2016/11/25

hudubar 25 safar 1438H Ta Husain AlushSheikh daidai da 25 nobanba 2016M








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
 JUMA'A, 25/SAFAR/1438H
Daidai 25/NOBANBA/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
S
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da ba a qididdige su.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da abokin tarayya, a lahira da duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, annabi zavavve, kuma bawa zavavve.
Ya Allah! ka yi daxin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta gaskiya da tsoron Allah ( taqawa).
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

'Yan'uwan Musulunci
A rayuwar al'ummarmu ta yau akwai fitintinu masu tsanani, da musibu nau'i-nau'i, da qalu-bale masu hatsari, da tsare-tsare na makirci.
Kuma lallai musulmai suna fatan ganin ababen da za su gyara halayensu, su kawo sa'ida a cikin rayuwarsu, su kuma tabbatar musu da farin ciki, da walwalar arziqi, sannan su tunkuxe musu tsanani da cutuka.
Kuma lallai nasarar wannan al'ummar da  rabautar ta da samun dukkan abinda ta ke kwaxayi, da kuma samun tsira daga dukkan abinda ta ke tsoro, ko sauran ababen qi, ba za su yiwu ba, sai idan ta yi riqo da gangariyar musulunci, wanda ke qunsar tataccen tauhidi, da ingantacciyar aqida, da cikakken miqa wuya ga abin bautawa guda xaya, a cikin dukkan nashaxoxin al'ummar da fagagen rayuwarta, Allah ta'alah ya ce: "Haqiqa muminai sun samu babban rabo" [Mu'uminuna: 1].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya ku mutane, ku faxi: La ilaha illal lahu, sai ku samu rabo",
Ibnu-Khuzaimah ya ruwaito shi a cikin "sahihinsa".

            Ya ku taron Musulmai!!
       Al'umma ba za tava samun sa'ada ba, kuma halinta ba zai tava gyaruwa ba, matuqar dukkan tsare-tsaren rayuwarsu da dukkan abinda su ka fiskanta ba su gudanar da su a qarqashin shari'ar Allah Mabuwayi da xaukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku yi ruku'i da sujjada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, ku riqa aikata alheri, domin ku samu rabo" [Hajj: 77].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ya samu rabo, Wanda ya musulunta, kuma aka bashi arziqin buqatunsa, kuma Allah ya bashi wadatuwa a zuciya, ga abinda ya bashi".

            Kuma wadacin arziqi ba zai tabbatu ba, da kwanciyar hankali, da walwala a cikin raywa, da aminci da zaman lafiya ga wata al'umma musulma, face sun sallamaa lamuransu ga hukuncin Allah, sun kuma yi aiki da shari'arSa, su kuma miqa wuya ga shiriyar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم), Allah (تعالى) ya ce: "Kawai maganar muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da manzonSa, domin ya yi hukunci a tsakaninsu ta kan kasance, su ce: Mun ji, kuma mun yi xa'a, kuma waxannan su ne masu samun rabo" [Nur: 51].

          Ya al'ummar Musulmai!!
            Tavewa da dukkan nau'ukansa mabanbanta ba za su xagu ba, duk yadda mu ka yi qoqarin rabuwa da hakan ta dukkan hanyoyi, matuqar ba mu tabbatar da tuba ta gaskiya ba, daga abinda ke aukuwa a rayuwarmu na sassava wa tsarin Ubangijinmu, da kuma sunnar annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم).

            Kuma lokaci ya yi, ga wannan al'ummar, alhalin tana xanxanar raxaxi da baqin ciki launi-launi (iri-iri), lokaci ya yi, ta koma ga Ubangijinta, tana mai qanqan da kanta a gare shi, da tuba, ta kuma gyara dukkan sha'aninta, gwargwadon yardarSa, Allah yana cewa: "Shin lokaci bai yi ba, ga waxanda su ka yi imani, zukatansu su yi tawali'u ga ambaton Allah, da abin da ya sauka daga gaskiya" [Hadid: 16].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya, Ya ku muminai! tsammaninku ku samu babban rabo" [Nur: 31].

            Idan kuma lamarin al'ummar ya cigaba akan turbar sabo, da kuma kukkutsawa cikin haramun da aiyukan laifi, to ta sani lallai hanyar samun rabo yana nesa da  ita, kuma kawo gyara ya yi hannun riga da ita, "Ya ku waxanda su ka yi imani lallai, giya da caca da gumaka da kiban quri'a qazanta ne daga aikin shexan, sai ku nisance shi, wa la'alla ku samu rabo" [Ma'ida: 90].

