2019/07/18

Dr Salah Albudair MARABA DA MAHAJJATA 16 Zulkiidah 1440










HUƊUBAR MASALLACIN ANNABI SAW
JUMA'A 16/ZULƘI'IDAH/1440H
Daidai da 19/Yuliyo/2019M






LIMAMI MAI HUƊUBA
Shehun Malami Dr. Salah ɗan Muhammadu Albudair








TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA


بسم الله الرحمن الرحيم
Ya ku Musulmai 
Waɗannan fa Matafiyan mahajjata ne suka kusanto, suna keta sahara mai halakarwa, suna kutso falalen ƙasa da kilomitoci
    Sun jigata a cikin tafiyarsu, sannan sun zo bi-da-bi
Tawaga tana biye da tawaga a cikin sahara

Ya fatana! shin zan tashi na wayi gari
Sai na sunsuni ciyawar izkhiri ta Makkah da karan shukinta (na jalil)

Sai kuma na kunce jakata a kasar Annabi
Domin na kwana a harami maɗaukaki ina baƙo


Sau dayawa, yawale mai yawo da tafiye-tafiye, yanki-yanki, ƙasa-ƙasa, birni-birni, mai yawaita kai-komo da bulaguro, wanda yake ƙarar da taronsa da sisi akan hakan, Sai ka samu, ya yi nawa da sakaci kan tafiyar sauke ibadar hajji, ba tare da uzuri ba, na tsawon shekaru, har ya tsufa.

Baya burge zuciyata, sautin ƙaramin tsuntsu mai rera waƙa
Haka kuma murmushin fikar ƙaramin yaro a lokacin bulaguro

???
Saboda ba kowane bulaguro ke ƙayatar da Ni ba,
???
Saidai bulaguro zuwa ga hajji wanda za a saka mana da Aljannah
Wannan kuma baiwa ce daga kyautar Allah Makaɗaici


YA KU MUSULMAI!!!
Makkah da Madinah gari biyu masu haske da tsarkaka, sune wuri biyu da suka fi sauran garurruka daraja, muɗlaƙan, kuma sune suka fi kowane bagire a doron ƙasa girman matsayi da ijma'in Maluma (ba tare da saɓani ba);

Saboda Makkah nan ne wurin da wahayi ya fara sauka, maɓuɓɓugar addini, gari amintacce, alƙiblar Musulmai, makarkata ga zukatan Muminai, uwar alƙaryoyi, wanda bata da makamanci a cikin birane, kuma bata da tsara a cikin kasashe.

Ita kuma Madina, ita ce gari abin so ga Masoyinmu SAW, ita ce gidansa matabbatarsa, kuma garin da ya yi hijirarsa ta farko, garin sunnah, mafakar imani kuma ganuwar imani mai bashi kariya, kuma mafakar Musulunci da Musulmai.

Wahayi bai sauka ba, face a ƙasar Makkah da Madinah, kuma fitilar Manzanci bata haska ba sai akan ƙasarsu, kuma Annabi SAW bai rayu ba face akan turɓayansu.
 
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas -Allah ya ƙara yarda a gare su- ya ce:
Manzon Allah -sallal Lahu alaihi wa sallama- a ranar da aka je yaƙin buɗe garin Makkah, ya faɗa cewa:

"Lallai Allah ya haramta wannan gari (Makkah), a ranar da ya halicci sammai da ƙasa, don haka; Makkah harami ne da haramtawar Allah, har zuwa ranar ƙiyama. Kuma lallai yaƙi a cikinsa bai halatta ga wani Mutum a gabanina ba, kuma nima bai halatta a gare ni ba, sai a cikin wani zangon lokaci na yini, kuma lallai Makkah harami ne da haramtawar Allah, har zuwa tashin ƙiyama; ba a yanke ƙayar harami, ba a korar abin farautar harami, ba a ɗaukar abin tsuntuwar harami, sai ga wanda zai bada cikiyarsa, ba a cirar ciyawar da ta tsira a cikinsa",
Sai Abbas ya ce: Saidai ciyawar izkhir, saboda amfanin maƙeransu, da bukkokinsu?
Annabi ya ce: "Sai dai ciyawar izkhir". Bukhariy [1834, 3189], da Muslim [1353], suka ruwaito shi.

Kuma Manzon Allah SAW ya mayar da Madina harami, kamar yadda annabi Ibrahima ya mayar da Makkah harami, kuma ya karkata zuwa ga Madina sai ya ce: Lallai Madinah harami ne amintacce.

