HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 25/SHA'ABAN/1439H
daidai da 11/MAYU/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
DR. HUSAIN BN ABDUL'AZIZ AL-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
HAKIKANIN DUNIYA
Shehin Malami wato: Husaini
bn Abdul'aziz Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DAGA CIKIN SUNAYEN ALLAH
KYAWAWA AKWAI: AS-SAMADU; WANDA AKE NUFI DA BUKATU, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Madaukakin da yafi daukaka, kuma ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin
tarayya a Lahira da Duniya.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa; annabi zababbe, kuma Manzon da Allah
ya zabo, Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka a gare shi, da kuma
iyalansa da sahabbansa; ma'abuta ilimi da takawa.
Bayan haka:
Ya ku, Musulunci …
!!!
Ina muku, wasici da ni
kaina da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka; domin "Duk wanda yay i takawar Allah, zai sanya masa mafita * Kuma
ya azurta shi, ta inda baya zato, kuma duk wanda yay i tawakkali ga Allah, to
lallai ya isar masa" [Dalak: 2-3].
Ya ku al'ummar Musulmai!!!
IMANI DA SUNAYEN ALLAH
KYAWAWA, DA SIFOFINSA MADAUKAKA, 'DAYA NE DAGA KARKASUWAN TAUHIDI (uku), Kuma yana cikin
ababen da imani da Allah ke hukunta su.
Sanin sunayen Allah da
sifofinsa, da yin bauta a gare shi da su, yana da matsayi mai girma, da daraja
madaukakiya.
Mumini ya kan tabbatar wa
Allah irin abinda Allahn ya bada labari akansa, da dukkan ababen da Manzon
Allah –صلى
الله عليه وسلم- ya bada labari akanSa; na sunaye kyawawa, da sifofi madaukaka;
yana mai yin imani da dukkan haka, ba tare da kamanta su da sifofin halittun
Allah ba, ko fadin kaifiyyarsu ba, irin fadin kaifiyyar kungiyoyin mushabbi'ah
(wato, masu kamanta Allah da halittu), kuma ba tare da an jirkita kalmomin
Allah daga gurabensu ba.
Kuma Mumini yana tsarkake Allah;
sai ya kore masa dukkan nakasa da aibi, ba tare da ya kore masa sifofinsa ba;
A'a! zai kore masa dukkan abinda Allahn ya kore wa kansa ne, wanda hakan ya
kunshi tabbatar da cikar sifofinsa, wato dunkulallen korewa wanda ya kunshi
tabbatar da kishiyoyin sifofin da aka kore, Misali, cikin fadinSa Ta'alah: "Masanin gaibu,
gwargwadon kwayar zarra ba ta nisanta ko ficewa daga iliminSa" [Saba'i: 3]. To, sai
Muminai suna tabbatar masa da cikar iliminSa.
A cikin fadinSa Madaukaki: "Kuma wata 'yar
gajiya bata shafe mu ba" [Kaf: 38], a nan, Muminai suna tabbatar masa cikar
kudurarSa.
Domin imaninsu ya kan
kasance ne kamar yadda nassoshi na shari'a suka tabbatar, ba tare da jirkitawa
ko korewa ba, kuma ba tare da korewa ko kamantawa ko misaltawa ba; domin babu wani
abu wanda yake yin kamantacceniya da Shi (Ta'alah) cikin zatinSa, ko sifofinSa,
da ayyukanSa; saboda Allah shine wanda ya sifantu da kamala ta kowace fiska,
cikin sifofinSa da sunayenSa da ayyukanSa; Allah Ta'alah ya ce: "Babu wani,
kwatankwacin Allah, Kuma shine Mai ji, Mai gani", [Shura: 11].
Ibnu-Abdulbarri –رحمه الله- ya ce: "AhlusSunnah sun yi
ijma'i, kan tabbatar wa Allah dukkan sunayen da suka zo cikin Alkur'ani da
sunnah, da yin imani da su, da daukarsu kan hakikaninsu; ba a kan majazi ba,
kuma lallai su AhlusSunnah ba su fadin yanayi da kaifiyyar kowace sifa, kuma
basu iyakance mata wata sifa iyakantacciya".
