2018/05/31

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 17 Ramadana 1439H DR BUAIJAN 1 YUNI 2018












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 17/Ramadhana/1439H
daidai da 01/Yuni/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
DARARE GOMAN KARSHEN RAMADANA SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU SHINE MAFI GIRMAN BAUTA
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DARARE GOMAN KARSHEN RAMADANA SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU SHINE MAFI GIRMAN BAUTA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya sanya hanya ga wanda ya nemi tuba zuwa gare shi.
Wanda kuma ya mayar da lamura gare shi, ya ke sanya masa matabbata da mafi kyan wurin kailula.
Wanda kuma ya rayu cikin bautar Allah, ya kan sanya masa inuwa mai matabbaciyar lumshi; Don haka; wanda ya so, sai ya riki hanyar kirki zuwa ga UbangijinSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, ina mai girmama shi, kuma ina darajanta shi.
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, madalla da shi jagora kuma mai nusar da mutane hanya,
Allah ka yi karin salati a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa, da sallamar amintarwa mai tarin yawa.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku -Ya ku bayin Allah- da ni kai-na, da jin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, domin babu samun jin dadi da sa'ida sai ta hanyar takawar Allah, kuma ba a samun babban rabo sai ta hanyar da'a ga Allah Majibinci.

Sannan ku sani, Lallai da'a ko biyayyar Allah shine mafi alherin abinda aka ribata kuma aka aikata, samun yardarSa kuma, shine mafi alherin abinda aka ribata kuma abin nema, ita kuma Aljannah an kewaye ta da ababe masu wahala, Wuta kuma, an kewaye ta abinda Rai ke sha'awa. Kuma lallai za a cika ladan kwadagonku ne a gare ku, a ranar Kiyama; kuma duk wanda aka nisantar da shi daga Wuta, sai aka shigar da shi Aljannah to hakika ya samu babban rabo.

Ya ku masu azumi!!!
Allah ya karbi ayyukanku na 'da'a, kuma ya gyara halayenku (Amin), kuma ina rokonsa ya muku dace cikin abinda ya rage na wannan watan, kuma ya rubuta muku tabbatuwa akan biyayya a gare shi, a sauran kwanaki na rayuwa.

Ya ku taron Musulmai!!!
Ku ribaci lokaci iyakar ribata, ku yi gaggawan aikin alheri kuna masu sauri da rigaggeniya, saboda watanku mai karamci ya dau hanyarsa ta raguwa da tafiya, kuma dararensa da yininsa sun dau hanyar karewa da gushewa, Sai ku riski abinda ya rage daga cikinsa ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, kuma ku yi gaggawan tuba zuwa ga Ma'abucin girma da buwaya, Ya kaiton masu sakaci! Ya asarar tababbu batattu!! Ya musibar gafalallu!!!
Domin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya hau minbari sai ya ce: Amin! Amin!! Amin!!! Yayin da ya sauka, sai aka tambaye akan haka, sai ya ce: mala'ika Jibrilu ne ya zo min sai ya ce: Hancinsa ya bugi turbaya; Wanda ya riski watan Ramadana, sai ba a gafarta masa ba; har ya shiga wuta, kuma Allah ya nisanta shi daga rahama! Ka ce: Amin! Sai na ce: Amin!
Kuma hancinsa ya bugi turbaya; Wanda ya riski iyayensa biyu, ko kuma daya, sai bai musu biyayya ba, har ya mutu ya shiga wuta, Kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce: Amin, sai na ce: Amin!!
Kuma hancinsa ya bugi turbaya, wato Wanda aka ambaci sunanka a wurinsa sai bai maka salati ba, kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce: Amin, sai na ce: Amin!!!".

