2016/02/29

SHIN KA SAN? (هل تعلم؟)











SHIN KA SAN?
(هل تعلم؟)




TANADAR
MUHAMMADU AL'ANSAARIY
www.wesalhaq.tv






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
            Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin talikai, Mai rahama Mai jin qai, Salati da sallama su qara tabbata ga shuganmu Manzon Allah, da iyalansa, da sahabbansa, da wanda ya jivinci lamarinsa.
Bayan haka:

'Yan'uwa, a cikin imani!
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATU ALLAHI WA BARAKATUHU.

1-  SHIN KA SAN? Don wani abu ne, Allah ya halitta Mutum da Aljani?!

"Kuma ban halitta Aljani da Mutum ba face don su kaxaita ni cikin bauta" [Az-zariyaat: 56].

2-  SHIN KA SAN? Don me, Allah ya tayar da Manzanni?!

"Kuma haqiqa a cikin kowace al'umma mun tayar da wani Manzo, don ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci Xagutu" [Nahl: 36].

3-  SHIN KA SAN? Abu mafi muhimmanci, wanda Allah ya haramta shi ga bayinSa?!

"Ka ce: Ku zo, in karanta abinda Ubangijinku ya haramta, Wajibi ne a kanku, kada ku haxa shi da komai" [An'am: 151].

4-  SHIN KA SAN?  Zaluncin da yafi tsanani?!

"Lallai shirka zalunci ne mai girma" [Luqman: 13].

5-  SHIN KA SAN? Shirka tana lalata kyawawan aiyuka?!

"Kuma lallai ne haqiqa an yi wahayi zuwa gare ka, da kuma zuwa ga waxanda su ke a gabaninka, Lallai idan ka yi shirka aiyukanka za su vaci, kuma lallai za ka kasance daga masu hasara" [Az-zumar: 65].

6-  SHIN KA SAN? Cewa lallai Mushirkai sun riqi gumaka daga waliyyansu, wai domin su kusantar da su izuwa ga Allah (mabuwayi da xaukaka)?!

"Waxannan da suka riqi waxansu majivinta ba Shi ba, (suna cewa): Ba mu bauta musu ba face domin su kusantar da mu zuwa ga Allah kusantarwar daraja" [Az-zumar: 3 ].

7-  SHIN KA SAN? Lallai rayuwarmu babu makawa dole ta kasance don Allah (mabuwayi da xaukaka), kuma baya halatta mu haxa shi da komai?!

"Lallai ne sallata da yankana da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai * Babu abokin tarayya a gare shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon Musulmai; masu sallamawa" [An'aam: 162-163].

8-  SHIN KA SAN? Lallai sallar da muke yi da layyarmu babu makawa dole su kasance don Allah ne (mabuwayi da xaukaka)?!

"Sai ka yi sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (raqumi dominSa)" [Kausar: 2].

9-  SHIN KA SAN? Lallai wata halitta bata mallakar amfanar da mu, ko cutar da mu, idan ba Allah (mabuwayi da xaukaka) ba?!

"Kuma kada ka kirayi baicin Allah, abin da ba ya amfanarka, kuma baya cutar da kai. idan ka aikata haka, to lallai ne kai kana cikin azzalumai * Kuma idan Allah ya shafe ka da wata cuta babu mai yaye ta face Shi, kuma idan ya nufe ka da wani alheri to, babu mai mayar da falalarSa. Saboda yana samun wanda yake so daga cikin bayinSa da shi, Kuma shine Mai gafara Mai jin qai" [Yunus:  106-107].

10-        SHIN KA SAN? Wanda yafi dukkan Mutane vata?           

"Kuma wanene mafi vata fiye da wanda ke kiran wanin Allah wanda ba zai amsa masa ba, har ranar qiyama. Alhalin su gafalallu ne dangane da kiransu da ake yi" [Ahqaaf: 5].

11-        SHIN KA SAN? Babu wani da yake da ikon ya taimaki mabuqaci face Allah mabuwayi da xaukaka?!

"Ko kuma, Wanene yake amsawa mai buqata idan ya roqe shi, kuma ya sanya ku masu mayewa a bayan qasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah? Kaxan ne kwarai ku ke yi tunani" [Naml: 62 ].

