2016/12/22

hudubar Masallacin Manzon Allah 24 RABIYUL AUWAL 1438H Ta Abdulmuhsin Alkasim daidai da 23 disemba 2016M









HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24 /RABIYUL AUWAL/1438H
Daidai da 23 /12/ 2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
GIRMAMA MASALLATAI
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a ta 24 Rabiyul Auwal, 1438H, mai taken: GIRMAMA MASALLATAI, Wanda a cikinta ya tattauna, kan haxin kai, da na zukata, da riqo da littafi da Sunnah, Yana mai bayyana falalarsa, da girman tasirinsa, da kasancewarsa sababi ne na tsira ga wannan al'ummar daga fitintinu, yana kuma tsawatarwa kan rarrabuwar kai da savani da jayayya; saboda abinda su ke sabbabawa na saukar jarabawa da bala'oi ga musulmai, da rarrabuwar kalmarsu, da kecewar sahunsu.

بسم الله الرحمن الرحيم

HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna yaba maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

       Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riqo da igiya mai qarfi daga Musulunci.

YA KU MUSULMAI !!!
Lallai Allah ya sanya fifiko tsakanin halittunSa, kuma ya zavi abinda ya so daga cikinsu, da falalarSa.

Kuma Allah ya bautar da mu, da sanin abinda dalilan shari'a su ka tabbatar cewa, yana da wata falala, domin mu qudurce haka a zukata, kuma mu yi bauta da abinda aka shar'anta a cikinsa.
Kuma a cikin haka, akwai zaburarwa zuwa ga rigaggeniya, cikin aiyuka masu falala, da tsere domin samun martabobi maxaukaka.

Kuma tushen fifiko tsakanin halittu shi ne: TAQAWAR ALLAH DA TABBATAR DA BAUTA A GARE SHI, DA NEMAN KUSANCI ZUWA GA ALLAH.
Kuma xaixaikun da su ke qarqashin jinsi guda, lallai, suna samun fifiko a tsakaninsu fifiko mai girma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya faxa dangane da mutane biyu: "Wannan mutumin ya fi irin wannan, cikin duniya", Bukhariy ya ruwaito shi.

Itama duniya, wuraren cikinta, haka su ke, wani ya fi wani, kuma wurin da Allah ya fi so, a cikin duniya shi ne wuraren da ake masa bauta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wuraren da Allah ya fi so, a cikin garurruka su ne, masallatansu", Muslim ya ruwaito shi.
Wannan kuma saboda abin da masallatai su ka kevanta da shi na ibadodi da zikiri, da haxuwar muminai, da bayyanar da alamomin addini.

Kuma mafi xaukaka daga cikin masallatai, kuma mafi girma daga cikinsu shi ne: MASALLACI MAI ALFARMA (na Makka), farkon masallacin da aka aza a doron qasa, kuma alamar shiriya ga mutane, "Lallai xaki na farko da aka aza domin mutane, shi ne wanda ke garin Bakka, mai albarka, kuma shiriya ga talikai" [Ali-imrana: 96].
Allah ya wajabta yin hajjin wannan xakin, da yi masa xawafi, kuma ya sanya shi ya zama alqiblar bayinsa muminai.
Kuma yin salla a masallacin daidai ya ke da yin salloli dubu xari (100, 000), a waninsa.

Masallaci na biyu, ta fiskar falala shi ne: MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم), kuma masallacin qarshe, da wani ba'annabe ya gina, "Sallah a masallacina wannan, ya fi alheri fiye da sallah dubu (1000) a waninsa; in banda masallaci mai alfarma", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma masallacin annabi masallaci ne da aka kafa harsashinsa, akan taqawar Allah, tun ranar farko, Abu-Sa'id Alkhudriy (رضي الله عنه) ya ce: Ya Manzon Allah! Wanne ne daga cikin masallatan nan biyu (Quba'a, da na Annabi) aka assasa shi akan taqawa?
Ya ce: Sai ya xauki yashi cikin tafin hannu, sai ya buga qasa da shi, sa'annan ya ce: "Shi ne masallacinku wannan", Muslim ya ruwaito shi.

