2015/11/30

ABUBUWA (20) DA SUKE TAIMAKO KAN HAKURI BISA GA CUTARWAR HALITTU (عشرون أمرًا تعين في الصبر على أذى الخلق)









ABUBUWA (20) DA SUKE TAIMAKO
 KAN
HAQURI BISA GA CUTARWAR HALITTU
(عشرون أمرًا تعين في الصبر على أذى الخلق)


TANADAR
SHEIKHUL ISLAM AHMAD XAN ABDULHALIM XAN ABDUSSALAM IBNU-TAIMIYYAH


FASSARAR
Abubakar Hamza

بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah,
Salati da sallama su qara tabbata ga Manzon Allah,
da iyalansa da sahabbansa da duk wanda ya bi Allah,
Bayan haka:

Lalli rayuwa jarabawa ce, kuma Bawa a cikinta ka iya fiskantar dangin cutarwa mabanbanta daga 'yan'uwansa halittu, Saidai akwai abubuwa masu yawa; waxanda suke taimakon Mutum kan haquri bisa ga cutarwar 'yan'uwasa halittu. Sheikul Islam Ahmad xan Abdulhlim Ibnu-Taimiyyah (wanda ya rasu, a shekarar hijira ta 728) a cikin littafinsa mai muhimmanci QA'IDATUN FIY ASSABAR (قاعدة في الصبر) wanda yake magana kan HAQURI (daga shafi na 94-103), ya ambaci abubuwa guda ashirin (20) kamar haka; a inda yake cewa:  
ويعينُ العبدَ على هذا الصبر عدةُ أشياء:
Ma'ana:
"Abubuwa dayawa za su taimaki bawa, akan wannan nau'i na haquri".
 Sai ya ambaci guda ashirin (20) daga cikinsu, kamar haka, Yace:
أحدها:
أنْ يَشْهَدَ أنَّ الله -سبحانه وتعالى- خالِقُ أفعالِ العِبَاد؛ حركاتِهِم وسكناتِهم وإراداتِهم، فما شاءَ الله كان، وما لم يشَأْ لم يَكُن، فلا يتحرك في العالم العلويّ والسفليّ ذَرَّةٌ إلا بإذنه، ومشيئتِه، والعباد آلة، فانظر إلى الذي سلَّطهم عليك، ولا تنظُرْ إلى فِعلهم بَكَ، تستريحُ مِنَ الْهمِّ والغمِّ والحزن.
NA XAYA:
Mutum (a zuciyarsa) ya ji cewa lallai Allah (سبحانه وتعالى) shine ke halitta aiyukan bayi (gabaxaya); motsawansu, da yin shirunsu, da nufinsu; Kuma duk abinda Allah ya yi nufi shi yake kasancewa, Wanda kuma bai nufa ba, shi kuma ba zai kasance ba. Akan haka; Daidai da kwayar zarra a cikin duniyar sama ko qasa ba za ta motsa ba face da izininSa da nufinSa, Su kuma bayi kamar kayan aiki ne. Don haka; Sai ka yi dubi zuwa ga wanda ya xora su akanka, kada ka yi dubi zuwa ga aikin da suka aikata maka; Sai ka huta daga baqin ciki da tashin hankali da vacin rai.

الثاني:
أنْ يشهد ذنوبه، وأن الله إنما سلّطهم عليه بذنبه، كما قال تعالى: {وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ}؛ فإذا شهد العبدُ أنَّ جميع ما يناله مِن المكروه فسببُه ذنوبُه، اشتغَلَ بالتوبة والاستغفار مِن الذنوب التي سلَّطهم عليه، عن ذمِّهم ولَومِهم والوقيعة فيهم، وإذا رأيت العبد يقَعُ في الناس إذا آذَوْه ولا يرجِع إلى نفسه باللوم والاستغفار: فاعلم أنَّ مصيبتَه مصيبةٌ حقيقيةٌ، وإذا تاب واستغفر، وقال: هذا بذنوبي، صارت في حقه نعمة.
قال علي بن أبي طالب -رضي الله عنه - كلمة من جواهر الكلام: لا يَرْجُوَنّ عبدٌ إلا ربَّه، ولا يخافَنّ عبدٌ إلا ذنبه. وروي عنه وعن غيره: ما نزل بلاءٌ إلا بذنب، ولا رُفع إلا بتوبةٍ.
NA BIYU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da zunubansa, yana mai jin cewa lallai Allah bai xora su akansa ba sai da zunubansa; kamar yadda Allah (تعالى) yace:
"Kuma babu abinda yake samunku na musiba face da sababin abinda hannayenku suka aikata, kuma yana yafe dayawa" [Shurah: ???].
Akan haka; Idan bawa yaji cewa dukkan abinda ya same shi na abin qi, sababinsa shine zunubinsa, to sai ya shagalta da yin tuba da neman gafara; daga waxannan zunuban da suka zama sababin xora Mutane akansa, Ya  bar kuma aibanta su da zarginsu, da cin mutuncinsu. Kuma idan ka ga yana kutsawa cikin mutuncin mutane idan suka cutar da shi, baya kuma komawa ga kansa da zargi, da neman gafara to ka sani lallai musibarsa musiba ce ta haqiqa. Idan kuma ya tuba ya kuma nemi gafara, sannan yace: Abinda ya same ni saboda zunubai na ne, to musibarsa ta zama ni'ima a haqqinsa.
Aliyu xan Abiy-xalib (رضي الله عنه) ya faxi wata magana wacce take cikin maganganu masu tsada, cewa:
"Kada bawa yayi fatan wani idan ba Ubangijinsa ba, kuma kada ya ji tsoron wani abu idan ba zunubinsa ba".
Kuma an ruwaito daga gare shi, da kuma waninsa cewa:
"Bala'i baya sauka sai da zunubi, kuma ba a xauke shi sai da tuba".

