2015/08/31

LITTAFIN TAJRIDUT TAUHID ALMUFID NA ALMAKRIYZIY










TACE TAUHIDI MAI AMFANI
(تَجريدُ التوحيد الْمُفيدِ)



Na babban Malami/
Ahmad bn Aliyu Almakariiziy Alhanafiy






Fassarar mai neman afuwar Ubangijinsa/
Abubakar Hamza Zakaria
(abusafiyya01@yahoo.co.uk)






Mukaddima
  Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu, Yabo da shira su kara tabbata ga fiyeyyen Annabawa da Manzanni; Annabinmu Muhammadu, da Iyalensa da Sahabbansa gaba daya … Bayan haka;
  Saboda tauhidin Allah mabuwayi da daukaka da kadaita cikin bauta a ka halicci dukkan halitta, kuma don tabbatar da shi (kadaita Allan) aka shar' anta dukkan bauta (sallah, azumi, addu'a,da sauransu); don haka: Shi tauhidi shi ne manufa mafi girma, kuma shi ne target mafi daukaka (da aka so kar mutum ya nufa da duk wani motsinsa da bautarsa sai shi), kuma abun nufa madaukaki mai girma, Allah madaukaki ya ce:
 ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ  [الذاريات: ٥٦].
(Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su kadaita ni da bauta).
Kuma hakika (ayoyin) Alqur'ani da sunnar (Manzon Allah s a w) sun zo kan cewa duk wadda ya TABBATAR DA TAUHIDI YA SHIGA ALJANNA BA TARE DA HISABI, KUMA BA TARE DA AZABA BA; SHI YASA MALUMA –ALLAH YA MUSU RAHAMA- SU KA YI TA KOKARIN SU BAYYANA WANNAN AL'AMARI MAI MUHIMMANCI KUMA SU KUSANTO DA SHI, DA BAYANINSA, A CIKIN WALLAFE WALLAFE DA LITTATAFA MASU YAWA; DAGA CIKINSU AKWAI WANNAN:
تَجريدُ التوحيد الْمفيد،
(TACE TAUHIDI MAI AMFANI),
''Littafi mai babban matsayi, Na Imam, mai yawan sani, Takiyyudden, Almakariiziy, Alhanafiy,  -Allah ya masa rahama-.
  Shi kuma TACE TAUHIDI (TAJRIDUT TAUHID) na nufin:
Tabbatar da shi,
da tace shi,
da kuma karkade masa kurar shirka mai girma da shirka karama,
da bidi'o'in kuduri, da bidi'o'in aiyuka,
da kuma barin sabo;
Hakan kuma zai kasance ne ta hanyar; Cikar Ikhlasi wa Allah a cikin zantuttuka, da aiyuka da niyyoyi, da kuma kubutuwa daga babban shirka da ke warware  tushen tauhidi (musulunci), da kuma kubuta daga karamar shirka da ke kore cikarsa (tauhidi), da kuma kubuta daga bidi'o'I da su ke kawo gibi ga tauhidi, da kuma sabo da ke tauye tauhidi, kuma ke hana cikarsa, sa'an nan ya ke katange shi daga samun tasirorinsa.

Muna fatan Allah ya amfanar (da bayinsa) da wannan littafin, sa'an nan ya girmama lada da sakayya ga mawallafinsa, da wadda ya yada shi, da kuma mai karanta shi.

Allah kuma ya yi dadin tsira ga shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu, da kuma Iyalensa da sahabbansa gaba daya.

(Gabatarwan) Mai yadawa.


**********
TARIHIN MAI LITTAFIN –Allah ya yi masa rahama-
  Shi ne takiyyuddeen Ahmad bn Aliyu bn Abdilkadir bn Muhammad bn Ibrahim bn Muhammad, bn Tamim, bn Abdissamad, bn Tamim Almakriiziy, Babban malami Ibnu Hajar –Allah ya masa rahama- ya masa alkunya da: Abu Muhammad, Yayin da Imam Sakhawiy ya masa alkunya da: Baban Abbas.
Shi kuma ''almakriiziy'' dangantawa ne zuwa ga unguwar ''makarizat'' a Ba'ala –bakka; wadda kakansa na sama Ibrahim ya taba sauka a wajen, Sai kuma ya shahara da haka.  
***********
 An haifi mai wannan littafi ne a ''Alkahirah'' (babban birnin Misra) a shekara ta dari bakwai da sittin da shida (766na hijira), a Unguwan da ake kiranta: ''Burjuwan''  a da, Unguwan a yanzu (wannan zamanin) na bin yankin ''jamaliyya'' wajen kal'ar (dutsen) Muhammadu bn Aliyu .

***********
  Ya tashi a cikin iyalai (haula) masu addini; sai ya hardace alqur'ani tun yana karaminsa, da kuma kananan littatafa na fiqhun (Mazhabar) Hanafiyya.
Amma babansa kuma to an haife shi a Damaskas (damashk), ya kuma yi karatun (sauraron) hadisi a can, sa'an nan ya yi kaura zuwa ga ''Alkahirah'', ya yi wassu aiyuka da su ke da alaka da alkalanci.
***********
  Mai littafi ya yi wassu aiyuka da su ked a muhimmanci, yayi wakilcin hukunci, ya zama shi ne mai sa hannu (signature), ya yi aikin hisba, da huduba a masallacin juma'a na Umar, ya kuma yi limancin (salloli biyar) a massalacin shugaba, sa'an nan ya karantar da hadisi a ''mu'ayyidiyyah'' a madadin ALMUHIB BN NASRULLAHI, Ya kuma tsayu wajen yin wadannan aiyukan mafi alkhairin tsayuwa; aka kuma yaba wa salonsa da tsarinas. Duk wadannan abubuwan sun kasance a Misra ne. Yayin da kuma yak aura zuwa damaskas, Sakhawiy ya ce –dangane da shi: ''Haka nan kuma ya shiga Damaskas sau da dama, kuma ya jagoranci kula da wakafin kalaniysiy, da Baimaristan Annuriy, da kuma karantarwa a makarantar ''darul hadith al'ashrafiyyah'' da '' makarantar ikbaliyya'', kuma an bijiro masa Shaf'iyya a shaam (seria)  amma sai ya ki,
Sa'an nan sai marubucin –Allah ya masa rahama- ya kaurace wa duk wadannan aiyukan; Sakhawiy yana cewa: ''Sa'an nan sai ya kaurace wa hakan, ya kuma zauna ya lazimci garinsa ya shagalta da tarihi har ambatonsa ya shahara da shi, kuma sautinsa ya yi nisa a cikinsa, kuma ya zama yana da wallafe wallafe a cikinsa''.
***********
Marubucin –Allah ya masa rahama- ya yi farkon rayuwarsa ne; a farkon neman iliminsa tun yana yaro kan hardatan alqur'ani da kuma wassu kananan littatafan fiqhun Hanafiyya; sai ya tashi akan mazhabar Abu hanifata
***********
  Yana da littatafa da yawa; wadda su ka fi muhimmanci daga cikinsu su ne:

١.  المواعظ والاعتبار بذكر الخطط والآثار
Shi ne wadda ya fi shahara da:
الخطط للمقريزي.
٢.  إمتاع الأسماع بما للرسول r من الأبناء والأموال والحفدة والمتاع.
٣.  الخبر عن البشر.
٤.  درر العقود الفريدة في تراجم الأعيان المفيدة.
٥.  الذهب المسبوك في ذكر من حج من الخلفاء والملوك.
٦. السلوك في معرفة دول الملوك.
Da kuma wassunsu na littatafansa.

***********
Ya rasu –Allah ya masa rahama- a watan ramadana na shekarar 845 na hijira, bayan ya doshi shekara tamanin, bayan tsawon rai (rayuwa) da ke cike da ilimi, karantarwa, da wallafe wallafe.


  Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu, kyakkyawar makoma ta tabbata ga masu tsoron Allah, kuma salatin Allah ya kara tabbata ga annabinmu Muhammadu; cika makon annabawa, da iyalensa da sahabbansa gaba daya.
Bayan haka:
  Wannan littafi ne mai fa'ida da yawa, mai kuma yaukakan dayaituttun fa'idoji a babinsu, wadda duk wadda ya nufi Allah da gidan lahira zai amfana da shi' Na sanya masa take:
LITTAFIN TACE TAUHIDI; MAI AMFANI
Allah kawai na ke rokon –da baiwansa- taimako kan aiki da shi.

  Ka sani Lallai Allah madaukaki shine ubangijin komai, mamallakinsa, kuma abun bautarsa; Shi kuwa ''RABBU'' tushen kalma ne na: Ya rena, yana reno, reno; kuma ma'anar fadin (Allah) madaukakin sarki: ''RABBUL AALAMINA'' shi ne mai renon (mai kula da) dukkan halittu, Kuma shi rabbu (s w t) shi ne mahalicci da ya samar da bayinsa, kuma shi ya tsayu da tarbiyyarsu (wajen kula da su) da kuma gyara su, wadda ke gyara su cikin halittansu, arzikinsu, lafiyansu, dama gyara addininsu da duniyarsu.

Shi kuma ''ILAHIYYA –Bautantaka-'' shi ne kasancewar bayi suna rikan (Allah) madaukaki abun so, abun bauta, kuma suna 'dayanta shi wajen so da tsoro, kauna da kan-kan-da-kai, tuba, bakance, da'a (biyayya), nema da tawakkali, da makamantan wadannan abubuwa.

Shi kuma TAUHIDI; HAKIKANINSA: Shi ne Mutum ya rika ganin al'amura dukkansu daga Allah ne madaukaki; ganin da zai yanke waiwaye zuwa ga sabbuba da tafinta (saboda sababi ba shi ya ke samar da abu ba, haka tafinta); don haka ba za ka ga alkhairi da sharri ba face tushensa daga Allah ne madaukaki.
Shi kuwa (imani) da wannan matsayi na haifar da; TAWAKKALI (saboda duk wadda ya san dukkan abubuwa daga Allah ne; don me zai dogara ga waninsa!), BARIN KOKA HALITTA (idan da mutum zai rasa wani abu… don me zai koka wani halitta irinsa  ya ce: Shi ya hana shi?), DA KUMA BARIN ZARGINSU, DA KUMA YARDA DA ALLAH, DA SALLAMA WA (MIKA WUYA) WA ABIN DA YA HUKUNTA.
Idan ka san wannan; to ka sani lallai RUBUBIYYA ya kasance daga Allah ne madaukaki zuwa ga bayinsa. Shi kuma ULUHIYYA (Bautantaka) ya kan kasance ne daga bayinsa zuwa gare shi, Ita kuma RAHAMA (Tausayi) itace ta hada tsakaninsu da tsakaninsa mabuwayi da daukaka.

Kuma ka sani lallai mafi tsadan ayyuka, wadda kuma ya fi su girman matsayi: shi ne KADAITA ALLAH MADAUKAKI (Tauhidi).
Sai dai kuma shi TAUHIDI yana da wassu abubuwa guda biyu da suke bayyana shi:
NA DAYA: Shi ne ka ce: LA'ILAHA ILLAL LAHU (ba wadda ya cancanci bauta sai Allah) da harshenka; Wannan maganan ana kiransa TAUHIDI; saboda yana karo da ukuntaka da nasara (crister) suka kudurce shi (yana kuma warware shi).
Sai kuma shi wannan tauhidin yana iya samuwa daga MUNAFUKIN da sirrinsa ya saba da abin day a bayyana.

ABU NA BIYU: Kada zuciya ya saba da abin da harshen ya fada, kuma kar ya musanta abin da ake fahimta na ma'anar abin da aka furta (na waccar kalmar). Abin da ya wajaba shi ne: Zuciya ya kunshi kudurce hakan, ya kuma gaskata shi; Wannan shi ne tauhidin gamagarin mutane.
Amma MADARAR TAUHIDI kuma shi ne: Ya ga al'amura gaba dayansu daga Allah ne madaukaki; sa'an nan ya yanke waiwaye ga barin tsanuka, ya kuma bauta wa Allah madaukaki bautar da zai kadaita shi da ita, ba zai kuma bauta wa waninsa ba.
Abin da ke fitar da Mutum kuma daga wannan tauhidin shi ne; Bin son zuciya; domin duk wadda ya bi son zuciyarsa to ya riki abin da zuciyar nasa yak e so a matsayin abun bautarsa; Allah madaukaki yana cewa:
ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ    ﭕ ﭪ  [الجاثية: ٢٣]
Ma'ana: " Shin baka ga wadda ya riki son zuciyarsa a matsayin abun bautarsa ba! … ".
Idan –kuma- ka lura za ka ga wadda ya bauta wa gunki a hakikanin gaskiya bai bauta masa ba; abun sani kawai shi ne ya bauta wa son zuciyarsa; wadda shi ne karkatuwan zuciyarsa ya zuwa ga addinin iyayensa, sai kuma ya bi wannan karkatar. Shi kuwa karkatan zuciya ya zuwa ga abubuwan da aka saba da su daya ne daga cikin abubuwan da ake kiransu SON ZUCIYA.
Abin da ke fitarwa daga wannan tauhidin shi ne: YIN FUSHI DA HALITTU, DA KUMA WAIWAYAWA ZUWA GARE SU; domin duk wadda ya ke ganin cewa komai daga Allah ne to ta yaya zai yi fushi wa waninsa (wai don –misali- ya rasa wani arziki), Ko kuma ta yaya zai kaunaci waninsa (wata ni'ima; saboda duka daga Allah ne; don haka sai a nema daga gare shi). Wannan matsayi a cikin tauhidi shi ne matsayin SIDDIKAN BAYI.

Kuma ba shakka lallai tauhidin RUBUBIYYA Mushirkai ba su musanta shi ba, hasali ma sun tabbatar da cewa (Allah) madaukaki shi kadai shi ne MAHALICCINSU, KUMA MAHALICCIN SAMMAI DA KASSAI, WADDA KE TSAYE KAN DUKKAN ABUBUWAN DA ZA SU GYARA HALITTUNSA GABA DAYANSU, Abin sani kawai shi ne su Mushirkai sun yi inkarin TAUHIDIN ULUHIYYA NE (tauhidin bauta) da soyayya, kamar yadda Allah ya hakaito akansu a cikin fadinsa:
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ     ﮇﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮞ  [البقرة: ١٦٥  ].
Ma'ana: '' Akwai daga cikin mutane wadda ya ke rikon wanin Allah a matsayin kishiyoyi; yana sonsu kamar yadda ya ke son Allah. Wadanda su ka yi imani sun fi tsananin so ga Allah ''.
Yayin da (wadannan) suka daidaita waninsa da shi a cikin wannan tauhidin; sai su ka zama mushirkai (masu hada Allah da wani) kamar yadda Allah ya ce:

ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ        ﭙﭚ ﭛ ﭜ ﭝ     ﭞ ﭟ ﭠ  [الأنعام: ١].
 Ma'ana: '' Yabo da godiya sun tabbata ga Allah day a halicci sammai da kassai, kuma ya halicci duffai da haske, sa'an nan wadanda su ka kafirta sun kasance: Ubangijinsu su ke daidatawa ( da wani). Madaukaki ya kara cewa:
ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ  [الأنعام: ١٥٠].  
Ma'ana: " ( Su kafirai) sun kasance dangane da ubangijinsu suna daidaita shi (da waninsa).
Kuma lallai Allah madaukaki ya ilmantar da bayinsa yadda za su rabu da shirka a cikin tauhidin ULUHIYYA, kuma Allah madaukaki shi ne ya cancanci kadaita shi a matsayin abun so, mai hukunci, kuma ubangiji; allah ta'ala yana cewa:
ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﯙ  [الأنعام: ١٤].
Ma'ana: " Ka ce: Yanzu wanin Allah zan rika masoyi!; wadda ya kagi halittan sammai da kassai ". Ya kuma ce:
ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮩ  [الأنعام: ١١٤].
Ma'ana: " Shin wanin Allah zan nema (zan rika) a matsayin mai hukunci? ". Ya kuma ce:
ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫﰇ  [الأنعام: ١٦٤].
Ma'ana: " Ka ce: Shin wanin Allah ne zan nema (zan rika) a matsayin ubangiji? ".
Don haka babu wani masoyi (waliyyi), babu kuma mai hukunci, sa'an nan babu ubangiji sai Allah; Wadda duk wadda ya daidaita waninsa da shi to ya yi shirka cikin tauhidin ULUHIYYAH, koda kuwa ya kadaita RUBUBIYYARSA. Shi tauhidin RUBUBIYYA shi ne wadda dukkan halittu su ka hadu akansa; Mumininsu da kafirinsu. Yayin da shi kuma TAUHIDIN ULUHIYYA shi ne: mararrabar hanyar muminai da mushirkai; don haka ne ma KALMAR MUSULUNCI ''La'ilaha illal lahu'' (ma'ana: ba wadda ya cancanci a bauta masa sai Allah). Kuma da mutum zai ce Babu mahalicci, ba mamallaki, ko ba mai juya al'amura Sai Allah; To da bai isar masa (ya shiga musulunci da shi) ba, A wajen maluma ma'abuta tahkiki (masu zurfi cikin ilimi tare da tacewa). Shi TAUHIDIN ULUHIYYA shi ne abun nema daga dukkan bayi, don haka ne ma asalin kalmar
     الله   
shi ne:   
الإلـه   
kamar yadda hakan shi ne fadin Babban Malamin harshen larabci SIBAWAIHI, Kuma shi ne magana mai inganci, kuma shi ne fadin mafi yawan Maluma daga sahabbansa, sai dai wanda ya yi shuzuzi (wato ya zo da sabani maganan maluma).
Kuma da wannan ma'anar dam u ka tabbatar da ma'anar ''AL ILAHU'' cewa shi ne (abun bauta) kuma abun so; saboda haduwar sifofin kamala (cika da bunkasa) a tattare da shi YA ZAMA LAFAZIN ''ALLAH'' shi ne sunan day a kunshe duk ma'anonin sunayen Allah mafiya kyan sunaye, da kuma sifofi madaukaka; kuma wannan shi ne abin da mushirkai ke inkarinsa (musanta shi).
Shi kuma ubangiji ya kasance yana kafa musu hujja da kadaita shi da su ke yi cikin rububiyyarsa (aiyukansa) kan su kadaita shi cikin uluhiyyarsa (wato aiyukansu da su ke yin a bauta); kamar yadda Allah madaukaki ya ce:
ﭳ ﭴ   ﭵ ﭶ   ﭷ ﭸ ﭹ ﭺﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ     ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔﮕ ﮖ ﮗ ﮘﮙ ﮚ ﮛ ﮜ    ﮝ ﮞ  [النمل:59-٦٠].
Ma'ana: " Ka ce: godiya ta tabbata ga Allah (wato: Alhamdu lillahi), kuma aminci ya tabbata ga bayinsa day a zaba. Shin Allah shi ne ya fi alkhairi akan abin da su ke tara shi da su! (Amsa lallai Allah shi ya fi!) *** Ko kuma wanene ya halicci sammai da kassai, ya kuma saukar muku dad a ruwa daga sama; sa'an nan ya tsirar muku da lambuna masu kayatarwa da shi, wadda ba ku da ikon (ba don ya muku ba) ku tsirar da bishiyar ta, Shin akwai wani abun bauta tare da Allah? (Amsa: Babu wani abun bauta na gaskiya tare da shi), Kai dai kawai naïf yawansu mutane ne da su ke daidaita wanin allah tare da shi (cikin bautarsu, su kuma karkatar da hakkinsa ya zuwa waninsa). (A wannan jerin gwanon ayoyin) duk lokacin da Allah madaukaki ya ambaci wani yanki na ayoyinsa sai ya bi bayanta da fadinsa:
ﮖ ﮗ ﮘﮙ
 Ma'ana: " Shin akwai wani abun bauta ne tare da Allah? ", Sai madaukaki mai tsarki ya bayyana –mana- da hakan cewa: Su mushirkai sun kasance suna tsayawa wajen tabbatar da tauhidin ULUHIYYA (basa tabbatar da shi), ba rububiyya ba; Duk da cewa a cikinsu akwai wadda ya hada Allah da wani har ma a cikin rububiyyar tasa –kamar yadda daga baya hakan zai zo; in Allah ya yarda-.
A dunkule dai Shi Allah ya kasance yana kafa hujja ga wadanda su ka musanta cancantar bautarsa (su ke yenta ga waninsa) yana kafa musu hujja da tabbatarwansu da tauhidin rububiyya (wato: Tun da kun gamsu allah shi ne mahalicci, mai juya al'amura to dole ne kuma ku tabbatar cewa wadda ya ke yin wadancan abubuwan shi daya, shi kadai ya cancanci ku yi masa bauta, ba tare da kun hada shi da wani ba).

