2016/08/18

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) 16/ZUL KA'ADAH/1437H Daidai da 19/Augusxus/2016M ta LIMAMI HUSAIN ALU AL SHEIKH








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 16/ZUL-KA'ADAH/1437H
Daidai da 19/Agusxus/2016M



LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALU- AL SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
GIRMAMA WURAREN BAUTAR ALLAH DA ABUBUWAN DA YA BASU ALFARMA, A CIKIN HAJJI
     Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Alu As-sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a, 16 zulqi'idah, 1437H, mai taken: GIRMAMA WURAREN BAUTAR ALLAH DA ABUBUWAN DA YA BASU ALFARMA, A CIKIN HAJJI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna kan farlanta hajji, da manufofin shari'a wajen shar'antata, kuma lallai maxaukakin manufa na shar'anta hajji shi ne kaxaita Allah mabuwayi da xaukaka, kuma lokacin hajji, dam ace na jaddada lamarin haxin kan al'ummah, kuma wajibi ne akan kowa, Yin taimakakkeniya wajen aiki da dokokin da su ke kawo tsari a cikin hajji, da lokacin umrah, Sannan ya tsawatar kan voye sharri ga mahajjata da masu umrah.
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah, a farko, da qarshe.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya a lahira da duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawan Allah ne, kuma manzonSa zavavve.
Ya Allah ka yi qarin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa masu cika alqawari.

Bayan haka:
Ya ku musulmai!
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah da taqawarsa (جل وعلا), da yin za'a a gare shi, a sirrance da a bayyane, domin ita ce: Nasara mai girma, da tsira mafi xaukaka.

Ya ku taron Musulmai!
Su ibadodi a cikin musulunci, suna da FA'IDODI manya da suke cimma wa, da MANUFOFI masu girma.
Kuma lallai AIKIN HAJJI ta fiskar manufofi ya tattara waxanda suka fi xaukaka ne daga cikinsu, da hadafi masu girma.
Kuma lallai manufar hajjin xakin Allah da ta fi hasken xaukaka, ita ce:  TABBATAR DA TAUHIDIN ALLAH, DA KUMA BARRANTA DAGA SHIRKA: Saboda a cikin jerin ayoyin da suke magana kan hajji Allah yana cewa: "Suna masu karkata zuwa ga Allah; ba waxanda suke yin shirka a gare shi ba" [Hajj: 31].
Ma'ana: Suna karkacewa; su bar kowani addini karkatacce, izuwa ga addinin gaskiya, suna masu ikhlasin addini ga Allah, da kuma yin bara'a daga bautar duk wanda ba Allah ba.

            'Yan'uwa Musulmai!
            Aiyukan da ake yi a cikin hajji, suna koyar da Musulmi cewa ya kasance abin fiskanta cikin zantukansa da aiyukansa da dukkan motsawarsa da hanyoyinsa na rayuwa, yana mai cikakken fiskantar Allah (سبحانه); a zahiri da baxini "Kuma kowace al'umma mun sanya mata yanayin bauta, da wurin yinsa domin su yi zikiri –wato su ambaci sunan Allah- akan abinda ya azurta su, na dabbobin ni'ima; Kuma abin bautarku abun bauta ne guda xaya, kuma a gare shi ne kawai za ku miqa wuya" [hajj: 34].

