FIKIHUN AZUMI
(فقهُ الصيام)
NA
SHEHIN MALAMI
HAISAM BN MUHAMMADU JAMIL SARHAN
Tsohon Malami a
Sakandaren Masallacin Annabi -SAW-,
kuma shugaban
shafin intanet
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Bismillahir
rahmanir Rahim
AZUMI
wato, SIYAAM a
harshen larabci, shine: Kamewa.
A shari'a kuma, Bauta wa Allah, ta hanyar kamewa
daga cin abinci, da abin sha, da sauran ababen da suke karya azumi, daga
ketowar alfijir na-gaskiya, zuwa faduwar rana.
RUKUNNAN AZUMI
1- Niyyah.
2- Kamewa daga
ababen da suke karya azumi.
KARKASUWAR NIYYA A
CIKIN AZUMI
1- Niyyar azumin farilla: Babu
makawa dole ne, sai an kwana da niyyar, ga azumin farillai, tun cikin dare,
wato gabanin ketowan alfijir. Kuma yana wadatarwa a kulla niyyar daga shigan
watan azumi. Kuma mahallin niyya zuciya ne, furta ta kuma da harshe bidi'a ne.
2- Niyyar azumin nafila: Kuma
niyyar tana inganta idan aka yi ta cikin kowace dakika ko lokaci na yini,
matukar bai kusanci abinda ke karya azumin ba. Sai dai zai fara samun lada ne,
daga yin niyya.
KARKASUWAR AZUMI
1- Azumi na
wajibi: (Ramadana, kaffara, da bakance).
2- Na nafila.
SHARRUDAN WAJABCIN
AZUMIN RAMADANA
1- Musulunci.
2- Hankali.
3- Balaga (Shi kuma Yaron da ya kai shekarun
tantancewa, za a rika kwadaitar da shi kan azumi, waliyyinsa ya rika umartarsa).
4- Zaman gari (Saboda azumi baya wajaba akan
matafiyi, kuma abinda yafi a gare shi, shine ya yi azumin, matukar azumin ba
zai yi tsanani a gare shi ba; saboda hakan shine aikin Annabi –صلى الله عليه وسلم-, kuma saboda hakan shi
yafi saurin sauke nauyin da ya doru a wuyansa, kuma yafi sauki ga mutum, kuma
domin ya riski falalar yin azumi a cikin wannan watan).
5- Lafiya.
6- Kubuta
daga jinin haila da na haihuwa.
CUTA KASHI BIYU NE
DANGANE DA AZUMI:
1-
Cutar da ba a tsammanin gushewarta.
Ana yin kiyasin tsofon da ya gajiya;
wanda kwata-kwata ba zai iya azumi ba, da majinyacin da ba zai iya shi ba; sai
azumin ya sauka akansa, sai dai kuma zai ciyar da miskini guda daya a madadin
kowane azumi; ko ta hanyar ya hada miskinai gwargwadon yawan kwanakin da bai yi
azuminsu ba, sai ya ciyar da su. Ko kuma ya rarraba abinci ga miskinan, na
tsawon wadannan kwanakin; ta hanyar baiwa kowane miskini rubu'i wato daya bisa
hudun sa'iy irin sa'in Annabi SAW; (1/4), (Ma'ana: ya
bayar da gwargwadon awun rabin kilo, da giram goma, na shinkafa ko alkama mai
kyau).
Kuma abu ne mai kyau ya hada da
abinda zai zama, kamar miya a gare shi, na mai, ko nama.
2-
Cutar da ake tsammanin za ta gushe; sai dai yin azumi zai tsananta ga
mai ita, Wannan kuma ana kiyasin mace mai haila da jinin biki (haihuwa), da mai
shayarwa, da matafiyi, da wannan nau'i na jinya, Sai majinyacin ya biya adadin
kwanakin da ya karya azumi a cikinsu; idan har ya warke. In kuma ya rasu
gabanin ya samu damar biya, to azumin ya fadi a wuyansa.
