2017/05/19

hudubar 23 SHA'ABAN 1438h ta Dr Abdullahi Albu'aijan daidai da 19 Mayu 2017M MASALLACIN ANNABI s a w











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 23/Sha'aban/1438H
daidai da 19/Mayu/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya saukar da Qur'ani a watan azumi, yana mai shiriya ga mutane, da hujjoji bayyanannu, daga shiriya, da kuma rarrabewa, kuma Ya fifita ramalana akan sauran watanni, da zamani.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, shaidawa irin ta gaskiya da imani,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, jagora ga qabilar Adnan, kuma mai ceton talikai, a yinin da yara a cikinsa ke fitar da furfura,
Allah ka yi qarin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su, da kyautatawa.

Bayan haka:
Ya ku bayin Allah;
Lallai ne Allah yana da kyautuka da baiwa, da kuma lokutan alkhairi da xa'oi, wanda a cikinsu rahamomi ke sauka, albarkoki kuma su ke gamewa,
Kuma yana daga cikin waxannan lokutan, tsarkaka masu daxi; WATAN DA A CIKINSA AKE RURRUFE QOFOFIN WUTA, SAI KUMA A BUXE QOFOFIN ALJANNONI,
Kuma haqiqa, ajalin wannan lokacin ya kusanto, zamaninsa kuma ya qarato, saboda babu abinda ya rage a tsakaninku da shi, face wasu yini qididdigaggu,
Sai ku zaburo, a cikinsa da aikata xa'oi, da kuma ninninka kyawawan aiyuka, tare da rabauta da samun kankare munanan ayyuka,
Kuna masu qara zage-damtse, kuma ahir xinku da jinkirin alkhairi, ko samun rauni, domin watan ramalana kwanaki ne qidayayyu, kuma awowi, qididdigaggu, wanda kuma babu fagen wargi a cikinsu ko wasa, kuma babu fagen nuna kasala, kuma ramalana ba fage ne na aikata savo ko munana ayyuka ba, saboda ayyuka, a cikin watan ana ninninka su, "Kuma wanda ya yi rowa, to haqiqa yana yin rowa ne a kansa" [Muhammadu: 38].
"Kuma duk wanda ya kafirce, to kafircinsa zai koma kansa" [Faxir: 39].
"Kuma wanda ya yi tsirfar zunubi, to yana tsirfarsa ne, kawai a kan kansa" [Nisa'i: 111].
"Kuma wanda ya warware, to lallai yana warwarewan ne, kawai akan kansa" [Fat-h: 10].
Don haka; ku nuna wa Allah alkhairin da ke cikin rayukanku, saboda shaqiyyi, shi ne wanda a cikin watan ramalana aka haramta masa samun rahamar Allah.

Tilas, ku yi tanadi da shiri, kuma ku tuba, kuna masu bin dokoki da taqawa, saboda tsoron Allah shi ne mafificin guzuri, "Ya ku waxanda su ka yi imani, an wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].

Ya ku Bayin Allah … !!!
Allah ya shar'anta yin azumin ramalana, kuma Ya farlanta muku shi ne, ba domin yunwa da qishi ba, ba kuma domin qishi da gajiyarwa ba, sai domin ku samu taqawa, saboda taqawa manufa ce abar nema, kuma "dayawa daga masu azumi, basu da komai daga azuminsu, face yunwa, da qishi", haka kuma masu sallar dare dayawa, basu da komai daga tsayuwansa, face hana kai barci, da gajiya.
"Kuma duk wanda bai bar maganar qarya ba, da yin aiki da ita, to Allah bashi da wata buqata; kan ya bar abin cinsa, da abin shansa".
"Kuma azumi garkuwa ne, don haka; idan yinin azumin xayanku ya zo, to kada ya yi 'rafasu' (wato, batsa cikin zance da iyali ko jima'i), kada kuma ya yi ihu, Idan wani ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi, sai ya ce: Ni Mutum ne mai azumi".
Don haka; ba zai yiwu a kusanci Allah ta'alah a halin azumi da barin ababen da mutum ke sha'awa na halal ba, sai bayan an kusance shi, ta hanyar nisantar abinda Allah ya haramta, a cikin kowani hali, kamar qarya da zalunci, da yin ta'addanci ga mutane, cikin jinanensu da dukiyoyinsu da mutuncinsu.
Sai ku azumci watan ramalana, kuma ku kiyaye shi, kuma ku sani lallai ku masu haxuwa ne da Ubangijinku.

