2018/04/27

HUDUBAR 11 Sha'aban 1439 Ta Dr Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 11/SHA'ABAN/1439H
daidai da 27/AFRILU/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA

Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AAAA,,, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah,
Alkhairi a hannayensa suke,
Kuma Shi Mai iko ne akan komai,
Wanda ke tsaye akan kowace Rai da abinda take aikatawa, ta hanyar cikewa kowace Rai da abinda ta aikata, kuma Ubangijinka baya zalunci dai-dai da kwayar zarrah, idan aikin ya kasance mai kyau ne, sai ya ninninka shi, kuma ya bayar daga wurinSa lada mai girma.
Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina godiya a gare shi, akan falalarSa mai girma.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masani Mai bada labari.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu, shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai bushara da gargadi, kuma fitila mai haskakawa.
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu wanda aka turo shi da littafi Mai haskakawa, da iyalansa da sahabbansa, wadanda Allah ya daukaka addini da su, kuma da su, Allah ya kaskantar da shirka walakantacce.

Bayan haka:
Ku bi Allah Ta'alah ta hanyar gaggawar aikata alkhairori, da nisantar haramun; domin ku rabauta da darajoji madaukaka, kuma ku tsira daga ababe masu halakarwa.

Ya ku, Musulunci … !!!
Lallai Allah, ya muku alkawari na gaskiya, kuma babu karyawa ga alkawarinsa, kuma babu mai yin gyara ga hukuncinSa; kuma Allah ya yi alkawari ga bayinSa masu da'a da samun rayuwa mai dadi, a duniyarsu, kuma ya musu alkawarin samun mafi kyan sakamako a lahirarsu; ta hanyar sauke musu yardarSa, da jiyar da su dadi da ni'ima tabbatacciya, a cikin Aljannar dawwama, tare da Annabawa da Salihai, wadanda suka bi hanyar Allah madaidaiciya, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma da lallai mutanen alkaryu sun yi imani, kuma suka yi takawa, hakika da mun bude albarkoki akansu daga sama da kasa", [A'araf: 96].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma da dai ma'abuta littafi sun yi imani kuma sun yi takawa, hakika da mun kankare miyagun ayyukansu, daga gare su, kuma da mun shigar da su gidajen Aljannar ni'imah * Kuma da lallai su, sun tsayar da Attaura da Injila, da abinda aka saukar zuwa gare su, daga UbangijinSu, hakika da sun ci daga samansu, da kuma daga karkashin kafafunsu" [Ma'ida: 65-66]. Ma'ana, da ma'abutan littafi, sun yi imani da Alkur'ani, kuma sun yi aiki da shi, tare da imaninsu da littafin da aka saukar musu, ba tare da jirkita sakon cikinsa ba, to, da Allah ya rayar da su rayuwa daddada a nan Duniya, kuma ya shigar da su Aljannar ni'ima a lahira.
        Kuma Allah ya ce, a inda yake bayanin yadda annabi Nuh –عليه السلام- ya ke kwadaitar da mutanensa: "Sai na ce, ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai ne shi ya kasance Mai yawan gafara * Sai ya saki ruwan sama akanku na-mamako * kuma ya karfafe ku da wasu dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku lanbuna, kuma ya sanya muku koramu" [Nuh: 10-12].
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah –رضي الله عنه-, ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Allah Ta'alah ya ce: Wanda ya yi adawa da waliyyina, hakika ina shelanta masa yaki, Kuma bawana bai kusance ni da wata ibadar da tafi soyuwa a gare ni ba, fiye da abinda na farlanta masa, kuma bawana ba zai gushe ba, yana kusanta ta da nafilfili face na kaunace shi, Kuma idan na so shi, sai in kasance jinsa wanda yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake damka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma lallai idan ya roke ni, hakika zan bashi, kuma idan ya nemi tsarina, lallai zan tsare shi. Kuma ban yi taraddadi kan wani aikin da nine mai aikata shi ba, kamar yadda nayi taraddadi wajen cire ran mutum mumini; yana kin mutuwa, ni kuma ina kin munana masa". Bukhariy ya ruwaito shi.
        Wannan ya nuna cewa lallai Allah Ta'alah da ludufinSa da karamarSa da jin-kanSa da rahamarSa da ikonSa, yana jibintar lamuran bayinSa masu da'a a gare shi, kuma yana juya lamuransu da mafi kyan tsari, a rayuwarsu ta duniya, da bayan mutuwarsu.
        Kuma alkawalin Ubangijinmu gaskiya ne; ba wani abu daga cikinsa da yake tashi, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya Ubangijinmu, lallai kai ne mai hada mutane ga yinin da babu kokonto akansa, Lallai ne Allah baya saba alkawali" [Ali-imrana: 9].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Ya Ubangijinmu, Kuma ka bamu abinda ka alkawarta mana, a harshen manzanninka, kuma kada ka tozarta mu ranar kiyama, lallai ne kai baka saba alkawali" [Ali-imrana: 194].
        Kuma Allah ya musu alkawarin gaskiya, a ranar lahira a cikin fadinSa: "Allah ya yi alkawali ga muminai maza da muminai mata, da shiga gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana daga karkashinsu, suna dawwama a cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin Aljannar, kuma yarda daga Allah ce mafi girma (akan shiga Aljanna), Wannan kuma shine babban rabo mai girma" [Tauba: 72].
       
