2019/10/16

SHIRYA MAMACI DA YI MASA SALLAH DA KUMA BUNNE SHI Shehun Malami Abdul'aziz dan Abdullahi Bn Baaz


SHIRYA MAMACI DA YI MASA SALLAH DA KUMA BUNNE SHI.

Na
Shehun Malami Abdul'aziz dan Abdullahi Bn Baaz


Tarjamar
Abubakar Hamza

Ga bayanin mas'alolin filla-filla kamar haka:
Na farko: An so a rika lakkanawa mai mutuwa  kalmar La ila illal Lahu; saboda fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare Shi: "ku lakkanawa mamatanku kalmar la ilaha illalLahu".
Abinda aka nufa da mamata a nan su ne: wadanda alamun mutuwa suka bayyana tare da su.
Na biyu: Idan aka tabbatar da mutuwarsa sai a rufe idanunsa, a daure gemunsa, kamar yadda sunna ta zo da shi.
Na uku: Wajibi ne a yi wanka ga Musulmin da ya mutu, matukar ba shahidin da ya mutu a wurin yaki ba ne, saboda  shahidin yaki ba a yi masa wanka, ba a yi masa sallah, haka ake rufe shi a cikin kayansa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi bai wanke wadanda suka yi shahada a yakin uhudu ba, haka bai yi musu sallah ba.
Na hudu: Sifar wankar  gawa:
Za a suturce wa mamaci al'aurarsa, sannan a daga shi kadan, sai a tatse cikinsa a hankali, sai wanda zai yi masa wankan ya daura kyalle ko makamancisa a hannunsa, sai ya masa tsarki da shi, daga nan sai ya masa al'walar sallah, sannan ya wanke masa kansa da gemunsa da ruwa da kuma magarya, ko makamancinta, sannan sai ya wanke bangaren damarsa, sannan sai bangaren hagu. Zai masa hakan har sau uku, a kowanne wanka zai bi da hannunsa ta cikinsa yana dan dannawa kadan-kadan, idan wani abu ya fito ya wanke shi. Sai kuma ya toshe duburarsa da auduga ko makamacinta, idan abin bai dena fitowa ba, sai ya toshe da tabon kasa, ko kuma ayi amfani da hanyoyin likitanci na zamani kamar sanya gam, ko plaster ko makamancinsa.
Sannan ya sake masa alwala. Idan aka masa wanka sau uku, sai bai fita ba, to sai a kara adadin zuwa biyar ko bakwai. Sa'annan a tsane shi da tawul. Sannan a shafa masa turare a hamatarsa da matsematsinsa da makamantansu, da kuma guraben sujaddarsa. Da za a shafe gaba dayan jikin mamacin da turare to hakan shi ne yafi. Kuma an so a kunna turaren wuta a gaba dayan likafaninsa. Idan gashin bakinsa ko faratansa sun yi tsawo dayawa sai a rage su, idan kuma aka bar su haka shima babu laifi. Ba zai taje masa kai ba, ko ya aske masa mara ko ya yi masa kaciya ba, domin babu dalilin da ya yi nuni akan hakan. Mace kuma za a yi mata kitso ne (yawo) guda uku daga goshinta su yi bayanta.
Na biyar: Sanya wa mamaci Likkafani:
Abinda aka fi so shi ne: a yi likkafani wa mamaci namiji acikin tufafi guda uku farare, ba tare da anyi masa Riga ko Rawani ba; kamar yadda aka yi wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a  saka shi a cikinsu shigarwa. Idan kuma aka masa likkafani  da Riga da Izari da Mayafi; to babu laifi.
Mace kuma ana sanyata  a cikin Likkafani biyar: Riga, da Zani, da dan kwali, sai kuma Mayafai biyu.
Yaro, ana masa likkafani cikin tufafi daya zuwa uku. Karamar yarinya kuma, cikin riga daya mayafai biyu.
Likkafani daya wadatacce wanda zai rufe jiki gaba daya; shi ne wajibi ga mace ko namiji.
Amma idan mamacin ya dauki harama da umrah ko hajji sai ya rasu; to za a yi masa wanka ne da ruwa da magarya, sannan a lullube shi a cikin ihramansa ko wasunsu, baza a rufe kansa ko fuskarsa ba, ba za a sanya masa turare ba; domin za a tashe shi ranar alkiyama yana yin Talbiyya (wato yana cewa: labbaikallLahumma labbaik), kamar yadda haidisi ingantacce ya zo daga Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Amma idan maniyyaciya ce, -wato- mace ce, to za a shirya ta ne kamar ba maniyyaciya ba, sai dai itama ba za a sanya mata turare ba, baza a rufe fuskarta da nikabi ba, ba za a sanya mata safar hannu ba, za a rufe fuskarta da hannayenta da likkafaninta ne kadai, kamar yadda bayanin ya gabata, a sifar yadda ake sanya wa Mace likkafani.
Na shida: Wanda ya fi kowa cancantar wanke mamaci namiji, da kuma yi masa sallah da rufe shi, shi ne wanda mamacin ya yi wasici da shi, sannan sai mahaifi, sai kaka, haka za a yi ta duba wanda ya fi kusa da shi a cikin magadansa.
Wadda kuwa tafi cancantar wanke Mace ita ce wadda ta yi wasici da ita, sa'annan sai mahaifiyarta, sai kakarta, sannan wadda ta fi kusanci da ita a cikin mata.
Kowanne daya daga cikin ma'aurata zai iya wanke dan'uwansa, (wato miji ya wanke matarsa, ko ita ta wanke shi); domin sayyidina Abubakar Assidik matarsa (Asma'u bnt Umais) ce ta wanke shi. Shi kuma sayidina Aliyu shine ya wanke matarsa –wato, Fatima, Allah ya kara yarda a gare ta.
Na bakwai: Sifar sallar gawa: za a yi kabbara hudu ne, a kabbara ta farko ana karanta Fatiha, idan aka kara da gajeriyar sura ko aya daya ko biyu ya yi kyau, saboda ingantaccen hadisin da ya zo daga Abdullahi dan Abbas a kan hakan. A kabbara ta biyu kuma sai a yi salati ga Annabi Muhammadu kamar yadda ake yi a Tahiya (salatin ibrahimiyya). Sai ayi kabbara ta uku, a ita ne ake yin addu'a kamar haka:
"Ya Allah Ka gafarta wa wadanda suke raye aciknmu da matattunmu, da wadanda suke nan da wadanda basu nan, da manyanmu da kanananmu, Mazanmu da Matanmu. Ya Allah wanda ka rayar da shi a cikinmu to Ka rayar da shi akan tafarkin musulumci, wanda kuwa Ka karbi rayuwarsa to Ka karbe ta akan Imani. Ya Allah Ka gafarta masa Ka ji kansa, Ka ba shi lafiya Ka yi masa rangwame, Ka kyautata masaukinsa, Ka yalwata mashigarsa, Ka wanke shi da Ruwa da kankara da kuma Raba, Ka tsarka ke shi daga kurakurensa kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga kazanta, Ka canza masa gida mafi alheri daga gidansa, da iyali mafiya alheri daga nasa, Ka shigar da shi Aljannah, ka tsare shi daga azabar kabari da azabar wuta, ka yalwata masa kabarinsa Ka haskaka masa shi, ya Allah kada Ka haramta mana ladansa, kada kuma Ka batar da mu a bayansa.
Sannan sai ya yi kabbara ta hudu, ya yi sallama daya bayanta a hannun dama. Kuma anso a daga hannaye  a kowacce kabbara.
Idan kuma gawar mace ce sai a yi anfani da lamirin mata, a ce: ya Allah Ka gafarta mata ….har zuwa karshe), idan kuma Mutum sama da daya ne sai a ce: (Ya Allah Ka gafarta musu….. har zuwa karshe).
Idan gawar yaro ce, sai a ce: (Ya Allah ka sanya shi ya zama marigayi kuma taska ga iyayensa, kuma mai ceto abin amsawa. Ya Allah! Ka nauyaya ma'auninsu da shi, Ka girmama ladansu da shi, Ka riskar da shi ga mummunai magabata nagari, Ka sanya shi karkashin rainon Annabi Ibrahim tsira da aminci su tabbata a gare shi, Ka kare shi daga azabar jahimu da rahamarka.
            Sunnah -a yayin sallah- ita ce: limamin ya tsaya daura da kan mamaci Namiji, Mace kuma a tsakiyarta, idan kuma mamatan sun hada da Maza da Mata, to namiji zai zamto yana bin liman ne –wato daga liman sai gawar Namiji-, ita kuma Mace tana bin alkibla. idan kuma a kwai gawar yara sai Namiji babba ya zanto shi ne kusa da liman, sai karamin yaro, sai babbar Mace, sai karamar yarinya. Kai na karamin yaron zai zamto a saitin kan gawar babban Mutum, tsakiyar babbar Mace kuma a saitin kawukansu. Haka nan karamar yarinya kanta zai zamto a setin kan babbar Mace, itama zai zamto a tsakiyarta tana dai-dai da kan Namiji;
Su kuma sauran Masallata za su zamto gaba dayansu a bayan liman, saidai wanda bai samu wuri a  bayan liman ba, sai ya tsaya kusa da shi a hannunsa na dama.
Na takwas: Sifar bunne mamaci: Abinda aka shar'anta shi ne zurfafa kabari gwargwadon yadda zai kai kwankwason Mutum, sannan Lahadu din ya zama a bangaren alkibla –za a tona shi-, kuma za a saka Mamacin ne ta bangaren damarsa, sai a warware kullin likafanin, ba janye zaren za a yi ba, kuma ba za a bude fuskarsa ba; Namiji ne ko Mace, daga nan sai a sanya tubala a daure shi da kwababbiyar laka; domin kada kasa ta shiga cikin kabarin. Idan kuma ba a sami Tubali ba sai ayi amfani da katanga/kasko, ko duwatsu, ko itace wanda zai iya hana kasa shiga cikin kabarin, sannan sai a tura turbaya a kai. An so yayin saka gawar a kabarinta a ce: Bismillah wa ala millati Rasulillah. Kuma za a daga kabarin gwargwado taqi daya, in an sami dama sai a dora dan dutse a kai, sai kuma a yayyafa ruwa a samansa.
Abin da aka shar'anta wa wadanda suka raka gawa shi ne: mikewa tsaye a makarbarta bayan rufe mamacin don su yi masa addu’a, saboda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ya kasance yana mikewa tsaye ne idan aka gama rufe gawa sannan ya ce: "ku nema wa dan'uwanku gafara, ku roka masa tabbatuwa, domin a halin yanzu za a masa tambayoyi".
Na tara:  Shari'a ta yarda ga wanda bai samu damar yi masa sallah ba ya yi masa bayan rufe shi da kimanin wata daya kawai, domin Annabi SAW ya aikata hakan,. Amma idan aka haura wata daya to bai halatta ayi sallah a makabarta ba, saboda rashin dalilin dake nuni cewa Annabi SAW ya aikata hakan bayan wata daya da rufe gawa.
Na goma: Haramun ne wadanda aka yiwa mutuwa su yi wa Mutane abinci, saboda hadisin Jarir dan Abdullahi Albajaliy -Allah ya yarda da shi- ya ce: (Mun kasance muna kirga taruwa a gidan wanda dan'uwansu ya rasu, da kuma yin abinci bayan rufe gawa daga cikin kururuwar Mutuwa).
Amma su yi abinci don su ci, ko su baiwa bakinsu babu laifi. Kuma an shar'anta wa yan'uwa da makwabta su yi musu abinci, saboda lokacin da labarin kashe Ja'afar dan Abi Talib ya zowa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi sai ya umurci iyalansa da su shirya abinci ga mutanen gidan Ja'afar, ya ce: “Hakika abinda zai shagaltar da su ya same su”.
Babu laifi idan yan'uwan mamaci suka kira makwabtansu ko wasu domin cin abincin da aka kawo musu kyautarsa. Kuma wannan bashi da wani kayyadajjen lokaci a iyakar saninmu da shari'a.
Na sha daya: Bai halatta Mace ta yi takabar sama da kwana uku ga wani mamaci ba, face ga Mijinta, shi kam wajibi ne ta yi masa takabar wata hudu da kwana goma, sai in ya barta da ciki, sai takabar ta zama zuwa haihuwarta, saboda zuwan ingantattun hadisai daga Annabi Muhammadu SAW akan hakan.
Namiji kuwa haramun ne ya yi takaba ga wani mamaci dan'uwansa ne ko ba dan'uwansa ba.
Na sha biyu: An shar'anta wa Maza ziyartar makabartai, lokaci bayan lokaci; domin yiwa mamatan addu'a, da nema musu rahama, da kuma tuna mutuwa da abinda zai zo bayan mutuwar, saboda fadin Manzon Allah: "Ku rika ziyartar makabartai; domin suna tunatar da ku Lahira".
Kuma Manzo Allah ya kasance yana koya wa sahabbansa addu'ar ziyartar makabartai kamar haka: "Amincin Allah ya tabbata a gare ku, Ya ku ma'abuta wannan gida daga Muminai da Musulmai, mu ma za mu riske ku in Allah Ya yarda, Allah ya ba mu lafiya mu da ku. Allah ya gafarta wa wadanda suka rigaye mu da jimawa da mutuwa, har da wadanda basu jima ba".
Mata kuma basu yin ziyarar makabartai saboda Manzon Allah ya la'anci mata masu yawan ziyartar makabarta, kuma saboda tsoron fitina da gajen hakuri idan suka yi ziyarar.
Haka nan baya halatta ga Mata su raka gawa zuwa makabarta ba, saboda Annabi ya hana su, amma yi wa mamaci sallah a cikin masallaci ko a waje halal ne ga maza da mata.
            Wannan shi ne karshen abin da ya sauwaka.
Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabinmu (Muhammad) da mutan gidansa da sahabbansa.

2019/10/15

Sifar Umrah da hajji Shehin Malami Muhammadu dan Salih AlUsaimin

Sifar Umrah da hajji

Sheikh Ibn Usaimin –Allah ya yi masa rahama- ya ce:

Idan kuka iso mikati, sai ku yi wanka, ku sanya turare a jikinku, kamar kai, gemu, sannan ku yi harama da umrah, da nufin yin tamattu'i ku tafi zuwa garin Makkah kuna yin LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIK…. Idan Kuka isa daki mai alfarma, ku yi dawafi sau bakwai, a matsayin dawafin umrah. Kuma ku sani, gaba dayan Masallacin wuri ne na dawafi; kusa ne da dakin Ka'aban ko nesa, saidai kusantar ka'aban shine yafi falala; matukar ba za ka cutu da cunkoso ba. Amma idan akwai cunkoso, to ka tafi nesa da dakin, al'amarin yana da fadi, Wa lilLahil hamd. Idan kuka kammala dawafi, to ku yi raka'oi biyu a bayan makamu Ibrahima –AS-, ko ta kusa da shi, idan an samu damar hakan, idan kuma ba a samu ba, to koda nesa ne da shi, kawai dai Makamu Ibrahima ya kasance a tsakaninku da tsakanin ka'abah. Sai ku fita zuwa ga sa'ayin umrah a tsakanin Safah da Marwah, ku fara da dutsen Safah, idan kuka kammala zagaye bakwai, sai ku rage gashin kanku ta dukkan kan, domin rage shi ta gefe daya baya wadatarwa, kuma kada ku rudu da aikin Mutane dayawa
Idan ranar takwas ga watan zulhijjah ta zo, sai ku yi wanka, ku sanya turare, ku yi harama da hajji, daga masaukanku. Ku fita zuwa ga Minah, ku yi sallar azahar, La'asar, Magriba, Isha'i, da asuba. Kuna masu kasaru, ba tare da kun hade salloli biyu ba; saboda Annabinku ya kasance yana yin kasarun salloli a Minah da Makkah, amma baya hada su. Idan rana ta fudo a ranarArafah, sai ku tafi, kuna yin Talbiyyah cikin kankan da-kai ga Allah, zuwa ga filin Arafah. Sai ku hade sallolin Azahar da La'asar a Arafah a lokacin azahar (jam'u takdim), kuma raka'oi bibbiyu ga kowacce.
Sannan ku shagaltu da addu'a da marairaice wa Allah, kuma ku yi kwadayin kasancewa cikin tsarki (da alwala), ku fiskanci alkibla, koda dutsen Arafah ya kasance ta bayanku; domin abinda aka shar'anta shine fiskantar alkiblah, kuma ku kula sosai da iyakokin Arafah da alamominta, sai ku kasance a cikinta, domin Mahajjata dayawa suna tsayawa ba a cikinta ba, kuma duk wanda bai samu Arafah ba, to bashi da hajji, saboda fadin Annabinmu  : "Hajji shine Arafah". Kuma matukar ka tsaya a farfajiyar Arafah, ta gabas ne ko ta yamma, ko ta kudunta ko ta arewa, to hakan ya yi, in banda Badanul wadiy (Wadiy Uranah); saboda fadin Annabi : "Na tsaya a nan, kuma Arafah dukkanta wurin tsayuwa ne".
Idan rana ta fadi, kuka tabbatar ta fadin, sai ku tafi zuwa ga Muzdalifah kuna masu Talbiyah da kankan da-kai ga Allah. Kuma ku lazimci natsuwa, gwargwadon iko, kamar yadda Annabinku ya umurce ku da aikata hakan, saboda ya fito daga Arafah alhalin yana jan linzamin rakumarsa baya, har kanta yana kokarin taba jikin tudun sirdi, alhalin yana fada da hannunsa mai karamci: "Ya ku Mutane! Abi a hankali, a tafi a natse".
Idan kuka iso farfajiyar Muzdalifah, ku yi sallar Magriba da Isha'i, sai ku yi barci har asubah. Kuma Annabi bai yi rangwame ga wani ya bar Muzdalifa ba, sai ga Mutane masu rauni; su kam ya musu rangwamen su tafi a karshen dare. Idan kuka yi sallar asuba, sai ku fiskanci alkiblah, kuna masu kabbara da gode masa, da yin addu'oi, har haske ya bayyana sosai, sai ku tafi gabanin fudowar rana, zuwa minah. Sannan ku tsinci duwatsu guda bakwai, ku tafi zuwa ga Babbar Jamrah wanda itace ta karshe, ta bangaren Makkah, Sai ku jefe ta, bayan fudowar rana, da duwatsu guda bakwai, kuna masu yin kabbara Allahu Akbar tare da kowane dutse, kuna masu kankan da-kai a gare shi, kuna girmama shi. Kuma ku sani lallai makasudin jifan shine girmama Allah, da tsayar da ambatonsa. Kuma wajibi ne dutsen ya fada cikin kewayen, amma ba sharadi ba ne, ya bugi ginshikin.
Idan kuka gama jifan duwatsun, sai ku yanka hadaya, kuma bata isarwa ga al'amarin hadaya; sai dabbar da take isarwa ga layya, kuma babu laifi ka wakilta wani ya yanka maka. Sannan bayan kun yi yanka, sai ku aske gashinku, kuma wajibi ne ku aske dukkan gashin, kuma baya halatta ku aske sashensa ku bar sashe. Mace kuma zata rage gashinta ta kowace kusurwa daga kanta gwargwadon kan 'yar yatsa.
Bayan haka, kun yi abinda ake kiransa tahallulul Awwal, sai ku sanya tufafinku, ku yanke farcenku, ku sanya turarenku, amma ba za ku sadu da matanku ba. Sa'annan sai ku sauka gabanin sallar azahar zuwa cikin Makkah domin yin dawafin hajji, kuma ku yi sa'ayi tsakanin Safah da Marwah. Sa'annan ku koma Minah. Kuma da yin dawafi, da aikata sa'ayi, tare da jifan Shedan da aski, to kun samu abinda ake kiransa: Tahallulus Saniy, kuma komai ya halatta a gare ku, har kwanciya da Matanku.
Ya ku Mutane! Lallai Mahajjaci a ranar idi yana aikata ayyuka ne guda hudu: Jifan jamrah, sa'annan yanka, sa'annan aski, sa'annan dawafi da sa'ayi. Wannan kuma shine jearanta ayyukan, wanda yafi falala. Saidai idan mutum ya gabatar da wani akan wani, sai kuka yi aski gabanin yanka ga misali, to babu komai. Kuma da za ku jinkirta dawafi da sa'ayi, har sai kun dawo garin Makkah daga Minah, to babu komai. Kuma da za ku jinkirta yanka zuwa ranar goma sha uku, sai ku yi shi a garin Makkah, babu komai, musamman idan akwai bukatar hakan, da maslaha. Ku kwana daren goma sha daya 11 a Minah. Idan Rana ta yi zawali (lokacin azahar) sai ku yi jifa jamraat guda uku, ku fara da jamrah ta farko, sa'annan ta biyu, sannan ta karshe; wato akabah, kowane daya da tsakuwa guda bakwai, za ku rika yin kabbara (Allahu Akbar), tare da kowace tsakuwa. Lokacin jifa, a ranar idi, ga mai iko (lafiyayye), daga fudowar Rana ne, Mai rauni kuma tun daga karshen dare ne. Karshen lokacin kuma zuwa faduwar rana. Lokacinsa kuma a sauran kwanakin (bayan idi), daga zawali ne, zuwa faduwar Rana. Amma baya halatta a yi jifan gabanin zawali. Kuma ya halatta ayi jifan a cikin dare, idan akwai cunkoso mai tsanani, a cikin yini. Wanda ba zai iya jifa ba, ko saboda kasancewarsa karami, ko tsufa, ko cuta, to yana da damar ya wakilta wanda zai masa jifan. Kuma babu laifi, wakilin ya yi jifa wa kansa, da wanda yake wakilta a tsayuwa daya, saidai zai fara jifa ga kansa. . Idan kuka yi jifan ranar sha biyu 12, to lallai hajji ya kare, Kuma kuna da zabi kan dawowa Makkah, ko kuma ku sake kwana a Minah zuwa yini na 13domin ku sake jifan, bayan Azahar ga wuraren jifan guda uku; Wannan kuma shine yafi, saboda shine aikin Annabi  .
Idan kuka so ku bar garin Makkah, Sai ku yi Dawafin bankwana. Saidai babu dawafin ga Mai haila da kuma mai jinin haihuwa (nifasi), kuma ba shar'anta musu zuwa jikin kofar Masallaci da tsayuwa a wurinsa ba .

2019/10/10

نفع البرايا من خير السجايا صلاح البدير 12 صفر 1441 Amfanar da Halittu







HUƊUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/SAFAR/1441H
daidai da 11/OCTOBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUƊUBA
SHEIKH DR. SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA

AMFANAR DA HALITTU YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI
(نفع البرايا من خير السجايا)
Shehin Malami wato: Salah ɗan Muhammadu  Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi huɗubar juma'a mai taken: AMFANAR DA HALITTU YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUƊUBAR FARKO
        Ya ku Musulmai
Amfanar da Halittu yana cikin mafi alherin sifofi,
MAFI ALHERIN RANAKUN MUTUM SHINE YININ DA YA AMFANAR
AIKATA ALHERI KUMA SHINE MAFI WANZUWAR ABINDA YA AIKATA
Kuma Mai yawan amfanarwa mai taimako shine: Wanda ya amfanar da Mutane da dukiyarsa, da matsayinsa, da iliminsa, da ɗabi'unsa, da kyautatawarsa, Mai gwaɓin alheri, mai kyauta dayawa, mai amfani cikin aikinsa. mai faffaɗar tukunya, tafinsa kamar girgije, yana dawwama akan sada zumunci da kyauta da sadaƙoƙi, yana tallafawa gajiyayye, yana falala ga mai neman falala, yana tsamar da mai neman agaji da taimako, yana ilmantar da jahilin dake neman shiryarwa, yana jin-ƙan maraya, yana share hawayen mai baƙin ciki, yana hulɗa da Mutane, cikin so, da kyautatawa, da taushi
MUTANE SUNA CINCIRINDO A ƘOFAR GIDANSA
DADDAƊAR MASHAYA, TANA DA YAWAN CUNKOSO

TSUNTSU YANA SAUKA A WURIN DA KWAYA TAKE WATSUWA
KUMA ANA KAI-KOMO A GIDAJEN MASU KARAMCI

Annabin Allah Isah –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Kuma ya sanya ni mai albarka a duk inda na kasance" [Maryam: 31].
Malaman tafsiri suka ce, wato Allah ya sanya ni Na zama mai yawan amfanarwa, a duk inda na fiskanta, mai biyan buƙatu, mai karantar da alkhairi, mai umurni da kyakkyawa, mai hani ga mummuna, mai albarka da nau'oin albarkoki.
Kuma Mutumin da yafi dukkan halitta amfanar da halittu shine Annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- " … abinda ke wahalar da ku yana masa nauyi, Mai kwaɗayi ne akanku, kuma ga muminai Mai tausayi ne Mai jin ƙai" [Taubah: 128].
BAN TAƁA GANI, KO NA JI LABARIN WANI A CIKIN MUTANE
GABA DAYANSU, KAMAR ANNABI MUHAMMADU BA

Kuma duk wanda ya kafa kansa domin amfanar da Mutane, sai ya rayu a gaba-gaba ana girmama shi, fiskarsa abar mutuntawa,
YABONSA DA DAƊI A BAKUNAN MUTANE
KUMA YABON YA KASANCE A KOWANE WURI
Matsayinsa zai ɗaukaka, ambatonsa kuma ya yi daɗi
DA ZAKA RIƘA BAYARWA A LOKACIN DA AKE ROƘONKA
SAI RANKA TA KOYI BAYARWAR, KUMA KOWANE MASOYI YA JI DAƊINKA

Ana cewa, Cikar hankali, da kyakkyawan ambato basu cika haɗuwa ga Mutum ɗaya ba.
Wani kuma ya ce: Hana kyauta, munana zato ne ga Allah abin bauta.
BATA TOZARTA BA, DUKIYAR DA TA GADAR WA MA'ABUTANTA SAMUN YABO
SAIDAI DUKIYAR MAROWACI ITACE, TA TOZARTA

Wasu Mutane babu abin tatsa ga hantsarsu, kuma ba a kwaɗayin samun amfaninsu,
MUTUM, MATUƘAR ZAMANSA BAI AMFANAR BA
TO GIRGIJE NE WANDA RANA TA TARE, BAI ZUBO DA RUWA BA, KUMA BAI TAFI BA
Wasu Mutane namijin dabino ne; babu abin tsinka daga gare su, kuma basu da inuwa, sai idan kai nasu ne.
Sai ka kasance, ga halittun Allah mai yawan amfanarwa, mai amsa wa mabuƙata, kuma ka miƙar da tafin hannunka domin bada alheri miƙarwa.
An ruwaito daga Abu-hurairata –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherinku daga mafi sharrinku ba? Sai Wani Mutum ya ce: E, ka bamu labarin Ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa, ake aminta daga sharrinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba a fatan alherinsa, kuma ba a aminta daga sharrinsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar –رضي الله عنهما- daga Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Mafi soyuwan Mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar da Mutane. Kuma mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da ɗaukaka shine farin cikin da ka shigar da shi zuciyar Musulmi, ko ya yaye masa baƙin ciki, ko ya biya masa bashi, ko ka kawar masa da yunwa, kuma wallahi na yi tafiya tare da ɗan'uwana Musulmi cikin buƙatarsa, yafi soyuwa a wurina fiye da na yi i'itikafi a wannan Masallacin, wato Masallacin Madina- na tsawon wata guda", Ɗabaraniy ya ruwaito shi a mu'ujamul Ausad.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairata -رضي الله عنه- lallai shi ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya kwaranye wa Musulmi wani baƙin cikin Duniya, Allah zai kwaranye masa baƙin cikin yinin ƙiyama. Kuma wanda ya sauƙaƙa wa Mutumin da yake cikin wahala, to Allah zai sauƙaƙa masa a Duniya da Lahira. Kuma wanda ya rufa asirin Musulmi a Duniya, Allah zai rufa asirinsa a Duniya da Lahira, Allah yana taimakon Bawa matuƙar Bawan yana taimakon ɗan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Nawawiy ya ce: "A cikin hadisin, akwai falalar biya wa Musulmai buƙatu, da amfanar da su da abinda ya sauƙaƙa, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko shawari a cikin wata maslaha, ko nasiha, da makamancin haka".
KA BIYA BUƘATU GWARGWADON IKO,
KUMA KA KASANCE MAI YAYE BAƘIN CIKI GA ƊAN'UWANKA

DOMIN MAFI ALHERIN KWANAKIN MUTUM SHINE
YININ DA YA BIYA WA WADANSU BUƘATU

Ya kai Bawan Allah!!!
Ka bayar da kyauta, ka riƙa amsa wa wanda yake cikin baƙin ciki, kuma kada ka raina abin da zaka yi kyauta da shi, kada ka ga karancin hidimar da zaka gabatar, domin ƙananan ayyukan sharri, mai aikata su zai same su a halarce dalla-dalla. haka kwayar zarra na alheri, wanda ya aikata ta zai same ta a cike, a ajiye.
An ruwaito daga Abu Jaryin Alhujaimiy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kada ka raina kyakkyawan abu; ka ki aikata shi, koda ka bada kyautar kulla igiya ne, kuma koda ka ɗiba daga gugarka zuwa ga kwaryar wanda ya nemi shayarwa ne, kuma koda ka haɗu da ɗan'uwanka Musulmi alhalin fiskarka tana shumfuɗe (kana murmushi) a gare shi, kuma koda ka ɗebe kewa ga wanda ke cikinta ne da kanka, ko kuma ka bayar da kyautar igiyar takalmi", Ahmad da Abu-dawud da Nasa'iy suka ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Jabir ɗan Abdullahi –رضي الله عنه- ya ce: Wata kunama ta harbi wani daga cikinmu, alhalin muna zaune tare da Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai wani Mutum ya ce: Ya Ma'aikin Allah, shin ba zan masa addu'ar ruƙiyya ba? Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Duk wanda ya samu damar ya amfanar da ɗan'uwansa to ya aikata", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, kada ka hana kyautarka, kada ka riƙe falalarka, kada ka killace alherinka, kada ka yi rowa, kada ka nuna ƙosawa, kada ka nuna takura ga mai roƙon da talauci ya buƙatar da shi ga roƙo, ka bashi koda kaɗan ne, ko ka mayar da shi da kyakkyawiyar magana, kada ka haɗa masa zafin talauci da ƙasƙancin dake cikin roƙo da kausasa harshe da jafa'i.
Kuma alƙawarin tallafin karimi faɗa ne da cikawa.
Shi kuma Marowaci alƙawarinsa jinkiri ne, da lalubo uzuri.
Kuma bada uzuri da laffuza masu kyawu shi yafi alheri fiye da jinkirtarwa mai tsawo.
Idan ka yi nufin ni'ima to ka zartar, idan kuma buƙatar ba za ta samu ba, to ka yi bayani a fili.
An ruwaito daga Abdullahi ɗan Amru –رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Allah, a wurin wasu Mutane, yana da ni'imomin da ya tabbatar da su a wurinsu –wato: ya dawwamar musu da su- matuƙar suna cikin buƙatun Musulmai; basu ƙosa daga gare su ba. To amma idan suka ƙosa daga biya musu buƙatu, sai Allah ya ɗauke ni'imomin zuwa ga wasunsu", Ɗabaraniy, a cikin mu'ujamul kabir ya ruwaito shi.
KA KYAUTATA MATUƘAR AKWAI DAMA DA IKO
DOMIN DAMAR, BA DOLE TA DAWWAMA GA MUTUM BA
Ina faɗar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi Mai yawan gafara.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUƊUBA TA BIYU
Ya ku Musulmai
Mustahabbi ne, yin ceto (ko sanya baki domin biya ma wani buƙata) a cikin al'amuran alheri, saboda amfanarwa ne ga Mutumin da aka nemi ceton dominsa.
Kuma idan Mutum ya yi ceto mai kyau, wanda yake fatan amfanarwa ga halittu, da biyan buƙatun Mutane, to lallai ya yi kyauta mai gwaɓi, kuma zai samu yabon Mutane.
An ruwaito daga Abu-Musal Ash'ariy –رضي الله عنه- ya ce: Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ya kasance, idan wani mai buƙata ya zo masa, sai ya fiskanci abokan zamansa, ya ce: "Ku yi ceto; zaku samu lada, Allah kuma zai hukunta abinda ya so ta harshen ManzonSa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
KA TAIMAKE SHI, KO DA MATSAYINKA NE, WANDA YA ZO MAKA DA WATA BUƘATA
DOMIN, KYAUTA DA MATSAYI, TAFI KYAUTAR DUKIYA
Imamus Shafi'iy –رحمه الله تعالى- ya ce: "sanya baki domin yin ceto, shine zakkar mutunci".
AN FARLANTA MINI FITAR DA ZAKKAR ABINDA HANUNA YA MALLAKA
SHI KUMA BADA ZAKKAR MATSAYINA SHINE, NA YI TAIMAKO, KUMA NA YI CETO