Shi kuma ''ALMALIKU'' (Mamallaki) shi n eke umurni da hani; wadda ba zai halicci halitta ba, kamar yadda rububiyyarsa ta hukunta, sa'an nan sai ya bar su kara zube, sakaka ba tare da an umurce su ba, ko kuma a hana su ba, haka kuma ba za a musu sakayya ba ko a musu horo ba; domin shi mai mulki (Allah) shi ne mai umurni da hani, mai bayarwa, mai hanawa, mai cutarwa da amfanarwa, mai kuma bada sawaba (sakamako kan mai kyau) da horo.
Shi yasa neman tsari day a zo a cikin SURATUN NASS da SURATUL FALAK ya zama da sukane masu kyau guda uku (ARRABBU, ALMALIKU,da AL'ILAHU);
Saboda yayin da ya ce:
ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ  [الناس: ١].
(Kace ina neman tsarin ubangijin mutane).
Wadda a cikin wannan akwai tabbatar da cewa shi (Allah) shi ne mahaliccinsu, makagin halittarsu, Abun day a saura shi ne: A ce: Yayin day a halicce su shin ya kallafa musu wassu aiyuka kuma ya umurce su, ya kuma hana su? Sai aka ce: Na'am; Sai fadinsa:
ﮅ ﮆ ﮇ  [الناس: ٢]
(Mamallakin mutane)
Ya zo, ya tabbatar da halitta da umurni,
ﮞ ﮟ ﮠ ﮡﮢ ﮧ  [الأعراف: ٥٤].
Ma'ana: Ku saurara! Halitta d umurni nasa ne (Na Allah ne ubanjin halittu, wadda albarkansa ta yawaita). Yayin da aka fadi haka, Sai aka ce: Idan ya kasance ubangiji mai samarwa, kuma mai mulki da ke kallafawa bayinsa (yi da hani) To shin ana sonsa, kuma ana nuna kwadayi zuwa gare shi; don ya zama fiskantarsa shi kadai ita ce: MANUFAR YIN HALITTA DA KUMA UMURNI?
Sai aka ce:
ﮈ ﮉ ﮊ  [الناس: ٣  ].
(Abun bautar mutane).
Ai abun bautarsu, kuma abun sonsu; wadda bawa halitta, da aka kallafa masa (wassu aiyuka), kuma mai bauta baya fiskantuwa sai zuwa gare shi; Sai ULUHIYYA ta zo don ta zama cika makon (sunaye ukun) kuma manufa (da aka yi halittan aljani da mutum don ita), abun day a zo gabaninta kuma ya zama kamar shumfuda ne a gare ta, kuma sharer fage.
Su kuma wadannan surori biyu (Falaki/ Nass) sun e mafi girman magani a cikin Alqur'ani (ruk'yah). Haka kuma neman tsari da su ya z one lokacin da aka bukaci hakan; wadda shi ne: lokacin da aka yi wa Manzon Allah (s a w) sihiri; har ma ake suranta masa –a kwakwalwarsa- cewa ya aikata wani abu alhali bai aikata shi ba; ya yi kwana arba'in (40) yana kan haka. Kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari da Muslim. Kuma kullin sihirin ya kasance kulli ne goma sha daya; Sai Allah ya saukar da ayoyi goma sha daya (11); Sai kowani kulli daya ya warware tare da aya daya.
Sai kuma neman tsari da ya zo a farkon Alqur'ani ya rataya da sunansa ''AL'ILAHU –ALLAHU-); wadda shi ne abun bauta shi kadai; saboda haduwar sifofin kamala a tattare da shi, da kuma ganawar bawa da wannan abu bauta mai kamala (cikakke) ma'abocin sunaye mafi kyau, da kuma sifofi madaukaka, wadda ake kwadayin ya tsare bawansa da ke ganawa da shi da maganarsa= daga shedan wadda ya ke sa shamaki shakaninsa da tsakanin ganawa da ubangijinsa.
Sa'an nan wannan rataya da sunan ''AL'ILAHU'' (a wuraren neman tsari)ya ci gaba da kasancewa a duk wuraren da ake cewa:
 ﮰ ﮱ  من الشيطان الرجيم
(Ina neman tsarin Allah daga shedan abun yasarwa); saboda sunan Allah "Allah'' Shi ne taget (abun nufi) ga sauran sunayen; don haka ne ma kowani sunan –waninsa- baya sanuwa ya ganu a wajen halittu sai an jingina shi da shi (Allah); Sai mu ce: Allah shi ne ''ASSALAMU, ALMU'UMINU, ALMUHAIMINU''; don haka suna mai girma (Allah) shi ya ke yin bayanin waninsa. Waninsa kuma ba ya yin bayaninsa.

Wadanda kuma su ka yi masa shirka cikin RUBUBIYYARSA; daga cikinsu akwai wadanda su ka tabbatar da wani abun halittan na daban tare da shi –duk da cewa ba su ce: wannan mai halittan (wadda ba Allah ba) yana daidai da Allah ba; Wadannan sun e Mushirkai da kuma wadda ya yi kama da su (cikin masu da'awar musulunci) da ake kiransu: AL'KADARIYYAT.
Ita kuwa rububiyyarsa –madaukaki- ga dukkan halittu rubuyya ce: CIKAKKIYA, SAKAKKIYA, DA TA GAME (dukkan halittansa), kasancewar rububiyyarsa da wannan sifar ta ruguje dukkan maganganunsu; saboda tana hukunta rububiyyarsa ga dukkan abin da ke cikinsa (duniya da lahira, mai kyau ko mummuna) na zatoci (jikkai) da sifofi, da dukkan motsi, da ayyuka.

Shi kuma hakikanin akidar KADARIYYA MAJUSIYYA shi ne: Lallai (Allah) madaukaki ba shi ban e UBANGIJIN (mahaliccin) ayyukan halittu, kuma rububiyyarsa –wai- bata shafe wannan ba; kuma ta yaya rububiyyar tasa za ta shafi abin da ba shi da iko akansa, bai kuma nufe shi ba, sa'an nan bai halicce shi ba?

Shi kuma shirkan dukkan al'ummai gaba dayansa nau'i biyu ne: Shirka cikin ULUHIYYA, da kuma SIRKA CIKIN RUBUBIYYA.
Shi shirka cikin (tauhidin) Uluhiyya; da ibada shi ne ya fi rinjaye ga ma'abota shirka, kuma shi ne shirkan masu bautar gumaka, da masu bautar mala'iku, da masu bautar aljanu, da masu bautar shehunai da salihan bayi; rayayyu da matattu; wadanda su ka ce: ABIN SANI KAWAI MUNA BAUTA MU SU NE DOMIN SU KUSANTAR DA MU –WANI- KUSANCI ZUWA GA ALLAH, kuma SU CECE MU A WAJENSA, Sa'annan saboda kusancinsu zuwa ga Allah, da kuma baiwar da ya yi musu (karrama su da ya yi) sai kusanci da karama muma ta same mu; kamar yadda abin yak e sabebbe a nan duniya; cewa akan samu karama da kusanci ga wadda ke hidima ga mataimakan mai mulki, da makusantansa, da wadanda ya kebanta da su.

Su kuma littatafan Allah daga farkonsu har zuwa karshensu (sun yi ittifaki) wajen ruguza wannan mazhabar (shirka cikin bauta) da kuma yi masa raddi, tare da munana wadanda su ka auka cikinsa, da nassanta cewa su makiya Allah ne madaukaki. Suma annabawa –wadanda Allah ya aiko amincin Allah ya kara tabbata a gare su- gaba dayansu sun yi ittifaki akan haka; daga na farkonsu zuwa na karshensu. Kuma Allah madaukaki bai halaka wadda ya halaka ba daga al'ummai face sababinsa shi ne wannan shirkan, kuma don shi.
Asalin wannan shirka shi ne shirka cikin son Allah madaukaki, Allah madaukaki ya ce:     
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ     ﮇﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮞ  [البقرة: ١٦٥  ].
'' Akwai daga cikin mutane wadda ya ke rikon wanin Allah a matsayin kishiyoyi; yana sonsu kamar yadda yak e son Allah. Wadanda su ka yi imani sun fi tsananin son Allah ''. Madaukaki –a cikin wanna ayar- ya bada labari cewa: Lallai wadda ya so wani abu tare da Allah kamar yadda yak e son Allah to lallai ya riki wannan abun kishiya wa Allah –wannan kuma shi ne mafi ingancin fassara biyu da ake yi wa ayar; Cewa lallai su suna sonsu kamar yadda su ke son allah.
Wannan kuma shi ne daidata wanin Allah da shi da aka ambata a cikin fadinsa madaukaki:
ﭛ ﭜ ﭝ     ﭞ ﭟ ﭠ  [الأنعام: ١].
 '' Sa'an nan wadanda su ka kafirta sun kasance: Ubangijinsu su ke daidatawa ( da wani). Ma'ana –ga mafi ingancin zance biyu- cewa; Lallai su sun kasance suna daidaita waninsa (Allah) da shi cikin bauta; sai su daidaita tsakaninsa da tsakaninsa cikin so da bauta, haka kuma fadin mushirkai –al'hali suna cikin wuta- fadinsu ga gumakansu:
ﮝ ﮞ ﮟ        ﮠ  ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ  [الشعراء: ٩٨].
Ma'ana: " Mun rantse da Allah! Mun kasance a cikin bata mabayyaniya*** yayin da mu ke daidaita ku da ubangijin halittu''.
Kuma sananne ne –yanke- cewa wannan daidatawa bai kasance tsakaninsu da tsakanin Allah ba cikin kasancewarsa shi ne ubangijinsu, kuma mahaliccinsu, da kuma cewa kasa da abin da ke cikinta na Allah ne shi kadai, kuma shi ne ubangijin sammai bakwai, da kuma ubangijin al'arshi mai girma, kuma lallai shi madaukaki shi ne mulkin komai ya ke hanunsa, kuma shi ne ke tunkude sharri ga bayinsa, kuma ba wadda ya isa ya tunkude abin da ya kaddara ga wani bawa; in shi bai kawar masa ba.
Abin sani kawai wannan daidaitawar ta kasance ne tsakaninsu da shi madaukaki cikin: SOYAYYA DA IBADA; don haka duk wadda ya so wanin Allah madaukaki, ya kuma ji tsoronsa, ya yi fatansa, ya kuma kankan da kai a gare shi kamar yadda ya ke son Allah, ya ke kuma tsoronsa, da kaunarsa to Lallai wannan shi ne shirkar da Allah ba ya gafarta shi! To kuma yaya ga mutumin da wanin Allah shi ya fi fifiko a wajensa akansa (Allah), yafi sonsa, ya fi kuma tsoronsa, sa'an nan ya zama wajen neman yardarsa ya fi tsananin aiki akan neman yardan allah?! To idan wadda ya daidaita Allah da waninsa cikin abin da ya gabata ya zama ''MUSHIRKI'' to menen zaton da wannan? (Ma'ana: wadda ya fifita waninsa akansa!); Muna neman tsarin Allah daga tobuwar zuciya da kadaita shi da kuma musulunci; kamar yadda maciji ya ke fita daga sabarsa, mutum ya tobu daga musulunci al'halin yana zaton shi musulmi ne mai tauhidi. Wannan shi ne daya daga cikin nau'oin shirka.
Su kuma dalilai da su ke nuni kan: (Allah) madaukaki ya wajaba ya zama shi kadai ake bautawa suna ruguza wannan nau'in na shirka, su kuma warware hujjoji (shubuhohin) ma'abotansa, yawansu kuma (wadannan dalilan) ba wanda ya isa ya kididdige su sai Allah madaukaki, KAI! DUK ABIN DA ALLAH MADAUKAKI YA HALITTA DALILI NE DA KE YIN SHAIDA KAN KADAITUWARSA, HAKA KUMA DUK ABIN DA YA YI UMURNI DA SHI. Don haka duk halittunsa, da umurninsa, da kuma abin da allah ya kagi halittunsa akansu, da abin da ya kimtsa musu na kwakwale = dukkansu dalilai ne da su ke shaida cewa ba wadda ya cancanci a yi masa bauta sai shi kadai, kuma duk abin bauta –waninsa- to barna ne, Shi kuma Allah shi ne gaskiya mabayyani –Ya tsarkaka kuma ya daukaka-.

وواعجبًا كيف يُعصى الإلـه

أم كيف يَجحَدُه الجاحدُ
ولله في كلّ تَحـريكةٍ

وتسكيـنةٍ أبدًا شـاهدُ
وفي كلّ شيءٍ لـه آيةٌ

تـدل على أنـه واحدُ
Ma'ana: " Ka yi mamakin yadda ake saba wa (Allah) abun bauta!
Kuma ka yi mamakin yadda mai musantawa ke musanta Allantakarsa!
Al'hali Allah na da –a cikin kowani motsi… har abada, da kuma kowani shiru, yana abin da ke masa shaida kan cancantarsa ga bauta!
Haka kuma cikin kowani abu yana da aya (alama) da ta ke nuni kan kadaitakarsa!

Shi kuma nau'i na biyu na shirka shi ne SHIRKA CIKIN RUBUBIYYA (wato: kudurta akwai wani mahalicci dare da Allah):
Hada Allah madaukaki da wani cikin rububiyya; misalinsa kamar wadda ya kudure cewa akwai wani mahaliccin na dabam; kamar masu bautar wuta (MAJUSAWA) da wassunsu; wadanda su ke cewa: WANNAN HALITTUN SUNA DA UBANGIJI GUDA BIYU; DAYA daga cikinsu shi ya halicci dukkan alkhairi; da yaren mutane Iran (Farisanci) suna kiran wannan Allan: YAZDAN.
'DAYAN KUMA; Shi ya halicci sharri, (majusawa da harshensu suna kiransa: AHRAMAN.

Kuma kamar misalin PILOSERPERS DA WADANDA SU KA BI SU; da su ke kudure cewa: Ba abin da ya samu daga Allah (ya halitta) sai abu guda kwara kadai; wadda kuma tushen halittu gaba dayansu daga kwakwale ne da rayuka; Shi kuma tushen wannan duniyar daga wani kwakkwaran hankali ne (da su ke kiransa: AL'AKLUL FA'AAL); Shi kuma shi ne ubangijin abin da ke karkashinsa, kuma mai jujjuya shi.

Wannan shirkan ya fi sharri fiye da ma shirkan masu bautar gumaka da majusawa (masu bautar wuta) da Nasara (crister), kuma shi ne mafi daudar shirka a duniya; ta yadda ya kunshi kore Allah, da musanta uluhiyyarsa (cancantarsa ga bautan bayi), da kuma rububiyyarsa, da jingina halittar halittunsa zuwa ga waninsa, da haka ne ya kunshi abin da ba wani shirkan wata al'umma ta kunshe shi.

(Misali na gaba) Shirkan KADARIYYA; Shi kuma an tsakuro shi ne daga wannan, sa'an nan –kamar- kofa ne na shiga wa wancan shirkan (Majusawa); Shi yasa sahabbai –Allah ya kara musu yarda- su ka kamanta su da majusawa kamar yadda ya tabbata daga (Abdullahi) dan Umar da (Abdullahi) bn Abbas. Allah ya kara musu yarda. Kuma ma'abucin sunan (Abu dawud) ya ruwaito haka din yana mai jingina shi zuwa ga Annabi (s a w) cewa: (Su kadariya) su ne majusawan wannan al'ummar([1]) .

Sau da yawa shirka biyu (na rububiyya da na uluhiyya) su kan hadu wa bawa, kamar yadda daya daga cikinsu kuma –a wassu lokutan- ya kan kebanta wajen siffantuwar wani da shi.

