2017/09/28

خطبة الحذيفي 9 محرم 1439هـ الموافق 29 سبتمبر 2017











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 09/MUHARRAM/1439H
daidai da 29/SATUMBA/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
,,
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:,,, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Mai hikima Maxaukaki, Ma'abucin nau'ukan girma, da xaukaka,
            Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda babu mai qididdige su, face Shi,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, ma'abucin falala da baiwa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka kevance shi da fiyayyun xabi'u da halaye,
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu gaggawar aikata kyawawan ayyuka.

Bayan haka:
Ku bi Allah Ta'alah da taqawa, ta hanyar kusantarsa da abinda ya ke so, kuma ya yarda, da kuma nisantar dukkan ababen da ya ke qi; baya so. Saboda taqawa, ita ce, ta ke gyara kowane abu, a wannan rayuwar, kuma da ita ake samun darajoji a bayan mutuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya yi taqawar Allah zai sanya masa sauqi a lamarinsa" [Xalaq: 4].
Kuma ya ce: "Wancan Aljannar ce wacce muke gadar da wanda ya kasance mai aiki da taqawa, daga bayina" [Maryam: 63].

Ya ku, Musulmai… !!!
Lallai shari'ar Allah mai tsarki ta yi umarnin samar da haxin kai da daidaito (ittifaqi), ta kuma yi hani kan savani da rabuwar kai, domin kiyaye addinin musulunci, wanda  rayuwa bata tsayuwa face da shi, kuma ba a samun Aljanna idan ba a yi aiki da musulunci ba. Kuma domin kiyaye zamentakewar al'umma daga kekkecewa, da wargajewa, da zaman kara-zube, da jayayya, da zalunci, da varna. Kuma domin kiyaye al'umma daga cin karo, da rabuwar kai, da qiyayya, da yin faxa da juna. Kuma domin kiyaye maslahohi da amfanoni da haqqoqi na xaixaiku da na al'umma. Kuma domin samar da kwanciyar hankali da adalci da zaman lafiya, Kuma domin waxannan manufofin ne gabaxayansu, Allah (S.W.T) ya yi umarni kan haxin kai, ya kuma yi hani kan savani, a inda ya ke cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba, kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, a lokacin da kuka kasance maqiya, sai ya daidaita tsakanin zukatanku, sai kuka wayi gari da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance akan gavar ramin wuta, sai ya tsamar da ku daga gare ta, Kamar haka, Allah yake bayyana muku ayoyinSa, domin ku samu shiriya" [Ali-imrana: 103].
Kuma Allah ya ce: "Kuma ku taimaki juna akan aikin kwarai da taqawa, kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci" [Ma'ida: 2].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma mumunai maza da mumunai mata, sashen majivincin sashe ne" [Tauba: 71].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Lallai muminai 'yan'uwan juna ne" [Hujurat: 10].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Sai ku tsayar da sallah, kuma ku bayar da zakkah, kuma ku yi riqo da Allah; domin shi ne majivincinku, madalla da Shi ya zama majivinci, madalla da Shi ya zama Mai taimako" [Hajj: 78].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya yi riqo da Allah, to lallai an shiryar da shi zuwa hanya miqaqqa", [Ali-imran: 101].
Kuma an ruwaito daga Abu-Musa (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mumini ga mumini, kamar gine ne wanda sashensa ke qarfafar sashe", Sai ya shigar da yatsu a cikin yatsunsa. Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma an ruwaito daga An-Nu'uman bn Bashir (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Misalin muminai, cikin soyayyarsu da jin-qai ga junansu, da tausasawarsu, misalin jiki ne guda xaya. Idan wata gava ta yi rashin lafiya, sai sauran jikin ya taya ta rashin barci da jin zafi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma ku kasance –Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna", Muslim ya ruwaito.

Riqo da juna da haxuwar kai, da kyakkyawar alaqa da daidaito da taimakon juna, da jin-qan juna, da taimakon gaskiya, da watsar da savani ko rarrabar kai, garkuwa ne da al'umma ke fakewa a jikinsu, kuma mafaka ce da ta wadaci dukkan mutane, kuma dalilin aminci ne ga al'umma, kuma samun qarfi ne ga addini, kuma kariya ne na kiyaye amfanonin duniya, kuma samaki ga fitintinu masu vatarwa, kuma aminci da samun kariya daga makirce-makircen maqiya da cutarwarsu.