        Kuma muminai suna ganin abinda Ubangijinsu ya alkawarta musu a rayuwarsu ta duniya, kuma ladan Allah yana zuwa musu bi-da-bi, kuma ni'imomin Allah suna saduwa da su, kuma suna bibiyansu, kamar yadda Allah (تعالى) ya ce: "Sai Allah ya saka musu da sakamakon duniya, da kuma kyakkyawan sakamakon Lahira. Kuma Allah yana son masu kyautatawa" [Ali-imrana: 148].
        Kuma a lahira, za su samu ladan da aka alkawarta musu, da wata ni'ima wacce bata yankewa, Allah (سبحانه) ya ce: "Shin fa, wanda muka yi ma wa'adi mai kyau, sa'annan shi mai haduwa da shi ne, yana zama kamar wanda muka jiyar da shi dan dadi irin na rayuwar duniya, sa'annan shi a Ranar kiyama yana daga masu shiga wuta?", [Kasas: 61].
       
Kuma, kamar yadda Allah ya yi kyakkyawan alkawari ga muminai masu biyayya, haka Allah ya tanadi narkon azaba ga kafiran da suke musun Allah, da masu sabo masu tsaurin kai, Kuma duk abinda ya gargade su na azaba abu ne mai aukuwa a gare su; Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Kuma wadanda suka kafirta suna jin dan dadi a Duniya, kuma suna ci kamar yadda dabbobi ke ci, kuma wuta itace mazauni a gare su", [Muhammad: 12].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma duk wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to lallai yana da wutar Jahannama, suna masu dawwama a cikinta, har abada", [Jinn: 23].
Kuma rayuwar kafirai da masu taurin kai, a Duniya itace mafi munin rayuwa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya bijire daga Anbatona (wato, Kur'ani), to lallai yana da rayuwa mai kunci, kuma za mu tayar da shi a ranar Kiyama yana makaho", [Daha: 124]. Koda kuwa an basu abin Duniya!
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kada dukiyoyinsu da diyansu su burge ka ko baka sha'awa, lallai Allah yana nufin ya musu azaba da su a rayuwar Duniya, kuma rayukansu su fita alhalin suna kafirai" [Taubah: 85].