Kuma an tambayi
Imamu Malikin kan fadinSa Madaukaki: "Mai-Rahama ya daidaita a saman
Al'arshi"
[Daha: 5], aka ce: Ta yaya ya daidaitu? Sai
ya ce: "Lafazin daidaito mana'arta sananne ne, Yanayinsa kuma, abu ne da aka
jahilta, Imani da shi kuma wajibi ne, Tambaya akansa kuma bid'ah ne".
Kuma wannan maganar an ruwaito ta daga Ummu-Salmah da Malamin
Malik, wato: Rabiy'ah.
Kuma SunayenSa kyawawa da sifofinSa madaukaka, sune ginshikin
yin bauta ga Allah, ta fiskar da ta fi kamala. Da tsarkake Allah, da yin yabo
ko godiya a gare shi; Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yana da sunaye masu kyawu; sai
ku roke shi da su, kuma ku bar wadanda suke yin ilhadi a cikin sunayenSa" [A'araf: 180].
Kuma lallai fadinSa: "Sai ku roke shi da su"
Ya game addu'ar bauta, da
addu'ar roko; ta yadda a kowace mas'ala, Bawa sai ya yi roko da abinda yake
dacewa da bukatarsa; kamar mai yin addu'ar ga misali ya ce: YA ALLAH, ka min
gafara, ka ji kaina; Lallai ne kai Mai gafara ne Mai jin kai. Kuma ka karbi
tubata Ya Mai yawan karbar tuba, Ka azurta ni, Ya Mai azurtawa, ka tausasa min
Ya Mai tausasawa,,, haka,dai, haka dai.
Kuma
lallai yana daga cikin sunayen Allah AS-SAMADU (Wanda ake nufi da
bukatu), "Ka ce, shine Allah Makadaici * Allah shine Wanda ake nufinSa da
bukatu * Bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba * Kuma babu daya da ya kasance
tamka a gare shi"
[Ikhlas: 1-4].
Don haka, idan bawa, bukatu suka dabaibaye ka, kuma tsanani ta
kowace fiska ya dufafo ka, kuma bakin-ciki ya kewaye ka, to sai ka nemi mafaka
daga Makadaici abin nufi da bukatu, domin shine ake nufi cikin wadaci da halin
tsanani, kuma shine ake nufa a lokacin bakin ciki, da halin nema.
Allah shine wanda ake neman agajinsa lokacin musibu, da
tashin-tashina, da lokacin fitintinu …
Mu –mutane- a cikin kowace dakika, muna da matsanancin
bukatar Ubangijinmu Mai girma, Makadaici Abin nufi da bukatu, kuma muna da
bukatar mu nufe shi da addu'a, cikin kan-kan-da-kai, da soyayya, da ikhlasi,
cikin tsoro da kwadayi.
Kuma lallai muna da matsanancin bukatar mu rika rokonSa (Ta'alah)
a yanayin sauki da halin tsanani, muna masu fatan samun abinsa a halin ni'imomi da cutuka, za mu rika kan-kan-da-kai
gare shi, mu firgita mu tafi ga neman mafaka daga gare shi, domin a ni'imtar da
mu da samun manufofi madaukaka, da bukatu masu girma, a Duniya da Lahira.
Kuma lallai muna da matsanancin bukatar mu karkade zukatanmu
daga wanin Allah SWT, kuma mafakarmu ta kasance zuwa ga Allah ne shi kadai, da
sunayensa masu kyau, da sifofinsu madaukaka, Allah Ta'alah ya ce: "Shine Rayayye, Babu
abin bautawa da cancanta face shi, Sai ku roke shi kuna masu tsarkake addini a
gare shi",
[Gafir: 65].
Ibnu-Taimiyya –رحمه الله- ya ce: "Manufar a nan
itace, lallai badadai biyu; wato annabi
Ibrahima da Muhammadu –عليهما الصلاة والسلام- sune suka fi dukkan
kebantattun mutane cikar tauhidi … Kuma cikar tauhidinsu yana nan ne ta hanyar
tabbatar da kadaituwar Allah cikin uluhiyya, wanda kuma shine; kada wani abu ya
wanzu, a cikin zuciya wanda ba Allah Ta'alah aka nufa da shi ba".
