SAI,,, GOMAN KARSHEN RAMADANA SUKA
SHIGO
(وجاءت العشر)
Tarjamar
Abubakar Hamza
DAMAR DA AKE SAMU A RAYUWA
Irin wannan suna ake sanya wa damammamkin da mutum ke wucewa ta kansu a
rayuwarsa,
Kuma idan mutum bai ribaci irin wadannan lakutan ba, to ba dole ne su
sake dawo mas aba.
Kuma lallai Allah a rayuwar mutane ya sanya dayawa daga wadannan
damammaki da lokuta na musamman domin yin ibadodi, wadanda idan mutum ya ribace
su, sai Allah ya ninninka ladansa, kuma ya daga darajojinsa, Kamar yadda Annabi
–sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"تعرَّضوا لنفحات رحمة الله؛ فإنّ لله نفحاتٍ من رحمته، يصيب بها مَن
يشاء مِن عباده"،
[رواه الطبراني، وصححه الألباني في صحيحه، رقم: 1890].
Ma'ana: "Ku bijirar da kayukanku ga busawar
rahamar Allah; saboda Allah yana da busawar iskar rahama; wanda yake samun
mutumin da ya so daga cikin bayinsa da ita", ['Dabaraniy ya
ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi a cikin sahihinsa, 1890].
Kuma yana daga cikin mafi girman wadannan damammaki da lokuta na
musamman domin yin ibada, KWANAKI GOMAN KARSHEN WATAN RAMADANA, wanda a cikinsu
akwai daren da alkhairinsa yafi na darare dubu, don haka Manzon Allah –sallal Lahu
alaihi wa sallama- ya kasance yana kara kokarin
neman yardarm Allah a kwanaki goman karshen Ramadana, irin kokarin da baya yi a
wasunsu" Muslim ya ruwaito shi [1175].
Don haka, duk wanda ya so
ya mori wannan damar, domin ya rabauta da samun ladan Allah a wadannan
kwanakin, to yana wajaba akansa, ya karanta biye wa ababen sha'awa, da kuma shagalin
duniya, sai kuma ya kara fiskantar ayyukan samun kusanci ga Allah, yana mai
koyi da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- wanda "ya kasance idan kwanaki goma suka shiga sai ya tamke
kwarjallensa, ya rayar da darensa, kuma ya tayar da iyalansa daga barci", Bukhariy da Muslim.
Saboda yana daga cikin SHIRIYAR ANNABI
S.A.W A WADANNAN KWANAKIN:
1/ Raya dukkan dare da salloli da kuma
tilawar Alkur'ani,
2/ da kuma tayar da iyalai daga barci,
domin aikata hakan.
Kuma MUSTAHABBI ne a cikin wadannan
kwanakin, yin itikafi a Masallaci domin shagaltuwa da aikin biyayya ga Allah,
saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa
sallama ya kasance- yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan
Ramadana", Bukhariy da Muslim.
Domin awowi ne kadan, a cikin yinin samun
gafara da jin-kai, da kuma 'yanta bayi daga fadawa cikin wuta.
SAI KA RIBACE SU, DOMIN AKWAI YIWUWAR BA
ZA SU SAKE DAWOWA BA.
No comments:
Post a Comment