HUKUNCE-HUKUNCEN I'ITIKAAFI
(أحكام الاعتكاف)
Tarjamar
Abubakar Hamza
ITIKAAFI shine
lazimtar Masallaci domin yin dangogin ayyukan biyayya ga Allah Ta'alah!
Kuma shi mustahabbi ne, ga Maza da Mata, a dukkan lokatan shekara, Allah
Ta'alah ya ce:
"وعهدنا إلى إبراهيم وإسماعيل أن طهرا بيتي للطائفين والعاكفين والركع
السجود"،
[البقرة: 125].
Ma'ana: "kuma Muka yi alkawari zuwa ga
Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake 'Dakina, domin masu dawafi da masu itikaf,
da masu ruku'i masu sujada" [Bakara: 125].
Mustahabbancin yin itikafi na kara karfi a watan Ramadhana, musamman kuma
a goman karshen watan, domin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya
kasance "yana yin itikafin kwanaki goman
karshen watan Ramadhana, har Allah ya masa wafati", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ga maganar da tafi inganci, babu gwargwadon lokaci iyakantacce ga
mafi karancin kwanaki ko lokacin yin itikafi, don haka yana inganta ayi itikafi
koda na dan wani lokaci ne kankani.
Kuma ana shardantawa, gabanin itikafi ya inganta ya kasance a cikin Masallaci,
saboda fadinSa Madaukaki:
"ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد" [البقرة: 187].
Ma'ana: "Kuma kada ku rungume su alhali
kuna masu itikafi a cikin Masallatai", [Bakara: 187].
Kuma sharadi ne gabanin itikafi ya inganta, mai itikafin ya kasance
tsarkakakke daga abinda ke wajabta wanka, kamar janaba da haila.
Kuma wajibi ne akan Mace ta nemi izinin Mijinta.
Kuma mai itikafi bashi da daman neman abinci da yin wata sana'a, ko kuma
saye da sayarwa, sai dai idan da bukata.
Kuma baya halatta a gare shi ya fita daga Masallaci, sai dai idan da
uzuri, koda kuwa zai fita ne saboda ziyartar maras lafiya, ko rakiyar gawa.
Kuma yana halatta a gare shi, mai itikafi ya fita, ga abinda babu makawa
akansa, kamar biyan bukata, da halarto da abinci da makamancinsa.
Kuma yana halatta a gare shi, mai itikafi ya yi wankan tsafta ko wanke
kansa, ko taje shi,
"Uwar muminai
A'ishah –Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce: Annabi –sallal Lahu alaihi wa
sallama- idan ya shiga itikafi, yana kusanto mini da kansa, domin na taje masa.
Kuma ya kasance baya shigowa gida, sai domin bukatar 'dan-Adam (shiga makewayi)",
Muslim ya ruwaito [1297].
'Da'arka
ga Allah ita ce shukar da zaka girbe a lahira, sai ka yi kwadayin wannan shukar
ta kubuta daga abinda zai tauye ta, da kuma kura-kurai, Allah Ta'alah yana
cewa:
"تلك حدود الله فلا تقربوها
كذلك يبين الله آياته للناس لعلهم يتقون" [البقرة: 187].
Ma'ana: "Wadancan
iyakoki ne na Allah, don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah ke
bayyana ayoyinSa ga Mutane, la'alla ko za su samu takawa" [Bakara:
187].
No comments:
Post a Comment