            Saboda, Ga al'ummar, ga misali tana rayuwa cikin juya baya wa juna, da yanke zumunta, da savani, da jayayya, da faxa, da qoqarin tunkuxe juna, wanda zubar da jini ke biyo bayansu, da keta alfarmomi, har sashen mutane ya zama xanxanar bala'in sashe, sai maganar Allah Mabuwayi da xaukaka ta tabbatu akan muatne: "Kuma kada ku yi jayayya sai ku raunana, sai qarfinku kuma ya tafi" [Anfal: 46].
Kuma maganar zavavven Annabi (صلى الله عليه وسلم) ta tabbatu akansu, a inda ya ce: "Kuma matuqar shugabanninsu ba su yi hukunci da littafin Allah ba, to sai Allah ya sanya faxansu ya dawo a tsakaninsu".

            Kuma ga al'ummar tana fama da koma-baya cikin tattalin arziqi, kamar yadda kuma hakan shi ne halin da duniya gabaxaya ta samu kanta a ciki.
Saidai kuma hanyar tsira ga al'ummar annabi Muhammadu daga durqushewar tattalin arziqi, da halin samun koma-baya ita ce, yin tafiya kamar yadda tsarin Allah yarjejje ya shumfuxa, wanda duk lokacin da al'umma ta kauce wa tsarin to sai ta faxa cikin cutuka da bala'oi "Ya ku waxanda su ka yi imani kada ku ci riba ninki-ninki tivanye, kuma ku bi Allah da taqawa, tsammaninku za ku samu babban rabo" [Ali-imrana: 130].

            Ya ku Musulmai!
       Lallai samun babban rabo yana qara rataya ne ga aikin al'ummar da ibadar umurni da kyakkyawa, da hani kan aikata ababen qi, da yin nasiha wa juna, cikin abinda zai kawo gyara a lamura, ya daidaita alqibloli, akan manhaji maxaukaki, da uslubin zance wanda ke cike da haquri, da manufa maxaukakiya, da kuma hadafi mai girma, Allah (سبحانه) yana cewa:
((ولتكُن منكم أمة...)) الآية.
Ma'ana: "Kuma wata al'umma daga cikinku su kasance suna kira zuwa ga alkhairi, kuma suna urmurni da kyakkyawa, kuma suna hani ga abin qi, kuma waxannan su ne samun babban rabo" [Ali-imran: 104].
Wasu maluman tafsiri su ka ce, kalmar "من" daga "منكم" a ayar, ba tana nuna sashe ne kawai ba, a'a "MIN" ta qarin bayani ce.
           
            Kuma duk lokacin da musulmai su ka kauce daga wannan hanyar to, sai su auka cikin hasara, su sake durqushewa, "Lallai ina rantsuwa da zamani * Lallai ne Mutum yana cikin hasara * Face waxanda su ka yi imani, kuma su ka aikata aiyukan kwarai, kuma su ka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma su ka yi wa juna wasiyya da yin haquri" [Asr: 1-3].

            'Yan'uwa Musulmai!
       Kuma lallai samun babban rabo yana qara rataya akan fahimtar tataccen musulunci; addinin tsakaitawa, wanda ya yi nesa da wuce iyaka da qaqale da tsanantawa, (ta xaya vangaren kuma) ya yi nesa da sakaci ko gajartawa, wanda ya zo cikin hukunce-hukunce tabbatattu, a cikin wahayi biyu (na qur'ani da sunnah).
Saboda qetare iyaka wajen fahimtar addini (wato: guluwwi), sau dayawa ya janyo wa musulunci da musulmai matsaloli masu girma, da sharrace-sharrace da ba za a iya qididdige su ba, domin wuce iyaka, ya sava wa abin da Allah ke nufi, da kuma sunnar Manzonsa zavavve (صلى الله عليه وسلم), "Kuma kamar haka ne, mu ka sanya ku al'umma matsakaiciya" [Baqara: 143].

Ya ku taron Musulmai!!
Lallai samun babban rabo a duniyance, wanda shi ne samun bunqasa a cikin al'umma, da samun wadacin jama'a, ta hanyar tunkuxowar ni'imomi masu yawa, da albarkoki xaya bayan xaya, baya kasancewa kawai da yin aiki da sabuba na zahiri, a'a, sai an haxa da yin aiki da sabuba na ma'ana na haqiqa, kamar tsayuwa akan sunna, da dawwama akan aiki da tsarin shari'a, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya bi Allah da taqawa, to Allah zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi daga inda baya zato" [Xalaq: 2-3].
Kuma Allah wanda sha'aninsa ya xaukaka ya ce: "Kuma da ma'abuta alqaryu sun yi imani, kuma su ka yi taqawa, to da mun buxe albarkoki akansu daga sama da qasa" [A'araf: 96].