Ya ku taron Musulmai!!!
Lallai ayyuka ana sakayya ne akansu da abinda aka cike su da shi. Sai ku kara kokari, domin ba komai ba ne watan Ramadana, face kwanaki kidayayyu.
Kuma lallai kwanaki goman da suke gabanku sune mafificin lokatai, kuma  lokuta na musamman don aikata alkhairi da yin da'oi sune mafi girma, kuma su suka fi cancantar dacewa da yin kokarin bawa cikin ayyukan kusanci ga Allah.
Kuma duk da cewa ayyukan da'a a cikin sauran kwanakin wannan wata mai albarka suna da falala, sai dai a cikin kwanaki gomansa na karshe sun fi girman falala, kuma matsayinsu yafi daukaka, kuma sun fi lada mai gwabi.
Domin sune kwanaki goman da ake goge tuntube a cikinsu, a kankare munana, ake amsa addu'oi, kuma don haka ne "Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yake kara kokarin bauta a cikinsu irin abinda baya yinsa a waninsu, Kuma ya kasance idan wadannan goman suka shigo sai ya tamke kwarjallanSa, ya rika raya darenSa, yana tayar da iyalanSa".
Sai ku bayyanar da kwadayinku akan kwanakin, domin su ganima ce mai girma.
Kuma madalla da mutumin da ya samu rabo a cikinsu, kuma ya ribaci alkhairin cikinsu da falalarsu.

Ya ku Bayin Allah … !!!
A cikin kwanakin nan guda goma, akwai wani dare wanda yafi watanni dubu alheri, Rahama da jin-kai suna sauka a cikinsa, kuma ana amsa  addu'oi, ana kankare kura-kurai, ana gafarta laifuka, "Wanda ya tsayu a cikin wannan daren (yana sallah) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa".
Wanda kuma ya yi sakaci a lamarin wannan dare, sai aka haramta masa alkhairinsa, to shine abin zargi, marashin rabo.
Lallai shi ne, daren Lailatul kadr, abin neman mutane muminai, abin fatan samun salihai, burin masu takawa, wanda a cikinsa ake rubuta daukacin ababen da aka kaddara, kuma a cikinsa ake rarrabe kowani lamari da ake hukuntawa, Sai ku yi kwadayin tsayuwa a cikinsa da salloli, kuma ku zage domin nemansa, ku kara kwazo kan bidar dacewa da shi, kuma ku kankan-da-kai zuwa ga Allah a cikin wannan dare; saboda wannan daren –Wallahi- ganima ce ta cikin ruwan sanyi, domin yin ibada a cikin wannan dare yafi alheri akan ibadar watanni dubu.
Kuma ya dace, ga duk wanda ya nemi dacewa da wannan daren, ya zamto ba a tabar da shi ba, domin Allah Ma'abucin falala ne Mai girma; "Lallai Mu mun saukar da Kur'ani a cikin daren Lailatul kadr * To me ya sanar da kai abinda ake cewa Lailatul Kadari * Lailatul Kadari tafi alheri akan watanni dubu * Mala'iku da Ruhi (wato Jibrilu) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu, da kowane lamari * Aminci ne wannan daren, har zuwa fitowan alfijir" [Kadr, 1-5].


,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya sanya da'a a gare shi ta zama hanyar samun yardarSa, kuma ya sanya yardarSa ta zama hanyar rabauta da AljannarSa, kuma ya yi taufiki ga bayinsa muminai sai suka lazimci yin bauta a gare shi, suka kaurace wa jin-dadinsu da sha'awowinsu, suka fifita neman yardarSa.

Ya ku bayin Allah !! …
Itikafi shine lazimtar Masallaci domin yin ibada, da killace Rai daga sha'awowinta da jin-dadinta, da juya baya ga duniya da fitinunta, da abubuwa masu shagaltawa da masu dauke hankali. Da debe kewa ko kadaici ta hanyar ganawa da Allah -سبحانه-, da warewa gefe da ficewa daga jama'a da yanke huldodi, da barin wargi da wasa, da yin hisabi ga Rai, da sabunta ko jaddada alkawari tare da Allah, da kokarin tsarkake zuciya daga abinda ka iya makale mata na daudar da take cikin wannan rayuwar.

Kuma Allah Ta'alah ya shar'anta yin itikafi a cikin Masallatai, kuma ya yi umurnin a shirya Masallatan domin haka, a inda yake cewa: "Kuma muka yi alkawali zuwa ga Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake dakina, domin masu dawafi, da masu itikafi, da masu ruku'i, masu sujada" [Bakara: 125].

Ya ku bayin Allah…!!
Itikafi sunna ne, sai dai a cikin watan Ramadana yafi zama abin so, a gomansa na-karshe kuma yafi kasancewa abinda yafi karin karfi, saboda an ruwaito daga A'isha –Allah ya kara yarda a gare ta- lallai ta ce: "Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana, har Allah Mabuwayi da daukaka ya masa wafati, sa'annan sai matansa suka yi itikafin a bayansu", Bukhariy da Muslim.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi bn Umar –Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: "Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana".