Kuma kamar yadda Allah Ta'alah ya yi umarnin a kiyaye alaqar al'umma da qarfinsu da jin-qan da ke tsakaninsu, To, haqiqa ya yi hani, kan yanke zumunci da baiwa juna baya, da savani, da rabuwar kai, da zaman kara zube, da buxe qofar sharri; Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance kamar waxanda suka rarrabu, kuma suka sava wa juna, bayan hujjoji sun zo musu, kuma waxannan suna da azaba mai girma", [Ali-imran: 105].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka da ku yi jayayya, har ku raunana, sai qarfinku ya tafi, kuma ku yi haquri, saboda Allah yana tare da masu haquri" [Anfal: 46].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma kada ku kasance daga mushirkai * wato, waxannan da suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance qungiya-qungiya, kowace qungiya da abinda ke wurinsu suna masu alfahari" [Rum: 31-32].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Musulmi xan'uwan musulmi ne, baya zaluntarsa, baya qin taimakonsa, baya yin qarya a gare shi, kuma baya raina shi, … kowane musulmi ga xa'uwansa musulmi, jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa haramun ne", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Musulmi xan'uwan musulmi ne, baya zaluntarsa, kuma baya qyale shi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abdullah ibn Umar (رضي الله عنهما).
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Musulmi xan'uwan musulmi ne, baya ha'intarsa, baya masa qarya, kuma baya qin taimakonsa", Tirmiziy ya ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Waxannan dalilai, hani ne da tsawatarwa kan tozartar da haqqoqin (masu haqqoqi), waxanda tozarta sun ke rarraba kawunan musulmai.

            Kuma yana daga WASIYYOTIN ANNABI MASU AMFANI, wanda ta qunshi umarni kan, haxe kai, da zamewa abu xaya, da tara hankali wuri guda, ta kuma yi hani kan, rarraba kai da savani, sai ta haxe lamarin addini da duniya = Faxinsa (صلى الله عليه وسلم) ga sahabbansa: "Ina muku wasici, da taqawar Allah, da jin umarnin shugabanni, da kuma biyayya, koda bawa ne ya ke mulkarku, saboda duk wanda ya yi tsawon rai daga cikinku, to zai ga savani dayawa, sai ku yi riqo da sunnata, da sunnar khalifofi shiryayyu, ku yi riqo da su, da fiqoqi. Kuma ina tsawatar da ku qirqirarrun lamura, domin kowace bidi'a vata ce", Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, kuma Tirmiziy ya ce:  hadisi ne hasan sahih. Daga hadisin Irbadh bn Sariyah (رضي الله عنه).

Kuma yana daga RAHAMAR ALLAH ga musulmai, yadda ya tsawatar da su, kan FITINTINU MASU GAMEWA, a inda Allah Mabuwayi da xaukaka ya ke cewa: "Kuma ku ji tsoron fitina, wanda bata samun waxanda suka yi zalunci a cikinku a keve, kuma ku sani lallai ne Allah, Mai tsananin uquba ne" [Anfal: 25].
Maluman tafsiri, suka ce: "Ku kiyayi sabubban kowace fitina mai cutarwa, wanda za su bijirar da ku, ga uqubar Allah Ta'alah".

            Kuma kamar yadda shari'a mai tsarki ta yi hani, kan fitina mai gamewar cutarwa, kuma ta tsawatar akansu; saboda abinda ke cikinsu na cutarwa, to lallai ta yi hani kan kevantacciyar fitina, wanda ta ke cutar da ma'abucinta, sai kuma ta cutar da mutane gaba xaya, saboda shari'a ta tsawatar kan vangarewar xaixaiku daga cikin jama'ar musulmai, domin an ruwaito daga Abu-zarrin (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya rabu da jama'a daidai da taqi xaya, to lallai ya sunce dabaibayin musulunci daga wuyarsa", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abdullah ibn Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Al'ummata ba za ta haxu akan vata ba, sai ku yi riqo da jama'a, saboda hannun Allah yana kan jama'a", Xabaraniy ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Mu'awuya (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya mutu, alhalin babu bai'a a wuyansa, to ya yi mutuwa irin ta jahiliyya", Xabaraniy ya ruwaito shi, a cikin mu'ujam Kabir.
Kuma an ruwaito daga Abu-zarrin (رضي الله عنه) lallai shi, ya yi inkari yin sallah a Mina raka'oi huxu, ga khalifa Usmanu (رضي الله عنه), sa'annan ya tashi ya yi raka'oi huxun tare da shi. Da aka yi masa maganar cewa ya aibanta yin raka'oi huxu ga amirul muminina, sai kuma ka aikata hakan. Sai ya ce: "Savani yana da tsanani, savani sharri ne", Ahmad ya ruwaito shi.

