2017/02/23

HUDUBAR 27 JUMADAL ULA 1438 daidai da 24 fabarairu 2017 ta HUZAIFIY daga MASALLACIN ANNABI











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27/JUMADAL ULA/1438H
daidai da 24/FABARAIRU/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HAQQOQI NA WAJIBI
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HAQQOQI NA WAJIBI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya yi falala ga bayinsa; sai ya yi bayanin HAQQOQIN da su ke kansu DA WAJIBAI, kuma ya yarje musu aiyuka masu kyau, ya kuma sanya musu qin munanan aiyuka, ya yi alqawarin alkhairori ga salihan bayi,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai amsa addu'oi,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka qarfafe shi da mu'ujizozi.
Allah ka yi daxin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu taimakon addinin Allah, da jihadi da kuma hujjoji bayyanannu,

Bayan haka:
Ku bi Allah da taqawa; kada ku tozarta farillanSa, kuma kada ku qetare dokokinSa, kuma lallai wanda ya yi taqawa, ya samu babban rabo, wanda kuma ya bi son zuciya ya tave,

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Ku sani
Lallai aiyukan bayi, sakamakonsu nasu ne, uqubar aiyukan kuma akansu ne, saboda biyayyar bawa bata amfanar da Allah, kuma aikata savo baya cutar da Allah, Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata aikin kwarai, to, domin kansa ne,  wanda kuma ya munana, to, a kansa. Sa'annan zuwa ga Ubangijinku za a mayar da ku" [Jasiya: 15].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata mummuna aiki, ba za a sakanta masa ba, face da kwatankwacinsa, wanda kuma ya aikata aiki na kwarai, daga namiji ko mace, alhali kuwa yana mumini, to waxannan za su shiga aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba" [Gafir: 40].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka a cikin hadisin qudusi ya ce: "Lallai ku, ba za ku kai ga cutar da ni ba, balle ku cutar da ni, kuma ba za ku kai ga amfanar da ni ba, balle ku amfanar da ni, Ya ku bayina! Lallai waxannan aiyukanku ne, na ke qididdige muku su, sa'annan sai in cika muku sakamakonsu, saboda haka; Wanda ya samu alheri to ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa, face kansa", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Abu-zarrin |(رضي الله عنه).

Lallai sauke HAQQOQIN DA SUKA WAJABA AKAN BAWA, Amfaninsu –a qarshen lamari- na komawa ne ga bawa mukallafi (mai hankali balagagge), ta hanyar bashi sakamakonsa a duniya da lahira, kamar yadda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Kuma duk wanda ya aikata, aiyukan kwarai, alhalin yana mumini, to babu musu ga aikinsa, kuma Mu a gare shi, masu rubutawa ne" [Anbiya'i: 94].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Lallai waxanda su ka yi imani, kuma suka aikata aiyukan kwarai, lallai ne Mu, ba Mu tozartar da ladan wanda ya kyautata aiki ba" [Kahf: 30].

            Kuma lallai sakaci, wajen sauke sashin HAQQOQIN DA SU KA WAJABTA GA BAWA (mai hankali, balagagge), ko tozarta haqqoqin gabaxaya da barin sauke su, cutar da ke cikin hakan da uqubarsa, yana komawa ne ga mutumin da ya tozarta irin haqqoqin da addini ya shar'anta;
saboda idan mutum ya tozarta HAQQOQIN UBANGIJIN TALIKAI, to, bai cutar da kowa ba, face kansa, a duniya da lahira, domin Allah, Mawadaci ne daga barin talikai, Allah (تعالى) ya ce: "Idan ku ka kafirta, to lallai Allah Wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda da kafirci (butulci) ga bayinSa, idan kuma ku ka yi godiya zai yarda da godiyar, a gare ku" [Zumar: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku, mutane! Ku ne masu buqata zuwa ga Allah, shi kuma Allah shi ne Mawadaci Abin godiya" [Faxir: 15].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Ga ku, Ya ku waxannan! Ana kiranku, domin ku ciyar ga tafarkin Allah, amma daga cikinku akwai mai yin rowa, kuma wanda ya yi rowa, to haqiqa yana yin rowar ne ga kansa" [Muhammadu: 38].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya aikata zunubi, to lallai yana tsirfarsa ne a kan kansa, kuma Allah ya kasance Masani Mai hikima" [Nisa'i: 111].