Shi kuma masallaci mai nisa (Aqsah) shi ne farko alqibla biyu, kuma wurin da aka yi isra'i da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), An aza shi a doron qasa bayan masallaci mai alfarma na Makkah, Abu-zarrin (رضي الله عنه) ya tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Wani masallaci ne aka aza shi farko a doron qasa?
Sai ya ce: "Masallacin harami (na Makkah)".
Sai ya ce: Sai kuma wane?
Ya ce: "Sai masallaci mai nisa (na Qudus)", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma, izuwa masallatan nan ne, guda uku ake yin bulaguro, ba izuwa ga wassunsu ba, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ba a xaura sirdi (a yi bulaguro domin lada) Sai in zuwa ga masallatai ne guda uku:
1) Masallaci mai alfarma (Makkah).
2) Masallacina wannan (Madina).
3) da masallaci mai nisa (na Kudus)", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Ibnu-taimiyya –رحمه الله- ya ce: "Sauran masallatai wanda ba waxannan ba, to, ba a shar'anta bulaguro zuwa gare su ba, da ittifaqin ma'abuta ilimi".

            Masallacin Quba'a shima an assasa shi akan taqawa, tun yinin farko, Allah yana cewa: "Masallaci wanda aka harsashinsa kan taqawa, tun farkon yini, shi ne mafi cancantar ka tsayu a cikinsa" [Tauba: 108].
Kuma "Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana zuwa masallacin Quba'a, a kowace asabat, da qafa ko da abin hawa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma "Duk wanda ya yi tsarki daga gidansa, sa'annan ya tafi masallacin Quba'a, domin yin salla a cikinsa, to yana da kwatankwacin ladan umrah", Ibnu-majah ya ruwaito shi.

            Kuma babu wani masallaci a garin Makka da Madina, waxanda aka shar'anta ziyartarsu in banda masallatan nan guda biyu, da masallacin Quba'a. duk masallatan da ba su ba kuma, to suna da hukunci ne irin na sauran masallatai.

            MASALLATAI xakunan Allah ne, Allah ya jingina su ga kansa, domin xaukakawa da karramawa. Kuma Allah ya yawaita ambatonsu. Kuma ya yi umurni kan gina su da basu kariya. Kuma Allah ya sanya daga manufofin tunkuxeniya tsakanin mutane (musulmai da kafirai): akwai kare masallatai da kiyaye su, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ba domin tunkuxewar Allah ga mutane, sashensu da sashe, da an rusa sauma'oin (ruhubanawa) da majami'oin Nasara, da gidajen ibadar Yahudu, da masallatai, da ake ambaton sunan Allah a cikinsu dayawa" [Haj: 40].

            Masallatai mala'iku suna halartarsu, kuma suna sauraron huxubobin da ake yi a cikinsu, suna kuma kewaye masu ambaton Allah daga ma'abutansu.
            Gina su, da tsayar da salla a cikinsu, kariya ne da aminci "Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana kaiwar farmaki (a lokacin yaqi) idan alfijir ya keto, kuma ya kasance yana jiran ya ji kiran salla, idan ya ji kiran salla sai ya kame daga kaiwar farmaki, idan kuma ba haka, sai ya kai farmaki", Muslim ya ruwaito shi.
            Allah ya yi izinin a xaukaka masallatai, kuma ya yi umurni da haka, Allah (سبحانه) ya ce: "A cikin waxansu gidaje waxanda Allah ya yi umurnin a xaukaka, kuma a ambaci sunanSa a cikinsu" [Nur: 36]. Kuma Allah ya yabi ma'abutan masallatai, a cikin faxinsa: "Suna yin tasbihi a gare shi a cikinsu da safiya da maraice * Waxansu maza…" [Nur: 36-37].

            Raya su ta fiskar gini, da aiwatar da dangogin xa'oi a cikinsu alama ce ta imani, Allah (سبحانه) ya ce: "Abin sani kawai, mai raya masallatan Allah shi ne wanda ya yi imani da Allah, da ranar lahira, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah, to lallai waxannan za su kasance daga shiryayyu" [Tauba: 18].
            Kuma nisantar masallatai da yaqar su, alamar tavewa ce, Allah (تعالى) ya ce: "Baya kasancewa ga mushirkai su raya masallatan Allah, alhali suna masu shaida akansu da kafirci" [Tauba: 17].
           
            Masu raya masallatai su ne zavavvu daga halittar Allah, na daga annabawa da mabiyansu, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma a lokacin da Ibrahimu ya ke xaukaka harsashin gini, ga xakin, da Isma'ilu, (suna cewa): Ya Ubangijinmu, ka karva daga gare mu, lallai ne kai Mai ji ne Masani" [Baqara: 127].
Kuma farkon saukar Annabi (صلى الله عليه وسلم) a garin Madina, sai ya gina masallacin Quba'a, sa'annan masallacinsa.