        Kuma hakika an jarrabi Mutum da ababen da suke kawar da shi daga abinda zai amfanar da shi, su kuma aukar da shi cikin wadanda za su cutar da shi, a matsayin ibtila'i da jarrabawa, masu sanyaya guiwa kan ayyukan da'o'i, masu kawata aikin sabo; domin Allah ya san wanda zai yi gwagwarmaya da ransa, ya saba wa son zuciyarsa, daga wadanda za su biye wa rayukansu kan son zukatansu, sai su biye wa Shedanunsu, Sai kuma Allahn ya fifita shiryayyu da basu darajoji, ya kuma yi ukuba ga masu bin soye-soyen zuciya masu halakarwa da ramuka a cikin wuta, Allah (تعالى) ya ce: "kuma lallai ne, za mu jarrabe ku, har mu san masu jihadi daga cikinku, da masu hakuri, kuma za mu jarraba labarunku" [Muhammadu: 31].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wadanda suka yi kokari wajen neman yardarmu, lallai ne za mu shiryar da su hanyoyinmu, kuma lallai ne Allah, tabbas yana tare da masu kyautatawa ga addininsu", [Ankabut: 69].

        Kuma lallai Rai, tana daga cikin manyan makiyan Mutum, kuma Shaidan baya iya shigar wa Mutum sai ta hanyar ita Rai, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne rai, hakika mai yawan umarni ne da mummunan aiki, sai ga abinda Ubangiji ya yi rahama", [Yusuf: 53].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ba komai suke bi ba face zato, da abinda rayukansu ke so" [Najm: 23].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya sabawa rowar ransa, to wadannan sune masu babban rabo" [Tagabun: 16].

        Kuma Rai da abinda take sifantuwa da shi; na jahilci da zalunci, tana nisanta ma'abucinta daga gaskata wa'adin Allah, kuma tana sace guiwar mutum daga ayyukan tsayuwa ga addini, sais u karkatar da mutum daga daidaituwa akan tafarkin Ubangiji, Ibnul-Kayyim –رحمه الله تعالى- ya ce: "Duk wanda ya san hakikanin Ransa, da dabi'unta, to ya san ita ce mabubbugar dukkan sharri, kuma matattarar duk wani aiki mummuna. Kuma zai gane cewa lallai kowane alherin da aka gani tattare da ita, to tsagoron falalar Allah ne wanda ya yi baiwa da shi a gare ta, ba daga wannan ran ba ne, kamar yadda Allah (تعالى) yake cewa: Ba domin falalar Allah akanku da rahamarsa ba, da wani daga cikinku har abada bai tsarkaka ba", maganarsa ta kare.

        Kuma Rai bata kubuta daga jahilci da wauta ba, face ta hanyar ilimi mai amfani, wanda shari'a ta zo da shi.

        Haka, Rai bata kubuta daga zalunci, sai ta hanyar aiki na kwarai.

        Kuma babu makawa, Musulmi koyaushe ya rika nuna kwadayinsa zuwa ga Allah; yana rokonsa domin gyaruwan Ransa; An ruwaito daga Zaid bn Arkam (رضي الله عنه) ya ce: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana cewa: Ya Allah! Ka baiwa Raina takawarta, ka tsarkake ta; domi kai ne mafi alherin mai tsarkake ta, kai ne masoyinta kuma Majibincinta. Ya Allah! Lallai ina neman tsarinka daga ilimi maras amfani, da zuciyar da bata da khushu'i, da Rai wanda bata koshi, da addu'ar da ba a amsa mata", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Tirmiziy ya ruwaito daga hadisin Imrana bn Husain: Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ilmantar da Husaini kalmomi biyu, wadanda zai rika addu'a da su: Ya Allah! Ka nusar da ni shiriyata, kuma ka tsare ni daga sharrin Raina".

        Kuma idan Rai bata tsarkaka ta hanyar ilimin shari'a da aiki na-kwarai ba, Sai jahilci da zalunci su dabaibaye ta, sai ta hade; da son zuciya, daga nan sai ma'abucinta ya karyata alkawalin Allah, ya biye wa sha'awowinsa, sai kuma ya halaka ya dulmuya cikin ramukan hasara da azaba da wulakanci, sai ya yi hasarar duniyarsa da Lahira, Allah (تعالى) yana cewa: "Babu wanda yafi bacewa fiye da wanda ya biye wa son zuciyarsa, ba tare da wata shiriya daga Allah ba, Lallai ne Allah baya shiryar da mutane azzalumai" [Kasas: 50].