Alqur'ani mai karamci, dama sauran littatafan (Allah) da aka saukar daga gare shi; dukkansu su fito karar sun yi raddi ga ma'abota wannan shirkar; misali fadinsa madaukaki:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa) Wannan na kore hada shi da wani cikin soyayya da bauta. Fadinsa kuma:
ﭤ  ﭥ  ﭦ   [الفاتحة: 5].
(kuma a gare ka kai kadai mu ke neman taimako) Shi kuma wannan na kore gama Allah da wani cikin halittarsa da rububiyya.
Wannan ayar ta kunshi: TACE TAUHIDI ga (Allah) ubangijin halittu cikin bauta, kamar yadda bai halatta a tara shi da wani ba cikin ayyuka, ko laffuza, ko cikin niyyoyi;
Misalin shirka da shi cikin ayyuka shi ne kamar: yin sujjada ga waninsa, da kuma yin dawafi ba ga daki mai alfarma ba, da kuma aske kai da nufin bauta da kankan da kai ga waninsa, da kuma sunbantan wassu duwatsu wadda ba ALHAJARUL ASWAD; wadda daman Allah ne a bayan kasa([2]) = ba, ko kuma sunbantar kaburbura da shafarsu, da kuma yi musu sujjada.
Kuma hakika Annabi (s a w) ya la'anci wadda ya riki kaburburan Annabawa da salihai masallatai da ke yi wa Allah salla a cikinsu, yaya kuma wadda kuma ya rike su abun bauta da ake bauta musu koma bayan Allah!! Wadda ya aikata haka bai san ma'anar:
  ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa), ba.
Ya zo cikin Sahihul (Bukhari da Muslim) daga Annabi (s a w) cewa shi ya ce:
" لَعَنَ اللَّهُ الْيَهُودَ اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ "
Ma'ana: " Allah ya la'anci yahudawa da Nasara; saboda sun riki kaburburan Annabawansu masallatai ".
A cikinsa kuma (Bukhari, amma ta'aliki) daga annabi s a w ya ce:
" إنّ مِن شِرَار النَّاسِ مَن تُدْرِكُهُمْ السَّاعَةُ وهم أَحْيَاء، وَالَّذِينَ يَتَّخِذُونَ القُبُورَ مَسَاجِدَ "
Ma'ana: " Lallai ashararan mutane su ne: wadanda kiyama za ta riske su al'halin suna da rai, da kuma wadanda su ke rikon kabari a matsayin wuraren salla ".
Ya zo kuma a ciki Sahuhu (muslim) daga Annabi s a w:
 " وَإِنَّ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ كَانُوا يَتَّخِذُونَ قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ، أَلا فَلَا تَتَّخِذُوا الْقُبُورَ مَسَاجِدَ إِنِّي أَنْهَاكُمْ عَنْ ذَلِكَ ".
Ma'ana: "Lallai wadanda su ka kasance gabaninku sun kasance suna rikan kaburburan Annabawansu da salihansu  a matsayin wuraren salla; Ku saurara! Kada ku riki kaburbura wuraren salla, lallai ni ina hana ku wannan ".
A cikin Musnad din Imamu ahmad da Sahihu bn Hibban daga Annabi s a w :
" لَعَنَ رَسُولُ اللَّهِ r زُوارَاتِ الْقُبُورِ، وَالْمُتَّخِذِينَ عَلَيْهَا الْمَسَاجِدَ وَالسُّرُجَ "
Ma'ana: " Manzon Allah s a w ya la'anci mata masu yawan ziyartar kaburbura, da kuma masu rikansu masallatai, da kuma sa musu fitila ". Ya kuma ce:
" اشْتَدَّ غَضَبُ اللَّهِ عَلَى قَوْمٍ؛ اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ "
Ma'ana: " Fushin Allah ya yi tsanani ga mutanen da su ka riki kaburburan Annabawansa masallatai ". Ya sake cewa:
" إنّ مَن كان قبلكم كانوا إِذَا مَاتَ فيهمْ الرَّجُلُ الصَّالِحُ بَنَوْا عَلَى قَبْرِهِ مَسْجِدًا، وصَوَّرُوا فِيهِ تِلْكَ الصُّورَةَ، أُولَئِكِ شِرَارُ الْخَلْقِ عِنْدَ اللَّهِ "
Ma'ana: " Lallai wadanda su ke a gabaninku sun kasance idan mitum na gari ya rasu a cikinsu; sai su gina masallaci a kabarinsa, su kuma suranta wancan suran akansa; wadnnan su ne mafi sharrin halitta a wajen Allah ".

Mutane a wannan babin –INA NUFIN ZIYARTAR KABARI- sun kasu kashi uku([3]) :
MUTANEN DA su ke ziyartar mamata; Sai su yi musu addu'a, Wannan ita ce ziyara irin ta shari'a.

MUTANEN DA su ke ziyartarsu; Sai kuma su roki Allah (bukatunsu) da su; Wadannan su ne MUSHIRKAI, KO KUMA JAHILAN GAMA GARIN MUTANE, DA KUMA WULAKANTATTU DAGA MASU WUCE GONA-DA-IRI (kan bayin Allah matattu tare da juyar da hakkin Allah zuwa gare su).

MUTANEN DA su ke ziyartarsu sai kuma su roke su (koma bayan Allah s w t); Al'hali Annabi s a w ya  ce:

" اللَّهُمَّ لا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا يُعْبَدُ "
Ma'ana: " Ya Allah! Kada ka sa kabarina ya zama gunki; da za a bauta masa!!  Wadannan su ne wadanda su ke hada Allah da waninsa (mushirkai) a cikin rububiyya.

Lallai hakika Annabi s a w ya bada kariya wa tauhidi; mafi girman kariya (ya kuma kiyaye shi; kiyayenwan da ba wadda ya masa irinsa); saboda ya tabbatar da fadin (Allah):

ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).
Har ma ya yi hani kan yin salla a lokuta biyu; (lokacin fitowar rana, da na faduwarta) don toshe kofar kamancecceniya da masu bautar rana; wadanda su ke mata sujjada a wadannan lokutan.

Haka kuma ya toshe kofa; ta hanyar hani kan yin sallah bayan la'asar, da kuma bayan sallar asuba; saboda haduwan lokuta biyun da lokutan da mushirkai su ke yin sujjada wa ranan([4]).
Amma dangane da sujjada ga wanin Allah kuma sai (Manzon Allah) s a w ya ce:
" لا ينبغي لأحدٍ أنْ يسجد لأحدٍ إلا لله "
(Bai dace ba ga wani ya yi sujjada ga wani in banda Allah ba)
Fadin (BAI DACE BA) kuwa a cikin maganan Allah da manzonsa; ana amfani da shi cikin abin da ya kai makura wajen hani (da muni); kamar fadin Allah:
ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ  [مريم: ٩٢]
(Kuma bai dace ga mai rahama ba ya riki da), Da fadinsa madaukaki:
ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰﯱ ﯸ  [يس: ٦٩].
(Kuma bamu ilmantar da shi waka ba, kuma ma bai dace da shi ba), Da fadin madaukaki:
ﭥ ﭦ ﭧ    ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ  ﭯ   [الشعراء:210-٢١١].
(Alqur'ani Sahidanu ba su su ka sassaukar da shi ba *** kuma bai dace musu ba (saukar da shi qur'anin) …), Da kuma fadin madaukaki:
 ﮜ ﮝ            ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ  ﮯ  [الفرقان: ١٨].
(Bai dace da mu ba mu riki waninka a matsayin majibinta -masoya- ).

Kuma yana daga cikin shirka da Allah madaukaki; wadda ya ke warware fadin (Allah) madaukaki:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).
Yana daga cikin haka: HADA ALLAH DA WANINSA CIKIN LAFAZI; kamar rantsuwa da waninsa, kamar yadda Imam Ahmad da Abu Dawuud su ka ruwaito daga gare shi (s a w) lallai shi ya ce:
" مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللَّهِ فَقَدْ أَشْرَكَ "
Ma'ana: " Duk wadda ya rantse da wanin Allah hakika ya yi shirka ". Hakim da Ibnu Hibban sun inganta shi.
Ibnu Hibban ya ce: Hassan bn Sufyan ya ba mu labari, yace Abdullahi bn Umar Alju'ufiy ya bamu labari, ya ce: Abdurrahim bn Sulaiman ya ba mu labari, daga Alhasan bn Ubaidullah Annakha'iy, daga Sa'ad bn Ubaidata, lallai ya ce: Na kasance a wajen Ibnu Umar (Allah ya kara yarda da su); Sai wani Mutum ya a wajensa ya rantse da ka'aba; Sai Ibnu Umar ya ce: Kaitonka! Kada ka aikata!! Lallai ni na ji manzon Allah s a w yana cewa:
" مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللَّهِ تعالى فَقَدْ أَشْرَكَ "
Ma'ana: " Duk  wadda ya rantse da wanin Allah madaukaki to hakika ya yi shirka ".

Yana kuma daga cikin shirka: FADIN MAI FADI GA WANI DAGA CIKIN MUTANE: Allah da kai ku kuka nufi (wannan alkhairin da ya same ni); kamar yadda ya tabbata daga Annabi s a w lallai shi wani mutum ya ce masa: Allah ya nufa kaima ka nufa, Sai ya ce:
" أجَعَلْتَنِي لِلَّهِ ندًّا؟ قل: مَا شَاءَ اللَّهُ وَحْدَهُ "
Ma'ana: " Shin ka sanya wa Allah kishiya?! Ka ce: Allah shi kadai ya ga dama (ya nufa).
Tare kuma da cewa; Lallai Allah madaukaki ya tabbatar wa mutum da nufi (ganin dama; misali cikin fadinsa:
ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ  [التكوير: ٢٨].
Ma'ana: " Duk wadda ya so daga cikinku ya yi istikama (tsayuwa akan tafarkin Allah; tare da bin umurni da hani).
(To idan shari'a ta hana wannan lafazin) to ya ya kuma ga wadda ya ke cewa: NI NA DOGARA AKNA ALLAH DA KANKA, KO KUMA NI INA CIKIN KULAR ALLAH DA KULARKA, KO KUMA BANI DA KOWA SAI ALLAH DA KAI, KO KUMA WANNAN YA SAMU NE DAGA ALLAH DA KAI, KO KUMA WANNAN NA DAGA CIKIN ALBARKOKIN ALLAH DA ALBARKOKINKA, KO KUMA A SAMA INA DA ALLAH, A KASA KUMA BANI DA KOWA SAI KAI?!
KA AUNA tsakanin wadannan laffuzan da su ke fitowa daga bakin yawan mutane da kuma tsakanin abin da aka hana na lafazin: ALLAH NE DA KAI KU KA NUFE NI DA WANNAN ALKHAIRIN, sa'an nan sai ka duba wanne daga cikinsu ya fi muni?!
Zai bayyana (bayan aunawan) maka cewa lallai wadda ke fadin wadannan na karshen shi ya fi cancantar nisa da:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).
Kamar yadda shi ya fi cancantar amsan Annabi s a w da ta gabata ga wadda ya fadi waccar karma! (Ka sanya wa Allah kishiya!). Sa'annanidan har wancan ya ya sanya manzon Allah s a w kishiya wa Allah; To shi kuma wadda ya fadi wadannan ya sanya wadda bai yi kusa da manzon Allah matsayi ba wa Allah kishiya!
A dunkule; Ibadar da aka ambata a cikin fadin:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).
(Wannan ibadar ita ce): Sujjada, da dogaro ga Allah (tawakkali), mayar da al'amari zuwa gare shi, da takawa, da tsoro, da tuba, da bakance, da rantsuwa, da tasbihi, da kabbara, da fadin La'ilaha illal lah, da cewa Alhamdu lillah, da neman gafara, da aske kai kaskantar da kai ga Allah da bauta, da addu'a; dukkan wadannan tsantsar hankin Allah ne madaukaki (da bai halatta a juyar da shi ya zuwa waninsa ba!).
Ya zo cikin musnad din Imamu Ahmad lallai wani mutum an zo da shi wajen Annabi s a w al'halin ya aikata wani zunubi, yayin da ya tsaya a gaba gare shi sai ya ce:
" اللَّهُمَّ إِنِّي أَتُوبُ إِلَيْكَ وَلا أَتُوبُ إِلَى مُحَمَّدٍ؛ فَقَالَ النَّبِيُّ r: عَرَفَ الْحَقَّ لِأَهْلِهِ ".
Ma'ana: " Ya Allah lallai ni ina tuba zuwa gare ka, bana tuba zuwa ga Muhammadu, Sai (Manzon Allah) s a w ya ce: Ya san gaskiya, kuma ya jingina ta zuwa ga ma'abocinta".
Kuma Hakim ya fitar da shi daga hadisin Alhasan, daga Al'aswad bn Sari'I, ya kuma ce: Hadisi ne ingancecce.
   Amma hada Allah kuma da wani cikin nufi da niyyoyi, to wannan kam kogi ne da bashi da iyaka, wadda kuma kadan ke tsira daga gare shi; saboda duk wadda ya yi nufin wanin fuskar Allah madaukaki da aikinsa; To bai tsayar hakikanin fadinsa ba:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).
Saboda:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa).  Ita ce taceccen addini (addinin da ba shirka) addinin annabi Ibrahim; wadda Allah ya umurci dukkan bayinsa da shi, Kuma Allah ba zai karbi wani addini ba waninsa, kuma shi ne hakikanin musulunci;
ﭯ  ﭰ  ﭱ  ﭲ    ﭳ  ﭴ  ﭵ  ﭶ  ﭷ  ﭸ  ﭹ  ﭺ  ﭻ  ﭼ    [آل عمران: ٨٥].
Ma'ana: " Duk wadda ya riki (nemi) wanin addinin musulunci a matsayin addini to ba za a karba masa ba, kuma lallai shi a lahira yana daga cikin masu hasara ".

Don haka; ka yi riko da wannan tushen mai asali, Sa'annan duk abin da 'yan bidi'a da mushirkai su ka fito da shi ka yi kokarin mayar da shi ya zuwa gare shi (don ka gane, girman nisansa da shi wannan asalin); In ka yi haka za ka tabbatar da ma'anar kalmar LA'ILAHA ILLAL LAHU; (za ka tsira).

Da ko za a ce: AI SHI MUSHIRKAI YA NUFI GIRMAMA ALLAH NE MADAUKAKI; KUMA DON MA GIRMAN NASA NE (ALLAH) BAI DACE A SHIGA MASA BA SAI DA TSANI DA KUMA MASU CETO, kamar dai halin masu mulki (sai da kamun kafa); KA GA KENAN SHI MUSHIRKI BAI YI NUFIN WULAKANTA ALLAH BA, HASALI MA YA YI NUFIN GIRMAMA SHI NE! ya kuma ce:
ﭢ  ﭣ    ﭦ 
( A kai kadai mu ke bautawa). KUMA AI INA BAUTA WA WADANNAN TAFINTOTIN (WADDA NA KE KAMA KAFANSU) DOMIN SU KUSANTAR DA NI ZUWA GARE SHI, SA'AN NAN SU SHIGAR DA NI KANSA; DON HAKA (ALLAH) SHI NE MANUFA, SU KUMA HANYOYI NE ZUWA GA MANUFA;
In ko haka ne; don me yasa wannan gwargwadon ya ke hukunta fushin Allah, kuma ya dawwamar (da mai yinsa) a cikin wuta, sa'an nan ya hukunta zubar da jinin ma'abutansa, ya halatta matansu da dukiyansu (matan mushirkai da dukiyansu, a lokacin yaki)?
Kuma shin –a hankalce- ya halatta Allah madaukaki ya shar'anta wa bayinsa su rika kusantarsa (bauta masa) da masu ceto da kuma tsanoni, Sai ya zama haramcin hakan kawai an fa'idanta da shi ne da ya zo cikin shari'a (aya, hadisi) kawai? Ko kuma hakan mummuna ne a shari'ance da kuma hankalce; wadda kwata-kwata ba zai yiwu ace wata shari'a daga cikin shari'oin (Allah) sun zo da shi ba??
Kuma menen sirrin da ya sanya shi ba a gafarta shi sabanin sauran zunbai? Kamar yadda Allah madaukaki ya ce:
ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ  ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ    ﯗ ﯘ  [النساء: ٤٨].
Ma'ana: " Lallai Allah baya gafarta a hada shi da wani (shirka, matukar an mutu akai ba a tuba ba); Yana kuma gafarta abin da ke kasa da haka ga wadda ya ga dama (ya nufa), kuma duk wadda ya hada Allah da wani to hakika ya kirkiri laifi (zunubi) mai girma "???

(Don Amsa wadannan tambayoyin) Sai mu ce:

Shirka iri biyu ne; Shirka da rataya da ZATIN ABIN BAUTA, DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA, DA KUMA AYYUKANSA.
Da kuma shirka a cikin YI MASA BAUTA DA MU'AMALANTARSA; koda kuwa ma'abucin wannan yana kudurta cewa –Allah madaukaki- ba shi da mai tarayya cikin zatinsa, haka kuma cikin sifofinsa (wato bai fada cikin shirka da take nau'I na farko ba).
Shi shirka na biyun nan shi ne mu ka gama magana akansa (dazu), kuma muka sa ke nuni zuwa gare shi –a nan-, kuma –a gaba- za mu kara magana a kansa kuma mu kosar.
Amma shirkar (nau'in) farko kuma, to shi kam ya kasu kashi biyu:

Na Farkonsu: Shirkan kore samuwan Allah (wadda malamai su ka masa lakabi da: SHIRKAN TA'ADIL); Wannan kuma shi ne mafi munin shirka; (misalinsa) kamar shirkar Fir'auna a cikin fadinsa:
ﭯ ﭰ ﭱ     ﭲ  [الشعراء: ٢٣].
(Wanene Ubangijin halittu?), Ya kuma ce wa Hamana:
ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞﮟ  ﮯ  [غافر:36-٣٧].
 (Gina min gini mai tsayi –bene- tsammani na zan isa kofofin; kofofin sammai; don na tsinkaya zuwa ga Allan Musa (da ya ke riyawa), Kai ni ina ma zaton karya ya ke yi).

Shi  shirka da kore samuwar Allah ko cancantarsa ga hakkinsa suna lazimtar juna; don haka duk mushirki to ya kore wa Allah cikarsa da zama wajibi a siffanta shi da ita, ko kuma ya ma kore samuwarsa. Haka kuma duk wadda ya yi haka (ta'adil) to mushirki ne. Sai dai kuma shirka ba ya lazimtar tushen ta'adil; saboda ai ana samun mushirkin da ya tabbatar da samuwan mahalicci madaukaki da kuma sifofinsa; Sai dai kuma ya wofantar da ba shi hakkinsa na kadaitawa.
Tushen shirka da kuma ka'idarsa da ke- kai- komo a kanta shi ne: Ta'adil; Shi kuma ya kasu kashi uku:
 Na farkonsu: Kore halitta daga mahaliccinsa: (misalinsa kamar cewa: Duniyan nan bata da mahalicci, ko aikin bayi ba halittan Allah ba ne, d. sauransu).
Na biyu: Kore wa mahicci kamalarsa (cikarsa da bunkasarsa) da ya tabbata masa (cikin ayoyi da hadisai).
Na uku: Tozarta mu'alarsa ga barin abin da ya wajaba masa akan bawa na hakikanin tauhidi (kadaita shi wajen ibada).
Yana daga cikin wannan (kason farko); Shirkan ma'abota addinin komai Allah ne (wadanda ake musu lakabi: SAMAMMUN ABUBUWA GABA DAYANSU ABU DAYA NE; -WIHDATUL WUJUD- wato da mai yanka da abin da aka yanka, da mai jima'I da wadda ake mata jima'in, da kuma mai halitta da wadda aka halitta).
Haka; yana daga cikinsa; Shirkar kafirai da su ke cewa: Halittu (duniya) babu wani lokacin da su ka faru – a ta baya; saboda tun da can can… akwaisu- kamar yadda kuma ba lokacin da za su kare (Ka ga wannan sifar Allah ne shi daya). Kuma su ke cewa: Lallai duk abin da ya faru (halittu) to sun jingina (dogara) ne ya zuwa wassu sabuba da kuma tsanoni da su ka hukunta samuwarsu; wadanda su ke kiransu: HANKULA DA RAYUKA (AL'UKUL DA NUFUUS).
Yana kuma daga cikin (kaso na biyu) Shirkar masu kore wa Allah sunayensa da sifofinsa; kamar Jahamiyya, da Karamida, da kuma mu'utazilan da su ka wuce gona da iri.
Nau'i na biyu: SHIRKAR MISALTAWA; (wadda ita ce shirkan wanda ya sanya wa Allah kwatankwaci) misali shirker wadda ya riki wani abin bautan daban tare da Allah madaukaki; kamar Nasara (creister) dangane da (Annabin Allah) Almasihu, da kuma yahudawa dangane da uzairu, da kuma masu bautar wuta (majusawa) da su ka kudure jingina abubuwan alkhairi ya zuwa ga haske, da kuma abubuwan sharri ya zuwa ga duhu.
Shirkan kadariyya  -majusawa wannan al'ummar- an tsakure shi daga wannan.
Wadannan su ne yawa – yawan mushirkan duniya, Kuma su bangarori ne masu yawa:
* Daga cikinsu akwai wadda ke bautawa wassu bangarori na sama (rana, taurari ko wata d. sauransu).
* Daga cikinsu kuma akwai wadda ke bautawa wassu bangare na kasa (kamar gumaka, kaburbura, waliyyai, da Annabawa da salihai).
* Daga cikin wadannan akwai wadda ke riya cewa abun bautarsa shi ne mafi girman abun bauta.
* Daga cikinsu akwai wadda ke riyawa cewa: abun bautarsa daya daga cikin abubuwan bauta.
* Haka kuma daga cikinsu akwai wadda ke riya cewa: Idan har ya kebe abun bautar dad a bautarsa, da kuma yankewa ya zuwa gare shi; Sai abin bautar ya fiskance shi ya kuma lura da shi.
* Kamar yadda a cikinsu akwai mai riya cewa abun bautarsa na kasa zai kusantar da shi ya zuwa ga abun bautarsa na sama, shi ko na sama ya zuwa ga na sama da shi; har wadannan abubuwan bautar su kusantar da shi zuwa ga Allah madaukaki mai tsarki; don haka wani lokaci –sai ka ga- wadannan shamaki su yi yawa, wani lokacin kuma sai su yi kadan.