Sau nawa mutum a cikin wannan rayuwa ya ke samun kansa cikin
wasu yanayi, wadanda ya ke jin yana cikin hatsari mai girma, Amma babu wurin
gudu daga wadannan hatsarin, sai ta hanyar komawa ga Mai kiyayewa, Mai karfi,
Abin nufi da bukatu, Mai girma, don haka; Allah ne shi kadai ke kiyaye
maslahohinka, kuma shi kadai ne, a hannunsa yake da ikon tunkude maka cuta da
hatsari, saboda shine mai kiyaye Majibintansa daga abubuwa masu halakarwa, ya
tausasa musu, cikin dukkan motsawa.
Allah shine Makadaici wanda ake nufinsa cikin bukatu da
matsaloli, kuma shine dukkan halittu suke nufansa, cikin dukkan bukatunsu, da
halayensu da lalurorinsu; saboda abinda ya sifanta da shi na kamala cikin
zatinSa da sunayenSa da sifofinSa da ayyukansa.
Ta yaya Musulmi zai tabe, alhalin Ubangijinmu shine Makadaici
abin nufi da bukatu, wanda ya siffanta da dukkan kamala; domin shine/
shugaban da ya zama kamili
cikin shugabancinSa,
Madaukakin da ya yi girma
cikin daukakarSa,
Mawadacin da yake da kamala
cikin wadacinSa,
Mai girman da ya samu
kamala cikin girmanSa,
Mai ilimi wanda ya samu
kamala cikin iliminSa,
Mai hikima wanda ya samu
kamala cikin dukkan sifofin daukaka da shugabanci da karamci da kyauta, da
sauran sifofin girma, da izza, da galaba, da buwaya da kudura, da rahama, da
jin-kai da kyauta.
Don haka; Izuwa gare shi kadai, -Ya kai bawa- zaka bayyanar
da kwadayi, sai kuma ka tsarkake shi da ibada, da tawakkali, da kuma cikin ibadodin
fata, da soyayya, da maida-lamari, da kan-kan-da-kai, da tsoro, da mika-wuya da
rusunawa, "Saboda haka, idan ka kare ibada, ka kafu zuwa ga rokon Allah * Kuma
ga Ubangijinka sai ka bayyanar da kwadayi", [Sharh: 7-8].
Ya Wanda hanyoyi suka kuntata a gare shi, Dabarun neman
mafita suka wahalar da shi, Ka nufi kofar Ubangijinka, ka fadi a gaba-gare shi.
فإذا
ضاقت بك الأحوال يومًا
DA 'DAI IDAN WATARANA
HALAYE SUKA KUNTATA A GARE KA
فثق
بالواحد الفرد العليّ
TO, KA AMINTU DA MAKADAICI
GUDA DAYA MADAUKAKI
Saboda Allah سبحانه shine Mai tausasawa ga bayinSa, wanda
iliminSa ya game dukkan sirri da ababe na boye, kuma yake riskar boyayyan
lamura, "Lallai Allah Mai taushi ne, Mai bada labari" [Lukman: 16].
"Lallai Ubangina Mai
tausasawa ne ga abinda yake so" [Yusuf: 100]. Don haka Allah shine Mai
tausasawan da idan ya nufi aukuwar abu, to sai ya samar da sabbuban aukuwarsa cikin
kamalar ludufinsa, a boye, har a wasu lokutan irin abinda baya aukuwa a
al'adance, sai ya auku.