الثالث:
أنْ يشْهَدَ العبدُ حُسن الثواب الذي وعَدَه الله لِمَنْ عَفَى وصبَر، كما قال تعالى: {وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِثْلُهَا، فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ، إِنَّهُ لا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ}. ولما كان الناس عند مقابلة الأذى ثلاثة أقسام: ظالم يأخذُ فوق حقه، ومقتصد يأخذُ بقدر حقه، ومحسن يعفو ويترك حقه. ذكر الأقسام الثلاثة في هذه الآية؛ فأولها للمقتصدين، ووسطها للسابقين، وآخرها للظالمين.
ويشهد نداء المنادي يوم القيامة: ألا لِيَقُمْ مَن وَجَب أجرُه على الله، فلا يقوم إلا من عفى وأصلح.
وإذا شهد مع ذلك فَوت الأجر بالانتقام والاستيفاء سَهُل عليه الصبر والعفو.
NA UKU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da kyakkyawan ladan da Allah yayi alkawarinsa ga wanda yayi yafiya kuma yayi haquri; a cikin faxinsa:
"Kuma sakamakon mummuna mummuna ne kwatankwacinsa, Wanda kuma yayi yafiya, yayi sulhu to ladansa yana kan Allah, Lallai shi (Allah) baya son azzalumai" [].
Kuma yayin da Mutane suka kasance a lokacin fiskantar cutarwar da aka yi a gare su, suke karkasuwa kashi uku; Azzalumi; wanda da yake xaukan fiye da haqqinsa, da Mai tsakaitawa; wanda shi kuma ke xaukan gwargwadon haqqinsa, da Mai kyautatawa; wanda shi kuma yake yafewa sannan ya bar haqqinsa = to sai Allah – a cikin wannan ayar- ya ambaci waxannan Kason guda uku, Sai farkon ayar ya zama na Masu tsakaitawa, Tsakiyanta kuma na Waxanda suke yin gaba cikin aiyukan alkhairi, Qarshenta kuma na Waxanda suke yin zalunci.
Kuma sai bawa (a cikin zuciyarsa) ya halarto kiran da mai kira zai yi a ranar tashin kiyama, cewa:
Ku saurara! Wanda ladansa ya tabbata akan Allah ya taso, Babu kuma wanda zai taso a lokacin sai wanda yayi yafiya, yayi sulhu.
Kuma idan bawa (a cikin zuciyarsa) ya halarto da cewa: Wannan ladan, zai kuvuce masa idan har ya xau fansa ko ya dawo da haqqinsa gabaxaya to yin haquri da afuwa sai ka ga yayi sauqi a gare shi.

الرابع:
أنْ يَشْهَد أنه إذا عفى وأحْسَن أوْرَثه ذلك مِن سلامة القلب لإخوانه، ونقائه من الغِشّ، والْغِلّ، وطلب الانتقام، وإرادة الشَّرّ، وحصل له مِن حلاوة العفو ما يَزيدُ لَذَّتَه ومنفعتَه عاجلا وآجلا على المنفعة الحاصلة له بالانتقام أضعافًا مضاعفة. ويدخُل في قوله تعالى: {وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}، فيصير محبوبًا لله، ويصير حالُه حالَ من أُخِذَ منه دراهمٌ فَعُوِّضَ عنها ألوفًا من الدنانير، فحينئذ يَفْرَح بما مَنَّ الله عليه أعظم فرحٍ ما يكون.
NA HUXU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da cewa: Idan har yayi afuwa, ya kuma kyautata sai hakan ya gadar masa da tsarkin zuciya ga 'yan'uwansa, da kuvutar zuciya daga alqus, da qulle mutum, da neman xaukar fansa, da yin nufin sharri, Sai kuma ya samu xanxanon zaqin da ake samu idan aka yi afuwa, wanda zai qara masa jin daxi da amfani a duniya da lahira, fiye da amfanin da ya samu lokacin xaukar fansa ninkin ba-ninkiya. Sai kuma ya shiga cikin faxin Allah (تعالى):
"Kuma Allah yana son masu kyautatawa" []; Sai ya zama abin so ga Allah, daga nana sai halinsa ya zama kamar wanda aka xauka masa dirhami guda xaya, Sai kuma aka yi masa canzi da dubban dinari, Kuma a lokacin ne, zai yi farin ciki da abinda Allah yayi masa baiwa da shi, mafi girman farin ciki .

الخامس:
أنْ يَعْلَمَ أنَّه ما انتَقَمَ أحَدٌ قطّ لنفسه إلا أوْرَثَه ذلك ذُلاً يجده في نفسه، فإذا عفى أعَزَّه الله. وهذا مما أخبر به الصادق المصدوق حيث يقول: "ما زاد الله عبدًا بعفوٍ إلا عزًّا"، فالعِزّ الحاصل له بالعفو أحبُّ إليه وأنفعُ له مِن العِزّ الحاصل له بالانتقام، فإنَّ هذا عِزٌّ في الظاهر وهو يُورث في الباطن ذُلاً، والعفوُ ذُلٌّ في الباطن وهو يُورثُ العز باطنًا وظاهرًا.
NA BIYAR:
Mutum ya sani cewa: Lallai babu wanda zai xau fansa wa kansa face Allah ya gadar masa da qasqancin da zai ji shi a cikin ransa, Idan kuma yayi afuwa sai Allah ya xaukaka shi, Wannan kuma yana daga cikin abinda Manzon Allah; Mai gaskiya abun gaskatawa ya bayyana a inda yake cewa:
"Allah bai yi qari ga wani bawa, kan afuwar da ya yi ba, face xaukaka". Wannan kuma saboda xaukakar da ake samu idan aka yi afuwa shi yafi sayuwa a gare shi, kuma shine yafi amfani, fiye da xaukakar da ake samu idan aka xauki fansa; saboda na qarshen izza ce ta zahiri, amma kuma tana gadar da qasqanci a baxini, yayin da shi kuma yin afuwa qasqanci ne a baxini, saidai kuma ya kan gadar da izza a baxini da zahiri. 

السادس - وهي من أعظم الفوائد -:
أن يشهد أن الجزاء من جنس العمل، وأنه نفسه ظالمٌ مذنبٌ، وأنَّ مَن عفى عن الناس عفى الله عنه، ومن غفر غفر الله له، فإذا شهد أن عفوه عنهم وصفحه وإحسانه مع إساءتهم إليه، سبب لأن يجزيه الله كذلك من جنس عمله؛ فيعفو عنه ويصفح ويحسن إليه على ذنوبه، ويسهل عليه عفوه وصبره ويكفي العاقل هذه الفائدة.
NA SHIDA –Wannan kuma yana cikin manya-manyan fa'idodi-:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da cewa: Lallai sakayya ya kan kasance daga jinsin aiki, Kuma lallai shima a karan-kansa mai zaluntar kansa ne, mai zunubi, kuma lallai duk wanda yayi afuwa ga Mutane sai Allah yayi masa afuwa, Wanda ya gafarta sai Allah yayi masa gafara, Don haka; idan bawa ya halarto da cewa: Lallai yafiyar da zai yi musu, da rangwantawarsa, da kyautatawarsa, a tare da munanawansu = sababi ne, na Allah ya sakanta masa daga jinsin aikinsa; sai yayi afuwa a gare shi, ya rangwanta masa, ya kyautata masa, tare da zunubansa, A haka; Sai yin afuwa da haquri yayi masa sauqi. Wannan fa'idar kuma ta ishi mai hankali!  

السابع:
أنْ يعلَم أنّه إذا اشتغَلَتْ نفسُه بالانتقام وطلَبِ المقابلة ضاع عليه زمانُه، وتفرَّق عليه قلبُه، وفاتَه مِن مصالحه ما لا يمكن استدراكُه، ولعل هذا يكون أعظم عليه من المصيبة التي نالَتْه مِن جهتهم، فإذا عفى وصفح فرغ قلبُه وجسمُه لمصالحه التي هي أهمُّ عنده مِن الانتقام.
NA BAKWAI:
Bawa ya san cewa: Lallai shi idan har ransa ta shagalta da neman xaukar fansa, ko sakayya to sai lokacinsa ya tozarta, kuma zuciyarsa ta rarraba, sannan maslahohinsa da ba zai iya riskarsu ba, sai su wuce masa, kuma la'alla wannan yafi girman muni a wurinsa fiye da musibar da ta shafe shi daga vangarensu. Amma idan kuma yayi afuwa, ya rangwanta to sai zuciyarsa da jikinsa su tafi zuwa ga maslahohinsa waxanda sun fi muhimmanci a gare shi fiye da xaukar fansa. 