12-        SHIN KA SAN? Dukkan ababen halitta basa mallakar komai daga lamarinka, kuma lamarin gabaxayansa na Allah ne (mabuwayi da xaukaka)?!

"Kuma waxanda kuke roqa WaninSa ba sa mallakar ko fatar jikin dabino * idan kuka roqe su ba za su ji roqonku ba, kuma ko sun jiya, ba za su amsa muku ba, Kuma a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku. Kuma babu mai baka labari kamar wanda ya sani" [Faxir: 13-14].

13-        SHIN KA SAN? Cewa lallai wani wanda ba Allah ba, baya mallakar daidai da kwayar zarrah? !

"Ka ce: Ku roqi waxanda kuke riyawa baicin Allah, basa mallakar daidai da kwayar zarrah, a cikin sammai, da a cikin qassai, kuma ba shi da wani abokin tarayya a cikinsu (sammai da qassai), kuma bashi da wani mai taimako" [Saba'i: 22].

14-        SHIN KA SAN? Cewa Waxanda Mutane suke neman taimakonsu, suna gajiyawa kan kowani abu, hatta kore quda ga kayukansu? !

"Ya ku Mutane! An buga wani misali sai ku saurara zuwa gare shi, Lallai ne waxanda kuke roqa baicin Allah, ba za su halitta quda ba, koda sun taru gare shi, kuma idan quda ya qwace musu wani abu ba za su iya kuvutar da shi ba daga gare shi. Da Mai nema da abun neman sun raunana" [Hajj: 74].

15-        SHIN KA SAN? Cewa babu wani abin da ke aukuwa a gare mu, ko ga wassunmu, sai da qaddarar Allah mabuwayi da xaukaka? !

"Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske ku, kuma ko da kun kasance ne a cikin ganuwowi ingantattu! Kuma idan wani alheri ya same su sai su ce: Wannan daga wurin Allah ne, kuma idan wata cuta ta same su sai su ce: Wannan daga gare ka ne, Ka ce: Dukkansu daga Allah ne, To me ya sami waxannan mutane, ba sa kusantar fahimtar magana?" [Nisa'i: 78].

16-        SHIN KA SAN? Cewa wanda ya yi shirka wa Allah ba zai tava shiga aljanna ba har abada? !

"Lallai ne lamarin shine, duk wanda ya yi shirka da Allah, to, lallai ne Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72].

17-        SHIN KA SAN? Cewa lallai su Mushirkai za a haramta musu ni'imar gani ko dubi zuwa ga Allah mabuwayi da xaukaka, ranar qiyamah? !

"Saboda haka wanda ya kasance yana fatan haxuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na qwarai, kuma kada ya haxa kowa cikin bautar UbangijinSa" [Kahf: 110].

18-        SHIN KA SAN? Cewa wajibi ne akan mumini bayan son Allah da manzonSa ya so masoya Allah, ya kuma qi maqiya Allah? !

"Lallai ne abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrahima da waxanda ke tare da shi a lokacin da suka ce wa mutanensu, Lallai mu babu ruwanmu da ku, da kuma abinda kuke bautawa baicin Allah, mun fita batunku, kuma qiyayya da jiyewa juna sun bayyana a tsakaninmu, sai kun yi imani da Allah shi kaxai" [Mummtahana: 4].

19-        SHIN KA SAN? Cewa lallai Allah mabuwayi da xaukaka ya hana mumini son kafirai? !

"Ya waxanda suka yi imani kada ku riqi Yahudu da Nasara majivinta, Sashinsu majivinci ne ga sashi, Kuma wanda ya jivince su daga gare ku, to lallai ne shi yana daga gare su, Lallai Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai" [Ma'idah: 51].

20-        SHIN KA SAN? Cewa lallai Allah mabuwayi da xaukaka ya haramta wa muminai yin sihiri? !

"Kuma (annabi) Sulaimanu bai yi kafirci (sihiri) ba, Saidai shexanun sune suka yi kafirci, suna karantar da mutane sihiri" [Baqarah: 102].
"Kuma lallai ne masihirta basa cin nasara" [Yunus: 77].
"Kuma mai sihiri ba ya cin nasara, a duk inda ya je" [Xaha: 69].