            Babban tambari ko bajin da ya zama alama ga hajji, wanda kuma hajjin ya banbanta da shi, shine: Amsawa Allah da kalmomin talbiyya (wato: LABBAIKA ALLAHUMMA LABBAIKA); Wanda ma'anoninsa suka qunshi: Tabbatarwar da Musulmi ke yi a cikin zuciya da rayuwa, da zance da aiki, cewa: Zai yi kammalallen girmama Allah, da cikakken qasqantar da kai, da kuma so wanda ya kai maqura, ga Allah (سبحانه), kuma zai yanke komai don yin biyayya a gare Shi, da yin aiki da umurninSa, da cikakken sallamawa ga shari'ar Allah.
Umar (رضي الله عنه) ya ce, a lokacin da ya sunbanci hajaru Al-aswad: "Wallahi! Lallai ne ni, na san kai dutse ne baka cutarwa kuma baka amfanarwa, kuma ba don naga Manzon Allah yana sumbantarka ba, to da ban sunbace ka ba".
            A lokacin yin xawafi kuma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana shiryar da mu cewa idan mun zo yin raka'oi guda biyu na xawafi/ mu karanta (Qul ya ayyuhal kafiruna) a raka'ar farko, domin tabbatar da raba hanya tsakanin turbar tauhidi da hanyoyin shirka, da nau'ukansa da sabubansa da hanyoyinsa. A raka'a ta biyu kuma, sai mu karanta (Qul huwal lahu ahad) wanda ta ke tabbatar da tauhidi da nau'ukansa guda uku.
            Kuma kamar haka ne, tafiyar hajji a dukkanin matakanta, kuma cikin dukkanin aiyukanta ta ke yin dashen ikhlasi ga Allah (سبحانه) cikin zukata, da yin biyayya a gare Shi, da sonSa, da jin tsoronSa, da fatan samun ladanSa.
Ibnu-Rajab yana cewa: ((Yana daga abinda wajibi ne nisantarsa ga mahajjaci, kuma sai da shi hajjinsa ke zama MABRUR: Kada ya nufi riya ko sum'ah da hajjinSa –wato yin ibada don a ji, ko a gani-, ko kuma alfahari ko jiji-da-kai, da girman kai, kuma kada ya nufi komai da shi sai fiskar Allah, da neman yardarSa, kuma ya yi tawali'u cikin hajjinsa, ya kuma nitsu, ya yi kushu'i ko qanqan-da-kai ga UbangijinSa; saboda an ruwaito daga Anas cewa: Lallai ne Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi hajji akan dabbar hawa, mai tsofaffin kaya, da katifar da bata wuce dirhami huxu ba, kuma ya ce: Ya Allah! Ka sanya shi ya zama hajjin da babu riya, babu sum'a a ciki!!!)).

            Don haka; Abinda yake madogara ga hajji shine, Samun faraga ko lokacin yin ambaton Allah (wato: zikiri), da girmama shi, da yin yabo a gare shi, da nuna karaya a gaba gare shi, da halartowar qanqan-da-kai a gare shi (سبحانه) a wajen aikata kowani aiki, daga cikin aiyukan hajji, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kowace al'umma mun sanya mata yanayin bauta, da wurin yinsa domin su yi zikiri –wato su ambaci sunan Allah- akan abinda ya azurta su na dabbobin ni'ima" [Hajj: 34].
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mafificin hajji shine, ajju da sajju". "Ajju" kuma shine: Xaga sauti lokacin yin kabbarori da talbiyyah.
Kuma Ahmad da Tirmiziy da Abu-dawud sun fitar, cewa lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne an shar'anta yin xawafin Xakin ka'abah, da kuma tsakanin Safah da Marwah, da jifan duwatsu domin tsayar da zikiri (wato: ambaton Allah)".
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan kuka gangaro daga arafaat, sai ku ambaci Allah (zikiri) a mash'arul haram -Muzdalifa-, kuma ku ambace shi saboda shiryar da ku da ya yi" [Baqara: 198].
"Sa'annan sai ku gangaro ta wurin da sauran mutane ke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, Lallai ne Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Baqara: 199 ]. A nan kuma abinda ake nufi da "gangarowa" shine: ifada ko gangarowa daga Muzdalifa, a xayan zantuka biyu da yafi inganci.
Dangane da aiyukan hajji kuma Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma idan kuka kammala aiyukanku na hajji, sai ku ambaci Allah -zikiri- kamar yadda ku ke ambaton iyayenku, ko kuma ambaton da ya fi haka yawa" [Baqara: 200].