الثامن:
أنَّ انتقامَه واستيفاءَه وانتصارَه لنفسه وانتقامَه لها، فإنَّ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم ما انتقم لنفسه قط، فإذا كان هذا خيرُ خلق الله وأكرمُهم على الله لم يكن ينتقم لنفسه مع أنَّ أذاه أذى لله، ويتعلق به حقوق الدين، ونفسُه أشرفُ الأنفس، وأزكاها، وأبرُّها وأبعدُها من كل خُلقٍ مذمومٍ، وأحقُها بكلّ خُلقٍ جميل، ومع هذا فلم يكن ينتقم لها. فكيف ينتقم أحدُنا لنفسه التي هو أعلم بها وبما فيها من العيوب والشرور، بل الرجل العارف لا تساوي نفسُه عنده أن ينتقم لها، ولا قدر لها عنده يوجبُ عليه انتصارُه لها.
NA TAKWAS:
Bawa ya ji cewa, Lallai xaukar fansansa da qoqarin maido da haqqoqinsa da neman ya ci nasara yana yi ne wa Ransa, kuma xaukar fansan shima wa ita yake yi, alhalin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) bai tava xaukar fansa ga kansa ba, daxai, To, idan wannan shine xabi'ar mafi alheri daga cikin halittun Allah, wanda kuma ya fi su, matsayi a wurin Allah: ya zama baya xaukar fansa ga kansa, tare da cewa lallai cutar da shi, cutar da Allah ne, kuma haqqoqi na addini suna rataya akan haka, kuma ransa itace tafi dukkan rayuka xaukaka, kuma ita ta fi su tsarki, da biyayya, kuma itace tafi nisantar kowace xabi'a abar zargi, kuma tafi cancantar kowani hali mai kyau, amma tare da haka; Bai kasance yana xaukar mata fansa ba! To, ta yaya xayanmu zai xauki fansa ga kansa, wanda shine yafi kowa sanin abinda take xauke da su na aibuka da sharrori.
Kai, lallai shi Mutum masani ransa a wurinsa bata kai ya xauka mata fansa ba, kuma bata da matsayi a wirinsa da zai wajabta masa neman kwato mata haqqinta.    

التاسع:
إنْ أوذي على ما فعله لله أو على ما أمَرَه به مِن طاعته ونهى عنه مِن معصيته وجب عليه الصبر ولم يكن له الانتقام، فإنه قد أوذي في الله، فأجرُه على الله، ولهذا لما كان المجاهدون في سبيل الله ذهبت دماؤهم وأموالهم في الله لم تكن مضمونة، فإنّ الله -تعالى- اشترى منهم أنفسَهم وأموالَهم، فالثَّمَنُ على الله لا على الخلق، فمَن طلب الثمن منهم لم يكن له على الله ثمَنٌ، فإنه من كان في الله تلَفُه كان على الله خلَفُه.
وإن كان قد أوذي على معصية، فليرجع باللوم على نفسه، ويكون في لومه لها شغل عن لومه لمن آذاه.
وإن كان قد أوذي على حظٍّ، فليُوطِّن نفسَه على الصبر، فإن نيل الحظوظ دونه أَمْرٌ أَمَرُّ من الصبر، فمن لم يصبر على حر الهواجر، والأمطار، والثلوج، ومشقة الأسفار، ولصوص الطريق، وإلا فلا حاجة له في المتاجر، وهذا أمر معلوم عند الناس أن من صدق في طلب شيء من الأشياء بذل من الصبر في تحصيله بقدر صدقه في طلبه.
NA TARA:
Idan har ya zama an cutar da shi ne akan wani aikin da ya aikata shi don Allah, ko akan wani abinda ya umurce shin a xa'arSa, ko wanda ya hana shin a savonSa to wajibi ne akansa ya yi haquri, kuma haramun ne akansa ya xauki fansa; saboda an cutar da shi ne a wannan yanayin akan Allah, kuma ladansa yana kan Allah; Wannan kuma shi ya sanya masu jihadi fiysabilil lahi, idan rayukansu da dukiyarsu suka tafi don Allah, ba a biyan fansansu, wannan kuma saboda Allah (تعالى) ya sayi rayukansu da dukiyoyinsu daga gare su; don haka; ladan yana kan Allah ne ba a kan halittu ba, kuma duk wani daga cikinsu da ya nemi kuxinsa to bashi da wani kuxi akan Allah; saboda DUK WANDA LALACEWAN ABUNSA YA ZAMA A HANYAR ALLAH NE, TO, MAYAR MASA DA GURBIN WANNAN ABUN YA KAN KASANCE AKAN ALLAH NE.
In kuma ya zama an cutar da shi ne akan wani savo; to sai ya dawo da zargi ko aibantawa ga kansa, sai kuma zarginsa ga kansa ya shagaltar da shi ga barin zargin wanda ya cutar da shi.
In kuma an cutar da shi ne, akan wani rabo (na duniya) to sai ya horar da kansa akan yin haquri; wannan kuma saboda samun rabo gabaninsa akwai lamarin da yafi haquri daci, kuma duk wanda bai yi haquri akan zafin rana, ko ruwan sama, ko qanqara, da wahalhalun tafiye-tafiye, ko varayin kan hanya ba, to, lallai bashi da buqatar yin kasuwanci. Wannan kuma sanannen abu ne a wurin Mutane; cewa: Duk wanda yayi gaskiya wajen neman wani abu, to ya kan yi haquri cikin nemansa gwargwadon gaskiyarsa cikin nemansa.      

العاشر:
أن يشهد معية الله معه إذا صبر، ومحبة الله له ورضاه، ومن كان الله معه دفع عنه من أنواع الأذى والمضرات ما لا يدفع عنه أحد من خلقه، قال الله تعالى: {وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ}، وقال: {وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ}.
NA GOMA:
Bawa ya ji cewa, Lallai Allah yana tare da shi idan yayi haquri, kuma zai samu soyayyar Allah da yardarSa, Duk kuma wanda Allah yake tare da shi to zai tunkuxe masa nau'ukan cutuka, da dukkan abubuwan da zasu cutar da shi, irin abinda wani daga cikin halittunSa ba zai iya tunkuxe masa ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi haquri; lallai Allah yana tare da masu haquri" []. Kuma yace:
"Kuma Allah yana son masu haquri" [].

الحادي عشر:
أنْ يشهد أنَّ الصبر نصفُ الإيمان، فلا يَبذُل مِن إيمانه جُزءًا في نُصرة نفسِه، فإنْ صبَر فقد أحرز إيمانَه وصانه من النقص، والله -تعالى- يدفَعُ عن الذين آمنوا.
NA GOMA SHA XAYA:
Bawa (a cikin zuciyarsa) ya ji cewa, Lallai haquri rabin imani ne, Don haka; ba zai bayar da sashin imaninsa wajen taimakon kansa ba, Idan kuma har yayi haquri to ya kiyaye imaninsa daga wata naqasa. Kuma lallai Allah -تعالى- yana bada kariya ga waxanda suka yi Imani.  