Kuma shigowan watan Ramadana yana
tabbatuwa, ta hanyar ganin jinjirin wata, ko kuma watan Sha'abana ya cika
kwanaki talatin (30).
ABABEN DA SUKE LALATA
AZUMI
(amma ana yin
uzuri ga Jahili, da Mai mantuwa, da wanda aka masa tilasci)
1-
Ci, ko sha da ganganci, Amma wanda ya yi
da mantuwa to azuminsa ingantacce ne.
2-
Jima'i,
Idan ya auku a cikin yinin Ramadana,
alhali yin azumin wajibi ne akansa, To dole ne ya yi kaffara mai tsanani, wanda
ita ce, 'yanta baiwa, idan kuma bai samu ba, sai ya yi azumin watanni biyu a
jere, idan kuma ba zai iya ba, sai ya ciyar da miskinai sittin.
3-
Fitar maniyyi, ta hanyar runguma, ko sumba, ko
hada jiki, ko makamancinsu.
4-
Abinda ke daukar ma'anar ci da sha, Misalin allurar abinci, Amma wanda
ba a sanya mata abinci a cikinta ba, ita kam bata karya azumi.
5-
Fitar da jini ta hanyar kaho, Amma fitar da jini kadan, domin
awu, ko makamancin haka, shi kam baya karya azumi.
6-
Yin amai da ganganci.
7-
Fitar jinin haila da na biki (haihuwa).
MUSTAHABBAN AZUMI
1-
Yin sahur.
2-
Jinkirta yin sahur.
3-
Gaggauta buda-baki.
4-
Yin buda-baki da dabinon da bai bushe ba (rudab), idan
bai samu ba, sai ya yi da busasshen dabino, kuma dabinon su kasance wutiri,
Idan kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa, Idan kuma bai samu wani abu ba, sai ya
yi niyyar karya azumin a zuciyarsa.
5-
Yin addu'a a lokacin buda-baki, da a halin azumi.
6-
Yawaita yin sadaka.
7-
Dagewa wajen yin sallolin dare.
8-
KaratunAlkur'ani.
9-
Yin umrah.
10-
Fadin: Ni mai
azumi ne, ga wanda ya zage shi.
11-
Kokarin neman Lailatul kadr.
12-
I'itikafi a goman karshen watan azumi.
MUKRUHAN AZUMI
1-
Kaiwa makura cikin kurkuran baki.
2-
'Dandana abinci, ba tare da bukatar hakan ba.
YA HALATTA GA MAI AZUMI
Hadiye yawu, 'dan'dana abinci yayin bukata, yin wankan
ibada, Yin asiwaki, shafa turare, da yin wanka domin jin sanyi.
HARAMUN NE GA MAI AZUMI
Hadiye kaki (sai dai baya karya azumi), Da yin sumba, ga
wanda ke tsoron lalacewar azuminsa, da fadin zancen zur ko shaidar karya (da
aikata kowane haramun), da aikin jahilci (wauta, da rashin hakuri), da yin
wucel (ma'ana ya yi kwanaki biyu bai yi buda-baki ba).
AZUMIN NAFILA
1-
Yin azumin ranaku shida a watan
Shawwal, ga wanda ya cika azuminsa na Ramadana. Kuma abinda ya fi, shine, a
fara yinsu daga yini na biyu, kuma a jeranta su.
2-
Azumin yinin Arafah, ga wanda ba Mahajjaci ba.
3-
Azumin yinin Ashura, da kuma ranar
tara, da ranar goma sha daya (9, 10, 11, na watan Muharram).
4-
Azumin ranar Litinin da Alamis, kuma na ranar
litinin sunnarsa tafi karfi.
5-
Azumtar kwanaki uku, a kowane wata,
kuma abinda yafi shine azumin su kasance a kwanakin da wata ke cika haskensa
wato, 13, 14, da 15.
6-
Azumtar yini, da shan ruwan yini.
7-
Yin azumi a cikin watan Allah na
Muharram.
8-
Azumtar yini tara na farkon watan
Zul-hijjah.
9-
Yin azumin watan Sha'aban, amma kada
ya kammala shi gaba daya.