Ya ku bayin Allah … !!!
Ramalana, wata ne na gafara, wanda ake 'yanta mutane a cikinsa, sai ku kusanci rahamar Allah, kuna masu aiki da sababi, saboda shi Allah, Mai baiwa ne, Mai karamci, Mai yawan kyauta, An ruwaito daga Anas –Allah ya qara yarda a gare shi- yana cewa: "Annabi ya hau matakalan farko na minbari, sai ya ce: AMIN!
Sai kuma ya sake hawa matakala na biyu, sai ya ce: AMIN!!
Sa'annan ya hau matakala na ukun, sai kuma ya ce: AMIN!!!
Sannan, ya daidaita; ya zauna, Sai sahabbansa su ka ce: Akan me ka ce, AMIN?
Sai ya ce: Mala'ika Jibrilu ne ya zo mini, sai ya ce: Allah ya turbuxa hancin mutumin da aka ambace ka a wurinsa, sai bai maka salati ba, Sai na ce: Amin.
Sai ya sake cewa: Allah ya turbuxa hancin mutumin da ya riski iyayensa biyu, sai ba a gafarta masa ba, Sai na ce: Amin.
Sai ya ce: Allah ya turbuxa hancin wanda ya riski watan azumi, sai ba a gafarta masa ba. Sai na ce: Amin".
Ina neman tsarin Allah daga hanin aikata alkhairi da tavewa, da kuma mummunan qaddara, da riskar tavewa.

Kuma hadisi ya zo daga Abu-hurairah  -Allah ya qara yarda a gare shi-, ya ce: daga Annabi (SAW) yana cewa: "Wanda ya yi azumin ramadana yana mai imani, da neman lada: an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar dare yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar lailatul-kadri, yana mai Imani, da kuma neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa".

Ya ku, bayin Allah…!!
Azumi yana cikin manyan ibadodi da ake kusantar Allah, da kuma xa'oi, waxanda su ka fi girma, da aiyuka mafiya girman lada, kuma lallai shi azumi ibada ne na masu haquri, kuma guzuri ne ga masu taqawa, kuma tanadin masu neman samun rabo, ladansa kuma, yana da girma, kuma alherinsa yana da yawa, kuma amfaninsa bashi da makamanci, saboda azumi waraka ne ga cutuka, kuma yana bada lafiya da qarfi da kuzari da magani, ga rayuka da jiki, kuma yana tarbiyya, kuma yana bada hutu ga jiki, sama da haka kuma gaba xaya, azumi ya kasance xa'a ne ga Ubangiji, kuma gafara, ga zunubai,

Kuma ya ishi azumi falala, kasancewar Allah ta'alah, da ya raba ayyukan 'yan'adam kashi biyu, Ya sanya azumi ya kasance kaso xaya mai cin gashin kansa, kuma ya jingina shi ga kansa, sannan kuma, ya sanya sauran ayyukan 'yan'adam (gaba xayansu) a matsayin xaya kason,  An ruwaito daga Abu-Hurairah –Allah ya qara yarda a gare shi- yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Dukkan  ayyukan xan adam ana ninninka masa, kyakkyawa da kwatankwacinsa goma, har zuwa ninki xari bakwai. Allah ta'alah ya ce: Sai dai kawai AZUMI, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, yana barin sha'awarsa da abincinsa domin Ni.
Mai azumi yana da farin cikin iri biyu, da zai yi su, farin cikin farko, a lokacin buxa-bakinsa, sai kuma wani farin ciki, a lokacin ganawa da Ubangijinsa.
Kuma lallai warin bakin mai azumi, ya fi daxi, a wurin Allah, fiye da turaren almiski".
            Kuma haqiqa Allah ya keve wa masu azumi shiga ta wata qofa daga cikin qofofin aljannah, wanda ba za a musu cinkoso ba ta wannan qofar, kamar yadda ya keve musu wata liyafa wanda ba za a yi tarayya da su cikin amfani da ita ba, An ruwaito daga Sahal bn Sa'ad –Allah ya qara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Lallai a aljanna akwai wata qofa, wanda ake ce mata: AR-RAYYANU, Wanda masu azumi ke shiga ta cikinta ranar qiyama, babu wani wanda ba su ba, da zai shiga tare da su, za a ce: Ina masu azumi? Sai su shiga ta wannan qofar, Idan na qarshensu su ka shiga, sai a rufe ta, kuma babu wani da zai shiga ta wannan qofar, kuma duk wanda ya shiga zai sha ruwa, kuma duk wanda ya shiga ba zai ji qishi ba, har abada".