الثاني عشر:
أنْ يشهَدَ أنَّ صَبْرَه حُكم منه على نفسه، وقَهْرٍ لها، وغَلَبَةٍ لها، فمتى كانت النفسُ مقهورةً معه مغلوبةً، لم تطمع في استرقاقه وأَسْرِه، وإلقائه في المهالك. ومتى كان مطيعًا لها، سامعًا منها، مقهورًا معها: لم تزل به حتى تُهْلِكه، أو تتداركه رحمةٌ مِن ربّه. فلو لم يكن في الصبر إلا قهره لنفسه ولشيطانه، فحينئذ يظهر سلطان القلب وتثبت جنوده، فيفرح ويقوى ويطرد العدو عنه.
NA GOMA SH BIYU:
A (cikin zuciyarsa) bawa ya ji cewa, Lallai haqurin da zai yi, cin nasararsa ne akan Ransa, da rinjayarta, da cin galaba akanta, kuma duk lokacin da Rai ta zama an rinjaye ta, an kuma yi galaba akanta, to, baza ta yi kwaxayin mayar da shi bawan da zata riqa bautar da shi ba, ko kuma jefa shi cikin abubuwan da za su halakar da shi. Yayin da kuma duk lokacin da Mutum ya zama mai yin xa'a ga Ransa, mai jin maganarta, wanda ta rinjaye shi, to ba za ta kyale shi ba har sai ta halaka shi, idan ba wata rahama ce ta fiskance shi daga wajen Ubangiji ba.
Kuma da haquri bashi da wata fa'ida sai yadda Mutum zai lankwasa Ransa, da Shexaninsa (to ya ishe shi). Kuma a lokacin ne qarfin zuciya zai yi rinjaye, kuma rundunoninsa za su tabbata, sai ya yi farin ciki, yayi qarfi, har ya iya korar maqiyansa daga gare shi.  

الثالث عشر:
أنْ يعلم أنَّه إنْ صبَر فالله ناصرُه ولا بد، فإنَّ الله وكيلُ مَن صبَر وأحال ظالمَه عليه، ومَن انتصر بنفسه لنفسه وكَّله الله إلى نفسِه، فكان هو الناصر لها، فأين من ناصرُه الله خيرُ الناصرين، إلى مَن ناصرُه نفسُه أعجزُ الناصرين وأضعفه.
NA GOMA SHA UKU:
Bawa ya sani cewa, Lallai idan yayi haquri to Allah zai taimake shi, babu makawa, saboda Allah ya kan wakilci wanda yayi haquri; sa'annan ya mayar da lamarin wanda ya zlunce shi zuwa ga Allah, Shi kuma wanda ya nemi ya taimakawa kansa da karan-kansa sai Allah ya jivintar da shi zuwa ga kansa, Sai ya kasance shine mai taimakawa Ransa, Shin kuma zaka haxa wanda mai taimakonsa shine (Allah) mafi alkhairin masu taimako, da wanda mai taimakonsa shine Ransa, gajiyeyyen mai tamako, kuma mafi rauni.   

الرابع عشر:
أنَّ صبْرَه على من آذاه واحتماله له يوجبُ رجوعَ خصمه عن ظلمه وندامته واعتذاره، ولوْم الناس له: فيعود بعد إيذائه له مستحييا منه، نادمًا على ما فعله، بل يصير مواليًا له، وهذا معنى قوله: {ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ فَإِذَا الَّذِي بَيْنَكَ وَبَيْنَهُ عَدَاوَةٌ كَأَنَّهُ وَلِيٌّ حَمِيمٌ وَمَا يُلَقَّاهَا إِلاَّ الَّذِينَ صَبَرُوا وَمَا يُلَقَّاهَا إِلاَّ ذُو حَظٍّ عَظِيمٍ}.
NA GOMA SHA HUXU:
Lallai haqurinsa kan cutarwansa, da jurewansa yana hukunta denawar abokin husumarsa daga zaluntarsa, d yin nadamarsa, da bada uzuri, da aibantawa dga wajen Mutane, a gare shi; Sai abokin husumarsa ya dawo –bayan cutarwar da yayi a gare shi- yana jin kunyarsa, yana nadam akan abinda ya aikata masa, Kai! Sai ya komo ya zama masoyi a gare shi, Wannan kuma shine ma'anar faxin Allah:
"Ka tunkuxe da abinda yafi kyau, Sai wanda a tsakaninka da tsakaninsa akwai adawa ya zama kamar wani masoyi makusanci   *   Kuma babu wanda ake bashi su sai waxanda suka yi haquri, kuma babu wanda ake bashi su face ma'abocin wani rabo mai girma" [Fussilat: 34-35].

الخامس عشر:
ربما كان انتقامه ومقابلته سببًا لزيادة شر خصمه وقوة نفسه وفكرته في أنواع الأذى التي يوصلها إليه كما هو المشاهد، فإذا صبر وعفى أمن من هذا الضرر. والعاقل لا يختار أعظم الضررين بدفع أدناهما. وكم قد جَلَب الانتقامُ والمقابلةُ مِن شرٍّ عجَزَ صاحبُه عن دفعه؟ وكم قد ذهبت به نفوس ورياسات وأموال وممالك؟ لو عفى المظلوم لبقيت عليه.
NA GOMA SHA BIYAR:
Kuma zai yiwu xaukar fansansa da zai yi da qoqarin maida martaninsa ya zama sababin qaruwar sharrin abokin husumarsa, da qarin qarfin ransa, da sake tunanin yadda zai isar da dangogin cutarwa  mabanbanta zuwa gare shi, kamar yadda ake ganin hakan a rayuwr mutane. Amma idn ya yi haquri, ya yafe to sai ya aminta daga wannan cutarwar. Kuma lallai mai hankali ba zai zavi mafi girma daga cikin nau'ukan cutarwa guda biyu; ta hanyar tunkuxe wacce tafi qaranci ba. Kuma sau nawa neman xaukar fansa da bqoqarin ramuko ya jawo sharrin da ma'abocinsa ya gagara tunkuxe shi. Kuma sau nawa da hakan rayuka da mulki da dukiyoyi da masarautu suka tafi, Wanda da mutumin da aka zalunta ya yi yafiya, da abubuwansa sun wanzu tare da shi?  