AZUMI NA MAKRUHI
Yinin Juma'a, da Asabat, da Lahdi, makruhi ne a kebance
kowanne da azumi, sai dai idan kebe shin ya zamo sakamakon wani sababi ne, to
ba makruhi ba ne, kamar yinin Arafah.
AZUMI NA HARAM
1-
Kebe watan Rajab da azumi.
2-
Azumtar yinin shakku, Amma wanda ya
saba da wani azumi, to babu komai akansa.
3-
Azumtar yinin idi guda biyu.
4-
Azumtar kwanaki uku na bayan idin
layya (Tashrik), sai ga mahajjacin da bai mallaki hadaya ba.
5-
Azumtar zamani (kullum-kullum).
Mustahabbi ne, a jeranta azumin ramuko, kuma ya dace, mutum
ya yi gaggawan yinsu, daga bayan idi, kuma bai halatta ya jinkirta ramukon da ke
kansa har wani Ramadanan ya sake shigowa ba, Idan kuma ya jinkirta shin, ba
tare da wani uzuri ba, to dai wadancan azumin da suka wucen, su zai rama (babu
kari), sai dai kuma ya yi zunubi.
ZAKKAR FID-DA-KAI (FIDR)
Tana wajaba ne ga wanda ranar
yinin Ramadana na karshe ta fadi masa alhalin yana Musulmi, sai sa'in abinci
'daya ya doru akan abincinsa da na iyalan gidansa da bukatunsa na asali.
Kuma mustahabbi ne a cire ta
ga 'Dan tayi (da ke cikin mahaifa).
HIKIMAR FITAR DA ZAKKAR FID-DA-KAI (FIDR):
1-
Domin ta tsarkake mai azumi daga
wargi da kwarkwasa.
2-
Domin a wadatar da miskinai; kada su
yi roko a ranar idi (yinin farin ciki).
LOKACIN FITAR DA ZAKKAR FID-DA-KAI (FIDR).
1-
Lokaci na halacci, shine kuma
gabanin ranar idi da yini daya ko biyu.
2-
Lokaci na mustahabbi, shi kuma shine, gabanin ayi sallar idi, bayan
ketowan alfijir.
3-
Lokaci na haramci wannan kuma
shine, Bayan yin sallar idi.
GWARGWADONTA (ZAKKAR FIDR)
Sa'iy daya ne na dangogin abincin da Mutane suka rika a
matsayin abinci, don haka, bata isarwa idan aka fitar da ita daga cikin kudi.
(Gwargwadon
sa'iy shine, kilo biyu, da giram arba'in na alkama mai kyau).
SALLAR IDI
Farilla ce akan kowane mutum.
Kuma ana sallatar ta ne, bayan dagowar rana daidai da
kibiya, har zuwa lokacin gotawar rana (wato, zawali).
Kuma ba a yin ramukonta, idan ta wuce.
Sunnah shine a yi ta a sahara ko fili, ba cikin gini ba.
Kuma ya halatta a yi ta a cikin masallaci.
Mustahabbi ne mutum ya ci dabino wutiri gabanin sallar
idi, kuma ya yi tsafta, ya fesa turare, ya sanya mafi kyan tufafinsa, ya tafi
ta wata hanya, ya komo ta wata hanya.
Babu laifi kan gaishe-gaishen idi, ta hanyar fadin:
TAKABBAL LAHU MINNAH WA MINKUM (Allah ya karba mana; mu da ku).
Kuma sunnah ne, yin kabbarori mudlakai, a daren idi, da
bayan salloli, har zuwa faduwar ranar yinin idi. Kuma SIFAR KABBARAR
ITACE:
ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL
HAMDU.
Kuma SIFAR SALLAR IDI ita ce Raka'oi biyu gabanin
yin huduba, zai yi kabbarori shida a raka'ar farko, bayan kabbarar harama.
A raka'a ta biyu kuma gabanin fara karatu, sai ya yi
kabbarori biyar, kari akan kabbarar tasowa.
No comments:
Post a Comment