Don haka, idan ganyen bishiyar harami da abin farautar harami su ka kasance masu alfarma ababen girmamawa, to yaya alfarmar Musulmi, da alfarmar hajji, da kuma alfarmar Mahajjata, da amincinsu da ayyukansu na hajji!; don haka baya halatta Musulmi ya haifar da abinda zai kawo tasgaro ga amincin gari mai alfarma, ko tasgaro ga tsarin garin, da natsuwarsa, da walwalar waɗanda suka nufo Makkah da mazauna cikinsa, kuma bai halatta Musulmi ya cutar da Musulmai da zancensa ko aikinsa ba.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya yi nufin ilhadi (karkatar da gaskiya) a cikinsa da zalunci, za mu ɗanɗana masa wata azaba mai radadi" [Hajji: 25].

Don haka, idan niyyatar zalunci da yin ƙudurin ilhadi ko karkatar da gaskiya yana hukunta uƙuba mai raɗaɗi, to yaya kuma ga Mutumin da ya yi ta'addancin aikata laifi mai haddi, ko ya aikata mummunan zunubi, ko ya zubar da jini (kisa), ko ya firgitar da amintattu, ko ya cutar da mai rauni, ko ya zalunci miskini, ko ya cuci Mahajjaci; ta hanyar gurɓata aƙidarsa, ko ha'intar alkawalinsa, ko cin amanarsa, To menene zai kasance sakamako da ukubarsa a wurin Allah, alhalin kuma ya keta alfarmar lokaci, da wuri, da Mutum!

Ɗana! Kada ka yi zalunci a Makkah; ƙanƙani ko babba
Ka kiyaye alfarmominta –Ya kai Ɗana- kada mai ruɗi ya ruɗe ka

Ɗana, lallai wanda ya yi zalunci a Makkah zai haɗu da sharrori
Domin za a bugi fiskarsa, kuma za a tuntsura shi wutar sa'ira akan kumatunsa

Ɗana, lallai ni na jarraba hakan, sai na samu mai yin zalunci a Makkah yana yin hasara
Allah ne ya mata baiwar aminci, da abinda aka gina a cikinta na benaye

Kuma Allah ya amintar da tsuntsayen cikinta, domin tsuntsu ba su da tsoro a Makkah

Giwaye, an halakar da rundunarsu ana jifansu a garin da duwatsu
Sai ka ji, idan ana baka labari, kuma ka fahimci yaya ƙarshen al'amura suke kasancewa

Yana shiga ma'anar zalunci da ilhadi a Masallacin harami: Aikata laifukan haram a Makkah, ko neman halatta su, kamar bayyanar da shirka da bidi'oi, da aukawa cikin zina da shan giya, da sace-sace, da cinye dukiyoyi, da makirci da wayo, da ɗaga tutoci domin raya bangaranci, da bidi'oi, da alamomin shirka, da shuka fitina da rura wutar saɓani da haifar da banbance-banbance a tsakanin Mahajjata, da ɗaukar taron hajji a matsayin wurin yaɗa jita-jita na ƙarya, da lalatattun aƙidu, ko yaɗa sabubban ƙiyayya da adawa, saboda wasu manufofi na siyasa, ko ƙabilanci ko ɓangaranci ko aƙida ko mazhaba.
Kuma hajji da waɗannan wuraren masu tsarki, lallai suna da girma da tsarkin da yafi ƙarfin a mayar da su wuraren yaɗa waɗannan ayyukan masu muni. Kuma al'amarin hajji da amincinsa yana ga hannaye masu ƙarfi, masu ginawa, masu bada kariya, masu tausayi, wanda ba za su bar miyagun Mutanen da suke nufin gurɓata lafiyar hajji, ko siyasantar da shi ba, domin shugabannin za su hana miyagun cimma manufarsu ko kaiwa ga samun burinsu.


YA KU MUSULMAI!!!
Wajibi ne akan 'yan Makkah da Madina da Masu zama a cikinsu, da sauran Mahajjata da masu umrah da ziyara, su riƙa girmama waɗannan wuraren masu tsarki, suna kiyaye su suna basu kariya, suna tsarkake su daga ayyukan saɓo da munanan laifuka ababen ƙi masu halakarwa.

Mummunan aikin da aka yi a harami ba a ninka shi ta fiskar adadi, saidai ya fi girman laifi, kuma ya fi tsananin zunubi, akan laifin da aka yi a wurin da ba harami ba.
Ibnul-ƙayyim –Allah Ta'alah ya yi masa rahama- ya ce: "Yin mummunan laifi a harami da kasar harami (Makkah), da kuma akan shumfuɗar Allah (Masallaci) yafi girman muni, akan aikata laifin, a wani ɓangare na Duniya".
Kuma ya ce, a cikin littafin Maɗalibi ulin nuha: "Kuma ana ninka kyawawan ayyuka da munana idan aka yi su a wuri mai daraja, kamar Makkah da Madinah da Baitul Maƙdis, da kuma a cikin Masallatai, haka kuma idan aka yi su a wani zamani mai falala, kamar ranar Juma'a, da watanni huɗu masu alfarma, da kuma a kwanakin watan azumi".
Shehun Malami Mar'iy bn Yusuf Alkarmiy ya ce: "Lallai an sani daga shari'a mai haske da addini miƙaƙƙe, cewa zunubi yana ninkuwa a wurare masu daraja da halaye maɗaukaka, to haka lamarin yake a wurare masu daraja. Sa'annan ya ce: Kowane wuri, ko zamani wanda yafi daraja, to saɓon Allah a cikinsa yafi muni, domin baƙar tawada tafi bayyana ga farin abu".

Nawawiy –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Zaɓaɓɓiyar magana itace, lallai yin makwabtaka da ɗakin Allah da kuma Masallacin Manzon Allah (jiwaar) a Makkah da Madina mustahabbi ne, sai ga wanda zato ya rinjaya masa cewa, zai auka cikin lamurra abin zargi, ko sashensu. Kuma haƙiƙa halittun da ba za a ƙididdige su ba, daga magabatan al'umma da wanda suke a bayansu, daga cikin waɗanda ake koyi da su, sun aikata mujawaran (a Makkah da Madinah)".
Kuma Ƙurɗubiy –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Haka kuma, shari'a a wurare dayawa ta bayyana cewa, lallai duk lokacin da alfarma ta ninku, sai aka keta su, to uƙubar itama sai ta ninku".
Kuma Shekhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Yin saɓo a kwanakin da ake girmamawa da wuraren da ake girmamawa, zunubinsu da uƙubarsu yana yin kauri, gwargwadon falalar zamanin, da wurin".

Kuma Ƙurɗubiy –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Kuma idan Allah Subhanahu ya girmama abu, ta ɓangare guda, to sai ya zama yana da alfarma guda ɗaya, idan kuma ya girmama shi ta ɓangarori biyu, ko ɓangarori dayawa, sai alfarmarsa ta kasance mai yawa, to sai a ninninka uƙuba akansa idan aka yi mummunan aiki, kamar yadda ake ninka lada idan aka yi aiki kyakkyawa; domin wanda ya yi biyayya ga Allah a cikin wata mai alfarma, a kuma gari mai alfarma, to ladansa ba kamar na Mutumin da ya yi masa biyayya a watannin da basu da wata alfarma, ko a garin da ba harami ba. Haka wanda ya masa biyayya a watan da bashi da alfarma, amma a gari mai alfarma, baya zama daidai da wanda ya masa biyayya a watan da bashi da alfarma, a kuma garin da bashi da alfarma".

YA KU MUSULMAI!!!
Ku girmama ababen da Allah ya basu alfarma a cikin halin haramarku da wajensa, kada kuma ku ƙetare iyakokinSa, kada ku halatta wurare masu alfarma, Allah Ta'alah ya ce: "Wannan kuma, saboda wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah حرمات الله, to shine mafifici a gare shi a wurin UbangijinSa" [Hajji: 30].
Alfarmomin kuma sune: Girmama mash'arul harami (wuraren hajji), da ɗaki mai alfarma, da Masallaci mai alfarma, da gari mai alfarma, waɗannan sune alfarmomin.
Kuma ku girmama abinda Allah ya umurce ku da girmama su, kuma ku gabatar da abinda Allah ya umurce ku da gabatar da su, kuma ku nisanci abinda Allah ya hukunta haramcinsa, don ku samu falalarSa da ladanSa da ni'imarSa.

Ina faɗan abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi Mai yawan gafara ne.