السادس عشر:
أن من اعتاد الانتقام ولم يصبر، لا بد أن يقع في الظلم، فإن النفس لا تقتصر على قدر العدل الواجب لها، لا علما، ولا إرادة، وربما عجزت عن الاقتصار على قدر الحق، فإن الغضب يخرج بصاحبه إلى حَدٍّ لا يعقل ما يقول وما يفعل. فبين هو مظلوم ينتظر النصر والعز، إذ انقلب ظالماً ينتظر المقت والعقوبة.
NA GOMA SHA SHIDA:
Lallai wanda ya saba xaukar fansa; baya yin haquri to babu makawa dole zai auka cikin zalunci, saboda kasancewar Rai ba za ta taqaita ga gwargwado na adalci da ta cancance shi ba; ta fiskar saninsa, ko yin nufinsa, kuma wani lokacin zata gaza taqaitawa akan gwargwadon gaskiyan ne, saboda fushi yak an fitar da ma'abocinsa zuwa ga yanayin da baya sanin abinda yake faxa ko yake aikatawa ba. Sai mutumin da ya samu kansa a matsayin wanda aka zalunta; mai neman taimako da izza daga Allah, sai katsam ya wayi-gari ya juye ya zama shine mai zalunci; wanda ke jiran fushin Allah da uqubarsa.

السابع عشر:
أن هذه المظلمة التي قد ظُلمها هي سبب إما لتكفير سيئة، أو رفع درجة، فإذا انتقم ولم يصبر لم تكن مكفرة لسيئته ولا رافعة لدرجته.
NA GOMA SHA BAKWAI:
Wannan zaluncin da aka yi masa, ko dai ya zama sababi ne kankare masa zunubi, ko xaukaka darajara, Idan kuma har ya xauki fansa, bai yi haquri ba, to lallai ba za ta kasance mai kankare masa zunubi ba, haka ba za ta xaga darajarsa ba.

الثامن عشر:
أنَّ عفوَه وصبْرَه من أكبر الجُند له على خصمه، فإنَّ مَن صبر وعفا كان صبرُه وعفوُه موجبًا لذُلِّ عدوِّه، وخوفه وخشيتِه منه ومِن الناس، فإنّ الناس لا يسكتون عن خصْمِه وإنْ سكَتَ هو، فإذا انتقم زال ذلك كله، ولهذا تجد كثيرًا من الناس إذا شتَمَ غيرَه أو آذاه يُحبُّ أنْ يستوفيَ منه، فإذا قابله استراح وألقى عنه ثقلاً كان يجده.
NA GOMA SHA TAKWAS:
Lallai yafiyarsa da yin haqurinsa suna daga mafi girmar rundunar yaqar waxanda yake husuma da su, saboda Mutumin da yayi haquri yayi afuwa to haqurinsa da afuwarsa sukan hukunta qasqancin maqiyansa, da kuma jin tsoronsa da tsoron mutane, wannan kuma saboda su mutane ba za su yi shiru akan abokin husumar tasa ba; koda kuwa shi ya yi shiru. Idan kuma ya xauki fansa to wannan gabaxayansa ya gushe. Kuma don haka ne; ka ke samu dayawa daga cikin mutane idan har ya zagi waninsa, ko ya cutar da shi = ya ke son wanda ya zaluntar ya yi qoqarin dawo da haqqinsa daga gare shi, kuma idan har ya raman to sai ya ji ya huta, kuma ya sauke wani nauyin da ya ke ji akansa.    

التاسع عشر:
أنه إذا عفى عن خصمه، استشعرت نفس خصمه أنه فوقه، وأنه قد ربح عليه، فلا يزال يرى نفسه دونه، وكفى بهذا فضلاً وشرفًا للعفو.
NA GOMA SHA TARA:
Lallai idan yayi afuwa ga wanda yake husuma da shi, Sai Ran wanda suke husumar da shi ya ji cewa, lallai mai yin afuwar yana sama da shi, kuma ya ci riba akansa, Kuma ba zai gushe yana ganin kansa a qasa da shi ba. Kuma wannan ya ishi afuwa falala da xaukaka.   

العشرون:
أنه إذا عفا وصفح كانت هذه حسنة، فتولد له حسنة أخرى، وتلك الأخرى تولد أخرى، وهلم جرا، فلا تزال حسناته في مزيد، فإن من ثواب الحسنة الحسنة، كما أن من عقاب السيئة السيئة بعدها، وربما كان هذا سببًا لنجاته وسعادته الأبدية، فإذا انتقم وانتصر زال ذلك.
NA ASHIRIN:
Lallai idan yayi afuwa, ya kuma yi rangwame sai hakan ya kasance lada a gare shi, sai ladan ta haifa masa wata ladan ta daban, sai itama waccar ta haifa masa wata, da sauransu; sai ya zama ladansa ba za su gushe ba suna ta qaruwa; saboda yana cikin ladan aikata aiki mai kyau, sake aikata wani aikin mai kyau, kamar yadda yana cikin uqubar aikata aiki mummuna, bawa ya sake aikata wata mummunan bayanta. kuma tayuwu hakan ya zama sababin samun tsiransa da rabutarsa ta har abada. Amma idan ya xauki fansan kuma, ya nemi samar wa kansa nasara sai hakan ya gushe.
وصلى الله على سيدنا محمد وآله وصحبه وسلم.

Kammalawa/ 19/ Safar/ 1437h,
Daidai da 01/ Disamba/ 2015m.
A garin Madinar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).

2015/11/19

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI Juma'a 08 Safar 1437h daidai da 20 Nobanba 2015m








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 08/SAFAR/1437h
Daidai da 20 /11/2015m



LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUSH SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya sanya yin biyayya a gare shi ya zama sababi na samun alkhairori, da kuma saukan albarkoki, Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Ubangijin qasa da sammai, Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma Manzonsa; Mafificin halittu, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa, har zuwa ranar mutuwa.
Bayan haka;
 Ya ku Musulmai!
Ina yin wasici a gare ku da ni kaina da kiyaye dokokin Allah mabuwayi da xaukaka, saboda da taqawar Allah ne ni'imomi suke sauka, kuma ake tunkuxe bala'oi.

'Yan'uwan Musulunci!
Halin da Musulmai suka samu kansu a wurare dayawa yana tada hankali kuma yana vata rai, musamman tare da bayyanar fitintinu masu makantarwa, da nau'ukan jarabawa mabanbanta, waxanda suka janyo wa Musulmai halaka da rushe-rushe da nau'ukan varna; a cikin ADDINI da RAYUKA da MUTUNCI da DUKIYOYI da GIDADDAJI, Bamu da damar juya hakan, kuma bamu da qarfi idan ba mun koma zuwa ga Allah ba (Wannan kuma shine ma'anar: لا حول ولا قوة إلا بالله).
Kuma lallai babban sababi, dangane da abinda ya sauka wa Musulmai na tashin hankali da fitintinu da kuma jarrabawa da musibobi shine: Nisantar Addinin Allah, da hanyar Annabi, a vangarorin rayuwa mabanbanta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk abinda ya same ku na musiba to sakamakon abinda hannayenku suka aikata ne, kuma (Allah) yana yafe abu dayawa",  [Shura: 30].
Kuma yana cewa:
"Varna ta bayyana a sarari da teku, saboda abinda hannayen Mutane suka aikata, don ya xanxana musu sashin abinda suka aikata, la'alla ko za su koma", [Rum: 41]. Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Kuma matuqar shugabanninsu basu yi aiki da abinda Allah ya saukar a cikin littafinsa ba, face Allah ya sanya yaqinsu a tsakaninsu". Kuma Aliyu (رضي الله عنه) yace:
"Bala'i baya sauka sai in anyi zunubi, Kuma ba a xauke bala'i sai idan an tuba".
            Don haka; Aikata munanan aiyuka, da sassavawa Ubangijin qasa da sammai = Suna gusar da ni'imomin da ake rayuwa a cikinsu, kuma suna yanke ni'imomi masu zuwa.  
Ibnul-Qayyim yana cewa: Bayani akan wannan a cikin Alqur'ani ya zo a fiye da wuri 1000 .
Kuma haqiqa fitintinun da suke sabbaba zubar da jini da kisa basu yi ta kai-komo, suka yawaita ga musulmai ba, Sai sakamakon yadda suka bayyanar da savawa karantarwar wahayin Alqur'ani da Hadisi.   Ya zo a cikin littafin (Musnad na Imam Ahmad) Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Idan savo suka bayyana a cikin al'ummata, to sai Allah ya game su da uquba daga wurinsa".

