YAYA 'DANKA ZAI ZAMA MAI YAWAN
KARANCE-KARANCE?
(كيف تصنع طفلا قارئا)
1- Sanin dabarun
hadda, da fahimta, da kwankwadar ilimi.
2- Yarda da kai
da samun karfin hali, da sanin kai.
3- Kyautata
karfin kwakwalwa.
Damammaki ne da kuma dabarun wanda 'danka zai koye su; idan
har dan yaro ne mai yawaita karatu, mai kuma son littafafai.
Sai ka yi kwadayi ya zama hakan, ta hanyar///
a.
Samar wa yaro littatafai da majalloli
da kissoshi masu kayatarwa a cikin hotuna wadanda suka dace da irin shekarunsa,
a cikin dakinsa, ko inda hannayensa za su iya dauka.
b.
Yin tarayya da shi cikin
karance-karancen littatafansa da kissoshin da ya ke so.
c.
Tafiya da shi dakunan karatu ko
laburare, da karfafa shi kan zaban wasu kissoshi da kansa.
d.
Amsa masa wasu daga cikin
tambayoyinsa, da kuma nusar da shi wasu littatafan da za su amsa masa sauran
tambayoyin.
e.
Yin amfani da salo mai cike da
hikima, ta hanyar hakaito masa kissoshi masu dadi, sai kuma a nuna masa
littatafan da suka kunshi kissoshin da suka fi nasan dadi.
f.
Karfafar yaro da kyaututtuka, da kuma
kalmomin karfafa guiwa da yabawa, ga dukkan cigaban da yaron ya samu ta
bangaren karatu.
g.
Sai kuma kulla alaka tsakanin
nashadodin da yaron ya ke so, da karance-karance.
Kuma da wadannan hanyoyin ne yaronka zai mallaki mabudan
ilimi da masaniya, Da fatan ya samu kansa cikin wadanda Allah ke magana akansu
cikin fadinSa: "ALLAH NA DAUKAKA DARAJOJIN WADANDA
SUKA YI IMANI, DAGA CIKINKU, DA NA WADANDA AKA BAIWA ILIMI"
[Mujadilah: 11].
No comments:
Post a Comment