        Idan kuma Rai ta samu tsarkaka ta hanyar ilimi mai amfani da aiki na-kwarai, to sai ta rikide zuwa ga Rai wanda take gaskata alkawalin Allah, natsattsiya, wacce take mayar da lamuranta zuwa ga Allah, wanda ake mata alkawalin samun karamomi a lokacin mutuwa; Allah (تعالى) ya ce: "Ya ke wannan Rai natsattsiya * Ki koma zuwa ga Ubangijinki kina mai yarda, abar yarda * sai ki shiga cikin bayina, kuma ki shiga Aljannata" [Fajr: 28-30].

        Kuma mai yanke dukkan hanyoyin alkhairi, mai kira zuwa ga dukkan sabo da sharri, shine makiyin mutum; wato Shedan abin korewa daga dukkan rahama, mai dauda, mai najasa, Allah ya tsare mu daga gare shi; kuma Allah ya sanya shi ya zama ibtila'i ko jarabawa ga mutane da aljanu; Kuma wanda ya masa da'a zai kasance a wani matsayi mafi dauda, Wanda kuma ya saba wa Shedan, zai kasance a mafificin wurin zama (a Lahira).
        Jin dadin Iblisu da farin cikinsa da ni'imarsa tana cikin batar da halittu da kawo barna; yana kiran mutum zuwa ga karyata alkawarin wa'ad da wa'id (na rahama, da narko), kuma yana kawata masa ababen haramun, kuma yana katange shi daga aikata farillai da mustahabbai, kuma yana sanya masa gurace-gurace na barna, kuma yana rudarsa da munanan waswasi, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai Shedan makiyi ne a gare ku, sai ku rike shi makiyi, kuma lallai yana kiran kungiyoyinsa ne domin su kasance ma'abutan wutar Sa'ira" [Fadir: 6].
Kuma Allah (سبحانه) yake magana akan Iblisu; da cewa zai yi huduba ga mabiyansa a cikin wuta: "Kuma Shedan zai ce, a yayin da aka kare lamari, Lallai ne Allah ya yi muku alkawalin gaskiya, Ni kuma sai na muku wa'adi, sai na karya muku, kuma babu wani karfi a gare ni akanku, face na kira ku, sai kuka amsa mini; saboda haka; kada ku zarge ni, sai ku zargi kayukanku. Kuma ni ba zan zama mai amfani a gare ku ba, kuma ba za ku zama masu amfani a gare ni ba. Lallai na barranta da abinda kuke hada ni da shin a shirka, gabanin wanga lokacin. Lallai ne azzalumai suna da azaba mai radadi" [Ibrahim: 22].
        Kuma lallai Shaidan tare da 'Dan-Adam yana da halaye guda bakwai;
1.  Domin Shedan yana kiransa izuwa ga kafirci, Allah ya tsare, kuma idan mutum ya amsa masa ga wannan, to lallai Shedan ya kai makura wajen batar da shi, sai kuma ya sanya shi, cikin rundunoninsa.
2.  Idan kuma bai amsa masa kan kafirta ba, To sai ya kira shi zuwa ga aikata bidi'a;
3.  Idan kuma ya tsira daga yin bidi'a ta hanyar riko da sunnah, da yin aiki da littafin Allah da hadisan Annabi SAW, to sai ya kira shi ga aikata manyan laifukan kaba'irai, har su rinjaye shi, su halakar da shi.
4.  Idan kuma bai amsa masa wajen yin manyan zunubai ba, sai ya kira shi zuwa ga aikata kananan laifuka na zunubai; yana mai sanya shi jin sauki ko raina su, domin ya doge akan aikata su, ya kuma yawaita, har su zama manyan laifuka sakamakon tabbatuwansa akansu, kuma sai ya halaka saboda nisantar tuba.
5.  Idan kuma bai amsa masa wajen yin kananan laifuka ba, sai ya shagaltar da shi da shagaltuwa da ababen halal, a madadin yawaita ayyukan da'a, sai ya shagaltar da shi da hakan kan yin guzuri da kokarin neman lahiransa.
6.  Idan kuma ya tsira daga wannan, to sai ya shagaltar da shi da ayyukan da ba sune suka fi falala ba, domin ya bar wadanda suka fi girman falala, saboda ladansa ya ragu; wannan kuma saboda ayyukan kwarai suna da fifiko cikin ladaddakinsu.
7.  Idan Shaidan ya gagara samun iko, akan wadancan gaba dayansu, to sai ya tirsasa rundunarsa da mabiyansa akan mumini, ta hanyar nau'ukan cutarwa da dangogin sharri.

        Kuma babu tsira daga sharrin Shedan, sai ta dawwama kan neman tsarin Allah, daga Shedan, da dawwama kan ambaton Allah Ta'alah, da kiyaye salloli a cikin jam'i saboda yin hakan (jam'i) garkuwa ne, mafaka, kuma tsira, da kuma ta hanyar tawakkali ga Allah Ta'alah, da dawwama kan yakar Shedan, da nisantar zaluntar bayi, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma imma wata fizga daga Shedan ta fizge ka, sai ka nemi tsarin Allah, lallai ne shi Mai ji ne Masani" [A'araf: 200].

        Kuma yana daga abinda ke katange mutane daga gaskiya ko tabbatuwa da tsayuwa akan addini, da son alkhairi (ya katange shi daga hakan gaba daya): SON DUNIYA DA YARDA DA ITA, AKAN LAHIRA, DA TARA DUNIYA DAGA HALAL DA HARAM, DA KARKATA ZUWA GARE TA DA MANCE GIDAN LAHIRA, Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne wadanda basu kaunar gamuwa da mu, kuma suka yarda da rayuwar duniya, kuma suka natsu da ita, da wadanda kuma suke gafalallu ne daga ayoyinmu * wadannan matattararsu Jahannama ce, saboda abinda suka kasance suke aikatawa" [Yunus: 7-8].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Shin kuna yarda da rayuwar Duniya ne daga Lahira? To, jin dadin rayuwar Duniya a cikin lahira, bai zama ba face dan kadan" [Taubah: 38].
        Kuma Duniya rayuwarta adawa ce ga mutum, idan har ta mamaye zuciyar mutum, sai ya shagaltu da ita, ya kuma bijire daga yin aikin lahira, kuma mafi yawan mutanen da ke bayan kasa suna fifita rayuwar Duniya, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, kuna zabin rayuwar Duniya ne * Alhali, lahira ita ce mafi alheri, kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma bone ya tabbata ga kafirai daga azaba mai radadi * wadanda suka fi son rayuwar Duniya fiye da ta Lahira, kuma suna kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta karkace, Wadannan suna cikin bata mai nisa" [Ibrahim: 2-3].