Kuma shine Ma'abucin karamcin da ya kai kololuwa; don haka,
duk lokacin da ababen bakin-ciki suka hadu akanka, musibu suka dabaibaye ka, to
ka nemi mafaka a wurin wanda ake nufinsa da biyan bukatu, Mai girma, wanda ke aikin
dora karyayye, ya ke tsamo bawa daga bakin ciki, yake kwaranye cutuka ga halittu da yaki, saboda babu wani
bakin ciki face Shine mai dauke shi, kuma babu wata cuta, face Shine ke warkar
da ita, kuma babu wani bala'i face Shine mai yaye shi; domin Shine ma'abucin
kudura cikakkiya, da nufi mai zartuwa, yana dauke bakin ciki, yana kwaranye
bala'oi, "Kuma wanene ke amsawa mabukaci, a lokacin da ya kira shi,
kuma ya ke kwaranye mummuna, kuma yake sanya ku masu mayewa a ban kasa!",
[Naml: 62].
"Ka ce, Allah shine
yake tsiratar da ku, daga gare su, da kuma dukkan bakin ciki", [An'am: 64].
Sai ka fake -Ya kai Musulmi-, izuwa ga wanda ke kubutarwa;
wato Ubangijinka, wanda idan ka kusance shi kake samun debe kewa, da farin
ciki, da gyaruwar lamura, da tsarki, da rabauta, da cin nasara, da natsuwa, da
aminci.
Ma'abuta littafin Sunan sun
ruwaito daga Abdullahi bn Buraidah, daga Mahaifinsa, lallai ne shi ya shiga
masallaci tare da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), sai ga wani mutum yana sallah yana
addu'a, a inda yake cewa: Ya Allah! Lallai ni ina rokonka, da kasancewar ina
shaidawa babu abin bautawa da cancanta face kai, Makadaicin da ake nufinsa da
bukata, wanda bai Haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani da ya
kasance tamka a gare shi", Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ina rantsuwa da
wanda raina ke hannunsa, lallai ya roki Allah da sunansa mafi girma, wanda idan
aka roke shi da shi ya kan bayar, idan kuma aka masa addu'a da shi sai ya amsa". Maluma dayawa sun
inganta shi. Kuma Ibnu-Hajar ya ce: Wannan hadisin, shine mafi rinjayen abinda
aka ruwaito dangane da sunan Allah wanda yafi girma, ta fiskar isnadi.
Ina fadar wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma
sauran Musulmai daga kowani zunubi, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai yawan gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah yabon
da ya dace da girmansa da kyawunsa da matsayinsa.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu bawansa ne manzonsa. Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a
gare shi, da kuma iyalansa da sahabbansa.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai!!!
Ina muku wasiyya da kaina
da bin dokokin Allah Mabuwayi da dauka, saboda takawa itace wasiyyar Allah ga
mutanen farko da na karshe.
Ya ku Musulmai!!!
Akwai bukata mai tsanani;
Kowane Musulmi zuciyarsa ta koshi da sanin ma'anonin sunaye kyawawa na
UbangijinSa, da abinda yake da shi na sifofin girma da kamala.
Kuma da aikata haka mutum zai
haifar, da ababen mamaki na imani da cikar yakini, sai ka same shi, baya sauke
bukatunsa sai ga Allah, Zuciyarsa kuma tana mai barranta daga jin tana da wayo
da karfi, sai kawai daga Allah; kuma sai zuciyarsa ta ratayu da Allah, da
ilimin saninsa, da sonsa, da girmama shi. Kuma rayuwarsa gaba dayanta sai ya yi
ta ga Allah, kamar yadda Allahn yake cewa: "Ka ce, lallai ne
sallata, da yanke-yankena, da rayuwata, da mutuwata ga Allah ne Ubangijin
Talikai * Bashi da abokin tarayya, kuma da aikata wannan aka umarce ni, kuma ni
ne farkon masu mika wuya ga Allah", [An'am: 162-163].
Sannan ya mana umarni da
wani lamari mai girma, wanda rayuwarmu zata tsarkaka da shi, wanda kuma shine:
Yin salati da sallama ga wannan Annabin Mai karamci;
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka ga bawanka kuma
manzonka annabinmu Muhammadu.
Kuma ya Allah! Ka
yarda da khalifofi shiryayyu, da kuma iyalan Annabi da sahabbansa gaba daya. Da
wadanda suke biye da su, da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Addu'a
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment