ABABEN DA BASU KARYA AZUMI
(ما لا يُفطِّر)
Lamura
dayawa ne Mai yin azumi ke bukatar amfani da su, Kuma zai iya zaton cewa, suna
karya azumi, amma ba haka lamarin ya ke ba;
Misalinsu,
shine
KURKURAN
BAKI, DA SHAKA-RUWA A HANCI, ba tare da zurfafawa ba.
DA SANYA KWALLI. DA 'DAN'DANAR
ABINCI, Idan akwai bukatar hakan.
Daga
cikinsu, akwai TONAN HAKORA, DA CIRE HAKORA, DA TSAFTACE SU, da aswaki
ne, ko brosh, tare da kiyaye isar makilin cikin makoshi. Tare da cewa, abinda
yafi tsantseni dangane da lamarin makilin shine yin amfani da shi, da dare.
Kuma daga
cikinsu, akwai ABIN WANKE KUNNE, DA ISKAR DA AKE FESAWA DOMIN MAGANIN ASMA
KO MATSALAR NUMFASHI (INHELA), DA KWAYOYIN MAGANI, WADANDA AKE IJIYE SU
KARKASHIN HARSHE, DOMIN SU BADA KARIYA KAN MATSALOLIN CIYON ZUCIYA. DA KUMA
ISKAR DA AKE MAGANIN WASU MATSALOLI DA SUKE CIKIN BAKI. Saidai haramun ne
mutum ya yi gangancin hadiye wani abu daga cikin abinda ya gabata, ko
isar da shi ga
makoshi.
HAKA
SUMA ABABEN DA AKE SANYA SU A CIKIN MAHAIFA DOMIN YIN MAGANI KO WANKI A GARE
SHI, DA MAKAMANCIN HAKA (BASU KARYA AZUMI), HAKA SUMA ALLURAI DON MAGANI GA
FATA KO JIJIYOYI, in banda alluran da suke dauke da abinci, wadannan su kam
suna karya azumi.
Haka
ababen da suke shiga cikin jiki, TA HANYAR FATAR JIKIN TA TSOTSE SU, Kamar
nau'ukan mayi, da sauran ababen shafawa, da mannawa na magani, da shigar da NA'URAR
GANIN MATSALAR DA TAKE CIKIN CIKI, TA HANYAR FATAR CIKI, KO TA CIKIN TUMBI, MATUKAR
BA A HADA DIRIB NA RUWA KO WASU SINADARAN NA DABAN BA.
Hakika Allah ya saukake mana addininsa,
sa'annan ya dauke duk wani abu mai sanya kunci, Kuma Annabinmu –sallal Lahu
alaihi wa sallama- ya yi gaskiya cikin fadinSa:
((بُعثتُ بالحنيفية السَّمْحة)).
Ma'ana: "An turo ni da
mikakken addini, mai sauki".
No comments:
Post a Comment