            To idan wannan lamari na gaskiya; wanda ya vuya ga zukata dayawa; musamman waxanda suka yi nisa daga karantarwar Alqur'ani da Sunnah = ya tabbata a zukata, To mu sani! Lallai akwai wassu GINSHIQAI MASU GIRMA, waxanda idan Musulmai suka fahimce su, suka yi aiki da su,  sannan suka yi kwaxayin ganin tabbatuwansu, To lallai zasu kuvuta daga na'ukan sharri mabanbanta, da kuma kaiton da fitintinu da jarrabawa suke jawowa;
            GINSHIQI NA FARKO: Tuba ta gaskiya zuwa ga Allah; ta hanyar komawa zuwa ga hanyar Allah, da yin aiki da shari'arSa, da bin umurninSa da kuma umurnin ManzonSa (صلى الله عليه وسلم);
            Wannan kuma, kasancewar da aikata tuba ne kawai, gyara cikin qasa ke tabbatuwa, a kuma yi aikin bunqasa rayuwa, sannan a tunkuxe nau'ukan sharri da fitintinu da musibu da bala'oi ga Mutane, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya, Ya ku Muminai, da fatan zaku samu rabo", [Nur: 31].
Kuma Allah yana faxa dangane da AnnabinSa Hudu:
"Ya ku Mutanena! Ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, Zai saki ruwan sama akanku mamako, kuma ya yi qarin qarfi a gare ku akan qarfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi" [Hudu: 51].
            Saboda haka;  Alkhairi da dukkan nau'ukansa yana nan ne akan tuba, Kamar  yadda shima kawo gyara da dukkan shakalinsa yake rataya akanta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan suka tuba zai zama alkhairi a gare su, Idan kuma suka juya baya, Allah zai azabta su azama mai raxaxi, a duniya da lahira, Kuma a cikin qasa basu da wani masoyi ko wani mataimaki" [Tauba: 74 ].
            Kuma tuba zuwa ga Allah; ta hanyar gyara abinda ya lalace, na barin wajibai, da aikata abubuwan haramun sababi ne na xauke bala'i, da tunkuxe musiba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah bai kasance zai azabta su, alhalin kana cikinsu ba, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba, alhalin suna neman gafara" [Anfal: 33].
Hasalima tuba ta kan zama sababin saukar alkhairori mabanbanta, da samuwar ababen farin ciki masu yawa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku daxi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma ya bai wa dukkan ma'abucin girma girmarsa" [Hudu: 3].
Kuma Allah yana faxa ta harshen Annabi Nuhu:
"Sai nace: Ku nemi gafarar Ubangijinku; lallai shi ya kasance mai yawar gafara  *  Zai saki ruwan sama akanku mamako  *  Kuma ya qarfafe ku da dukiya da 'ya'ya, kuma ya sanya muku lanbuna, kuma ya sanya muku qoramai" [Nuhu: 10-12].

            GINSHIQI NA BIYU: Yawaita aikata aiyukan xa'a, da sauran ababen qara kusantar Allah;
            Saboda da aikata haka, ake tunkuxe bala'oi, ake kuma jawo ni'imomi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya kiyaye dokokin Allah zai sanya masa mafita  *  Kuma ya azurta shi ta inda baya tsammani, Kuma duk wanda ya dogara ga Allah, to shi, ya isar masa" [Xalaq: 2-3 ].
            Ibnul-qayyim yana cewa:
"Shi mai kyautatawa mai yin sadaka: Yana amfani ne da runduna da mayaqan da suke yaqi a madadinsa, alhalin yana cikin barcinsa akan shumfuxinsa. Shi kuma wanda bashi da wata runduna ko mayaqa gashi kuma yana da maqiya, to lallai maqiyan nasa sun yi kusa su ci nasara akansa, koda kuwa lokacin hakan ya yi jinkiri. Allah ne mai taimako".

            Kuma ma'abuta Imani masu aiki da xa'ar Allah, da hanuwa da haninsa, Suna da wata kula ta musamman daga Allah, da kuma cikakkiyar kiyayewa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne, Allah yana bada kariya ga waxanda suka yi imani" [Hajji: 38].

            GINSHIQI NA UKU: Lokacin da gajimaren fitintinu suka lulluve sararin samaniyar wannan al'umma, kuma kumfar bala'oi suka kasance sune suke tuqa kwale-kwalenta = To a lokacin buqatuwar wannan al'ummar na ta zauna; ta zana hanyar tsiranta; don ta samu ta kai ga tudun tsira, ko gavar samun aminci , buqatuwarta zuwa ga haka Ya kan qara girma.
            Kuma lallai ba za ta tava samun hanyar hakan ba matuqar bata magance mushkilolinta da cutukan da suka addabe ta da hasken Alqur'ani mai girma, da kuma sunnar Annabi mai karaici ba.
            Kuma idan kayan baqanta rai da musibu, suka zama suna xakar fiskar wannan al'ummar, a cikin kowani kwari, To lallai babu abinda aka fi fatan samun mafita daga gare su fiye da neman warwaran waxannan matsalolin daga cikin wahayin Alqur'ani da Sunnah, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103]. kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun saukar da littafi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku, Ashe ba za ku hankalta ba", [Anbiya'i: 10]; Yana nufin: A cikinsa akwai xaukakarku da buwayarku, da kasancewanku shugabanni.
            Kuma Imamu Malik ya fitar a cikin (Muwaxxansa) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai shi yace:
"Na bari a cikinku al'amari guda biyu; ba za ku vata ba matuqar kun yi riqo da su; Littafin Allah, da sunnar AnnabinSa".
Kuma Abu-dawud ya fitar a cikin (Sunan, xinsa)| daga hadisin Irbadh xan Sariyah, Yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yayi mana sallah, sa'annan ya fiskanto mu, yayi mana wa'azi; irin wa’azi mai isarwa (mai ratsa jiki); wanda zukata suka tsorata, Idanu kuma suka zubar da hawaye daga gare ta. Sai muka ce: Ya Manzon Allah (s.a.w) kamar wa’azin mai bankwana; to kayi mana wasici, Sai yace, "Ina yin wasici akanku da bin dokokin Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama shugaba a kanku, lallai wanda ya rayu a cikinku da sannu zai ga savani dayawa, Na umarce ku da yin riqo da sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu. Ku riqe ta da haqoranku (Fiqa), kuma ku kiyaye fararrun ala’mura; domin kowace, bidi’a vata ce".
            Saboda riqo da wahayin Alqur'ani dana Sunnah a lokacin fitina, da kuma yin aiki da su a halin jayayya da savani, da neman hukunci a cikinsu a kowace rabewar kai da jayayya da husuma = su ne kaxai hanya guda xaya kwara; da za ta tunkuxe sharri, da nau'ukan vata, da tashin hankali masu yawa mabanbanta, da rashin nitsuwar da ta yaxu a duniyar Musulmai; ta yau.

