ni'imar Allah akanku, Lallai ya turo muku da iska masu albishir, da girgije masu nauyi, masu barin ruwan sama, girgije bayan girgije, da suka sassauka a cikin kwari masu jin kishi, da saharori masu wahalar samun ruwa, da kuramen duwatsu daskararru, wanda tuni rashin ruwan ya jigata su, ,,, sai suka jijjika da ruwan sama,  sai gashi kasarku -da falalar Allah- tayi ciyawa, sai dausayinku ya zama abin kaye da saukan wannan ruwan, duwatsunku suka yi kore da rahamar Allah, a cikin shekararku da ta cika da yabanya, da wani yanayi mai kyau mai kayatarwa, wanda yake nuni kan ikon Allah da hikimarSa da rahamarSa da yalwar falalarSa, da arzikinSa da kyautatawarSa.

HAR LOKACIN DA DAUSAYI YA RUNGUME KASA
SAI CIYAWAR FARKO-FARKO MASU KARFAFAR JUNA SUKA FUFFUDO

AKAN KASA DAYA, SAI SUKA ZAMTO KAMARSU DAYA TA FISKAR KYAWU
YAYIN DA TA FISKAR LAUNUKA BASU ZAMTO ABU DAYA BA

IDANUNKA NA NUNA MAKA IDANIYAR RUWA
MASU KYAU DA DADI, WANDA SUKA FI IDANIYAR YANKIN JA'AZIRI

BA ABINDA YAFI KYAN GANI, IN KA ZIYARCE SU,
KO KA GA HAKIKANINSU, NA KYAN DAUSAYI KORE

IDAN KA JE MUSU, SAI SU BAKA GANI MAFI KYAWU, IDAN KUMA BAKA JE BA,
SAI YA ZIYARCE KA CIKIN DADDADAR ISKAR DA TAKE ZUWA DA SAFIYA

Sai ku buda idanuwanku cikin kyawun halittar Allah Ta'alah, tare da kula da ladduban fita yawon buda ido, kuma kada ku bata, ko ku sanya najasa a wuraren da Mutane suka rike su a matsayin inuwowin zama, da kailula, haka wuri mai dausayi da ciyawoyi, ko karkashin bishiya mai 'ya'ya, ko wurin diban ruwa, ko hanyar da ake binta da kafa, ko da dabbobi, ko da motoci. saboda an ruwaito daga Abu-hurairah -رضي الله عنه-, lallai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku kiyayi wuraren tsinuwa guda biyu, Sai suka ce: wadanne ne wurare biyu na la'ana Ya Ma'aikin Allah! Sai ya ce: Wanda yake biyan bukata akan hanyar Mutane ko inuwarsu", Muslim ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga gare shi, رضي الله عنه ya ce: lallai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi kashi a hanyar da ba matacciya ba, daga cikin hanyoyin Musulmai, to tsinuwar Allah ta tabbata a kansa, da ta Mala'iku, da ta Mutane gaba daya", Baihakiy ya ruwaito.
 Sai ku yi salati da sallama ga …………………………

2018/12/06

TSARKAKE ZUCIYA Hudubar Masallacin Manzo SAW ta د حسين آل الشيخ 29 Rabiyul Awwal 1440H daidai 7 Disemba 2018M












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 29/RABIYYUL AWWAL/1440H
daidai da 7/DISEMBA/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUS-SHEIKH





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TSARKAKE ZUCIYA
(سلامة الصدر)
Shehin Malami wato: Husain bn Abdu'aziz AlusSheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TSARKAKE ZUCIYA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah, Mai hakuri Masani,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Ubangijin Al'arshi Mai girma,
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa wanda aka turo shi da kowace dabi'a Mai karamci, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bi su, kuma suka yi koyi da riko da addininsa mikakke.

Ya ku Musulmai
Ina muku wasiyya da ni kaina da takawar Allah Mabuwayi da daukaka, da kuma yin da'a a gare shi a cikin tsananin rayuwa da lokacin walwala, domin "Wanda ya yi da'a ga Allah da Manzonsa hakika ya rabautu da rabo mai girma", [Ahzab: ].

Ya ku Musulmai
A zamanin da lamarin son Duniya ya bayyana cikin sifofi da fiskoki masu yawa, Musulmi yana bukatar tunatarwa kan abinda zai rika zaburar da shi kan son Mutane, da basu alkhairi da yin kyauta a gare su, da kamewa daga cutar da su, ko yin sharri ga Musulmai, lallai hakan zai kasance ne, ta hanyar riko da hali ko dabi'ar TSARKAKE ZUCIYA (سلامة الصدر) wanda Musulmi ke rayuwa da shi, cikin jin dadi, yana abin yarda.
Lallai tsarkake zuciya yana cikin managartun dabi'u, da halaye mafi daukaka, wadanda Musulmi yake riskar lada masu tarin yawa da su, da kuma samun kyakkyawan makoma, Allah Ta'alah ya ce: "A ranar da dukiya bata amfani, kuma diya basu yi * face wanda ya je wa Allah da zuciya mai tsarki" [Shu'ara'i: 87-88].