            Allah ya sanya ni da ku, daga cikin masu riskar azumi, waxanda za su samu karvuwa.

Ina faxan abinda ku ke ji, …

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ke karvar tuba daga bayinSa, kuma ya ke yafe laifuka, kuma yana sane da abinda ku ke aikatawa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, rahamarSa ta game kowani abu, kuma ni'imarSa ta game komai.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, kuma zavavve daga cikin halittarSa, kuma badaxinSa, kuma Shi ne ya fi jivintar muminai fiye da kansu, kuma matansa Uwayensu ne, kuma cetonsa shi ne tsiransu, addu'oinsa kuma shi ne rabautarsu,

Allah ya qara salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu da shiriyarsa, kuma ya yi addu'ar neman yarda ga sahabbansa.

Ya ku bayin Allah !! …
Musiba a cikin addini ita ce, mafi girman musiba, (Malam) As-Saffariniy yana cewa: "Musibu; wata ta fi wata, sai dai kuma wanda ta fi su girma, ita ce musibar da ta kasance a cikin addini –Muna neman tsarin Allah daga hakan-, saboda ta fi kowace musiba, kuma mutumin da aka wawashe, shi ne wanda aka xauke masa addininsa;
Saboda,
dukkan karaya, ana fatar Allah zai yi xorin ta
Sai dai babu xori ga karayar da ta kasance, a addini
Don haka,
idan ka ga wani mutum, baya damuwa da abinda ya same shi ta vangaren addininsa, kamar ta fiskar aikata zunubai da laifuka, ko barin juma'a da sallar jam'i, da sakaci da lokutan xa'a, ko aukawa cikin haramun, kamar keta alfarmar shari'a, da qetare iyakokin Allah, da tsallake su, to ka san, lallai wannan mutumin an jarrabe shi, alal haqiqa, sannan ka qara sani cewa, lallai wannan ya mutu; shi yasa ba ya jin raxaxin wannan musibar".
Musibarsa ta yi girma, kuma ta fanqama, kuma abin a masa taziya ya yi girma, nadamarsa kuma za ta yi tsayi, Wa? Mutumin da ya tozarta damarsa ta yin azumin ramadana, har lokacin hakan ya wuce.

Haqiqa an gafarta zunubai, kuma an suturce aibuka, an kankare laifuka, kuma an yi afuwa ga kura-kurai, an xaukaka darajoji, an ninnika kyawawa, shi kuma, dolon an haramta masa (waxannan gaba xaya), kuma ya halaka kansa, kuma bai yi rahama ga raunin ransa ba, kuma bai xora karayar ransa ba, ya kuma wuce iyakar shari'a akan haka, muguntarsa ta  halaka shi, kuma walaqancinsa ya tavar da shi, baqin ciki kuma, ya dabaibaye shi.
Ya mai neman aikata alkhairi, ka fiskanto!
Ya mai neman aikata sharri –kaitonka- ka taqaita!

