2018/05/31

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 17 Ramadana 1439H DR BUAIJAN 1 YUNI 2018












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 17/Ramadhana/1439H
daidai da 01/Yuni/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
DARARE GOMAN KARSHEN RAMADANA SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU SHINE MAFI GIRMAN BAUTA
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DARARE GOMAN KARSHEN RAMADANA SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU SHINE MAFI GIRMAN BAUTA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya sanya hanya ga wanda ya nemi tuba zuwa gare shi.
Wanda kuma ya mayar da lamura gare shi, ya ke sanya masa matabbata da mafi kyan wurin kailula.
Wanda kuma ya rayu cikin bautar Allah, ya kan sanya masa inuwa mai matabbaciyar lumshi; Don haka; wanda ya so, sai ya riki hanyar kirki zuwa ga UbangijinSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, ina mai girmama shi, kuma ina darajanta shi.
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, madalla da shi jagora kuma mai nusar da mutane hanya,
Allah ka yi karin salati a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa, da sallamar amintarwa mai tarin yawa.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku -Ya ku bayin Allah- da ni kai-na, da jin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, domin babu samun jin dadi da sa'ida sai ta hanyar takawar Allah, kuma ba a samun babban rabo sai ta hanyar da'a ga Allah Majibinci.

Sannan ku sani, Lallai da'a ko biyayyar Allah shine mafi alherin abinda aka ribata kuma aka aikata, samun yardarSa kuma, shine mafi alherin abinda aka ribata kuma abin nema, ita kuma Aljannah an kewaye ta da ababe masu wahala, Wuta kuma, an kewaye ta abinda Rai ke sha'awa. Kuma lallai za a cika ladan kwadagonku ne a gare ku, a ranar Kiyama; kuma duk wanda aka nisantar da shi daga Wuta, sai aka shigar da shi Aljannah to hakika ya samu babban rabo.

Ya ku masu azumi!!!
Allah ya karbi ayyukanku na 'da'a, kuma ya gyara halayenku (Amin), kuma ina rokonsa ya muku dace cikin abinda ya rage na wannan watan, kuma ya rubuta muku tabbatuwa akan biyayya a gare shi, a sauran kwanaki na rayuwa.

Ya ku taron Musulmai!!!
Ku ribaci lokaci iyakar ribata, ku yi gaggawan aikin alheri kuna masu sauri da rigaggeniya, saboda watanku mai karamci ya dau hanyarsa ta raguwa da tafiya, kuma dararensa da yininsa sun dau hanyar karewa da gushewa, Sai ku riski abinda ya rage daga cikinsa ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, kuma ku yi gaggawan tuba zuwa ga Ma'abucin girma da buwaya, Ya kaiton masu sakaci! Ya asarar tababbu batattu!! Ya musibar gafalallu!!!
Domin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya hau minbari sai ya ce: Amin! Amin!! Amin!!! Yayin da ya sauka, sai aka tambaye akan haka, sai ya ce: mala'ika Jibrilu ne ya zo min sai ya ce: Hancinsa ya bugi turbaya; Wanda ya riski watan Ramadana, sai ba a gafarta masa ba; har ya shiga wuta, kuma Allah ya nisanta shi daga rahama! Ka ce: Amin! Sai na ce: Amin!
Kuma hancinsa ya bugi turbaya; Wanda ya riski iyayensa biyu, ko kuma daya, sai bai musu biyayya ba, har ya mutu ya shiga wuta, Kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce: Amin, sai na ce: Amin!!
Kuma hancinsa ya bugi turbaya, wato Wanda aka ambaci sunanka a wurinsa sai bai maka salati ba, kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce: Amin, sai na ce: Amin!!!".

Ya ku taron Musulmai!!!
Lallai ayyuka ana sakayya ne akansu da abinda aka cike su da shi. Sai ku kara kokari, domin ba komai ba ne watan Ramadana, face kwanaki kidayayyu.
Kuma lallai kwanaki goman da suke gabanku sune mafificin lokatai, kuma  lokuta na musamman don aikata alkhairi da yin da'oi sune mafi girma, kuma su suka fi cancantar dacewa da yin kokarin bawa cikin ayyukan kusanci ga Allah.
Kuma duk da cewa ayyukan da'a a cikin sauran kwanakin wannan wata mai albarka suna da falala, sai dai a cikin kwanaki gomansa na karshe sun fi girman falala, kuma matsayinsu yafi daukaka, kuma sun fi lada mai gwabi.
Domin sune kwanaki goman da ake goge tuntube a cikinsu, a kankare munana, ake amsa addu'oi, kuma don haka ne "Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yake kara kokarin bauta a cikinsu irin abinda baya yinsa a waninsu, Kuma ya kasance idan wadannan goman suka shigo sai ya tamke kwarjallanSa, ya rika raya darenSa, yana tayar da iyalanSa".
Sai ku bayyanar da kwadayinku akan kwanakin, domin su ganima ce mai girma.
Kuma madalla da mutumin da ya samu rabo a cikinsu, kuma ya ribaci alkhairin cikinsu da falalarsu.