HUƊUBA TA BIYU
  
YA KU MUSULMAI!!!
Sunnah ta tabbata kan ninka ladan sallah a Masallaci mai alfarma da Masallacin Annabi SAW, wato ninkawa ta fiskar adadi, ga farilla da nafila, ga maganar da tafi inganci daga cikin maganganun Maluma biyu.

An ruwaito daga Jabir -Allah ya ƙara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Yin sallah a Masallacina wannan yafi salloli dubu a waninsa falala; in banda Masallaci Mai alfarma. Sallah kuma a Masallaci Mai alfarma yafi  salloli dubu ɗari, a Masallacin da ba shi ba". Ahmad ya ruwaito shi, [14694، 15271], da Ibnu-majah.

Saidai babu wani dalili ingantacce da ya nuna cewa, kyakkyawan aikin da aka aiwatar a garin Makkah ana ninka ladansa zuwa lada dubu ɗari. Ko yake cewa ana ninka ladan azumin Ramadhana idan aka yi shi a garin Makkah, ko a Madinah zuwa ladan azumin watanni dubu ɗari, ko a bada ladan Ramadhana guda saba'in. Dukkan wannan babu sunnar da ta tabbatar da shi, kuma babu wani dalili akan hakan. Kuma hadisan da suke ɗauke da wannan ma'anar ko dai da'ifai ne, ko yasassun hadisai na ƙarya.
Magana ingantacciya itace, lallai kyawawan ayyukan da aka yi a lokaci mai daraja, da wuri mai daraja, ana ninka ladansu, ninkawa ta fiskar girma, ba ta fiskar adadi ba, sai abinda dalili (ingantacce) ya yi nuni akansa.
Kuma suma munanan ayyukan da aka zartar da su a wurare ko lokatai masu daraja zunubinsu yana bunƙasa ta fiskar girma, ba ninkuwa ta fiskar adadi ba.

YA KU MAHAJJATA DA MASU UMRAH DA ZIYARA!!!
Ku ribaci lokacin zamanku a garin Makkah da Madinah, ta hanyar kwazo wajen aikata kyawawan ayyuka, da yawaita aikata su, kuma ku yawaita tuba da neman gafara, kuma ku bayyanar da rusunawarku da ƙan-ƙan-da kai da nadama, da nuna buƙatuwarku ga Ubangijnku, da bayyanar da lalura; domin kuna wurin saukowar rahama, kuma wuraren karɓar ayyuka, da fagagen da ake zaton amsa addu'oi da gafara, da 'yanta Bayi daga faɗawa Wuta.

Ku riƙa tuna girman wuraren, da falalar lokatan.
Allah ya haɗa addu'oinku da amsawa, neman gafararku kuma da yarda, ayyukan da kuke yi kuma ya karɓa.

Addu'a ….
……………….


HUSAIN ALUSSHEIKH 2 zulkiidah 1440H



HUDUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A 2/ZUL KI'IDAH/1440H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI Husain bn Abdul'aziz AlusSheikh







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم

Huɗubar farko

Cikin zuwan zamani wani bayan wani, akwai abin lura, kuma cikin sassaɓawar dare da yini akwai abin tunani, Allah Subhanahu yana cewa: Kuma shi ne ya sanya dare da yini akan mayewa, ga wanda yake son ya wa'azantu, ko yake nufin ya yi godiya [Alfurƙan: 62].

Abin nufi da faɗinSa khilfah shine masu maye wa juna, a fiskar halitta da ƙaddara, ma'ana ɗayansu ya kan zo ya maye gurbin ɗayan, kuma kowanne yana zama mayewar ɗan'uwansa, wannan a bayan wannan, ɗaya  bayan ɗayan; da haske ko dufu, ko tsawo ko nuƙsani, kamar yadda Allah Subhanahu ya ce: Sai  muka shafe  ayar dare, kuma muka sanya ayar rana  mai sanya a iya gani [Isra'i: 12].
Kuma Allah Mabuwayin Sha'ani  ya ce: Kuma dare aya ce  a gare su Muna feɗe rana daga  cikinsa, sai ga su suna masu shiga dufu [Yashin: 37].