            Haqqin Ubangiji, wanda ya wajaba a kiyaye shi, shine TAUHIDI, Kuma haqiqa Allah ya yi mafi girman alqawari akansa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma an kusantar da aljanna ga masu taqawa, ba da nisa ba * Wannan shi ne abinda ake yi muku wa'adi da shi, ga dukkan mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (umurninsa)" [Qaf: 31-32].

Kuma duk wanda ya tozarta HAQQIN ALLAH Mabuwayi da xaukaka, ta hanyar SHIRKA  a gare shi, da riqon wasu koma bayan Allah a tsakani, yana yin bauta a gare su, ko yana roqonsu, neman yaye cuta, da baqin ciki, ko biyan buqata, kuma yana tawakkali a gare su, to lallai ya tave, kuma ya yi hasara, kuma aikinsa ya ruguje, kuma Allah ba zai karva masa farilla ba, ko fansa, kuma za a ce masa, ka shiga wuta tare da masu shiga, Sai dai idan ya tuba daga aikata shirka, saboda ya zo cikin hadisi, cewa: Za a faxawa mutum, daga cikin 'yan wuta, cewa: "Da abinda ke cikin duniya naka ne, shin za ka fanshi kanka da shi, daga shiga wuta? Sai ya ce: E, sai a ce masa: Ai an umurce ka da abinda ya fi hakan sauqi, cewa kada ka yi shirka wa Allah", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Idan kuma mutum mukallafi (mai hankali balagagge) ya tozarta HAQQOQI, ya kuma qi bada haqqoqin bayin Allah na wajibi akansa, to haqiqa ya haramtawa kansa lada, a duniya da lahira. Idan kuma ya yi sakaci wajen bada sashensu, to lallai za a haramta masa alherori ne, gwargwadon sakacin da ya yi, wajen bada haqqoqin halittun Allah.
            Kuma rayuwa tafiya ta ke yi, da abinda mutum ke samu na tsanani ko wadaci, da hanawa ko baiwa, kuma rayuwar ba za ta tava tsayawa ba, akan yadda xan'adam ke samun haqqoqinsa na wajibi, da ke wajen mutane ba, Sai dai kuma a wurin Allah ne masu husuma za su haxu, sai Ya baiwa wanda aka zalunta haqqinsa, daga mutumin da ya zalunce shi, ya kuma tozarta haqqinsa, Ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai, za ku bada haqqoqi ga ma'abutansu, a ranar qiyama, har sai an xauki fansa ga akuyar da bata da qafo, daga akuya mai qaho", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma mafi garman HAQQOQI        bayan haqqin Allah, da ManzonSa, su ne HAQQOQIN IYAYE BIYU,
Kuma saboda girman haqqinsu ne, Allah ya gwama ambaton haqqoqinsu da haqqinSa, a inda ya ce: "Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa face Shi, kuma mahaifa biyu ku kyautata musu kyautatawa, ko da xayansu zai kai ga tsufa a wurinka, ko dukkansu biyun, to, kada ka tsawace su, kuma ka faxa musu magana mai karimci * Kuma ka sassauta musu fikafikan tausasawa na rahama, kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda su ka yi renone ina qarami" [Isra'i: 23-24].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga mutum, game da mahaifansa biyu; Uwarsa ta xauke shi, a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu, (mu ka ce masa:) Ka gode mini da kuma mahaifanka biyu, Makoma zuwa gare Ni ne ta ke" [Luqman: 14].
            Kuma Allah ya girmama haqqin iyaye biyu ne, saboda Allah ya samar da kai ne; ya halitta ka ta hanyarsu; su biyu.
            Ita kuma Uwa ta samu mafi tsananin wahala, a matakan renon ciki, kuma ta yi kusan halaka a lokacin haihuwa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga mutum, game da mahaifansa biyu; da kyautatawa, uwarsa ta yi cikinsa da wahala, kuma ta haife shi da wahala" [Ahqaf: 15].
Kuma shayar da mutum, aya ce daga cikin ayoyin Allah.
            Shi kuma Uba yana kulawa, yana tarbiyya, kuma yana yin aiki domin kawo abinci ga xansa.
            Kuma iyaye biyu suna neman magani ga cutukan 'ya'ya,
Kuma suna tashi cikin dare (su hana idanunsu barci) domin xansu ya yi barci,
Suna gajiyar da kansu domin xansu ya samu hutu,
Suna kuma wahalar ko takura wa kayukansu, domin su yalwata wa xansu,
Kuma suna jure wa qazantar yaro, domin ya ji daxi,
Kuma suna ilmantar da xansu, domin ya zama kamili, madaidaicin mutum,
Kuma suna so xansu ya zamto ya fi su, ta kowace fiska