            Kuma yana daga abinda shari'a ta TSAWATAR AKANSA, FITINUWA DA DUNIYA, DA KUMA BARIN YIN AYYUKAN LAHIRA, KO MANCEWA DA ITA.
            Kuma lallai, samun rabo, wato cikakken rabo, yana nan ne, cikin yin aiki domin lahira, da kuma yin aiki don gyara duniya, da raya ta, da dukkan abu mai amfani, da fa'ida, wanda zai xaukaka addini, kuma zai biya buqatun musulmai, kuma ya bada kariya ga mutum musulmi daga qasqancin da ke cikin, xabi'ar roqo, har ya shumfuxa hannunsa da ciyarwa, ta qofofin alkhairi, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku mutane lallai alqawarin Allah gaskiya ne, don haka, kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma kada shexan maruxin nan ya ruxe ku, game da Allah", [Luqman: 33].
Kuma Allah ya ce: "Kuma wannan rayuwar ta duniya ba komai ba ce, face abar shagala da wasa, kuma lallai lahira, ita ce rayuwa, da sun kasance suna sani", [Ankabut: 64].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kowace rai mai xanxanar mutuwa ce, kuma kawai za a cika muku ladanku ne, a ranar qiyama, kuma wanda aka nisantar da shi daga barin wuta, kuma aka shigar da shi aljannah, to haqiqa ya yi babbar rabo, kuma rayuwar duniya bata kasance komai ba, face jin daxin ruxi", [Ali-imrana: 185].

            Saboda shi fiskantar duniya, ta hanyar tara kayan cikinta, ta halal da haram, uquba ne ga ma'abucinsa, da cutarwa da sharri ga xaukacin al'umma.
            Kuma tara duniya, ta hanyar ta'addanci ga haqqoqin wasu, da zaluntarsu cikin haqqoqinsu, da dukiyoyinsu, yana rarraba kan mutane, kuma yana kawo raunin alaqoqi da danganta.
            Shi kuma yin tseren tara duniya, tare da nuna kwaxayi da rowa, da husuma, yana yin jagora, zuwa ga haifar da qiyayyar zukata, da abaucewarsu, da nuna rashin sani ko sabo; An ruwaito daga  Uqbah bn Amir (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi salla, ga waxanda aka kashe a yaqin Uhud, sa'annan ya hau minbari, kamar mai yin bankwana ga rayayyu da matattu, a inda ya ce: "Lallai ne Ni mai jiranku, a tafkin alkausara ne, kuma lallai faxinsa kamar tsakanin garin Aila da Juhfa ne. Kuma lallai ne ni bana tsorace muku yin shirka a bayana, sai dai ina tsorace muku duniyar da za ku yi rigaggeniyar tara ta, har ku yi ta karkashe juna, sai ku halaka kamar yadda al'ummar da ke gabaninku ta halaka", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, kuma lafazin na Muslim ne. 
Kuma an ruwaito daga Abu-sa'id (رضي الله عنه), lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne duniya, tana da zaqi, kuma koriya ce, kuma lallai Allah zai baku mayewa a cikinta domin ya ga yadda za ku aikata, ku saurara! Ku kiyayi duniya, kuma ku kiyayi mata", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma DUNIYA, Ita ce, ta kange yawa-yawan mutane, daga addinin Allah Ta'alah, da qawan cikinta, da kayan daxinta dana sha'awowinta, da kayan cikinta, Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Kuma bone ya tabbata ga kafirai daga azaba mai tsanani * waxanda suka fi son rayuwar duniya fiye da lahira, kuma suna kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta karkace, waxancan na cikin vata mai nisa", [Ibrahim: 2-3].

