Matashiya kan
azumin watan Ramadhana (03)
لا
يجوز تقدُّم رمضان بصومٍ للاحتياط
1/ عن أَبِي هُرَيْرَةَ
رضي الله عنه،
عَنِ
النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
"لاَ
يَتَقَدَّمَنَّ أَحَدُكُمْ رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ أَوْ يَوْمَيْنِ، إِلاَّ
أَنْ يَكُونَ رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمَهُ فَلْيَصُمْ ذلِكَ الْيَوْم".
أخرجه
البخاري [1914]، ومسلم [1082].
BAI HALATTA A
RIGAYI RAMADHANA DA AZUMTAR YINI BIYU KO DAYA A GABANINSA, DON TSANTSENI KO
NEMAN FITAR DA KAI DAGA SABANI
Fassara:
An
ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Annabi
-sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Kada ku rigayi Ramadana da azumtar yini daya, ko biyu, sai
dai ga mutumin da ya kasance ya ke yin wani azumi, to ya azumce shi".
Bukhariy
[1914] ya rawaito shi, da Muslim [1082].
2/ وعَنْ صِلَةَ بْنِ
زُفَرَ رحمه الله قَالَ:
كُنَّا
عِنْدَ عَمَّارِ بْنِ يَاسِرٍ فِي الْيَوْمِ الَّذِي يُشَكُّ فِيهِ، فَأُتِيَ
بِشَاةٍ مَصْلِيَّةٍ، فَقَالَ: كُلُوا، فَتَنَحَّى بَعْضُ الْقَوْمِ، فَقَالَ:
إِنِّي صَائِمٌ،
فَقَالَ عَمَّارٌ:
«مَنْ صَامَ الْيَوْمَ الَّذِي يَشُكُّ فِيهِ النَّاسُ، فَقَدْ عَصَى
أَبَا الْقَاسِمِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ".
أخرجه
أبو داود [2334]، والترمذي [686]، وقال:
حديث
حسن صحيح.
Fassara:
An
ruwaito daga Silatu bn Zufar -Allah ya yi masa rahama-, ya ce:
Mun
kasance a wurin sahabi; Ammar bn Yasir -Allah ya kara yarda a gare shi- a ranar
da ake shakku a kansa, sai aka zo masa da akuyar da aka gasa namanta,
sai
Ammar ya ce: ku ci,
sai
wani daga cikin mutanen ya matsa can gefe,
Sai
Ammar ya ce:
"Wanda ya yi azumin yinin da mutane ke kokwanto a kansa, to
hakika ya saba wa Abul-kasimi -sallal lahu alaihi wa sallama".
Abu-dawud
[2334] ya ruwaito shi, da Tirmiziy [686],
kuma
ya ce: hadisi ne hasan ingantacce.
Tsokaci
Wadannan
hadisan suna nuna;
(1)
Hani kan rigayar watan Ramadhana da azumin yini daya ko biyu, da nufin idan
wannan yinin ya kasance -a hakikanin lamari- daga kwanakin Ramadhana, to, shi
dai ya kubuta, idan kuma baya cikinsu, to hakan ya zame masa nafila.
Da
kasancewar aikata hakan saba wa Manzon Allah ne, sallal lahu alaihi wa sallama,
saboda ya shar'anta mana a tashi da azumi Ramadhana idan aka ga wata, bayan
dubiyar wata, da ganinsa, a lokacin da watan Sha'abana ya ke da kwanaki 29.
Idan
kuma ba a gani ba, to sai ya yi hani kan azumtar yinin da ke biye, ya kuma
umarci halittu da mu cike kidayar Sha'abana kwanaki 30, sa'annan sai mu tashi
da azumin Ramadhana bayan hakan.
(2)
Azumi a musulunci an gina shi ne akan abu na sarari, wato ganin jinjirin
wata, ko cike kidayar Sha'abana kwanaki 30.
(3)
Wanda ke da sauran azumin kaffara akansa, ya halatta ya cigaba da yin azumi,
koda kuwa a cikin yini daya ko biyu da su ka rigayi Ramadhana ne.
Haka
mutumin da ya saba azumin ranakun litinin da alamis, idan su ka kasance a ranar
shakku (wato, yinin da ya zo bayan 29/Sha'abana, idan ba a ga watan Ramadhana a
daren 29n ba).
No comments:
Post a Comment