Idan har ka san wadannan kungiyoyi, kuma ka san tsanantawar kama daga Manzon Allah s a w ga wadda ya hada Allah madaukaki da wani (shirka) cikin ayyuka da zantuka da kuma niyyoyi –kamar dai yadda ambaton haka ya gabata- To; (SAI A CE): KOFAR AMSA WADANNAN TAMBAYOYI (DA SU KA GABATA) YA BUDE MAKA; Sai mu ce:
Ka sani Lalllai hakikanin shirka shi ne: Kamanta mai halitta (Allah) da kuma halitta (ko wanene shi; mala'ika ne ko annabi; ballentana waninsu), da kuma kamanta halitta da mai halitta.
Amman a farkon ; To lallai mushrki ya kamanta halitta da mai halitta a cikin abubuwan da allah ya kebanta da su (WADANDA DA LARABCI AKE KITANSU; KHASA'ISUL ILAHIYYA; kuma shi ne: cikar zati, da kamalar sunaye da sifofi;wadda ke haifar da cancantar fiskantar da dukkan bauta zuga Allah kamili shi kadai); sun e kuma kadaitaka da mallakan cutarwa da amfanarwa, da bayarwa da hanawa; don haka duk wadda ya rataya hakan zuwa ga wani halitta; to lallai ya kamanta shi da mai halitta madaukaki, ya kuma daidaita turbaya da ubangijin alloli.
To wani irin fajirci ne, ko kuma wani irin zunubi ne ya fi wannan girma?!

Kuma ka sani lallai na daga cikin abubuwa da Allah ya kebanta da su; Gama-garin kamala kuma tumbatsttse ta kowace fuska; wadda ba nakasa a cikinsa ta kowace fuska daag cikin fuskoki; hakan kuma na wajabta dukkan bauta ta zama nasa ne shi kadai (da a fuskantar da ita zuwa ga wani sai shi daya); a hankalce, a shari'ance da kuma a fidirance (wato yadda ya Allah ya kimtsa wa bayinsa lokacin day a halicce su).   Duk kuma wadda ya sanya hakan ga waninsa (wanin Allah; ya bauta masa) to lallai ya kamanta wannan din da wadda ba shi da makamanci. Kuma saboda tsananin muninsa (shirka; kamanta wani da Allah) da kuma yadda hakan ya kunshi kololuwan zalunci; Shi yasa ( Allah) da ya wajabta wa kansa rahama ya bada labari kan har abada ba zai gafarta shi ba ( baya kankare shirka).

 Yana kuma daga cikin abubuwan da Allah ya kebanta da su; Cancantar bauta da bata tsayuwa sai akan dugadugan soyayya da kan-kan-da-kai; duk wadda ya bada abubuwa biyun nan ga waninsa (wadda ba Allah ba) to hakika ya kamanta shi da Allah madaukaki cikin tsagoron (madarar, kuma taceccen) hakkinsa. Munin wannan kuma tabbacecce ne a cikin kwakwale da fidirori.
Sai dai yayin da Shedanu su ka jirkita (canza) fidirorin yawa-yawan halitta (mutum da aljan) su ka kuma gusar da su daga kan addininsu, su ka umurce su su hada Allah (da wassunsa; shirka) wadda Allah bai saukar da dalili ba akan haka, -kamar yadda mafi  sanin Allah kuma mafi sanin bayin Allah (Manzon Allah s a w) ya  ruwaito haka din-; (Su ko mushirkai) sun makanta ga sanin shirka har su ka yi zatonsa a matsayin abu mai kyau.

Yana kuma daga cikin abubuwan da Allah ya kebanta da su; Sujjada; duk wadda ya yi sujjada ga waninsa (wadda ba Allah ba) to lallai ya kamanta shi da shi (ya yi shirka).

Yana kuma daga cikin haka; Tawakkali; Duk wadda ya dogara ga waninsa (wadda ba Allah) to lallai ya kamanta shi da shi (ya kuma yi shirka).

Yana kuma daga cikin haka; Tuba; Duk wadda ya tuba zuwa ga waninsa (wadda ba Allah) to lallai ya kamanta shi da shi (ya kuma yi shirka).

Yana kuma daga cikin haka; Rantsuwa da sunansa cikin halin girmama shi; Duk wadda ya rantse da waninsa (wadda ba Allah) to lallai ya kamanta shi da shi (ya kuma yi shirka).  

Yana kuma daga cikin haka; Yanka a gare shi; Duk wadda ya yi yanka ga waninsa (wadda ba Allah) to lallai ya kamanta shi da shi (ya kuma yi shirka).

Yana kuma daga cikin haka; Aske kai; ..da wassun wadannan…., Wannan kuma duk a bangaren kamantawa ne;

Amma a bangaren kamantuwa To;

Duk wadda ya ya girmama, ya yi girman kai, sa'an nan ya kirayi mutane ya zuwa ga  wuce gona-da-iri, da fatan samun abin da ke wajensa, da tsoronsa … To lallai hakika ya nemi kamantuwa da Allah, kuma ya yi jayayya da shi cikin rububiyyarsa (da ma sunayensa da sifofinsa); don haka; ya cancanci Allah ya wulakanta shi matukar wulakantawa, sa'an nan ya sanya shi ya zama kamar kwayar zarra (don kaskanci; sabanin abin day a nema na girma dab a hakkinsa ba ne) karkashin diddigen halittunsa.
Ya zo cikin Sahihu Muslim da Annabi s a w, lallai shi ya ce:
"يقول اللَّهُ U: الْعَظَمَةُ إِزَارِي، والْكِبْرِيَاءُ رِدَائِي؛ فَمَنْ نَازَعَنِي وَاحِدًا مِنْهُمَا عذّبتُهُ "
Ma'ana: " Allah yana cewa: Girma tufa ta ne (da na kadaita da siffantuwa da ita), girman kai mayafina; Duk wadda ya yi jayayya da ni daya daga cikinsau (ta hanyar siffantuwa da shi) To zan azabtar da shi ".

Kuma idan mai daukar hoto; da ke daukar daukar hotunan da hanunsa yana cikin wadanda su ka fi tsananin azaba a ranar tashin kiyama; saboda ya yi kamancecceniya da Allah a gundarin sana'ntawa; To menene kuma zatonka da wadda ya ke kamantuwa da Allah cikin rububiyya da uluhiyya?   Kamar yadda Annabi s a w ya ce:
" أَشَدُّ النَّاسِ عَذَابًا يَوْمَ الْقِيَامَةِ الْمُصَوِّرُونَ، يُقَالُ لَهُمْ: أَحْيُوا مَا خَلَقْتُمْ "
Ma'ana: " Lallai mafi tsananin azaba ranar kiyama su ne: masu dauakr hoto; za a ce musu: ku raya abin da ku ka halitta ". Ya zo kuma cikin Sahihul  Bukhari da Muslim daga Annabi s a w; lallai shi ya ce:
" يَقُولُ اللَّهُ U: وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ ذَهَبَ يَخْلُقُ كَخَلْقِي؛ فَلْيَخْلُقُوا ذَرَّةً فليخْلُقُوا شَعِيرَةً ".
 Ma'ana: "Allah yana mabuwayi da daukaka yana cewa: Babu wadda ya fi zalunci fiye da mutumin da ya tafi yana halitta irin halittata; to su halicci kwayan zarra, su kuma halicci Sha'ir ". ( A cikin hadisin) Sai Allah ya fadakar (da mutane) da kamar kayar zarra, sha'ir don ya ya yi nuni kan (rashin iya halittar) abin da ke sama da su!

Haka kuma mutumin da ya yi kamancecciniya da shi madaukakin sarki a cikin sunan da baya dacewa sai da shi (shi kadai) kamar; Sarkin sarakuna, Mai hukuncin masu hukunci, da kuma Alkalin alkalai … da makamantansu; ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari da Muslim daga Annabi s a w; lallai shi ya ce:

" إنّ أَخْنَعُ الأَسْمَاءِ عِنْدَ اللَّهِ رَجُلٌ تَسَمَّى بشَاهَانْ شَاهْ؛ مَلِكِ الْملوكِ، لا مالك إلا الله "
Ma'ana: "Lallai yana daga cikin mafi munin sunaye a wajen Allah; Mutumin da ya sa wa kansa suna: SHAHAN-SHAH; Sarkin sarakuna, babu sarki (mai mulki) sai Allah".
A cikin wanilafazi:
" أَغْيَظُ رَجُلٍ عند اللَّهِ رَجُلٌ تسَمَّى مَلِكَ الأَمْلاكِ ".
 Ma'ana: " Mutumin da ya fi bakanta wa Allah rai shi ne: Mutumin da ya sa wa kansa suna: Sarkin sarakuna … "

  A dunkule dai; Kamantawan (wata halitta da mahaliccinta) da kamantuwa wannan shi ne hakikanin shirka; shi ya sa ma wadda ya yi zaton cewa: Idan ya nemi kusantuwa da wata ibada zuwa ga wanin Allah, wai wannan wanin zai kusantar da shi zuwa gare shi madaukaki; to idan ya yi haka ya yi kuskure; saboda ya kamanta shi da shi, ya kuma yi abin da (ibada) da bai dace ga wani ba sai ga shi (Allah); sai ya hada wanin Allah da Allan a cikinta; ya kuma tauye wa madaukaki hakkinsa; Yin haka kuma mummuna ne a hankalce da kuma shari'ance;
Shi ya sa ba shar'anta (yin shanin ba), kuma ba a gafarta wa mai aikata shi.

Kuma ka sani Lallai wadda ya yi zaton cewa: Lallai Ubangiji baya ji, ko baya amsa (addu'a ko karbar bauta) sai in an yi ta da kamun kafa (tsani); wadda za su tsinkayar da shi hakan, ko kuma su roki abin da aka roka daga gare shi;   To lallai irin wannan mutum ya yi mummunan zato da Allah;

Saboda in har ya yi zaton cewa (Allah) baya sanin (abin da aka roke shi), ko kuma ba ya ji Sai waninsa ya isar masa (ya ilmantar da shi) ko ya jiyar da shi; to wannan kore wa Allah ne: iliminsa, da jinsa, da kuma cikar riskarsa ga abubuwa, Hakan kuwa ya ishe ka girman zunubi!

In kuma har ya yi zaton cewa (Allah) na ji, kuma na gani, sai dai kuma ana bukatan wadda zai (lallabe shi) ya sa ya ji tausayin bayinsa, kuma ya tattausar da shi akansu; To ya munana zato kan falalolin ubangijinsa, da kyautatawarsa, da kuma yalwar kyautarsa.

  A dunkule dai: Mafi girman zunubai a wajen Allah madaukaki shi ne: Munana zato da shi (allah); Shi ya sa ya fadi narkon azabarsu mai girma a cikin littafinsa (Alqur'ani) akan munana zato da shi, kamar yadda madaukaki ya ce:
ﮜ    ﮝ ﮞ ﮟﮠ ﮡ ﮢ ﮣﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ  ﮫﮬ ﮭ ﮮ ﮯ  [الفتح: ٦].
 Ma'ana: " (Munafikai da mushirkai) masu yi mummunan zato ga Allah, mugunyar masifa mai kewayewa ta tabbata akansu, kuma Allah ya yi fushi da su, ya kuma tsine musu, ya musu tanadin jahannama; tir da ita (ta kasance) makoma. Madaukaki yana cewa dangane da masoyinsa (Annabi) Ibrahim a. s:
ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ  ﮊ ﮋ ﮌ  [الصافات:86-٨٧].
 " A karya, abubuwan bauta koma bayan Allah ku ke nufa (da bauta) ** To menene zatonku da ubangijin halittu?
Ma'ana: Menene zatonku kan abin da zai muku sakayya idan har kuka bauta wa waninsa tare da shi, Sa'an nan ku ka yi zaton cewa (Allah) na da bukatar wajen tsinkayar bukatun bayinsa = yana bukatar wadda zai zamo kamar kofa na bukatunsu zuwa gare shi (shamaki), da makamancin haka?

Wannan kuma sabanin sarakuna (masu mulki); wajen bukatuwansu bukatuwa ta lalura (dole) zuwa ga tafintoti; saboda bukatuwansu da gazawansu, da rauninsu, da kuma gajercin (karancin) iliminsu kan sanin bukatun masu bukata, lalura (talakawa).
Amma wadda jin wani wani maganan ba ya shagaltar da shi ga barin jin wani (Alllah kenan), wadda rahamarsa ta rinjayi fushinsa, ya kuma wajabta wa kansa rahama, To me tafintoti za su yi a wajensa?! Duk kuwa wadda ya riki tafinta a tsakaninsa da tsakanin Allah madaukaki to hakika ya zata masa mafi munin zato. Kuma hakan korerre ne Allah ya shar'anta shi ga bayinsa, kai! Dadin- dadawa, hakan korerre ne a cikin kwakwale da fidrori.

  Kuma ka sani lallai kan-kan-da-kai da bauta da Bawa ke sanya shi ga wadannan tafintoti mammuna ne shi a karan-kansa –kamar yadda mu ka zayyana-; musamman ma idan wadda aka yi masa haka (aka yi masa ibadar): Bawa ne na MAI MULKI, MAI GIRMA, MAI RAHAMA, MAKUSANCI KUMA MAI AMSAWA; kamar yadda Allah ya ce:
ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ         ﮘﮙ ﮟ  [الروم: ٢٨].   
(Allah " Ya buga muku misali daga karan-kanku; Shin kuna abokin tarayya daga cikin abin da damarku ta mallaka (bayinku) kan abin da mu ka azurta ku! Da ku ke tsoronsu kamar yadda ku ke tsoronsu kamar tsoronku ga karan kanku ".
Ma'ana: Idan dayanku na kin a ce bawansa da ya mallaka ya yi tarayya da shi cikin arzikinsa, to ta yaya za ku sanya mini wassu daga cikin bayina abokan tarayya cikin abin da ni kadai na kebanta da shi; wadda shi ne cancantar bauta bauta da na ked a shi, wadda kuma bat a dacewa ga wanina, kuma bata inganta ga wadda ba nib a; Duk kuwa wadda ya riya haka to bai girmama ni iyaka girmama ta.

A dunkule; Duk wadda ya bauta wa wanin Allah tare da shi da zaton wai zai isar da shi zuwa gare shi, (to wannan) bai girmama Allah ba iyaka girmama shi; Allah yana cewa:
ﭑ ﭒ   ﭓ ﭔ ﭕ ﭖﭗ ﭘ ﭙ  ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ  ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵﭶ ﭷ   ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ  الحج:73-٧٤].
(Ya ku mutane! An buga mu ku misali; ku saurara masa; Lallai wadanda ku ke roko (bauta) koma bayan Allah ba za su taba iya halittan kuda ba koda kuwa sun taru masa (saboda rauninsu), kuma idan kuda ya dauke mu su wani abu ba za su iya tsamo shi ba (kwato shi) daga gare shi, mai nema da abin da ake neman sun yi rauni (wadda ake bauta masa … ya yi rauni) ** (mushirkai) ba su girmama Allah ba iyaka girmama shi; lallai Allah mai karfi ne mabuwayi ).
(Allah) Madaukaki ya ce:
ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ  [الزمر: ٦٧].
(Kuma basu girmama Allah ba iyaka girmama shi; Kassai gaba daya damkarsa ne a ranar tashin alkiyama, sammai kuma suna nade a damansa, tsarki ya tabbata masa kuma ya daukaka ga barin abin da su ke tara shi da su (shirka).

  Don haka; Bai girmama (Allah ) mai karfi mabuwayi ba wadda ya tara shi (ya yi masa shirka) da mai rauni makaskanci.

  Kuma –ka sani- Idan ka yi lura cikin daukacin (dukkan) kungiyoyin bata da bidi'a ('yan bidi'a gaba dayansu) za ka samu cewa; Tushen batansu yana komawa ne zuwa ga abubuwa guda biyu:
Na farkonsu: Mummunan Zatonsu ga Allah.
Na biyu: Lallai ba su girmama shi ba iyaka girmamawansa;
Lallai wadda ya yi zaton cewa Allah bai turo wani manzo ba, kuma bai saukar da wani littafi ba;  kawai dai ya bar halitta haka siddan (ba umurni ba hani), ya kuma halicce su don wasa, to hakika bai girmama shi ba iyaka girmamawansa.

Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa wadda ya kore masa gamewar ikonsa (ga dukkan halittu da ayyukansu), da kuma ratayarta da aiyukan bayinsa; da'arsu ne da sabonsu, ya kuma cire su (aiyukan bayin) daga cikin halittunsa da kuma ikonsa (Wadannan mutanen su ake kira da KADARIYYA).

Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa kishiyoyin wadannan; wadanda su ka ce (su ka kudurta):Allah yana horo wa bawansa akan abin da bawan bai aikata ba, wai Allah yana masa horo ne kan aikinsa shi Allan mai tsarki (Wadannan mutanen su ake kira da JABARIYYA).
Kuma idan ya koru a kwakwale a ce shugaba ya tilasta wa bawansa kan aikata wani aiki, sa'an nan sai ya masa horo akansa, To ta yaya wannan zai kasance daga mafi adalcin adilai (Allah), Zancen wadannan (Jabariyya) ya fi sharri fiye da zancen masu kama da majusawa; wato kadariyya makaskanta.

Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya kore rahamarsa da soyayyarsa, da yardarsa da fushinsa, da hikimarsa a sake , da hakikanin aikinsa, kuma bai sanya masa wani aiki ba da zabinsa; kawai dai aiyukansa halittu ne da su ke daban da shi (masu wadannan kuduri su ne ASHA'IRAH).
 
  Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya sanya masa mata da 'da, (KAMAR MUSHIRKAN LARABAWA, DA YAHUDU DA NASARA) ko kuma ya sanya shi ya zama yana shigewa cikin abubuwan da ya halitta (KAMAR HULULIYYA), ko kuma ya sanya shi ya zama shi ne zatin wannan duniyar (KAMAR 'YAN WAHDATUL WUJUD).

Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya ce: (Allah) ya daukaka makiyan annabinsa da kuma iyalen gidansa (MASU WANNAN MAGANAR SU NE: RAFIDA; 'YAN SHI'A) kuma su ka ce; (Allah) ya sanya mulki cikinsu (wato; suna nufin sahabbai; ta yadda Allah ya bada khalifanci wa Abubakar, Umar, sa'an nan Uthmanu radiyallahu anhum, kafin bawa Aliyu –r. a-), wai kuma ya kaskantar da manzonsa da kuma iyalen gidansa (ahlul baiti); Wannan ya kunshi matukar sukar ubangiji; Allah madaukaki ya daukaka ga barin zancen rafidawa ('yan shi'a). Wannan kuma ('yan shi'a) sun tsamo shi ne daga fadin Yahudawa da Nasara (creister) kan ubangijin halittu; cikin cewarsu: (Allah) ya turo wani mai mulki ne azzalumi sai ya riya cewa shi Annabi ne, ya kuma yi karya wa Allah, ya zauna wani zamani mai tsayi (Manzon Allah ya yi shekara 23), alhali yana cewa: (Allah) ya umurce ni da kaza, ya kuma hana ni kaza, (shi wannan mai riya annabcin, a cewarsu): ya ci gaba da halatta jinanen annabawan Allah da waliyyaensa (masoyansa); Shi kuma Allah madaukaki yana ta daukaka shi, yana karfafa shi, sa'annan kuma ya yi ta tsayar da dalilai da mu'ujizozi kan gaskiyarsa, haka kuma ya yi ta fiskantar da zukatan halittu da jikinsu ya zuwa gare shi (su ka yi ta imani da shi) yana mai tsayar masa da daularsa; tana ta daukaka da karuwa, ya kuma kasakntar da makiyansa, fiye da shekara dari takwas (wato har lokacin da mai littafi ya ke rubuta shi).
Ka auna tsakanin maganan wadannan (Yahudu da Nasara akan Annabi s a w) da kuma maganan 'yan uwansu Rafida 'yan shi'a (kan Sahabban Manzon Allah s a w) za ka samu ceawa maganganu biyu daya ne.

Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya riya cewa Allah ba zai rayar da mamata ba, kuma ba zai tashi wadanda su ke cikin kabari ba, domin ya bayyana wa bayinsa abin da su ka kasance su ke ta sabani, sa'an nan kafirai su san cewa sun kasance –a rayuwarsu ta duniya- makaryata.

 A dunkule dai;  Wannan (maganar) kofa ne mai fadi, manufa dai shi ne; Lallai duk wadda ya bauta wa wanin Allah tare da Allah to lallai ya bauta wa Shedan; Allah yana cewa:
 ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ   ﭻ ﭼﭽ ﭾ ﭿ  ﮀ ﮁ ﮂ  [يس: ٦٠].
Ma'ana: " Shin ban yi alkawari ba ne zuwa gare ku, Ya ku 'yan adam cewa kada ku bauta wa shedan; domin shi a gare ku makiyi ne mai bayyana adawa! ";
Don haka; Wani ba zai bauta wa wani ba daga cikin 'yan adam –ko kuma wanene shi- face bautarsa ta auku ga shedan; Sai mai bautar ya dan ji da'di da abin bautar nasa wajen samun biyan bukatarsa, Shi kuma wadda aka bauta masan shi ma ya ji da'di da da wadda ya bauta masan; wajen girmama shi da ya yi, da kuma gama shi (shirka) da Allah madaukaki, WANNAN KUMA SHI NE KOLOLUWAN ABIN DA SHAIDAN YA YARDA DA SHI; Shi yasa Allah madaukaki ya ce:
ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐﮑ  
" (Ya Muhammad! Ka ambata musu) ranar da Allah zai tattara su gaba daya, (yana mai ce musu): Ya ku taron Aljanu kun ya waita wa mutane " Ma'ana: Kun yawaita tabar da su da kuma batar da su, (Allah ya ci gaba da cewa:
ﮒ ﮓ  ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ   ﮝ ﮞﮟ ﮠ ﮡ  ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ   ﮦ ﮧ ﮨﮩ ﮪ       ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ  [الأنعام: ١٢٨].
( Sai majibintansu daga mutane su ce: Ya ubangijinmu; Lallai sashenmu ya ji dadi da sashe, ya zuwa ajalin da ka yanka mana! Sai ya ce: Wuta ce makomarku, kuna masu tabbata a cikinta, sai abin da Allah ya nufa; Lallai ubangijinka mai hikima ne masani".
  Lallai abin da ya gabatan nan nune karami kan dalilin da yasa shirka ya zama shi ne mafi girma a wajen Allah kan kowane babban laifi (KABA'IR), kuma lallia shirka ba a gafarta shi matukar ba a tuba ba daga gare shi, haka kuma shi na wajabta dawwama a cikin azaba mai girma. Kamar kuma yadda haramcinsa da muninsa ba wai kawai ya kasance ba ne saboda tsurar hani da aka yi a kansa (a cikin Alqur'ani da hadisai) ba ne, A'ah! Yana koruwa ga Allah s w t ya shar'anta (wa bayinsa) bautar wani abun bauta koma baya gare shi, kamar kuma yadda ya ke korerre ne a gare shi duk abin da zai warware sifofin kamalarsa da daukakarsa.

*********

[KASUWAN MUTANE KASHI HUDU DANGANE DA BAUTAR ALLAH MADAUKAKI DA NEMAN TAIMAKONSA]
   Sa'an nan ka sani Lallai mutane dangane da bautar Allah madaukaki da neman taimakonsa sun kasu zuwa kashi hudu:

MAFI GIRMANSU DA FIFIKONSU SU NE: Ma'abota ibada da kuma neman taimakon Allah akan haka; (su wadannan mutanen) Bautar Allah ita ce karshen manufarsu, Neman kuma ya taimake su akanta, ya kuma datar da su wajen tsayuwa da ita shi ne karshen burinsu; Shi yasa ya zama mafi girman abin da aka roki Ubangiji (Allah) ta'ala akansa shi ne: NEMAN TAIMAKONSA KAN YARDARSA; Kuma shi ne abin da Annabi s a w ya koyar da shi wa Mu'azu (bn Jabal r a) ya ce:
 " يَا مُعَاذُ! واللهِ إِنِّي لأُحِبُّكَ؛ فَلا تَدَعْ أَنْ تَقُولَ فِي كُلِّ صَلاةٍ: اللهم أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ، وَشُكْرِكَ، وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ "
Ma'ana: " Ya Mu'azu! Wallahilalallai ni ina sonka; don haka; Kada ka bari fadin –bayan kowace salla-: Ya Allah ka taimake ni kan ambatonka, da gode maka, da ku yi maka mafi kyan bauta ".
Don haka; Mafi amfanin addu'a shi ne: Neman taimako kan abubuwan da Allah madaukaki ya yarda da su.

  WADANDA SU KE KISHIYANTAR WADANNAN KUMA SU NE; 'Yan kaso na biyu: Masu kawar da kai ga barin bautar Allah da neman taimakonsa; Su wadannan basu da bauta kuma basu da neman taimako, Kai! –in da ma- 'dayansu zai roki madaukaki, ya kuma nemi taimakonsa, To zai roke shi ne kan rabonsa da sha'awowinsa.
Shi kuma Allah s w t duk wadanda su ke cikin sammai da kassai suna rokonsa; Masoyansa da makiyansa duk suna rokonsa; Sai kuma ya ba wa wadannan, ya bawa wadannan.
Kuma mafi kiyuwan halittunsa a wajensa shi ne IBLIS; amma duk da haka; Allah ya amsa masa addu'arsa, ya kuma biya bukatarsa, ya jiyar da shi dadi da ita, Sai dai kuma yayin da bai zama taimako kan biyayya wa Allah ba, sai ya zama karin tabewarsa da nisansa.

To kuma haka abun ya ke ga duk mutumin da ya roki madaukaki, ya kuma nemi taimakonsa akan abin da ba mai taimakonsa ba ne kan biyayya wa Allah, Sai rokonsa ya zama mai kara njisantar da shi daga Allah.

  Don haka mai hankali ya yi tunanin wannan, Sa'an nan ya san cewa: Amsa addu'ar da Allah ya ke yi ga wassu masu rokon, Ba wai saboda karamarsu ne (matsayinsu ne) a wajensa ba.  Kai ai wani lokaci ma bawa ya kan roke shi wata bukata; Sai kuma ya biya masa ita, alhali a cikinta akwai halakarsa, (a irin wannan yanayin) hana bawan abin da ya roka shi ne kariyarsa da gyaransa. Kawai dai kiyayeyye shi ne wadda Allah ya kiyaye, Mutum kuma shi ya fi sanin kansa.
Shi kuma alamar wannan (abin da aka ambata a baya) Shi ne: Ka kan ga mutumin da Allah ya kare shi daga haka (abin da halakarsa ke cikinsa) alhali yana mai jahiltar hakikanin al'amarin; Idan ya ga (Allah) mai tsarki yana biyan bukatun wassunsa sai ya munana zatonsa da madaukaki, zuciyarsa ta cika da haka (munana zato ga Allah) alhali bai sani ba. Kuma (wata alamar haka) ita ce: Jin haushin abubuwan da aka kaddara, da kuma zarginsa –ta cikin zuciyarsa- a gare ta.

 Kuma hakika Allah madaukaki ya yaye wannan ma'anar iyaka yayewa (ya kuma yi bayaninsa dalla-dalla) a cikin fadinsa madaukaki:
ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ  ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ    ﮩ ﮪﮫ ﮰ [الفجر:15-١7].
( Amma mutum idan ubangijinsa ya jarrabe shi; sai ya karamta shi, ya kuma ni'imta shi, Sai ya ce: Ubangijina ya karrama ni *** Amma idan ya jarrabe shi; Sai ya kuntata masa arzikinsa Sai ya ce: Ubangijina ya walakanta ni *** A'a ha, (al'amarin ba haka ya ke ba!).

Ai; Ma'ana: Al'amarin ba haka ya ke ba; Saboda ba duk wadda na masa baiwa ba ne, na yi masa ni'ima, na kuma sakar masa ba ne, wai na karrama shi; sai dai na kan yi haka da nufin jarabawa daga waje na zuwa gare shi; don na ga shin zai gode min sai na masa baiwa fiye da yadda na ba shi, ko kuma zai kafirce min (ya butulce) sai na kwace daga gare shi, na kuma canza shi ya zuwa waninsa!

Haka kuma ba duk wadda na jarrabe shi ba ne; na kuntata masa arzikinsa; ta yadda na sanya (arzikin nasa) kan wani gwargwadon da bai fi bukatarsa ba, cewa hakan wai saboda kaskancinsa ne a wajena; Sai dai kawai (hakan) ya kan zamo jarabawa ne daga gare ni zuwa gare shi; don na ga shin zai yi hakuri ne; sai na bashi ninkin ba ninkin abin da ya kufce, ko kuma zai yi ta nuna fushi sai ya zamo rabonsa shi ne fushin?

 A dunkule; Allah madaukaki ya yi bayanin cewa lallai karramawa da wulakantawa ba sa rataya kan dukiya da kuma yalwar arziki, da kuntata shi; Saboda Allah mai tsarki yana yalwata wa kafiri, ba don matsayinsa ba (karamarsa a wajen Allah ba). Haka kuma ya kan kuntata (arziki) ga mumini ba wai don shi kaskantacce ne a wajensa ba. Kawai dai abin sani (Allah) mai tsarki ya kan karrama (wadda ya so) daga cikin bayinsa; ya kuma datar da shi zuwa ga SANINSA DA SONSA DA BAUTARSA TARE DA NEMAN TAIMAKONSA.

Don haka; Kololuwar tsira ta har abada na kasancewa ne cikin bautar allah da kuma neman taimakonsa akanta.


KASHI NA UKU: Su ne wadanda su ke da nau'in bauta ba tare da neman taimako (Allah) ba;
Wadannan nau'I biyu ne:

Na farko: Ma'abuta kaddara da su ke cewa (su ka kudure cewa): Lallai (Allah) mai tsarki ya gama aikata wa bawa duk abin da ya ke da iko na ludufi (maban banta), kuma ba wani taimako kan wani aiki da ya saura masa; saboda ya riga ya taimake shi ta hanyar halitta masa gabbai da kuma bashi lafiya a cikinsu, ya kuma nusar da shi hanyar (tsira), ya turo manzo, sa'an nan ya bashi damar yin aiki; don haka babu wani taimako da ke da iko kanta wadda (bawan) zai tambaye shi ita.

Wadannan an tabar da su, kuma an dogarar da su zuwa ga kayukansu, An kuma toshe musu kofar neman taimako da tauhidi; Ibnu abbas –Allah ya kara musu yarda- ya ce:
" الإيمان بالقدر نظام التوحيد؛ فمن آمَن بالله، وكذَّب بقدره نقض تكذيبُه توحيدَه ".
Ma'ana: " Imani da kaddara shi ne wani tsari ne (igiya) da ya rike tauhidi; Don haka duk wadda ya kadaita Allah, sa'an nan ya karyata kaddara to karyatawarsa ya warware tauhidinsa ".

  Nau'I na biyu:  Su ne wadanda su ke da ibada da da wuridin (zikrori ko karatun alqur'ani ko salla, ko duka), Sai dai kuma rabonsu na tawakkali (ga Allah) da neman taimakonsa yana da rauni; saboda zukatansu ba su yi yalwar da za su kulla sabbuba da kuma kaddara ba (shi ya sa su ke ga tun da su allah ya kaddara musu yi masa bauta to wannan abun ba shi da wassu sabbuba; wadda hakan sai ya kai su ya zuwa ga rashin neman taimakonsa da dogara da shi), sa'an nan su sabbuban idan aka tobe su daga abin da Allah ya kaddara (wajen rashin tasirinsu) kamar mamacin da ba shi da wani tasiri ne, kai kamar babu ne da bai taba samuwa ba, Shi kuma kaddaran kamar rai ne da ke motsa sabbuban, sa'an nan kuma ya rataya akan mai motsawa na farko (Allah).
Su wadannan mutanen basirarsu ba ta wuce ganin sababi ya zuwa ga mai sanya sababin ba (Allah), haka kuma bata wuce ganin abin da aka yi halitta da shi ba ya zuwa ga wadda ya yi halittan (wato sun kasa hada tsakanin sababi da kuma Allah da ke sa sababin da ya halitta ya yi tasiri; domin shi ya halicci sababi, kuma shi ke sa shi ya yi tasiri); Don haka; Sai rabunsu na neman agaji ya yi karanci.

  Wadannan mutanen su na da rabo na tasarrufi gwargwadon dan neman taimakon da su ka yi da kuma dogararsu (ga Allah), Suna kuma da rabo na rauni da tabarwa gwargwadon karancin neman taimakonsu da tawakkalinsu; saboda da bawa zai dogara ga Allah iyaka dogara akansa (dogara na hakika) wajen gusar da dutse (mai girma) daga gurbinsa da (Allah ya taimake shi) ya gusar da shi.

   Idan da za a ce: Menene hakikanin neman taimakon a aikace??

Sai mu ce: (Neman taimako) Shi ne in an fadi lafazin tawakkali ake nui da shi;  Shi kuma (neman taimako) wani hali ne a cikin zuci da ke haifuwa saboda sanin Allah madaukaki, da kuma (sanin) kadaituwarsa da yin halitta da al'amari da juya al'amari, da cutarwa da amfanarwa, haka kuma duk abin da ya so shi ya ke kasancewa abin da bai so ba kuma baya kasancewa; SAI WADANNAN ABUBUWAN SU WAJABTA DOGARA AKANSA, DA FAWWALA ABUBUWA ZUWA GARE SHI, TARE DA SAMUN AMINTUWA DA SHI.

SAI jinginan bawa zuwa gare shi madaukaki ya zama kamar jinginuwan 'da ne zuwa ga iyayensa kan abin da ya sako shi a gaba na abin da ya ke fatan samu (kaunar samu) ko kuma tsoro; da wani abin da aka hukunta zai dufafo shi na cutuwa zai dufafo shin to da ba zai fake ba sai zuwa gare su (ubansa da uwarsa); Idan bawa –tar da wannan dogaran- ya kasance daga cikin masu takawa sai kyakkyawar makoma, kuma abar yabo ta kasance masa; domin:
ﮚ ﮛ  ﮜ ﮝ ﮞ  ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﯚ  [الطلاق:2-٣].
( Duk wadda ya ji tsoron Allah; to zai sanya masa mafita *** Ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani, Duk wadda ya dogara ga Allah, Allah ya isar masa ).

  Kaso na hudu: Su ne wadanda su ke da neman taimako ba tare da bauta ba, Wannan kuma shi ne halin wadda ya shaida wa Allah da cutarwa da amfanarwa, amma kuma bai san abubuwan da (Allan) ya ke so kuma ya yarda da su ba; don haka sai ya dogara akansa a cikin rabonsa (na duniya), sai Allan kuma ya taimake shi ya bashi su.

Irin wannan mutum bashi da kyakkyawar makoma; kuma daidai ne abin da aka bashin dukiya ne ko kuma mulki ko matsayi a wajen halitta ko makamancin wannan; saboda abin da ya samun kawai shi ne rabonsa a duniyarsa da lahirarsa.

[SHARRUDAN KARBAN AYYUKA GUDA BIYU; IKHLASI TARE DA KOYI DA MANZO]
  Kuma ka sani lallai bawa baya kasancewa bawan Allah na hakika (da ake karbar aikinsa) sai da tabbatar da asaloli guda biyu:

 Na farkonsu: Bin manzon Allah s a w.
 Na biyu: Tace bauta (da yinta ga Allah shi kadai; ikhlasi).



[KASUWAN MUTANE KASHI HUDU DANGANE DA WANNAN]
  Mutane akan wadannan asaloli guda biyu sun kasu kashu hudu:

Na farko: Ma'abota ikhlasi (yi don Allah) da kuma bin Manzon Allah s a w: Wadannan aiyukansu da zancensu dukkansu suna yinsu ne don Allah, da hanawansu da bayarwansu, da sonsu da kinsu, dukkan wannan ya kan kasance ga Allah ne madaukaki, ba sa nufan wani sakamako ko godiya daga bayi. ('Yan wadannan kason) sun dau mutane kamar wadanda ke cikin kabari; basa mallakan cutarwa ko amfanarwa, haka (basa mallakan) kashewa, rayarwa, ko tayarwa; saboda ba wadda ke mu'amalantar wani daga cikin halittu (ya nema daga wajensa; yana mai barin Allah) sai saboda jahiltarsa ga Allah, da kuma jahiltarsa ga halitta.

  Shi kuma ikhlasi shi ne: Aikin da Allah baya karba wa mai aiki aikinsa da ya dace da sunna (Annabi s a w) ba tare da shi ba (ikhlasi), kuma shi ne allah ya lazimta wa bayinsa aikata shi har zuwa mutuwa, (Allah) madaukaki yana cewa:
ﭟ ﭠ ﭡ  ﭢﭣ ﭤ     ﭥ     ﭦ  ﭧ  [الملك: ٢  ].
(Domin -Allah- ya jarrabe ku wanene daga cikinku ya fi kyan aiki).
Ya kuma ce:
ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ  ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ  [الكهف: ٧  ].
(Lallai mun sanya abin da ke kan kasa ya zama ado a gare ta, domin mu jarrae ku wanene daga cikinku zai fi kyan aiki ).