            Farkon savanin da aka samu a cikin wannan al'ummar ita ce, vangarewar munafikai da ficewar khawarijawa ga shiryayyen shugaba; Usman (رضي الله عنه), Abinda ya janyo hakan kuma, son duniya ne, kamar yadda ya tabbata, kuma ya ke rubuce a tarihi, sun yi hakan, suna masu kwaxayin samun matsayi irin na duniya, sai dai basu sami komai ba face baqin ciki da wulaqanci, da haramta musu buqatunsu, da qiyayya, kuma sai suka halaka xaya bayan xaya, akan mummunan hali, A'uzu billahi. Allah Ta'alah ya ce: "Sai aka shamakance tsakaninsu da tsakanin abinda suke sha'awa, kamar yadda aka aikata da irin qungiyoyinsu a gabaninsu. Lallai sun kasance cikin shakka mai sanya kokonto" [Saba'i: 54].

            Kuma lallai a cikin wannan zamanin wanda annabta ya qara nisa, Duniya ta qare zamewa fitina ga mutane dayawa, saboda husumomi suna kasancewa ne domin duniya, qulla alaqoqi da 'yan'uwantaka suna yi ne domin samun amfanin duniyar, daidaito kuma suna samar da shi akan maslahohinta, qin juna da yanke zumunci da qauracewa juna suna yi ne akan duniya, baiwa mutane matsayi su kan alaqanta shi da saninsu ga duniya, sai Duniya ta zama babban sababin sassavawar ra'ayoyi, sai kuma soyayya don Allah, samunta ya yi qaranci, Abdullah ibn Abbas (رضي الله عنهما) ya ce:  "Haqiqa, yawa-yawan 'yan'uwantakar mutane a yau, ta kasance akan lamarin duniya, wannan kuma baya amfanar da ma'abutansa da komai", Ibnu-Jarir ya ruwaito shi.

            SAMUN KARIYA DAGA SHARRIN FITINAR DUNIYA, zai kasance ta hanyar Musulmi ya san, matsayin duniya a wurin Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, da irin matsayinta a wurin AnnabinSa (عليه الصلاة والسلام), domin an ruwaito daga Sahl bn Sa'ad (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Da duniya ta kai daidai da fiffiken sauro a wurin Allah, to da bai shayar da kafiri abinda ke cikinta, ko daidai da kurvin ruwa xaya ba", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.

            Da kuma tuna halin sahabbai (masu zaman masallaci) ma'abuta suffa, daga cikin wanda suka yi hijira, da yadda suka qaurace wa duniya, domin Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: "haqiqa na ga mutane saba'in daga cikin mutanen suffar masallaci, babu wani da ke da mayafi, sai dai kwarjalle ko rigar da suka xaura ta ga wuyoyinsu, daga cikinsu akwai wanda ke kaiwa izuwa rabin kwabrinsa, daga cikinsu kuma akwai wanda ke kaiwa ga idanun sawu biyu, sai ya tattara tufan da hannunsa, tosron kada a ga al'aurarsa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abu-sa'id (رضي الله عنه) ya ce: "Na zauna a cikin wata jama'a daga raunanan waxanda suka yo hijira (wato, muhajirai), kuma lallai sashensu yana vuya a bayan sashe, saboda tsoron bayyanar tsiraici, sai Annabi S.A.W ya zo ya tsaya akanmu, sa'annan ya ce: Albishirinku –ya ku talakawan masu hijira- da samun cikakken haske a ranar qiyama, domin za ku shiga Aljannah gabanin mawadatan mutane, da tsawon rabin yini, wannan kuma daidai da shekaru xari biyar kenan", Tirmiziy ya ruwaito shi, da Abu-dawud, kuma wannan lafazin nasa ne.

            Kuma, Ku –ya ku taron musulmai- an shumfuxa muku arziqin duniya ne, da jihadin da waxancan muhajiran suka yi, sai ku yi godiya wa Allah akan hakan, kuma ku bauta masa, kada ku sava masa.