            Gina masallatai kusanci ne ga Allah, kuma ibada, wanda Allah ya yi alqawarin aljanna ga ma'abuta haka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya gina masallaci ga Allah, Allah zai gina masa kwatankwacinsa a aljanna", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Wanda ke nufan masallatai (tafiya gare su) ladansa yana da girma, kuma yana da lada masu yawa gwargwadon takunsa, kuma a daga darajarsa gwargwadon yawan takunsa, sannan a kankare masa munanansa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Babu wani mutum da zai tsarkaka, sai ya kyautata tsarkinsa, sa'annan sai ya nufi wani masallaci daga cikin waxannan masallatan, face Allah ya rubuta masa lada da kowane takun da ya yi, kuma ya xaga masa daraja da kowani taku, kuma ya kankare masa mummuna da kowani taku", Muslim ya ruwaito shi.
            Kuma yana daga cikin ribaxin lada, yawaita taku zuwa ga masallatai, da jiran salloli a cikin masallatai.
            Kuma "Duk wanda ya yi sammako zuwa ga masallaci, ko ya tafi da yamma, Allah zai masa tanadin wata liyafa a aljanna, duk lokacin da ya yi sammako, ko ya tafi da yamma", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
            Kuma "Wanda ya fi mutane girman lada a lamarin sallah, shi ne wanda gidansa ya fi nisa, sai wanda ke biye da shi a nisan taku, kuma mutumin da ke jiran salla, domin ya sallace ta, tare da liman, ya fi girman lada, akan wanda ke yin salla, sannnan ya yi barci", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Yana daga sabbuban gafarta zunubai, tafiya zuwa ga masallaci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya yi alwalar sallah, sai ya kyautata alwalar, sa'annan ya tafi zuwa ga sallar farilla, ya sallace ta tare da mutane, ko da jama'a, ko a masallaci, Allah ya gafarta masa zunubansa", Muslim ya ruwaito shi.

            Lazimtar masallatai da sonsu, yana daga sabbuban shiriyar mutum da gyaruwarsa. Kuma yana daga jinsin mutane bakwai (7) waxanda Allah zai sanya su a inuwar al'arshinsa ranar da babu wata inuwa sai tasa, "Mutumin da zuciyarsa ke rataye da masallatai", Muslim ya ruwaito shi.
Nawawiyرحمه الله- ya ce: Ma'anar hadisin shi ne: "Mai tsananin son masallatai, mai lazimtar yin jam'i a cikinsu".
            Kuma "Idan musulmi ya shiga masallaci ya kasance a cikin salla, matuqar sallarce ta hana shi fita, kuma mala'iku za su riqa masa addu'a matuqar yana wajen zamansa  da ya yi salla a cikinsa, (suna cewa:) Ya Allah ka gafarta masa, Ya Allah ka yi masa rahama", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Masallatai ababen girmamawa ne a cikin al'umman da su ka gabata, Allah ya umurci annabi Ibrahima da Isma'ila, ya ce: "Kuma mu ka yi alqawari zuwa ga Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake xakina, domin masu xawafi, da masu lazimtar i'itikafi, da masu ruku'i, masu sujada" [Baqara: 125].
Kuma matar Imrana, ta yi bakancen abinda ke cikinta, ga hidimar masallaci mai nisa (na qudus) "Ya Ubangijina ! lallai ne, na yi bakancen abinda ke cikin cikina, gare ka, ya zama 'yantacce" [Ali-imrana: 35].
Abdullahi bn Abbas (رضي الله عنهما) ya ce: "''Yantacce domin hidimar masallaci".

