Matashiya
kan azumin watan Ramadhana (02)
بمَ
يدخل شهر رمضان؟
1/ عَن ابْن عُمَرَ
رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ:
سَمِعْتُ
رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
"إِذَا
رَأَيْتُمُوهُ فَصُومُوا، وَإِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَأَفْطِرُوا، فَإِنْ غُمَّ
عَلَيْكُمْ فَاقْدُرُوا لَهُ"،
أخرجه
البخاري [1900]، ومسلم [1080].
وفي
رواية عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ:
"فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ".
أخرجه
البخاري [1909]، ومسلم [1081].
SHIGAN
WATAN RAMADHANA YANA TABBATUWA DA GANIN JINJIRIN WATAN, KO CIKAN WATAN SHA'ABAN
30, HAKA KUMA YA KAN FITA DA GANIN JINJIRIN WATAN SHAWWAL, KO CIKAR RAMADHANA
30
An
ruwaito daga Abdullahi dan Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce:
Na
ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:
"Idan ku ka ganshi –ma'ana: jinjirin wata- sai ku yi azumi,
Idan kuma kuka gan shi, sai ku ajiye azumi –ku yi idi-, Idan kuma aka yi muku
hazo, sai ku kaddara masa (cikar talatin)".
Bukhariy
ya ruwaito shi [1900], da Muslim [1080].
A
wata riwaya, daga hadisin Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce:
"Idan aka yi muku hazo, sai ku cika kirgen Sha'abana kwanaki
talatin".
Bukhariy
ya ruwaito shi [1909], da Muslim [1081].
2/ وعَنِ ابْنِ عُمَرَ
رضي الله عنهما، قَالَ:
"تَرَائِى
النَّاسُ الْهِلالَ، فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، أَنِّي رَأَيْتُهُ فَصَامَهُ، وَأَمَرَ النَّاسَ بِصِيَامِه".
أخرجه
أبو داود [2342] والحاكم [1/423]، وصححه.
Fassara:
An
ruwaito daga Abdullahi dan Umar -Allah ya yarda a gare su- ya ce:
Mutane
sun fita dubiyar wata, Sai na bada Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-
labarin cewa, na gan shi, Sai ya azumce shi, kuma ya umarci Mutane da
azumtarsa".
Abu-dawud
[2342] ya rawaito shi, da Alhakim [1/423], kuma ya inganta shi.
Tsokaci
Wadannan
hadisan suna nuna;
(1)
A Musulunci an gina lamarin azumin Ramadhana ne, a kan abu na zahiri, wanda
kuma shi ne, ganin jinjirin watan Ramadhan, a lokacin da Sha'abana ya kai yini
29.
Idan
kuma ba a ganshi ba, sai a cika kidayar watan kwanaki 30.
(2)
Ba dole sai kowa ya ga jinjirin watan da kansa ba, saboda Manzon Allah -sallal
lahu alaihi wa sallama- ya dau azumi, kuma ya umarci mutane da su dauka,
lokacin da Abdullahi bn Umar, ya ga jinjirin watan. Don haka, matukar mutumin
da ya ganin Musulmi ne, adali, mai gani ba makaho ba, to shi kenan.
(3)
Shugaba shi ke da alhakin umartar mutane, da cewan su dau azumin.
Su
kuma mabiya ana neman su isar masa da labarin ta hanyoyin da su ka dace.
(4)
Yana da kyau a rika fita, dubiyar wata, musamman bayan gari (inda babu abinda
zai shamakance ganin watan).
Allah
Shi ne mafi sani.
No comments:
Post a Comment