Ya ku Bayin Allah … !!!
A cikin kwanakin nan guda goma, akwai wani dare wanda yafi watanni dubu alheri, Rahama da jin-kai suna sauka a cikinsa, kuma ana amsa  addu'oi, ana kankare kura-kurai, ana gafarta laifuka, "Wanda ya tsayu a cikin wannan daren (yana sallah) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa".
Wanda kuma ya yi sakaci a lamarin wannan dare, sai aka haramta masa alkhairinsa, to shine abin zargi, marashin rabo.
Lallai shi ne, daren Lailatul kadr, abin neman mutane muminai, abin fatan samun salihai, burin masu takawa, wanda a cikinsa ake rubuta daukacin ababen da aka kaddara, kuma a cikinsa ake rarrabe kowani lamari da ake hukuntawa, Sai ku yi kwadayin tsayuwa a cikinsa da salloli, kuma ku zage domin nemansa, ku kara kwazo kan bidar dacewa da shi, kuma ku kankan-da-kai zuwa ga Allah a cikin wannan dare; saboda wannan daren –Wallahi- ganima ce ta cikin ruwan sanyi, domin yin ibada a cikin wannan dare yafi alheri akan ibadar watanni dubu.
Kuma ya dace, ga duk wanda ya nemi dacewa da wannan daren, ya zamto ba a tabar da shi ba, domin Allah Ma'abucin falala ne Mai girma; "Lallai Mu mun saukar da Kur'ani a cikin daren Lailatul kadr * To me ya sanar da kai abinda ake cewa Lailatul Kadari * Lailatul Kadari tafi alheri akan watanni dubu * Mala'iku da Ruhi (wato Jibrilu) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu, da kowane lamari * Aminci ne wannan daren, har zuwa fitowan alfijir" [Kadr, 1-5].


,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya sanya da'a a gare shi ta zama hanyar samun yardarSa, kuma ya sanya yardarSa ta zama hanyar rabauta da AljannarSa, kuma ya yi taufiki ga bayinsa muminai sai suka lazimci yin bauta a gare shi, suka kaurace wa jin-dadinsu da sha'awowinsu, suka fifita neman yardarSa.

Ya ku bayin Allah !! …
Itikafi shine lazimtar Masallaci domin yin ibada, da killace Rai daga sha'awowinta da jin-dadinta, da juya baya ga duniya da fitinunta, da abubuwa masu shagaltawa da masu dauke hankali. Da debe kewa ko kadaici ta hanyar ganawa da Allah -سبحانه-, da warewa gefe da ficewa daga jama'a da yanke huldodi, da barin wargi da wasa, da yin hisabi ga Rai, da sabunta ko jaddada alkawari tare da Allah, da kokarin tsarkake zuciya daga abinda ka iya makale mata na daudar da take cikin wannan rayuwar.

Kuma Allah Ta'alah ya shar'anta yin itikafi a cikin Masallatai, kuma ya yi umurnin a shirya Masallatan domin haka, a inda yake cewa: "Kuma muka yi alkawali zuwa ga Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake dakina, domin masu dawafi, da masu itikafi, da masu ruku'i, masu sujada" [Bakara: 125].

Ya ku bayin Allah…!!
Itikafi sunna ne, sai dai a cikin watan Ramadana yafi zama abin so, a gomansa na-karshe kuma yafi kasancewa abinda yafi karin karfi, saboda an ruwaito daga A'isha –Allah ya kara yarda a gare ta- lallai ta ce: "Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana, har Allah Mabuwayi da daukaka ya masa wafati, sa'annan sai matansa suka yi itikafin a bayansu", Bukhariy da Muslim.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi bn Umar –Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: "Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana".

Ya ku masu zuwa dakunan Allah (Masallatai)!!!
Masallatai sune dakunan Allah a doron kasa, Sai ku sane musu hakkokiknsu, ku ladabtu da laddubansu, kuma ku kiyaye wa masallatai matsayinsu da falalolinsu, domin an gina su ne domin bauta, sai ku yi aiki a cikinsu da ladabi da natsuwa, kuma kada ku rike su a matsayin wuraren wargi da wasa ko kamar kasuwa, kuma kada ku cutar da Masallata a cikinsu da masu itikafi, saboda cikin aikata hakan akwai hana su yin ibada, da kuma fitar da su daga cikin natsuwarsu.

Ya ku Ma'abuta itikafi!!!    
Kun zo dakunan Allah ne da nufin yin bauta, da yanke alakokin Duniya da fiskantar gidan Lahira, Sai ku fiskanci Allah da zukata masu mayar da lamura gare shi, masu cike da tsoronsa, kuma ku kankan da-kai zuwa gare shi tare da jin kaskanci, da rusunawa, da karayar zuciya. Kuma ku kiyayi abubuwan da suke daddatse muku hanya, ku kiyayi shagaltuwa da na'urorin komfiyutoci da wayan salula, da maganganun kila-da-kala. Kuma ku kiyaye wa Masallatai alfarmominsu.

Ya ku Ma'abuta itikafi a Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-!!!
Lallai ne babban ofishin ofishin kulawa da Masallatan Harami Biyu sun yi ayyuka tukuru ababen yabawa, wajen tarbanku, kuma sun shishshirya hawan ginin sama na Masallacin Annabi –صلى الله عليه وسلم- sun tanade shi, kuma sun kebance shi ga masu shiga itikafi. Kuma koyaushe suna cikin hidimarku, sai ku taimaki ma'aikatanmu; ta hanyar yin aiki da dokoki da tsare-tsare, don girmama Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, kuna masu yin hidima da aikata haka ga wadanda suka bakunce shi, masu taimakon bayin Allah akan ayyukan da'a, kuna masu fatan samun lada da sakayya, masu aiki da shari'a, saboda Allah Ta'alah yana cewa:
"Kuma a lokacin da muka iyakance wa Ibrahimu wurin daki, muka ce: Kada ka hada komai da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake dakina, domin masu dawafi da ma'abuta tsayuwar sallah, da masu ruku'i da sujada", [Haj: 26].

Allah! Ya karba muku irikafinku, da sauran dangogin ayyukanku na da'a.
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da …

,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...