            Ya al'ummar musulunci!
       Haqiqa dayawa daga musulmai bayan gushewan zamanin mulkin mallaka sun jarraba a cikin rayuwarsu, sun jarraba bin misalai na ra'ayoyin da aka shigo da su (daga wajen islama) da waxanda su ka shigo, sai dai al'ummomin musulmai ba su samu komai daga waxannan ra'ayoyi tsare-tsaren ba, face varna cikin ra'ayoyi, da rauni ta fiskar soja, da koma-baya cikin tattalin arziqi, da lalacewar halayya, da rabuwar kai a cikin al'umma, su waxannan ra'ayoyin duniya mutane bata gyaru da su ba, kamar yadda ta lalata wa wasu (dayawa) addininsu.
            Sai dai lokaci ya yi bayan mun ga dalilai a zahiri (a qasa), lokaci ya yi mu koma ga hasken wahayi guda biyu (qur'ani da sunnah), kuma lokaci ya yi ga wanda ya ximauce saboda ruxuwa da ya yi da wayewar da su ke nuna halayya a zahiri, waxanda dalilai kuma na zahiri waxanda aka shaida su ka tabbatar cewa qarya ne da varna aka lulluve, wanda su ke bayyana a lokacin maslahohi ko amfani irin na-qashin kai, don haka waxannan dokoki (ko tsare-tsare) suna kama ne da zane mai kyau da aka tabbatar da rubutunsu a jikin kundayen qasashe, saidai kuma duk lokacin da aka yi aiki da su, to suna rushe qasashen musulmai, da ababen da su ka mallaka, sannan su zama sababi tabbatacce na kwashe alkhairorin (da dukiyar) qasashen, saboda dokoki ne da su ka fice daga dabaibayin gyaran da Allah Ubangiji ya yarda da shi, kawai manufar irin waxannan dokokin ita ce, rushe tsare-tsare na  addini, da halayya, da ladabi, da mutum-taka, Allah Mabuwayi da xaukaka yana cewa: "… Babu wanda ya fi Allah kyan hukunci, ga mutane masu yaqini" [Ma'ida: 50].

Ina faxar wannan maganar,
kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran musulmai daga kowani zunubi,
sai ku nemi gafararsa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU

            Al'ummar musulmai ta mallaki sabuban samun buwaya da nasara, irin abinda wata al'ummar bata mallaka ba. Kuma wannan al'ummar ta kevanta da ababen da su ke tsayar da gyara da sa'ada, irin abinda babu a wajen wata al'ummar.
            Kuma tarihin wannan al'ummar a qarnuka da suka shuxe babban mai shaida ne akan haka, kuma hujja mafi girma.
            Saidai kuma samun nasararta an sharxanta masa wasu sharuxoxi, kuma na rataye da ababen da su ke jawo shi, "Ya ku waxanda su ka yi imani idan ku ka taimaki Allah, zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku " [Muhammadu: 7].
"Lallai ne mu za mu taimaki manzanninmu da waxanda su ka yi imani a rayuwar duniya, da ranar da masu shaida su ke tsayawa" [Gafir: 51].

            Shima kiyayewan da Allah zai yi ga wannan al'ummar ana sanya masa sharaxin yin aiki ko xa'a ga shari'arSa, da nisantar mutane ga abinda ya tsawatar, "Lallai ne Allah yana bada kariya ga waxanda su ka yi imani" [Hajji: 38].
A wata qira'ar sai aka ce, "يدفع" a gurbin "يدافع".
Kuma ya zo cikin hadisi ingantacce: "Ka kiyaye Allah, sai ya kiyaye ka".

            Amincin wannan al'ummar da zama lafiyanta, da walwala a rayuwarta, a qulle ya ke da tsayuwar al'ummar da imani, da duk abin da imanin ke hukuntawa, da kuma musulunci da haqqoqinsa, "Waxanda su ka yi imani, kuma basu gauraya imaninsu da zalunci ba, waxannan suna da aminci, kuma su ne shiryayyu" [An'am: 82].