            Don haka;
Kada ka yi mamaki –ya kai yaro- yawaitar wasiyyar da Allah (تعالى) ya yi, dangane da iyaye biyu,
kuma kada ka yi mamakin yawan narkon azabar da aka tanadar, ga mutumin da ya qi yin biyayya ga iyayensa,
            Kuma "xa" ba zai kai ga cikakken biyayya ga mahaifi ba, duk yadda ya yi qoqarin ya kwatanta, sai a hali xaya tak, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Xa ba zai iya sakanta wa mahaifi ba, sai dai idan ya same shi a matsayin bawan da aka mallaka, sai ya saye shi, sannan ya 'yanta shi", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud da Tirmiziy.

Kuma iyaye biyu, qoqfofi ne biyu daga cikin qofofin aljanna; wanda ya musu biyayya, zai shiga aljanna, saboda ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Hancinsa ya turbuxi qasa! Hancinsa ya bugi turvaya!! Hancinsa ya turbuxi qasa!!! Sai aka ce wanene, ya Manzon Allah! Sai ya ce: Wanda ya riski iyayensa biyu da rai, a halin tsufa, ko xaya daga cikinsu, sai kuma bai shiga aljanna ba", Muslim ya ruwaito shi.

Ya kai Musulmi>>> !!!
Idan har iyayenka biyu, su ka yarda da kai, to lallai Ubangijinka ya yarda da kai, Ya zo daga Abdullahi bn Amr (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yardar Allah tana cikin yardar mahaifi, Fushin Allah kuma, yana cikin fushin mahaifi", Hadisi ne ingantacce, Tirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim, a cikin Almustadrak, kuma ya ce: hadisi ne ingantacce.

Kuma biyayya wa iyaye biyu, shi ne:
Yin xa'a a gare su, a cikin umurnin da babu savon Allah a cikinsa,
Da zartar da umurnin da iyayen biyu su ka bayar, da yin aiki da wasiyyar su,
Da tausasa musu,
Da shigar da farin ciki a zukatansu,
da yalwata musu ga ciyarwa,
da bada dukiya a gare su,
da jin qansu, da tausaya musu,
da shiga vacin rai, saboda vacin ransu,
da janyo abinda zai xebe kewa a gare su,
da xa'a ko biyayya ga abokan iyaye biyu,
da sada zumuntar masoyansu,
da sada zumuncinsu,
da kamewa daga dukkan nau'ukan cutarwa a gare su,
da barin aikata dukkan abinda su ka yi hani a kansa,
da son tsawon rayuwarsu,
da neman gafara a gare su a cikin rayuwarsu da bayan mutuwarsu

Shi kuma BIJERA WA IYAYE KO RASHIN BIYAYYA a gare su (wato, Uquq) shi ne abin da ke kishiyantar hakan gabaxayansa,
            Shi kuma yawaitar bijire wa iyaye (Uquq) yana daga alamomin qiyama, saboda ya zo cikin hadisi: "Lallai yana daga alamomin qiyama, ruwan sama ya yawaita, Xa kuma ya zama fushi (ga iyaye), ashararun mutane kuma su yi mungun yaxuwa, su kuma mutanen kirki su qaranta mummunan qaranci".

Yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Kai iyaye; su biyun, ko kuma xaya daga cikinsu, gidan bada kulawa ga masu shekaru dayawa (tsofi), da fitar da su daga kulawar Xansu,  WAL IYAZU BILLAHI,
Kuma yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Yin girman kai a gare su, da ta'addanci akansu ta hanyar dukansu, ko yin wulaqanci a gare su, da zaginsu, da hana su buqatar duniya, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Lallai aljanna, ana samun qamshinta daga tafiyar shekaru xari biyar, kuma mai cutar (ko bijire) wa iyaye ba zai samu qamshinta ba", Xabaraniy ya ruwaito shi.
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku haxa wani da Shi, kuma ga mahaifa biyu ku kyautata musu, kuma ku kyautata ga ma'abucin zumunta, da marayu, da miskinai, da makwabci ma'abucin kusanta, da makwabci manisanci, da aboki a gefe, da xan hanya (matafiyi), da abinda hannunku na dama su ka mallaka, Lallai ne Allah ba ya son wanda ya kasance mai taqama mai yawan alfahari" [Nisa'i: 36].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai tsananin qarfi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,

Ya Allah ka qara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa gaba xaya.

Bayan haka … !!
Sai ku yi taqawar Allah, iyakar taqawa, kuma ku yi riqo, a musulunci da igiya mai qarfi,

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai haqqoqin iyaye biyu –tare da abinda ke cikin tsayuwar xansu wajen sauke su, na tarin lada mai girma, da kuma albarka- to kuma, bada su yana daga manyan halayyar musulunci, yana kuma nuna karamcin xabi'u, waxanda mutumin da zuciyarsa ta yi kyau ke tsayuwa wajen bada su, kuma asalinsa ya kyautata, xabi'unsa su ka tsarkaka,
Ku lallai sakamakon kyautatawa shi ne kyautatawa,
Kyakkyawan abu kuma, duk wanda ya maka shi, to, haqqinsa shi ne a kula da shi, a yi masa sakayya,
Kuma abu mai kyau ana fiskantarsa ne da mai kyau irinsa,
Kuma babu mai bijire ga kyakkyawan abu, face mai yasassun halayya, maras mutunci, mai mummunar zuciya, Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma kada ku manta da falalar da ta ke a tsakaninku, Lallai ne Allah ga abinda ku ke aikatawa Mai gani ne" [Baqara: 237].

            Kuma Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Isah (عليه السلام): "Kuma Ni mai biyayya ne ga Uwata, kuma bai sanya ni mai kaushin zuciya, marashin alheri ba" [Maryam: 32].
            Kuma ya faxa, dangane da annabi Yahya (عليه السلام): "Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai, mai savo ba" [Maryam: 14].
            Kuma Allah ya ce, dangane da shaqiyyi marashin alkhairi: "Kuma wanda ya ce ga mahaifansa biyu, Tir gare ku, Shin kuna tsoratar da ni cewa za a fitar da ni daga qabari ne, alhali kuwa qarnonan mutane dayawa sun shusshuxe, a gabanina (basu komo ba), Kuma su (mahaifan) suna neman taimakon Allah, suna ce masa: Kaitonka! ka yi imani, domin alqawarin Allah gaskiya ne, ,,," [Ahqaf: 17].
            Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه),

daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)

Lallai wani Mutum ya zo wurin Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ya ce: Ya Manzon Allah! WANENE A CIKIN MUTANE YAFI CANCANTAR KYAUTATA MU'AMALATA?
Sai ya ce: "Mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sa'annan sai Mahaifinka, sa'annan sai wanda ke kusa da kai, sai wanda ke kusa da kai", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Ya ku Bayin Allah… !!!
            "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,