Kuma kalmar Khilfah tana iya zuwa da ma'anar  da take alaƙa da shari'a, domin Allah ya sanya dare da yini kowannensu yana zuwa a bayan ɗayan, saboda abinda ya kufce na aikin da ake yinsa ga Allah a cikin wani lokaci, a iya ramukonsa a wani lokacin na-daban.
An ruwaito daga Shaƙiƙ, ya ce: Wani Mutum ya zo wurin Umar ɗan  Khaddab -RA- sai  ya ce: Sallahta ta kuɓuce min, a wannan daren? Sai  ya ce: Ka riski abinda ya kuɓuce maka na sallar darenka a cikin yininka.
Don  haka, ya zo a cikin sunnah ko hadisi  faɗinsa SAW: Babu wani Mutum wanda sallar dare zata kasance masa, ko wani abu  na bauta a cikinsa, (wanda  bai yi su ba), sai  ya karanta shi a tsakanin sallolin asuba da na azahar, face Allah ya rubuta masa ladan sallarsa, shi kuma barcinsa zai kasance sadaka ne, a gare shi. Muslim ya ruwaito shi.
Wannan ya sanya Mutum idan ya yi barci bai yi sallar wutiri ba, ko ya manta, ko suka kuɓuce masa, sai ya sallaci abinda ya saba sallatarsu a cikin dare, da rana, zai rika sallama duk bayan raka'oi biyu, sai kuma ya sanya wuturin ya zama raka'oi biyu, da niyyar wutiri, A'isha -R.A- ta ce: Annabi -SAW- Idan barci ko cuta  suka shagaltar da shi bai yi sallar wutirinsa ba, sai  ya sallaci abinda ya kuɓuce masa raka'oi goma sha biyu a cikin yini. Muslim ya ruwaito.
Lallai cikin sassaɓawar dare da yini, da jirkitan sifofin zamani, akwai babban abin lura wanda zai jagoranci Musulmi yin tunani kan girman kudurar Allah da ikonsa, da cikakken ganin damarsa, da gane girmarsa wanda  bata da iyaka, sai hakan ya masa  jagora izuwa ga ƙanƙan  da kai da risinawa ga Mahaliccinsa Mai girma, sai kuma ya kwashe shi ga miƙa wuya a gare shi, da amsa masa  kan shari'arsa miƙaƙƙiya, Allah Ta'alah ya ce: Ga wanda ya so ya wa'azantu, ko ya yi nufin godiya.

Kuma lallai Ma'abuta imani, sune suke wa'azantuwa mai amfani, sai hakan ya haifar musu da tsoron Mahaliccinsu, da tsoron uƙubarSa, da kiyayarSa; sai  ya samar  musu da kammalallen taƙawa, da cikakken imani, da tauhidi mai tsarki, Allah Ta'alah ya ce: Lallai cikin mayewar dare da yini da abinda Allah ya halitta a cikin sammai da ƙassai akwai ayoyi ga Mutane masu taƙawa [Yunus: 6].

Kuma Allah Mabuwayin sha'ani ya ce: Shine Wanda ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, yini kuma abin ayi gani, lallai ne  cikin haka akwai ayoyi ga Mutane masu ji [Yunus: 67].
Na'am, saboda masu ji sune suke amfanuwa da ayoyin Allah na halitta, sai su wa'azantu da su, su kuma samu abin lura, sai hakan ya haifar musu da imani na gaskiya, da aiki mai tsarki, Allah Ta'alah ya ce: Ashe basu gani ba, lallai mun sanya dare domin su natsu a cikinsa, yini kuma mai sanya gani, lallai cikin wannan akwai ayoyi ga Mutane masu imani [Naml: 86].

Ya kai Mumini, Ka riƙi wa'azi da tunatarwa daga  sassaɓawar zamani, kuma ka kasance -a cikin halayenka- mai godiyar Allah, mai aiki da ɗa'oinsa, mai nisantar nau'ukan saɓa masa, Allah Ta'alah ya ce: Yana daga rahamarSa, Ya sanya muku dare da yini domin ku natsu a cikinsa, kuma domin ku  nema daga falalarSa, kuma tsammaninku za ku yi godiya [Ƙasas: 73].
Ibnu Kasir -Allah ya yi masa  rahama- ya ce: Ma'ana ku  yi godiya ga Allah ta hanyar aiki da nau'ukan ibadodi a cikin dare da yini.