            Ya ku taron Muminai!
            Lallai hajji kamar baji ne mai girma, da ke tunatar da al'umma gabaxayanta, kan: Girmama ababen da Allah ya basu wata alfarma, da kuma tsayuwa a kan shari'arSa; da bin tsari ko dokokin Allah, "Duk kuma wanda ya girmama wuraren bauta wa Allah, to lallai su suna daga taqawar zukata" [Hajj: 32].
Kuma babu tsira ga al'ummarmu a yau, daga abinda ta samu kanta a cikinsu na fitintinu da musibobi, sai lokacin da waxannan manufofin suka samu tabbatuwa a cikin rayuwarta, kuma suka yi aiki da su a cikin sha'anoninsu, aqidarsu ta zama garau, haryar tafiyarsu ko manhaji ya zama akan sawaba (ta dadai), da kyakkyawar hanya cikin halayya, Sai al'umma ta rayu cikin izza, mai kwar-jini, maxaukakiyar geffa, da matsayi, wacce halinta zai rabauta.

            Kuma daga ibadar hajji, Al'umma ya da ce ta fahimci cewa: lallai yana daga cikin manya-manyan manufofi na shari'oin addini: Samar da kaxaitaka ta imani da 'yan'uwantaka ta musulunci, wanda bata san qabilanci ko vangaranci ba, Kawai 'yan'uwantaka ce da ta ke tsayuwa akan maslahohin addini da duniya, akan mafi kyan hali, "Tabbas Muminai 'yan'uwan juna ne",  [Hujuraat: 10].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "'Xayanku baya zama mai imani sai ya so wa xan'uwansa abinda yake so wa kansa".
Kuma da haka ne, Al'umma za ta san cewa lallai yadda ta samu kanta a wasu wurare ko wajen wasu 'ya'yanta bai yi daidai da addini ba, kuma baya dacewa da manufofinsa, saboda ta yaya Musulmi zai kafirta xan'uwansa, kuma ta yaya zai zubar da jininsa? Ko ya keta alfarmar mutuncinsa, ko ya xauke dukiyarsa?
Hajji makaranta ce, wacce daga abinda aka koya a cikinta  Tsare-tsaren maqiyan musulunci da suke tsattsarawa domin kekketa wannan al'ummar, ko su raunata sha'aninta, ko su yi gunduwa-gunduwa da vangarorinta, ko don rarrabe al'amarinta, da kuma watsa kashinta, domin bala'i ya auku, a kuma faxa cikin wahala = Hajji makaranta ce da idan an bi darrusanta za su rurrushe tsare-tsaren maqiyan musulmai.

            Ya ku taron Musulmai!
            Lallai wannan daula mai albarka (Masarautar larabawa ta Saudia) tana samun qarin xaukaka, da yin hidima ga mahajjata, tana ganin hakan a matsayin wajibi da ya doru a wuyanta ta fiskar addini, kuma qara samun xaukaka, a duniyance. Kuma wannan qasar don ganin tabbatuwan haka tana bayar da duk wani abu mai tsada, ga duk abinda zai tabbatar da hutu ko amfani ga baqin Allah (Mai rahama), waxanda suka nufo masallacinsa (mai alfarma).
            Kuma wajibin kowani musulmi ne ya girmama waxannan wurare masu tsarki, kuma ya kula da alfarmar su da suka tabbatu a cikin littafin Allah da Sunnah, da ijma'i. kuma ya yi kwaxayin samar da aminci da zaman lafiya ga musulmai, da hutu a gare su, saboda yana daga manya-manyan laifin alkaba'ira: Cutar da baqin Mai rahama (wato: mahajjata), da qunsa nufin sharri a gare su, "Wanda a cikin harami ya yi nufin karkata da zalunci, za mu xanxana masa daga azaba mai raxaxi" [Hajj: 25].