        Kuma babu hanyar tsira daga sharrin Duniya da cutarwarta, kuma babu kariya daga munanan halayenta, sai ta hanyar neman dukiya ta hanyoyin halal, wadanda aka shar'anta, da kuma jin dadi a cikinta da abinda Allah ya halatta, ba tare da an ketare iyaka ko an yi facaka da almubazzaranci ba, kuma ba tare da an yi girman kai ko takabburanci ga halittu ba, kuma ba tare da an nuna farin ciki da alfahari da ita ba, kuma ba tare da yin azarbabiya da abin duniya kan hakkokikn bayi ba.
        Kuma mutum dole ya san hakikanin duniya, da kasancewarta takaitaccen jin dadi ne na rudi, mai saurin gushewa, wanda halinta ka iya canzawa. Kuma ya rika tuna wannan lamari a koda-yaushe, saboda cikin haka, gyaruwar zuciyarsa ta ke; An ruwaito daga Almustaurad Alfihriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai shi ya ce: "Duniya kwatancinta da Lahira, ba komai ba ne, sai kamar dayanku ya sanya yatsarsa a cikin teku, sai ya ga da mai zai koma", Ahmad da Tirmiziy da Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana su ka ruwaito shi.
        Kuma sai mutum ya kasance cikin tsoron sharrin Duniya, da mummunar akibarta.
        Kuma ya ji tsoron kada Shaidan ya ce masa, Ai Allah ya baka wannan Duniyar ne, saboda falalarka, da ilimin da kake da shi na hanyoyin samunta, kamar yadda Shedan ya rudar da Karuna da irin wannan maganar, sai karshensa ya zama kamar yadda kuka sani.
        Kuma wani lamari mai muhimmanci, wanda ke wajaba akan mutum a cikin wannan Duniyar; shine: Ya fitar da hakkin Allah, daga cikin abinda yake da shi na Duniya, haka ya bayar da hakkokin halittu na wajibi, wanda sune: Bayar da zakkah da ciyar da iyalai da 'ya'ya, da bako, da taimakon mabukata, da ciyarwa ta dukkan kofofin alkhairi, da ikhlasi; ba tare da riya ko yin aiki domin a ji a fada, ko neman yabon mutane ba; saboda Riya tana lalata ayyuka.
        Kuma lallai manyan sahabbai ya kasance suna da tarin dukiya, saidai kuma sune suka fi dukkan mutane gujewa Duniyar, Abu Sulaiman ya ce: Usman da Abdurrahman bn Auf sun kasance taskoki ne daga cikin taskokin Allah a duniyarsa, suna ciyar da dukiyarsu cikin biyayya a gare shi, kuma mu'amalarsu ga Allah ta kasance a cikin zukatansu; su biyu.
Kuma ya zo cikin hadisi cewa: Ka guje wa Duniya (zuhudu) sai Allah ya so ka, kuma ka guje wa abin hannun mutane, sai mutane su soka. Ibnu-Majah ya ruwaito shi daga sahl bn sa'ad.
Ma'anar gujewa abin hannun mutane shine, kada mutum ya musu ta'addaci, ko ya zalunce su cikin hakkokinsu, ko ya yi fatan ganin gushewar ni'imomi daga gare su, kuma ya debe tsammani daga abin hannunsu.
Kuma yana daga cikin ZUHUDU ABIN YABO: Kada Mutum ya so daukaka cikin abin Duniya; Allah (تعالى) ya ce: "Wancan shine gidan lahira wanda muke sanya ta ga wadanda basu nufin daukaka a cikin rayuwar Duniya, kuma basu son barna, kuma akiba mai kyau tana ga masu takawa" [Kasas: 83].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah,
Yabo na Ubangijina ne cikin rayuwar Duniya da Lahira, Yana da sunaye mafiya kyau

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Muna siffanta shi, kuma muna yabonsa da sifofinsa madaukaka,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, zababbe.

Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa, masu takawa.

Bayan haka … !!
Ku yi takawar Allah, iyakar takawa, kuma ku yi riko da addininsa wanda yafi karfi.

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai Ubangijinmu ya ce: "Ya ku mutane, lallai alkawalin Allah gaskiya ne; don haka kada Rayuwar duniya ta rudar da ku, kuma kada Shedan mai rudi ya rude ku game da Allah" [Fadir: 5].
Ya zo cikin wani hadisi cewa: "Mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga Ransa, kuma yake aiki ga abinda ke bayan mutuwa. Gajiyayye kuma, shine wanda ya bi son zuciyarsa, sai ya ke kwallafa gurace-gurace ga Allah", Hadisi ne hasan, daga Shaddad.
Kuma An ruwaito hadisi daga Ibnu-Abbas, daga Annabi, cewa: "Lallai Mala'ika yana da wata shafa ga zuciya; shafar mala'ika ita ce, gaskata alkawali, da gaskata labarin gaskiya. Kuma shima Shaidan yana da shafa cikin zuciya, shafar Shedan kuma ita ce karyata alkawali, da karyata labarin gaskiya".
Kuma musulmi wajibi ne ya rika hisabi ga Ransa, yana kokarin tsayar da ita akan tafarki madaidaici, kuma ya kiyaye makircin Shaidan, da bin son zuciyarsa, da ruduwa da rayuwar Duniya; domin jin dadin cikinta kadan ne.

        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...