            GINSHIQI NA HUXU: Aminci abun nema ne ga kowace al'umma, kuma gaya ce, da kowace qasa take neman cimma sa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanda ya wayi gari a cikinku, da aminci ko rashin tsoro a cikin kansa da jama'arsa (wato: iyalansa), ko hanyarsa, Da kuma lafiya a cikin jikinsa, A wurinsa akwai abincinsa na yininsa = To kamar an tattara masa Duniya ne gabaxayanta", Tirmiziy da Ibnu-Majah suka ruwaito shi, da isnadi mai kyau (hasan).

            Kuma lallai shi AMINCI yana dogara ne, akan haqqaqa ko tabbatar da gangariyar Imani da Allah mabuwayi da xaukaka, cikin aqida, da zantuka, da aiyuka. Kuma shi aminci asasinsa yana ginuwa ne akan yin aiki da umurnin da suka zo a cikin Alqur'ani, da kuma tarin faxakarwar da suka zo daga Annabi, tare da yin aiki da shari'ar Musulunci, cikin kowani sha'ani, daga cikin sha'anin rayuwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Waxanda suka yi Imani, kuma basu gauraya imaninsu da zalunci ba, Waxannan, sune suke da cikakken aminci, kuma sune shiryayyu" [An'am: 82].

            Kuma duk lokacin da wassu garurruka suka kauce wa shari'ar Allah, suka kuma bi abubuwan da zukatansu suke so, sai tsarinsu mummuna ya jagorance su = To sai su rasa amincin da suke fatan samu, sa'annan tsoro da firgici da rashin kwanciyar hankali ya maye gurbin aminci, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Allah ya buga misalin wata alqarya, wacce ta kasance amintacciya natsattsiya; arziqinta yana zuwa mata a wadace daga kowani wuri, Sai ta kafirta da ni'imomin Allah; Sai Allah ya xanxana mata tufafin yunwa da tsoro saboda abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahli: 112].

            GINSHIQI NA BIYAR: Lallai mafi muhimmanci daga cikin sabbuban da suke sanya al'umma ta yi qarfi sune: Taimakakkeniya a tsakanin Mutane; akan biyayyar Allah da taqawa, da haxa kai akan alkhairi da shiriya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya, kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103].
            Kuma lallai yana daga cikin manya-manyan musibun da aka jarrabi al'ummar Musulmai da su, kuma suka raunata qarfinta, suka kuma yasar da tutotin xaukakarta: Savani da rarrabuwar kai da husuma da jayayya, wanda mulkin mallakan da ya gabata a qarnonin da suka shuxe ya haifar da su ; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ku yi jayayya sai ku raunana, sai qarfinku ya tafi, Kuma ku yi haquri; lallai Allah yana tare da masu haquri" [Anfal: 46].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Kada ku yi qiyayya , kada ku yi hassada wa juna, kuma kada ku juya wa juna baya, Ku kasance bayin Allah 'yan'uwan juna, Baya halatta Musulmi ya qaurace wa xan'uwansa fiye da yini uku", Ahmad ya ruwaito shi, Amma asalin hadisin yana wajen Imam Muslim.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya ku Mutane! Na hore ku, da lazimtar jama'a, kuma ina hana ku rarraba kai. Ya faxi wannan har sau uku", Ahmad ya ruwaito shi.

            Kuma lallai abubuwan da suka auku a tarihi dalilai ne manya da suke nuna cewa lallai rarrabuwar kai halaka ne, kuma sababi ne na zagwanyewar al'umma da rushewarta;

(Wani MAWAQI yana cewa dangane da qasar Andalus wacce hakan ya same ta, a shekaru darurrukan da suka gabata, a yayin da aka samu rarrabuwar kai, da yawaitan qananan Sarakuna da masarautu):

Daga cikin abubuwan da suke sanya ni guje wa qasar "Andalus",
(مما يُزهِّدني في أرض أندلسٍ)
Sunayen "Mu'utadidu" a cikinta, da "Mu'utamidu".
(أسماءُ مُعْتضِدٍ فيها، ومُعْتَمِد).

A matsayin;
Laquban masarautu; waxanda aka sanya su, ba a gurbinsu ba.
(ألقاب مملكة في غير موضِعها).

Kamar muzurun da ke kumbura don ya kwaikwayi tuben Zaki.
(كالهِرّ يَحْكِي انتفاخًا صَوْلةَ الأسد).

            Wajibi ne akan Musulmai su kiyaye dokokin Allah, kuma kada su samu rarraba alhalin littafin Allah yana cikinsu; yana hukunci, da karantar da su, salon rayuwa.
Sunnar ManzonSa kuma (صلى الله عليه وسلم) tana haskaka musu, tana basu shiriya.
Tarihin halifofin Annabi shiryayyu shi kuma yana, abin koyi, kuma misali rayayye.
Kuma duk lokacin da suka karkace daga wannan hanya, to halinsu zai kasance kamar faxar mai faxi:

Kowa yana ganin wani ra'ayi, Yana kuma taimakon maganarsa
(كلٌّ يرى رأيًا وينصُرُ قولَه).
Kuma akanSa, yake adawa da sauran 'yan'uwa
(وله، يعادي سائر الإخوان).

Dadai ace, Su, a lokacin jayayya, za a datar da su,
(ولو أنهم عند التنازع وُفِّقوا).
Da miqa hukuncinsu zuwa ga Allah, ba tare da wani saivi ba.
(لتحاكموا لله، دون توان).

Kuma da sun wayi gari –bayan husuma- suna masoyan juna,
(ولأصبحوا –بعد الخصام- أحبةً).
Suna masu baqanta ran maqiya, waxanda kuma Shexan ke qara qasqanta da su.
(غيظ العدا، ومذلة الشيطان).

Amma duk lokacin da kansu ya rarraba, suke ta yin husuma da jayayya to kawai za su zama loma ce mai daxin lankwamewa a wajen maqiyansu da kuma Shexan.