Qarshen addu'armu itace faxin:
ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.

Allah ya yi daxin salati ga shugabanmu kuma masoyinmu; Muhammadu, da iylanSa da sahabbanSa, kuma ya yi qarin sallama a gare shi.

2016/02/18

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 10 /JUMADAH AL'ULAH/1437H daidai da 19/ Fabarairu/ 2016m Ta Sheikh As-Subaitiy











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10 /JUMADAH AL'ULAH/1437H
daidai da 19/ Fabarairu/ 2016m




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
            Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya karrama Mutum, kuma ya sanya shi, ya zama khalifa a bayan qasa, Ina yin godiya a gare shi kuma ina yaba masa, a kan ni'imar imani da ta falala. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, kuma yin bauta a gare shi Shine manufar samar da halittu.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa; Ya tsarkake mu daga qulle mutane a rai, da hassada, kuma yansa zukatanmu suka zama lafiyayyu.
Allah ya yi qarin salati a gare shi da sallama, Shi iyalansa, da sahabbansa; waxanda suka kasance a kan mafi alherin xabi'a.  
Bayan haka:

Ina yin wasici a gare ku da Ni kaina da bin dokokin Allah,  Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].
Kuma Allah; Allah yana cewa:
"Kuma a lokacin da Ubangijinka yace wa Mala'iku: Lallai ne Ni zan sanya wani halifa a doron qasa" [Baqarah: 30].

            Lallai yana daga HIKIMAR ALLAH -wanda ya baiwa kowani abu halittarsa sannan ya shiryar- Sanya Mutum ya zame halifarSa, a doron qasa; Don ya tsayar da addininSa, ya kuma bayyanar da ababen mamakin da suka qunsu cikin halittarSa (Allah), da sirrace-sirracen da suke cikin halittarSa, da kyawawan hikimominSa, da nau'ukan amfanin da suke cikin hukunce-hukuncenSa.
            Kuma, shin akwai wata alama ko aya bayyananniya; da ta ke nuna kamalar Allah (تعالى), da yalwar iliminSa fiye da WANNAN MUTUM; wanda Allah ya halitta shi cikin mafi kyan halitta?        (Amsar itace: A, a!).
            RAHAMAR ALLAH DA SUNNARSA CIKIN HALITTUNSA Sun hukunta ya bada mayewa a kan doron qasa, ga wanda ya nufa daga cikin bayinsa "Lallai ne qasa ta Allah ce, yana gadar da ita ga wanda ya nufa daga cikin bayinSa" [A'araf: 128].
            Kuma lallai ne bada mayewa a doron qasa (halifanci) jarraba, ce, Allah (تعالى) yana cewa:
"Akwai tsammanin Ubangijinku ya halaka maqiyanku, sai ya baku mayewa a doron qasa, don ya gani yaya za ku aikata!" [A'araf: 129].
            Kuma yana gaje qasa ne, Wanda ya kyautata tsayuwa da abinda khilafanci  ya wajabta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai ne haqiqa Mun rubuta a cikin littatafai, baicin alqur'anin, cewa Lallai ita qasa bayiNa salihai ne, su ke gadonta" [Anbiya'i: 105].

            MAYEWA A BAYAN QASA (ko halifanci): Yana hukunta: Yin bauta wa Allah, da aiki da tsarin Allah (wato, shari'arSa), da gyaruwa da kawo gyara, da rayar da qasa, da kuma gina rayuwa da zantuka da aiyuka, da sana'antawa, da neman ilimi, da ilmantarwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Suna yin bauta a gare Ni; basa haxa komai da Ni" [Nur: 55 ]. Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah ya yi alqawari ga waxannan da suka yi imani daga cikinku, kuma suka aikata aiyukan kwarai, lallai zai shugabantar da su a doron qasa" [Nur:  55].