            Kuma wannan al'ummar za ta samu xaukaka ne akan maqiyanta, ta yi rinjaye akansu, gwargwadon abinda ke tare da ita na imani da haqiqaninsa da wajibabbunsa, kamar yadda Ibnulqayyim ya ke faxan hakan.
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baqin ciki, alhali kuwa kune mafiya xaukaka, idan kun kasance masu imani" [Ali-imran: 139].
"Kuma lallai rundunarmu sune masu rinjaye" [Saafaat: 173].
Ibnu-kasir (Allah ya yi masa rahama) a qarqashin tafsirin faxin Allah Maxaukakin sarki : "Ya ku waxanda su ka yi imani, ku yaqi waxanda suke kusa da ku daga kafirai, kuma su sami tsanani daga gare ku, kuma ku sani cewa Allah yana tare da masu taqawa" [Tauba: 123] Ibnu Kasir ya ke cewa: ((Kuma duk lokacin da wani sarki daga sarakunan musulunci ya tsayu, ya kuma yi biyayya ga umurnin Allah, ya dogara ga Allah, to sai Allah ya buxe masa garurruka, sai kuma ya dawo da wasu garurrukan daga hannun maqiya, gwargwadonsa, da kuma gwargwadon abinda sarkin ya ke da shi, na jivintar la,arin Allah –wato: walittaka-)).

            Sannan ku sani, lallai yana daga cikin mafi tsarkin abinda rayuwarmu za ta tsayu da shi, shagaltuwa da yin  salati da sallama ga Annabi mai karimci,
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu, masoyinmu Muhammadu.
            Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, shugabanni masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu.
            Ya Allah! Ka gyara halinmu da halin musulmai,
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, da vacin rai.
Ya Allah! Ka tsamar da bayinka musulmai, daga kowace fitina, da bala'i.
Ya Allah! Ka yi maqanin maqiya musulmai, saboda su basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu musulmai a kowani wuri,
Ya Allah! Ka kasance a gare su, Mai taimako, mai basu nasara, Ya Mabuwayi Ya Mai tsananin qarfi.
            Ya Allah! Ka datar da mai hidimar harami biu maxaukaka, zuwa ga abin da ka ke so, kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka bada nasara ga addini da shi, kuma ka xaukaka kalmar musulmai da shi, Ya Allah ka gafarta wa musulmai maza da musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu,

            Ya Allah! "Ka bamu mai kyau a duniya, da mai kyau a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].

2016/11/20

BUSHARORI GOMA GA MASU KIYAYE SALLAR ASUBA ( البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر)






البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر
(BUSHARORI GOMA GA MASU KIYAYE SALLAR ASUBA)





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA



بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذا المقطع في ذكر البشائر العشر للمحافظين على صلاة الفجر، جعلنا الله منهم بمنه وكرمه.

البشارة الأولى
 قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"بَشِّرِ الْمَشَّائِينَ فِي الظُّلَمِ إِلَى الْمَسَاجِدِ، بِالنُّورِ التَّامِّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ".
أخرجه أبو داود والترمذي وصححه الألباني.

BUSHARAR FARKO
(CIKAKKEN HASKE RANAR KIYAMA GA MASU TAFIYA CIKIN DUFFAI ZUWA GA MASALLATAI)
 
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-  ya ce:
"Ka yi bishara ga masu tafiya cikin duffai zuwa ga masallatai, da samun haske cikakke a ranar kiyama".
Abu-dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma Albaniy ya inganta shi.

البشارة الثانية
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"رَكْعَتَا الْفَجْرِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا".
أحرجه مسلم.

BUSHARA TA BIYU:
(RAKA'OI BIYU BAYAN KETOWAR ALFIJIR SUN FI DUNIYA GABA DAYANTA ALHERI)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Raka'oi biyu bayan ketowar alfijir sun fi alheri akan duniya da abinda ke cikinta".
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة الثالثة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ خَرَجَ مِنْ بَيْتِهِ إِلَى الْمَسْجِدِ كُتِبَ لَهُ بِكُلِّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا عَشْرُ حَسَنَاتٍ، وَالْقَاعِدُ فِي الْمَسْجِد يَنْتَظِرُ الصَّلاَةَ كَالْقَانِتِ، وَيُكْتَبُ مِنَ الْمُصَلِّينَ، حَتَّى يَرْجِعَ إِلَى بَيْتِهِ".
أخرجه أحمد.

BUSHARA TA UKU
(LADAN TATTAKI ZUWA GA MASALLACI, ZAMAN JIRAN SALLAH KUMA KAMAR YIN SALLAH NE)

Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya fita daga gidansa, zuwa masallaci, za a rubuta masa lada goma da dukkan takun da ya ke yi.
Wanda kuma ke zaune a masallaci yana jiran sallah kamar wanda ya ke tsayar da salla ne, kuma za a rubuta shi cikin masallata, har ya dawo gidansa".
Ahmad ya ruwaito shi.

البشارة الرابعة :
قال جل في علاه:
"أَقِمِ الصَّلاَةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا". 
سورة الإسراء : ٧٨.