2017/02/16

hudubar masallacin Annabi SAW ta 20 jumadal ula 1438h ta Sheikh Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 20/JUMADAL ULA/1438H
daidai da 17/FABARAIRU/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TSORON ALLAH A VOYE DA A BAYYANE
Shehin Malami wato: Abdullahi Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TSORON ALLAH A VOYE DA A BAYYANE, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; (ALMUJIBU) Mai ji da amsawa,
(AR-RAQIBU) Mai tsinkayar abinda aka voye,
(ALHASIBU) Mai qididdiga da hisabi da kiyayewa,
wanda iliminsa ke tsinkaya ga abinda ke cikin zukata, Masanin ababen da aka asirce, yana sane da abinda ke cikin qiraza, kuma izuwa gare shi kawai ake mayar da lamura,
ya qididdige wa bayi aiyukansu,
kuma ya qaddara musu ajalinsu.
Ina yabon Ubangijina kuma ina gode masa, akan falalolinsa da ni'imominsa da ba a qididdige su,
Tsarki ya tabbata ga wanda ya xaukaka ga barin abokan tarayya da kishiyoyi,
kuma masu girma da shugabanni su kan qanqan-da-kai ga qarfin mulkinsa,
kuma hanta da zuciya su kan tsattsage saboda girmansa,
kuramen duwatsu daskararru, kuma su kan faffashe saboda tsoronsa.
Tsarki ya tabbata ga Allah, gwargwadon yawan halittunsa, da iya yardar ransa, da nauyin al'arshinsa, da tawadar rubuta kalmominsa,
Tsarki ya tabbata a gare ka; Ubangijinmu, mamakin irin girmanka !
Tsarki ya tabbata a gare ka, saboda girman jin-kanka da rahamarka !!
Tsarki ya tabbata a gare ka, sunanka albarsa ta yawaita, kuma matsayinka ya xaukaka, babu kuma abin bautawa koma-bayanka !!!
           
Ina shaidawababu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, ka xaukaka daga barin kishiyoyi da kini da 'ya'ya.

kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanka ne manzonka, ya isar da manzanci, kuma ya sauke amana, ya kuma yi nasiha ga bayi.
Allah ka yi daxin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da kyautatawa, har zuwa ranar komawa (ga Allah, wato: qiyama).

Bayan haka:
Ya ku Bayin Allah… !!
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah Mabuwayi da xaukaka, a asirce da kuma a cikin ganawa, saboda ita ce wasiyyar Allah ga na farko da na qarshe, "Kuma haqiqa mun yi wasiyya ga waxanda ke gabaninku, da ku kanku, da cewa: ku ji tsoron Allah" [Nisa'i: 131].

Ya ku Mutane … !!
Ashe bai fi dacewa a gare mu (musulmai), mu riqa tuna Allah ba, muna yin tunatarwa ga kayukanmu,
muna masu sabunta alqawari da shi; ta hanyar tuba, da kuma horas da rayukanmu akan savawa bin son zukata, da lazimtar taqawa,
muna kuma jin cewa; Allah yana ganin bayi, da jin girmansa,
muna masu tuna hisabin Allah, da uqubarsa,
sai kuma mu yi tanadi, domin lokacin barin duniya, da kuma haxuwar wahalhalun barin duniya, da na farkon shiga lahira,
mu kuma yi guzuri domin shirin bijiro da mu ga Allah, "a ranar da mutum ke guje wa xan'uwansa, da kuma uwarsa da ubansa, da matarsa da 'ya'yansa, ga kowani mutum, a wannan yinin akwai sha'anin da ya wadace shi" [Abasa: 33-37].