            Kuma lallai haqiqa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya buga misalin Mutum MUMINI, da itaciyar dabino; kowani abu a jikinta mai amfani ne. Su kuma muminai fiskokin amfaninsu da amfanarwarsu, da kuma tasirunsu a cikin al'umma suna banbanta; daga mutum zuwa mutum, Allah (تعالى) yana cewa:
"Shin ba ka gani ba, yadda Allah ya buga wani misali; Kalma mai kyau, kamar bishiya ce mai kyau; tushenta yana tabbatacce, Ressanta kuma suna cikin sama * Tana bayar da abin cinta, a kowani lokaci da izinin Ubangijinta" [Ibrahim: 24-25].
            Shi mumini dukkansa alkhairi ne, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"A kan kowani Musulmi akwai sadaka, Sai aka ce: To idan bai samu ba fa? Sai ya ce:
Yayi aiki da hannayensa; sai ya amfanar da kansa, ya kuma yi sadaka.
Sai ya ce: To idan bai samu iko ba fa? Sai ya ce: Ya taimaki ma'abucin buqata; wanda aka zalunta.
Ya ce: Sai aka ce masa: To idan bai samu iko ba fa?
Sai yace: Ya yi umurni da kyakkyawa, ko da alkhairi.
Ya ce: To idan bai aikata ba fa?   Sai ya ce: Sai ya kame daga aikata sharri; don yin hakan sadaka ne".

            Shi kuma Musulmin da ya karvi musulunci a matsayin addini: Saqon da yake xauke da shi zai wayi-gari: Aiki ne da wannan addinin, da yin da'awa ko kiran mutane izuwa gare shi, da amfanar da halittu.
Kuma da aikata haka ne kawai Musulmi zai kasance mutum mai amfani; wanda ya ke haifar da alkhairi, ya ke kuma fiskantar abu mai daraja; na biyayya. Ya kuma wayi-gari yana haskakawa da wani haske, yana zuwa da albarka; saboda zuciyarsa tana cike da qauna, Harshensa kuma shatab yake da bayyanar da soyayya, Hannunsa ya shumfuxa ni'ima da shi,  Yana bada ni'ima kuma ya shumfuxa fiska ga duk wanda ya haxu da shi. (irin wannan) ana fatan samun alkhairinsa, tare da amintuwa daga sharrinsa.

MUSULMI yana rayuwa ne saboda wani saqo mai girma, da wata manufa maxaukakiya, yana yin rayuwarsa don ita, yana iya fiskantar kowani abu a hanyarsa ta tabbatar da ita, yana kuma tabbatar da gamammen maslaha, kuma yana jiran samun aminci a qarqashin haka, (Musulmi) yana aikinsa saboda saqon da ya ke xauke da shi; ba wai don kuxi ba, kuma ya kan yi hidima daga cibiyar aikinsa, yana mai rayar da saqonsa, kuma yana yin rayuwa da shi.

Kana iya ganin Mutum mai lafiyayyen jiki, mai cikakken qira, saidai kuma yana cikin ximuwa a rayuwa; saboda babu wata manufa da yake tafiya da ita, ko wani aikin da yake aikata shi, haka kuma, Bashi da wani saqon da yake ji da shi ko yake sadaukar da ransa don ganin tabbatuwansa. Imam As-Shafi'iy (رحمه الله) yana cewa:
"Idan har baka shagaltar da ranka da gaskiya ba, sai ta shagaltar da kai da varna".
Kuma daga tunbin "zaman banza" ake kyankyasar "munanan halaye".

            Wanda yake xauke da "Saqo" ya kan fara qoqarin gyara kansa, da yi mata hisabi, saboda duk wanda ya yi watsi da kansa, ya bar "hisabi a gare ta", sannan ya doge cikin gafala, ya runtse idanuwansa daga sakamakon da zai kasance a qarshen lamura, ya shantake kan faxin "Allah Mai afuwa ne", to sai ya bijirar da kansa ga halaka.

            (Daga nan), Sai "Saqon da Musulmi" ke xauke da shi ya tafi zuwa ga: xoruwar amfani, da qoqarin gyara wani, ko wassu, tare da basu kulawa, cikin gaya ko manufa maxaukakiya, da babbar himma, ta bada kariya ga addini, da yin hidima ga al'ummah, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Lallai ne Allah (تعالى) yana son lamura maxaukaka masu girma, kuma yana qin qananan lamura".