Ya kai mutumin da ya yi sakaci a ramadanan da ya gabata, ya tozarta watan, ya bar shi ya wuce, Sai kuma Ubangijinsa ya masa baiwar qarin lokaci a rayuwa, har ya sake riskar wani ramadanan na daban, To ka gode wa Allah, a kan wannan ni'imar (riskar ramadana), kuma ka fiskanci Ubangijinka, gabanin mutuwa ta zo kwatsam, ko rayuwarka ta qare cikin tavewa, ko qarfinka ya yi rauni, furfura kuma ta yi qarfi,
A lokacin, (babu abinda zai rage) sai, YA HASARATA! YA KAITONA!! YA BAQIN CIKINA!!!
"Ya Ubangijina! Don me ba ka yi mini jiinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci, domin in gaskata, kuma in kasance daga salihai" [Tagabun: 10].
"Ya Ubangijina! Ku mayar da ni (duniya) * tsammanina in aikata aiki na kwarai, cikin abinda na bari, Kayya, lallai ne ita kalma ce da ya ke faxinta, alhali a baya gare su, akwai wani shamaki, har ranar da za a tayar da su" [Mu'uminuna: 99-100].
"Kuma Allah ba zai jinkirta wa rai ba idan ajalinta ya zo" [Munafiquna: 11].
KAITONSA!!! Kuma sannan KAITONSA!!!

Ya ku bayin Allah…!!
Lallai wahalar da ke cikin aikin xa'a tana tafiya, sai daxinta ya wanzu a cikin wannan rayuwar, Ladanta kuma a lahira, taska ce da aka tanada,
Kuma daxin da ke cikin savo yana tafiya; ya qare, sai tavewa ta wanzu na tsawon zamani, wahalar cikinta kuma na tsawon rayuwa, A lahira kuma uquba, da hasara.
Daxi na qarewa daga mutumin da ya samu madararta
Daga haramun, sai zunubi da aibi su wanzu,,,

Aqibar mummunan abu yana wanzuwa a qarshensa
Babu alheri, ga daxin da wuta ce a bayansa,,,

Daga qarshe,
Ya ku bayin Allah…!!
            Lallai Allah ya kwararo mana ni'imomi, kuma ya karrama mu da aminci da zaman lafiya, ya kuma nisantar da mu fitintinun da mu ke ganin suna sauka ga wasunmu a wannan zamanin, har su halaka shuki da 'ya'ya, sannan su rarraba haxin kan mutane.

            Don, haka, Ya wajaba akanmu mu yi ta godiya a kowani lokaci, kuma GODIYA TA TABBATA GA ALLAH a kan ni'imar zaman lafiya da imani, kuma godiya ta qara tabbata ga Allah, wanda mu ke roqon ya kai mu watan ramadana.
            Kuma wajibi akanmu, mu tsayu sahu xaya, a fiskar wanda ransa ta ke saqa masa, ya kawo mana barazana ga zaman lafiyarmu, ko kuma ya shuka fitina a cikin tafiyarmu da haxin kanmu, ko domin ya raunata qarfinmu.
            Saboda abinda ake nufin a lalata mana –Ya ku taron 'yan'uwa- shine aqidarmu da addininmu,

Kuma duk lokacin da musulmai su ke shirin shiga wani lokaci na musamman, daga cikin lokutan addininsu, sai a qulla musu makirci, domin a hana su amfana da shi, a kuma kikkitsa musu qulle-qullen fitina.
Kuma lokutan zartar da rukunnan musulunci, masu shaida akan haka; lokutan ramadana suma sun shaidi hakan, lokutan aikin hajji da umrah suma sun shaidi hakan,

Sai dai kuma imaninmu da Allah, da amintuwar da mu ka yi da jagororinmu shiryayyu, da aqidarmu tabbatacciya, za su sanya masu ha'intarmu yin hasara, rabonsu kuma ya zama tavewa, kaidin da su ka qulla kuma, ya koma ga qirazansu, saboda "makircin cuta baya faxawa, sai ga mutanensa" [Faxir: 43].
Kuma daularmu ba za ta canza daga aqidarta, ko haxin kanta ba.
Kuma da sannu Allah zai kiyaye amincinmu, da kuma addininmu, "Sai su bauta wa Ubangijin wannan xakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].

            Ya Allah! Ka kiyaye wannan qasar da kiyayewanka,
 Ya Allah! Ka dawwamar mata da amincinta da zaman lafiyanta, da haxin kanta,
Ya Allah! Ka kiyaye ta daga fitintinu; wanda su ka bayyana daga cikinsu da waxanda su ka vuya,
Ya Allah! Wanda ya nufi qasar nan da mummuna, ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka mayar da kaidinsa zuwa ga qirjinsa

Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.

,,,          ,,,          ,,,



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...