Kuma shin –Ya kai Mai gani- Tare da girman abinda ya samu Musulman Duniya, Shin za su dawo zuwa ga shiriyarsu, su kuma sake haxuwa qarqashin tuta guda xaya (wato jagoransu a duniya ya zama Mutum xaya!),
Kundin xaukar salon rayuwarsu Wahayin Allah guda biyu (Alqur'ani, da sunnar Manzo?),
Me musu hukunci kuma shari'ar mai rahama (Allah)?
Muna roqon Allah ya tabbatar da haka, kusa-kusa; ba nesa ba. Lallai shi mai amsar addu'a ne.

            NA QARSHEN WAXANNAN GINSHIQAN SHINE: Mutane a lokacin bayyanar fitintinu su lazimci hanyoyin shari'a, da karantarwar Alqur'ani, da sunnar Annabi; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan wani lamari na tsoro ko aminci ya zo a gare su, sai su watsa shi, Kuma da za su mayar da shi zuwa ga Manzo, da kuma ma'abuta al'amari daga cikinsu, da waxanda suke bincikensa daga cikinsu za su san shi" [Nisa'i: 83]. Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Yin ibada a lokacin kashe-kashe kamar yin hijira ne zuwa gare ni".
            Kuma Musulmai –a lokacin fitintinu- dole su sani cewa lallai sha'anin HARSHE, da ALQALAMI (wato: yin magana, ko rubutu) yana da hatsari wajen tada fitina ko qara ruruta wutarta, kuma a lokacin fitina, lokaci ne da ake zaton zamewar qafa da yin kuskure, Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke marabarsa da harsunanku, kuma kuke faxa da bakunanku abinda baku da ilimi akansa, kuma kuna zatonsa mai sauqi, alhalin kuwa Shi, a warin Allah mai girma ne" [Nur: 15].

            Kuma lallai MALAMAI da SHUGABANNI, da WAYAYYU, da MASU AIKIN WATSA LABARU wajibin dake kansu –musamman a wannan zamanin- yana da girma, wajen bin diddigi da qoqarin tabbatar da abu, a lokacin fitina, tare da rashin tunzuruwa ko faxar duk wani abinda zai haifar da  fitina, ko qara ruruta wutarta.
Kuma duk wanda ya bibiyi fitintinun da suka yi ta aukuwa a qasashen Musulmai, a shekarun baya zuwa yau = Zai san gaskiyar abinda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada labara akansa, kuma zuciyarsa zata samu yaqini;  Cikin wani hadisin da wassu Maluma suka raunata shi, Wassu kuma suka nuna cewa  zai iya zama hadisi hasan (mai kyau), Saidai kuma ma'anar da hadisin ke xauke da ita ta zo cikin qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi kevantattu da gamammu. Wannan kuma shine hadisin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) yake cewa:
"Wata fitina, kurmiya, bebiya, makauniya zata kasance, Wanda ya nemi ya leqa ta to zata kama shi, Kuma tsoma baki a cikinta kamar aukar da tokobi ne", Abu-dawud ne ya rawaito shi.
Kuma a tarihi gabaxaya babu wata fitina da ta auku face tushenta maganar baka ne, ko rubuta, Wannan kuma shine dalilin da ya sa Abdullahi xan Abbas yake cewa:
"Lallai fitina da harshe take, Fitina bada hannu take ba".
Kuma abinda Musulmai suka gani na fitintinun wannan zamanin; waxanda sharrinsu yayi girma, cutarwarsu kuma tayi ta yaxuwa =  Na qara tabbatar da wannan maganar.
Allah shine mai taimako.

            Allah ya sanya mana albarka cikin wahayi guda biyu, ya kuma amfanar da mu da shiriyar da take cikinsu.
Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah a ni da ku, da kuma sauran Musulmai, Ku nemi gafararSa; lallai shi, Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU:
            Ina yabon Ubangijina kuma Ina gode masa, Kuma ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne. Ya  Allah ka yi salati da sallama a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa.
            Bayan haka;
            Ya ku Musulmai!
            Lallai yana daga mafi alkhairin aiyuka, waxanda suka fi tsarki: Yawaita yin salati da sallama ga Annabi mai karimci; saboda yin salati a gare shi da yawaita hakan sababi ne na sauqar albarka a bayan qasa, kuma sababi ne na tunkuxe bala'oi, Sai ku yawaita aikata hakan musamman a ranar Juma'a da darenta.

            Kuma lallai ne Mu, a qasar harami guda biyu masu xaukaka, An ni'imtar da mu da ni'imomi masu girma,
Mafifitansu kuma sune: Aiki da shari'a mai tsarki da yin hukunci da ita, da samun dunqulewa tsakanin shugabanni da waxanda ake shugabanta, wanda hakan kuma, suka haxu, suka sabbaba samun aminci da nitsuwa da kwanciyar hankali da wadaci,
Don haka;
Wajibi ne akan Mutanen wannan qasa da mazauna cikinta, da kuma sauran Musulmai, muyi godiya akan waxannan ni'imomin, mu kuma nisanci fushin Allah, da kuma yin aiki tuquru don neman yardarSa, da kuma kwaxayin tabbatuwan danqon alaqa tsakanin shugaba da waxanda ake shugabanta, akan gaskiya da shiriya.

            Kuma lallai wajibi ne akanmudangane da addininmu, da kuma Annabinmu: Mu bayyana wa Duniya girman Musulunci; Mu nuna musu cewa lallai addinin Musulunci addinin jin qai ne, da kyautatawa, da adalci, da kuma sauqi da tausasawa, da haxin kai.   Sannan kuma Duniya ta ga cewa lallai shi Musulunci shine yake samar da mafi girman al'umma ta fiskar wayewa da bunqasa, wanda suke rayuwa ko ni'imtuwa cikin walwala da wadaci da jin daxi da aminci, da soyayya da taimakakkeniya, da sauran ma'anoni masu girma maxaukaka, waxanda kowani halitta ke fatan dacewa da rabauta da su. Yin haka kuma wajibi ne; wanda Allah ya wajabta shi akanmu, dangane da addininmu.
Ya Allah!  Lallai Mu, muna roqonka –Ya Ubangijinmu, Ya abun bautarmu- muna roqonka ka bada buwaya ga addininka, kuma ka xaukaka kalmarka. Kuma ka haxa kan Musulmai akan alkhairi.
Ya Allah ka haxa kan Musulmai akan alkhairi da shiriya.
Ya Allah! Ka gyara halinmu da halin Musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, ka kore ababen vacin rai.
Ya Allah! Ka tseratar da bayinka Musulmai daga kowani ibtila'i da fitina.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiyan Musulmai; Lallai su, basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu Musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance mai taimako a gare su; Ya Mabuwayi ya Mai matsanancin qarfi.
Ya Allah! Ka datar da Mai hidiman Masallatan harami guda biyu zuwa ga abinda kake sonsa, kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka taimaki addini da shi, kuma ka xaukaka kalmar Musulmai da shi.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bamu mai kyau a Duniya, a Lahira itama mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar Wuta.

Bayin Allah!
Ku ambaci Allah ambato mai yawa,
Ku yi masa tasbihi safiya da maraice;
Qarshen addu'armu itace:

الحمد لله رب العالمين

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...