Ya ku masu zuwa dakunan Allah (Masallatai)!!!
Masallatai sune dakunan Allah a doron kasa, Sai ku sane musu hakkokiknsu, ku ladabtu da laddubansu, kuma ku kiyaye wa masallatai matsayinsu da falalolinsu, domin an gina su ne domin bauta, sai ku yi aiki a cikinsu da ladabi da natsuwa, kuma kada ku rike su a matsayin wuraren wargi da wasa ko kamar kasuwa, kuma kada ku cutar da Masallata a cikinsu da masu itikafi, saboda cikin aikata hakan akwai hana su yin ibada, da kuma fitar da su daga cikin natsuwarsu.

Ya ku Ma'abuta itikafi!!!    
Kun zo dakunan Allah ne da nufin yin bauta, da yanke alakokin Duniya da fiskantar gidan Lahira, Sai ku fiskanci Allah da zukata masu mayar da lamura gare shi, masu cike da tsoronsa, kuma ku kankan da-kai zuwa gare shi tare da jin kaskanci, da rusunawa, da karayar zuciya. Kuma ku kiyayi abubuwan da suke daddatse muku hanya, ku kiyayi shagaltuwa da na'urorin komfiyutoci da wayan salula, da maganganun kila-da-kala. Kuma ku kiyaye wa Masallatai alfarmominsu.

Ya ku Ma'abuta itikafi a Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-!!!
Lallai ne babban ofishin ofishin kulawa da Masallatan Harami Biyu sun yi ayyuka tukuru ababen yabawa, wajen tarbanku, kuma sun shishshirya hawan ginin sama na Masallacin Annabi –صلى الله عليه وسلم- sun tanade shi, kuma sun kebance shi ga masu shiga itikafi. Kuma koyaushe suna cikin hidimarku, sai ku taimaki ma'aikatanmu; ta hanyar yin aiki da dokoki da tsare-tsare, don girmama Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, kuna masu yin hidima da aikata haka ga wadanda suka bakunce shi, masu taimakon bayin Allah akan ayyukan da'a, kuna masu fatan samun lada da sakayya, masu aiki da shari'a, saboda Allah Ta'alah yana cewa:
"Kuma a lokacin da muka iyakance wa Ibrahimu wurin daki, muka ce: Kada ka hada komai da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake dakina, domin masu dawafi da ma'abuta tsayuwar sallah, da masu ruku'i da sujada", [Haj: 26].

Allah! Ya karba muku irikafinku, da sauran dangogin ayyukanku na da'a.
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da …

,,,          ,,,          ,,,

GOMAN KARSHEN WATAN RAMADANA العشر الأواخر من رمضان









SAI,,, GOMAN KARSHEN RAMADANA SUKA SHIGO
(وجاءت العشر)









Tarjamar
Abubakar Hamza


DAMAR DA AKE SAMU A RAYUWA
Irin wannan suna ake sanya wa damammamkin da mutum ke wucewa ta kansu a rayuwarsa,
Kuma idan mutum bai ribaci irin wadannan lakutan ba, to ba dole ne su sake dawo mas aba.
Kuma lallai Allah a rayuwar mutane ya sanya dayawa daga wadannan damammaki da lokuta na musamman domin yin ibadodi, wadanda idan mutum ya ribace su, sai Allah ya ninninka ladansa, kuma ya daga darajojinsa, Kamar yadda Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:  
"تعرَّضوا لنفحات رحمة الله؛ فإنّ لله نفحاتٍ من رحمته، يصيب بها مَن يشاء مِن عباده"، [رواه الطبراني، وصححه الألباني في صحيحه، رقم: 1890].
Ma'ana: "Ku bijirar da kayukanku ga busawar rahamar Allah; saboda Allah yana da busawar iskar rahama; wanda yake samun mutumin da ya so daga cikin bayinsa da ita", ['Dabaraniy ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi a cikin sahihinsa, 1890].