            Wanda yake xauke da wani saqo: Yana tarbiyyantar da kansa akan qarfin nufin aiki da umurnin Allah, da tsayuwa da abinda ya wajabta, da rashin qetare iyakokinSa, yana kuma nisantar bin son zuciyarsa da sha'awowinsa.

            SHUGABA MUSULMI Saqonsa a cikin rayuwa shine, qoqarin tabbatar da maslahohin waxanda yake shugabanta; ta hanyar tsayar musu da adalci, da tabbatar da gaskiya. Kuma shugaba (wajibi ne akansa) ya yi qoqarinsa wajen aikata duk abinda zai amfani talakawansa, da tunkuxe musu abinda zai cutar da su a cikin addininsu da duniyarsu, Sa'an nan ya kame hannayen wawayen Mutane da fasiqai, ya tsawatar da su aikata savo da zalunci da aikin kara-zube.

            MALAMAI Saqonsu a cikin rayuwa yana da girma; saboda sune halifofin Manzanni, kuma magada annabawa. Kuma wajibi ne akan ma'abuta ilimi su kare al'umma daga cutar jahilci, ko rugujewar aqidu da lalacewansu. Sannan su riqa haskaka hanyoyi(wa Mutane); ta hanyar yaye musu shubuhohi (da abubuwan da suka shige musu duhu), suna ilmantar da Mutane lamuran addininsu; Saboda shi malami yana gyara abinda Mutane suka vata ne, yana kuma faxakar da su izuwa ga alkhairi, yana yin umurni da kyakkaya, yana hani kan munkari da abin kyama, yana kuma yin haquri kan cutarwa.

            MAI BADA TARBIYYA MUSULMI Shi kuma xawainiyar da take wuyansa itace: Ya zana misali ingantacce, na Musulmin kirki; ta hanyar gyara halin da ake ciki, da tarbiyya wa 'ya'ya da jikoki, ko aikin misalta mai halayya maxaukaka; domin saqonsa ya isa izuwa ga kowace zuciya, kuma ya tsaftace aqidu da tunani, da busa sabuwar rayuwa gangariya cikin rayuwa; saboda halayen mai bada tarbiyya ababen koyi ne, aiyukansa kuma adalci ne da hikima, matsayoyinsa kuma, abu ne mai falala.

            ITA KUMA MACE MUSULMA Saqonta a cikin rayuwa shine: Kula da kyawawan halaye a cikin al'umma; wajen gina su (a cikin zukatan yara) da basu kariya, da kuma samar da al'umma ta gari, kamar mata, da uwa tagari; ta yadda matar za ta kasance nitsuwa ce da kwanciyar hankali da aminci ga mijinta, Sannan ta sanya gida ya zama mazaunin walwala, kana matabbatar qauna da tausasawa; tana mai bada kula ga 'Ya'ya da tausasawarta da kuma soyayyarta.
Mace musulma tana tarbiyyantar da yaranta ne akan manufofin Musulunci, da kyawawan halaye, ta kan hakaito musu da qissoshin annabawa, da manyan mutanen da aka yi a tarihin Musulunci, tana kuma fahimtar da su addini, tana kuma bayyana musu shiriyar shugaban Manzanni (S.A.W).

            SHI KUMA SAURAYI MUSULMI ; yana jin buwaya da Musuluncinsa, yana kuma qarfafa imaninsa, yana fahimtar addininsa, tare da tafiya akan karantarwarsa, yana katange hankalinsa, yana kuma yin aiki don gyara kansa, yana kuma kiyaye zaman lafiyan al'ummarsa da amincinsu, ya tsaftace zuciyarsa, ya kuma gyara aibukansa, yana kuma fahimtar ababen da suke aukuwa ko wakana, tare da sanin cewa yana da saqon da yake xauke da shi, da kuma gudumawar da zai bayar a cikin rayuwa. Yana kwasar ilimi daga mavuvvugarsa, a cikin kowani fannin ilimi da (تخصص).  