            Saboda gujewa duniya (zuhudu) yana daga sabbuban samun kariya daga husumomi da jayayya, Annabi (صلى الله عليه وسلم ) ya ce: "Ka guje wa duniya sai Allah ya so ka, kuma ka guje wa abinda ke hannun mutane, sai mutane su so ka", Ibnu-Majah ya ruwaito shi daga hadisin Sahal bn Sa'ad As-Sa'idiy (رضي الله عنه).
Nawawiy ya ce, hadisi ne hasan.
            Kuma zuhudu shi ne qauracewa haramun da barin haramun, da wadatuwa da abinda Allah ya baka. Da yin aiki domin lahira, da rashin karkata zuwa ga duniya, da rashin samun natsuwa da ita duniya, kuma ka hana ranka tava abinda ke hannun mutane, kuma kada ka yi hassada ga wani, akan abinda Allah ya bashi.

            Ya ku musulmai …
Lallai yana daga cikin SABUBBAN KARE AL'UMMA DA KIYAYE SU, KUMA SU ZAMA ABU XAYA, SU YI QARFI, SU TABBATU A GABAN GUGUWAR FITINTINU, HAR SU IYA TUNKUXE MAKIDAR MAQIYA, DA VARNAR KOWANE MA'ABUCIN SHARRI,  YIN DAWWAMAMMEN NASIHA GA MAJINTA LAMARI (SHUGABANNI), DA IRIN SALON NASIHAR MAGABATAN KWARAI,Domin ma'anar faxin Allah koyaushe ya tabbatu: "Kuma ku taimaki juna akan aikin kwarai da taqawa" [Ma'ida: 2].
Kuma Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) ya ce: "Lallai ne Allah ya yarda da abu uku a gare ku, ya yarda ku bauta wa Allah kada ku haxa shi da kowa, kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada ku rarraba, kuma ku riqa nasiha ga wanda Allah ya jivintar masa da lamarinku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
            Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda suka yi imani ku yi xa'a ga Allah, kuma ku yi xa'a ga ManzonSa, da ma'abuta al'amari daga cikinku. Idan ku ka yi jiyayya a cikin wani lamari, to ku mayar da shi ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kun yi Imani da Allah da ranar lahira, wannan shine mafi alheri, kuma mafi kyau ga makoma" [Nisa'i: 59].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai hikima, Mai haquri Mai jin-qai, Ina yin yabo ga Ubangijna, kuma ina gode masa, akam ni'imominSa, waxanda waninsa ba zai iya qididdige su ba,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Maxaukaki Maigirma,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, wanda Allah ya shiryar da halittunsa da shi, zuwa ga hanya madaidaiciya,

Ya Allah ka qara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa, masu bin tafarkinsa miqaqqe.

Bayan haka … !!
Ku yi tsoron Allah, a sirrace da kuma a bayyane, saboda taqawar Allah ita ke kiyaye ni'imomin da suke nan, kuma take qaro ni'imomi masu zuwa wanda basu nan, Allah Ta'alah ya ce:  "Yak u waxanda suka yi imani ku bi Allah da taqawa, kuma ku faxi Magana madaidaiciya * Zai kyautata muku ayyukanku, ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da ManzonSa, to lallai ya rabauta da babban rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

Ya ku Musulmai … !!
Lallai yana daga ABINDA MUSULUNCI YA TSAWATAR AKANSA, KURAKURAN HARSHE DA AYYUKANSA MASU HALAKARWA, saboda maganar baka, da rubutun alqalami, suna iya raba kan mutane, su wargaza dunqulalle, har su kawo mummunan savani a tsakanin fiskoki, da samar da mabanbantan ra'ayoyi, su vatar da mutane daga bin gaskiya, tare da faxaxa girman da'irar savani, Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) ya ce:  "Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to ya faxi alheri ko ya yi shiru", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).

Kuma a lokacin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar kan fitintinu, sai bayyana mana, ba sau xaya ba, ba sau biyu ba, cewa: lallai faxin varna a lokacin fitina, halaka ne, a inda ya ce: "Harshe a cikin fitina yafi suka fiye da tsananin sukar takobi", Tirmiziy ya ruwaito shi da Abu-dawuda daga hadisin Abdullah ibn Amrin (رضي الله عنهما). Kuma ya sake cewa: "Kuma varnar harshe a lokacin fitina kamar suka ne da takobi", Abu-dawud ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Ya faxi hakan, domin jin-qan wannan al'ummar, kuma domin ya kashe wutar fitina.