Ya ku Bayin Allah … !!!
Tare da fantsamar ilimi, da cigaba ta fiskar sadarwa, da buxewar duniya, da qara zurfafa lamarin yaqar kwakwale (da addinai), da yawaita ko nau'antuwar hanyoyin sadarwa na al'umma, waxanda su ka yi kutse cikin gidaje, su ka wayi-gari a hannun qananan yara da manya, da maza da mata, = To, lallai musulmi yana buqatuwa, a karan-kansa, da tarbiyyar iyalan gidansa; wajen samun garkuwa da yin riqo DA TSORON ALLAH ta'alah, a zuciya, da jin cewa Allah yana ganinsa, domin tsoron Allah shi ne ke sanya shamaki tsakanin mutum, da aikata savo, kuma da tsoron Allah ne mutum zai cire kansa daga abubuwa na haram, ya kuma fiskanci aiyuka na biyayya, kuma tsoron Allah shi ne ginshiqin samun kowani matsayi, kuma sababi na aikata kowani aiki na xa'a, kuma tsoron Allah shi ke tabbatar da girman Allah a cikin zuciya.
Tsoron Allah a voye, matsayi ne daga cikin maxaukakan matsayi, kuma sifa ne daga cikin sifofi masu darajoji mafi girma, kuma da tsoron Allah ake samun ibadar taka-tan-tan (الورع), kuma tsoron Allah, bin dokokin Allah a jikinsa ke rataya, kuma shi ne hujjar da ta ke nuna imani, kuma shine abinda tauhidi da ikhlasi, su ke haifarwa, kuma tsoron Allah shi ne mavuvvugar kyawawan halayya, Mutum yana da buqatuwar samun tsoron Allah a aikace, domin ya iya rayuwa a matsayin mutum miqaqqe.
Tsoron Allah a voye shi ne abinda martabar IHSAN ta ke hukuntawa, wato, martabar ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, domin idan kai ba ka ganinsa, ai shi yana ganinka.

Yana daga ababen da tsoron Allah ke lazimtawa, JIN CEWA ALLAH YANA GANINKA, da samun ilimi ko jin cewa Allah yana gani kuma yana kula da zukatun bayinsa da aiyukansu, ya san idanu maha'inta, da abinda qiraza ke voyewa, kuma lallai Allah yana tare da bayinsa a duk inda su ka kasance, "Babu abinda ke kasancewa na ganawar mutane uku face shi ne na huxunsu, ko kuma biyar face shi ne na shidansu, ko kuma qasa da haka, ko fiye, face ya kasance tare da su, a duk inda su ka kasance" [Mujadila 7].
Saboda, duk wanda ya san cewa Allah yana ganinsa a duk inda ya kasance, kuma lallai iliminsa yana tsinkaya ga baxinin mutum da zahirinsa, da sirrinsa da abinda ya bayyanar, mutum ya kuma riqa halarto da hakan a lokacin da ya ke keve, to lallai hakan zai wajabta masa nisantar savo, a asirce.

Ya ku Bayin Allah … !!!
Tsoron Allah a voye shine mabuxan qofofin gafara, kuma a cikinsa akwai alkhairi mai yawa, da lada mai girma, "Lallai waxanda su ke tsoron Ubangijinsu a voye, suna da wata gafara, da kuma lada mai girma" [Mulk: 12].

Tsoron Allah a voye sababi ne na sauke yardarm Allah ga bawa, da kuma shiga cikin aljannoninsa, "Wanda ya ji tsoron Mai rahama a voye, kuma ya zo da zuciya mai tuba * ku shiga aljanna da salama, wannan yini ne na dawwama" [Qaf: 33-34].
"Lallai waxanda su ka yi imani, kuma su ka aikata aiki nagari, waxannan su ne mafi alherin halittu * sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne aljannonin zama, wanda qoramu su ke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi, wannnan sakamako ne, ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa" [Bayyinah: 7-8].

            Tsoron Allah a voye sifa ce daga cikin sifofin masu taqawa, "Kuma haqiqa mun baiwa Musa da Haruna littafi mai rarrabewa, da haske, da tunatarwa ga masu taqawa * waxanda su ke tsoron Ubangijinsu a voye, kuma su, dangane da lokacin qiyama masu tsoro ne" [Anbiya'i 48-49].