Kuma yana daga ALAMOMIN TSARKIN ZUCIYA bayan imani da takawa da tauhidi da yakini, zuciyar ta tsarkaka daga kulli, hassada da kyashi ga Musulmai, sai Musulmi ya rayu tare da 'yan'uwansa Musulmai cikin tsarkin zuciya da dadin rai, da kyakkyawan nufi, ta yadda ba zai rike su da kyashi ko kiyayya ba, kuma ba zai boye kulli akansu ko algus ko makirci ba, A'a, Musulmi ya kan rayu da 'yan'uwansa ne da zuciyar da take yada alkhairori da kyautatawa, da dabi'u masu kyau, cikin tsaftar zuciya da tsarkinta, ta yadda shi yana cikin hutu a ransa, sauran Mutane kuma, su  samu kubuta daga sharrinsa.
Mutane basu samun bala'i da sharri daga wurinsa
Kuma basu dandanar cutarwa da wahala daga gare shi
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: " 'Dayanku baya zama Mumini, face ya so wa 'Dan'uwansa abinda yake so ga kansa".

'Yan'uwa, a cikin Musulunci!!!
Yana daga ni'imomin da ake gaggautar da bayar da su tun a wannan rayuwar, wanda kuma shine Aljannar Duniya, kuma da shi rayuwa take yin dadi, Shine Bawa, ya yi kwadayin sifantuwa da ni'imar tsarkin zuciya, ga dukkan wadanda suke rayuwa da shi, ko suke hulda, dama sauran Mutane, Allah ya fada a inda yake sifanta 'yan Aljannah: "Kuma muka fitar da abinda ke cikin kirazansu na kiyayya" [A'araf: 43].
Ibnu-Adiyyah –رحمه الله- ya fada a tafsirin wannan ayar: "Wannan kuma, saboda wanda ke dauke da kiyayya yana azabtuwa da ita, kuma babu azaba a gidan Aljannah".

Kuma ya zo cikin muhimman addu'oin Ma'abuta imani: "Da wadanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana, kuma ka yi gafara ga 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya kyashi ga wadanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tsananin tausayi ne, Mai jinkai", [Hashr: 10].
'Yan'uwa, a cikin Musulunci!!!
Yana daga cikin ayyukan da suka fi falala, Tsarkake zuciya daga dukkan nau'ukan adawa da kiyayya gaba dayansu, An ce wa Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- wanene Mutumin da yafi falala? Sai ya ce: "Duk mai tsarkin zuciya, mai yawan gaskiyar harshe", Sai suka ce: Mai gaskiya a harshe, mun san shi, Wanene kuma: makhmumul kalb, Sai ya ce: "Shine tsaftatacce, Mai takawa (النقي التقي), wanda bashi da zunubi, kuma baya zalunci, kuma bashi da kyashi, kuma baya hassada", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma Almunziriy ya inganta isnadinsa, da Albusiyriy, a cikin littafin Zawa'id, da Irakiy, kuma Albaniy ya inganta shi.
Kuma hakika Magabatan wannan al'ummar sun riski wannan lamari, kuma wannan shine Zaid bn Aslam, yana shiga wurin Abu-Dujanah, alhalin bashi da lafiya, amma sai ga fiskarsa tana ta sheki, sai ya ce da shi: "Me yasa fiskarka take sheki? Sai ya ce: "Babu aikin da na aikata wanda nafi aminta da shi, fiye da guda biyu, Amma na farkonsu shi ne lallai na kasance bana magana sai ga abinda ya shafe ni. Shi kuma na biyun, Zuciyata ta kasance ga dukkan Musulmai mai tsarki".
Kuma Fudail bn Iyadh –رحمه الله- ya ce: "Wanda a cikinmu ya riski falala, bai riske ta saboda yawaita nafilfilin sallah ko azumi ba, A'a, a wurinmu ya riski hakan ne, saboda fadin rai, da tsarkin zuciya, da kuma nasiha ga Al'ummah".