KUMA YANA DAGA CIKIN WAJIBIN MUSULMAI:
  Su yi aiki da dukkan tsarin da zai tabbatar da maslahar musulmai cikin hajjinsu, ya kuma tunkuxe musu dukkan abinda zai cutar da su; YANA KUMA DAGA CIKIN HAKA: Yin aiki da takardun izinin isa wuraren aiwatar da aikin hajji, saboda aikata hakan an gina shi ne akan qa'idar WAJABCIN TAIMAKAKKENIYA CIKIN BIYAYYAR ALLAH DA TAQAWA, Kuma duk abinda musulmai suka haxu wajen ganin kyansa, to mai kyau ne.
Sai musulmi ya kiyayi yin wayo ga hakan, ko kuma sakaci wajen tabbatuwansa; saboda maslahar al'umma gabaxayanta, ana rinjayar da ita akan maslahar xaixaiku, wannan kuma har a cikin ibadodi na nafilfili, kamar yadda ILIMIN SANIN MANUFOFIN SHARI'A  ya yi nuni akan haka.

            'Yan'uwan Musulunci!
            A cikin hajji, akwai gyaran xabi'u, da kuma tsarkake rai daga dukkan sifofi munana, da hanyoyi ababen kyama, waxanda suke iya cutar da musulmi a addinance ko a duniyance, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya niyyaci hajji a cikin watannin, to babu kwarkwasa, kuma babu fasikanci, kuma babu jidalin jayayya a cikin hajji" [Baqara: 197].  
Kuma Manzo (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci wannan xakin –aikin hajji-, bai yi batsa ko jima'i ba, da fasikanci: to zai fita daga zunubansa kamar ranar da uwarsa ta haife shi".

            Wajibi ne akan kowani musulmi, ya fahimto –daga wannan ibada ta aikin hajji- ya fahimto manufofinta, sannan ya yi miqaqqiyar rayuwa a cikin wannan rayuwar akan darrusan da ya koya daga gare ta (ibadar hajji).

            Allah (سبحانه) ya datar da mu izuwa ga shiriyarSa, kuma ya nuna mana abinda a cikinsa ake samun yardarSa.

Allah ya sanya mana albarka cikin wahayi guda biyu, ya kuma amfanar da mu da shiriyar da take cikinsu.
Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah a ni da ku, da kuma sauran Musulmai, Ku nemi gafararSa; lallai shi, Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU:
            Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma gode masa, Kuma ina shaidawa babu abin bautawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka, akansa, da iyalansa da sahabbansa.

Al'ummar musulmai!
            Lallai ne al'ummar musulmai ba za ta samu rabauta da buwaya ba, kuma ba za su tava samun wata bunqasa, ko wadaci, ko walwala, ko aminci ba, matuqar ba su tsayar da rayuwarsu akan shari'ar Allah ba (سبحانه). Kuma sai har littafin Allah, da sunnar zavavven Manzo (صلى الله عليه وسلم) sun kasance fitila, kuma tsari da salon da suke gudanar da sha'aninsu na rayuwa akansu.
            Kuma wajibi ne ga al'umma ta xauka, daga irin hudubar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a hajjin bankwana, su xauki tabbatacciyar manufar da za su riqa tafiya a kansa, a cikin siyasosinta, da alaqoqinta, da cikin tattalin arziqi, da sauran sha'anoninsu.
            Kuma da aikata haka ne kawai, za su rabauta, kuma al'umma sai ta yi ta hauhawa izuwa ga matakan kamala, da bunqasa, da wayewa. Idan kuma suka qi aiki da hakan, to lallai al'umma tana cikin asara da wahala, kuma tana cikin tsanani da bala'i.

            Sannan ku sani, lallai mafi tsarkin abinda rayuwarmu take tsayuwa da shi, shine: Shagaltuwa da yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
Ya Allah!  Ka yi salati da sallama da albarka da ni'ima ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu.
Ya Allah!  Ka yarda da khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu. Da iyalan annabi da sahabbai gabaxaya, da wanda ya bi su, da kyautatawa zuwa ranar sakamako.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah ka datar da musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke ciki, Ya Allah ka datar da musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke, Ya Allah ka datar da musulmai zuwa ga abinda yardarsa ta ke.
Ya Allah ka kiyaye mahajjata da masu umrah, kuma ka mayar da su zuwa garinsu, cikin salama da riba, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah ka datar da majivincin lamarinmu ga abinda ka ke so, kuma ka yarda.
Ya Allah! Ka kiyaye qasar harami biyu, da sauran qasashen musulmai.