            Kuma musulunci ya girmama, sannan ya xaukaka matsayin masallatai, domin su zama alama mai haske da su ke nuna musulunci, sai kuma ya girmama sha'anin mutumin da ke tsayuwa domin hidimar masallaci; Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya tambayi labarin matar da ta kasance ta ke sharar masallacinsa, Sai su ka ce: Ta mutu, Sai ya ce: "Ku nuna min qabarinta", sai su ka nuna masa, Sai ya yi mata salla. Sannan ya ce: "Lallai waxannan kaburburan, gabanin haka: suna cike da duhu ga ma'abutansu", Bukhariy ya ruwaito shi.
            Kuma an bijiro wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ga kyawawan aiyukan al'ummarsa da munanansu, ya ce: "Sai na samu daga cikin munanan aiyukansu, kakin da ke kasancewa a cikin masallaci, ba a bunne shi ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma "Zubar da kaki a masallaci laifi ne, kaffararsa kuma ita ce: Bunne shi", Muslim ya ruwaito shi.
            Kuma yayin da balaraben qauye ya yi fitsari a masallaci, sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada umarnin a zuba gugan ruwa, sai aka kwara akansa, sannan ya ilmantar da shi alfarmar masallatai, ya ce masa: "Lallai waxannan masallatan basa dacewa da fitsari, ko qazanta, kawai an gina su ne domin ambaton Allah Mabuwayi da xaukaka, da salla da karatun alqur'ani", Muslim ya ruwaito shi.

            Yana daga LADDUBAN MASALLATAI zuwa musu cikin tsarki, da yin ado domin su, Allah ta'alah ya ce: "Ya xiyan Adam ! ku riqi adonku wurin kowani masallaci" [A'araf: 31].

            Kuma yana daga GIRMAMA MASALLATAI, Tafiya zuwa gare su, cikin yanayin da ya fi kamala, kuma duk wanda zai je masallaci to ya lazimci natsuwa da tsanaki, cikin yanayinsa da tafiyarsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan aka tsayar da salla kada ku zo mata kuna gudu, ku zo mata cikin tafiya, ina kuma horonku da natsuwa, duk abinda ku ka riska, ku sallata, duk abinda ya kufce muku ku cika", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Kuma idan mutum zai shiga masallatai domin ya girmama su, sai ya gabatar da qafarsa ta dama, qafar hagu kuma a yayin fitansa daga masallatai.
            Kuma masallatai wurin yin bauta ne, da samun rahama, da addu'a, idan zai shiga sai ya ce: "ALLAHUMMAF TAH LIY ABWABA RAHMATIKA (YA Allah! Ka buxe min qofofin rahamarka), Idan kuma zai fita ya ce: ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA MIN FADLIKA (Ya Allah! Lallai ni ina roqonka daga falalarka)", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma domin gaisar da masallatai, duk wanda ya shiga cikinsu ba zai zauna ba, har sai ya yi raka'oi biyu.

            Kuma SAHUN GABA-GABA a cikin masallatai masu rigaye cikin aiyukan alkhairi suna yin tsere wajen dacewa da su, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Da mutane sun san ladan da ke cikin lamarin kiran salla, da sahun farko, sai kuma basu samu ba sai ta hanyar quri'a, da sun yi quri'ar", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma domin girmama sallolin farillai a cikin masallatai, "Idan aka tsayar da salla, to babu wata sallar in banda farilla", Muslim ya ruwaito shi.

            Masallatai wuraren samun rahama ne, kuma musulunci yana kwaxaitarwa wajen zuwa masallatai, kuma yana hana mutane dukkan abinda zai iya kore mutane daga masallatai, kuma duk wanda ya kasance yana da wani wari; abun kyama, sai a masa uquba, da hana shi shiga masallatai, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa, ko albasa, to ya nisance mu, ko ya ce: Ya nisanci masallacinmu, kuma ya zauna a gidansa", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Ibnul-Asirرحمه الله- ya ce: "Wannan ba a babin bada uzuri ba ne, a'a kawai annabi ya umurce su ne da qaurace wa masallatai a matsayin uquba a gare su, da azabtarwa".