KUMA MAFI KYAN AIKI SHI NE: Wadda ya fi ikhlasi, kuma ya fi dacewa da zama sawaba (daidai da koyarwar manzon Allah s a w; don haka;

Aiki tacecce (mai ikhlasi) shi ne: wadda ya aka yi shi don Allah.

Shi kuma wadda ya dace shi ne: Ya zama daidai da sunnar manzon Allah s a w.

Kuma shi wannan aiki na kwaren shi ne aka ambata a cikin fadinsa madaukaki: 
ﰐ ﰑ          ﰒ  ﰓ ﰔ ﰕ  ﰖ ﰗ ﰝ  [الكهف: ١١٠  ].
(Duk wadda ke fatan haduwa da ubangijinsa (lami lafiya) to ya yi aiki aiki na kwarai).

Kuma shi ne aiki mai kyau cikin fadin (Allah) madaukaki:
ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮢ  [النساء: ١٢٥].
(Babu wadda ya fi kyan addini fiye da wadda ya mika fiskarsa ga Allah (tare da ikhlasi), alhali yana mai kyautata aiki ).

 Kuma shi ne Annabi s a w ya yi umurni da shi a cikin fadinsa:
" كلّ عَمِلٍ لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ"
(Kowani aikin da babu umurninmu akansa to shi abun mayarwa ne).
Kuma dukkan aikin da aka yi shi ba koyi (da Manzon Allah s a w) to ba zai kara komai wa mai aikata shi ba sai nisantarwa daga Allah, saboda Allah madaukaki ana bauta masa ne da umurninsa, ba da son zuciya ba ko ra'ayoyi ba.


 Nau'I na biyu: Su ne wadanda ba su da ikhlasi kuma ba su da koyi da (Annabi s a w); Wadannan su ne mafi sharrin halittu, Su ne masu sa rigar ayyukan alkhari, suna riya da su awa mutane.

Wannan nau'in su kan yi yawa cikin wadanda su ka kauce wa madaidaiciyar hanya na daga masu nasabta kansu zuwa ga fiqhu da ilimi da talauci da ibada; saboda kasancewar su kan aikata bidi'o'I da bata da riya da sum'a (yin ibada don mutane su ji da kunnuwansu, ba don Allah ba), sa'an nan su na son a rika yaba musu da abin da ba su aikata ba.

Kuma akan irin wadannan nau'oin nen fadin madaukaki ya sauka:
ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ   ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ  [آل عمران: ١٨٨  ].
(Kada ka yi zaton wadanda su ke farin ciki kan abin da su ka bayar, kuma su ke son a yabe su da abin da ba su aikata ba, kada ka yi zaton za su tsira daga azaba, kuma suna azaba mai radadi).


Nau'I na uku: Su ne wadda ya zama yana ikhlasi cikin ayyukansa; sai dai kuma (ayyukan) sun kasance ba tare da bin umurnin (ma'aiki s a w) ba; misalinsu kamar JAHILAN MASU YAWAN BAUTA, DA KUMA MASU NASABTA KANSU ZUWA GA GUDUN DUNIYA DA TALAUCI, DA MA DUK WADDA YA BAUTA WA ALLAH BA AKAN YADDA ALLAH YA NUFA BA.

Saha'anin ba kawai cikin a bauta wa Allah ba ne kadai, A'a! a bauta masa ne akan yadda Allan ya nufa (shari'arsa).

Shi yasa; Daga cikin wadannan nau'in akwai wadda ke zama a wajen da ya ke khalwa (wurin da ya kebe wa kansa don bauta) yana mai barin zuwa sallar juma'a, kuma yana ga hakan wai bauta ne, kuma kusantan Allah ne. Haka kuma (irin wadannan) suna ganin sadar da azumin dare da yini ma karin kusanci ne ga Allah. Haka kuma yin azumin ranar idi ma wai karin kusanci ne (bayan shari'a ta hana). Da makamantan haka.


Nau'I na hudu: Wadanda aiyukansu su ka kasance kan bin umurni (shari'ar manzon Allah s a w), sai dai kuma yana yin su ne ba don allah madaukaki ba; misalin wannan shi ne; kamar da'ar masu yin riya, da kuma kamar mutumin da ya yi yaki da nufin riya da sum'a (ya yi suna, a ji shi, da a ganshi), da me yi don kabilanci, ko a ce shi gwarzo ne, ko ya ke yi don ganima. Ko wadda ya ke yin hajji don a ce ( shi mai hajji ne, Alhaji; a niyyarsa ya yi don haka, ba don Allah ba). Haka wadda ya ke yi karatun domin a ce (shi makaranci ne, ba don Allah ba). Da me neman ilimi ko mai koyar da shi don a fada (ba don Allah ba). Wadannan duk ayyuka ne na gari, sai dai ba za a karbe su ba; Allah yan cewa:

ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮩ  [البينة: ٥].
(Ba a umurce su ba sai da su bauta wa Allah suna masu tsarkake masa addini, karkatattu ga barin shirka zuwa ga tauhidi).

Don haka ba a umurci mutane ba sai da bauta wa Allah akan bin manzo da kuma tsarkake niyya ga Allah shi kadai a cikinsu. Wadda kuma ya tsayu akan haka to shi ne ma'abocin:
ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ  [الفاتحة: ٥].
(Kai kadai mu ke bauta wa, kuma a gare ka –kai kadai- mu ke neman taimako).
************


[IBADAR DA YA KAMATA MUTUM YA FI FIFITAWA; SABODA FIFIKON AMFANINTA DA FALALARTA]
    Sa'annan su ma'abota:
ﭢ ﭣ    .
(Kai kadai mu ke bauta wa), -dangane da mafificin bauta, kuma mafi amfaninta, wacce kuma ta fi cancantar a gabatar da ita (a yawaita yi), da kuma kebe ta- dangane da haka su na da hanyoyi hudu, kuma su sinfi hudu ne::

Kaso na farko:  A wajensu Ibadar da ta fi amfani kuma ta fi fifiko ita ce: Wacce ta fi wahala ga rayuka, ta kuma fi tsanani.

Su ka ce: (abin da ya fi wahala) shi ne mafi nisa ga barin son zuciyar bawa, wadda (gudun son zuciya kuwa shi ne): hakikanin nuna bauta, shi ma lada yana nan gwargwadon wahala.

(Dalilinsu): Su ka ruwaito hadisin da ba shi da asali cewa:

" أفضل الأعمال أحمزها "
Wai mafifcin ayyuka shi ne wadda ya fi tsananin wahala ''.

  Wadannan mutanen su ne ma'abutan wahalar da kai, da zaluntar rayuka, su ka ce: AI ABIN SANI KAWAI, ZUKATA NA SAMUN ISTIKAMA (TSAYUWA KAN TAFARKIN ALLAH) NE DA HAKA, saboda an 'dabi'antar da rai kan kasala, da kaskanci (wato kin aikata abin da zai daukaka rai, saboda gudun wahala), da kuma tabbatuwa zuwa ga neman hutu; don haka rai ba za ta daidaita ba sai da aikata abubuwa masu wahalwalu, da kuma aikata abubuwa masu tsanani.


Kaso na biyu: Su ka ce: mafificin ibadu kuma wadanda su ka fi amfani shi ne: Tobuwa da kuma gudun duniya, da kuma karanta wa daga gare ta gwargwadon iko (iya iyawa), da kuma watsar da himmatuwa da ita, tare da barin mai da hankali kan duk abubuwanta.

Sa'an nan su wadannan din kashi biyu ne:

Gama garinsu; Sun yi zaton cewa hakan wani abu ne da ake nufansa don kansa; don haka sai su ka zage dantse zuwa gare shi, su ka yi ta yin aiki tukuru don shi, su ka kuma ce: Ai hakan (gudun duniyan) ya fi falala fiye da darajar neman ilimi da kuma ibada, sa'an nan su a ganinsu: gudun wannan duniyar shi ne manufar kowace bauta.

Amma kebantattunsu kuma; Su suna ganin zuhudu abu ne da aka nufe shi saboda waninsa; kuma lallai abin da ake nufi da shi shi ne: Killatuwan zuci (lazimtarta) Allah madaukaki, da kuma dulmuyuwa cikin sonsa, da mayar da al'amari zuwa gare shi, da kuma dogara akansa, da shagaltuwa da abubuwan da su ke yardar da shi; don haka sai su ke ganin cewa: MAFIFICIN IBADU SHI NE DAWWAMUWAR AMBATONSA A ZUCI DA HARSHE.

Sa'an nan wadannan sun kasu kashi biyu:

Masana (da ake musu lakabi da: AL'ARIFUNA) daga cikinsu: Su kan kasance idan umurni da hani ya zo, to sai su yi gaggawa zuwa gare shi; ko da kuwa zai rabe su da taruwar zuciyarsu.

Karkatattun kuma daga cikinsu sai su ce: Abin da ake nema daga zuciya shi ne; haduwarsa; don haka idan abin da zai raba shi da wannan haduwar zuciyar ta sa ya zo masa daga Allah (kaman karantarwa, raka gawa, ko wani umurni alhali yana cikin khalwarsa ya gama hada zuciyarsa gu guda) to ba zai juya ya zuwa ga wannan umurnin ba; har ma cewa su ke yi:

يُطالَبُ بالأوراد مَن هو غافلٌ

فكيف بقلبٍ كلُّ أوقاته وردُ
 Ma'ana: " Rafkanenne shi ake nema da ya yi wurudi!
To kuma ta yaya za a nemi zuciyar da dukkan lokutanta wurudi ta ke yi?

Sa'an nan su wadannaan din ma sun kasu kashi biyu:

Daga cikinsu akwai wadda ke barin wajibai da farillai wai saboda yana cikin yanayin da ya hada zuciyarsa.

Daga cikinsu kuma akwai wadda ke tsayuwa da su (wajibai da farillu) amma sai ya bar sunnoni da nafiloli, da neman ilimi mai amfani wai saboda hada zuciyarsa.

Gaskiyan al'amari kuma shi ne; lallai shi hada zuciyan rabon zuci ne, yayin da amsa wa mai kira zuwa ga Allah kuma rabon Ubangiji ne; don haka duk wadda ya fifita hakkinsa akan hakkin Ubangijinsa; to ba komai ba ne a cikin bauta!


 Kaso na uku: Su wadannan su na ganin cewa mafificin bauta shi ne wadda a cikinsa akwai amfanarwa da ke tsallake wadda ya yi bautar ya zuwa ga waninsa; don haka su ke ganin irin wannan nau'in bautan ya fi matsayi akan wadda ke takaituwa kan wadda ya aikata bautan; Sai su ke ganin cewa: Hidima wa talakawa, da kuma shagaltuwa da maslahohin mutane, tare da biya musu bukatunsu, da taimakonsu da matsayi, da dukiya, da kuma amfanarwa shi ya fi; saboda fadinsa s a w:
"الْخَلْقُ عِيَالُ اللَّهِ، فَأَحَبُّهم إِلَى اللَّهِ أَنْفَعُهُمْ لِعِيَالِهِ "
(Halittu iyalai ne na Allah; wadda ya fi su soyuwa zuwa ga Allah shi ne wadda ya fi amfanar da iyalensa).

Su ka ce: Shi aikin mai bauta yana takaita akansa, yayin da aikin mai yawan amfanar da mutane kuma ya ke naso ya zuwa waninsa, to ta yaya za a kwatanta wannan da wancan? Kai shi fa ya sa falalan malami akan mai bauta ya ke kasancewa kamar falalan wata ne a daren haske (13-15) akan sauran taurari,
Kuma ga shi Annabi s a w ya ce wa Aliyu:
" لأَنْ يَهْدِيَ اللَّهُ بِكَ رَجُلا وَاحِدًا خَيْرٌ لَكَ مِنْ حُمْرِ النَّعَمِ "
(Ai! Allah ya shiryi mutum daya da kai (ta sababinka) ya fi maka alkhairi fiye da jajayen dabbobi ni'ima (rakuma). Ya kuma ce:
" مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنْ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ غير أنْ  يَنْقُص  مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا "
(Wadda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, ya kasance yana da kwatankwacin ladan wadda ya bi shi, ba tare da an tauye wani abu ba daga ladansu). Ya kuma ce:
 " إِنَّ اللَّهَ وَمَلائِكَتَهُ لَيُصَلُّونَ عَلَى مُعَلِّمِي الْخَيْرَ "
(Lallai Allah da Mala'iku suna addu'a ga masu koyar (da mutane) alkhairi. Ya kuma cewa:
"إِنَّ العالم لَيَسْتَغْفِرُ مَنْ فِي السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ حَتَّى الْحِيتَانُ فِي الْبحر، والنَّمْلَةَ فِي جُحْرِهَا"
(Lallai malami halittun da su ke cikin sammai da kassai suna nema masa gafara, har kifaye a cikin teku, har kuma tururuwa a cikin raminta).

Sua ka ce: Shi ma'abucin bauta idan ya mutu aikinsa ya yanke (da mutuwarsa), yayin da ma'abocin amfanarwa aikinsa ba zai yanke ba, matukar amfanarwan da ya zama sababin samuwarsa yana nan.

Kuma suma annabawa –yabon Allah da tsiransa su kara tabbata a gare su- abin sani kawai an turo su ne da kyautatawa wa halitta, da shiryad da su, da kuma amfanar da su a rayuwarsu ta duniya da makomansu, ba a turo su da shiga khalwa ba da kuma yanke khulda da mutane (kebewa gefe da bauta tare da nisantar cikin al'umma).

Shi ya sa ma Annabi s a w ya yi inkari ga wadnnan mutanen da su ka yi niyyar yanke khulda da mutane, tare da kebewa gefe da bauta.

Su ka kuma ce: (yana daga cikin abubuwan da amfaninsu ya kan zarta wadda ya tsayu da su ya wuce don ya yi naso ga waninsa): Neman ilimi da karantarwa. Da makamantan wadannan al'amura masu falaloli.


Kaso na hudu:  Mafificin ibada shi ne: AIKI DON NEMAN YARDAN UBANGIJI MAI TSARKI, TARE DA SHAGALTAR DA (CIKA) KOWANE LOKACI DA ABIN DA SHI NE AIKIN WANNAN LOKACIN KUMA SHI LOKACIN KE HUKUNTA (SAMAR DA SHI);
Don haka; Mafificin bauta a lokacin jihadi shi ne: jihadin; koda kuwa al'amarin zai kai ga barin wurudi na sallan (tsayuwar) dare, da kuma barin azumin yini, kai! Koda zai kai ga barin cika sallar falilla –a yi ta ba kamar a halin aminci da rashin yaki ba!

Abin da kuma ya fi a lokacin da bako ya halarto shi ne: tsayuwa wajen bada hakkinsa, da kuma shagaltuwa da shi.

Abin da ya fi kuma a lokutan sahur shi ne: shagaltuwa da salla, qur'ani, zikiri da addu'a.

Abin kuma da ya fi a lokacin kiran salla: Shi ne: Barin barin abin da mutum ke cikinsa na wurododi, da shagaltuwa da amsa wa mai kiran salla.

Amma a lokutan salloli biyar kuma abin da ya fi shi ne: Kokari da aiki tsayin daka wajen a ga an aikata su a mafificin (kammalellen) fiska, tare kuma da yin gaggawa zuwa gare su a farkon lokaci, da fita zuwa masallaci; koda kuwa ya yi nisa.

A lokacin lalurar wani mabukaci (shi kuma abin da ya fi a wannan lokacin shi ne): Sauri wajen taimaka masa da matsayi, da dukiya, da kuma jiki.

Abin da ya fi a hali na tafiya shi ne: Taimaka wa mabukaci, da abokan tafiya, tare da fifita hakan akan wurudodi da kebewa.

Abin da ya fi a lokacin karatun alqur'ani shi ne: tara zuciya, da himmatuwa kan tadabburinsa (kai kawo da zuci da nufin fahimtar abin da ake karantawa), tare da yin azama kan zartar da umurninsa, (a tara zuciya akan haka) fiye da tara zuciyar mutumin da littafi (wasika) ya zo masa daga wani sarki.

Abin da kuma ya fi a lokacin tsayuwar arfa shi ne: Yin kokari wajen kan-kan-da-kai, da addu'a, da zikiri.

Shi kuma abin da ya fi a kwanaki goman (10) zul hijja shi ne: Yawaita bauta, musamman ma kabbarori da hailaloli da godiya (wa Allah), yin haka kuma ya fi falala fiye da jihadin da wajabcinsa bai aiyana ba akan mutum.

Abin kuma da ya fi a goman (10) karshen ramadan shi ne: Lazimtar masallatai, da kebewa a cikinsu, tare da I'itikafi, da kuma kawar da kai ga barin khuldar mutane da shagaltuwa da su, Yin haka ya fi falala har akan fiskantarsu don karantar da su ilimi, da kuma ba su karatun alqur'ani a wajen yawa yawan maluma.

Abin da ya fi kuma a lokacin rashi lafiyar dan uwanka musulmi ko rasuwarsa shi ne: Ziyartarsa, da halartar sallarsa tare da raka shi, da gabatar da hakan akan kebewansa da hada zuciyarsa gu guda.

Abin da ya fi kuma a lokacin da wassu bala'I su ka sauka (maka), da kuma cutarwan mutane a gare ka shi ne: Yin abin da Allah ya wajabta na hakuri tare kuma da ci gaba da khulda da su; saboda muminin da ke cakuduwa da mutane kuma ya ke hakuri kan cutarwansu shi ya fi falala akan muminin da baya khulda da mutane, kuma baya hakuri kan cutarwansu.
Kuma yin khulda da su cikin alkhairi shi ya fi alkhairi akan kaurace musu akan haka. Kwaurace musu kuma cikin sharri shi ya fi fiye da khulda da su a cikinsa;
Amma idan mutum ya san cewa idan ya yi khulda da su zai gusar da shi, ko ya karanta shi (sharrin) to a irin wannan halin yin khulda su din yafi alkhairi fiye da kaurace musun.


