TA YAYA ZAN YI ALWALA
(كيف أتوضأ؟)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Abokaina!
ASSALAMU
ALAIKUM WA RAHMAULLAHI WA BARAKATUHU
Yaya ku ke?
Shin 'dayanku, ya san ma'anar kalmar
"Wudu'u"; alwala?
E, kun kyauta.
"Wudu'u", daga kalmar
"wada'ah" ne, wanda itace: tsafta.
Hakika Musulunci ya shar'anta mana yin
alwala gabanin kowace sallah,
Don haka, Na zo, domin mu koyi yadda za
mu yi alwalar, a tare?
Gabanin yin alwala, dole ne mu ambaci
sunan Allah Ta'alah; sai mu ce: BismilLahi.
Sa'annan mu wanke tafukan hannayenmu
biyu, sosai har sau uku, kuma ya dace mu tsettsefe yatsunmu da ruwa, kamar
haka.
Sa'annan mu shigar da ruwa cikin
bakunanmu, domin mu wanke su, sosai, kamar haka, kuma za mu aikata hakan har
sau uku. Kuma wannan aikin ana kiransa da suna: kurkuran baki.
Sai kuma mu sanya sashin ruwa a cikin
hancinmu, sai kuma mu fitar da shi, za mu aikata hakan har sau uku shima. Kuma
wannan aikin ana kiransa da sunan: Shaka ruwa a hanci da fyacewa.
Sa'anan mu wanke fiskokinmu gaba daya,
kamar haka, har sau uku. Kuma dole ruwan ya game dukkan fiska; tun daga kunnen
dama, zuwa kunnen hagu. Sannan kuma daga farkon goshi har zuwa haba, kamar
yadda kuke gani.
Sa'annan sai mu wanke hannayenmu biyu,
sau uku, tun daga kan 'yan yatsunmu, har zuwa guiwowin hannu, kamar haka. Kuma
za mu fara ne da hannun dama, daga farko. Sai kuma hannun hagu ya biyo baya.
Sa'annan mu shafi kanmu gaba dayansa, sau
daya, sai mu fara shafan, ta gaba, har zuwa baya. Sai kuma daga bayan mu tafo
gaba, kamar yadda kuke gani.
Sa'annan sai mu shafi kunnuwanmu biyu
gaba daya, sau daya, da ruwan da muka shafi kanmu dazu.
Sa'annan mu zo ga wanke kafofinmu, sai mu
wanke su sosai, har zuwa idanun sawu, sau uku. Kuma za mu fara da kafar dama
daga farko, sai kuma mu biyar da wanke kafar hagu.
To, da wannan ne –Ya ku abokaina- za mu
zamto mun gama alwala, Sai kuma mu yi irin addu'ar da Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ke fadanta a bayan kammala alwala. Mu fada tare, mu ce:
ASH-HADU AN
LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN
ABDUHU WA RASULUHU, ALLAHUMMAJ AL'NIY MINAT TAWWABINA, WAJ'ALNIY MINAL
MUTADAHHIRINA.
Hum, Yanzu ya ku abokaina, mun wayi gari
cikin shirin yin sallah.
Allah ya karba mana, mu da ku.
Wassalamu alaikum wa rahmatul Lahi wa
barakatuhu.
No comments:
Post a Comment