BUSHARA TA HUDU
(MALA'IKU SUNA HALARTAR SALLAR ASUBA)
Allah Madaukaki yana cewa:
"Ka tsayar da salla daga gotawar rana, zuwa duhun dare, da tsawaita karatun alfijir, lallai sallar alfijir ta kasance abar halarta"
[suratul Isra'i: 78].

البشارة الخامسة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"لَنْ يَلِجَ النَّارَ أَحَدٌ صَلَّى قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا، يَعْنِى الْفَجْرَ وَالْعَصْرَ".
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA BIYAR
(KIYAYE SALLAR ASUBA DA LA'ASAR KARIYA NE DAGA SHIGA WUTA)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama-  ya ce:
"Ba zai shiga wuta ba, mutumin da ya yi salla gabanin fudowar rana, da faduwarta", yana nufin sallar asuba da ta la'asar.
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة السادسة:
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْعِشَاءَ فِي جَمَاعَةٍ فَكَأَنَّمَا قَامَ نِصْفَ اللَّيْلِ، وَمَنْ صَلَّى الصُّبْحَ فِي جَمَاعَةٍ فَكَأَنَّمَا صَلَّى اللَّيْلَ كُلَّهُ". 
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA SHIDA:
(YIN SALLAR ISHA CIKIN JAM'I KAMAR SALLATAR RABIN DARE NE, YIN ASUBA CIKIN JAM'I KUMA, KAMAR SALLATAR DAREN NE GABADAYA):
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya yi sallar isha, a cikin jam'i, kamar ya sallaci rabin dare ne, Wanda kuma ya yi sallar asuba a cikin jam'i, to, kamar ya sallaci daren ne gabadaya".
Muslim ya ruwaito shi.

البشارة الثامنة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْفَجْرَ ثُمَّ جَلَسَ فِي مُصَلاَّهُ، صَلَّتْ عَلَيْهِ الْمَلاَئِكَةُ، وَصَلاَتُهُمْ عَلَيْهِ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ، اللَّهُمَّ ارْحَمْهُ".
أخرجه أحمد.

BUSHARA TA BAKWAI
(YIN SALLAR ASUBA DA ZAMA A WURIN SALLAR, SABABI NE NA SAMUN ADDU’AR MALA'IKU)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya sallaci sallar asuba, sai ya zauna a wurin sallarsa, Mala'iku za su rika masa salati, kuma salatin da za su masa shine, Ya Allah! Ka gafarta masa, Ya Allah! Ka yi rahama a gare shi".
Ahmad ya ruwaito shi.


البشارة التاسعة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى الْغَدَاةَ  الفجر فِي جَمَاعَةٍ، ثُمَّ قَعَدَ يَذْكُرُ اللَّهَ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ، كَانَتْ لَهُ كَأَجْرِ حَجَّةٍ وَعُمْرَةٍ تَامَّةٍ تَامَّةٍ تَامَّةٍ". 
أخرجه الترمذي وصححه الألباني.

BUSHARA TA TAKWAS
(YIN SALLAR ASUBA DA ZAMA DOMIN AMBATON ALLAH, DA RAKA'OI BIYU BAYAN FUDOWAR RANA, LADANSU KAMAR NA YIN HAJJI NE DA UMRAH CIKAKKU )
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya sallaci sallar asuba a cikin jam'i sa'annan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta fudo, sa'annan ya yi raka'oi biyu, ya kasance yana da ladan hajji da umrah, cikakku, cikakku, cikakku".
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.

البشارة العاشرة
قال النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
"مَنْ صَلَّى صَلاَةَ الصُّبْحِ فَهْوَ فِي ذِمَّةِ اللَّهِ، فَلاَ يَطْلُبَنَّكُمُ اللَّهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَىْءٍ، فَإِنَّهُ مَنْ يَطْلُبْهُ مِنْ ذِمَّتِهِ بِشَىْءٍ يُدْرِكْهُ، ثُمَّ يَكُبَّهُ عَلَى وَجْهِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ".
أخرجه مسلم.

BUSHARA TA TARA:
(SALLAR ASUBA TANA SANYA BAWA CIKIN KULAWAR ALLAH)
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Wanda ya yi sallar asuba to yana cikin alkawari ko amana da kulawar Allah, kada Allah ya nemi wani abu daga abinda ya yi alkawari da ku akansa, saboda duk wanda Allah ya nemi abu daga cikin abinda ya dauki alkawari da shi, zai riske shi, sa'annan ya tuntsurar da shi cikin wutar jahannama akan fiskarsa".
Muslim ya ruwaito shi.



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...