Kuma yana daga cikin mafi girman wadannan damammaki da lokuta na musamman domin yin ibada, KWANAKI GOMAN KARSHEN WATAN RAMADANA, wanda a cikinsu akwai daren da alkhairinsa yafi na darare dubu, don haka Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana kara kokarin neman yardarm Allah a kwanaki goman karshen Ramadana, irin kokarin da baya yi a wasunsu" Muslim ya ruwaito shi [1175].  
Don haka, duk wanda ya so ya mori wannan damar, domin ya rabauta da samun ladan Allah a wadannan kwanakin, to yana wajaba akansa, ya karanta biye wa ababen sha'awa, da kuma shagalin duniya, sai kuma ya kara fiskantar ayyukan samun kusanci ga Allah, yana mai koyi da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- wanda "ya kasance idan kwanaki goma suka shiga sai ya tamke kwarjallensa, ya rayar da darensa, kuma ya tayar da iyalansa daga barci", Bukhariy da Muslim.

Saboda yana daga cikin SHIRIYAR ANNABI S.A.W A WADANNAN KWANAKIN:
1/ Raya dukkan dare da salloli da kuma tilawar Alkur'ani,
2/ da kuma tayar da iyalai daga barci, domin aikata hakan.

Kuma MUSTAHABBI ne a cikin wadannan kwanakin, yin itikafi a Masallaci domin shagaltuwa da aikin biyayya ga Allah, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama ya kasance- yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana", Bukhariy da Muslim.

Domin awowi ne kadan, a cikin yinin samun gafara da jin-kai, da kuma 'yanta bayi daga fadawa cikin wuta.
SAI KA RIBACE SU, DOMIN AKWAI YIWUWAR BA ZA SU SAKE DAWOWA BA.



2018/05/30

SAI,,, GOMAN KARSHEN RAMADANA SUKA SHIGO (وجاءت العشر)









SAI,,, GOMAN KARSHEN RAMADANA SUKA SHIGO
(وجاءت العشر)









Tarjamar
Abubakar Hamza


DAMAR DA AKE SAMU A RAYUWA
Irin wannan suna ake sanya wa damammamkin da mutum ke wucewa ta kansu a rayuwarsa,
Kuma idan mutum bai ribaci irin wadannan lakutan ba, to ba dole ne su sake dawo mas aba.
Kuma lallai Allah a rayuwar mutane ya sanya dayawa daga wadannan damammaki da lokuta na musamman domin yin ibadodi, wadanda idan mutum ya ribace su, sai Allah ya ninninka ladansa, kuma ya daga darajojinsa, Kamar yadda Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:  
"تعرَّضوا لنفحات رحمة الله؛ فإنّ لله نفحاتٍ من رحمته، يصيب بها مَن يشاء مِن عباده"، [رواه الطبراني، وصححه الألباني في صحيحه، رقم: 1890].
Ma'ana: "Ku bijirar da kayukanku ga busawar rahamar Allah; saboda Allah yana da busawar iskar rahama; wanda yake samun mutumin da ya so daga cikin bayinsa da ita", ['Dabaraniy ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi a cikin sahihinsa, 1890].

Kuma yana daga cikin mafi girman wadannan damammaki da lokuta na musamman domin yin ibada, KWANAKI GOMAN KARSHEN WATAN RAMADANA, wanda a cikinsu akwai daren da alkhairinsa yafi na darare dubu, don haka Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana kara kokarin neman yardarm Allah a kwanaki goman karshen Ramadana, irin kokarin da baya yi a wasunsu" Muslim ya ruwaito shi [1175].  
Don haka, duk wanda ya so ya mori wannan damar, domin ya rabauta da samun ladan Allah a wadannan kwanakin, to yana wajaba akansa, ya karanta biye wa ababen sha'awa, da kuma shagalin duniya, sai kuma ya kara fiskantar ayyukan samun kusanci ga Allah, yana mai koyi da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- wanda "ya kasance idan kwanaki goma suka shiga sai ya tamke kwarjallensa, ya rayar da darensa, kuma ya tayar da iyalansa daga barci", Bukhariy da Muslim.

Saboda yana daga cikin SHIRIYAR ANNABI S.A.W A WADANNAN KWANAKIN:
1/ Raya dukkan dare da salloli da kuma tilawar Alkur'ani,
2/ da kuma tayar da iyalai daga barci, domin aikata hakan.

Kuma MUSTAHABBI ne a cikin wadannan kwanakin, yin itikafi a Masallaci domin shagaltuwa da aikin biyayya ga Allah, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama ya kasance- yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana", Bukhariy da Muslim.