gyara halinmu da halin Musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, ka kore ababen vacin rai.
Ya Allah! Ka tseratar da bayinka Musulmai daga kowani ibtila'i da fitina.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiyan Musulmai; Lallai su, basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu Musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance mai taimako a gare su; Ya Mabuwayi ya Mai matsanancin qarfi.
Ya Allah! Ka datar da Mai hidiman Masallatan harami biyu izuwa ga abinda kake sonsa, kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka taimaki addini da shi, kuma ka xaukaka kalmar Musulmai da shi.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bamu mai kyau a Duniya, a Lahira itama mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar Wuta.

Bayin Allah!
Ku ambaci Allah ambato mai yawa,
Ku yi masa tasbihi safiya da maraice;
Qarshen addu'armu itace:
الحمد لله رب العالمين


2016/08/17

LADUBAN SALLAMA DA ATISHAWA DA ZIYARAR MARAS LAFIYA (ابن باز)

SHAR'ANTA YIN SALLAMA DA AMSATA, DA YIN ADDU'A GA MAI ATISHAWA IDAN YACE: "ALHAMDU LILLAH", DA ZIYARAR GAIDA MARAS LAFIYA([1])
An karvo hadisi daga Abdullahi xan Amru bn Al-aas (y), lallai wani mutum ya tambayi Annabi (r):
أَيُّ الْإِسْلَامِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلَامَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ، وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
Ma'ana: "Wanne musuluncin ne ya fi alheri? Sai ya ce: Ka ciyar da abinci, ka kuma yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba"([2]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An karvo hadisi daga Abu-hurairah (t), ya ce: Manzon Allah (r) yace:
«لَا تَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا، أَوَلَا أَدُلُّكُمْ عَلَى شَيْءٍ إِذَا فَعَلْتُــمُوهُ تَحَابَبْتُمْ؟ أَفْشُوا السَّلَامَ بَيْنَكُمْ».
Ma'ana: "Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, Shin ba zan nuna muku wani abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? Ku watsa sallama a tsakaninku"([3]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai Annabi (r) ya ce:
«خَمْسٌ تَجِبُ لِلْمُسْلِمِ عَلَى أَخِيهِ: رَدُّ السَّلَامِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَعِيَادَةُ الْمَـــرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ».
Ma'ana: "Abubuwa guda biyar suna wajaba ga musulmi akan xan'uwansa, amsa sallama, da addu'a ga mai atishawa, da amsa gayyata, da ziyarar gaida maras lafiya, da rakiyar gawa"([4]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An sake samowa daga gare shi (t) daga Annabi (r) lallai ya ce:
«حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ سِتٌّ» قِيلَ: مَا هُنَّ يَا رَسُولَ اللهِ؟، قَالَ: «إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ، وَإِذَا دَعَــــاكَ فَأَجِبْهُ، وَإِذَا اسْتَنْصَحَكَ فَانْصَحْ لَهُ، وَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللهَ فَسَمِّتْهُ، وَإِذَا مَرِضَ فَعُدْهُ وَإِذَا مَاتَ فَاتَّبِعْهُ».
Ma'ana: "Haqqin musulmi akan musulmi guda shida ne, Sai aka ce: Menene su ya ma'aikin Allah? Sai ya ce: Idan ka gana da shi ka yi masa sallama, idan kuma ya gayyace ka to ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya ce: alhamdu lillah to sai ka yi masa addu'a, idan ya yi jinya ka ziyarce shi, in kuma ya mutu ka raka gawarsa"([5]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai Annabi (r) ya ce:
«إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْعُطَاسَ وَيَكْرَهُ التَّثَاؤُبَ فَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللَّهَ فَحَقٌّ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ سَمِعَهُ أَنْ يُشَمِّتَهُ، وَأَمَّا التَّثَاوُبُ فَإِنَّمَا هُوَ مِنَ الشَّيْطَانِ فَلْيَرُدَّهُ مَا اسْتَطَاعَ، فَإِذَا قَالَ: هَا ضَحِكَ مِنْهُ الشَّيْطَان».
Ma'ana: "Lallai Allah ta'alah yana son atishawa, yana kuma qin hamma, don haka; idan xayanku ya yi atishawa sai kuma ya ce: alhamdu lillah, to haqqi ne ga kowani musulmin da ya ji shi ya masa addu'ar nema masa rahama (ya ce: Yarhamukal lahu), Amma shi kuma hamma to daga Shexan ne, don haka; mutum ya mayar da shi gwargwadon iko, Idan ya ce: Ha,a,a Sai shexan ya yi ta yi masa dariya"([6]). Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
An sake karvowa daga gare shi, daga Annabi (r) yace:
«التَّثَاؤُبُ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَإِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ فَلْيَكْظِمْ مَا اسْتَطَاعَ».
Ma'ana: "Yin hamma daga shexan ne, idan xayanku ya yi hamma to ya kame gwargwadon iko"([7]). Muslim ya ruwaito shi.
An karvo daga Abu-sa'id alkhudriy (t), ya ce: Manzon Allah (r) yace:
«إِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ، فَلْيُمْسِكْ بِيَدِهِ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ».
Ma'ana: "Idan xayanku zai yi hamma to ya kame bakinsa da hannunsa, saboda shexan yana shiga"([8]). Muslim ya ruwaito shi.
Daga Abu-hurairah (t) lallai shi ya ce:
«إِذَا عَطَسَ أَحَدُكُمْ، فَلْيَقُلِ: الْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلْـيَـقُلْ لَهُ أَخُوهُ أَوْ صَاحِبُهُ: يَرْحَمُك اللهُ، وإذا قال له: يَرْحَمُك اللهُ فَلْيَقُلْ: يَهْدِيكُمُ اللهُ وَيُصْلِحُ بَالَكُمْ».
Ma'ana: "Idan xayanku ya yi atishawa yace: ALHAMDU LILLAH, Sai xan'uwansa ko abokinsa ya ce: YARHAMUKAL LAHU, Idan ya ce masa: Yarhamukal lahu, to sai yace: YAHDIYKUMUL LAHU WA YUSLIHU BAALAKUM"([9]). Bukhariy ya ruwaito shi.
Abu-musa al-ash'ariy (t) yace:
«إِذَا عَطَسَ أَحَدُكُمْ فَحَمِدَ اللَّهَ فَشَمِّتُوهُ، وَإِذَا لَمْ يَحْمَدِ اللَّهَ فَلَا تُشَمِّتُوهُ».
Ma'ana: "Idan xayanku ya yi atishawa sai ya ce: alhamdu lillah, to ku yi addu'ar neman rahama a gare shi, idan kuma bai ce: alhamdu lillahi ba kada ku yi masa wannan addu'ar"([10]). Muslim ya ruwaito shi.
$&$
$&$




([1])  Wannan ya zo ne a cikin littafin: TUHFATUL AKHYAAR, BI BAYANI JUMLATIN NAFI'ATIN MIMMA WARADA FIL KITABI WAS SUNNATIS SAHIHATI MINAL AD'IYATI WAL AZKAAR, Na Ibnu-baaz, (fasalin da yake kusa da na qarshe, 34), yana nan kuma a cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (26/49-52) .
([2])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 12), da Muslim (lamba: 39).
([3])  Muslim ya ruwaito shi, (lamba: 54).
([4])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 1240), da Muslim (lamba: 2162).
([5])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 6223), da Muslim (lamba: 2162).
([6])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 6223).
([7])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 3115), da Muslim (lamba: 2994).
([8])  Muslim ya ruwaito shi, (lamba: 2995).
([9])  Bukhariy ya ruwaito shi, (lamba: 6224).
([10])  Muslim ya ruwaito shi, (lamba: 2992). 

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...