            Masallatai wuraren samun qarin imani ne, da xaguwar darajoji, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Masallatai kawai, domin yin zikirin Allah ne Mabuwayi da xaukaka, da salla da karatun alqur'ani", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma su, masallatai wurin saukar natsuwa ne, da lulluvewar rahama, da kewayewar Mala'iku, kuma wurin da Allah ke yabon waxanda suka halarce shi, saboda ana karantar da alqur'ani mai girma a cikinsu, ko ilimi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma mutane ba za su haxu a wani xaki daga cikin xakunan Allah ba, suna tilawar littafin Allah, suna yin darasunsa a tsakaninsu, face natsuwa ta sauka a cikinsu, kuma rahama ta lulluve su, kuma mala'iku sun kewaye su, kuma Allah ya ambace su ga waxanda su ke wurinsa", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma xaukar ilimi a cikin masallatai ya fi alkhairi akan samun mafificin kayan daxin duniya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Shin xayanku ba zai yi sammako zuwa ga masallaci domin ya san ko ya karanta ayoyi biyu daga littafin Allah (عز وجل) ba, wanda ya fi masa alkhairi akan samun taguwa biyu, uku kuma ya fi masa alkhairi a akan taguwa uku, huxu ya fi masa alkhairi akan taguwa huxu, da kuma wannan adadin na raqumai maza", Muslim ya ruwaito shi.
            Kuma haqiqa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya riqi masallacinsa a matsayin wurin karantarwa, sai ya samar da mutanen da ba a yi ba kuma ba za a yi kamar su ba.
            Kuma ya kasance yana kwaxaitarwa kan zama a halqoqin zikiri da ilimi, a masallatai, sai ya ce, dangane da mutanen nan guda uku: "Amma xaya daga cikinsu, sai ya fake zuwa ga Allah, sai Allah ya bashi mafaka, Amma xayan kuma, sai ya ji kunya, sai Allah ya ji kunyarsa, Amma xayan kuma, sai ya kawar da kansa, sai Allah ya kauce daga gare shi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Masallatai ruhi da rayuka suna nitsuwa a cikinsu, wannan ya sanya ba a xaga sauti, don jayayya ko husuma ko hauragiya a cikinsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ina tsawatar muku kan cakuxa da husumomi da hauragiya irin ta kasuwanni", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma yayin da Umar (رضي الله عنه) ya ji wasu mutane suna xaga sautinsu a cikin masallaci, sai ya nemi aka zo masa da su, sa'annan ya ce: "Da kun kasance 'yan wannan gari (na Madina, da na yi rauni a bayanku saboda kuna xaga sautinku a masallacin Manzon Allahu sallal lahu alaihi wa sallama)", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Yana daga CUTARWA A CIKIN MASALLATAI tsallake wuyan masu salla, Wani mutum ya zo, yana ta tsallaka wuyan mutane, ranar juma'a, sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) y a ce: "Ka zauna, lallai ka cutar", Abu-dawud ya ruwaito shi.

            Masallatai wuri ne na aminci da natsuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi umarnin a toshe dukkan abinda zai cutar, a inda ya ke cewa: "Duk wanda ya shige masallatanmu, ko kasuwanninmu da kibau, to ya riqe kan kibiyar da tafinsa, saboda kada ya soki musulmi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Kuma masallatai sune wuraren hutu, da nisantar duniya, da tuna lahira, da qarfafa alaqa da Allah, Sai aka hana saye da sayarwa a cikin masallatai, kuma aka tsawatar akan haka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan ku ka ga mutumin da ke saye ko sayar da kaya a masallaci, ku ce: Kada Allah ya sanya riba a kasuwarka", Tirmiziy ya ruwaito shi.
            Har ma ya yi hani kan shagaltar da mutane, a cikin masallatai da damuwoyin duniya, a inda ya ce: "Wanda ya ji mutumin da ke cikiyar vataccen kaya,a cikin masallaci to ya ce: KADA ALLAH YA DAWO MAKA DA SHI, saboda masallatai ba a gina su domin wannan ba", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma ba a faxi, ko a ji a cikin masallatai, sai abinda alkhairi ne, wannan kuma aiki ne da umarnin da yazo kan xaukaka masallatai, a cikin faxinsa: "A cikin waxansu gidaje waxanda Allah ya yi umarnin a xaukaka, kuma a ambaci sunansu a cikinsu"[Nur: 36].
Ibnu-kasirرحمه الله- ya ce: "Ya yi izinin a xaukaka su, ma'ana: a tsarkake su daga dauxa, da wargi, da aiyuka ko zantukan da basu dace da masallatai ba".

            Kuma saboda kasancewar masallatai su ne tushen samun rabo, da yin dace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance "Idan ya dawo daga tafiya, yak an fara da masallaci, domin ya yi salla a  cikinsa", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Kuma masallatai xakunan Allah ne, kuma farkon wajibin kowani musulmi shi ne, tsarkake addini a gare shi, kuma kada ya roqi kowa a cikin masallatai baicin Allah, Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma, masallatai na Allah ne, kada ku roqi wani tare da Allah" [Jinn: 18].