Domin awowi ne kadan, a cikin yinin samun gafara da jin-kai, da kuma 'yanta bayi daga fadawa cikin wuta.
SAI KA RIBACE SU, DOMIN AKWAI YIWUWAR BA ZA SU SAKE DAWOWA BA.

2018/05/27

HUKUNCE-HUKUNCEN ITIKAAFI (أحكام الاعتكاف)









HUKUNCE-HUKUNCEN I'ITIKAAFI
(أحكام الاعتكاف)









Tarjamar
Abubakar Hamza


ITIKAAFI shine lazimtar Masallaci domin yin dangogin ayyukan biyayya ga Allah Ta'alah!
Kuma shi mustahabbi ne, ga Maza da Mata, a dukkan lokatan shekara, Allah Ta'alah ya ce:
"وعهدنا إلى إبراهيم وإسماعيل أن طهرا بيتي للطائفين والعاكفين والركع السجود"، [البقرة: 125].
Ma'ana: "kuma Muka yi alkawari zuwa ga Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake 'Dakina, domin masu dawafi da masu itikaf, da masu ruku'i masu sujada" [Bakara: 125].

Mustahabbancin yin itikafi na kara karfi a watan Ramadhana, musamman kuma a goman karshen watan, domin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance "yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadhana, har Allah ya masa wafati", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Kuma ga maganar da tafi inganci, babu gwargwadon lokaci iyakantacce ga mafi karancin kwanaki ko lokacin yin itikafi, don haka yana inganta ayi itikafi koda na dan wani lokaci ne kankani.

Kuma ana shardantawa, gabanin itikafi ya inganta ya kasance a cikin Masallaci, saboda fadinSa Madaukaki:
"ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد" [البقرة: 187].
Ma'ana: "Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu itikafi a cikin Masallatai", [Bakara: 187].

Kuma sharadi ne gabanin itikafi ya inganta, mai itikafin ya kasance tsarkakakke daga abinda ke wajabta wanka, kamar janaba da haila.

Kuma wajibi ne akan Mace ta nemi izinin Mijinta.

Kuma mai itikafi bashi da daman neman abinci da yin wata sana'a, ko kuma saye da sayarwa, sai dai idan da bukata.
Kuma baya halatta a gare shi ya fita daga Masallaci, sai dai idan da uzuri, koda kuwa zai fita ne saboda ziyartar maras lafiya, ko rakiyar gawa.
Kuma yana halatta a gare shi, mai itikafi ya fita, ga abinda babu makawa akansa, kamar biyan bukata, da halarto da abinci da makamancinsa.
Kuma yana halatta a gare shi, mai itikafi ya yi wankan tsafta ko wanke kansa, ko taje shi,
"Uwar muminai A'ishah –Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce: Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- idan ya shiga itikafi, yana kusanto mini da kansa, domin na taje masa. Kuma ya kasance baya shigowa gida, sai domin bukatar 'dan-Adam (shiga makewayi)", Muslim ya ruwaito [1297].

        'Da'arka ga Allah ita ce shukar da zaka girbe a lahira, sai ka yi kwadayin wannan shukar ta kubuta daga abinda zai tauye ta, da kuma kura-kurai, Allah Ta'alah yana cewa:
"تلك حدود الله فلا تقربوها كذلك يبين الله آياته للناس لعلهم يتقون" [البقرة: 187].
Ma'ana: "Wadancan iyakoki ne na Allah, don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah ke bayyana ayoyinSa ga Mutane, la'alla ko za su samu takawa" [Bakara: 187].

I'ITIKAAFI KEBANCEWA TARE DA ALLAH (خلوة مع الله)









I'ITIKAAFI
الاعتكاف
KEBANCEWA TARE DA ALLAH
(خلوة مع الله)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Shin kana samun matsalar kaikashewar zuciya?

Shin kana koka yawaitar damuwa da bacin-rai, da ayyuka masu shagaltarwa, da mushkilar sakaci ko karanta ibada??

Shin kana son karin yawaita kusantar Allah, sai dai baka samun iya aiwatar da hakan???

Idan kana samun 'daya daga cikin wadannan matsalolin, to kada ka yi sakaci kan aiki da wannan ibadar; wato: I'ITIKAAF!
Saboda I'ITIKAFI dama ne mai girma, domin kakkabe ko rage ayyukan da suka shagaltar da zuci, tare da yin sauri ko yawaitar karin taku domin tafiya zuwa ga Allah Ta'alah,


Kuma cikin yin i'itikafi, akwai bada foro ko yin training ga rai, kan kyautata amfana da lokaci.