'Yan'uwa Masu imani
Yana daga abin lura da wa'azozin sassaɓawar sifofin zamani, abinda halittu suke samun kansu a lokacin bazara na tsananin zafi, sai Mutane su riƙa neman  hanyoyin samun inuwa mai inuwantarwa, da iska mai sanyi da daɗi, to shin Musulmi -da irin  wannnan- yana tuna wutar Jahannama da zafinta, Allah ya tsare mu  daga hakan, Allah Ta'alah ya ce: Kuma suka ce: Kada ku fita zuwa yaƙi a cikin zafi, Ka ce: wutar Jahannama ce mafi tsananin zafi da sun kasance suna fahimta [Taubah: 81].
Kuma ya zo a cikin Bukhariy da Muslim, lallai Annabi -SAW- ya ce: Wuta ta kai kuka ga Ubangijinta, ta ce: sashena yana cinye sashe! Sai  ya mata izinin ta riƙa numfashi  biyu, na farko a lokacin sanyi, da kuma a lokacin zafi, kuma shine mafi tsananin abinda kuke samu na zafi, da abinda kuke samu na jaura (wato, sanyi). Bukhariy da Muslim.

Sai kayi sauri da gaggawar aikata dukkan aiki na kwarai; wanda zai kusantar da kai ga Mabuwayi Mai girma, kuma ka kiyaye ayyukan saɓo masu halakarwa, Allah Ta'alah ya ce: Kuma ina muku gargadin wuta mai babbaka * Babu mai shigarta sai mafi shagawa * Wanda ya ƙaryata kuma ya juya baya * kuma lallai za a nesanta mafi taƙawa daga faɗawa cikinta * Wanda ya bayar da dukiyarsa yana neman tsarkaka * alhalin babu wani da ya ke da wata ni'imar da ake neman sakamakonta * face dai neman yardar UbangijinSa mafi ɗaukaka * Kuma da sannu zai yarda.

Kuma Magabatan kwarai dangane da al'amarin kulawa da sassaɓawan zamani lallai suna da sha'ani mai girma, Ga Umar -Allah ya ƙara yarda a gare shi- yana yin wasiyya ga ɗansa cewa, ya riƙa aiki da sifofin imani, kuma daga cikinsu sai ya ambaci, Yin azumi a lokaci matsanancin zafi.
Kuma a lokacin da Umar ya yi jinyar ajalinsa sai  ya ce: Ya Allah! lallai ka  san ba ina  son zama a Duniya ne, domin janyo ƙoramai, ko dashen bishiyoyi ba, sai domin ƙishin azumi a lokutan zafi, da yin ibadar dare, da shiga jikin Malamai a halƙoƙin zikiri.

Kuma an hakaito daga Abdullahi ɗan Umar da wasu daga magabatan kwarai -Allah ya ƙara yarda a gare su- lallai su idan suka sha ruwan sanyi sai su yi kuka, suna masu tuna faɗin Allah Ta'alah dangane da kafirai: Ku zubo akanmu daga ruwa, ko daga abinda Allah ya azurta ku. Sai su ce: Lallai ne Allah ya haramta su ga kafirai [A'araf: 50].

Huɗuba ta biyu

Watan Zulƙi'idah yana cikin watanni hajji, kuma yana cikin watanni huɗu masu alfarma, waɗanda Allah ya ɗaukaka, kuma ya basu girma da alfarma, Abdullahi ɗan  Abbas -Allah ya ƙara yarda a gare su- ya ce: Allah ya kebance watanni guda huɗu, ya sanya suka zama masu alfarma, kuma ya girmama alfarmar tasu, kuma ya sanya aikin zunubi a cikinsu ya zama mafi muni, kuma ya sanya aikin kwarai da lada a cikinsu suka fi girma.

Kuma Ma'abuta ilimi sun bayyana cewa yin Umrah a watan Zulƙi'idah sunnah ne, saboda umrar Annabi SAW guda huɗu dukansu sun kasance a cikin Zulƙi'idah kamar  yadda ambaton hakan ya zo cikin Sahihul Bukhariy da Muslim daga Anas -Allah ya ƙara yarda a gare shi-.
Kuma an ruwaito daga A'isha -Allah ya ƙara yarda a gare ta- ta ce: Manzon Allah SAW- bai taɓa yin umrah ba, sai a cikin watan Zulƙi'idah. InbuMajah ya ruwaito shi da isnadi mai inganci.

Ibnul-Ƙayyim -Allah ya yi masa rahama ya ce: Saidai Allah bai kasance zai zaɓa wa AnnabinSa  a al'amarin umrorinsa ba, face lokutan da suka fi dacewa, kuma suka fi cancantar ayi umrar a cikinsu.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...