            SHI KUMA MUSULMI A GARURRUKAN DA BA NA MUSULMAI BA: Xawainiyar da take wuyansa tana da girma: Ta fiskar ya bada misalin Musulunci cikin aiki da halayya, da kuma hukunce-hukuncensa, ya kuma gabatar da hoton Musulunci mai haske, da sauqinsa mai shiryarwa, a cikin aqida da halaye; saboda su Musulmai (a ko-yaushe) sune mafi alherin Mutane ga Mutane, kuma sune Mutanen da suka fi dukkan Mutane tausayi.

            HANYOYIN SADARWA NA MUSULMAI Saqon da suke xauke da shi yana da girma, saboda girman tasirin kafafen, da yadda suke isa ga Mutane dayawa; (Suna da babban aiki) wajen isar da saqon Musulunci, da bayyanar da  abubuwan da ya ginu akansu, tare da baiwa Musulunci kariya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai Manzo! Ka isar da abinda aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, idan baka aikata ba to baka isar da saqonsa ba, Kuma Allah zai tsare ka daga Mutane. Lallai ne Allah baya shiryar da Mutane kafirai" [Ma'idah:  67].
Hanyoyin sadarwa suna yin hidima wa Musulunci; cikin zance da aiki, suna yaqar karkacewa da ilhadi da munanan aiyuka, suna kare hankali da ruhi da zuciya daga munanan halaye, da dauxar ficewa daga karantarwar addini, da kuma bayanin jinsin vatan da suke cikin karkatattun aqidu.

            SAQON GARRURUKA KO AL'UMMAR MUSULMAI zuwa ga duniya saqon aminci ne da tausasawa, da zaman lafiya.
Kuma lallai (As-Salam; wato: Mai bada aminci) suna ne daga cikin sunayen Allah masu kyau.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zo don ya zama aminci da rahama; kuma don tsamar da Mutane daga duffai izuwa ga haske, Kuma ya xaukaka su zuwa ga martabobi maxaukaka a cikin halayya; kamar cika alqawari, da hana zalunci da qetare iyaka, da tsayar da adalci, da tunkuxe zalunci.

            Kuma lallai ne al'umma zata gaza sauke saqon da ke wuyanta a lokacin da suke shantaqewa cikin wadaci da ni'imomi da wuraren wargi (da wasa), suka kuma dulmuya cikin sha'awowinsu da jin daxinsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Sunnar Allah ne ga waxannan da suka shuxe gabaninka, kuma ba zaka samu wani canji ba ga sunnar Allah" [Ahzab: 62].

            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai  * Mai rahama mai jin qai  * Mamallakin ranar sakamako.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,  abun bautan na farko da na qarshe.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, majivincin masu taqawa.
Allah yayi daxin salati da sallama a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa gabaxaya.
Bayan haka:

Ina yin wasici a gare ku da Ni kaina da bin dokokin Allah,  Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi Imani ku bi dokokin Allah, kuma ku faxi Magana ta daidai   *   Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, Kuma wanda ya yi biyayya wa Allah da ManzonSa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71 ].

Yana daga abubuwan da suke hana musulmi sauke saqon da yake wuyansa: TUNKUXUWA A BAYAN ABABEN DA SUKE YIN RUXI A RAYUWAR DUNIYA, DA FITINTINUNTA, Kuma babu wani abin da yafi lalata zuciya fiye da rataya zuciya ga duniya, da karkata izuwa gare ta, da fifita ta akan lahira.
            Ruxin duniya, da aukawa cikin tarkonta yana zaunar da Musulmi daga zaquwa zuwa ga lahira, da yin aiki don ita, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane, lallai ne alkawarin Allah gaskiya ne; kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma kada mai ruxi (Shexan) ya ruxe ku daga Allah" [Luqman: 33]. Kuma Allah (تعالى) ya ce: "A'aha! Ba haka ba, Kuna son mai gaggawa ce (wato: Duniya) * Kuma kuna barin gidan qarshe; (Lahira)" [Qiyamah: 20-21].