Da yawaita yin ibadodi.

Da neman kubuta daga wasu munanan al'adodi, kamar yawaita cin abinci, da yawaita barci, da yawaita magana.

Kuma domin musulunci ya tsinki ALFANO KO FA'ODODIN I'ITIKAF, to ya dace, a lokacin I'itikafinsa ya shagaltu da/

Ambaton Allah Ta'alah
Da salloli
Da tilawar Alkur'ani,
Da sauran abinda ke kama da wadannan daga dangogin ayyukan 'da'a,

Sai kuma ya nisanci dukkan abinda bashi da wata fa'ida, ko kuma ba a bukatuwa zuwa gare shi.

Da dukkan abinda ke iya sace lokaci, ko ya dauke hankali, daga barin ibada.


Lallai i'itikafi ibadar kebancewa ne, wanda Musulmi ke ribatarta, domin kara-samun kusanci zuwa ga Allah Ta'alah; kuma Allah Ta'alah yana fada a cikin hadisin kudusiy:
"إذا تقرب العبد إليّ شبرًا تقربت إليه ذراعًا، وإذا تقرب مني ذراعًا تقربتُ منه باعًا، وإذا أتاني مشيًا أتيتُه هرولة"، رواه البخاري: 7536، ومسلم: 2675.
Ma'ana: "Kuma idan Bawana ya kusance ni da kamar taki 'daya, to ni kuma zan kusance shi da kamar zira'i, idan kuma ya kusance ni da kamar zira'i, to zan kusance shi da kamar tsawon hannu 'daya. Idan kuma ya zo min cikin halin tafiyar kafa, ni kuma zan zo masa cikin sassarfa " [Bukhariy: 7536, da Muslim: 2675]. 

2018/05/20

GABANIN 'DANKA YA SHIGA MAKARANTA (قبل أن يدخل ولدك المدرسة)








GABANIN 'DANKA YA SHIGA MAKARANTA
(قبل أن يدخل ولدك المدرسة)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Neman Makaranta mai kyau, da Malamai zaka-kurai, da kayayyakin Makaranta, lamura ne da iyaye ke bincike akansu, domin shirin shigar da 'yayansu ga Makaratu.
Saidai wadannan ababen duk da muhimmancinsu, ba za su isar ba, su kadai, wajen sauke nauyin abinda ya wajaba na tarbiyyar Yara. Saboda tarbiyyar Yara ta fiskar halayyansu da 'dabi'unsu amana ce, da daukanta a farkon fari ke wuyan Uwa da Uba, a cikin gida, domin
"Namiji a cikin gidansa mai kiyo ne, kuma shi abin tambaya ne kan abinda akabashi kiyo. Kuma itama Mace a cikin gidan mijinta mai kiyo ce, kuma ita abar tambaya ce akan abinda aka bata kiyo", Bukhariy da Muslim. Wannan ya nuna, bada kulawa ga 'ya'ya ya kan fara ne tun suna kanana, gabanin a shigar da su Makarantu; Ta hanyar
shuka ma'anonin tsoron Allah da girmama shi a cikin zukatansu,
da karantar da su Alkur'ani mai karamci,
da wasu daga cikin hadisan Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-,
da tarbiyyantar da su akan ladduban Musulunci, a cikin lamuran ci da sha, da ladduban barci da kuma tasowa daga gare shi, da makamantansu.
Da nuna musu muhimmancin yin salla akan lokacinta, ta hanyar Mahaifi ya bada misali abin koyi, da gamammen kwadaitarwa,
Haka kuma jiyar da su kissoshin musulunci da tarbiyya, wadanda za su shuka manyan fahimtoci a zukatan yara, su kuma bunkasar da bangarorin alkhairi da gyaruwan halaye a tattare da su.

        Kuma rawan da iyaye ke takawa ta tarbiyya, bata karewa, wai domin 'ya'yansu sun shiga makarantu, a'a, bal, za su kara da lamarin fadakar da 'ya'yan kan girmama da karrama malumansu,
Da karfafa su kan zaben abokai natsattsu wajen dabi'unsu da halayensu,
Da bibiyar ababen da suke daukowa daga Makaranta; na darrusa da nau'ukan tunani,
Da basu damar yin wasa, wanda zai tafi tare da bukatar yaro, da kuma yawa ko karancin shekarunsu, tare da zaba musu nau'ukan wasanni masu amfani, da nisatar da su irin wasannin da suke zaburar da yaro kan keta, da munanan dabi'u.