Ya ku bayin Allah,
Ku nemi, dawwamar ni'imar aminci da kwanciyar hankali da zaman lafiya, da wadaci a cikin rayuwa, ta hanyar, kusantar Majivincinmu Allah, da ibadodi, da nisantar laifuka na haramun, Allah Ta'alah ya ce: "Sai su yi bauta ga Ubangijin wannan xakin * wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].

Ya ku Musulmai… !!!
            "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
 ……………………………

,,,          ,,,          ,,,

2017/09/15

خطبة بديلة 3 للدكتور صلاح البدير عن النعم











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24/ZULHIJJAH/1438H
daidai da 15/SATUMBA/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
       Ya ku musulmai …
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda rahamarSa ta game dukkan komai, kuma ta yalwace su, kuma ni'imarSa ta cika wa bayi ta kuma girmama,
Muna yin yabo a gare shi aka ni'imominSa da suka jeru akanmu, kuma suka yalwatu,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya; shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya; shaidawar da take tseratar da wanda ya furta ta, a ranar da kowace mai shayarwa zata shagala daga abinda take shayar da shi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammdu bawanSa ne manzonSa, Wanda ya yi jihadi iyakar jihadi domin Allah, har Kalmar tauhidi ta samu xaukaka
Allah ka yi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, a duk lokacin da mahajjata suka qanqan da kai a wuraren bauta masu girma, ko suka yi addu'a.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah, saboda taqawarSa itace hajar da tafi riba, kuma ku kiyayi savon Allah; domin bawan da ya yi sakaci kan lamarin Allah, ko ya tozarta umarninsa to haqiqa zai tave, "Yak u waxanda suka yi Imani ku yi taqawar Allah, kuma ku faxi magana madaidaiciya * Sai ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi xa'a ga Allah da ManzonSa to lallai zai rabauta da babban rabo mai girma", [Ahzab: 70-71].

Ya ku Musulmai
Yin bautar Allah shine muqamin da yafi xaukaka, kuma darajar da tafi zama qololuwa.
Kuma a cikin kwanaki qalilan da suka shuxe ne, Mahajjata suka kammala ibadar da tana cikin manya-manyan ibadodi, da xa'ar kusantar Ubangiji wanda take daga jerin manyan xa'oi, wanda a cikinta suka tove xinkakkun tufofinsu daga miqatai, kuma hawayen tuba ya bayyana akan kumatu a filin Arfah, kuma sautukan bayyanar da buqata zuwa ga Allah suka xaukaku
To, lalen yin hajji ga mahajjata!
Kuma lalen yin bauta ga masu bauta, kuma lalen qoqarin da suka nuna!!

Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ku yi godiya ga Allah akan abinda ya baku, kuma ku yaba masa akan abinda ya muku baiwa, saboda yadda ya jera kyautarsa a gare ku, ya kuma sadar da muku da alkhairinsa, ya game ku da kyautukansa, ya cika muku falalolinsa ya kuma kammala muku su, domin "Babu wata ni'imar da ke tare da ku face daga Allah ne", [Nahl: 53].
"Kuma idan kuka so qidaya ni'imar Allah, baza ku qididdige su ba, Lallai ne Allah Mai gafara ne Mai jin qai", [Nahl: 18].
Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ku yi zaton kyawawa daga Ubangijinku, kuma ku yi fatan alkhairi mai yawa daga gare shi, kuna masu qarfafa fatan Allahn ya karva muku hajjinku, ya kuma kankare muku abinda ya shuxe na zunubanku, domin y azo a cikin hadisin qudusiy: "Allah Ta'alah ya ce: Ni ina wurin da bawana ya ke zatona", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Ya ku Musulmai
Ya waxanda suka hajjin xaki mai girma,
Kuka fito daga kowani longu mai zurfi,
Kuka xauko talbiyya daga kowani vangare mai nisa,
To, ga kun nan, bayan hajjinku ya cika; ya kammalu,
Bayan kun yi tsayuwa a waxancan wuraren bauta,
Kun sauke waxancan ayyukan ibadodi,
Ga kun, nan kuna ta shirin kokkomawa gidajenku,
Sai ku kiyayi komawa cikin zunubai da kuma cakuxa da ayyukan haramun, da kutsawa cikin aibobi, da shumfuxa cikin ababen zagi,  "Kuma kada ku kasance kamar wanda ta warware zarenta bayan tukka", [Nahl: 92].
Wata mace, mai wauta, mai qarancin hankali, wanda take wahala safiya da maraice wajen sassaqa gashin dabbobi, har zuwa lokacin da ya zama zare lafiyayye mai karfi, sai ta dawo tana warware gashinsa, tana kukkunce shi, har ta mayar da shi bayan qarfinsa warwarerre, kuma sincacce, kuma bata tsinki komai ba daga aikinta wahalar da kai da vata lokaci,
To kada ku kasance kamar wannan mata, har ku rushe abinda kuka gina, ko watse abinda kuka tattara, ko ku since abinda kuka kyautata tufkansa.

Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Haqiqa kun buxe wani shafi mai haske mai tsafta a cikin rayuwarku, kuka bayan hajjinku kun sanya tufafi masu tsarki,
Don haka, wallahi ku kiyaye komawa cikin ayyukan wulaqanci, da bin hanyoyi masu vatarwa, ko ayyuka masu aibi,
Saboda tsananin  kyan aikata aikin kwarai bayan aiki mai kyau, da kuma munin aikata mummuna a bayan mai kyau.

Ya ku Musulmai
Lallai hajji mabaruri yana da alama, kuma dangane da karvuwarsa akwai alamar haske, saboda an tambayi Alhasan Albasariy –رحمه الله تعالى- cewa Menene hajji mabaruri? Sai ya ce, Ka koma kana mai qauracewa duniya, kana mai kwaxayin lahira.
Hajjinku ya kasance shamaki ne daga aukawa wuraren halaka, kuma mai hani daga ababen zamiya masu vata aiki, kuma ya kasance mai zaburar da ku kan qara alkhairori da aikata ayyukan kwarai.
Kuma ku sani, Lallai mumini babu wani lokacin da zai gama aikata ayyukan kwarai, sai lokacin zuwan ajali.

Ya ku Musulmai
Abu ne mai matuqar kyau, mahajjaci bayan hajjinsa ya koma ga iyalansa da qasarsa da xabi'a mafi kamala, da hankalin da yafi cika, da natsuwar da tafi cika, da kuma mutuncin da ake matuqar kiyaye shi, da xabi'u yardaddu, da halayya masu karamci.
Me yafi, ace mahajjaci ya koma da kyakkyawar mu'amala ga abokan zamansa, mai karamcin mu'amala ga 'ya'yansa, yana mai tsarkakakken zuciya, yana bin salo irin na gaskiya da adalci da aikata daidai, abinda ke cikinsa ya kasance yafi alheri akan abinda ke waje, wanda ya vuya kuma ya kasance yafi abinda ya bayyana.
Kuma lallai wanda ya koma bayan hajjinsa yana xauke da waxannan sifofin masu kyau, shine wanda a haqiqanin lamari ya amfana da hajjinsa, da kuma hikimominsa da darussansa da fa'idodinsa.

Ya ku Musulmai
Lallai mahajjaci tun daga lokacin talbiyyarsa, har y agama hajjinsa ya qare; to lallai dukkan ayyukansa na hajji suna sanar da shi Allah, suna kuma tunatar da shi kan haqqoqinsa, da abinda ya kevanta da sun a cancantar bauta ko uluhiyya,  da kasancewar babu wanda ya cancanci ayi masa bauta idan ba Allah ba.

Ya Mahajjatan xakin Allah mai alfarma
Ya waxanda kuka hanu daga ababen da haramarku ta tsawatar akan tava su, a lokacin yin hajjin xakin Allah, lallai akwai abubuwan da aka yi hani akansu a tsawon zamani da shekaru da rayuwa, sai ku kiyaye tava su, ko kusantarsu, Allah Mabuwayi cikin xaukakarsa yana cewa:  "Waxancan iyakoki ne na Allah kada ku qetare su, kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah, to waxannan sune azzalumai", [Baqara: ].