            Kuma yana daga abubuwan da suke hana Musulmi sauke saqon da yake wuyansa: Zama da ma'abuta wargi, da kuma kutsawa cikin mas'alolin ilimi masu tsaurin fahimta, ko kuma cikin mas'alolin da basu auku ba, saboda neman tayar da fitina. Alhasan Albasariy (رحمه الله):
"Ashararen bayin Allah sune waxannan da suke bin mas'aloli masu sharri, suna makantar da bayin Allah da Su". Kuma Al'auza'iy yana cewa:
"Lallai ne Allah idan ya nufi ya hana wani bawansa albarkar ilimi, to sai ya jefa mas'aloli marasa fa'ida (magalix) akan harshensa. Kuma lallai na ga irin waxannan Mutane su ne Mutanen da suka fi qarancin ilimi".

انتهى. 
Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
            Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka aljanna, da abinda yake kusantarwa zuwa gare ta, na zance ko na aiki, kuma muna neman tsarinka daga wuta, da kuma abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko na aiki.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta rayuwarmu take, kuma ka gyara mana lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, ka sanya rayuwa ta zama qarin alkhairi ne a gare mu, mutuwa kuwa ka sanya ta hutu ne a gare mu daga kowani sharri. Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka shiriya da taqawa da kamewa da wadaci da arziqi.
            Ya Allah! Ka taimake mu kada ka taimaki wassu akanmu, ka bamu nasara kada ka bada nasara ga wassu akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla ma wassu akanmu, ka shirye mu, kuma ka sauqaqe shiriyarka a gare mu, kuma ka taimake mu akan wanda ya yi zalunci akanmu.
            Ya Allah! Ka sanya mu zama masu ambatonka, masu yin godiya a gare ka, masu qanqan da kai a gare ka, masu yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
            Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, ka tabbatar da hujjojinmu, kuma ka daidaita harshenmu, ka zare dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imarka, da canzuwar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan abinda zai sanya ka fushi.
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da rahamarka da falalarka da arziqinka.
            Ya Allah! Ka yi mana albarka cikin shekarunmu, kuma ka sanya mana albarka cikin matanmu, da 'ya'yanmu, da zurriyarmu, da aiyukanmu da shekarunmu, ka sanya mu; mu zama masu albarka a duk inda muke, Ya Ubangijin talikai.   
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka tabbatuwa cikin lamarin addini, da kuma azama akan aikin shiriya, da ribatar kowace biyayya, da kuvuta daga kowani savo, da rabauta da aljanna, da kuvuta daga wuta.
            Ya Allah! Ka taimaki wanda ya taimaki addini, kuma ya Allah ka tavar da duk wanda ya tavar da musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka taimaki addininka da littafinka da sunnar annabinka da kuma bayinka muminai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulmai… a kowani wuri, Ya Ubangjin talikai, Ya Allah! ka kasance wa musulmai… a qasar Sham Ya mafificin masu jin qai, Ya Allah! Ka kasance musu Mai qarfafawa, Mai taimako, Mai tallafawa, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ubangijin gaskiya, Ya Allah wanda ya saukar da littatafai, mai gudanar da gajimare, wanda ya rusa rundunoni, ka kwace nasara daga maqiyanka; maqiyan addini, kuma ka taimaki musulmai akansu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi! Ka taimaki musulunci da ma'abotansa, a kowani wuri.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada lafiya ga majinyatanmu, ka yaye baqin cikinmu, ka sunce fursunoninmu, ka jivinci lamarinmu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka yi dace wa shugabanmu da abinda kake so, kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shugabanmu mai hidimar harami guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu, Kuma ina roqonka ka datar da na'ibansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, lallai kai mai iko ne akan  komai.
            Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai gabaxaya wajen yin aiki da littafinka, da yin aiki da shari'arka, Ya mafificin rahamar masu rahama.
            Ya Allah! Kai ne abin bauta; babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma faqirai, ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! Shayarwar rahama, ba shayarwar azaba ko bala'i ko rusau, ko dulmuya ba, Ya Allah! Ka rayar da garurruka da shi, ka bada ruwan sama ga bayi, ka sanya shi ya kai birni da qauye, Ya mafificin rahama masu rahama.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da imani, kada ka sanya a cikin zuciyarmu wani qulli ga waxanda suka yi imani; Ya Ubangijinmu lallai kai ne Mai tausasawa ne Mai rahama" [Hash,ri: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...