SHA’ABAN WATAN DAGA AYYUKAN BAYI NA
SHEKARA GA UBANGIJIN TALIKAI
فضائل شعبان
Watan Rajab ya shude, Sai Sha’aban ya fiskanto
Kuma an sanya masa suna SHA’ABAN ne, saboda yadda kabilu ke
yin kungiya-kungiya domin fita yaki da kai farmaki, bayan ficewan watan Rajab Mai
alfarma (wanda ba a yaki cikinsa).
Sha’aban, Me ya sanar da kai abinda ake kiransa: WATAN
SHA’ABAN?
Wata ne na yi tanadi da shiri ga watan Ramadhana,
Watan yawaita azumi ne (nafila), da tilawar Alkur’ani; domin Annabi
–sallal lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yawaita azumi a cikinsa, saboda
wata ne da mutane ke gafala akansa, kuma shine watan da ake daga ayyukan bayi
na tsawon shekara; gaba dayansu; Usamah bn Zaid –radiyal Lahu anhu- yana cewa:
“NACE: YA MANZON
ALLAH, BAN GA KANA AZUMTAR WANI WATA BA, IRIN YADDA KAKE AZUMTAR WATAN
SHA’ABAN, SAI YA CE: SABODA SHI, WATA NE DA MUTANE KE GAFALA AKANSA, DA KE
TSAKANIN RAJAB, DA WATAN RAMADHANA, KUMA SHINE WATAN DA AKE DAGA AYYUKAN BAYI
GA UBANGIJIN TALIKAI; SAI NAKE SON A DAGA AIKINA GARE SHI ALHALIN INA AZUMI”.
Ibnul
kayyim -rahimahulLahu- yace:
“LALLAI AYYUKAN SHEKARA ANA DAGA SU ZUWA GA ALLAH NE A CIKIN
WATAN SHA’ABAN”.
Kuma Magabatan kwarai sun kasance, suna yawaita karatun
Alkur’ani a cikin watan Sha’aban, domin a cikinsu akwai wadanda suke rufe
shagunansu domin su shagaltu da yawaita karatun Alkur’ani;
Salamah bn Kuhailin yana cewa:
“ANA FADIN CEWA: WATAN SHA’ABAN, WATAN MASU KARATUN KUR’ANI
NE”.
Kuma Magabatan kwarai sun kasance suna kwadayin taimakon
miskini a cikin watan Sha’aban, domin ya fiskanci watan Ramadhana da abinda zai
jiyar da iyalansa da ‘ya’yansa dadi; domin an ruwaito daga wasu daga cikin
magabantan kwarai cewa, sun kasance idan watan Sha’aban ya shigo, sai su fitar
da zakkar dukiyarsu, domin su karfafa wa mai rauni da miskini, akan azumtar
watan Ramadhana.
Kuma a cikin watan Sha’aban akwai sabar wa Rai, da shirya ta,
saboda ta iya fiskantar watan Ramdhana da mafificin zantuka da kuma ayyuka.
No comments:
Post a Comment