'Yan'uwa, a cikin Musulunci!!!
Daga cikin SABUBAN DA SUKE TAIMAKO, KAN SAMUN TSARKIN ZUCIYA, akwai Yin ikhlasi ko tsarkake niyya ga Allah Mabuwayi da daukaka,
da yarda da kaddara, da kuma dukkan abinda Allah Mabuwayi da daukaka ya rubuta shi ga Bawa a wannan rayuwar,
da lazimtar biyayya ga Allah Mabuwayi da daukaka,
da yawaita tilawar littafinsa Subhanah,
tare da yin kokari wajen yakar rai daga munanan halaye ko cutuka, kamar algus, da kulli, da hassada,
tare da tuna irin abinda munanan halayen suke janyowa ga Mutum na sharri mai tsanani, a Duniya da Lahira.
Sa'annan sai Bawa ya yi kokari kan Allah ya azurta shi da zuciya tsarkakakkiya da harshe mai gaskiya,
Da kuma aikata dukkan abinda zai janyo kauna da soyayya, ya rika tunkude kyashi da kiyayya, kamar yada sallama,
da kuma Mutum ya rika barin abinda bai shafe shi ba, daga lamuran halittu,
da kokarin bayar da kyauta, saboda tana janyo soyayya, kuma tana tunkude kiyayya,
da kuma yin addu'a ga Musulmai gaba daya,
da yafiya ga wanda ya munana,
da lamarin kyautatawa, da dukkan nau'ukansa,
da kokarin shigar da farin ciki ga zukatan Musulmai,
da yin farin ciki a lokacin samuwar abinda ke faranta musu,
da kuma tarayya da su cikin abinda rarrashi ne, kuma hakurtarwa, a lokacin bacin ransu da bakin ciki.
Kuma Bawa ya yaki Shedan, domin yana da aniyar cuccusa dukkan abinda suke tunzura zukata, suke lalata su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka ce wa Bayina: su fadi kalma wanda take mafi kyau, lallai ne Shedan yana sanya barna a tsakaninku, Lallai ne Shaidan ya kasance ga Mutum, makiyi bayyananne", [Isra'i: 53].
Kuma ya zo cikin abinda Muslim ya ruwaito, lallai Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Lallai Shedan ya debe tsammanin cewa Masallata za su bauta masa a yankin tsibirin Larabawa, saidai zai yi ta sanya husuma a tsakaninsu".
Kuma lallai yana daga abinda Bawa zai samu tsarkin zuciya da su, Nisantar jayayya da husuma akan mas'aloli da kuma lamuran da suke aukuwa na yau-da-kullum, saboda hakan yana tayar da bacin rai da kiyayya, kuma yana rura wutar gaba, kuma yana haifar da sabani.
Saboda ana yabon jayayya ko tattaunawa ne kawai idan aka yi ta domin tabbatar da wata gaskiya ta addini, daga Malami mai tsarkin zuciya da ikhlasi da gaskiya, wanda ya sifantu da dukkan sharudda da sifofi da ababen lura a lokacin tattaunawar ko mujadala, kewaye da ladabi mai yawa da halaye managarta. Allah Mabuwayi da daukaka y ace: "Kuma ku fadi magana mai dadi ga Mutane" [Bakara: 83].

Ina fadan wannan maganar, kuma ina neman gafara Allah a ni da ku da sauran Musulmai daga dukkan zunubai, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai yawan gafara ne Mai jin-kai.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,



HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah kamar yadda ya dace, da girman fiskarsa da mulkinsa mai girma,
        Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninsa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, yana kira zuwa ga samun yardarsa, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi da kuma iyalansa da sahabbansa.

Bayan haka … !!
Ya ku Musulmai
Lallai tsarkin zuciya kofa ce mai girma zuwa ga samun tabbatacciyar ni'ima madawwamiya, Wani daga cikin Magabata ya ce: "Asalin addini shine tsantseni da kamewa, kuma ibadar da ta fi girman falala ita ce, yin fama cikin dare (salloli), kuma gajeruwar hanyar da take kaiwa ga Aljannah ita ce, tsarkake zuciya".
Sai ku lazimci ibadar tsarkake zuciya, da tsaftace rai, da gyaran niyya, kuma saboda haka ne, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ke kwadayin abinda zai tabbatar ko dasa wannan ginshiki (a cikin rayuwa) ta Mutum, sannan ya tunkude dukkan cutukan da zasu iya bijirowa a gare shi, a inda Annabin –صلى الله عليه وسلم – ya ce: "Kada ku yi kiyayya, kada ku yi hassada, kada ku juya baya, kuma ku kasance –Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juma. Kuma baya halatta Musulmi ya kauracewa dan'uwansa fiye da kwanaki uku" Muslim ya ruwaito shi.
Sai ku kasance –Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna masu soyayya, kuma akan takawa ku kasance masu nuna kauna, kuma akan ayyukan da'a masu yin wasici ga juna.

Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,




TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...