            Kuma masallatai wurare ne wanda rayayyu ke amfani da su, kuma shigar da qaburbura a cikin masallatai yana cin karo da hakan, kuma hanya ce daga hanyoyin bauta ga wanin Allah.
Kuma yin savo abun qi ne, a kowani zamani da wuri, kuma zunubai suna qara muni idan aka yi su a cikin xakunan Allah (masallatai), kamar cin nama, da annamimanci, da kallon haram, da bayyanar sautin kaxe-kaxe a cikin masallatai, ta hanyar kafafen sadarwa (kamar waya).

Kuma yana daga MANUFOFIN MASALLATAI, haxa tsakanin zukata, da haxuwar kalma, don haka, baya halatta, a riqi masallatai a matsayin wurin kawo rarrabar kai, da qungiyanci, Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma waxanda su ka riqi wani masallaci domin cuta, da kafirci, da rarraba tsakanin zukatan muminai, da kuma jiran wanda ke yaqar Allah, da manzonsa, gabanin ginin wannan masallacin, kuma suna yin rantsuwa cewa, ba ma nufin komai ba face alheri" [Tauba:107].

Kuma duk wanda ya gina wasu gine-gine domin su yi kama da masallatan musulmai, kamar kaburbura, da wasunsu, to waxannan kamar masallacin cuta su ke, hasali ma sun fi shi tsananin muni.
Kuma asalin addinin musulunci shine kada a keve wuni wuri, da nufin yin ibada a cikinsa, saidai masallatai kawai, a ko'ina su ke, kuma dukkan masallatai sun yi tarayya kan ayi ibada a cikinsu, sai abinda aka keve masallacin haramin Makka mai alfarma, da shi na yin xawafi da makamancin hakan.

            BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
            Masallataiya, buwaya ce ga musulmai, kuma sune xaukakarsu, kuma alama ce ga addininsu.
            Duk wanda ya raya su ta hanyar yin salla a cikinsu, da ambaton Allah, sai Allah ya xaukaka shi, kuma ya bashi sa'adar zuci, ya kuma yaye masa qirjinsa.
            Kuma rayar da ilimi a cikin masallatai, ta hanyar karantar da alqur'ani da sunna, raya masallatai ne, kuma shine gininsu na haqiqa.
            Duk kuma wanda ya haramta abinda ke cikin masallatayya na alkhairi, ko ya hana isowarsa, to lallai falala mai girman yawa ta wuce shi.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
            "Wanda ke neman izzar xaukaka to, Allah ne ke da izza gabaxaya, zuwa gare shi ne Magana mai daxi ke hawa, kuma aiki na kwarai ke xaukaka shi. Kuma waxanda ke yin makircin munanan aiyuka suna da wata azaba mai tsanani, kuma makircin waxannan yana yin tasgaro" [Faxir: 10].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA, ya kuma amfanar da ni, da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima, Ina faxan maganata wannan, kuma ina neman gafara wa ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, Sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya kasance Mai gafara Mai rahama.
             
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya;  Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
Sallar jam'i, a cikin masallatai, da yin kiran salloli guda biyar a masallatai, suna daga alamomin musulunci. Kuma salla a masallaci yana daga manyan ibadodi, na samun kusanci ga Allah, kuma cikin wajibabbu. Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya nufi ya qona, wanda ya qi halartar sallar jam'i, kuma ya qirga wanda ya qi yin sallar jama'a daga cikin sifofin munafiqai, kuma Annabi bai yi izini wa makaho kan rashin zuwa jam'i saboda bashi da mai jagora ba. Kuma duk wanda ya ji kiran salla, sai ya qi amsawa, to bashi da salla saidai idan yana da uzuri,Ibnul-qayyim ya ce: "Duk wanda ya yi nazarin hadisai haqiqanin nazari, zai bayyana masa cewa, yin sallolin jam'i a masallatai farilla ne akan kowa".
Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Duk wanda zai faranta masa rai; ya haxu da Allah a gobe qiyama, yana musulmi, to ya kiyaye wadannan sallolin a lokacin da ake kiranSu, saboda lallai Allah ya shar'anta ma annabinsa (saw) hanyoyin shiriya, kuma lallai waxannan sallolin suna daga hanyoyin shiriya, kuma da dukkanku za ku yi sallah a cikin gidaddajinku kamar yadda wannan mai qin zuwa masallaci ke yin sallah a cikin gidansa, da kun bar sunnar annabinku, da kuma za ku bar sunnar annabinku to, da kun bace " Muslim ya ruwaito shi.