Su wadannan nau'in su ne ma'abota sakekkiyar bauta (da ake kiranta: ATTA'ABBUDUL MUDLAK). Su kuma nau'uka (uku) da su ke kafinsu su ne  ma'abota nau'in bauta kayyadedde (ATTA'ABBUDUL MUKAYYAD); don haka; dul lokacin da 'dayansu ya fita daga reshen da rataya da shi na bauta, sa'an nan ya rabu da shi (in mai sallan dare ne, ya zama bai yi ba, ko sadaka, ya zama bai samu ikon mikawa ba, haka alqur'ani wani uzuri ya hana shi karanta abin da ya saba karantawa d. sauransu) sai ya ga kansa cewa ya samu tawaya, ya kuma sauka daga ibadarsa; saboda shi yana bauta wa Allah ne ta fiska daya. Yayin da ma'abota sakekkiyar bauta ('yan nau'in farko) basu da wta manufa akan wata ibada a karan-kanta; da su ke fifita akan watanta, Kawai dai burinsu shi ne: BIBIYAN ABUBUWAN DA SU KE YARDAR DA ALLAH MADAUKAKI.; Don haka;

In har ka ga maluma sai ka ganshi tare da su, haka ya ke cikin masu ambato Allah (zikiri), da masu sadaka, da wadnda su ke kokarin tar zuciyarsu da lazimtar da ita Allah.
Yin haka kuwa shi ne: gamemmen abin da zuciyar mai tafiya zuwa ga Allah ta kowane hanya ke bukata, mai kuma tafiya fatauci zuwa gare shi tare da kungiyar kowani fatake (masu zikiri ne, masu sadaka ne, maluma masu nusar da al'umma ne d. sauransu).
A nan zai yi kyau ka halarto hadisin Abubakar Assidiq –r . a- tare da fadin Annabi s a w a gaba gare shi:
" هلْ مِنْكُمْ أحدٌ أَطْعَمَ الْيَوْمَ مِسْكِينًا؟ " قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. قَالَ: " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ أَصْبَحَ الْيَوْمَ صَائِمًا؟ " قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ عَادَ الْيَوْمَ مَرِيضًا؟ " قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ تَبِعَ الْيَوْمَ جَنَازَةً؟ " قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ r: " مَا اجْتَمَعْنَ فِي امْرِئٍ إِلا دَخَلَ الْجَنَّةَ "
   (Shin daga cikinku akwai wadda ya ciyar da miskini a yau? Sai Abubakar ya ce: Ee! Ni na yi. Sai ya ce: Shin a cikinku akwai wadda ya wayi gari yana mai azumi? Sai Abubakar ya ce: Ee! Ni ina yi. Sai ya ce: Shin a cikinku akwai wadda ya ziyarci maras lafiya a yau? Sai Abubakar ya ce: Ee! Ni na yi. Sai ya ce: Shin a cikinku akwai wadda ya raka gawa a yau? Sai abubakar ya ce: Ee! Ni na raka. Sai Manzon Allah s a w ya ce: Wadannan abubuwan ba zu taba haduwa ga mutum ba face ya shiga aljanna)([5]).

Kuma wannan hadisin an ruwaito shi daga hanyar Abdulganiy bn abiy Akiili, ya ce: Yagnam bn Salim ya bamu labari, daga Anas bn Malik –Allah ya kara yarda da shi- ya ce:

« كان رسول الله r جالسًا في جماعة مِن أصحابه فقال: مَن صام اليوم؟ فقال أبو بكر: أنا. قال: مَن تصدّق اليوم؟ قال أبو بكر: أنا. قال: مَن عاد اليوم مريضًا؟ قال أبو بكر: أنا. قال: فمَن شهد اليوم جنازة؟ قا أبو بكر: أنا. قال: وجبت لك –يعني: الجنة- ».
(Manzon Allah s a w ya kasance a cikin masallaci a zaune cikin jama'ar sahabbansa; Sai y ace: Wenene ya yi azumi yau? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. Sai y ace: Wanene kuma ya yi sadaka a yau? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. sai ya ce: Way a ziyarci maras lafiya yau? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. Sai ya ce: Wanene kuma ya halarci sallan gawa? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. Sai ya ce:  Shiganta ya wajaba maka –yana nufin aljanna-.

Shi yagnam bn Salim duk da cewa akwai Magana akansa sai dai Salamatu bn Wardan ya masa mutaba'a (wato ya ruwaito irin hadisinsa).
Kuma hadisin yana da asali ingancecce na daga hadisin: Malik daga Muhammadu bn Shihabin, daga Humaid bn Abdirrahman bn Auf, daga Abu Hurairata –Allah ya kara masa yarda- Lallai Manzon Allah s a w ya ce:
" مَنْ أَنْفَقَ زَوْجَيْنِ فِي سَبِيلِ اللَّهِ نُودِيَ فِي الْجَنَّةِ: يَا عَبْدَ اللَّهِ! هَذَا خَيْرٌ؛ فَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الصَّلاةِ نُودِيَ مِنْ بَابِ الصَّلاةِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الْجِهَادِ نُودِيَ مِنْ بَابِ الْجِهَادِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الصَّدَقَةِ دُعِيَ مِنْ بَابِ الصَّدَقَةِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الصِّيَامِ دُعِيَ مِنْ بَابِ الرَّيَّانِ. فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ t: بِأَبِي –أَنْتَ- وَأُمِّي! يَا رَسُولَ اللَّهِ! مَا عَلَى مَنْ يدعَى مِنْ هذه الأَبْوَابِ مِنْ ضَرُورَةٍ، فَهَلْ يُدْعَى أَحَدٌ مِنْ تِلْكَ الأَبْوَابِ كُلِّهَا؟ قَالَ: نَعَمْ؛ وَأَرْجُو أَنْ تَكُونَ مِنْهُمْ ".  
(Duk wadda ya ciyar da abu kala biyu a tafarkin Allah to za masa kira da babban murya daga aljanna (ta kofofin aljanna), an ace masa: Ya kai bawan Allah! Wannan shi ya fi alkhairi! Duk wadda ya kasance daga cikin ma'abota salla sai a kira shi daga kofar salla, Wadda kuma ya kasance daga ma'abota jihadi sai a kira shi ta kofar jihadi. Wadda kuma ya kasance daga ma'abota sadaka sai a kira shi ta kofar sadaka. Wadda kuma ya zamo daga ma'abota azumi sai a kira shi ta kofar Rayyan (kofar kasha kishi).
Sai Abubakar –Allah ya kara masa yarda- ya ce: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai wata cut ace ga wadda aka kira shi ta wadannan kofofin; Kuma shin za a kira wani kuwa ta dukkan wadannan kofofin? Sai ya ce: Ee! Ina ma fatan ka zama daga cikinsu.

Haka nan Yahya bn Yahya, da Ma'an bn Isah, da Abdullahi bnul Mubarak su ka ruwaito shi daga Malik da sanadinsa zuwa ga Annabi s a w. Amma Yahya bn Bukair da Abdullahi bn Yusuf sun ruwaito shi daga Malik daga Ibnu Shihab, daga Humaid a matsayin mursal (wato: hadisin da tabi'I ya ce: Manzon Allah s a w ya ce). A wajen Alka'anabi kuma hadisin ba MURSALI BA NE KUMA BA MUSNADI BA NE.

Ma'anan:

 " مَنْ أَنْفَقَ زَوْجَيْنِ ... "
Shi ne wadda ya ciyar da abu biyu daga nau'I daya; misalin dirhami biyu, ko dinari biyu, ko doki biyu, ko riguna biyu. Haka ma wadda ya yi salla raka'a biyu, ko kuma ya yi tafiya taku biyu a tafarkin Allah madaukaki, ko kuma ya yi azumin yini biyu. Da makamancin haka.
Allah shi ne mafi sani; Amma dai la'alla abin da (Annabi s a w) ya nufa da wannan shi ne: Mafi karancin maimaita abu, da kuma mafi karancin fiskokin dawwama akan aiki daga cikin ayyukan biyayya; saboda biyu shi ne mafi karancin jam'i.

(Su 'yan nau'I na hudun nan) kamar rowan sama su ke; duk in day a zuba to zai yi amfani (haka su ma al'amarin ya ke); saboda a wajen mu'amalantar Allah suna mu'amalantarsa ne ba tare da waiwaya ya zuwa ga halitta ba, suna kuma manta da kansu in sun zo mu'amalantar halittu (sai su fifita su har akan kansu); Idan ya kasance tare da Allah to sai ya yi uzula wa dukkan halittu tare da kasancewarsa yana cikinsu (ba wai ya yi hijira ban e ya koma jeji ko …), sai ya kyale halittu, Idan kuma ya kasance tare da halittunsa to sai ya tobe kansa daga cikinsu, ya kyale ran nasa (ya ki kula da ita), KAI IRIN WANNAN BAKO NE A CIKIN MUTANE! Kuma ka yi mamakin tsananin kadaitakarsa a cikinsu! Sa'an nan ka yi mamakin debe kewarsa da Allah da farin cikinsa da shi, da nitsuwarsa da kwanciyar hankalinsa da Allah!

[ Ya Allah ka sa mu cikin irin wannan kason don zatinka da sifofinka madaukaka].

********
  
[KARKASUWAN MUTANE DANGANE DA AMFANIN BAUTA DA HIKIMARTA DA MANUFARTA SUN KASU KASHI HUDU]
   Kuma ka sani mutane ne dangane da amfanin bauta da hikimar da ta sa aka shar'anta ta, da kuma manufar da ta ke tabbatarwa suna da hanyoyi hudu; don haka sun kasu kashi hudu:

Kashi na farko: Su ne wadanda su ke kore hikimomi da sababi; wadanda su ke mayar da umurni zuwa ga tsagoron ganin dama (misali; su a wajensu da Allah ya yi umrni a yi salla, azumi, zakka, babu wassu sabbuba da su ka sa ya shar'anta wadannan bautan, sai kawai haka ya ga dama, haka kuma day a hana shan giya, zina, sata, nan ma ba wassu sabbuba da su ka hukunta hanawan, sai haka ya ga dama); don haka –a wajen wadannan- tsayuwa da bin umurni da hani bas u da wassu sababi sai kawai don an yi umurni; ba tare da akwai wani sababi na tsira a cikin rayuwar duniya ko lahira ba, ko wani sababin tsira; kai dai mutum yak an tsayu da bin umurni ne saboda an yi umurni, da kuma tsantsan ganin daman (Allah),

kamar yadda –DANGANE DA HALITTA MA- su ka ce; Allah bai halicci halitta ba don wata manufa, ko saboda wani sababin day a nufa da su, ko kuma wata hikima wacce za ta dawo ya zuwa gare shi daga gare su. (Su ka sa ke cewa): Babu wassu sabbuba a cikin halittu da sun e su ka hukunta halittarsu, kamar yadda (a fadinsu) babu sababin kuna a cikin wuta, haka ruwa ba shi da karfi na dulmuyarwa (ga wadda ya shige shi alhali bai iya gudanar da shi ba) ko sanyintarwa.

To haka ma umurni ya ke a wajensu ba banbanci, kuma (a wajensu) -a hakikanin al'amari- babu banbanci tsakanin abin da aka yi umurni da shi, da kuma wadda aka hana (wato kamar zina da aure); kawai dai! Ganin damansa ne (Allah) ta hukunta ya yi umurni da wannan, ya kuma hana wannan, ba tare da an samu wata sifa da ta tsayu da abin da aka yi umurni da shi ba, da ta ke hukunta kyansa, haka kuma wata sifa da tsaya tare da abin da aka hana wacce ta ke hukunta muninsa.

(WADANNAN MUTANEN SU AKE KIRA JABARIYYA).

Shi dai wannan asalin da su ka kafa yana da (munanan) abubuwan da su ke biyo bayansa, da kuma ressa da yawa. (Babu dammar ambatonsu a nan).

 Su wadannan; mafi yawansu basa samun zakin ibada ko dadinta, haka kuma bas a ni'imtuwa da ita; shi yasa ma su ke kiran: salla, azumi, zakka, hajji, tauhidi, da ikhlasi, da sauransu: (su ke kiransu): Abubuwan da aka kallafa wa (bayi); DA KUWA MAI RIYA SOYAYYAR WANI SARKI DAGA CIKIN SARAKUNA KO WANINSA ZAI KIRA ABIN DA YA UMURCE SHI DA SU (NA AYYUKA); KALLAFE – KALLAFE TO DA BAI ZAMA MASOYINSA BA! (Sai Allah ne za a kira abin da ya umurci masoyinsa, wadda sa'adarsa ta duniya da lahira na cikin abin day a umurce shin ne kawai, za a kira wadannan umurni: abubuwan da aka kallafa wa mutum!? ).

Wadda wannan maganan ta fara fitowa daga wajensa shi ne: ALJA'ADU BN DIRHAM (shugaban masu kore wa Allah sifofin day a tabbatar wa kansa).


Kashi na biyu: Masu kore kaddara (DA AKE KIRANSU: ALKADARIYYATU ANNUFATU); Wadanda su ke tabbatar da nau'I na hikima da sababi (amma ba dukkansa ko kuma ta kowace fiska ba), amma (wadda su ke tabbatarwan) ba tsayuwa da Ubangiji, kuma bay a komawa zuwa gare shi, kawai dai (a wajensu) yana komawa ne ga tsantsan maslahar bawa da amfaninsa.
Kuma a wajensu su wadannan ibadun an shar'anta sun e don su zama kudi da bawa ya bayar don sayan abin da bayi ke samu na lada da ni'imomi, wato su (ibadun) suna nan kamar ace: neman cika hakki ne da wadda ya bada kwadago ke yi daga wadda ke masa aiki (kafin kuma ya bada sakamako da ke ta bangarensa).

Su ka ce: Shi ya sa Allah mai tsarki ya ke sanya su a matsayin canji (wato kamar an karbi aikinku an mu ku canji da aljanna, kamar yadda dan kasuwa ke karban kudinka sai ya baka bukatar ka); kamar fadinsa:
ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ               ﰉ ﰊ  [الأعراف: ٤٣].
(Sai aka musu kolo cewa ga can aljanna –ku shiga- an gadar mu ku da ita sakamakon abin da ku ka kasance ku ke aikatawa)
ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ            ﭩ ﭪ  [النمل: ٩٠].
(Ba a saka mu ku sakayya sai da abin da ku ka kasance ku ke aikatawa).
ﯝ ﯞ ﯟ   ﯠ ﯡ ﯢ  [النحل: ٣٢].
(Ku shiga aljanna saboda abin da ku ka kasance ku ke aikatawa).
ﰒ ﰓ ﰔ ﰕ ﰖ ﰗ ﰘ ﰙ  [الزمر: ١٠].  
(abun sani kawai; ana cika wa masu hakuri ladansu ne ba tare da lissafi ba).

Ya kuma zo cikin sahihu (muslim):
" إِنَّمَا هِيَ أَعْمَالُكُمْ أُحْصِيهَا عليكُمْ ثُمَّ أُوَفِّيكُمْ إِيَّاهَا "
(-Ya ku bayi na!- Ku sani lallai wannan aikin kun e; na ke kiyaye mu ku, sa'an nan sai in cika mu ku (sakayyansa),

Su ka ce: kuma ga shi (Allah) ya kira su da: sakayya, lada,; saboda wani abu ne da ke dawowa ya zuwa ga mai aikin na daga aikinsa.

Abin da ke nuni kuma kan haka (wato, canji) shi ne: aunawa da ake yi; saboda ba don ratayar lada da ayyukan ba a matsayin canjinsu to da awon ba shi da ma'ana.
(A nan shubuhohinsu su ka kare, saura mayar da martini tare da bayanin inganceccen ma'anonin ayoyi da hadisan)


Wadannan bangarorin guda biyu suna karo da juna;
Su dai Jabariyya ba su sanya wa aiyuka ba wani kulluwa da sakayya kwata-kwata; shi ya sa (a kwakwalensu, da akidarsu) su ka halatta Allah ya yi azaba ga mutumin da ya karar da rayuwansa cikin da'a (wa Allah), ya kuma ni'imtar da wadda ya karar da rayuwarsa cikin sabonsa; domin dukkansu (wadda ya mutu a kan da'a da sabo) dangane da shi Allah wadannan daya ne (haka su ka fada); saboda kowannensu na komawa ne zuwa ga gundarin haka yaga dama!

Su kuma kadariyya sun wajabta ma Allah madaukaki kula da maslahohi, sa'an nan su ka sanya hakan - gaba dayansa- ya zama na rataye ne da tsuran aiyuka, kuma wai isar sakamako zuwa ga bawa ba tare da aikinsa ba; cikin haka akwai nakasawa; wai saboda: akwai yiwuwar a masa gorin sadakar da aka masa saboda bai bada wani aiki ba a madadin (wannan ladan); don haka; Sai su ka sanya bada lada da Allah mai tsarki ke yi wa bawansa kamar sadaka ne da bawa ke yi wa wani bawan (ta yadda –in dai- mai bada sadakar bai ji tsoron Allah ba zai iya yin gori ga wadda ya karba, to su ka ce; in ba ka yi aikin lada ba sai aka baka to ai akwai yiwuwar a maka gori; subhanallah). Kuma (su ka ce) bayar da abin da Allah ke bayarwa bawansa na ladan aikinsa ya fi soyuwa ga bawan fiye da abin da zai ba shi haka kawai a matsayin falala daga gare shi ba tare da wani aiki ba. Kuma kwata-kwata ba su sanya wa aiyuka ba wani tasiri cikin sakamako.

Duka wadannan kungiyoyin guda biyu sun bace ga barin madaidaiciyar hanya, wadda shi ne:

Su dai ayyuka sabbuba ne da su ke kaiwa ya zuwa ga sakayya; su ko na kwarai daga cikin ayyuka suna daga cikin datarwan Allah madaukaki (ga bawansa) da falalarsa, amma (ayyuka) ba cuf cuf (dai dai da dai dai) su ke da sakamakonsa da ladasan ba. Makurarsu –idan aka yi su- akan mafi kamalar fiskoki shi ne su zamo: GODIYA AKAN DAYA DAGA CIKIN BANGARORI  KADAN DAGA NI'IMOMINSA –MAI TSARKI (Allah)-; Shi yasa da zai azabtar da dukkan halittun sammansa da kassensa to da ya azabtar da su alhali ba wai yana zaluntar su ba. Da kuma zai musu rahama to da rahamar ita tafi musu alkhairi fiye da aiyukansu.

Kuma ka yi tunani cikin fadinsa madaukaki:
ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ             ﯲ ﯳ  [الزخرف: ٧٢].
( Waccar ita ce aljanna da aka gadar mu ku da ita saboda abin da ku ka kasance ku ke aikatawa)
(ka yi tunanin wannan ayar) tare da fadin Manzon Allah s a w:
" لَنْ يَدْخُلَ أَحَدٌ الْجَنَّةَ بِعَمَلِهِ "
Ma'ana: " Ba wani da zai taba shiga aljanna da aikinsa ".

(In ka yi tunanin ) za ka samu cewa ayar tana nuna cewa lallai shiga aljanna ya kan kasance ne da ayyuka. Shi kuma hadisin yana kore shigan aljanna da aiyuka, amma ba cin karo a tsakaninsu;
saboda masaukar kore da tabbatarwan ba a gurbi daya su ke sauka ba, (balle a yi zaton cin karo);
Wadda aka koren (harafin BA'UN NE) da ke nunin kudi da kima (kamar mutum ya ce: Na sayi biro da kudi; a wannan yanayin shi kudin kimar biro ne, aljanna kuma ba haka ta ke dangane da aiyukan bayi).; don haka abin da aka kore shi ne cancantar aljanna da tsagwaron aiyuka ( ba tare da shigar rahamar Allah ba), wato raddi kenan (mai da martani) ga kadariyya majusawa; wadanda su ka riya cewa: haka kawai a ba wa bawa lada ba tare da ya yi aiki ba (kawai dai falalan Allah) yana kunsan … (nakasa); saboda gori na bata garautakar hakan.

Shi kuma (harafin) BA'UN da aka tabbatar da shi; wadda ya zo cikin alqur'ani harafi ne da ke nuna sababi; raddi ga jabariyya da su ke cewa: Babu alaka tsakanin aiyuka da sakayyansu, kuma su (aiyuka) ba sabbubansu (sakamako) ba ne, Kawai dai makuransu (su aiyuka su zama) alamomi (na sakamako; wato wadda aiyukansa su ka yi muni; kenan hakan alamar yi masa mummunan sakayya ne, ba sababin haka ba, haka kuma idan aiyukan su ka yi kyau).