        Ayyukan iyaye biyu -kenan- suna da girma, kuma wajibin da ke kansu babba ne, Ibnul-kayyim –Allah yay i masa rahama- yana cewa:
"BABU ABINDA KE BATA TARBIYYAR 'YA'YA, FIYE DA GAFALA DA KO-OHON IYAYE DA KYALE YARAN, KUMA SAU DAYAWA UBA YANA HARAMTA WA 'DANSA ALHERIN DUNIYA DA LAHIRA,,, KUMA DUKKAN WANNAN YANA DAGA ABABEN DA SAKACIN IYAYE KAN HAKKOKIN ALLAH DA TOZARTA SU, DA JUYA BAYANSU GA ABINDA ALLAH YA WAJABTA SHI AKAN IYAYE; NA NEMAN ILIMI MAI AMFANI DA YIN AIKI NA-KWARAI KE HAIFARWA" (Tuhfatul Maudud: 240).


TA YAYA ZAN YI ALWALA (كيف أتوضأ؟)








TA YAYA ZAN YI ALWALA
(كيف أتوضأ؟)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Abokaina!
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMAULLAHI WA BARAKATUHU
Yaya ku ke?
Shin 'dayanku, ya san ma'anar kalmar "Wudu'u"; alwala?
E, kun kyauta.
"Wudu'u", daga kalmar "wada'ah" ne, wanda itace: tsafta.

Hakika Musulunci ya shar'anta mana yin alwala gabanin kowace sallah,

Don haka, Na zo, domin mu koyi yadda za mu yi alwalar, a tare?

Gabanin yin alwala, dole ne mu ambaci sunan Allah Ta'alah; sai mu ce: BismilLahi.

Sa'annan mu wanke tafukan hannayenmu biyu, sosai har sau uku, kuma ya dace mu tsettsefe yatsunmu da ruwa, kamar haka.

Sa'annan mu shigar da ruwa cikin bakunanmu, domin mu wanke su, sosai, kamar haka, kuma za mu aikata hakan har sau uku. Kuma wannan aikin ana kiransa da suna: kurkuran baki.

Sai kuma mu sanya sashin ruwa a cikin hancinmu, sai kuma mu fitar da shi, za mu aikata hakan har sau uku shima. Kuma wannan aikin ana kiransa da sunan: Shaka ruwa a hanci da fyacewa.

Sa'anan mu wanke fiskokinmu gaba daya, kamar haka, har sau uku. Kuma dole ruwan ya game dukkan fiska; tun daga kunnen dama, zuwa kunnen hagu. Sannan kuma daga farkon goshi har zuwa haba, kamar yadda kuke gani.

Sa'annan sai mu wanke hannayenmu biyu, sau uku, tun daga kan 'yan yatsunmu, har zuwa guiwowin hannu, kamar haka. Kuma za mu fara ne da hannun dama, daga farko. Sai kuma hannun hagu ya biyo baya.

Sa'annan mu shafi kanmu gaba dayansa, sau daya, sai mu fara shafan, ta gaba, har zuwa baya. Sai kuma daga bayan mu tafo gaba, kamar yadda kuke gani.

Sa'annan sai mu shafi kunnuwanmu biyu gaba daya, sau daya, da ruwan da muka shafi kanmu dazu.

Sa'annan mu zo ga wanke kafofinmu, sai mu wanke su sosai, har zuwa idanun sawu, sau uku. Kuma za mu fara da kafar dama daga farko, sai kuma mu biyar da wanke kafar hagu.

To, da wannan ne –Ya ku abokaina- za mu zamto mun gama alwala, Sai kuma mu yi irin addu'ar da Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ke fadanta a bayan kammala alwala. Mu fada tare, mu ce:

ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, ALLAHUMMAJ AL'NIY MINAT TAWWABINA, WAJ'ALNIY MINAL MUTADAHHIRINA.

Hum, Yanzu ya ku abokaina, mun wayi gari cikin shirin yin sallah.
Allah ya karba mana, mu da ku.
Wassalamu alaikum wa rahmatul Lahi wa barakatuhu.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...