Kuma sallar mace, a cikin gidanta shi ya fi alkhairi akan sallarta a masallaci, kuma idan za ta fita dole ta lazimci lulluvi da hijabi, kuma ta nisanci dukkan abinda zai fitini mazaje, domin ta samu lada, ta kuma tunkuxe zunubai.

****
Kuma musulunci maxaukaki ne, mabuwayi, da masallatansa, da hukunce-hukuncensa, da kuma muminai. Kuma idan aka yaqi musulunci sai ya qara qarfi, idan kuma aka kyale shi, sai ya qara yaxuwa, kuma babu wani da zai iya hana yaxuwarsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Suna nufin su dusashe hasken Allah da bakunansu" [Tauba: 32].
Ibnu-kasirرحمه الله- ya ce: "Misalin waxannan mutanen su ne kamar misalin mutumin da ke son kasha hasken rana, ko hasken wata da furawar da yak e yi da bakinsa, kuma wannan bashi da hanyar cimma nufinsa. To haka, abinda Allah ya turo manzonsa da shi, babu makawa sai ya cika, ya samu bayyana, wannan kuma ya sanya Allah faxin: KUMA ALLAH YANA QI, FACE YA CIKA HASKENSA KUMA KODA KAFIRAI SUN QI" [Tauba: 32].

            Kuma duk abinda ke jeruwa ga musulmai na fitintinu da yaquka, da rusau, da fatattaka, da fin qarfi daga maqiya, suna tunatar da mu ne, kan komawa zuwa ga Allah, da salloli, da masallatai, da alqur'ani, Allah (سبحانه) ya ce: "Domin ya xanxana musu sahen abinda suka aikata, ko za su koma (zuwa ga Allah)" [Rum: 41].

            Kuma haqiqa Allah ya yi alqawarin bada nasara ga muminai, koda kuwa sabuban samun nasarar sun yi rauni, ko an rasa su. Kuma Allah ya taimaki musulmai a yaqin badar, alhalin su 'yan kaxan ne. kuma mushirkai daga ko ina sun haxu akan qaqaba wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) dokar hana shigi da fici, da kuma yaqarsa, Sai Allah ya turo musu a lokacin yaqin Ahzab, wata iska da rundunar da ba su ga irinta ba, sai mushirkai kansa ya rarraba, kuma suka tave.

            Allah Mai ikon taimakon bayinsa muminai ne, kuma saboda hikimar da ta ke cikin jarrabawa, zai iya bada nasara ga maqiya akansu, domin ya samu wanda za su yi mutuwar shahada, ko don ya ga waxanda za su yi haquri akan musibu, ko rataya zukatansu ga Allah, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Da Allah ya yi nufi da sai ya xauki fansa daga gare su (ba tare da yin yaqi ba), sai dai kuma (ya wajabta jihadi) domin ya jarrabi sashenku da sashe" [Muhammadu: 4] . kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma kada ka yi gaggawa akansu, lallai muna musu qidayar ajali ne qidaya" [Maryam: 84].

            Kuma addu'a it ace takobin mumini, a halin walwala da qunci.
            Yin xa'a kuma yana janyo samun nasara, kuma yana gaggautar da zuwansa, "Kuma Ubangijinka ba zama mai gafala ba, ga abinda ku ke aikatawa" [Hud: 123].

            Sannan ku sani; Lallai  Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga Annabinsa …
Sai yace, a cikin mafi kyan littafin da ya saukar: "Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
            Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.
            Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
            Ya Allah Ka sanya qasashensu su zama wurin aminci da zaman lafiya, Ya ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka haxa kalmarsu akan gaskiya da shiriya, Ya Ubangijin halittu.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga shiriyarka, ka sanya aikinsa cikin yardarka.
Kuma ka datar da xaukacin jagororin lamuran musulmai zuwa ga aiki da littafinka, da yin hukunci da shari'arka, Ya ma'abucin girma da karramawa.
            Ya Allah! Ka taimaki rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka taimake su akan maqiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi.
            "Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
            Ya Allah Ka karva wa mahajjata hajjinsu, ka mayar da su, garurrukansu, suna kuvutattu, masu riba, Ya ma'abucin girma da karramawa.

       Bayin Allah!!!
            "Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...