Ya ku Musulmai
Wanda ya amsa wa Allah, a lokacin hajji, yana mai amsa kiransa, ta yaya a bayan haka zai amsa ga wani lamarin da ya sava wa Qur'ani da Sunnah, da kuma shari'a.
Wanda ya amsa wa Allah a lokacin hajji, to ya amsa masa a kowani wuri da zamani, ta hanyar amsa umarninsa, a duk inda abin hawansa ya fiskanta.

Ya kai bawan Allah
Ya wanda lokutan xa'oi da rahamomi suka shuxe masa, alhalin ya dulmuya cikin wargi da laifuka ababen qi, Shin baka ga tawagar mahajjata da masu umrah da masu bauta ba ne?
Shin baka ga yadda masu harama suka tuve tufafi ba ne, da xaga hannayen masu kwaxayin rahama, da hawayen masu tuba ba ne?
Shin baka jin sautin masu talbiyya da kabbarori da hailala ba ne?
To me ya same ka, har mafi alkhairin kwanakin duniya suka shuxe maka, alhalin kana cikin son zuciyarka da ta tamke maka xauri?

Ya wanda ke kai-komo cikin savo safe da yamma
Yana cewa, ai zan tuba, yau ko gobe

Ya wanda ya wayi gari cikin son zuciya, a watse
Ya kuma yi yammaci a cikin jahilci, a daskare
Ya kuma kasance cikin sha'awowinsa cikin dabaibayi a xaure
Ka tuna daren da za kwana a cikin qabari kai xaya!,
Sai ka yi gaggawan tuba, tunda kana cikin lokacin haka
Ka kuma risko abinda ya wuce, gabanin lokacin da ba a gyaran tuntuve,
Ka kuma tsaya daga aikata zunubai da laifuka,
Kuma "Lallai ne Allah yana shumfuxa hannunsa da rana, domin wanda ya munana aiki cikin dare ya tuba, kuma yana shumfuxa hannunsa da dare, domin wanda ya munana da rana ya tuba, har rana ta fudo daga mafaxarta. Kuma wanda ya tuba daga zunubi, kamar wanda bashi da zunubi ne".

Allah ya mini albarka Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma, Kuma ya namfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsu na ayoyi, da hikima.
Ina faxar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, ga Ni da Ku da Sauran musulmai, daga kowani zunubi da laifi, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, wanda yana bada mafaka ga wanda ya nemi mafaka daga tausasawarSa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammdu bawansa ne manzonsa, wanda ya bi shi to ya kasance akan alkhairi da shiriya, kuma ya sava masa ya kasanci cikin vata da halaka.
Allah ya yi qarin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, da sallama mai yawa.

Bayan haka
Ya ku musulmai
Ku ji tsoron Allah, kuma ku kiyaye shi, kuma ku masa xa'a kada ku sava masa, "Ya ku waxanda suka Imani ku bi dokokin Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya", [Tauba].

Ya ku musulmai!!!
Lallai a duniya, abincin mutuwa ne, kuma qasar bala'oi,
Kuma kune kuka maye waxanda suka gabata, kuma da sannu kuma za ku kasance magabatan masu mayewa,

Sai ku ribaci zamaninku, kuma ku yaqi kawunanku, saboda yin aiki hajar masu bauta ne, kuma shine jarin masu gujewa duniya, kuma akansu gyaruwar rayuka a rataya, sai ku aikata daidaita, kuma ku kwatanta, kuma ku yi aiki safe da yamma, da wani loto na duhun dare, kuma ku yi aiki da tsakaita, domin ku isa ga tsira. Kuma ku rigayi fitintinu ta hanyar aikata ayyukan kwarai, kuma ku nisanci fitinoni masu vatarwa, masu ruxarwa. Saboda an ruwaito daga Abu-hurairah –رضي الله عنه- lallai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku rigayi wasu fitintinu masu kama da yankin dare mai duhu, ta hanyar aikata ayyuka na kwarai, wanda mutum zai wayi gari yana mumini, amma ya yi yammaci yana kafiri, ko yayi yammaci yan mumini, amma sai ya wayi gari yana kafiri, yana sayar da addininsa da wani abu na duniya", [Muslim ya ruwaito shi.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...