            Tsoron Allah a voye yana daga abubuwa masu warware tavewa, kuma yana shiryar da zukata zuwa ga aikata alkhairi, da karvar tunatarwa da nasiha, Allah ta'alah ya ce: "Lallai kana yin gargaxi ne ga waxanda su ke jin tsoron Ubangijinsu a voye" [Faxir: 18].
Kuma Allah ya ce: "Lallai wanda ke amfana da gargaxi shi ne wanda ya bi littafin tunatarwa, kuma ya ji tsoron Mai rahama a voye " [Yasin: 11].
Kuma Allah ya ce: "Da sannu, zai wa'aztu, Wanda ya ke tsoron Allah, * kuma zai nisanci tunatarwa, mutum shaqiyyi" [A'alah: 10-11].

            Tsoron Allah ta'alah a voye tana sanya wa'azi da tunatarwa da nasiha su zama suna da tasiri ga zukata da kuma jiki, "Allah shi ne wanda ya saukar da mafi kyan zance; littafi mai kamantacceniya (cikin kyansa da hukunce-hukuncensa), wanda ake maimaita shi (hujjojinsa da qissosinsa da hukunce-hukuncensa, kuma ake maimaita tilawarsa ba tare da qosawa ba), fatu ko tsikar jikin waxanda su ke tsoro Ubangijinsu suna kaxawa (saboda tasiri), sa'annan sai fatunsu da zukatansu su yi taushi zuwa ga ambaton Allah" [Zumar: 23].

            Kuma haqiqa Allah ya jarrabi imanin masu harama (da hajji ko umra) dangane da jin tsoronsa a voye, a inda ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani lallai ne Allah zai jarraba ku da wani abu; na abin farauta (r tudu), wanda hannunku da mashinku za su same su (a kusa da ku), domin Allah ya san wanda ke tsoronsa a voye (sai tsoron Allah ya sanya shi kamewa daga yin farautarsa)" [Ma'ida: 94].

            Ya ku bayin Allah … !!1
Lallai duwatsu, alhalin basa jin magana, kuma suna daskare, suna yin sujjada, kuma suna tsattsagewa, suna faxowa, saboda tsoron Allah, kuma kasancewarsu daskararru ko basu da hankali,
ko don kasancewar su ba mukallafai (da aka basu umurni da hani ba)  bai hana su ji, ko tasirantuwa da tsoron Allah ba,
kuma qarfi da sandarewa bai amfanar da su wajen fito-na-fito da wannan yanayi na tasirantuwa ba, "Kuma akwai daga cikin duwatsu, wanda qoramu su ke vuvvuga daga gare su, kuma daga cikinsu akwai wanda ke tsattsagewa; domin ruwa ya fita daga cikinsu, kuma akwai daga cikinsu, wanda ke gangarowa ya faxo domin tsoron Allah" [baqara: 74].
To, yaya su kuma mutane?
Kuma ina zukatansu su ke, idan an kwatanta da waxannan halittun?
Ina kuma hankulansu?

A UZU BILLAHI MINAS SHAIXANIR RAJIM:
"Da za mu saukar da wannan alqur'anin ga dutse, da ka gan shi, cikin kushu'i yana tsattsagewa saboda tsoron Allah, kuma waxannan misalai ne, waxanda mu ke buga su ga mutane, la'alla ko za su yi tunani" [Hashr: 21].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya shayar da zukata da addininsa da kuma tsoronsa,
Kuma zukata su kan qan-qan-da kai, domin fatan Ubangijinsu da tsoronsa,
Kuma, Ya shiryar da mu, da falalarsa da rahamarsa,

Salati da sallama su qara tabbata ga cikamakon manzanninsa da annabawansa

Ya ku bayin Allah … !!
Ku cika alkawari,
kuma ku yi tanadi domin gobe, saboda lahira ta fiskanto, duniya kuma ta juya baya, ajali kuma yana karatowa, tafiyar kuma tana da nisa, guzurin kuma ya yi kaxan, hatsarin kuma yana da girma,
Kuma ku sani, lallai a kanku akwai masu bada shaida, waxanda ba ababen tuhuma ba ne, su ne; gavovinku, sai ku kula da su, kuma ku bi dokokin Allah a asirce, da kuma a bayyane, saboda babu wani voyayyen da ke voyuwa ga Allah, kuma sirri a wurin Allah, a fili ya ke,

Ya ku taron musulmai… !!
Lallai tsoron Allah ta'alah a voye na yanyo daddaxar rayuwa ko sa'ida da natsuwa, da kuma hutu da kwanciyar hankali, kuma garkuwa ne daga fitintinu.
Kuma daxin hakan, a cikin zuciya, babu wanda ya san shi, sai wanda ya xanxane shi, sai mu yi azama, mu dage, mu kuma yi kwaxayin sabar wa rai jin tsoron Allah, a voye, da kuma hana rai aikata aibi, tare da horas da rai akan hakan, gabanin zuwan furfura, saboda zuciyar mutum, idan har ta cika da tsoro da girmama Allah mabuwayi da xaukaka, to sai gavvai su kame ga barin aikata savo.
Ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya ke ruwaito shi daga Ubangijinsa mabuwayi da xaukaka, cewa: "Na rantse da buwayata, Ba zan haxa wa bawana tsoro biyu da aminci biyu ba; idan bawana ya ji tsorona a duniya, sai in amintar da shi ranar qiyama, idan kuma ya aminta da ni a duniya, sai in tsoratar da shi ranar qiyama".
Kuma ya inganta daga gare shi (SAW): "Abu guda uku suna tseratarwa;  adalci a cikin halin fushi ko yarda, da tsakaita ciyarwa a halin talauci da wadaci, da kuma tsoron Allah a asirce da a bayyane".

            Kuma ku sani –Ya ku bayin Allah- lallai tsarkake zuciya, da samun tsoron Allah, sun rataya ne da gyaruwar zukata, domin "a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta vaci dukkan jikin ya vaci, ita ce zuciya".

            Sai ku nemi taimako akan samun haka, ta hanyar addu'a, kuma jagoranku abun koyi akan haka shine Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).

            Ya Allah! Ka bamu kaso daga tsoronka, wanda za ka shamakance tsakaninmu da tsakanin yin savo a gare ka, daga xa'arka kuma, irin abinda za ka isar da mu ga aljannarka, daga yaqinin kuma, abinda z aka sauqaqe mana musibun duniya da shi, kuma ka jiyar da mu daxi da jinmu da ganinmu da qarfinmu, har abada matuqar muna raye, kuma ka sanya su, su zamto masu wanzuwa daga gare mu, kuma ka sanya fansarmu ga wanda ya zalunce mu, kuma ka bamu nasara akan wanda ya yi adawa da mu, kuma kada ka sanya duniya ta kasance mafi girman burinmu, ko kuma qarshen iliminmu, kuma kada ka qaqaba mana –saboda zunubanmu- shugabannin da basa tsoronka, kuma basa jin qanmu, Ya mafi jin qan masu rahama!

Ya Allah! Lallai ne mu, muna roqonka, tsoronka a voye da a bayyanae, da kalmar adalci da gaskiya, a cikin yanayin fushi da kuma yarda, kuma ina roqonka tsagaita ciyarwa a cikin talauci da wadaci, kuma muna roqonka ni'imar da bata qarewa, da sanyin ido, wanda baya yankewa, kuma muna roqonka yarda da qaddara, kuma muna roqonka rayuwa mai sanyi bayan mutuwa, kuma muna roqonka jin daxin kallon fiskarka, kuma muna roqonka shauqin saduwa da kai, ba a cikin cuta mai cutarwa ba, ko kuma wata fitina mai vatarwa. Ya Allah! Ka qawata mu da qawar imani, kuma ka sanya mu, mu zama shiryayyu masu shiryarwa.

Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.

,,,          ,,,          ,,,


TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...