DON HAKA, IDAN KA MALLAKI ABU, TO KA YI KYAUTA,
IDAN KUMA BAKA SAMU IKO BA, TO KA YI IYA ƘOƘARINKA WAJEN GANIN KA AMFANAR
Wanda ya yi ceto, domin a kai ga wata ɗa'a, ko don samun sauƙi cikin abu mai wahala, ko janyo alheri, ko domin tunkuɗe wani sharri, ko domin sulhu tsakanin masu husuma biyu, ko domin kaiwar wanda ake masa ceton ga haƙƙinsa, to lallai, yana da rabo daga alherin ceton, da kuma ladanta.
Wanda kuma ya yi ceto, don a lalata wani haƙƙi, ko domin tabbatar da ɓarna, ko domin tabbatar da zalunci, ko domin a fifita wanda bai cancanta ba, akan wanda ya cancanta, ko domin a baiwa wanda bashi da kwarewa, a kuma daƙushe mai kwarewar, ko don bada aiki ga wanda aka nema masa ceto, a haramta shi ga  wanda ya fishi cancanta, to lallai yana da zunubin wannan ceto, mummuna, na zalunci.
Allah Mabuwayi da ɗaukaka ya ce: "Wanda ya yi ceto, ceto mai kyau, zai samu rabo daga gare shi. Wanda kuma ya yi ceto ceto mummuna, to zai samu rabo daga cikinsa" [Nisa'i: 85].
Kuma karɓar kyauta, sakamakon amfanar da wani da matsayinka ko saboda ceto, yana tozarta ladan ceton, kuma yana tafiyar da falalarta, don haka, kada ka yi gaggawar ladan cetonka, kuma ka bar ladan a matsayin guzurin Lahirarka.
Abdullahi ɗan Mas'ud –رضي الله عنه– ya ce: "Duk wanda ya yi ceto, domin a dawo da wani haƙƙi, ko domin ya ɗauke wani zalunci, sai aka masa kyauta, ya karɓa, to wannan suhut ne (haramun)".
Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah Albahiliy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi ceto ga ɗan'uwansa, sai aka ɗauko kyauta aka bashi akanta, to lallai haƙiƙa ya faɗa ta wata ƙofa daga ƙofofin riba", Ahmad da Abu-dawud suka ruwaito shi, saidai akwai magana akan ingancinsa, Amma wasu Maluman sun ce hadisi ne hasan.
SAI KU YI SALATI DA SALLAMA, GA MUHAMMADU MAI SHIRYAR DA HALITTU GABA ƊAYA
DOMIN IDAN MUTUM YA MASA SALATI GUDA ƊAYA, ALLAH ZAI NINKA MASA DA WANNAN HAR GUDA GOMA

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...