Sunnar Annabi –s a w- na nuna lallai gamewar nufin Allah da ikonsa (ga komai) ba ya kore kulla sabuban da abubuwan da sabuban ke zama dalilin samuwarsu, da kuma kulluwansu da su.

Kuma kowace kungiya ta bar wani nau'I na gaskiya To kuma za ta auka wa wani nau'I na barna saboda shi (ma'ana: barin gaskiyan), Kai! (za ta auka wa) awssu nau'uka (ba daya ba na barna). Sai Allah da izininsa kuma ya shiryad da Ahlus sunna zuwa ga gaskiya cikin abin da aka yi sabani akansa. (walhamdu lillah).


Kashi na uku: Sune wadanda su ke riya cewa: Lallai kawai fa'idan ibada (da amfaninta) shi ne: Motsa rayuka (kamar yadda ake motsa jiki da wasa) ta yadda zukatan za su zamo sun shirya wa kwararowar ilimi da wassu sani mabanbanta akan zukatan. Tare kuma da fitar karfi rai irin na su damusa (jarumta da ke haifar da zalunci) da kuma na su ayu da sauransu (sha'awa da kawai nufin biyan bukata); don haka da za a daina bauta  to da rayukan sun hadu da rayukan damusosi da dabbobi, don haka ibada ce ke fitar da rayukan ya zuwa kama da kwakwale (hankali irin na mala'iku) don haka sai su zama za su iya karbar zanuwar potunan sani a cikinsu.

Wannan maganar kungiya biyu ne su ke fadansa:

Na farkonsu: Wadanda su ka yi kusa da musulunci da shari'oi na philoserpers da su ke cewa: (Wai) duniya bata da farko, kuma wai babu mahalicci da ke halitta cikin zabinsa. (Amma wadannan fa ba musulmai ba ne).

Kungiya ta biyun su ne: Wadda ya koyi phalsafar daga cikin sufayen da su ke cikin musulunci, sa'an nan su ke kusa da philoserpers To wadannan na riya cewa: Wai ibadodi motsa rayuka ne don rayuka su zama sun shirya wa ilimomi da ke kwararowa ga hankula, da kuma saba wa al'adu.

Sa'an nan su wadannan akwai daga cikinsu da baya wajabta yin bautan sai don samun wannan ma'anar; don haka idan hakan ya samu wa zukatan nasu (kamar yadda su ke riyawa) to sai su tsaya suna dimautattu; Shin ya kiyaye abin da ya saba ne na wurudi? (Salla ne, zikiri ne, ko waninsu) Ko kuma ya shagaltu da abin da ya kwararo masan ga barin bautan nasa da wurudin da ya saban??

Akwai daga cikinsu wadda ya ke wajabta tsayuwa da wurudin (bautan da mutum ya saba), da kuma barin sakaci da su.

Su kuma wadannan suma kashi biyu ne:

Na farkonsu: Wadda ya ke ce: wajibi ne a kula da ibadar saboda kiyaye kanuni, da kuma rike mala'ikan da ya sauko (da ilimin a zuciya; tsoron kar ya kaura).

Sauran kuma suna cewa: Wajibi ne a ci gaba da bautar har bayan samun ilimin (da su ke riyawa) saboda kiyaye abin da ya zon, da kuma tsoron kar ran –a sannu a hankali- bayan barin yin bautar ta koma zuwa ga halinta na farko na dabbobi.


  WANNAN FA (WATO KASO UKU DA SU KA GABATA) SHI NE KARSHEN KAI KOMON MUTANE WAJEN BAYANIN MENENE HIKIMAR DA TA SA AKE BAUTA, DA KUMA DALILIN DA YA SA AKA SHAR'ANTA TA, Kuma ba za ka taba samun wani hanyan ba in banda daya daga wadannan hanyoyi uku ko gaba dayansu a cikin littatafan WADANDA AKE CE MUSU MUTAKALLIMUNA (wadanda su ka dauki yawa yawan akidarsu ko salonta daga philoserpers).


Kashi na hudu: Su ne wadanda su ke kudurta hade tsakanin halitta da umurni, da kaddara da sababi; (wadanda su ka yi aiki da dukkan ayoyi da hadisai; Ahlus sunna waljama'a); A wajensu: Sirrin bauta da kuma manufarta ya ginu ne akan sanin hakikanin uluhiyya (bauta wa Allah shi kadai), da kuma ma'anar kasancewarsa madaukaki shi ne: Abun bauta, sa'an nan ita kuma bauta shi ne kasancewarsa ILAHU ya ke hukuntawa, haka kuma shi ne athar (alama/ gurbi) na kasancewarsa ILAHU (domin in kace: yana cikin sifofin Allah: WADDA YA CANCANCI A YI MASA BAUTA to hakan tun da sifa ce muta'addiyat –kamar yadda maluma ke bayyanawa- to tana da tasirin a samu masu bauta masan, bayan an ciri suna da sifa). To kuma ratayuwan samun bauta ga wadda ya cancanci a masa bautar kamar ratayuwan sifa ne ga wadda ya siffanta da ita, haka kuma kamar ratayuwan abin da aka sani ne da sanin, da abin da ake da iko akansa da ikon, da kuma ratayuwan sautuka da ji, da kuma ratayuwan kyautatawa da rahama, da ratayuwan bayarwa da kyauta (kowanne daga cikin misalan da su ka gabata shi ne tasirin samuwar sifar da ta rataya da shi).

A wajensu (Ahlus sunna) duk wadda ya tsayu da saninta (wato: sifar uluhiyya, ko kalmar la'ila illallahu) akan yadda mu ka fassara ta –a harshen larabci da shari'a, tushenta da yadda ta ke faduwa- (duk wadda haka ya samu masa) to sanin hikimar ibadodi da manufofinsu (salla, azumi, addu'a da sauransu) zai inganta masa (kuma ya yi sauki), kuma zai san cewa (samar da kadaiceccen bauta ga Allah, da barin hada shi da wani, shi ne karshen abin da kowane ibada ke nufa) don haka a ka halicci bayi, kuma do wannan manufar aka turo manzanni, kuma aka saukar da littatafa, sa'an nan aka halicci aljanna da wuta.
 Kuma hakika (Allah) madaukaki ya bayyana wannan karara a cikin fadinsa:
ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ  [الذاريات: ٥٦].
(Kuma ban halicci aljani da mutum bai sai don su kadaita ni cikin bauta).
Kai ita kuwa bauta ita ce don ita aka samar da halittu, kamar yadda madaukaki ya ce:
ﮚ     ﮛ  ﮜ ﮝ  ﮞ ﮟ  [القيامة: ٣٦].
(Shin mutum na tsammanin za a bar shi kara zube ne (haka siddan), Ai! Kara zube;
Shafi'I –r . l- yana cewa: Ba za a masa umurni da hani ba.
Waninsa kuma ya ce: Ba za a masa sakayya da horo ba.
Dukkan wadannan tafsiri biyun ingantattu ne; saboda bada sakayya da horo yana rataya ne kan umurni da hani, su kuwa umurni da hanin su ne neman yin bauta da neman mutane su nufe ta.

Hakikanin bauta kuwa sh ne: aiki da su (umurni da hani); don haka (Allah) madaukaki ya ke cewa:
ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ   ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮪ  [آل عمران: ١٩١].
(Kuma su ke yin tunani cikin halittan sammai da kassai; Ya ubangijinmu: Baka halicci wannan don barna ba).
Madaukaki ya ce:
ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ  ﮬﮭ ﯖ  [الحجر: ٨٥].
(Bamu halicci sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu ba sai don gaskiya -Allah da bautansa shi ne gaskiya, abin da ake bautawa koma bayansa kuma shi ne tantagaryan barna- ) .
ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ        ﯺ ﯻ ﯼ ﰀ الجاثية: ٢٢
(Kuma Allah ya halicci sammai da kassai da gaskiya, kuma don a saka wa kowane rai da abin da ya aikata).
Allah madaukaki ya bada labarin cewa lallai shi ya halicci sammai da kassai da gaskiya; wadda hakan kuma ya kunshi: ya yi umurni, ya hana, ya yi sakayya, ya yi horo.

To idan sammai da kassai ( da ma abin da ke tsakaninsu) ya zama an halicce su ne don wannan, wadda kuma shi ne manufar yin halitta daukacinta TA YAYA ZA A CE: (Allah) ba shi da manufa (na halittansa da ya yi) haka kuma babu wata hikima da ya nufa?
Ko (a ce) ya halicce su ne don kawai bada kwadago wa ma'aikata (wato halittu su yi aiki, shi kuma ya bada aljanna ko watanta); (za su yi aiki don) har kar ladan ya ki yin dadin amfana da shi; saboda gori (in da hka kawai aka basu ba tare da aiki ba)??
Ko kuma (ace: akan yi ibadu ne) don kawai horas da rayuka don wasu sani na hankali su kwarara musu, da kuma motsa ran don ya saba wa al'adu???

Idan mai hankali ya yi tunanin banbanci da ke tsakanin wadannan maganganun, da tsakanin (maganan) da wahayi ya yi nuni zuwa gare shi karara= Zan san (sani na yakini) cewa: Lallai Allah madaukaki ya halicci halitta ne don bauta masa; da ya game cikar sonsa, tare da kan-kan-da-kai a gare shi, da kuma mika wuya ga umurninsa.

Saboda tushen bauta shi ne: Son Allah, kai! Kadaita shi madaukaki da soyayya, ba a son waninsa –ko wanene shi- tare da shi, kawai dai (bawa) na son wadda ya ke so saboda shi, da kuma a cikisa kamar yadda ya ke son Annabawansa da manzanninsa da Mala'ikunsa; saboda sonsu na cikin cikar sonsa. Amma ba kamar son wadda ya riki kishiyoyi koma bayansa; da ya ke sonsu kamar sonsa.

To kuma idan son Allah ya zama shi ne hakikanin bauta masa, kuma sirrin bautar kenan To –ka sani- abin sani kawai soyayyar tasa ta kan tabbatu ne da bin umurninsa, da hanuwa da haninsa; Kenan a wajen bin umurni da hani hakikanin bauta da soyayyan ke bayyana.
  Don haka ne (Allah) mai tsarki ya sanya bin manzonsa s a w ya zama alama ne da ke nuna sonsa, kuma (bin nasa) ya zama mai shaida ne akan son, kamar yadda madaukaki ya ce:

(قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببم الله) [آل عمران: ٣١].

(Ka ce: In kun kasance kuna son Allah; to ku bi ni, Allah zai so ku).
(A cikin ayar) Sai ya sanya bin manzonsa an shardanta shi kafin ace ya tabbata suna son Allah madaukaki, sa'an nan (son) kuma shi ne sharadin Allah ya so su. Shi kuwa samuwan abun da aka shardanta ba tare da tabbatuwan sharadinsa ba kuwa abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.

To daga nan; Sai aka san koruwan soyayyar Allah a lokacin da aka rasa bin manzo. Kai! Hakan ma bai isa ba har sai Allah da manzonsa su su ka fi soyuwa a wajensa akan wadanda ba su ba.

Kuma duk lokacin da aka samu wani abu a wajensa ya fi soyuwa a wajensa fiye da su biyun to wannan shi ne shirkar da Allah madaukaki baya gafartawa, madaukaki yana cewa:
ﭻ ﭼ    ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ    ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ  [التوبة: ٢٤].
(Ka ce: Idan iyayenku da 'ya'yanku da 'yan uwanku da matanku da danginku da dukiyar da ku ka gaji wajen tara ta da kuma kasuwancinku da ku ke tsoron tasgarowanta, da gidajen zama da ku ka yarda da su (Idan wadannan abubuwan duka, ko sashinsu) ya fi soyuwa a wajenku fiye da Allah da Manzonsa da jihadi a kan tafarkinsa (in haka ya kasance to ku fasikai ne azzalumai) to ku jira har sai Allah ya zo da al'amarinsa; kuma lallai Allah baya shiryar da mutane fasikai ).

 Duk kuma wadda wadda ya gabatar da zancen wanin Allah akan zancen Allah, ko kuma ya yi hukunci da shi, ko ya kai hukuncinsa zuwa gare shi to baya cikin wadanda su ke sonsa.

 Sai dai wani lokaci al'amarin na rikice wa wadda ya gabatar da maganan wani, ko kuma hukuncinsa, ko biyayyarsa akan maganansa (Allah); da zaton wannan mutumin ba zai yi umurni, ko ya yi hukunci, ko ya fadi wani abu sai abin da Manzo s a w ya yi umurni; sai ya masa biyayya –a irin wannan halin- ya kuma kai hukuncinsa zuwa gare shi, haka kuma ya rungumi maganansa hanu bibbiyu kamar haka. To irin wannan yana da uzuri idan ba shi da iko akan wanin haka.

Amma idan ya samu ikon isa ya zuwa ga manzon s a w, ya kuma kuduri cewa: Wanin wadda ya bi (manzo s a w) ya fi masa wadda ya bi shi a dukkan hukunce –hukunce, ko a sashin al'amura; kamar wata matsala aiyanenniya (sananniya); don haka sai ya ki juyawa zuwa ga maganan Manzon s a w, haka kuma ya karkata ga barin maganan wadda ya fi kusanci da shi (manzon; ta wajen binsa) To irin wannan ana tsorace masa.

 Kuma dukkan abin da kamawa a matsayin hujja da kuma dalili da hana binsa na:
1- Rashin ilimi.
2- Ko rashin fahimta.
3- Ko kuma rashin bamu ilmukan da za su taimake mu wajen fahimta cikin addini.
4- Ko kuma kafa hujja da wassu mas'aloli da su ka yi kama da wannan, sai dai kuma a hakika hukuncinsu ya banbanta.
5- Ko kuma cewa: Wane magabaci (Abu hanifata, Malik, Shafi'i, Ahmad) ya fi mu sanin manufar Annabi s a w.
Duk wadannan neman dalili ne, da baya amfanarwa (Kawai dai ka bi Manzon Allah s a w).

Dadin-dadawa tare da ikrarin halarcin yin kuskure ga duk wanda ba ma'asumi ba (ma'ana: wanda ba Annabi ba);
Saidai idan aka yi jayayya kan wannan ka'idar (cewa: wanin ma'asumi yana iya yiwuwa ya yi kuskure) idan mutum ya yi jayayya kan wannan ka'idar to bai ma cancanci a yi magana da shi ba; Don haka in ya kaddamar da maganansa akan na Annabi s a w sai ya shiga cikin wannan narkon (da ayar ta rufe da shi).

Idan kuma tare da haka ya halatta aibanta wanda ya saba masa, da sukan mutuncinsa da addininsa da harshensa, Ko kuma ya ciratu daga haka zuwa yi masa horo (duka ko kisa) ko kuma kokarin cutar da shi To wannan yana cikin azzalumai masu wuce gona-da-iri, haka kuma yana cikin na'iban mabarnata.

********


[KAIDOJIN IBADA GUDA HUDU]
  Kuma ka sani lallai ibada tana da ka'idodi guda hudu;
Su ne: Hakikicewa (tabbatarwa) cewa wannan aikin Allah da manzonsa su na sonsa kuma sun yarda da shi, da kuma tsayuwar hakan a zuci da harshe da kuma gabbai.

Ita kuma bautantaka: Suna ne da ya game wadannan martabobi guda hudun. Su kuma ma'abotan ibada ta gaskiya su ne ma'abotan hakan (martabobi hudun);

Shi FADIN ZUCI SHI NE: kudurce abin da Allah ya bada labari akan kansa, kuma Manzonsa ya bada labari akan Ubangijinsa na sunayenSa, da sifofinSa, da aiyukanSa, da Mala'ikunSa, da saduwa da Shi (a kiyama) da makamantan haka.

SHI KUWA FADIN HARSHE SHI NE: Bada labari dangane da shi (Allan) da harshen, da kuma yin da'awa zuwa ga Allah (da harshen), da kuma bada kariya a gare shi, da bayyana batancin bidi'a da su ka saba masa, da tsayuwa da ambatonsa madaukaki, da kuma isar da al'amarinsa (addininsa).

SHI KUMA AIKIN ZUCI SHI NE: Kamar son Allan, da dogara zuwa gare shi, da mayar da al'amari zuwa gare shi, da tsoro, da fata, da ikhlasi, da yin hakuri kan umurce –umurcensa da haninsa da kaddaransa, da kuma yarda da shi, da yarda don shi, da kuma soyayya don shi, da kiyayya don shi, da kuma kan-kan-da-kai da mika wuya zuwa gare shi, da natsuwa da shi, da makamantan wannan na aiyukan zuciya; wadanda farillancin farillensu ya fi karfi kan farillancin aiyukan gabbai, haka kuma wadanda su ke mustahabbai su kuma sun fi soyuwa zuwa ga Allah madaukaki fiye da mustahabban aiyukan gabbai.

AMMA AIYUKAN GABBAI KUMA; Misalaensu kamar su salla, jihadi, taku zuwa masallacin juma'a da jam'o'I (na salloli biyar na yau-da-kullum), da kuma taimakon gajiyeyye, da kyautatawa ga halittu, da makamantan wadannan.

Don haka; Fadin bawa a cikin sallansa:
ﭢ ﭣ
(A kai kadai mu ke bauta)
(Fadin hakan) lazimtar hukunce-hukuncen wadannan (martabobi) hudun ne, da kuma tabbatar da su.
 Fadinsa kuma:
ﭤ ﭥ ﭦ  [الفاتحة: ٥].
(Kuma a gare ka –kai daya- mu ke neman taimako).

(Fadin haka kuma) neman taimakonsa ne akansu, da kuma datar da shi zuwa gare su (nau'ukan bauta).

Fadinsa kuma:

ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ  [الفاتحة: ٦].
(Ka shiryad da mu hanya madaidaiciya);
Ya kunshi abubuwa biyun (bauta da kuma samun taimakon Allah wajen tsayar da itan), akan bayani dalla-dalla (da ya gabata), tare kuma neman Allah ya yi wa bawa ilhama wajen tsayuwa da su, da bin turbar masu tafiya zuwa ga Allah ta'ala (na Manzanni, da Siddikai, da Shuhada'u da Salihai).

Allah shi ne mai datarwa da baiwarsa da kyautarsa.

Kuma godiya ta tabbata ga allah shi kadai.

Yabon Allah ya kara tabbata ga wadda babu annabi bayansa da iyalensa da sahabbaansa; magadansa kuma rundunansa.


LITTAFIN YA CIKA, DA TAIMAKON ALLAH MAMALLAKI MAI YAWAN BAIWA.



Fassarar: Mai neman afuwar Ubangijinsa/ Abubakar Hamza zakaria,
Ina baran kura-kuraina ta wannan adireshi/

An gama fassara shi ranar 26/ 7/ hijirar Manzon Allah s a w daga Makka zuwa Madina tana shekarar 1431, a garin Madina –Allah ya kara mata daukaka-, wanda ya yi daidai da / 8/ 7 /2010 miladiyyar Annabi Isa (a s w),





Shafi

Abubuwan da ke cikin littafin




1



2



3



4



5



6



7



8



9



10



11



12



13



14



15



16



17




















































































































































































































































  ([1])
 ([2])
  ([3])
  ([4])  
  Muslim ne ya ruwaito shi.([5])  

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...